Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya daho yayi wara-wara ta sauke ta juye a kula, sai da ta kai darning sana ta dawo ga miyarta, tana bud'ewa har mai ya fito sosai ta kashe gas d'in, ta juye ta itama a kula, ta kaita darning, ta dawo kitchen d'in ta gyara ko ina, sana ta bud'e firiza ta d'akko ayarta da dabino da kwakwa ta wanke su ta tsaftace su tasa a bilanda ta had'esu ta markad'e sai da ta tabbatar sunyi laushi sun markad'u, sana ta juye su, ta tace su ta d'akko wani jok mai tsawo ta juye a ciki, sai kuma ta d'akko madarar da ake yin iloka da ita, guda d'aya ta juye rabi a ciki, tasa cukali ta motsa ko ina ya had'e, saita d'akko k'ank'ara ta fasa ta ta juye a cikin kunun ayarta, ta aje gefe guda ta k'ara gyara kitchen d'in ko ina yayi kyau, sana ta fita ta aje shima kunun ayar akan darning.


D'an zaunawa tayi tana rik'e k'ugunta saboda ta gaji sosai, sai da ta d'an huta sana ta shige bathroom tayi wanka ta sake fashe jikinta da turare tasa turaran wuta tasa hijabinta ta rufe kanta dashi sai da ta tabbatar ko ina na jikinta ya d'au k'amshin turaran wutar, sana ta aje shi a gefe yana ba d'akin k'amshi, sallah tayi ganin har hud'u tayi, tana gamawa ta fito parlo ta zauna jiran mijin nata.



RAMADAN POV

Sai da ya gama sallah a masallaci sana ya shiga motarsa ya nufi unguwarsu, yana zuwa mai gadi ya wangale mai get ya shiga harabar gidan nasu yayi parking d'in motar yana kallon harabar gidan naso a cikin zuciyarsa yana tunanin da Abbansa yana raye da duk wannan matsalolin basu faru ba, sai da suka gaisa da mai gadi sana ya nufi cikin gidan naso.


A babban parlon gidan nasu ya tadda duka y'an gidan da k'annansa guda biyu sai Yayyansa guda biyu Ya Aysha ce kawai babu itama dan tayi aure su kuma Inteesar da Nawwara Auntys d'insa kenan basuyi auran ba sai k'annansa guda biyu Hasana da Usaina.


Suna ganinsa suka gaida sa shi kuma ganin Yayyan nasa mata na mai wani kallo yasa ya murtuke fuska yana gaida su badan yaso ba.


Amsawa sukai ba yabo ba fallasa Hajiya ce ke sakkowa, d'aga kai yayi yana kallonta ganin irin kallon da take aika mai dashi ne yasa yayi k'asa da kansa, tana k'arasowa har kasa ya duk'a ya kwashi gaisuwa, sai da ta zauna ta d'ora kafa d'aya kan d'aya tasha mur ta bud'e baki cike da isa ta ce "sai yanzu kaga damar zuwa ko kuma sai yanzu y'ar gwal d'in taka ta baka umarnin zuwa?" ta idasa maganar tana tsaresa da ido, shi kuwa cike da mamaki yake bin Hajiya da kallo, shikam ba duka jiya ne Ya Ayshar ta zo ta gaya mai sakon Hajiyar ba, katse mai tunani tai da cewa "koma dai minene ka sanar da ita cewa nanda wata biyu masu zuwa zaka k'ara aure, nanda sati biyu kuma zanzo har gidan naka da amarya, zata zab'i inda yayi mata koda d'akin da Munnirar take zaune ne kuwa, idan ta nuna nan ne yayi mata dole ta kwashe komatsanta taba amarya waje, kaji na gaya maka karma kace ban sanar dakai ba", wani irin kallo mai wuyar fassarawa yake bin Hajiya dashi wannan k'iyayya har ina kai jama'a ta ina zai fara ne, Hasana ce ta buga tsalle dama ba kunya ne da ita ba tana cewa "haba ai gara ta matsa taba amarya waje duk ta kanainaye komai dama... Kamin ta idasa maganar Ramadan ya tashi a zuciye yana d'auketa da wani gigitaccan mari ji kake tasss tasss, su duka sai da suka tashi tsaye, Hasana sai hawaye tana b'oyewa bayan Hajiya ganin yadda yake huce kamar zai rufeta da duka, Hajiya cike da masifa ta rufesa da fad'a tana cewa.........✍️



*Washhh Allah na gaji mu had'u zuwa gobe idan Allah ya kaimu*



ZAHRA ROYAL STAR CE



SHARE FISABILILLAHI🥰🙏


*👩‍❤️‍👨💞 WAYAFI K'AUNATA 👩‍❤️‍👨💞*
(Love Story)




PAID BOOK #500






MALLAKIN
*©ZAHRA ROYAL STAR*





*Littafin kud'i ne wadda ya shirya yin tafiyar dashi zai iya turo kud'insa, ko katin MTN ko hoton katin saika turo shaidar biya #500 ne kacal*




8130479973
*FATIMA RABI'U OPAY BANKA*




Zaka turo shaidar biyanka ko hoton katin ta wannan number d'in,
(08130479973.08035023054)





Free Page 5-6



بسم الله الرحمن الرحيم العالم



Muka ji saukar maganar ta akanmu cike da masifa tana cewa "kai dai Hafiz ban san irin ka ba wallahi, shin wai mika gani wajan wannan yarinyar mai kama da aljanu?, ka wani mak'ale mata, to tun wuri bari na gaya maka idan wani abunne a zuciyarka wallahi kayi gaggawar cire shi a ranka" ta idasa maganar tana hararara ta gaida ta nayi ina cewa "Inna Rabi ina wuni" wani banzan kallo data yi min tana cewa "da ban wuni ba kin ganni uwar iyayin tsiya, kai kuma bita zai-zai sai ka ciga ba da bin bayan ta kamar wani jelar doki, ai shi yasa d'an uwanka yake birgeni ya za'ai ma ya tsaya da wannan kucakar yarinyar", ta idasa maganar tana jan wani dogon tsaki tayi gaba abinta.


Shi kuwa girgiza kai kawai yayi yana kamo hannuna ganin nayi k'asa da kaina ya ce "Maryam" ya kira sunana a hankali d'agowa nayi ina dubansa cike da sona ya sake cewa "am so sorry my Maryam... Da sauri na katse shi da cewa "kai Ya Hafiz miye na bani hakuri to?, ai itama uwata ta ce dan tayi min fad'a ba wani abu bane" murmushi ya sakar min yana k'ara kallon kyakkyawar fuskata, shi dai Allah ya sani ina matuk'ar birgesa.


Ganin lokaci naja na ce "Ya Hafiz bari na shiga daga ciki kar Iya taga na dad'e" saki na yayi yana cewa "Ohh na ma manta aiken mu fa aikai oya jeki ina nan shigowa sashin naku" da to na amsa inayin gaba.


Da sallama na shiga Iya na zaune, ta tasa fulawar da zatai d'an wake a gaba tana jira na, murmushi na saki ina zama kusa da ita, tashi tayi tana d'ebo ruwa ta zauna tana cewa "yanzu fisbilillahi Maryam tun d'azo na aike ki sai yanzu kikaga damar dawowa saura masifaffan can ya shigo duk ya damu mutane" tana maganar dai-dai ta gama kwab'a d'an waken tashi nayi ina cewa "kai Iya wallahi a hakama nayi sauri kuma harda shi ya tsayar dani yana faman min tsiyar daya saba min yanzu dai kawo na jefa d'an waken" sakar min tayi, tana zama a tabarma, dama tuni ta d'ora ruwan zafi harya tafasa, zama nayi gefen murhun na fara jefa d'an waken, Iya dake kallona ta ce "yanzu sabo da Allah shi dai duk inda ya ganki hankalinsa bazai kwanta ba saiya jaki fad'a, ni na rasa wannan k'iyayya taku keda shi, to idan Allah ya k'addara zaku zauna inuwa d'aya fa..... Kamin ta idasa maganar da sauri har ina shirin zubar da kwab'un d'an waken na ce "kai Iya wannan wane irin fata ne kike min dan Allah ki daina ma wannan maganar karma mala'iko suji su amsa ina dalili ina zankai rigimar Ya Abbas kashe ni zaiyi wallahi", dariya ta sakar min tana cewa "ke ki bimin sanwa a hankali karki zubar min da kwab'i , wasa nake miki koni bazan bari a had'a ki da wancan mai bak'ar zuciyar ba".


Tashi tayi bayan na gama jefa d'an waken na d'akko roba da ruwa a ciki ina tsamewa ina cewa "yauwa Iya ta ai nasan baza ki bari ba Allah sarki da Kakana mai shano na nan ai da mai wannan bak'ar zuciyar bazai min duk wannan abubuwan ba", Iya dake zaune cike da damuwa da kewar mijin nata yau kusan shekaru bakwai da rasuwa, ta ce "Allah dai ya jik'an Malam" da amin na amsa nima zuciyata ba dad'i Allah baya barin wani dan wani yaji dad'i.



Bayan na gama Iya ta ce nasa mai nashi a kula, sai da nasa masa na aje gefe, na had'a mana nida ita muka zauna muka fara ci d'an waken yayi mun dad'i sosai saboda yaji kayan had'i an yanka su tumatur dasu albarsa harda kwai a ciki.


Bayan mun gama na shige d'aki nayi alwala ganin har mangaruba tayi ina cikin sallah naji muryarsa ya shigo suna gaisawa da Iya data idar da sallah, jawo mai d'an waken tayi ta zuba mai, saida ya fara ci yana tand'e hannu sai da ya gama ci tas ya wanke hannu yasha ruwa ya goge baki, da kamar bazai tankama Iya ba can kuma sai ya ce "na ce dai Iya ba wannan k'azamar yarinyar taki ce kika ba ta jefa min d'an wake ba" wani dogon tsaki Iya taja tana cewa "kai Abbas bafa nason rashin ta ido ka kalli zabar ido na sai da ka gama lashe abinci zaka zo kana kawo min wani suki burutsu, to ita ce tayi, kaga saika amayoshi ko", ta idasa maganar cike da gatse tashi yayi yana murmushi wadda Iya ce kawai take ganinsa zaro kud'i yayi zasu kai dubu uku ya aje mata yana cewa "haba Iya ta kar aji kanmu mana yanzu ga wannan ladar yimin d'an wake da kikai ne" tashi Iya tayi tana washe baki dan Iya akwai son kud'i ta ce "yauwa d'an albarka yanzu kayi zance mai kyau to na gode Allah shi k'aro bud'e" da amin ya amsa yana ficewa daga sashin.


Ni kuwa dake cikin d'aki, fitowa nayi ina sane nak'i fitowa yana nan samu nasan bazamu kwashi ta dad'i ba nida shi kamar wuta da ruwa ne.

Zaunawa nayi ina zunb'uro baki gaba ina cewa "Iya kinji fa mi ya ce wai ni ce k'aza ma" na k'arashe maganar cike da jin haushinsa a raina tashi Iya tayi tana d'aure kud'in daya bata a hab'ar zaninta tana cewa "ke kinga ni bana son wannan sokiburutsin naku keda shi wadda baya k'arewa ba kinsan halinsa ba?, fad'a yayi fa dama dan kiji haushi ai", tashi nayi ina cewa "yauwa Iya candynmu fa ya kusa na gama secondary school kuma kinmin alk'awari zan wuce ko ina so nima nayi karatun likitancin nan", Iya dake zama kusa dani ta kunna rediyon ta tana cewa "eh nima ina son haka amma dole sai mun zauna da Iyayanki kinsan dai bake kad'ai zaki gama makarantar ba bansan mi suka yanke a kanku ba idan aure suka yanke a kanku haka zakiyi hakuri kiyi shi banda ta cewa tunda bake kad'ai ce ba" hankali na yayi mugun tashi matsowa nayi kusa da ita ina cewa "Iya aure kuma?, ni dai gaskiya wallahi Allah ban shirya mashi yanzu ba dan Allah Iya karki bari a durkusar min da rayuwata duka nawa nake da za'a ce wai aure", tashi Iya tayi tana janye ni daga jikinta itama kanta zata so na wuce d'in sai dai kuma abun zai zama abun magana a cikin gidan ta ce "Maryam bawai bana so kiyi karatu bane a'a abunne zai zama abun magana dama yanzu ana min surutu nida ke cewa nafi sonki, ke kuma kin tare ko ina kin hana sauran jikokina suji d'umin jikina, kuma ba haka bane ke kad'ai ce marainiyar babu wadda zaki rab'a kiji dad'i idan ba niba, ina suke so kije to? shi yasa nake k'ara jawoki a jikina dan bana so kiyi kukan maraici amma gani ake kamar son kai ne nake nunawa a kanki gani suke kamar soyayyar da nake ma Mahaifinki ce ta dawo kanki, Maryam Mahaifinki sadda yana raye kwata-kwata baya so yaga kuka na ko b'acin raina yana min biyayya sosai koda zai cutu kuwa , duk cikin y'ay'ana nafi jinshi a raina badan komai ba sai dan harga Allah zuciya na son mai kyautata mata, Mahaifinki kullum cikin kyautata min yake, to taya za'ai bazan so jininsa ba?, kawai kiyi hakuri muga miye suka yanke komi Allah ya tsara miki Maryam a rayuwa ki karb'esa hannu biyu-biyu kinji?", shigewa nayi kawai jikinta ban k'ara cewa komai ba dan baki na yayi min nauyi.........





*KADUNA* POV




Hajiya cike da masifa ta rufesa da fad'a tana cewa "kai kai kai tsaya daga nan na ce, dukanta zakai akan waccar abar akan ta fad'i gaskiya, ai gaskiya ta fad'a, uban miye take a cikin gidan naka inba taci ta kwanta ba, tabi ta kanainaye komai, sai abunda ta ce shi kakeyi, dan haka karka sake ka k'ara kai hannunka akan yarana indai akan waccar matar taka ce", ficewa yayi daga gidan gaba d'aya ranshi idan yayi dubu ya b'ace.


Yana fita Nawwara ta ce "ai wallahi kin min dai-dai wallahi waccar matar ba'a banza ta barshi ba kina ganin daga anyi maganarta ance tayi kaza harya tashi a hargitse", zaunawa Hajiya tana jawo Hasana dake bayanta ta ce "ke kuma gobe ki k'ara shiga harkarsa idan yayi miki illa ke kika sani" k'unkuni ta farayi tana zama kan kujera Inteesar ce da har yanzu bata sa baki ba tana danne-dannen waya ta ce "nifa wallahi wani lokacin ban ganin laifin Munnira saboda tsantsar kulawa ce take bama mijinta kun kasa fahimta ne ba wani asiri a ciki", da sauri Hajiya ta ce "kinga Inteesar ki fita ido na rufe ki fita samgar wannan sha'ani tunda naga kema ta shanye ki ta gama dake, dan haka karna k'ara jin bakinki a ciki, tunda naga keda Ramadan d'in kamar an canza min ku, ke Nawwara maza idan kin gama abunda kike ki kira min Halima", da to ta amsa Inteesar kuwa tab'e baki tayi tana tashi tabar masu parlon dan ita Allah ya gani bata ga wani abunda Munnira take na rashin kyautawa ba kawai dai dama can Hajiya ba son Munnirar take ba.





Ramadan yana isa gida ya saita kansa baya so ya shigar mata da b'acin rai bata ji ba bata gani ba,

Amma duk da haka Munnira na ganinsa tasan ransa a b'ace yake, ruwa mai sanyi ta kowa mai ya sha yana sauke ajiyar zuciya bata ce mai komai har sai da ta taimaka mai yayi wanka ta kaishi har darning ta zaunar dashi sai da ta zuba mai abinci, yadda k'amshin girkin ya bigi hancinsa yasa ba shiri ya lumshe idonsa har miyan bakinsa na tsinkewa zama tayi kusa dashi tana d'an tsotsar alawa dake bakinta kallonta yayi ya ce "minene kika ta tsotsa ne wai?" murmushi ta sakar mai, mai tsada ta ce "alawa ce fa" jawota yayi jikinsa yana cewa "oya zan sha bani nima" turo mai d'an k'aramin bakinta tayi, ta had'e da nasa ta tura mai alawar cikin bakinsa sai kuma ta d'an kamo harshansa tayi mai wata irin tsotsar da yasa lumfashin Ramadan d'aukewa na wucin gani, can kuma saita sakar mai bakin har yanzu idonsa lumshi yake yadda yake jin zak'in alewar da miyan bakinta sai suka bashi wani irin gard'i kamar karta saki idonsa harya canza launi murmushi ta k'ara sakar mai tana jan kujerar da yake kai ta zauna akan cinyarsa ta fara basa abincin da kanta, shima haka tana bashi yana bata haka har suka gama cin abincin, satin abincin kuwa ta shashi kamar mi ji yayi kamar kunnunasa zai tsinke tsabar yadda abincin yake jin dad'insa.



Suna gamawa ya fita masallaci saboda jin ana kiran sallar magaruba bai dawo gidan ba sai bayan anyi isha'i koda ya shigo bai ganta a parlo ba kai tsaye bedroom d'in ya shiga, tana tsaye bakin madubi tana d'an shafa man baki, rungumeta yayi ta baya lumshe idonta tayi jin yana hura mata iskar bakinsa a dai-dai wuyanta wata wawar ajiyar zuciya ta sauke tsigar jikinta na tashi.

D'aukarta yayi cak sai kan gado kwantar da ita yayi yana mata runfa da faffad'an k'irjinsa, had'e bakinsu yayi waje d'aya yana sa hannunsa ya cire mata y'ar ficiciyar rigar data sa, ajiyar zuciya ya sake jin hannunsa a ciki na shanonta sakin bakinta yayi yana kai bakinsa a kansu wata irin ajiyar zuciya ta sauke tana k'ara tallafo kansa yadda yake shan na shanonta kamar wani yaro cike da wani irin salo tasan mijinta ba abinda yafi k'auna yake kuma d'auke mai hankali irin su.


Sai da komai ya lafa har sunyi wanka suna kwance manne da juna har yanzu yana wasa da na shanonta sai jagwalgwala su yake son ransa, yi tayi kamar zata mik'e ya d'an kwafe fuska yana cewa "please ki k'ara min nasha kinji" wata irin kasala ke k'ara saukar mata ta ce "anya my idan muka haihu zaka bar yara su sha kuwa?" dariya ya saki yana cewa "hmm gaskiya sai dai suyi hakuri" ya idasa maganar cike da zolaya murmushi ta saki tana kamo kansa ta ciro guda d'aya tana manna mai a baki kamar wani jariri haka ya kama ya fara sha haka sukayi bacci d'aya yana bakinsa d'aya yana shafawa...........✍️





ZAHRA ROYAL STAR CE



SHARE FISABILILLAHI🥰🙏


*👩‍❤️‍👨💞 WAYAFI K'AUNATA 👩‍❤️‍👨💞*
(Love Story)




PAID BOOK #500






MALLAKIN
*©ZAHRA ROYAL STAR*





*Littafin kud'i ne wadda ya shirya yin tafiyar dashi zai iya turo kud'insa, ko katin MTN ko hoton katin saika turo shaidar biya #500 ne kacal*




8130479973
*FATIMA RABI'U OPAY BANKA*




Zaka turo shaidar biyanka ko hoton katin ta wannan number d'in,
(08130479973.08035023054)





Free Page 7-8



بسم الله الرحمن الرحيم العالم



Washe gari haka na tashi suku-suku ko arzik'in shiryawa naje makaranta banyi ba, yau ta kasance al'hamis ne duk da muna ta shirye-shiryen gama school d'in amma maganar da mukai jiya da Iya ita ce duk ta sakar min da gwaiwa.


Iya ce a kaina kallona take tana nazari na, ta ce "nikam Maryam makarantar ce bazaki ba ko kuwa?, idan ma zaki saki ranki ki saki ranki ni banga abun tada hankali a nan ba, duk abinda Allah ya rubuta a cikin kuddun k'addararki to tabbas sai faru da kai, babu mahaluk'in daya isa kawar dashi, ki tashi ki shirya ki daina wannan k'uncin dan Allah?", tashi nayi ina d'an zunb'uro baki na ce "nifa Iya yau bana jin zuwa makarantar ne shi yasa hutawa nake so nayi" fita Iya tayi tana cewa "ai shikenan sai kiyi ta zama".



Wajajan k'arfe biyu na fito Iya na tsakar gida tana aikin danbu ina ganin yadda take murza danbun na ce "kai Iya yauma dan Ya Abbas zakiyi danbun nan na sani daya zo garin nan sai abunda yake so shi kike yi" na idasa maganar cike da jin haushinsa murmushi Iya tayi ta ce "kinga bana son kilbibi kema duk da rashin jituwar taku irin abinci d'aya kuke so keda shi kunfi son abincin gargajiya dannayi kuma sai kice danshi nayi, kinga ki wuce inda zaki nasan sashin Kawu Mamman zaki sai kin dawo".


Tafiya na farayi ina cewa "eh Iya can zani ina so mud'anyi fira da y'an uwa na nasan suna can kar ayi ba ni", ina jin maganar Iya na cewa "ai dai duk kun kusa bamu waje duk ku tafi gidan mazajan ku" nidai harna idasa barin sashin bance k'ala ba dan wani irin haushi nake ji idan akai maganar auran nan wallahi, toni wama zan aura dan gaskiya ni a cikin zuciyata har yanzu bazance ga wadda nake so ba ko Ya Hafiz kawai shak'uwa ce amma bana jin sonsa a raina.



Ina tunani na idasa sashin Kawu Mamman ai kuwa na taradda yawanci y'an matan gidan na sashin sunje duba Zeena zama nayi cikinsu dan dukkan muna samun jituwa dasu garama Sa'ida ita ce mai d'agin kai cikinmu ba wani shiga harkarta nake yi ba.


Hajara ce ta ce "Ohh ni tun jiya rabon dana ganki Maryam" d'an gyara zama nayi ina cewa "hmm ina zaku ganni Boss d'in gidan nan ya dawo shi yasa ko son fita bana yi danma karmu had'u dashi" dariya suka sa gaba d'aya can Sa'ida uwar iyayi an tab'o mata inda ke mata k'aik'ayi ta ce "hmm bari kedai ai Ya Abbas yayi wallahi matarsa ta more daga gani zata ga soyayya irinsu ne basa da sakin fuska ga jama'a, amma ga iyalansu ba'a magana irinsu idan kaga suna nunama matansu soyayya zaka sha mamaki wallahi" duka sakin baki mukai muna kallonta na ce "ke amma Sa'ida baki san wadda suka iya soyayya ba yo ni Allah na tuba mi Ya Abbas ya iya idan ba d'aure fuska ba, haka zaije yana ma matar tasa yayita firgita d'iyar mutane ko wacece ma" na idasa maganar ina rik'e baki.



Shewa suka saki gaba d'aya Zeena ta ce "ai kuwa irinsu sun iya soyayyar Maryam kuma sun iya gigita mace nanne dai zasu nuna mana jan ido", da sauri Sa'ida ta ce "yauwa kin gane kenan" tab'e baki nayi ina cewa "ku kuke ganin haka, kuda kuke da samari a hannu, ai dole kusan wadda suka iya soyayya a cikin maza" shewa suka k'ara saki, har suna had'a baki wajan cewa "kai Maryam kema fa kina soyayyar nan ina Ya Hafiz d'in kika barsa" dariya na saki ina d'an jawo kwanon da Zeena kecin waina na ce "ke ba tayi kin tasa abu gaba sai narka kike?" na fad'a dan ina so a kauda zancan da sauri ta turo min kwanon tana cewa "yanzu fa nake shirin tashi na zubo miki nasan kina sonta sadda zaki shigo duk su Hajara sun gama ci" idasa cinye ta cikin kwanon nayi ina cewa "yanzu dai tashi ki k'aro min dama yunwa nake ji yau Iya ta tsiri danbu saboda Boss har yanzu bata gama ba", tashi tayi tana d'ebo min ta kawo min sai kuma ta zauna tana kallon Sa'ida dake cewa "ya kamata fa mu fara shirye-shiryen gaba school d'inmu tunda kusan dukanmu zamu gama a tare" na cika bakina da waina na ce "nima nama Iya magana zata ban wasu kud'i zamuje shago mu sayo irin su alawa zanje a bugo min sticker kuma amma ba mai pictures ba, mai suna nake so" da sauri Hajara tayi karaf ta ce "nima gaskiya bana son mai hoto mai rubutu nafi so nima, amma ni inaga Bashir zai kawo min a ranar" dariya muka saki muna cewa "ahh kaga masu samari", bugu ta kaima Sa'ida data fi mata tsiya tana cewa "kuma fa da samarin nan naku kowacce tana dashi wallahi, shawarar da zan baku ma karku wani wahalar da kanku zaso yo muku ne su kawo muku" dariya aka saki ana shewa, dama idan muka had'u kamar zamu tada waje.



Muna cikin fira Aunty dake madafa har yanzu tana tuyar waina muka ji maganarta suna gaisawa da Ya Abbas, ai ko danda nan kowa cikin mu ta shiga hankalinta.


Lek'o d'akin yayi bayan sun gama gaisawa yana zafga mana hararara da manyan idonsa ko waccanmu sai da ta had'e wani miyau, banda ni dake cin wainata ko kallo bai isheni ba sosai na kama kaina dan bana ma son disginsa.


Cikin kakkausar muryarsa ya ce "dakuka zo kuka rarrashe nan kuna surutun banza da wofi ina islamiyar?" Sa'ida ce cike da iyayi ta ce "Ya Abbas ai yau al'hamis" tsaki yaja ba haka ya so ba, so yayi na tanka mai ya samu kafar da zai min rashin mutumci, nima shi yasa nayi kunnan uwar shegu dashi, nayi kamar bana wajan, duk da haka sai da ya samu kafar da zai tanka min, kallo na yayi yana cewa "ke kuma kici a hankali mana kina cin abinci sai kace akuya nacin abinci ke komai idan za kiyi bakya duba cewa ke macece kiyita abu na rashin dacewa da'alla" wani tuk'ukin bakin ciki ne ya rufe ni na bisa da kallo ya gama yab'a min bak'ar magana yayi gaba abinsa ko a jikinsa kamar bashi yayi ba.


Da kyar na had'iye wacce ke bakina Zeena na ban hakuri shuru kawai nayi, can naji muryar Hajara na cewa "ke yanzu Sa'ida a haka kike son Ya Abbas komi kayi baka iya masa ba, ga shegen miskilancin tsiya da fad'an da babu gaira babu dalili, yanzu dan Allah miye cin abincin Maryam yayi da zaice wai kamar akuya nacin abinci kai jama'a, ni a yadda nake gani ma ita da yanga take cin abincin ta, amma shi yanzu ji abinda ya ce" girgiza kaina nayi ina jin abincin ya fice min a rai tashi nayi ina wanko hannuna na wanke baki na na dawo, Sa'ida

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment