Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[12/15, 1:59 PM] Abu~ammar: *🕊️RAINON SOJA...!🕊️*




*#Through the gate of love a Valiant, fearless heroical and Sympathetic Story.*





Free Page 1



*Labari da Rubutawa daga:©Ayshatou Maman-teddy*
*December 02-12-2023 .....7:30am*



#Rainon soja#whispering of love💔#Book 1#chapter 1#hand salute 💃🏻#travelling .


Wata moto ce ke guda a tsakiyar ƙwalta inda babu gida gaba babu baya sai Falfalan dajin ALLAH.

Mota ce irin ta haya wanda yake dauke da mutane sun kai Goma zuwa goma sha biyu , kallo ɗaya zaka yi masu ka fahimci matafiya ne wanda suka fito daga cikin garin Zaria zasu iso Garin Abuja . Kowa hankalin sa yana akan hanya banda Mace Ɗaya wacce tun da suka shigo moton idanun ta ke tsiyayar da Ƙwallah, daga saman jikin ta kuma yarinya ce Wacce a shekaru ba zata Haura Ɗaya ba zuwa ɗaya da Rabi a Duniya . Tausayin yarinyar nata take jin yana ratsa ta haka zuciyar ta na kuka mata . Juyawa tayi tana kallon mai gidan nata wanda shima jimami ne da kuma tsoro fal a zuciyar sa. Hajara kina ganin idan muka je Muka koma a halin yanzu Ƴan uwan ki zasu amshe mu? Zasu amince da Auren namu a yanzu kuwa? Hajara ko zamu koma ne.....Ɗaga masa hannu tayi tana saurin riƙo hannun shi kamin cike da Raunanniyar murya ta fara cewa " A'a Salihu " kar ka ƙara furta hakan , yanda muka ƙudurci kawo Zahra dangina Don taga iyayen ta da kakanni a yau babu abun da zai fasu daga yin hakan sai kuma idan ƙaddara ta Gifta .

Ka janye Tsoro ka manta da komai nasan su ma a yanzu sun manta kuma kowa zai yafe mun inshallah. Fatan mu a yanzu shine Allah yasa mu sauka lafiya .

"Hummm" .

Sauke Ajiyar zuciya Salihu yayi kana yakai hannun shi yana ɗaukar ƙaramar yarinyar tasu yana daura ta bisa jikin sa . Ƙurrrr yayi mata da ido kamin yace " Wai Haihuwar ki ce aka ce mun ba alheri a rayuwa ta Zahra , Ni nasan Allah shine mai yin komai shine wanda yasan ƙaddara ba ɗan Adam ba. Ko ina raye ko ina a mace ina rokon ALLAH ya kare mun ke da kariyar sa. Shiru Hajara tayi tana kallon uba da ƴar wanda yake ji tamkar ya haɗa ta da jikin sa ya zamana babu wani abun cutarwar da zai iso gareta . Murmushi take bin su dashi kamin ta juya tana kallon dajikan da suke wucewa.

Kaman wanda aka ɗaga moton suka ji tayi sama tayar gaban ta yana fita fittttttt ji kake kwaltan da tayar suna fidda wani irin ƙugi ƙuuuuuuiiiiiiii nan take moton ta ɗaga tare da kifowa kif kaman wanda aka dirkake su . A dai dai kuma wannan sa'ilin da babu gida gaba babu gida baya ,sai falfalan dajin ALLAH . Yanda moton tayi ƙwatsa ƙwatsa jini na malala a tsakiyar titin ga hayaƙi dake tashi tamkar an kunna Masu fetur da ashana wurin yayi baƙiƙirin kai daga Ni kasan babu mutum ɗaya daga cikin moton nan da ya shura sai dai muce Allah yajiƙan wanda suka rigamu gidan Gaskiya 😢 .

**
Nigerian defence academy ( NDA)
#Nd 1 .
Yaran sojoji ne birjik a ƙame rana na dukan tsakiyar kan su , amma yanda wurin yayi shiru da yanda sukya a ƙame tamkar wanda ruwa yaci yacinye su . Mutumin dake daga nesa ba zai taɓa kawowa da akwai mutum ko ɗaya a wurin ba,bare kuma sojoji da sun haura 100 ɗari duka a layi . Kasancewar su Nd 1 yasa duka yawancin su yara ne matasa wanda daga secondary ne suka shigo , duk girman yaron dake wannan wuri babu guda ɗaya da ya haura 18 . Duka ƙasa da haka ne sai kuma 18 din , ciki har da masu 15 years yayan manyan kenan masu faɗa aji a ƙasa . Sune suke kawo yaran su tun da yarinta .

Cike da Wani irin ƙaraji tamkar zai tashi wurin da yaƙi Muryar Major ɗin su ya katse su yana furta " Hand salute! Daram dam dam....kaji takon su duka ya sauya suna juyawa ga Major ɗin a lokaci guda suna ɗaga yatsunsu tare da ƙamewa da ƙafafun su . Bin su da kallo yayi dukan su Sanye suke cikin t.shirt na sojoji sai wandon su mai ratsin tambarin su na soja.

Idanun Major Jibril ne ya sauka akan Wani kyaƙyƙyawan yaron dake daga can tsakiyar layi , su duka a ƙame suke amma shi a wannan lokacin Wayar hannun sa yake latsawa cike da kula murya ƙasa-ƙasa yake furta " Mami...Hello .

Wani irin Tsawa Major Jibril ya daka masa Wanda sai da Hantar cikin Duka yaran ya kaɗa yana bada amon ƙulululu... Mamaki ne ya kama su Ganin Yanda Aliyou Haidar bai Girgiza ko ya saki wayar tasa tayi ƙasa ba ,sai ma ƙara mannata da yayi da kunnen sa yana furta " Mami I'm in trouble Major Jibril ya na mun magana bye bye .kamin ya jira jin mene Zata furta ya datse kiran da Sauri yana maida Wayar cikin Aljihun sa .

Cike da shouting da ɗaga murya irin na Sojoji Major ya furta " Who are you ? ....kamin ya rufe baki cike da Ƙwarin gwiwa tare da gigiwa irin na Aliyu ya furta" ALI HAIDAR ". yana furta zancen tare da ƙamewa kaman yanda suka saba yi don respect. Kallon shi Major Jibril yayi kana ya bashi umarnin ya fito wajen layin . Cike da kuzari da Sauri ya fito yana gyara tsayuwar sa , kallo Ɗaya Major yayi masa yaga tsayayyen namiji ne a gaban sa tun kan ya girma a yanzu ma zaka fahimci hakan , ƙwayar idanun sa ya kalla ganin rashin tsoron sa yasa shi Furta " Waye Soja a tare da kai ? .

Sorry sir
Fa furta yana kame ma Major ɗin , Tambayar ya kara nanata masa karo na biyu wato a dangin sa Waye soja? Wanda a wannan karon kai tsaye Ali haidar ya basa amsa da my Dad...! Ya furta da ƙarfi yana Ƙara ƙame ma Major Jibril . Meye sunan Mahaifin ka ? General Saleh Yelwa . Girgiza kai Major Jibril yayi tamkar General ne a gaban sa , don yasan Waye General Yelwa babban sune shine ya basu horo a lokacin tasowar su .

Kallon Aliyou Haidar yayi kana ya cigaba da cewa " Ya ake yin Hand salute?

Ok sir . Ya furta yana Sara masa tare da hade ƙafafun sa .

Kallon Sauran sojojin abokanan sa yayi shigowan yanzu Nd 1 kana cike da Arrogant voice ɗin sa ya fara cewa Hand salute!

"You raise the right hand smartly in the most direct manner a kuma lokaci guda extending and joining the fingers ...keep the falm plat and facing the body.

"Yana maganan tare da nuna masu yanda ya kamata suyi don haka Majorn ya sanar dasu a jiya . "

Komai dai dai ya faɗa , Wannan yasa Major kallon sa yana basa horo da ya fita can Rana ya fara tsallen kwaɗo shine punishment ɗin sa na yau , Gobe ba zai ƙara kuskuren da yayi irin na yau ba.

Ficewa Ali haidar yayi yana nufar inda Major yace yayi tsallan kwaɗon , Ɗan waigawa naga yayi yana kallon wani direction yana murmushi .

Gani nayi wani Matashin yaro wanda ba zai haura 17 ba yana kallon Aliyu idanun shi sunyi ja na damuwa ga gumin dake karyo masa , damuwa duka sun bayyana ƙarara a fuskar shi . Haɗa ido suka yi da ƙanin nasa yana jifan sa da harara tare da cewa a zuciyar sa " Yaushe Haidar zai daina rashin ji ne? Yau sai ya sani bari ya gama mu koma . Murmushi Aliyu haidar yayi yana furta to menene na dumuwa Yaya Khaleel bafa wuya ne dashi ba . Yanzun xanyi na gama .



Tsallan ƙwadon ya fara yi su kuma sauran sojojin suna fara fareti . Fiye da Awa ɗaya yake aikin tsallan ƙwaɗon amma babu alamar gajiya a tare da shi , don shi jin sa yake tamkar training din da suka saba yi ne a gida yake yin sa a yanzu. Ni Ko nace yo ba dole ba , Mahaifin su soja mahaifiyar su babban Ƴar sanda ce , Wanda a yanzu take da matsayin mataimakiyar Commissioner of police. Hajiya Nafisat Yelwa kenan . Ƙaramar ƙanwar su kuma jidderh itace take makarantar yara na karatun architecture . Sauran labari zamuji shi a gaba inshallah ku dai ku cigaba da biyo wannan Golden pen din don wannan tafiyar ta musammance .


Ali Are You not tired ? Baka gaji ba Haidar? Muryar Areef ya katse shi wanda yake fareti dai dai inda Aliyou Haidar yake . Cike da hade gira tamkar wani bad boss yace " Na riga da na saba da ko wani horo na soja tun kamin nazo nan. Ɗan wannan tsallen kwaɗon ba zai gajiyar Dani ba .

Da kyau!

Muryar Major Jibril ya katse su wanda basu san yana tsaye da a bayan su ba. Tabbas wannan yaron yana da jan rai da zuciya kangararriya , haka ake son soja ya kasance , Major yayi maganan a zuciyar sa yana juyawa tare da kallon Manyan sojojin dake bayan sa. Ina so ku bi mun bayan Ali haidar Yelwa yayi gudu tun daga nan Kaduna jaji har zuwa Zaria ya dawo a ƙasa ba tsayawa ko Hutawa yanzu . Ok sir ......! Suka yi maganan cike da amsa kuwa . Juyawa Ali haidar yayi yana kai hannun sa tare da miƙa yana miƙewa tsaye . Da sauri ya furta " Major idan ba damuwa zan iya ɗaukar Helmet da Armor idan ba damuwa da ruwa ma . Wani irin kallo duka suka bi shi dashi , yayin da Major Jibril cikin Tsawa yace " Kai ba yaƙi aka ce zaka tafi ba , You Are under punishment now , shine har kake tambayar Helmet da Armor rigar kariyar harbi me zai maka ? Ruwa kuma ba zaka sha shi ba har kuje ku dawo .......................!


*Ina kuke masoyana💃🏻 nasan yawan ku kun haura irin billions ɗin nan😹 kuyi mun share page ɗin nan ga mutanen ku nasan ƙaranci yanda nake da jama'a billions haka kuma ƙaranci 1 million people😹. Ga masu buƙatar na tallah masu hajar su ƙofa a buɗe take zaki zanzare kuɗin aljihun ki ayi Miki tallah don samun customers sai ki tuntuɓeni ta WhatsApp ga nombibina nan a daga ƙasa*

*Labarin RAINON SOJA na kudi ne kar ki fara karantawa tun fari idan kin san baki da kuɗin saya don Allah... Book 1 free ne shine wannan ,idan mun gama shi book 2 na kuɗi ne kar azo ana ayi haƙuri da sauran su , Sannan group din littafin guda uku ne 3 , muna da na ƙasa shine ₦500 (regular group) sannan aƙwai yan tsakiya shine ₦1000 (Vip group)sannan aƙwai na sama shine ₦1500 (Special payment)...Zaki iya payment din ki ta wannan account number 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank shaidar biya ko katin MTN ta wannan number 08081202932 idan Vtu transfer ne ga MTN numbern da zaki tura tanan 09061466409 zaku iya fara payment naku tun yanzu don na samu damar sakaki group da wuri kamin mutane suyi yawa kunsan hidimomin da yawa ...to hajiya ta wannan salon tafiyar ta daban ce kar ki bari ayi babu ke a barki a baya .labari ne mai ɗauke da darussa 😹💃🏻✨yanda yazo a ƙarshen shekara haka daɗin sa ya kasance na musamman kun san alƙalamin mmnteddy baya rubuta labari mara ma'ana ato.*

*Anty Aysha Mamanteddy*
[12/15, 1:59 PM] Abu~ammar: *🕊️RAINON SOJA🕊️*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and sympathetic story.*






_Book 1_
_Free page 2_




*Littafin rainon soja book 1 free ne , book 2 na kuɗi ne regular group ₦500 Vip group ₦1000 special payment ₦1500 .*
*Zaki turo da kuɗin ki ta wannan account number 7782217014 Mohammed Hassana FCMB shaidar biya ta wannan number 08081202932. Idan Vtu transfer ne sai ki tura ta Wannan number 09061466409 ku fara payment da wuri a page 10 Free page zai ƙare*

Maman Teddy.
Marubuciyar
My Lady boss
Yar tsakar gida
Bafullatanan Ruga
Walijaam
The sexy Boss
Gidan Ƙwarata
Siyasata
The virgin maid
Habibi da'iman
Mr romantic
Duniyar shahara x world
Yar Aiki
Dijama yar Fulani
Zuma da maɗaci
Kwarton manya
Da sauran su .

Yayin da Major Jibril cikin Tsawa yace " Kai ba yaƙi aka ce zaka tafi ba , You Are under punishment...shine har kake tambayar Helmet da Armor rigar kariyar harbi? , Amfanin mene Helmet zai maka ? Ruwa kuma ba zaka sha shi ba har kuje ku dawo ban yarda ko Hutawa kayi ba . Cike da ɗaga murya tamkar saukar Aradu Aliyu ya ƙame tare da furta " Yessss sir ". Yana furta hakan ya fara cika umarnin Major Jibril yayin da Wani soja dake gaba dasu ɗan ND 3 yake bin bayan Aliyu haidar da ya fara gudun sassarfa kaman yanda Major yace dashi . Tun daga jaji yake gudu a wani irin tartsatsin rana gashi ba hulan su ta soja wanda yake tare dukan Rana ,ko ruwa kuma ba'a yarda mishi yasha ba .

**
A hankali take bin bord ɗin da kallo , tana sakin Murmushi tare da kai laɓɓanta tana kissing ɗin zanen fuskar Aliyuu Haidar . I love You Booo mie. Ta furta tana shafan giran sa wanda yake a tattare ya haɗe kaman hadari. Ƙamshin turaren da taji ne yasa ta saurin juyowa tana kallon inda Mami ke saukowa cas-cas-cas cikin shigar suit ƙafarta tasa cover irin na mata , Fuskar ta cikin baƙar gilashi da gani kasan no respect ba zaka taɓa cewa itace ke da yara uku maza biyu mace ɗaya ba wato jidderh, Khaleel da kuma iyayen kafiya da naci wato Aliyu haidar. Mami....! Ƙaramin Muryar Jidderh ya katse Ni cike da yarinta tana sakin mawa Mahaifiyar nata fara'a . Cikin sauri Mami ta nufo inda take tana rage tsawon ta tare da hugging ɗin jidderh tana cewa " Morning my baby love". Ana nan kina kallon Khaleel da Aliyu ? . Yes mami i really miss Booo mie da kuma Ya Khaleel . "Hummmmmm" Hajiya Nafisat ta sauke Sanyayyar ajiyar zuciya kana ta kai hannun ta tana shafa kan Jidderh cikin sanyi da Muryar rarrashi ta furta " Sorry my lav zasu dawo nan kusa bada jimawa ba '.

Gyaɗa ma Mami kai jidderh tayi tana sakin Murmushi haƙoranta da wawulo na bayyana wannan yasa Mami dariya tana cewa"Alright muje kiyi breakfast sai na kai ki school daga nan Ni na wuce Office . Hannunta ta kama suna nufar Dinning room.....yanda Mami ke tafiya kadai zaka fahimci zaman gidan Na sojoji ne masu kaki komai oya-oya ake yin shi babu shauƙi irin na mata , tun tasowar yaran nasu a haka cikin gidan ya kasance, Daddy Soja Mami Police yar sanda 🫡 . Haka suka taso basu san suga iyayen su kullum a tare ba ,idan yau Daddy yana hutu to gobe Mami zakaji an sauya mata wurin aiki ko bata gari , dukan su yaran sun taso cikin horan sojoji ne ,don gidan baki ɗaya har ta masu girki cook sojoji ne , masu kulawa dasu sojoji masu kai su school sojoji Wannan yasa duk horo suke shan baƙar wahala , gashi General Saleh Yelwa ya ƙudurci son ganin yaran nashi sun zama tamkar shi Wato Sojoji . Wanda a yanzu a lokaci guda Duka su biyun suka fara NDA . A yanzu Aliyuu Haidar shekarunsa sha shida ne Bama ce ya cika ba ,sai Khaleel babba shine gaba da Haidar shi kuma shekarun sa 17-18 don tazaran su ba nesa bane shiyasa kan su yake daya ,sau tari wanda basu sani ba ma kiran tagwaye suke yi masu .

Sai dai Khaleel na fama da shan Wahalar Aliyu saboda Neman magana irin nasa ga kafiya da fusata ga saurin ƙufula da zuciya, a haka kuma yake zafin son Ƙanin nasa . Wannan shine taƙaitaccen labarin Gidan General Saleh Yelwa da iyalan sa . Bari mu Jah gaba muji wani hali Aliyu yake ciki a yanzu .

**

Tafiya ce suka yi ta mai dogon zango yayin da Ali ya haɗa gumi iya gumi a wannan lokacin har sun kai wuraren Gwargwaje sannan suka kuma juyowa zuwa jeji. A tsakiyar wani ƙaramar jeji ne kan hanya idanun Aliyu da Yaron Captain Lawal suka sauka kan Wata moto da tayi ƙwatsa ƙwatsa a titin wuta na tashi ta sama da ƙasanta . Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un kalmar da Lawal yayi kenan yayin da Haidar ya cigaba da Gudun sassarfa yana ƙoƙarin wuce moton . Amma kai baka da Hankali Wani irin mara imani ne kai Ali ? Wucewa zaka yi kana ganin halin da Mutanen moton ke ciki . Tsayawa Haidar yayi yana ƙamewa tare da seniority ya furta " I'm under punishment Sir ".

Kama kai Lawal yayi kana yace " Mu ceci mutanen nan ka dakata da Wannan Gudun da kake yi haka nan ,idan mun koma xanyi ma Major bayani . Ok sir . Aliyu ya furta yana saurin ƙarikowa inda moton yake hannun sa yasa duk da ƙarfen da tayi zafi ga moto ba karama ba . Tura moton suka yi da ƙarfin na sojoji suna ɗaga ta , Saurin rufe ido Ali yayi don wannan shine karon shi na farko da ya fara ganin gawa ido da ido a rayuwar sa . A takaice gaba ɗaya moton babu wanda ya shura dukan su sun zama gawa, gashi mutuwar wahala abun ba dadin faɗi da gani sai ka zubda masu da Hawaye jini ne kawai ke malala.....Hu'uhhhhmmmmmmm Suka ji wani jan iska da karfi anyi tare da fara tsala ihu irin na yara jarirai . Hasbunallahu wani'imal wakeel ". Lawal ya furta da sauri yana kai hannun sa yana fuzgo yarinyar da take maƙale jikin mahaifiyar ta , har ta fara sanƙarewa.

Aliyu Ruwa ruwa Aliyu Ruwa kawo ruwa .! Yana maganan hankalin sa a tashe da kuma yanda yarinyar ke ihu iya ƙarfin ta numfashin ta na kokarin ɗaukewa.

Kallon Sa Aliyu yayi kana yace " Ai Major yace ba zan taho da ruwa ba ko ka manta ne ? .

Ba tare da ya tsaya ba Aliyu amsa ba ya fara gudu da yarinyar a hannun sa ,hakan yasa Aliyu shima bin bayan sa don su nemi ruwa su bata a wannan falfalan hanyar jejin da babu gida babu gida baya ,itako yarinya ƙiwuya ne yayi mata yawa ganin bata san fuskokin ba. Wannan yasa ta take kuka har da shirin riɗewa . Sir Lawal ka daka ta gudun nan , wannan ihun yarinyar yayi yawa kaman mun sato ta? . Cak Lawal ya dakata da gudun yana kallon Aliyu kamin ya juya yana kallon kyaƙyƙyawar fuskar yar lukutar yarinyar wanda nan take ya furta " Laaa Aliyu kalla? Kai take kallo tayi shiru Aliyuu kalli dariya ma take yi maka yanzu . Ɗaga gira Aliyu yayi yana zuba ma yarinyar Manyan idanun sa da suke warwaje na rashin tsoro , Ganin yanda take Wangale masa baki kaman ba itace mai kukan ba ko kuma ta san shi yasa shima jin wani irin yanayi lokaci ɗaya na shigar sa gami da yarinyar . Amshe ta Ali zata yi shiru a hannun ka yanzu . Ba musu Aliyuu ya miƙa hannun sa yana amsan Yarinyar da take ta Wangale bakin nata tana dariya tare da miƙa masa hannayen ta duka na yara . Lawal ne ya bude baki zai masa magana da nuna masa yanda zai riƙe yarinyar don ya lura bai ma iya daukar yara ba , Kawai caraf yaga ya ɗaga yarinyar yana ɗaura ta bisa wuyan sa tare da riƙe hannayen ta a sama . Zamu iya tafiya Yallaɓai.! Yayi mganan cike da amsa kuwa da ƙamewa , cikin sauri Lawal yace " Kai Ali mu aje wannan duk abin a gyefe yanzu ina zamu kai yarinyar nan. ?

Shiru Aliyu yayi masa yayin da Lawal ya cigaba da cewa " mu tafi Barack da ita. Mu sanar mawa Major.

A'a gidan General Saleh Yelwa zan kaita yanzu. Ko mun dare zan dawo barack . A'a kana fa bisa laifi ne ,idan ka tafi zaka iya samun wata matsalar, sannan kuma dole mu nemi abun hawa don yarinyar a gajiye take . Gudu Haidar ya fara yi mai sassarfa kana ya yi gaba tare da daga murya yana cewa " Sai na dawo Yallaɓai".

*
Ali Meye haka nake gani? Wacece wannan a saman wuyar ka ka ɗauro? . Muryar Mami ya katse shi cike da amsa kuwa take maganan cikin ɗaga murya don kallo ɗaya tayi masa jikin ta sam bai bata ba .

Mami abani ruwa na bata . Meye sunan ta ? Kuma Meye na kawo mana ita cikin gidan nan? .

Ban san sunan ta ba , Amma na kawo ta gare ki ne , domin ki sanya mata sunan da ya dace . Ki kuma raine ta. Yanda yake maganan idanun sa kafe akan Mami yasa ta Fahimtar bafa wasa yake yi ba ,don dama shi ba ma'abocin yin shirme bane sam baya wasa . You're very stupid Ali..! Baka da hankali . Ka dauko yarinya nayi mata raino , ko ku kan ku a haka kuka taso

5 Comments On RAINON SOJA
avatar
hauwa-u-2

11 months ago

Reply

Beyin download

avatar
taskar

11 months ago

Reply

Replying to hauwa-u-2

dole sai kin yi subscription sannan zai downloading

avatar
taskar

11 months ago

Reply

Replying to hauwa-u-2

dole sai kin yi subscription sannan zai downloading

avatar
taskar

11 months ago

Reply

dole sai kin yi subscription sannan zai downloading

avatar
taskar

11 months ago

Reply

dole sai kin yi subscription sannan zai downloading

Please Login or Register in order to submit comment