Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin dakin
Nasa.
Sai da Jarumi Salmanu ya yi sallar
issha kurma ya kammala 'yan addu'o'insa
sannan ya fito daga cikin dakin nasa.
Da fitowarsa cikin harabar gidan sai ya
hango Gimbiya Lamrita zaune a can nesa
AA Misau ke Magana
kadan kusa da bakin wani karamin Lambu
mai dauke da 'yan shuke-shuke.
Cikin nutsuwa Salmanu ya karasa inda
Lamrita take ya zauna da a kalla tazarar taku
uku sannan ya numfasa ya ce, "Ya ke wannan
'yar Sarki me ki ke dauke da shi a cikin ranki
wanda ki ke son ki bayyana mini?"
Sa'adda Lamrita taji wannan tarnbaya
sai ta yi gyaran murya sannan ta ce, "Da farko
dai ina son na baka shawara ne akan wannan
gasa da ka shiga ta kambun jarumtaka.
Ina son ka sani cewa yanzu ne fa za ka
sami makiya irin wadanda za subi kowacce
irin hanya don ganin sun sami nasara akanka,
kuma su ga bayanka.
Ba komai ne zai janyo hakan ba face
yanzu ne wannan gasa za ta kara tsamari da
tsawo tunda jaruman Gasar sun yi RAGAS,
wato Sarki Gurzalu da Jarumi Imhal, kuma
sun kwanta jinya. Babbar matsalar ita ce,
yanzu bamu san hukuncin da AIkalan gasar za
su yanke ba.
Shin an kori gasar su Sarki Gurzalu ke
nan ko kuwa za a basu dama ne har su gama
jinyarsu su ci gaba da wasan?"
Koda jin wannan batu sai Salmanu ya
yi murmushi ya ce, "Damgane da batun
sababbin makiya da zan yi a cikin wannan
gasa, ko kadan bana tsoronsu sabo da na
dogara da Ubangijina, kuma na san cewa Zai
kareni daga dukkan sharrinsu.
Abin da ban gane ba shi ne, dangane da
matsayin su Jarumi Imhal a cikin gasar, kuma
kamata ya yi ace mun yiwa Sarki Taryan
wannan tambaya.
Abin da na ke so da ke shi ne, ki ci
gaba da zama a kan matsayinki na Shugabata
wadda ta kawoni wannan gari, tunda dai babu
wanda ya san sirrinki face Sarki Taryan.
Abu daya da na ke zargin zai iya
faruwa shi ne, Jarumi imhal zai riga Sarki
Gurzalu samun lafiya, kuma ko yaushe zai iya
mikewa ya ci gaba da yin wannan gasa.
Ko ma dai menene zai faru yanzu
bamu da abin yi face sa ido da jiran lokaci".
Gama fadin hakan ke da wuya sai
Jarumi Salmanu mike tsaye ya tafi izuwa
dakin da aka yi masa masauki ya shige izuwa
ciki ya turo kofa ya rufe ya bar Gimbiya
Lamrita zaune a wajen tana tunani.
Sai da ta shafe 'yan dakiku a cilkin
wannan hali sannan ilama ta mike ta nufi
dakin nata ta shige tare da turo kofa.

SARKI GURZALU na zaune akan
gado Kuyangi biyu na tallafe da
bayansa, daya kuma na zaune a
gabansa tana bashi ruwan Magani a cikin
wani jan Kofi na zinare, sai ga wani hadimi
nasa ya shigo.
Hadimin ya zube kasa cikin biyayya
kansa na sunkuye ya ce, "Y ashugabana Sarki
Taryan ne ya zo domin ya dubaka"
Koda jin wannan batu sai fuskar Sarki
Gurzalu a fadada da murmushi ya ce, "Ma za
a bude masa kofa ya shigo".
Nan take Hadimin ya mike tsaye ya
juya ya fice.
Jim kadan sai gashi ya dawo Sarki
Taryan na biye da shi.
A wannan lokaci
Kuyangin sun
kwantar da Sarki Gurzalu akan gadon suna
dan gyara masa shimfidarsa.
Koda shigowar Sarki Taryan cikin
Turakar sai Kuyangin suka fice da sauri. Sarki
Taryan ya Karasa daf da Gadon ya zauna a
gele ya Rurawa Sarki Gurzalu idanu cikin
alamun tausayawa ya yi masa sannu sannan
ya ce, "Ya kai Abokina, yanzu me ka
yankewa kanka hukunci akan wannan gasa?
AA Misau ke Magana
Sa'adda Sarki Gurzalu yaji wannan
tambaya sai ya yi murmushi mai nuna rashin
gazawa ya ce, "Likitana ya gaya mini cewa a
Kalla sai na shafe wala uku a kwance ina jinya
sannan zan sami karfin jikina.
Abin da na ke so yanzu shi ne, nan da
cikar sati biyu zuwa uku zan koma Birnina
domin ba zan iya yin jinyar wata uku anan ba,
amma lallai bayan na warke zan dawo domin
na yi gumurzun karfe da Jarumi Imhal.
Ina so ka sa aci gaba da wannan gasa
har izuwa tsawon wannan lokaci, kuma ko
bana nan ka aika mini da sakamnakon
gumurzun wannan bakon Jarumi da Imhal. "
Sa'adda Sarki Gurzalu ya zo nan a
zancensa sai Sarki Taryan ya bushe da dariya
ya ce, "Ai babu wata dama da za ta sa Jarumi
Imhal da wannan bako su hadu a filin gasa
facc bayan kai da Imhal kun sake kafsawa
wanda ya yi nasara cikinku shi ne zai kafsa da
bakon Jarumi, domin haka dokar wasan take".
Koda jin wannan batu sai Sarki Gurzalu
va kamu da matukar farinciki ya yi wani
sannan ya ce.
guntun murmushi na murna
"Ashe ke nan dai burina zai cika akan Imhal"
Da jin haka sai Sarki Taryan ya sake
bushewa da dariya a karo na biyu ya ce, "Ya
kai Abokina, yanzu kana nufin kace nan da
cikar kwanaki goma sha hudu ko ashirin da
daya manzon da ka tura izuwa Birninka
domin ya gano maka labarin yarka Gimbiya
Lamrita ya dawo ke nan, kuma a sannan ne za
ka dauki matakan da ya kamata ka dauka
akanta?"
Koda jin wannan tambaya sai Sarki
Gurzalu ya kadu ainun, kuma ya kamu da
Tsananin mamaki bisa yadda aka yi Sarki
Taryan ya san wannan al'amari nasa wanda ya
shirya a sirrance ba tare da wani ya gani ko ya
ji ba.
Kawai sai Sarki Gurzalu ya yunkura
cikin matukar karfin hali duk da cewa yana
jin tsananin zogi da radadin ciwon da ke
jikinsa, take ya dubi Sarki Taryan ya bushe da
dariya, lokaci guda kuma ya turbune
fuska
ce. "ya kai Abokina ka yi sani cewa zai fi
kyau mu daina sa ido akan junanmu, domin
kowa ya gabatar da lamarinsa yadda ya ke so.
Kamar yadda ka tura Dakarunka a boye
cikin 6atar da kama suka duba gawar yata
don su tabbatar da cewar ta mutu da kuma
yadda a yau din nan ka bi bayan bakon
Jarumi da Gimbiya Lamrita domin ka karbo
Jarumi Imhal a hannunsu babu abin da ban
gani ba a jikin bangon dakin nan da iarfin
sihirin tsafi.
Ka ga ke nan bana bukatar dawowar
đan aikena daga Birnina na san cewa 'yata
tana nan cikin Birninka tare da Jarumi
Salmanu, kuma na san cewa a duniya yanzu
babu abin da ta sana sama da ni, domin ta
sami labarin yadda aka yi na hau kan Karagar
Mulki bayan na kashe dan uwana MahaifinJarumi Imhal.
Ni kuma AA Misau Anan nace Musu su duka Da Sarki Guzalu din da Taryan KIFI NA GANINKA MAI JAR KOMA hhhh

Zamu dakata anan saikuma wani lokaci zamu cigaba insha Allah

Admin
AA Misau ke Magana
WhatsApp group

https://chat.whatsapp.com/E0GMznXcaxwC0avNVdF30Q

Facebook page
https://www.facebook.com/profile.php?id=100063661782295RIJIYA GABA DUBU💕
Littafi Na Bakwai (7)🩸
Part C 💎
Na Abdulaziz Sani M Gini 🤴
Typing By AA Misau
✍️⭐⭐⭐

(Kucigaba da yi mana likes and comments domin samunsu akan lokaci)

Labari ya isowa Shagala cewa
Marubucin yaci gaba da cewa....
Mulki bayan na kashe dan uwana Mahaifin
Jarumi Imhal.
Na sani cewa ba zan hadu da 'yata ba
domin a yau din nan zan bar Birninka na tafi
izuwa nawa Birnin.
Sakon da za ka gayawa 'yata shi ne,
cikin biyu ta zabi đaya, ko dai ta hakura da
Jarumi Imhal ta zabeni ko kuma ita da Jarumi
Imhal din su rasa rayuwarsu gaba daya.
Sannan kaima jan kunnen da zan yi
maka guda daya ne; Kamar yadda na kawo
maka Jarumi Imbal da hannuna na sa ka
tsareshi a cikin gidan sarautarka to ka bani
kayana na tafi da shi ko kuma ka aika mini da
shi bayan ya sami lafiyar jikinsa, domin na
mayar da shi cikin Kurkukuna mai đauke da
masifafliyar RIJIYAR nan ta GABA DUBU!
Ba zan fito da shi ba har sai a ranar da
nima na warke sosai sannan mu dawo kasarka
mu yi gumurzun jarshe ni da shi na
KAMBUN JARUMTA.
Idan kuma kana ganin cewa za ka ci
amanata ko za ka yaudareni ko kuma za ka
iya cutar da ni to mu zuba mu gani! Kai kanka
ka san cewa ni da kai KAR TA SAN KAR
ne!"
Koda gama fadin hakan sai Sarki
Gurzalu ya koma ya kwanta akan Gadon ya
juyar da fuskarsa can gefe đaya.
Sarki Taryan ya mike tsaye yana kyalkyala
dariya amma mai dauke da yake sabo da
tsananin mamakin jin abin da bai taba zato ba.
Cikin jin izza da yarda da kai ya dubi
Sarki Gurzalu ya ce, "Ya kai Abokina, ka yi
sani cewa kai Sarki ne, kuma nima Sarki ne
babu yadda za a yi na so wani abu wanda zai
kawo karyewarka ko hallakarka.
Abin da na ke so kawai na shaida maka
shi ne kowanne mutum yana iya yin kuskure
a rayuwarsa, kuskuren da zai yi nadamarsa
har izuwa ranar karshe ta rayuwarsa.
Kuskurenka guda daya ne rak! a
rayuwa da ka aikata, abin da ya janyo
rugujewar soyayyar da ke tsakaninka da
yarka.
Babbar matsalar kuma ita ce, babu
yadda za ka iya gyara wannan kuskure, kuma
dole ne a karshe a cikin mutum biyun nan ka
kashe daya.
Ko dai ka kashe 'yarka, ko kuma ka
kashe Jarumi Imhal, amma ka sani cewa
kashe kowanne daga cikinsu matsala ne. Idan
ka kashe Imhal tamkar ka kara rura wutare
kiyayya ne tsakaninka da yarka, idan kuma
ka kashe 'yarka shi ke nan baka da sauran ya
magaji a duniya.
A matsayina na tsohon Abokinka,
shawara daya zan baka, ka gana da Jarumi
Imhal a sirrance ka sanar da shi cewa kaine ka
kashe Mahaifinsa da Mahaifiyarsa da zuri'arta
gaba daya, kuma ya yi kokarin daukar fansa
akanka idan zai iya, amma kana neman
alfarma guda daya a wajensa.
Alfarmar kuwa ita ce duk yadda zai yi
ya tankwara Lamrita ta janye gabar da take yi
ma ka, don kada ta mutu kokai ka mutu da
bakin cikinta.
A karshe ina mai tabbatar maka da
cewa zan rike amanarka na dawo maka da
Jarumi Imhal kamar yadda ka bukata, amma
ka iya takunka".
Koda Sarki Taryan yazo nan a zancensa
sai Sarki Gurzalu ya juyo da fuskarsa da sauri
kuma a fusace ya dakawa Sarki Taryan tsawa
yana mai tarar numfashinsa ya ce, "Ta ya ya
ka ke zaton zan iya neman wata alfarma a
wajen Bawana ina matsayin Sarkinsa?
Ka fice ka bani wuri! bana bukatar
wata shawara daga gareka!! Domin ba ka biyo
hanyar da zan iya aminta da kai ba!"
Koda jin haka sai Sarki Taryan ya yi
murmushi sannan ya juya ya fice daga cikin
AA Misau ke Magana
Turakar ransa a bace yana mai cewa a cikin
"Ai kowa ya kiji ba ya kỉ gani ba ".
ransa,
Fitar Sarki Taryan ke da wuya sai Sarki
Gurzalu ya sake yunkurawa ya mike zaune ya
kira sunan daya daga cikin Kuyangin da ke
kula da shi wacce ake kira SAHAIRA ya
dubeta ya ce, "Ma za ki je ki gayawa sauran
Dakaruna cewa su yi sauri su yi shirin tafiya.
Lallai na basu rabin sa'a kacal kowa ya gama
kintsawa".
Koda jin wannan batu saimamaki ya
karna Sahaira ta dubi Sarki Gurzalu cikin
alamun firgici da tsananin damuwa ta ce
"Haba ya shugabana, ya za ka ce mu yi taliya
alhalin kana cikin wannan hali?
Ka yi hakuri mana har izuwa sa'adda za
ka ji kwarin jikinka?"
A fusace Sarki ya dakawa Suhaira
ISawa, jikinta ya kama tsuma sabo da tsananin
Tsoro, ya ce, "Kin fini sanin halin da na ke ciki
ne?
To ki sani cewa idan na ci gaba da
Zama a wannan gari kuma a cikin wannan hali
zan iya rasa rayuwata".
Koda jin haka sai Sahaira ta mike da
sauri ta fice daga cikin dakin.
Tana fita ta fara yin kicibus da Likitan
Sarki, ta sanar da shi umarnin da Sarki ya
bayar.
Ta ke hankalin Likitan ya dugunzuma
ainun ya dimauce ya fada cikin Turakar, ita
kuma Sahaira ta nufi inda Dakarunsu suke da
sauran 'yan uwanta IHadiman Sarki Gurzalu.
Likitan na shiga Turakar ta Sarki
Gurzalu ya kame kamar Gunki sabo da
Tsananin mamaki bisa abin da ya gani.
Ba wani abu ya gani ba facc Sarki
Gurzalu a tsaye bisa kafafunsa biyu ya dogara
da Sandarsa ta Sarauta.
Nima Fa AA misau saida na dan razana naso dakatawa anan amma na daure naa cigaba🤓
A sanin Likitan ko Sarki Gurzalu zai
iya jarraba mikewa
Tsaye sai ya shafe a kallah
Kwanaki arba'in yana shan Magani, anma
gashi kwana uku kacal har ya fara iya
mikewar duk da ya tabbatar da cewar ko
kadan raunin da ke cikin nasa bai Soma
warkewa ba.
Ya yin da Sarki Gurzalu ya dago kai ya
vi arba da fuskar Likitansa wanda ya yi tsuru-
tsuru kamar ace kyat! ya fitra da gudu saho da
tsoro da marmaki sai ya yi murmushi ya
dubeshi ya ce, "Kwantar da hankalinka ya kai
babban Likita babu abin da zai sameni har mu
isa Birnina.
Tabbas na san cewa babu alamar wani
sauki a tare da raunin da ke jikina amma ina
So ka sani cewa na sami wannan sauki ne
Kawia ta haryar amfani da karfin sihirina,
amma ba saukine na zahiri ba.
Da wannan dama zan kiyaye dukkanin
dokokin da ka kafa mini na
rashin motsa
gabban jikina har izuwa lokacin da ka bani
umarni"
Koda jin wannan batu sai fuskar Likitan
ta fada da murmushi na samun nutsuwa da
kwanciyar hankali sabo da yanzu ya tabbatar
da cewar aikinsa ba zai baci ba.
Nan dai aka cigaba da shirye-shiryen
tafiya har aka kammala.
Ba tare da bata wani lokaci ba kuwa
aka sanya Sarki Gurzalu a cikin kcken
dokinsa Kuyangi biyu suka shiga ciki don
kula da shi.
Shugaban Dakarun nasa na gefen dama
na Keken Dokin bisa dokinsa.
A gefen hagu kuma Likitansa ne a
Zaune .
Sauran Dakarun da suke yiwa Sarki
Gurzalu rakiya a cikin wannan tafiya kuwa
sun kaisu dubu daya da dari biyu, don haka
sai suka rabu gida biyu, rabi suka tsaya a bayan Kcken Dokin Sarki, rabi kuma suna
gaba.
A hakasuka kama tafiya har suka fice
daga cikin Bìrnin gaba daya suka nausa izuwa
cikin dajin.

AL'AMARIN JARUMI Imhal
kuwa, lokacin da ya farfađo daga
dogon suman da ya yi sai ya tsinci
kansa a kwance akan wani luntsumemen
Gado cikin wani kasaitaccen daki wanda babu
abin da babu a cikinsa na jin dadin duniya.
A gefe đaya ga kayan Abinci iri-iri a
cikin Kwanuka bisa wani Tebur an jera gami
da Tambulan na Ruwa da Ruwan Inibi.
Koda ganin wannan al'amari sai Jarumi
Imhal ya kamu da matukar mamaki, domin
shi a saninsa kamata ya yi idan ya farka ya
tsinci kansa a cikin Kurkukun da aka saba
tsareshi.
"To yanZU mene ne daliin đa ya sa aka
karramashỉ aka kawoshi cikin wannan daki na
alfarma?" Amsar da ya kasa baiwa kansa kenan.
A dai-dai wannan lokaci ne yaji wata
irin azababbiyar yunwa ta kamashi tamkar an
yashe duk abin da ke cikin cikinsa.
Koda ya yunkura domin ya mike tsaye
ya tafi izuwa inda wannan Teburin cin abinci
yake sai yaji kamar zai mutubisa tsananin zafi
da zogin da yaji a cikinsa.
A firgice ya yaye rigar da ke jikinsa
sama kuma ya koma kan gadon da sauri ya
Zauna,
Nan take ya yi arba da babban raunin
da ke gefen cikinsa wanda tuni an dinkeshi.
Imhal ya daga kansa sama, take ya tuno
da karon karshe da suka yi shi da Sarki
Gurzalua sama, sa'adda Kowannensu ya sami
nasarar sukar dan uwansa da Takobi.
Koda ya gama wannan tunani sai
hankalin Jarumi Inhal ya dugunzuma ainun,
kuma zuciyarsa ta kama tafarfasa sabo da
tsananin bakinciki.
Abin da ya fara fado masa a rai shi ne
Gimbiya Lamrita.
Wai shin da gaske ne cewar Gimbiya
Lamrita ta nutu sakamakon gumurzun da
suka yí shi da ita?
Ta ya ya ma za a ce ta mutu alhalin shi
ya tabbatar da cewar bai kasheta ba da
hannunsa?
Kai! Abin la akwai rudani a cikinsa
tun da na ga hawaye na zuba a cikin idanun
Sarkí Gurzalu, Lallai na tabbatar da cewa da
Lamrita ba ta mutu ba, to babu abin da zai sa
Sarki Gurzalu yi ya wannan kuka.
ldan har Gimbiya Lamrita tana raye ba
Ta mutu ba mene ne matsayina a wajenta idan
har Sarki Gurzalu ya mutu sakamakon sukar
da na yi masa da takobina?
Lallai na tabbatar da cewa Gimbiya
Lamrita za ta kara tsananta gaba da tsanata ke
nan a rayuwarta fiye ma da ko yaushe
sakamakon kashe Mahaifinta.
Imhal na cikin wannan tunani ne
kwatsam! ya ji an turo kofar dakin da yake an
shigo.
Ya dago kansa da sauri ya yi arba da
wanda ya shigo.
Ba wani ne ya shigo ba face Sarki
Taryan tare da Jarumi Salmanu yana mai take
masa baya.
Koda Imhal da Salmanu suka hada
idanu sai kowannensu ya kasa kau da kansa
ga barin kallon daya.
Ba komai ne ya janyo haka ba face sun
taba haduwa da junansu kimanin shekaru uku
baya, amma sai kowannensu ya kasa tuno
inda suka taba haduwar.
Cikin annuri da walwala Sarki Taryan
dubi Jarumi Imhal ya ce, "Ya kai Jarumin
jarumai,na tayaka farinciki bisa tsira da ka yi
da rayuwarka, amma babu wanda ya cancanci
ka yi masa godiya face wannan bakon Jarumi
dake tare da ni, domin shi ne ya ceci
ayuwarka ya yi maka maganin da ni kaina na
yi matukar mamaki sabo da cire
tsarnmanin za ka rayu".
Koda jin wannan batu sai fuskar Jarumi
Imhal ta fadada da murmushi, nan take ya
mikawa Jarumi Salmanu hannu suka gaisa.
Ba tare da sun saki juna ba sai Imhal ya
ce, "Ina godiya mara adadi a gareka ya kai
Wannan saurayi ma'abocin kyawu da kwarjini.
Ina fatan wannan taimako da ka yi min
ya zamo tubalin kafa
kafa sabuwar
sabuwar Abota
tsakaninmu.
Kai kuwa mene ne dalilin da ya sa ka
ceci rayuwata har ka yi mini Magani?"
AA Misau ke Magana
Sa'adda Salmanu yaji wannan tanbava
sai ya yi ajlyar numtashi sanann ya ce, "da
farko dai ba nỉ ne na cacanci ka lara yiwa
godiya ba, Ginbiya Lamrita ya kamata ka
yiwa",
Koda jin wannan batu sai Jarumi Imhal
ya kamu da tsananin manmaki ya ce, "Kana
nufin ka ce akwai sa hannun Gimbiya Lamrita
a cikin ceton rayuwata?"
Jarumi Salmanu ya ce "Kwarai kuwa,
kuma ita ce ma ta sa nasa hannuna akan ceton
rayuwarka a lokacin da ku ka yi RAGAS kai
da Mahaifinta Sarki Gurzalu.
In ba don mun daukeka ba daga filin
gasar mun gudu izuwa cikin daji daga filin
gasar ne ma makiya za su karasa hallaka ka
sabo da filin ya yamutse har yan kallo sun
gwamutse a cikinsa"
Koda jin wannan jawabi sai Jarumi
Imhal ya kyalkyale da dariyar farinciki duk da
cewar dariyar na Kara masa tsananin zogi da
radadi na rauninsa.
Kawai sai ya dubi Jarumi Salmanu ya
ce. "Ya kai Abokina yanzu kana nufin ke nan
ka ce Lamrita ta sauya ra'ayinta a kaina ta
daina gaba da ni?"
Kafin Salmanu ya budi baki ya ce wani
abu sai Sarki Taryan ya tari numfashinsa ya
ce, "Kwarai kuwa, kuma a yanzu tana
Tsananin kaunarka fiyc da komai a duniya
kamar yadda 'yata ma Gimbiya Shumaira ta
kamu da tsananin sonka.
Ni kaina yanzu alfarma daya zan nema
a wajenka sabo da bana son lafiyar 'yata ko
rayuwarta ta tabu.
Kada ka zamo mai wulakaniata ko ka
kyamaceta.
Ka lallabata a hankali ku rabu lafiya
tunda darna ta gane cewa zIciyarka ta karkata
Akan Gimbiya Lamrita".
Daga wannan lokaci ne na fara koyar
da ita yadda ake tafiyar da harkokin Mulki da
sirrikan tsafi, amma ko kadan ba ta da
sha'awa akan wadannan abubuwa guda biyu,
shi yasa na yi takaici ainun.
Kai! ina mai sanar da kai cewa har yau
kuma har gobe Gimbiya Shumaira ba ta damu
da komai na duniya ba, kuma ban taba ganin
ta so wani abu ba face kai a rayuwarta.
A yanzu da na ke cin wannan Abinci
tare da kai sai na aiyana a zuciyata na ce ina
ma dai ace kai dana ne na cikina wanda zai
gaji Karagar Mulkina, tabbas da na gama cika
dukkanin burina na duniya.
Babban abin bakincikina shi ne, idan na
mutu shi ke nan đaukakata da jarumtakata za
su dusashe tun da bani da da namiji.
Bisa wannan dalili ne ma yanzu na
yanke shawarar na shiga cikin wannan gasa ta
kambun jarumta a wannan karon'"
Kai Nima Dai AA Misau zan shiga wannan gasa duba da tsantsagwaron JARUMTATA nasan dai baku manta Yadda Nayi JARUMTA ba a wajan Samun yarinya Alfila A SARKIN SARAKAI ba hhhhh

Zamu dakata anan saikuma wani lokaci zamu cigaba insha Allah
Admin
AA Misau ke Magana

Ku bibiyemu a wannan shafuka
Dandalin Litattafan Yaki By Al'ameen Ahmed Misau

DANDALIN LITATTAFAN YAKI BY REAL AA MISAURIJIYA GABA DUBU💕
Littafi Na Bakwai (7)🩸
Part D. 💎
Na Abdulaziz Sani M Gini 🤴
Typing By
AA Misau ke Magana
✍️⭐⭐⭐

Labari ya isowa Shagala cewa
Marubucin yaci gaba da cewa
BISA WANNAN DALILI NE MA YANZU NA
YANKE SHAWARAR NA SHIGA CIKIN WANNAN GASA TA
KAMBUN JARUMTA A WANNAN KARON'"
jama'ar gari da jaruman gasa suna kan
matsayin cewa ta mutu.
Akwai sauran shawarwari wadanda
Sarki :zai baka yanzu.
Zan rinka kawo maka ziyara har izuwa
lokacin da za ka sami karfin jikinka ka iya
mikewa sOsai har ka iya taka kafafunka".
Koda Jarumi Salmanu ya zo nan a
Zancensa sai ya koma gefc guda ya zauna, shi
kuma Sarki Taryan ya juya ya dauko wannan
Teburi mai dauke da kayan Abinci, ya
kawoshi daf da inda Jaruni Imhal ke zaune ,
sannan shima ya zauna daf da Imhal din a
gefen Gadon da yako kai ya dubeshi ya ce,
"Ya kai Jarurnin jarumai, na sani cewa kana
jin yunwa, bisa haka ne nasa aka shirya maka
wannan Abinci, kuma nima ina jin yunwar
domin tun daga ranar da ku ka fafata kai da
Sarki Gurzalu ban sami damar cin Abincin
kirki ba.
Lallai ina son mnu ci wannan Abinci tare
domin mu sami damar tattaunawa akan
muhimman maganganu".
Ba tare da wata gardama ba sai Jarumi
Imhal ya sa hannunsa a cikin Abincin, shima
Sarki Taryan ya sa hannunsa suka kama ci.
Tsawon 'yan dakiku masu yawa suna
cin Abincin tare amma dayansu bai ce uffan
ba, kumna kowannensu kansa na sunkuyce can
kamar hadin balki sai suka dago kai gaba
dayansu a tare kuma lokaci guda suka dubi
junansu.
Ko da suka hada idanu sai zuciyar
Jarumi Imhal ta buga da karfi, ba komai ne ya
haddasa hakan ba face ganin kwallah a cikin
Idanun Sarki Taryan.
Al'amarin da ya dugunzuma hankalinsa
ke nan, ya dubeshi ya ce, "Ya kai wannan
Sarki mai daraja, ina dalilin zubar wannan
hawaye na ka?"
Sa'adda Sarki Taryan yaji wannan
Lambaya sai ya yi ajiyar zuciya kuma ya yi
shiru kam ba zai ce komai ba, sannan ya ce, ya kai Inhal, ka yi sani cewa tun kafin na
sarmi haihuwa na ke ta fatan na sami haihuwar
da namiji, amma ban samu ba.
Babu irin kokarin da ban yi ba akan
hakan, amrna sai bukata ta ki biya.
A karshe ma sai Bokaye suka tabbatar
mini da cewa 'ya mace zan haifa guda daya
jal! a duniya, kuma daga kanta ba zan sake
samun haihuwa ba.
Bisa wannan dalili ne na yi bakinciki
mara misaltuwa, ba don komai ba sai sabo da
sanin cewa 'ya mace tana da rauni ba lallai
bane ba ta iya tafiyar da harkokin Mulki ba
kaar yadda ya kanata a bayan raina.
A ranar da aka haifi Gimbiya Shumaira
ban yi wani farinciki ba kuma ban soma jin
kaunarta va a cikin zuciyata har sai da ta kai
shekaru shida a duniya.
Daga wannan lokaci ne na fara koyar
da ita yadda ake tafiyar da harkokin Mulki da
sirrikan tsafi, amma ko kadan ba ta da
sha'awa akan wadannan abubuwa guda biyu,
shi yasa na yi takaici ainun.
Kai! ina mai sanar da kai cewa har yau
kuma har gobe Gimbiya Shumaira ba ta damu
da komai na duniya ba, kuma ban taba ganin
ta so wani abu ba face kai a rayuwarta.
A yanzu da na ke cin wannan Abinci
tare da kai sai na aiyana a zuciyata na ce ina
ma dai ace kai dana ne na cikina wanda zai
gaji Karagar Mulkina, tabbas da na gama cika
dukkanin burina na duniya.
Babban abin bakincikina shi ne, idan na
mutu shi ke nan đaukakata da jarumtakata za
su dusashe tun da bani da da namiji.
Bisa wannan dalili ne ma yanzu na
yanke shawarar na shiga cikin wannan gasa ta
kambun jarumta a wannan karon'"
Koda jin wannan batu sai hankalin
Jarumi Imhal ya dugunzuma, kuma ya kamu
da tsananin mamaki, ya dubi Sarki Taryan
cikin alamun damuwa ya ce, "Haba ya
shugabana, ya ya kai da kafi kowa sanin illar
Wannan gasa za ka ce za ka shigeta
musarnman a yanzu da bakon Jarumi Salmanu
ya shigota?"
Koda jin haka sai Sarki Taryan ya yi
muraushi ya ce, "Ai shi kadai ka sani, a jiya
ma wasu bakin jaruman sun zo daga kasashe
uku.
Daya daga Birmin Farisa yake, daya
daga Bimin Askar, na ukunsu kuma daga
Bimin Sumari.
Ni kam a iya yawona na duniya da
kuma tsawon shekarun da na dauka ina shirya
wannan gasa a Birina ban ta ba ganin jarumai
irin su ba "
Cikin marnaki Imhal ya dubi Sarki
Taryan ya ce, "Kana nufin kace baka taba
AA Misau ke Magana
ganin jarumai masu kirar sadaukantaka bane
kamarsu?"
Sarki Taryan ya yi rourmushi ya ce,
"A'a ba haka nake nufi ba, abin da na ke nufi
shi ne, ban taba ganin jarumai masu tsananin
zafin nama da tsantsar jarumtaka irin tasu ba,
sabo da na gansu sa'adda suke motsa jini ne
jiyan da suka zo.
Ma'ana sun nuna irin jarumtakarsu anan
kofar gidan sarautata ta hauyar yakar junansu,
domin kowannensu ya ga irin jarumtakar
sauran, kasancewar tafiya ta hadosu tare tun
daga Birnin Farisa,
Ina mai tabbatar maka da cewa jama'ar
gari ma sun tsinke da al'amarinsu "
Koda Sarki Taryan yazo nan a zancensa
sai Jarumi Inhal ya yi mnurmushi ya ce, "AI
ba a sanin maci Tuwo sai Miya ta kare! Idan
akwai wani abu mafi muhimmanci da ka ke
son ka sanar da ni ina sauraro, amma ni yanzu
batun wadannan bakin jarumai da suka zo
Bai taba firgitani ba ko ya karyar min da
zuciya."
Sa'adda Sarki Taryan yaji wannan batu
sai ya yi dan shiru kamar ba zai ce komai ba,
sannan daga can ya numfasa ya ce, "Tabbas
akwai magana mai matukar muhimmanci
wadda nake son na gaya maka.
Maganar da zan gaya maka kuwa ita ce
ka yi kokari ka gano asalinka da matsayinka,
domin ta hakan ne kadai hanyar da za ka gane
dalilin da ya sa ka tsinci kanka a cikin halin
da ka ke ciki a yanZu, kuna ta hakan ne za ka
zabawa kanka abin da ka ke ganin cewa zai
fissheka a rayuwarka".
Koda gama fadin hakan sai Sarki
Taryan ya mike tsaye ya juya zai fice daga
cikin dakin amma sai Jarumi Imhal yai sauri
ya ce, "Ya shugabana ka taimaka min ka gaya
min yadda zan yi na gano asalina da
matsayina.
Ga dukkan alamu ka san komai
kaina, ko kuma ka san waní abu akan 'yar uwata wacce ta

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment