Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[13/12, 10:25 am] Ashanty 💞🌙: 💎𝐌𝐔𝐋𝐊𝐈💎

👑
By

Ashanty love.
(M Afnan)

ASHANTY©AREWABOOKS.COM


✯D͟A͟Z͟Z͟L͟I͟N͟G͟ S͟✯T͟✯R͟'✯W͟R͟I͟T͟E͟R͟S͟✯


Gargaɗi
Ban yarda a juyar min da littafi ta ko wace siga ba ba tare da iznina ba.


✍️𝑩𝒊𝒔𝒎𝒊𝒍𝒍𝒂𝒉𝒊 𝒓𝒂𝒉𝒎𝒂𝒏𝒖𝒏 𝒓𝒂𝒉𝒊𝒎.


P 1/2


Sauri nake kaman zan fadi saboda gudun dukan malam Halliru. Sam bashi da mutunci idan a kan duka ne. Ko ubanki ne ya mutum idan baki kawo masa uzuri kwakkwara ba ki yi fashin makaranta zagewa yake ya zane mutum bare kuma ka makara ko na minti daya ne. Tun daga nase na hango dalibai yan makara durƙushe gaban sa da sharɓeɓiyar duruna sai haƙuri suke bashi wasu har sun fara sharar hawaye tun ma bai taɓa su ba. Matsanan cin faɗuwa gabana ya ke na tsani abunda zai tabamin lafiyar jiki duk da kuwa idan duka ne ya zamemin sabu ,idan shi bai dake ni ba to Baba Lantana za ta yi har ya zama duk irin dukan da za'a min bana kuka,wannan rashin kukan da nake ko reacting nasan ba karamin ciwo yake masa ba ni kuma naki bashi satisfaction d'in da yake nema. Duk irin uzurin da zan kawo masa bazai hana ya fasa duka na ba na lura har so yake yaga na makara dan kawai ya dake ni. Duk ranan kuwa dana zo da wuri toh ya dinga sunturi cikin ajin namu ko zaiyi kuskuran kamamu munyi wani abu da zaisa ya dake mu. Mugun murmushi ya yi hango ni da ya yi nabi sawun ƴan makara. Inda nake durƙushe ya tako

"Yau kuma wane uzuri gare ki?"

Duk da nasan cewa ba yarda zai yi da abunda zance ba ban fasa ɗago kai na kalle shi ba ,abunda ban iya ba shi ne karya duk ɗacin abu sai na faɗe shi.

"Baba lantana ce ta aike ni na kai mata niƙa kuma da naje sai na tarar da layi"

"Baba Lantana kaza,Baba Lantata kaza. Ita bata sanin lokacin aike sai lokacin makaranta?"

Baki na zumɓura"toh nikam ban sani ba sai dai ko zaka tambaye ta"

"Rashin kunya za kimin?"

Ban bashi amsa ba na ɗauke kai na gefe . Dan tsabar mugunta da yazo kaina sai da ya yi min bulala goma a maimakon biyar da yake yi. Yana gamawa na kaɗe hannuna na shige aji. Ƙarfe biyar dai-dai muka tashi ban jira Sahiba ba dan yau ina da suyar awara. Shi kaɗai ne abunda nake samun y'anci idan nayi ciniki mai maiko to ranan zanci na koshi har sai na ture. Saboda haka nake ta zuba uban sauri dan naci burin awarar nan da muka kwana biyu ba muyi ba tun safe ban saka wani abuncin kirki a ciki na ba. A kofar gida na hango Baffa na zaune kan tabarma da ya saba zama a koda yaushe. Baffa na (Ridwan Mus'ab) dattijon mutum ne da a ƙalla ya doshi shekaru 57. Bashi da wata cikakkiyar lafiya saboda halin girma. Yana yawan fama da ciwon kafa shi yasa sau tari da sanda yake takawa. Baba Lantana abokiyar zaman Mama nace. Niɗin marainiyace dan uwata ta rasu tun bayan haihuwa ta. A yanda Kaka ke gayamin mu biyu kawai ta haifa akwai yayata da shekara biyu kawai ta yi a duniya Allah ya karb'i a bunsa. Har sun fidda rai samun wata haihuwar dan cikin farko ma saida ta shekara biyu kafin ta same shi,
sai kuma Allah ya basu cikina. Tana haihuwa ta ance ko ganina bata yiba Allah ya yi mata rasuwa. Da Mama na da Baffa na duk yan Abzunawa ne (NIGER). Baffa ya fito ahli mai girma suna da yawa shi ne na uku a gurin ne Kaka. Sai ya kasance suna da ɗan hali in mutum ya ɗan tasa sai a nema masa aiki Nigeria, kaman zaman Gadi, Derebanci da sauransu. Toh shi Baffa na sai aka samo masa Gadi anan jahar Gombe da a yanzu muke zaune cikin ta. Bayan samun da ya yi anan ɗin da karɓar da yake ganin Gomben ta masa ya dawo nan da zama. Wani hutu da ya koma gida Niger ne ya ga Mamana(Fateema Harun) dake da shekarun kuruciya a lokacin. Shekara biyu da Auren su ya dawo ya ƙara dawowa neman wani aikin ya ƙara samun gadi a nan ne ya haɗu da Baba Lantana suka yi aure. Yar maƙocin wani mai gadi ne da suke maƙota dashi. Shida iyalen sa suke zaune a gidan da yake gadi. Ganin farko tace duniya babu wanda take so sai shi. Mutuncin da dattakon Baban ta yasa ya amince mata bai tashi dawowa ba sai da auren Baba Lantana a kanshi. A lokacin Mamana nada tsohon ciki. Daga zuwan Baba Lantana ta amshe gidan dan ta girmewa Mamana. A yanzu haka yaran Baba Lantana Biyara akwai

Hadiza
Rabi
Ibrahim ,Baba lantana ta b'ata masa suna da Iro, kowa haka yake kiran sa Iro.
Rakiya
Sai autar su
Bilkisu.

Duk sunyi aure banda Iro da Bilkisu da muke sa'a ɗaya da ita . Yaran Hadiza uku, Rabi biyu, anma na biyun ya koma. sai Iro da Baffan mu ya tura shi karatu chan zaria . sherakun mu ɗaya da Bilkisu wata biyu kawai ta bani amma nike yin komai a gidan tana kwance ko cokali bata ɗauka sai dai a kawo mata. Wani irin shagwaɓa ta Baba Lantana ta yi saboda Bilkisu duk tafi sauran yaran ta kyau ita kaɗai ce tayo hasken Baffan mu da kuma gashin sa. Har wani kirari za kaji tana mata wato Bilkisu mai gadon zinare Mijinki sai sarki ko attajiri. A hanzarce na ƙarasa gaban sa na durƙusa ina yi masa sannu da gida. Murmushi ya yi min cike da so

"Kin taso Uwata?. (Sunan Kaka naci wato SAHLA) , sannun ki da dawowa, maza kije gida ki huta kici abinci Allah ya yi miki Albarka "
Cikin jindaɗi na amsa da "Amin" na shige gida. Bai taɓa sanin irin halin muguntar da Baba Lantana takemin ba nunawa take a kan idansa tamkar ita ta haifeni ,dani da ƴaƴanta duk ɗaya muke a gurin ta. Wannan salon kissar tata yasa ta ƙara samun matsayi mai girma a gunsa saboda sanda yaga tana nuna min. Yasan ina yin awara shima da maganganu da daraba ta shawo kansa ya barni dan sam baya son suyan awarar nan da nake a ƙofar gida ,ta fake da ace Bilkisu na da cikakkiyar lafiya babu abinda zata sa tace na mata suyar awara bare ya nuna mata cewar ba ita ta haifeni ba . Toh sai Allah yasa titi ya biyo ta layin namu baka rabon layin namu da samari a koda yaushe.

Kaka babu irin faɗan da bata yi ba a kan hakan har cewa ta yi idan shi bazai iya tsayawa a kaina ya jajir ce ba toh ita zata ɗauke ni na koma gurin ta can Niger da zama.tun wani hutu ne da tazo nan Gombe taga ina yin awara ta tada billi sai ta tafi dani. Nima naso binta ko na huta da jarabar Baba Lantana amma da yake akwai ta da iya kissa sai ta zauna tana kuka wai Kaka ta nuna mata matsayin ta ashe dama bata ɗauke ta a matsayin Uwata ba , yanda ta ɗauke ni tamkar ƴar data haifa bata taɓa banbance ni tsakanina da yaran ta. Iri-ire wannan kalamai ne ya sakarwa da Kaka gwiwa ta fasa tafiya dani da sharaɗin ba kullum zan dinga yi ba. A sati sau uku kawai nake yi. Laraba,Alhamis da kuma juma'a kafin ta tafi sai da ta tambayi dalilin da yasa Ita Bilkisu bata suyan awarar sai dai kullum tana kwance kaman kasa. Buɗar bakin Baba Lantana itama tace mata wai bata ishashiyar lafiya ne. Har yau kuma taki faɗan taƙamaiman wane irin ciwo ke damunta. Maganan dai ɗaya ce a koda yaushe bata da ishashiyar lafiya.

Tsakir gidan na tadda su. Bilkisu kwance kan tabarma tana danna waya kirar tencnor ƙarama da Baba lantana ta dage sai yayyen ta sun siya mata ita yar gatan su. dole a bata waya. da Baffa ya yi magana sai tace ai Bilkisu ta girme ni in an bata ba laifi bane tunda takai munzalin riƙewa,kuma ai ƴan uwan tane suka siya mata,dole ya haƙura ya ƙyale ta.
Can gafe Baba Lantanan ce ke kwashe awara data sauke a kan wuta. Sannu nayi mata nayi saurin shigewa d'akin mu na ajiye jakata na cire uniform na chanza zuwa riga da sket na atamfa da hijabi. Kai tsaye na d'auki kayan yaji na fara dakawa na fito waje na sami yaro ya fara fitomin da kayan suya ta.

"Gashi nan awarar dubu biyu da dari uku ce, ko guda d'aya ta bata sai kinci ubanki a gidan nan "

Ban amsa ba na kwashi kayan nayi waje . Wannan babatun nata baya hanani cin awara yanda naga dama idan na dawo ta jibgeni amma gobe bazai hana na k'ara ciba. Tun tana dukan tana zagin har ta daina sai ta daina bani abinci. Duk ranan da hakan ta faru ta babu ni a kwanan abincin dare, dama ba ci nake na koshi ba gani da shegen cin tsiya amma ba auki. Kaman ka bushe ni na fad'i. Shi yasa nake san yin awarar ko babu komai zanci na koshi bazan kwana da yunwa ba. Ina fitowa kuwa maza suka yi caa a gurin kowa da kuɗin sa a hannu. Daga mai ta hamsin,d'ari,biyu da sauran. Babu fashi duk kaskon dana sauke sai na ci d'aya ko biyu. Har Baffa dake can zaune kofar gida na zubawa a d'an plate na kai masa. Toh a gidan ba bashi ake ba sai tace wai bayanan aka fita da ita kuma kayan sana'a indai kullum za'a dinga d'ebar masa zai karya mata kasuwa,ita daga ita sai y'ar ta. Shi yasa idan na fito sai na tabbatar da na soya masa yanda zaici ya koshi. Gabansa na ajiye ya kalle ni da murmushi kan fuskarsa kana kallon ta kasan bada san ransa nake wannan Awarar ba fin karfin sa aka yi. Baya son yana ganin yanda samari ke layi a kaina.

"Allah ya yi miki Albarka Uwata"

Na amsa da "Amin" na koma gaban awara ta ina cigaba da sallaman mutane. Can gefe na naji hirar wasu samari dake kan layi. Hankali na baya kansu amma kalman Dan sarki Saif da naji na fita cikin hirar tasu yasa na kasa kunne ina saurara.

"Wai kaji labarin wannan hatsabin yaron sarki ya shigo garin kuwa?"

"Wai kana nufin KING AJ?"

"Shi fa, tantirin yazo Nigeria, jiya aka ce gaba d'aya masarauta basu yi barci ba suna gudun tashin hankali sa. Ni na rasa wane irin dan iskan mutum ne shi dan baza'a kirashi da yaro ba. A kalla fa ance zai doshi 30 amma kaga yaki yin hankali lamuran sa sai kara tabarbarewa suke. Kasan wancan zuwan da ya yi cewa aka yi wata Baiwa ta bige shi cikin rashin sani walh in kaga irin jini da majinan da aka ce ya had'a mata sai ka tausaya mata. Har kwanciya ta yi gadon asibiti bai barta ba saida ya yi sanadin barinsu garin Gombe gaba d'aya da dangin ta. Bashi da imani ko kaɗan wlh"

Mugun tsaki dayan yaja ya wani karkace kai gefe irin na gogaggun yan iska yana cewa"ina zaiyi imani ka manta waye shi ne?. AJ ne fa. Kasurgumin Dan iska bayahuden banza. Kaga kuwa zuciyar kafirai gareshi tunda har yanzu babu tabbas ya karb'i musulunci. Ga dai Baban sa Dattijon mutum mai tsanani tsoron Allah malinta ya gaje ta gaba da baya amma Allah ya had'ashi da yara fitinannu musamman ma AJ, ko da yake ai ance uwarsu ce Baturiya ta kuma ki yarda su karb'i musulunci duk irin sanda Maimartaba yake na ganin yaransa sun karb'i Addinin gaskiya. duk cikinsu AJ ne kawai yake zuwa gurin Uban nasu kuma shine karami cikin su shi kuma Maimartaba yake burin ganin ya gajeshi tunda shi kaɗai ne namiji cikin ya'yansa, shi yasa yake ke ta k'ok'arin wajen ganin yaron ya shiryu har aure naji an shirya yi masa da wata yar cousin din Maimartaba, amma zuwan sa ance bai bar kasar ba sai da ya tabbatar ya lalatawa yarinyar rayuwa ta hanyar yi mata ciki. Allah ya taimaka ance cikin ya zube zance aure kuma ya rushe."

Na ukun cikin su da tunda suka fara maganan bai tofa ba sai yanzu yace
"Ni kuwa kunga yana masifar burgeni. Mulki ya gajeshi ta uwa ta uba. Gaba da baya kenan tantiranci ai sai inda maina ya tsaya .wlh idan nike da gatan da Aj yake dashi sai nayi abunda yafi wanda yake. MULKI duniya ne wlh ka taka wanda ka ke so ,kayi abunda ranka keso babu uban da ya isa ya tsawatar ma musamman ma MULKI irin na AJ. Uba sarki Uwa sarauniya. Sarauniyar ma ta kasar waje ai sai dai kawai Allah ya yafe mana. Ni wai naji ana cewa ma kaman AJ d'in inkiya ne ake masa. Ainihin sunan ALEXANDER ALEX sunan da uwarsa ta rada masa kenan, J d'in kuma sunan sane na yanka da Maimartaba ya saka masa JABEER. Kaga sunan ya tashi AJ. Can abokan sa na waje ance suna kiran sa KING "

Oh gulma irin ta mutanen mu.ka take naka laifin ka hango na wani. Kalle su dai duk cikinsu babu mai shigar arziƙi amma na wani suke hange Allah ya kyauta yanzu mene abun burgewa kan wannan kedarin da suke fad'a?asthagfurulla, har yanzu babu wanda yake da tabbas ya karb'i musulunci ko A'a amma yana yawan zuwa Nigeria ganin ubansa duk cikin su,su uku shi kaɗai ke san Ubansu sauran sunki zuwa suna gudun zuwa dan basu san su rabi bak'ar fata sun kuma k'i jinjin talaka. Sai gashi sun fito daga tsatson bakin mutum wata kila da suna da hali sai sun chanza uba. K'aramin tsaki naja ina k'are musu kallo ta kasan ido. Kana ganin su kaga tantiran yan iska sunci wasu shegon kananan kaya ga wando anyi masa Assdown underwear duk a waje. Babu abunda yafi bani takaici irin gashin kansu. An tara uban gashi ya cukurkude babu kyan gani. An aske ta gefe da gefe an masa wani nannad'a cibiri-cibiri ya zubo gaban goshi. Harda mai kitso ma cikin su. Yoo ai dole ya burge su domin dai kallo d'aya zaka musu kaga tantiran yan iska kaman yanda suke kiran wani. Nima da shegen gulma da sa ido.

"Ya dai Sahla Baby har yanzu layin baizo kanmu bane. "

"Ta nawa za'a sa muku?"

"Ta dari shida mana Sahla Baby, har kin manta ne?"

Ban basu amsa ba na zuba musu ina k'ok'arin kulla musu yaji yaro da bai wuce shekara goma ba ya k'araso gurin.

"Aunty Sahla wai inji Baffan ki Awarar bata k'are bane?"

Juyawa nayi inda Baffan ke zaune gaba d'aya hankalinsa da nutsuwar sa yana kaina. Murmushi nayi nasan saboda wannan yan duniyan ya turo yaro. Kwanun awarar na kalla da bata wuce ta hamsin ba wani ya yi wuff ya mik'o kuɗi .

"Gashi ki bani ta ragowar data rage"

Karban kuɗin nayi na miƙawa samarin tasu a gurun suka hauci da yake akwai benci. Yaron na kalla da ke tsaye .

"Fara kwashe min kayan nan Imrana ka miƙa min su gida."

Saida muka gama kwashe kayan tas muka shige gida. Kaman ni take jira ina shiga hannu kawai ta miƙo na bata kuɗi. Dubu biyu na lale cis na bata. Bayan ta gama kirga kuɗin ta d'ago rai a bace tana kallo na.

" me ya samu chanjin d'ari ukun dake kai?"

Shiru nayi ban bata amsa ba. Ta taso a fusace ta zubamin rankwashi mai shegan zafi ta kama kunne na. Bilkisu dake kwance sai dariya take.

"Nace uban me ya samu chanjin d'ari ukun dake kai?,wato kin zama mai taurin kai ko?,duk dukan da zanyi da zagin da zanyi bazaki fasa sacemin awara ba, dan wannan sata ce tunda ba baki nayi ba. Za kici ubanki cinikin da ki ke yasa nake kyale ki amma zanyi maganin ki . Zan cire wannan shegon idan naki da suke kaman na mujiya tashi ki bani guri"

Tashi nayi na zumbura baki ina sosai kai dan rankwashin ya shige ni. Kaman yanda nayi zaton kuwa ba'a bani abinci ba nima kuma bansa rai ba dan naci na koshi a waje.Kayan jikina na cire na d'ora hijabi kan daurin kirjina na fito dan watsa ruwa. Duk da cewar dare ya yi amma garin dal yake da hasken farin wata da kuma fitolu da alhaji Maishinkafi yasa aka dasa layi-layi. Da yake lokacin zafi ne. Ruwan babu sanyi na watsa a gurguje na fito nayi sallan magriba. Ina kan dadduma ina tilawa a kayi kiran isha. Dan haka ina yin ishan na miƙe na kwanta kan katifarmu dake d'akin sai barci.
[13/12, 10:25 am] Ashanty 💞🌙: 💎𝐌𝐔𝐋𝐊𝐈💎

👑
By

Ashanty love.
(M Afnan)

Marubuciyar

NOOR
SILAH
KAIDIN MACE

& NOW

MULKI


ASHANTY©AREWABOOKS.COM


✯D͟A͟Z͟Z͟L͟I͟N͟G͟ S͟✯T͟✯R͟'✯W͟R͟I͟T͟E͟R͟S͟✯


P 3/4.


Baffan mu mutum ne da bai damu da ilimin boko ba sai na islama. Shi yasa kaf cikin mu babu wanda yake da ilimin boko amma akwai na addini. Sauka ta biyu duk da karancin shekarun da nake dasu ina shirin yin ta uku. Bilkisu ce har yanzu bata sauke ba amma babu wanda bai sauke ba cikin mu. Idan Baffa ya yi magana Baba Lantana tace yana takura mata. Kowa da irin tashi kwakwalwar itama za ta yi. Toh ta ina? makarantar ma da sai taga dama take zuwa. Ba abun mamaki bane idan aka ce har yanzu bata iya had'a baki ba. Sai dai kullum tana kwance ,da daddare sai ta raba dare tana hira da samari. Har mamaki take bani. Duka-duka nida ita shekara 17 muke ,amma yau ka ganta da wancan saurayin gobe ka ganta da wani. Kodan ta fini girman jiki ne shi yasa ake yi mata kallan mai shekaru tana da k'iba tayo Baba Lantana. Ni kuwa tsigarallahu sai tsayi babu laifi. baza'a kirani gajera ba ina da tsayi na daidai misali. Wani lokacin har mamakin cikar Kirjin Bilkisu nake. kirjinta a cike yake fam kaman wadda keda shekaru masu yawa. Ni kuwa nono na mitsi-mitsi ne kaman kwallon mangoro. Sai dai ina da hips kuguna a baje yake amma cikina a mugun shafe yake kaman bana cin abinci. Ina da dogon gashi mai santsin gaske da ko ribbon baya kamawa sai da dabara. Bani da haske. Bakuma zaka kirani bak'a ba bak'ina irin bakin nan ne mai shek'i.(brown skin) .ina da manyan ido da koda yaushe sai an tanka su ga kwayar idon tawa bak'a waluk da ita. Shi ne abu na farko da ake fara hangowa a tare dani. Ni mutum ce da ke masifar san hijabi. Gashi dai ba wani jikin kirkine dani ba amma in bansa hijabi ba sai naji kaman ina yawo tsirara. Ko barci bana iyawa saida hijab. Haka yake jawomin bakar magana gurin su Baba Lantana da Bilkisu.

"Abu kaman itace ko me take boyewa ohoo.? Ki bari masu abun boyewar su boye mana. Kina fama da wani kirji kaman kwallon mangoro"

Bana tankawa ,zaginsu kuma bai hanani sa hijab ba. Gadai Baffa na mutum da baisan karatun Boko amma nikam Allah ya jarrabeni dasan karatun Nasara. Ina so nayi ilimi mai zurfi na zama wata a duniyar. Kaji ana professar Sahla, ko Dr Sahla, ko lawyer Sahla,ko ..ko. ina da buri da yawa da basu da adadi,Shi yasa indai muka had'u da Sahiba sai nasa ta koya min kad'an daga cikin karatun Nasara. A yanzu nasan kalmomi kaman

Yes. Eh
Welcome. Barka da zuwa.
Hello. Sallama
Name. Suna
Goodbye. Sai anjima
Kaf ranakun nasansu da turanci. Wato Monday,Tuesday,Wednesday,Thursday, Friday, Saturday, Sunday.
Inka cire wannan babu abunda na sani game da harshen Nasara. Har sha'awa nake idan naga yara da uniform na makarantar boko. Ina da burin ganin nayi wannan ilimin ban kuma cire rai ba babu Abunda yafi karfin Ubangiji. Idan banyi ba toh dama baya cikin kaddarata ne.

Yau tunda na tashi ban zauna ba. Daga tace yi kaza sai tace yi kaza. Har Allah-Allah nake ayi sallan Azhar na tafi makaranta ko na huta . Anayin azahar kuwa nayi shirin makaranta na fito a sukwanne zan fice Allah ya taimake ni Baba Lantana ta shige banɗaki. Nayi wuf zan fice Bilkisu dake zaune tana fama da waya ta kwale baki

"Ina zakije bayan naji Baba na cewa zata aike ki gurin Hamisu ki karbo min d'inki na"

Mugun kallo na zuba mata mai dauke da harara.
"Kije da kan ki bazanje ba d'in."
Baki ta hangame "ni ke kewa rashin kunya?" Ina k'ok'arin mayar mata da martani naji muryar Baba Lantana dake k'ok'arin fitowa daga bayi. Tsabar masifa da jaraba tana bayin ma bata hak'ura da bala'i ba.

"Ki bari nazo nan na same ki Bilkisun ce take magana ki ke mayar mata?".

Harara na k'ara zuba mata nayi wuff na fice da gudu dan banga wanda ya isa hanani zuwa makaranta ba sai ikon Allah. Yau tunda naje makarantar na lura da cece kucen da ake sam na kasa fahimtar abunda ya jawo wannan surutu duk inda ka wuce za kaga an had'a karamin grp ana kuskus ko me ke faruwa a

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment