Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

BY

*♡ MHIZ INNOCENT ♡*


..Sanadin 'kaddarata na kudi ne akan N300, da zarar mun gama free pages zamu cigaba da tafiya ne da wadanda sukayi payment kawae, zan ajiye muku yadda zakuyi payment din a last page na The Beginning..


Free page_11

______Cikin wani irin farin ciki mara misaltuwa Alhaji wadata yace fuskarsa d'auke da mad'aukakin murmushi

"Alhamdulillah..nagode 'kwarae da gaske kyakykyawa" ita dae bata ce komae ba dan tun bayan data furta ta amince ta dena fahimtar komae, se take jin kamar bata yiwa kanta adalci ba, amma tayi watsi da hakan, ta fara tattaro nutsuwarta dan saurarar abinda yake fad'a d'in

"Yanzu zan sami Malam da maganar, In Sha Allah bana so a wuce sati 2 ba'ayi auren nan ba" Bayan bugun zuciyarta daya 'karu yanzu, se taji ya 'kara gudu fiye da d'azun, sedae ta kaasa furta komae, Alhaji wadata yace

"Hakan yayi ko ? Jinjina kae tayi kamin a hankali ta furta

"Ehh"

"Toh Allah ya rufa asiri" ya fad'a da murmushi kan furkarsa, yauma kamar rannan seda yazo mata da tsaraba, koda ta koma gida kae tsaye d'akinta ta wuce ta zube akan tabarma, tun d'azu take so tayi kuka amma bata samu damar hakan ba se yanzu, dan haka tana zama kuwa kukan ya "kwace mata, ba kukan komae bane sena tunanin yadda zamanta ze kasance da mutumin daya haefeta, me 'ya'ya 10, dududu nawa take da zata iya kula da 'ya'ya har 10 ? She is just 15 fa "Ya ilahi ka kawomin d'auki" ta fad'a tana sake fashewa da kuka... Ranakun da suka biyo baya abubuwa da yawa sun faru, ciki kuwa hadda tsaeda ranar biki da akayi sati 2 masu zuwa, Alhaji wadata yace bayason Malam su tada hankalinsu base sun mata komae ba, shi zeyi mata, sannan ya bawa Inno kud'ad'e masu yawa wanda za'a siyawa amarya kayan biki da sauran kayan amfani.. Rannan Inno na tsakar gida tana kashe wutar girkin data gama, wani yaro yayi sallama, Inno ta amsa, yaron yace

"Wae Alhaji wadata yace a masa iso wajen Inno" Inno ta saki murmushi tace

"Eyyah, Alhaji wadata.. Ce masa ya shigo, yanzu kam aeya zama d'an gida" daga haka ta juya cikin d'aki ta d'auko mayafi, shima yaron ya juya ya fita, wajen minti 2 sega Alhaji wadata ya shigo da sallama fuskarsa d'auke da murmushi, Inno fad'i take

"Lale marhabin da surukina..barka da zuwa" ta fad'a tana gyara masa zaman tabarmar, ya 'karasa ya zauna hannunsa ri'ke da babbar rigarsa, seda ya gama zama sannan yace

"Barka da dare, mun sameku lafiya" Inno tayi murmushi tace

"Lafiya 'kalau, se shirye_shiryen biki kuma"

"Gaskiyane..Allah ya taemaka..dama akan abinda ya kawoni kenan" Alhaji wadata ya fad'a yana gyara zama, Inno tace

"Tohh..Allah yasa lafiya ?

"Lafiya lau.. Dama nazo ne inji ko akwae wani abu da kuke bu'kata, saboda zanje Kaduna ne inyi kwana 2, toh nasan kona tambayi ita Azrah d'in..ba fad'amin zatayi ba shiyasa nace bari nazo wajenki" Murmushi Inno tayi tace

"Laaa..kaji kuma, ae ita haka take ba dae kunya ba" Alhaji wadata yace

"Hakan nada kyau..sannan zancen lefe, ita zan bawa kud'in ta had'o ko kuwa in had'o mata ? Murmushin ya'ke Inno tayi tace

"Ahhh kaeda zakayi tafiya kuma..a'ah...a'ah kawae ka bayarda kud'in se in shiga kasuwa in had'o mata masu kyau"

"Toh shikenan..dama akan maganar kenan" Alhaji wadata ya fad'a yana zura hannu a aljihu ya fito da wasu damin kud'i ya ajjiye yace

"Gashi..se a had'o d'in, sannan kuma a 'karasa wasu abubuwan dae da ba'a rasa ba" daga haka ya mi'ke, Inno ta kalli uban kud'in daya ajiye tana had'iye wani uban yawu, sannan itama ta mi'ke tana fad'in

"Har zaka tafi kuma ? Yace

"Wallahi kuwa, a gaeda Malam d'in idan ya dawo"

"Toh zeji kuwa, angode Allah ya 'kara arzi'ki"

"Ameen" ya fad'a yana ficewa daga gidan, Inno ta dawo ta d'auki kud'in tana kallo kamar idanunta zasu fad'o, lallae basu yi raenon banza ba, dan kuwa gashi se kur6ar romon damokrad'iyya sukeyi... Shirye_shiryen biki fa ya kankama dan kuwa har an bugo kati an fara rabo, ita dae Azrah jinta take kamar wadda aka sauyata, kallan komae take kamar a mafarki, haka dae take komae sakaka kamar mara lafiya, siyadda abinci kuwa ta daena shi tun bayan da aka tsaeda ranar bikin, 'bangaren Inno kuwa babu wani lefe data had'owa Azrah, tadae shiga kasuwa ta siyo mata atamfofi 2 da less 1 da kuma shadda 1, se wasu barbad'ad'd'un kayan kwalliya data siyo kamar na wata yarinya 'karama bana amarya ba, se kayan bacci data siyo suma guda 2, da takalma da jaka da mayafi guda bibbiyu, daga haka tace ba za'ayi 6arna ba, kayan sun isa haka... Ranar wata asabar wadda ta kasance daga ita se kuma ta biki ta shirya cikin wata kod'ad'd'iyar atamfarta amma fa gall take a wanke fess_fess, ta zura hijab d'inta sannan ta d'auki katin bikin ta fito tsakar gida, bata samu Inno a tsakar gidan ba dan haka ta d'an bud'e murya tace

"Na tafi" Inno data jiyo ta ta fito daga d'akin tana kallanta

"Ina zakije ? Seta d'anyi 'kasa da kanta tace

"Zan kaewa abokan sana'ata katin biki ne, kada suga kamar ban kyauta musu ba" Inno ta jinjina kae kafin tace

"Yayi" Azrah ta juya ta fita daga gidan, tunda ta fita se taga kamar yanayin yadda ake kallanta ya chanja, kamar duk inda tabi kallanta ake, duk se taji ta a tsarge, a haka dae harta "karasa bakin company, tana tafiya a hankali kamar yadda ta saba ta 'karasa wajen wani yaro wanda tasu tafi zuwa 1, yana ganinta ya mi'ke da murmushi kan fuskarsa yace

"Kwana 2 kin gujemu, kodae munyi miki laefi ne" Seta 'ka'kalo murmushi tace

"Haba..haba..nikam babu wani laefi da kukamin" yace

"Toh madallah, Allah yasa dae lafiya ce ta 'boyeki" Nan da nan murmushin kan fuskarta ya d'auke seta ciro hannunta dake cikin hijab ta mi'ka masa katinan dake hannunta tace

"Gashi.., ka bawa duk wanda ya dace, sannan don Allah karka manta akwae wani Irfan a cikin companyn nan, ka bashi don Allah" kallan katinan yayi sannan ya kalleta yana murmushi yace

"Masha Allah, Allah ya sanya alkhaeri, Allah yasa gidan zamanki ne" ita dae batace komae ba, se can kuma tace

"Bari na tafi"

"Toh amarsusu.." Ya fad'a yana murmushi, daga haka ta juya..... Tafiyarta da wajen mintuna 10, wata mota sabuwa dall ta shawo layin da companyn ke ciki, Irfan ke driving yayinda Don ke zaune a kujerar me zaman banza, yana zuwa dae_dae gate d'in me gadi ya wangale masa gate d'in, yana shirin shiga, yaji ana fad'in kasancewar glass d'in 'barinsa a zuge yake

"Yalla6ae, an bani sa'ko na baka" jin haka ya sanya Irfan d'an dakatawa kad'an, yana kallan Don daya kwantar da kansa kan kujera idanunsa a lumshe, yaron ya 'karaso ya mi'kawa Irfan katin yace

"Wata yarinya fara me zama anan tana saeda abinci ? Itace tace a baka" Irfan ya kar6a zuciyarsa na harbawa ya ajiye gefe, sannan yaja motar zuwa cikin companyn, yana gama parking ya d'auki katin ya fara karantawa

"Damn it" ya fad'a yana buga hannunsa kan steering motar, Dae_dae lokacin da Don ya bud'e lumsassun idanunsa ya kalleshi sedae bece komae ba, Irfan yace ransa a had'e

"Gaskiya an kwafsa min wallahi, dana sani banbi komae a hankali ba" Yana gama fad'a ya juyo ya kalli Don

"Wae kasan meya faru kuwa ? Kasan katin auren waye a hannuna ? 'Daga kafad'a Don yayi kafin a hankali ya furta

"Noo..bansani ba and banaso na sani" daga haka ya sauka daga motar dan dama tun d'azu 1 daga cikin bodyguard d'in ya bud'e masa, binsa da kallo Irfan yayi yana 'kara buga hannunsa akan steering motar kafin yace

"Shettt"


.........Dawowarta kenan daga wani gidan 'kawar Inno data aeketa zata kar6o mata sa'ko, tafiya take tana tunanin da yanzu ya aureta, a gefen titi take tafiyar har bata san ta hau kan titi ba, Irfan yaja wani uban birki ji kake 'kuuuuu, wanda hakan yasa sukayi gaba sannan suka koma baya, Don ya d'ago a fusace yana kallan abinda ya saka Irfan d'in taka birki, tana tsaye a gaban motar hannayenta kare a fuskarta dan kuwa ta riga da ta sada'kar motar nan seta taka ta, sedae me se kuma taji shiru, hakan yasa ta d'ago kyawawan brown eyes d'inta da suka d'an rine saboda yadda ta tsorata, 'kirjinta na bugawa ta kalli motar, Don ya 'kan'kance idanunsa yana kallan ta, idan be manta ba wannan yarinyar itace ta shigo company ranar nan, yanzu kuma gata anan ta hau kan titi, anya kanta d'aya kuwa ?... Tana nan tsaye Irfan ya fito daga motar yana kallan ta yace

"Babe..ina kika shiga kwana 2 ? Me kike akan titi haka ? Seta d'ago ta kalleshi ba tare da tace komae ba dan kuwa ita kad'ae tasan yadda zuciyarta take bugawa, ganin kamar ma bata tare da shi ya sanyashi hura mata iska a idanunta, se tayi firgigit tana sake kallansa yace

"Ashe bikinki za'ayi ? Seta jinjina kae kawae, yace

"Toh sakamin numberki zamuyi waya ko kafin bikin ne, inaso mu had'u" ya fad'a yana ciro wayarsa daga aljihun rigar jikinsa, seta kalli wayar ta kalleshi tana mamakin yadda abinda ya mi'ko matan ya zama waya, sannan ta girgiza kae tace a sanyaye

"Bani da waya" kafin ya 'kara cewa komae, suka ji wani jahilin horn wanda ya sanya dukkansu seda suka juya, Azrah ta kalli wanda ke cikin motar tace a zuciyarta

"Yawwah koda naji mana, Ashe wannan bugaggen ne" ita kam bata san yadda akayi mutumin kirki kamar Irfan yake abota da irin wannan mutumin ba.. Irfan ya katse mata tunani ta hanyar fad'in

"Se anjima babe, nafi kowa sanin iskancin Don, ba 'karamin aekinsa bane ya tafi ya barni a wajen nan ba" ya fad'a yana wucewa da sauri, bata sake cewa komae ba, tazo ta wuce ta gefen motar ta cigaba da tafiya gida.... Irfan na shiga motar ya kulle 'kofar yace

"Don..kasan wae wannan yarinyar za'a aurar ? Da kamar baze bawa al'amarin muhimmanci ba tunda be shafeshi ba, amma seya kalli Irfan, Irfan ya jinjina kae yace

"Wallahi kuwa, wae auranta za'ayi, katin bikin ne aka bani ranar nan" Wata dariya da ban ta6a ganin Don yayi ba ya fashe da ita, kamar bashi ba, kawae sena tsaya ina kallan ikon Allah, yadda dariyar ta masa kyau sosae, daya san yadda take masa kyau kamar haka, daya dinga yinta koda ba koda yaushe ba, shi dae Irfan kallansa kawae yake, se can yaji yace

"Wannan abin ? Ita za'a aurar ? Lallae kuwa na yadda en 'kauye ba abinda ba zasu aekata ba, yoh wannan inba raeno ba..ae shi aka kaewa mijin yayi, dan dae am very sure wannan ba lallae tasan yadda ake girki ba ballantana ta kula da gida" Don ya fad'a yana sauke numfashi gami da sake sakin dariya, Irfan yace

"Kaefa d'an iska ne wallahi, meye abin dariya anan, ae sedae idan mijin nata beso ba wallahi, amma baka ganta bane cute babe, wallahi daga ganinta zazzafa ce" A hankali fuskar Don ta sauya daga dariyar da yake zuwa asalin yadda take yace

"Kasan bansan shashanci Irfan, pls ka wuce mu tafi, enough is enough"Irfan be sake cewa komae ba yaja motar yabar wajen...

....Toh Inno fa hae'kan shirye_shirye ake na biki babu kama hannun yaro, haka Malam ma, ana i gobe d'aurin aure Malam da Inno suna zaune a tsakar gida suna hira, Malam ya kalli Inno yace

"Wae kina nufin ba za'a sanar da ilyasu zancen bikin nan ba ? Ta6e baki Inno tayi tace

"Meze mana idan yazo Malam ? Kaga don Allah rabu dashi" kafin Malam yace komae sega sallamar wani yaro yana fad'in

"Wae ana sallama da Malam Habu" baban ilyasu ya kalli yaron yace

"Inji waye ? Yaron ya girgiza kae

"A'ah bansan shi ba" Malam ya kalli Inno bece komae ba, se Inno ta kalli yaron tace

"Je kace yana zuwa" daga haka yaron ya juya ya fita, Malam yace

"Toh waye kuma yake sallama da daren nan haka ? Inno tace

"Ae dae kaje kaji koh ? Yace

"Hakane" ya fad'a yana mi'kewa ya zura takalminsa ya wuce 'kofar gidan nasa...............

Innocent Gee.......✍️




https://chat.whatsapp.com/CNoLsXVGhSe9XZXghGxjZV


*♡☆SANADIN KADDARATA☆♡*

( _Is similar to *DON ADNAN's* destiny_ )




⚡ *THE BEGINNING*⚡




STORY AND WRITTEN

BY

*♡ MHIZ INNOCENT ♡*


..Sanadin 'kaddarata na kudi ne akan N300, da zarar mun gama free pages zamu cigaba da tafiya ne da wadanda sukayi payment kawae, zan ajiye muku yadda zakuyi payment din a last page na The Beginning..


Free page_12

______Wlh comments d'inku na jiya sun bani dariya 😂😂 wato haka Alhaji wadata yke d baqin jini ashe, Anyway dae ina jin dad'in comments naku, Allah y bar qauna 😻

____Da mamaki Baban Ilyasu ke kallan malam Yusuf (maqocinsa), seya 'karasa ya mi'ka masa hannu suka gaesa yana kallan yanayinsa kafin yayi 'karfin halin fad'in

"Malam yusuf lafiya dae koh?" Ya fad'a har lokacin kallansa yake, Malam Yusuf yace

"Da alama baka san meya faru ba" Jikin baban ilyasu se yayi sanyi haka kawae amma se yayi 'karfin halin fad'in

"Meya faru? Malam Yusuf yace

"Ha'ki'ka komae se Allah ya nufa yake yiwuwa, yanzu yanzu nan na fito zanje kemis (chemist) naga wata mota irin ta d'akko gawar nan a bakin layin nan, ashe ashe kuma Alhaji wadata lokaci yayi, ya samu mummunan hatsari akan hanyarsa ta shigowa kano, kafin ma su 'karaso nan ya rasu" Tunda ya fara magana baban ilyasu ke kallansa jikinsa na wani irin rawa kamar wanda zazza6i ke shirin kamawa ya gaza furta komae, Malam Yusuf yace

"Dama zuwa nayi na sanar dakae saboda gobe da wurwuri za'a tafi kaeshi, dan nasan ba lallae a samu wanda ze sanar damu ba tunda harta drivern nasa ya raunata sosae, Allah yaji 'kansa" ya fad'a yana kallan yadda malam habun ya rud'e a lokaci guda, se a lokacin baban ilyasu ya iya bud'e bakinsa da yayi masa nauyi ya furta

"Innalillahi wa inna ilaehi raji'un, Allah yaji 'kan rae"

"Ameen" amalam yusuf ya fad'a yana juyawa, baban ilyasu ya juya a sanyaye ya shigo gidan kamar mara laka, Inno da har lokacin take zaune akan tabarma ta kalli yadda taga malam d'in ya shigo jikinsa a sanyaye, seta mi'ke tana fad'in

"Lafiya kuwa malam? Seya cigaba da tahowa yana kallanta kafin yace cikin sanyi

"Alhaji wadata ya rasu" Da wani matu'kar tashin hankali gami da mamaki Inno ke kallan baban ilyasun, kafin a hankali ta tafi baya luu ta zube a wajen a tayi zaman da6aro tana dafe kanta fad'i take

"Innalillahi wa inna ilaehi raji'un, mun shiga 3, Alhaji wadata ya rasu?.... Tana kwance a d'akin nata ta nannad'e jikinta da hijab d'inta saboda wani sanyi da takeji yana ratsata alamar zazza6i ke shirin rufeta, tunda ta bud'e idanunta ranar juma'ar ta tabbatar da cewa gobe fa za'a d'aura mata aure da Alhaji wadata ta kasa sukuni, gaba d'aya jikinta a sanyaye yake da 'kyar take motsawa ko nan da can, haka kawae take jin fad'uwar gaba tun d'azun, gashi kuma zazza6i yana shirin rufeta, kamar daga sama ta jiyo maganar Inno wanda hakan ya sanyata mi'kewa zaune akan 'kafafunta tana rarraba idanu a cikin d'akin haka 'kirjinta na wani irin bugawa, bata san lokacin data mi'ke ta yaye labulen d'akin ba ta fito tsakar gidan tana kallan Inno da Malam wad'anda ko basu maemaeta abinda ya faru ba yanayinsu kad'ae ya isa ya tabbatar mata da abinda kunnuwanta suka jiye mata, Inno ta d'ago ta watsa mata jajayen idanunta sannan tace tana kallan baban ilyasu

"Nikam Allah yasa ba wani abun ke tare da wannan yarinyar nan ba, tunda take ba wanda ya ta6a cewa yana sonta se Alhaji wadata daya cije ya nace akan sonta yake da aure gashi kuma ya mutu, anya kuwa malam? Ta fad'a tana share 'kwallar idanunta, tunda ta fara magana Azrah ke kallanta da narkakkun idanunta babu ko 'kiftawa, so take ta tantance abinda kunnuwan nata suke jiye mata, sedae ina..zuciyarta ta'ki bata wannan damar, seta lumshe idanunta a hankali wasu zafafan hawaye suna sauka akan kuncinta kafin ta juya da gudu kae tsaye ta fad'a d'akinta ta fashe da wani marayan kuka, wanda tasan babu me lallashinta, meyasa a koda yaushe wani abin kirki baya shiga tsakaninta da Inno? Kullum sedae zargin sharri ne ke shiga tsakaninsu? Wannan wace irin rayuwace...... Washe_gari aka kae Alhaji wadata makwancinsa, malam habu ya zauna hadda shi akayi zaman makokin, seda akayi uku sannan ya dena zama, toh mudae sedae muce Allah yaji 'kan Alhaji wadata da rahama....



............Kwana 3 da rasuwar Alhaji wadata wajen 'karfe 4 ne na yamma Inno na zaune a tsakar gida tana tsintar alkama, yayinda Azrah ke cikin d'aki kamar koda yaushe da yanzu hakan ya zame mata jiki, har yanzu ji take kamar ba Alhaji wadatan ne ya rasu ba, tana tunanin ranar da suka had'u na 'karshe ranar da yazo yi mata sallama...sallamar da akayi a tsakar gida ne ya sanyata mi'kewa dama fita zatayi dan tun d'azu wata yarinya tazo akan kiranta da hauwa'u take zasuje wata dubiyar er ajinsu, seta mi'ke ta fito tsakar gidan, dae_dae lokacin da wasu dattijae su 2 suka 'karasa shigowa gidan, ta amsa sallamartasu ba tare data kallesu ba, ta kalli Inno tana fad'in

"Bari naje" Bata jira Innon tace komae ba ta wuce, duka matan suka bita da kallo harta fice, Inno tace tana ajje farantin hannunta

"Lale marhabin ku shigo mana" Se suka 'karaso suka nemi waje suka zauna, Inno na kallansu itama ta nemi waje ta zauna, Hajja kaltume tabi tsakar gidan nasu da kallo kafin ta dawo da kallanta wajensu tace

"Sannunku da zuwa" Gaaje tace

"Yawwah habee, kin gammu bagatatan koh ? Inno tace

"Ahh haba haba gaaje ae naga bake kad'ae bace, naga tafe kike da ba'kuwa" gaaje ta gyara zama tace

"Qwarae kuwa, toh ki nutsu ki sauraremu ta wajena, alkhaeri ne ya biyoki har cikin gidanki" Inno ta washe baki tana kallan matar da har lokacin take bin Inno da kuma gidan da kallo kafin tace

"Toh masha Allah, meya faru gaaje? Gaaje ta kalli hajja kaltume tace

"Hajiya bismillah, wannan ce mari'kiyarta ta" hajja kaltume ta ajje numfashi kafin ta gyara zama tace tana kallan Inno

"Dama magana ce akan er wajenki"

"Toh..toh Allah yasa lafiya" Inno ta fad'a tana 'kara gyara zama, hajja kaltume tace

"Lafiya ce ta kawomu, ina yarinyar take? Inno tace

"Wallahi yanzu ta fita, afff !! Ae kamar ma kun had'u sanda kuka shigo" gaaje tace

"Qwarae kuwa hajiya, itace wadda muka gani sanda zamu shigo tana 'ko'karin fita" Hajja kaltume ta kalli gaaje tana tuno kyakykyawar farar yarinyar da suka gani, dukda bata bari ma ta ganta sosae ba, amma ko a kallo 1 data mata ta gano zallar kyaun dake tattare da yarinyar, ta jinjina kae kafin tace

"Lallae, wannan ce yarinyar? Tayi sosae" seta maeda kallanta kan Inno wadda take ta kallanta tun d'azu tace

"Wato akwae wata uwar d'akina tana neman 'karamar yarinya haka dae kamar wannan yarinyar taki, toh shiyasa na nemi wata ma'kociyata itace ta had'ani da gaaje, shiyasa kika gammu tare, and naaga yarinya tayi, abinda ya rage yanzu ita uwar d'akin nawa zatazo ta ganta sannan ta miki bayani akan komae, ni yanzu dama aekina kawae shine samo yarinyar, ki jira zuwanta cikin satin nan" Inno dama tun d'azu da matar ta shigo take kallanta dan daga ganin shigarta ta fahimci akwae kaya, seta saki murmushi tana gyara zama

"Ahh tohh..toh masha Allah, Allah ya kawota lafiya, ina jiranta" Hajja kaltume ta zuge zip d'in jakarta ta fito da 10k ta ajjiye a gaban Inno tace

"Gashi nan, idan tazo zakiji cikakken bayani" Inno ta maeda dubanta kan gaaje tace

"Nagode 'kwarae da gaske gaaje, Allah ya bar zumunci" gaaje ta kalli kud'in dake ajjiye kan tabarmar sannan ta kalli Inno tace cikin er daburcewa

"Ahh ba komae, ae ni ina sonki da alkhaeri" Daga haka hajja kaltume ta mi'ke tana fad'in

"Se kin jimu" dukkansu mi'kewa sukayi, Inno ta kalli hajja kaltume tace

"Nagode fa 'kwarae hajiya, sekun zo d'in" Gaaje tace

"Toh se kin jini" daga haka suka fice daga gidan, Inno ta dawo cikin gidan tana d'aukar kud'in, fuskarta d'auke da mad'aukakin murmushi, lallae ita kam akwaeta da sa'a, daga wannan se wannan? "Toh akan me aka baki wannan kud'in? Wani 6angare na zuciyarta ya sa'ka mata hakan, se kuma a lokacin ta fara tunanin meye dalilin da yasa matar nan tazo hadda bata kud'i duk akan Azrah ? Toh koma dae menene ita kam ta dafe dubu goma saboda haka tana nan tana jiran ranar da zasu dawo suyi mata cikakken bayanin....


..........Wayarta dake 'kara kan kujerar d'akin ta kalla, seta kalli Yakumbo tace

"Yakumbo bari naje ciki"

"Toh hadeeza zaki koma? Yakumbo ta fad'a tana kallanta, Mami tace

"Ehh, bari naje, Asha ruwa lafiya" daga haka ta mi'ke ta fito daga d'akin, kae tsaye ta wuce part d'inta, bata tsaya ko'ina ba se bedroom d'inta, tana shiga ta kulle 'kofar sannan ta lalubo number hajja kaltume ta danna kira, kira 1_2 ta d'aga, Mami tace

"Ya ake ciki? Hajja kaltume tace

"Ae wato hajiya hadeeza ki saka ranki fess a inuwa, na samo miki zankad'ed'iyar yarinya kyakykyawa kamar ita tayi kanta" Mami ta gyara zama akan gadon da take tace

"Really?"

"Sure, wallahi tayi, abinda ya rage kawae kije gidan ki ganta da idanunki sannan ki musu bayanin 'kudurinki" Sauke ajiyar zuciya Mami tayi kafin tace

"Alright, yaushe kike ganin zamuje?

"Ko gobe ma, dan da ganin yanayin matar nan koda wane irin 'kuduri akaje mata zata amince dan naga yadda jikinta yake 'bari akan d'an kud'in dana bata" Hajja kaltume ta fad'a, Mami tace

"Good, aekinki na kyau, In Sha Allah zuwa jibi se muje" hajja kaltume tace

"Madallah, ina jiranki hajiyata" daga haka sukayi sallama, Mami bata ajiye wayar hannunta ba seta lalubo number Don ta kirashi, kiran farko be d'aga ba se ana 2 ya d'aga ya kara a kunnensa Mami tace

"Kana ina Son? Seya d'an lumshe idanunsa kad'an kamin yace

"Zuwa anjima zan dawo"

"Ohk idan ka shigo gidan nan, make sure ka fara shigowa part d'in nan" Seya bud'e idanunsa sosae kamin yace

"Wani abu?

"Kae dae se ka shigo uhmm" jinjina kae yayi kamar yana ganinta, sannan ya kalli sameer da shigowarsa office d'in kenan, shima sameer d'in kallansa yake kafin yace komae sameer ya rigashi fad'in

"Hope komae normal uhmm? Ya lumshe idanu sannan ya bud'e a lokaci guda yana kallan sameer

"Yeah, ka dawo lafiya? Sameer yaja kujera ya zauna sannan yace

"Ehh..alhamdulillahi, ya aekin? 'Dan d'aga kafad'a kad'an Don yayi sannan yace

"Alhamdulillah" daga haka sameer ya shiga kora masa jawabae akan tafiyar da yayi, shi kuma yana saurararsa daki_daki, wani lokacin ya amsa wani lokacin kuma ya jinjina kae.... 'Bangaren Mami kuwa tana zaune parlour tana kallo aka kira wayarta, seta 'karasa ta d'auki wayar tana kallan me kiran, tana d'agawa Momy tace

"Sannu hadeeza" Mami tace tana neman waje ta zauna

"Yawwah Yaya Ameena, kina lafiya?

"Ahh nikam lafiya lau nake, sedae ko d'iyarki" Momy ta fad'a cikin gatse, Mami tace

"Subhanallahi, wani abu ya samu Simrahn? Momy tace

"Uhmm, wato hadeeza na d'auka idan Simrah tana bu'katar wani abu se inda 'karfinki ya 'kare, amma se naga ashe ba haka bane, kamar kanki kawae kika sani" Mami ta sauke numfashi kafin tace

"Duk yadda kuke tunani ba haka abin yake ba Yaya Ameena, amma ki sake bani lokaci In Sha Allah zanyi wani abun akae"

"Haka dae, kullum abinda kike fad'i kenan" Mami tayi shiru tana sauraren Momyn, se can tace

"Ki dae sake bani lokaci" daga haka ta katse wayar tana furzar da iska daga bakinta, dae_dae lokacin Don ya shigo d'akin, sanye cikin riga samfurin parka ya sauko da hularta, kasancewar ana d'an sanyi ne a lokacin, Mami ta kalleshi da murmushi kan fuskarta, a hankali ya 'karasa ya zauna akan kujerar da Mamin ke kae, Mami na kallansa tace

"Barka da dawowa Son" Seya d'an murmusa kad'an yace

"Barka" tace

"Dawowarka kenan? Ya d'an murza goshinsa kafin yace

"Yeah" Mami ta gyara zama tace

"Zaka ci abinci ne? Ya yamutsa fuska yana shafa cikinsa

"Noo..meya faru? Mami ta gyara zama tana kallansa kafin ta sauke numfashi tace

"Adnan.." Besan sanda ya d'ago ya kalleta ba jin yadda ta ambaci sunansa, dan shi kansa baze iya tuna when last da Mamin ta kirashi da aenahin sunansa ba, ganin ya bata dukkan hankalinsa ya sanyata fad'in

"Son.. Zaka iya auren Simrah? Seya

Please Login or Register in order to submit comment