Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

taimakeni tun a iokacin da na
Fara yin wannan gasa ta kambun jarumta?"
Koda jin wannan tambaya sai Sarki
Taryan ya gyada kansa kuma ya juyo yana
mai duban Imhal cikin murmushi ya ce,
"Dukkanin Jarumi na kwarai yana samnun
nasara akan dukkan abin da ya sa a gabansa.
Babu abin da zai gagareka muddin za
ka zage dantsenka ka yi iya kokarinka.
Ina kara tunatar da kai ka ci gaba da
mai DAKAKKIYAR ZUCIYA
wadda ba ta san tsoro ko fargaba ba,
zamoWa
Idan ka yi hakan za ka fita daga cikin
kowanne irin hadari, kuma za ka sami nasara
a bisa dukkan abin da ka sa a gabanka.
Shawara ta biyu, ko in ce ta karshe
wacce zan baka ita ce, ka ja Jarumi Salmanu a
jikinka, kuma ka
shawarwarinsa".
Gama fadin hakan ke da wuya sai Sarki
Taryan ya juya ya fice daga cikin dakin gaba
daya ya barsu su biyu kacal shi da Jarurni
Salmar u.
Koda fitar Sarki Taryan sai Jarumi
Salmanu ya mike ya karaso daf! da Imhal ya
zauna sannan ya dafa kafadarsa suka fuskanci
juna sosai ya ce, "Ya kai Abokina ka kwantar
da hankalinka, domin na fuskanci cewar
zuciyarka akwai imani da adalci.
In da ace ma ka yi imani da abin da na
y imani da shi da babu wani abu da za ka yi
shakkarsa".
Cikin marmaki Jarumi Imhal ya dubi
Jarumi Salmanu ya ce, "Mene ne abin da ka yi
imani da shi?"
Jarurni Salmanu yai gyaran murya
Sannan ya sake duban Jarumi Imhal cikin
Nutsuwa ya ce, "Ni na yi imani da Allah,
wanda Shi ne Sarki guda daya abin bauta.
Shi ne wanda ya halicci sammai da
Kassai da duk abubuwan da ke cikinsu.
Kuma Shi ne Ya halicci Mutum da
Aljan ba don komai ba sai domin su bauta
maSa,"
Koda Jarumi Salmanu yazo nan a
zancensa sai jikin Jarumi Imhal ya yi sanyi
kuma ya kurawa Jarumi Salmanu idanu.
Daga can ya kau da kansa ga barin
kallon Salamanu tare da yin murmushi ya ce,
"Sai yanzu na tuno da inda muka taba haduwa
ni da kai".
Caraf! Sai Salmanu ya tari numfashinsa
yana murmushi ya ce, "A dajin Birninku
muka taba haduwa a lokacin ina gabatar da
Addinina, kai da wani tsoho ku ka zo za ku
gifa ta gabana'"
Koda jin haka sai Imhal ya maidawa
Salmanu martanin murmushin da ya yi masa
ya ce, "Tabbas an yi haka. To wai shin wane
irin Addini ne wannan na ga kana yi, kuma
me ka ke bautawa?"
Sitmanu ya ce, "Ai na gaya maka,
Allah na ke bautawa, Ubangijin da bai haifa
ba, kurma ba a haifeShi ba.
Sannan kuma sunan Addinin nawa
ADDININ MUSULUNCI.
Addini ne wanda ya zo da adalci, kuma
Vasa gaskiya ta kori karya.
Addini ne wanda ba ruwansa da
matsayi ko nasaba, Talaka da Attajiri da
Basarake babu wanda ya fi wani face wanda
ya fi tsoron Aliah".
Sa'adda Jarumi Salrmanu ya zo nan a zancensa sai Jarumi Imhal ya yi ajiyar zuciya
sannan ya ce, "Ya kai wannan Jarumi, ka yi
sani cewa ni rainon da na taso a cikinsa ba a
taba nuna mini wani abu mai kama da Addini
ba, kuma ba a taba kOyar da ni tsafi ba, kuma
ko a cikin zuciyata ban ji na yi imani da su ba,
anrna yanzu da naji ka yi mini bayanin
wannan Addini sai na ji alamun cewa zai iya
zama shi ne na gaskiya.
Yanzu wacce hujja za ka iya zuwar
mini da ita wacce za ta sa na kara gamsuwa
cewa lallai wannan Addini shi ne Addinin
gaskiya?"
Koda jin wannan batu sai Salmanu ya
yi murmushi a karo na biyu ya ce, "Hujjar da
zan baka yanzu mai sauki ce.
Wannan rauni da Sarki Gurzalu ya yi
maka a ciki, rauni ne wanda ba zai warke ba a
cikin wata biyu ba ma, amma sabo da na yi
maka addu'o'i na roki Ubangijina akan Ya
baka lafiya gashi har ka iya taka kafafunka.
Kuma da izinin Ubangijina nan da sati
biyu ma kacal! za ka warke gaba daya".
Koda jin haka sai Jarumi Inmhal ya sake
cika da mamaki, ya ce, "Y anzu kana nufin ka
ce nan da sati biyu kacal Ubangijinka zai iya
warkar da ni?"
AA Misau ke Magana
Salmanu ya ce, "Kwarai kuwa, ko
shakka bana yi.
Sarki Gurzalu kuwa da ya sami irin
wannan rauri naka, ina mai tabbatar maka da
cewa sai ya shafe wata uku cur! A kwance
yana jinya.
Shin yanzu idan ka sami lafiya ka
warke sumul! Nan da cikar sati biyu za ka yi
imani da Ubangijina?"
Jarumi Imhal ya num fasa ya ce, "Ko
darr ba zan yi ba zan karbi wannan adduni
naka mai daraja matukar hakan ta kasance".
Koda jin wannan batu sai farinciki ya
mamaye Jarumi Salmanu, sake duban Imhal
ya ce, "Tabbas zaton da nake yi maka na
alheri yana daf! da tabbata.
Idan ba za ka damu ba zan so ka bani
takaitaccen tarihin rayuwarka kafin ka ji
nawa".
Ba tare da 6ata wani lokaci ba sai
Jarumi Imhal ya kwashe labarinsa tsaf! tun
daga lokacin da aka raineshi a cikin daji yana
yaro karami kawo izuwa lokacin da Sarki
Gurzalu ya turo Dakarunsa domin
hallakasu shi da Tsoho kawo izuwa lokacin da
aka kamashi aka kaishi Kurkukun RIJIYA
GABA DUBU, da yadda ya sami damar
guduwa aka sake kamoshi aka tafi da shi
izuwa Birnin Kisra domin halartar gasar
jarumtaka.
Su
Koda Jarumi Imhal ya zo karshen
labarinsa sai Jarumi Salmanu ya kamu da
tsananin tausayinsa har kwallah ta ciko
idanunsa ya ce, "Ya kai Abokina hakika
rayuwarka abar tausayi ce, kuma abin da na
fahimta a cikin labarinka duk yadda aka yi kai
ba jaramin mutum bane , lailai ka fito daga
babban gida.
Ka ci gaba da hakuri da sannu za ka san
ko kai waye."
Imhal ya girgiza kai gami da dafa
kafadun Salmanu ya ce, "Na gode da kyau ya
kai Abokina bisa nuna tausayinka a gareni.
kuma ina dada godiya bisa kara min karfin
guiwata da ka yi.
Haka kuma ina mai sanar da cewa ko
da wannan rauni nawa bai warke ba zan kar6j
Addininka, sabo da tun a yanzu ma na fara ji a
jikina cowar lallai wannan Addini naka
Addinin gaskiya ne"

Tafiya Fa Ta Fara Nisa AA Misau ke magana

SHIIN JARUMI IMIIAL YANA
KARBAR ADDININ MUSULUNCI?

ME ZI FARU IDAN SARKI
GUZALU YA KARASA BIRNINSA YA
SIIIGA DAKIN TSAFINSA?

YAUSIIE ZAI SAMU LAFIYA HAR
YA DA WO YA CI GABA DA GASAR
KAMBUN JARUMTA?

YA YA MAKOMAR SOYAYYAR
GIMBIYA SIIUMAIRA DA LAMRITA GA
JARUMI IMIIAL?

MAL ZMI FARU TSAKANIN BAKIN
JARUMAI UKU DA SUKA BAYYANA
DOMIN YIN GASAR
JARUMTA?

YAUSHIE JARUMI IMIIAL ZAI SAN ASALINSA?

YAUSIIE ZA A YI HADUWAR
KARSIIE TSAKANIN SARKI GUZALU
DA JARUMI IMHAL?

IDAN SU YI
HADUWAR KARSHIE
WAYE ZAI SAMU
NASARAR HALLAKAR
DAN UWANSA
DA KAMBUN?

Mu hadu a littafin RIJIYA GABA
DUBU (8) kashi na takwas, don jin ci gaban
wannan kasaitaccen kayataccen labari.
Daga mai Ä‘ebe muku kewa a kullum da
ko yaushe .
Sarkin Marubuta Litattalan Yaki
ABDUL'AZIZ SANI M/GINI

Typing
AA Misau ke Magana
Ku bibiyemu a shafukan nan

Dandalin Litattafan Yaki By Al'ameen Ahmed Misau

DANDALIN LITATTAFAN YAKI BY REAL AA MISAU
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment