Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daga yau se yau nan zaki dinga zuwa ba ruwana da kome zakice, kika sani ma ko mu samu dad'in masu siya a koma cika miki bokiti 4, ke ko dae ba'kin ciki kike min bansani ba ? Inno ta fad'a tana ri'ke ha6a... Dae_dae lokacin Baban ilyasu ya shigo gidan yana kallan inno yake fad'in

"Toh..toh tun daga waje nake jiyo hayaniyarku hala wani abu ya faru"

"Ganemin hanya baban ilyasu, Ashe ni ina zaune da er tsintuwa bansani ba ba'kin ciki take min, ni ban mata ba'kin ciki na d'auketa ba sanda uwarta ta yasar da ita ba seni zata yiwa, kaji min fa.." Seya kalli Azrah da tunda Inno take magana kanta na 'kasa ta kasa furta komae ga kanta se wani sara mata yake, kamar daga sama ta jiyo muryar baban ilyasu yana fad'in

"Ke uwar ri'kon taki kikewa ba'kin ciki dan rashin ta ido ? Bata san sanda tayi saurin girgiza kae ba cikin rashin sanin abinyi tace

"A'ah wallahi baba.." Inno ta katseta ta hanyar fad'in

"Ni dae na fad'a miki, daga yau can zaki dinga zuwa ahh tohh" Daga haka ta mi'ke jikinta a matu'kar sanyaye ta wuce d'akinta.... Cikin dare tana kwance a d'akin nata tun d'azu take juyi sedae bacci ya'ki zuwar mata bata san dalili ba, tafi awa 1 a haka har bata san sanda baccin ya kwasheta ba.. Can cikin baccin taji kamar ana shafa mata 'kafafunta, a hankali ta fara bud'e idanunta harta gama bud'esu, se a lokacin ta fahimci ba kamar bane da gasken hakane, da wata iriyar azama ta mi'ke zaune tana kallan inuwar mutum gashi har an d'age mata skirt, cikin tsananin tsoro firgici ta 'kwalla 'kara sannan a miliyan ta mi'ke zata fice, da sauri ya fara 'ko'karin ri'kota sedae ina cikin 'karfin da bata san tana dashi ba ta fizge se hakan ya bata damar fad'uwa shi kuma ya fice daga d'akin da wani irin gudu, duk da haka bata yadda ba seda ta fito tsakar gidan idanunta na fidda 'kwalla tana wani irin kuka me tsuma zuciyar me sauraro.. Inno ta fito daga d'akin ta kamar an jefota tana kallan Azrah tace

"Uban meya faru kikewa mutane ihu" Azrah data gama rikicewa ta nuna d'akin ta tace

"Wani..wani..ne a ciki" Inno ta kalli d'akin nata sannan ta maeda dubanta kan Ilyasu dake tahowa daga soro yana kallansu cikin fad'in

"Menene yake faruwa Inno...."


Kuyi manage da wannan pls 🥺


Mhiz Innocent............✍️



https://chat.whatsapp.com/CNoLsXVGhSe9XZXghGxjZV


*♡☆SANADIN KADDARATA☆♡*

( _Is similar to *DON ADNAN's* destiny_ )




⚡ *THE BEGINNING*⚡




STORY AND WRITTEN

BY

*♡ MHIZ INNOCENT ♡*


..Sanadin 'kaddarata na kudi ne akan N300, da zarar mun gama free pages zamu cigaba da tafiya ne da wadanda sukayi payment kawae, zan ajiye muku yadda zakuyi payment din a last page na The Beginning..


Free page_6

____Da wani irin kallan tuhuma inno kebin ilyasu dashi, shi kuma se kakkauda kae yake ya'ki bari su had'a idon, cikin haka ya jiyo muryar inno tana fad'in

"Qofar gidan a bud'e take ne" Ilyasu ya girgiza kae yana wata in'ina kamar mara gaskiya

"A'ah..a kulle take, shine nima nake mamaki, 'kila mafarki tayi" Ita dae Azrah bama fahimtar zancen da suke take ba, dan kuwa iya rud'ewa ta gama rud'ewa, inno ta ta6e baki tana kallan Azrah tace

"Seki koma ae, tunda dae kinji 'kofar gidan a rufe take" daga haka ta juya ta koma d'aki bayan ilyasu yayi hanyar soro. A hankali ta mi'ke, brown eyes d'inta sunyi jajir saboda kukan da tasha ta bud'e labulen ta shiga tana 'karewa d'akin kallo kamar meson gano wani abu, seta nemi waje daga bakin 'kofar ta zauna ta tattare dukka jikinta ta cure waje 1 kana a hankali ta d'ora kanta akan cinyarta wasu sababbin hawaye na sirnano mata, wani abune yake fad'o mata arae sedae ta kaasa yadda ta kar6i abin a matsayin hujja dan haka ta lumshe idanunta tana sake curewa waje 1, baccin da bata koma ba kenan dan kuwa ta riga data sani kota kwanta d'in ba iyawa zatayi ba, bama zata iya kwanciyar ba dan tana ganin kamar tana kwanciyar za'a 'kara shigo mata d'akin...



_____Mami ta kalli Ammi ( me yiwa don girki, mamansa na dab da rasuwa ta d'auke ta tanawa don girki kasancewar mamantasa ma'aekaciya ce, toh ko a yanzu ma itace take masa girki har kwanan gobe girkinta kawae yake ci ) tace

"Ammin yara har kin shirya ? Murmushi tayi kafin tace

"Wallahi kuwa tafiya zanyi"

"Toh madallah seda safe" Inji Mami, Ammi ta amsa da

"Allah ya tashemu lafiya" tana ficewa daga d'akin....Dae_dae lokacin simrah ta fito daga wani d'aki fuskarta a maraeraece kamar zata saka kuka ta zauna kusa da Mami

"Mami tafiya zanyi fah kuma har yanzu ban ganshi ba" ta fad'a kamar zatayi kuka, Mami ta kalleta kafin tace komae simrah ta d'ora da

"Don Allah ki kiramin shi"

"Baki da contact d'in sa ? Mami ta fad'a tana kallan simrah, Seta sake maraeraecewa

"Mami kona kirashi ba d'agawa zaeyi ba"

"Ohk kiyi trying"

"Ohk lemme try" ta fad'a tana d'aukar wayarta ta danno numbersa ta danna kira...... Wani 'katon club ne had'ad'd'e wanda ya amsa sunansa dan se wanda ya amsa sunansa ya tayar dakae da nera shi zaka gani a wajen, wasu different colours ne suke tashi gwanin birgewa sannan wani sassanyan kid'a mara hayaniya yana tashi a hankali babu hayaniya, kowa da abinda yake, wasu rawa suke, wasu suna zaune ne mata kawae, wasu maza ne kawae suna kwal6ewa, yayinda wani wajen kuma both mata da maza ne, A d'an wani ke6antaccen waje wanda dukda wajen ya kasance na classy babes and guys ne ya zamana akwae wajen VIPs, anan na hango don suna zaune su 3 a wani zagayayyen kujera, shisha ce akan bench d'in dake gabansu wanda jefi_jefi don kan matsa yayi amfani da ita se kuma ya koma ya cigaba da danna wayarsa,

"Don" Irfan ya fad'a dae_dae lokacin da don ya gama amfani da wayarsa ya ajjiyeta a gefensa, seya d'aga shanyayyun idanunsa ya zubawa Irfan su, Irfan ya kalli gefensa sannan ya dawo da kallansa kan don yace

"Heyy buddy, wae ba kaga yanda waccan babe d'in ke satar kallan ba tun d'azu" Wanda ke kusa da Irfan ya juya ya kalli inda Irfan d'in ke kalla seya shiga 'karewa babe d'in kallo wadda ke sanye cikin riga da wando tiet, kanta cikin kitso wanda yasha gashin doki, jefi jefi takan danna waya se kuma ta d'ago ta kalli don ta maeda kanta kan wayar, Hameed ya juyo yana cije le6ensa ya kalli Irfan

"Lallae akwae kayan aeki a wajen nan" Irfan dae kallan don kawae yake ganin ko nuna alamar yaji zancensa beyi ba ballantana ya saka ran ze sami amsar tambayar, dae_dae lokacin wayar don ta fara ruri, ya kalli wayar tasa dake ajje gefensa, ganin number ce ke yawo ya sanyashi d'auke kae dan mutanen da basu da amfani a rayuwarsa bashi da lokacin 6atawa da har zeyi saving contact d'insu.... Daga 1 6angaren simrah ta karyar da wuya tana kallan Mami

"Mami dama na fad'a miki, kona kira ba d'agawa zeyi ba, Don Allah ki kirashi" ta fad'a tana d'aukar wayar Mami ta dan'kata a hannunta, Badan Mami taso ba ta kar6a ta danna kiran don d'in....Wani kiran yaji ya sake shigowa, ya juyo a fusace da niyyar kashe wayar yaci karo da sunan Mamina, Seya lumshe ido yana d'aukar wayar ya kaara a kunnensa, daga 1 6angaren Mami tace

"Son..yaushe zaka dawo, simrah na jiranka tun d'azu kaaga kuma dare yana ta 'karayi" Kamar me koyon magana ya maemaeta sunan data fad'a d'in akan la66ansa sannan se kuma yace

"Ohhh..plsss Mami let her go.. Banson ganinta" daga haka be jira amsar mamin ba ya katse wayar yana dafe kansa..Simrah ta kalli Mami

"Me yace ? Mami ta kalli simrahn cike da tausayawa tace

"He said baya son ganinki" Simrah bata iya cewa komae ba ta cigaba da kallan Mamin kawae sedae idanunta sunyi rau rau kamar zatayi kuka...


........Fitowarsa kenan daga wanka ya sanya farar riga ta ciki, kasancewar yanzu ya fito daga wankan ya sanya akwae ruwa a jikinsa hakan ya bawa ba'kar gargasar jikinsa damar sake kwanciya luff luff kamar yadda sumar kansa take, wayarsa ya nufa wadda ya jiyo tana ringing, ya 'karasa ya d'auka yana kaewa kunne, daga can 6angaren Mami tace

"Son.. Ka fito parlour na dad na jiranka"

"Ohk" ya fad'a a ta'kaece yana ajje wayar, ya shirya kamar koda yaushe cikin shigar 'kananan kaya riga da black jeans, yayi matu'kar kyau kamar shi yayi kansa, a haka ya fara takawa har zuwa cikin parloun Mamin, A hankali ya 'karasa cikin parlourn hango mahaefinsa zaune kan kujera yasa ya 'karasa ya zauna kan hannun kujerar

"Morning dad" da fara'a kan fuskar dad yace

"Morning son, ka tashi lafiya"

"Ehh" ya amsa da hakan, Yakumbo dake ta kallansa tun d'azu tace

"Ina kwana adnan" Se a lokacin ma ya lura da halittarta ya juya ya watsa mata lumsassun idanunsa yace cikin basarwa

"Kin tashi lafiya" Seta jinjina kae tana ta6e baki tace

"Lallae, Allah ya 'kara shiryaka" ta fad'a 'kasa 'kasa, dad daya gama amsa waya ya kalli don yace a hankali

"Ka gaeshe da Yakumbo" Jinjina kae kawae don yayi ba tare da yace komae ba.. Dae_dae lokacin Mami da Fawaz suka 'karaso, fawaz ya tafi da sauri wajen don ya rungume shi yana fad'in

"Gud morning bhai" wani sassanyan murmurshi don ya saki a hankali ya furta

"Morning boy, ka tashi lafiya"

"Lafiya 'kalau na tashi, kaefah"

"Same" inji don ya 'karasa fad"a yana kallan Mami dake fad'in

"Ka tashi lafiya son" Seya maeda mata da martanin murmushin yace

"Ehh"...Dad ya kalli don

"Ka gama shiryawa son" Jinjna kae kawae don yayi yana kallan dad d'in wanda ya d'ora da fad"in

"Ohk..akwae tawagar da zasu kaeka..yanzu haka sun gama shiryawa kae kad'ae suke jira" Seya kauda kae kafin ya juyo ya kalli dad

"Dad... kasan bana 'kaunar wasu bodyguards, plsss ina son privacy a komae" Dad dae kallansa kawae yake se daga baya yace

"Nooo..wannan ba harkar privacy bace harkan tsaron lafiyarka ce, saboda haka indae baka so nayi fushi toh kabi mutanannan"

"But dad.. Tare zamuje da sameer and Irfan ya kenan" ya fad'a kamar a d'an kufule, dad yace

"They will wait for them"

"Ohk.." Ya fad'a yana gyara zamansa, Fawaz ya 'karaso kusa da don yace

"Congratulations bhai, zan iya binka ?

"Noo boy ka tafi school" don ya fad'a ba tare daya kalli fawaz ba, fawaz yace

"Ohk wataran zanje"

"Yeah" inji don

"Toh adae kula don Allah, a kiyaye abinda ze iya janyo magana, a gujewa abokanan banza, Allah ya taemaka yayi ri'ko da hannayenka" Ya tsinci muryar Yakumbo na fad'in hakan, kallanta kawae yayi bece komae ba se su dad ne suka amsa da

"Ameen"... Shigowar sameer d'akin ne ya sanyasu dukka suka d'aga ido suna kallansa, ya 'karaso ya zube yana murmushi yace

"Barka da safiya dad" dad ya amsa cike da kulawa, sameer ya juya suka gaesa da Mami gama Yakumbo ma, fawaz ya kalleshi da murmushi yace

"Gud morning yah sameer"

"Morning boy, ya makaranta"

"Alhamdulillah" Yakumbo ta kalli sameer tace

"Toh kae sameer seku kula, don Allah ka dinga d'ora abokinka akan abinda ya dace, Ku kula sosae kaaji koh" Sameer ya jinjina kae yace

"In Sha Allah Yakumbo zamu kula, adae dinga mana addu'a kawae" Yakumbo tace

"Dama addu'a kullum cikin yinta ake" don dake jinta ya faki idon dad ya wurga mata harara...


_____A hankali ta tako zuwa tsakar gidan kamar zata fad'i saboda rashin 'kwarin jiki, wani irin ciwon kae ke damunta ga rashin baccin da take fama dashi kullum, dan tunda abinnan ya faru bata iya bacci sedae ta zauna tayi ta nafilfili da karatun qur'ani, da tana samun lokaci nema da da safe se ta dingayi, amma sedae babu, bata da wannan damar dan kuwa aekin gidan ma da take shi kad'ae ya isheta.. Ta 'karaso ta tsugunna a gaban inno dake rufe bokitin data gama zuba abincin a ciki tace

"Ki tabbatar kin kaemin bakin ma'aekatar nan, idan ya 'kare da wuri ko wani yaron ne ki turo ya fad'amin se a sake yin wani kinji koh" Jinjina kae tayi kamin cikin sanyi tace

"Toh" daga haka ta mi'ke sannu a hankali ta fice daga gidan d'auke da bokitin nata.. Kae tsaye can d'in ta nufa tana tafiya tana tunane_tunane iri_iri, a dae_dae kan kwanar da zata sha ta isa companyn suka had'u da hauwa'u, cikin farin ciki suka tsaya suna gaesawa da juna, hauwa'u na kallanta tace

"Yau kuma ina zakije na ganki a hanyar nan" seta lumshe idanunta tace

"Bakin sabuwar ma'aekatar nan zanje, nan inno tace inje" Hauwa'u ta jinjina kae tace

"Toh Allah ya kawo kasuwa, yasa ki fara zuwa a sa'a"

"Ameen_Ameen" Azrah ta fad'a, Hauwa'u ta kalli Azrah sosae

"Amma kamar baki da lafiya koh" Azrah tayi wani ya'ke

"A'ah me kika gani"

"Kamar kin rame" Seta sake janyo wani murmushin ta wanzar tace

"A'ah fah, lafiyata 'kalau"

"Tohm shikenan amma fah ban yadda ba" Inji hauwa'u

"Uhmmm" Azrah ta fad'a tana murmushi, daga haka sukayi sallama kowacce ta wuce inda zataje......Tana zuwa ta fara kallan yadda taga mutane nata shige da fice, wasu suna shiga wasu suna fita, seta 'karasa ta nemi waje gefe daga bakin 'katon gate d'in inda babu maza dan kuwa masu siye da siyarwa akwaesu da yawa a wajen kowa da abinda yake siyarwa, Seta ajje bokitan nata kana ta nemi waje ta zauna tana kallan abinda ke faruwa a cikin garin... Tana nan zaune ta fara hango wasu jerin gwanon kyawawan tsadaddun motoci suna tahowa inda suke, kafin kace menene sun 'karaso bakin companyn, masu gadi suka wangale musu gate d'in gaba d'aya, sannan da d'ad'd'aya suka fara danna hancin motocin nasu zuwa cikin companyn... Suna gama parking d'in ragowar da suke cikin motocin suka fara fiffitowa wanda kana ganinsu kasan bodyguards ne, suka fito cikin wata irin azama kowanne ya fara 'ko'karin bud'ewa don 'kofa, wani yayi nasarar bud'e 'kofar gidan baya wadda don ke ciki, sannu a hankali ya zuro 'kafafunsa wanda ke cikin takalmi samfurin slip_on kasancewarsa favourite nasa, dukka bodyguards d'in suka 'karaso suka zagayeshi, a haka harya 'karasa sakkowa, kae tsaye ya fara 'ko'karin yin gaba, sameer daya fito daga cikin wata motar ya 'karaso 'kasa_'kasa a saetin kunnensa yace

"Akwae abinda za'a gabatar kafin ka shiga fah" Shidae don bece masa komae ba ya cigaba da tafiya, seda yaje dae_dae wajen da aka zagaye da wani jan 'kyalle sannan ya dakata, kafin yace komae wani dake gefensa ya mi'ka masa almakashi, be jira an gabatar da komae ba ya saka almakashin ya yanka, se kuwa wajen ya d'auki tafi da shewa sannan ya wuce wajen da aka tanada dan office d'insa bodyguards d'in na binsa har yanzu, yana shirin hawa step d'in ya dakata ya juyo ya kallesu cikin tsare gida yace

"Ku barni haka nan" kafin ya gama fad'a dukka suka juya suka cika umarnin nasa, sameer da key d'in ke hannunsa ya 'karaso ya bud'e 'kofar sannan suka shige ciki, wani irin 'katon office ne wanda girmansa yakae wani babban parlourn, 6angare guda dama shine wajen da desk chair ke anan, se kuma wani 6angaren wanda aka shirya had'ad'd'un kujeru kamar a parlour. Kae tsaye ya 'karasa wani waje shima dake d"auke da bowl chair ya zauna yana lumshe ido, sameer dake kallansa yace

"Bafa lokacin zama bane yanzun don, ya kamata mu fara gudanar da abinda ya kawomu" Seda ya d'auki wajen sekanni 10 sannan ya d'ago ya kalli sameer kafin yace

"Ohk..but ka bari na huta koh ? Kafin sameer ya kaega bashi amsa akayi knocking 'kofar, sameer yace

"Yes" Irfan ya shigo cikin office d'in yana wani murmushi ya kalli sameer bece komae ba ya maeda dubansa kan don yace

"Don..ina son magana dakae" ya 'karasa maganar yana kallan sameer, sameer ya kallesu su duka fuskarsa a had'e kafin ya juya bece komae ba ya fice daga office d'in, Irfan ya juya ya kalli don yace

"Wae kasan me kuwa don ? Don ya d'ago ya zuba masa idanunsa ba tare da yace komae ba, ganin haka ya sanya irfan cigaba fa fad'in

"Ina ganin kamar 'kauye muka shigo, ashe akwae zafafan en matan dazan iya hutawa dasu" Ran don ya 6aci matuqa jin zancen da Irfan d'in ke masa, Seya mi'ke yana cusa hannunsa cikin sumar kansa kafin yace cikin d'aga murya kamar bashi ba

"Wae meyasa kae duk wani al'amarinka seka saka mace a ciki ? Meye mace ? Me mace zata tsinana maka ? Kae wae in tambayeka mana meye amfanin mace banda tayi girki sannan ta gyara gida ? Tell me if there is any other important of a woman bayan wad'annan"......



Mhiz Innocent.........✍️



https://chat.whatsapp.com/CNoLsXVGhSe9XZXghGxjZV


*♡☆SANADIN KADDARATA☆♡*

( _Is similar to *DON ADNAN's* destiny_ )




⚡ *THE BEGINNING*⚡




STORY AND WRITTEN

BY

*♡ MHIZ INNOCENT ♡*


..Sanadin 'kaddarata na kudi ne akan N300, da zarar mun gama free pages zamu cigaba da tafiya ne da wadanda sukayi payment kawae, zan ajiye muku yadda zakuyi payment din a last page na The Beginning..


Free page_7


____Tsayawa Irfan kawae yayi yana kallan don cike da mamakin furucinsa, se kuma ya saki wani miskilin murmushi ba tare da yace komae ba, se can kuma yace

"Sorry Don.." Daga haka ya juya ya fice daga office d'in, shi dae don ko kallansa beyi ba dan ba 'karamin haushi Irfan d'in ya bashi ba kasancewarsa mayen mata kullum zancensa mace mace, shiyasa yau kam ya taka masa birki. Basu suka bar companyn ba a ranar se wajen maghrib, dan seda aka gabatar da wata 'kwarya 'kwaryar walima, bada son ransa ya zauna aka gabatar d'in ba, kawae dae ya zauna ne saboda mutane da dama zasuyi farin ciki da hakan... Ita dae Azrah tana nan zaune tana kallan ikon Allah, dan kuwa harta bar wajen ba'a dena shige da fice ba, ga masu zuwa kallo da suke 'kara tittid'owa, aekam ba 'karya ranar tayi ciniki sosae dan kuwa kafin lokacin data saba komawa gida yayi abincin ya 'kare....

.......Washe gari da safe bayan ya shirya, kae tsaye ya wuce parlourn Mami, babu kowa a d'akin dan haka ya wuce kan dinning, befi mintuna 5 da zama ba Ammi (er aekinsu) ta fito daga kitchen hannunta d'auke da warmers ta 'karaso ta ajjesu kan dinning d'in, tana kallansa tace

"Barka da safiya yalla6ae" A hankali ya d'ago ya kalleta sannan ya maeda dubansa kan abincin da take zuba masa yace

"Barka Ammi.." Ya fad'a kamar me koyon yadda zeyi pronouncing Ammin, murmushi sosae Ammin ta saki cikin jin dad'in yadda ya fad'i sunanta dan yana fad'a amma jefi_jefi, ta 'karasa zuba masa komae sannan ta wuce tana fad'in

"Ayi break lafiya" bece komae ba itama bata damu ba ta wuce cikin kitchen d'in dan akwae abubuwan da bata gama ba.. Yana gamawa ya mi'ke ya koma cikin parlourn Mamin hannunsa d'auke da waya yana dannawa, da sallama ta shigo d'akin, ganinsa ya sanyata nutsuwa sosae ta 'karaso ciki ta nemi 'kasan kujera ta zauna tana fad'in

"Gud morning bhai"

"Morning" ya fad'a ba tare da ya d'ago ya kalleta ba, seta gyara zamanta a hankali tace

"Ya aeki" Se a lokacin ya d'ago ya watsamata lumsassun idanunsa wanda hakan yaso rikitata duk seta daburce tana sake gyara zamanta, bece komae ba ita kuma ta mi'ke cikin sanyi tace

"Allah ya taemaka" daga haka tayi gaba, dae_dae lokacin da Mami ke saukowa daga stairs, ta 'karaso fuskarta d'auke da murmushi tace

"Welcome son..jiya banji shigowarka ba, how was ur first day a wajen aeki" ta 'karasa fad'a da murmushin dae, seya mi'ke daga zaunen da yake yana 'ka'kalo murmushi yace

"Alhamdulillah..gud morning"

"Toh madallah..kayi break" inji Mami, jinjina kae yayi kana a hankali yace

"Yeah"

"Ohk toh kaje ka gaeda Yakumbo" d'an murmushin daya 'ka'kalo seya koma yana juyar dakae, Mami tace

"Plsss mana"

"Mami..ta fiya surutu.." Murmushi Mami tayi tace

"Toh ae seka biye mata, nidae yanzu ba wannan ba, kaje ka gaesheta uhmmm" gyad'a kae yayi alamar "ehh" yana ficewa a lokaci guda.... Yana dab da shiga part d'in nata yayi dae_dae da lokacin da Alh Abubakar (Abban Buhaisa) ke shirin fitowa, seya d'an dakata yace yana kallan Abban

"Gud Morning Abba.." Abba na murmushi ya amsa da

"Morning Adnan, ya aekin ? Komae dae lafiya koh ?

" Ehh" kawae ya amsa da ita, sukayi sallama da Abban ya wuce cikin d'akin, kan kujera ya wuce ya zauna ba tare daya kalleta ba yace

"Gud morning" Shirun da yaji ya sanyashi d'aga ido ya kalleta, itama kallansa take, seya kauda kae yana jan numfashi yace

"Kin tashi lafiya"

"Alhamdulillah" Yakumbo ta fad'a tana kallansa, seya mi'ke ba tare daya 'kara cewa komae ba, Yakumbo ta katseshi da fad'in

"Ya aekin ? Allah ya taemaka, don Allah ka kula kaji koh ?

"Se anjima" ya fad'a yana ficewa daga d'akin, Yakumbo ta bishi da kallo tana girgiza kae sannan a hankali tace

"Allah ya 'kara shiryaka d'annan"... A compound d'in ya had'u da dad wanda dawowarsa kenan daga Abuja da yaje jiya kafin maghrib, bayan sun gaesa dad ya kalli don yace

"Companyn zaka wuce" Seya girgiza kae yace

"A'ah zanje training ne..."

"Ohk bodyguards zasu bika, idan ka gama abinda kake sesu kaeka companyn" Kallan dad d'in yayi kafin a dake yace

"Plss dad.. Bana son wad'annan bodyguards d'in, zan iya kula da kaena plss" Kallansa kawae dad yake, shiya rasa gane meye aebun bodyguard da don d'in baya sonsu, amma seya share yace

"Zuwa companyn fa ?

"Zankae kaena plss" Dad ya sauke ajiyar zuciya

"Ohk...Allah ya taemaka"

"Ameen" don ya fad'a yana wucewa kae tsaye wajen wata baqar hamsha'kiyar mota...



...........Washe_gari da safe ta shirya fes kamar yadda ta saba, ta saka hijab d'inta har 'kasa ta fito tsakar gidan, dae_dae lokacin da ilyasu ya shigo gidan hannunsa d'auke da wata jaka, yana kallanta yace

"Qanwata ke nake jira nayiwa sallama" Seta d'ago ta kalleshi ba tare da tace komae ba, kallan data masa ya sanyashi lumshe ido yana sake kallan narkakkun idanunta, seta sake jiyoshi yana fad'in

"Zanje cikin kano ne, amma bazan wuce sati 1 ba" Ba tare data kalleshi ba tace

"Eyyah" Inno da tun d'azu take kallansu tace

"Maganin uban shishshigi, ae yanzu ya maka kyau koh ? Ni bansan a'ina ka d'akko wannan shishshigin ba wallahi, yarinya se wula'kantaka take kae kuma kana sake cusa kae" Ita dae Azrah batabi takan kowa ba, ta 'karasa ta d'auki bokitanta tace

"Na tafi" bata jira amsar da zata bata ba dan tasan bama lallae ne ta amsa d'in ba tayi ficewarta, ilyasu ya bita da wani mayataccen kallo... Kae tsaye inda ta zauna jiya ta 'karasa ta zauna tana kallan yadda har an bud'e companyn... Wajen 'karfe 12 tana nan zaune, wata had'ad'd'iyar mota ta karyo kwanar 'katon layin, da gudu me motar ke tu'kin har suka 'karaso bakin gate d'in, Irfan dake driving ya kalli Don yace

"Pls Don..bani mintuna 2" Don dake zaune a wajen me zaman banza ya juyo ya kalli Irfan kafin yace

"Mekake nufi.. In jiraka"

"Yes pls, yanzu zanje na dawo" Irfan ya fad'a ba tare daya fahimci tambayar da Don d'in ya masa ba

"Pls just go out, I will drive my self" Don ya fad'a a fusace, yana kae tabar dake hannunsa baki ya zu'ka sannan ya cire daga bakinsa, Irfan ya sauka daga cikin motar ya zagayo ya bud'ewa Don motar, A hankali ya sauko, dae_dae lokacin da Azrah ta d'ago idanunta ta saukesu akan Don, seta maeda dubanta kan hannunsa wanda ke ri'ke da taba, a hankali ya jefar da ita yana saka 'kafa ya taketa sannan ya wuce ya koma mazaunin driver, kawae seta tsinci kanta da siffanta mutumiñ, tsaf ya saka manyan kaya za'a iya kiransa da babban mutum sedae dama ance dont judge a book by its cover, ashe mutumin banza ne.. Se kuma taja tsaki na yadda take 'ko'karin shiga abinda babu ruwanta, aedae kowa yayi me kyau kansa.. Wasu mutane su 3 wad'anda ke sanye da ba'ka'ken kaya suka 'karaso da saurinsu zuwa wajen Don, ko kallansu beyi ba kawae ya d'aga musu hannu, basu 'kara cewa komae ba kowannensu yayi baya, shi kuma ya tada motar ya shige cikin companyn.. "Allah karka bani arzi'ki indae ze zama silar dazan wula'kanta wani bawa" Azrah ta fad'a a hankali,

"Salam en mata" Taji wata murya ta fad'a daga gefenta, seta juya da

Please Login or Register in order to submit comment