Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[2/25, 21:46] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞

🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀


*STORY & WRITTING*


*BY*


*MARYAM AHMAD PAKI*
(07037004285)



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*✍🏽



Bismillahir rahmanir rahim
Dukkan yabo ya tabbata ga Allah (S.W.A) da ya ba ni ikon shiga sabon wani littafin.
Wannan littafin nayi shi dan fad'akarwa, nishad'antarwa, ilimantarwa da kuma du ba da halin da muke ciki a yanzu.

Dafatan za ayi amfani da darasin dake ciki ayi watsi da abin da bai da kyau a littafin



*Wannan shafin sadaukarwa ce ga duk wani mai son littafi na da kuma wanda su kai ta min Magana akan fitowar wannan littafin*
*Nagode da kulawa sosai*



*Har kullum ki na raina*
*Mufida mu’azu*
(Marubuciyar Auren dole)
*Ba zan gaji da nuna kulawa ta gare ki saboda yadda kike ba ni k’warin gwiwa*,
*ba abin da zan ce miki sai dai in ce Allah ya bar kauna kuma ya biya miki buk'atun ki*


Tunatarwa:

*Ko kasan/kinsan ina ake sanya zunuban mu yayin da muke sallah?

Manzon Allah (S.A.W) ya ce: duk lokacin da bawa yake sallah ana sanya dukkan zunuban sa a wuyan sa da kafad’un sa, duk lokacin da yayi ruku’u ko sujada zunuban sa za su dinga fadowa kamar yadda ganye yake fadowa daga bishiya don haka mu tsawaita sujada da ruku’u domin zunuban mu su ragu.



1&2


Yau a garin Kaduna an tashi da matsanancin zafi kasancewar zafi ya fara shigo wa wanda yake hana mutum sakat, dawo wa ta daga makaranta kenan na cire uniform d’ina na fada toilet d'in dake jingine a d'aki na, ko side d'in Ummu ban shiga ba saboda zafin da ke son sa min wani ciwon, ko minti 5 ban d'auka ba na watsa ruwan sanyi kana na fito na zira 'yar t-shirt da wani simple skirt na nufi d'akin Ummu wanda na same ta zaune a 3 sitter rike da hisnul muslim a hannun ta tana nazari.


Sallamar da nayi ne yasa ta katse karatun da take yi ta d'ago ta na kallo na tare da murmushi a fuskar ta, jikin ta naje na kwanta kasancewa ta mai son jiki duk da yaya Aminu ba ya so amma Ummu cewa take yi a k’yaleni ni ce auta kuma d’iya mace a gaban ta.

"Ummu sannu da gida"

"Yawwa Fatima an dawo? ya lesson d’in"

Cikin shagwa ‘ba na ce "gaskiya Ummu na gaji da wannan lesson d'in waec da neco d’in nan, mutum ya dawo a gajiye gashi ba a tashi da wuri ga zafi yazo, a class mutum yaji kamar ya cire kayan jikin shi saboda zafi yanzu fa daga dawo wa ta sai da na watsa ruwa amma ji nake kamar ana kara min wani zafin, gaskiya ki yi ma yaya Aminu magana saboda shine d’an sa ido shi da wannan abokin nashi yaya Faruk, zan daina zuwa lesson d’in nan, yanzu ban da na school da nake attending kuma an kara sa ni a wani extra school ran weekend sai kace wata mango park"

Dariya Ummu tasa tace "kai auta ina laifin wanda ya damu da ilimin ka ai in ba a gode mai ba bai ci kuma a kushe shi ba, kiyi hakuri ki k'arasa lesson din tunda kun kusa zana waec da neco d’in sai ki huta gaba d’aya tun da kinyi jamb kafin admission ya fito a fara zuwa jami’a

Cikin jin dad'i na rungume Ummu ina murna ina cewa "wa ya ganni a jami’a?

dariya Ummu tayi tace "auta kenan"

sallamar yaya Khaleel ce ya katse mana hirar da muke yi

Amsawa muka yi kana ya saki murmushi yace "auta me ake tattaunawa ne don na ga hirar ta muku dadi"

Hararar wasa na mai tare da murgud’a baki nace "ba sai kaji ba kuma ni kadaina ce min auta saboda na girma kuma in k'awaye na suka ji dariya zasu min"

Dariya yayi yace "to shikenan sister na daina tun da kin girma"

Kallon Ummu yayi yace "yaya Faruk ya dawo yace in gaishe ki kafiin ya zo"

Yalwata murmushin ta tayi tace "ikon Allah yaushe ya dawo"

Amsa mata yayi da cewa "jiya ya sauka kin san ya kwana biyu bai zo Kaduna ba ya ‘boye a Abuja, kin san aikin sojoji sai a hankali ba sa samun hutu, nima na biya gidan ne in gaida momi mu ka hadu"

Ummu juyowa tayi tana kallo na wadda tun san da naji an ambaci yaya Faruk nayi shiru kamar ba na d’akin tace "kin ji yayan ku ya dawo ki tashi ki je ki shirya mai abinci saboda nasan anan zai ci na dare"

d’aure fuska nayi nace "gaskiya Ummu na gaji, kina gani yanzu na dawo daga makaranta sannan ki ce in dafa mishi abinci, ba ga iya talatu nan ba, basai ta dafa mai ba, yanzu yana zuwa ni zai fara sa wa ido da fad’a, indai ya dawo ban da sukuni a gidan nan, ya dinga d’akko laifi yana d’ora min ko banyi komai ba, Allah-Allah nake yi ya koma ga kuma takurawar yaya Aminu in yazo gaishe ku, ni ko ta ina a takure nake, na fara matse hawayen da ya fara zubo min

Shi kuwa yaya Khaleel murmushi kawai yake yi saboda yasan halina na rashin shiri da yaya Faruk saboda yadda bai wasa a family, yafi yaya Aminu zafi ko dan kasancewar sa soja ne? oho! haka kuma abokai ne shi da yaya Aminu kasancewar su sa’annin juna, don haka ya matsa kusa da ni yace " oh Fatima miye abin kuka? kin san yaya Faruk baya cin abincin ‘yan aiki kuma ba ya d’aukan raini yanzu sai ya baki purnishment d’in da zaki kwana biyu kina jinyar kanki don ma na lura kamar ke yana raga mi ki kuma kin san indai yazo sai kin dafa abincin nan saboda shi yace a dinga barin ki kina dafa abinci, Ummu ta dinga hutawa kuma yana da gaskiya kinga kince kin girma, kwanan nan za a fara zancen auren ki kinga in kin je gidan mijin ki basai ki dinga dafa wa mijin ki kala kala abinci mai dad’i ba kinga anan ai yaya Faruk yayi taimako ya k'arasa maganar yana dariya.
[2/25, 21:46] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞

🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀


*STORY & WRITTING*

*BY*

*MARYAM AHMAD PAKI*
(07037004285)





*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*✍🏽



*Dedicated to Maimuna* (On top)
*Marubuciyar*(‘yar shugaban kasa)

*I really care 4 u*, *because u a so special to me*




*QUESTION OF THE DAY*

Wace mata ce a cikin matan manzon Allah (S.A.W) Allah ya ba ma Annabi Muhammad (S.A.W) umarni ya janye sakin da ya mata saboda ta kasance mai yawan azumi?




3&4


Mik'ewa na yi ba tare da na ce komai ba saboda in na biye ma yaya Khaleel sai ya sa ni kuka saboda in ya fara tsokana ta wani sa’in sai yaga nayi kuka yake kyale ni.


Kitchen na nufa ina tunanin mai zan dafa mai wanda bazai d’au tym ba don ni a gaskiya ta mu bata zo d’aya da shi ba kasancewar yadda yake da zafi da fad’a ga salon mugunta duk ya iya shi, ko da yake ai ba a banza ba tunda soja ne dole yasan style na mugunta ga son girma kamar gyambo, duk da wani sa’in ya na ja na da wasa amma duk da haka na kasa sabawa dashi.


Farfesun kayan ciki na dafa mai da soyayyar taliya na had'a da zob’o wanda yaji kayan had'i na ajiye akan dining table

Tun da naci abinci na wuce d'aki na fara chat da friends d'ina don ina ganin ya fi min akan in zauna ayi hira da ni in dai yaya Faruk na nan.
Ina chatting ina jin hirar su da yaya Khaleel da yaya Aminu da yazo gaishe da su Ummu kasancewar shi yayi aure, jefi- jefi nake jan tsaki saboda yadda na takura a d’akin, ban san tym d’in da na d'auka ba ina chatin sai tsayuwar mutum naji a baya na, ganin haka ne yasa na juyo don in ga wani gwanin ne ya tsaya a baya na ba tare da yayi sallama ba.

Waigowar da zanyi na gan shi ya k'ure ni da ido fuskan nan ba alamar fara’a kamar an aiko mai da sak'on mutuwar shi cikin shigar shi ta wani lallausan yadi an mishi simple d’inki.


Cikin karkarwar murya na jawo miyau da k’yar na had’iye ina addu’a a raina Allah yasa kar ya amshi wayar nan saboda ya hana ni chatting yace wai nayi yarinya da chat.

"Ina wuni…yaya Faruk! ka dawo lafiya?

Ci gaba yayi da kallo na ba tare da ya amsa gaisuwar da nayi mai ba illa hannun shi da ya mik’o min.

A raina na ce "wannan yayan akwai rainin wayau to ni mai zan mik'a mai da ba zai iya min Magana ba, amma nasan maganin shi duk da nasan waya ta yake nufin in bashi.

Juyawa nayi ina dube-dube kamar ina neman wani abu sannan na juyo na kalle shi nace "yaya me zan baka?

Sai da ya gama shan k'amshin shi kana yace "au baki san me zaki bani ba koh?
To mik’o min wayar ki tun da kin zama mai kunnen k’ashi, how many times did i warn you that i don’t want you to involve yourself in this social media amma baki ji ba? nasan matakin da zan d'auka a kanki don kin ga ina raga miki ne ki je ki tambayi Anisa za ta baki labari na don na ga alamar kin manta ni"

Raina ne ya so ma ‘baci saboda ganin har yau yaya Faruk d’in nan kallon yara yake mana, in ban da haka ya za ace ina class d'in karshe a secondary amma yace wai ban kai in yi chat ba wanda yanzu kowa yasan harkar socialization ake yi amma shi kullum yafi son ya gan mu a local.

Tsawar da ya min ce tasa hannu na yana rawa na mik'a mai hawaye na zuba a ido na.

Ko da ya amshi wayar whatsapp d’ina ya fara bincika kasancewar ina online,
ya d’au kusan 5 min yana latsa wayar kafin ya d’ago yana watsa min harara sannan yace

"Teemah! ya ambaci suna na kasancewar wani sa'in haka ya ke kira na.

d’ago wa nayi na kalle shi saboda yau ban san kalar muguntar da zai min ba, ni dai addu’a ta ita ce kar ya hana ni wayar saboda ta na min amfani, ga internet da nake research a ciki, ga chat d’in nan da nake k'aruwa dashi, ga online novels da na ke karanta wa yake sa ni nishad'i da kuma darusa da nake koya a ciki.

Katse min tunani yayi da cewa "Fatima wai ba ki ji kiran da nayi miki bane? Ko zaki nuna min yanzu kin yi girman da baza a miki fad’a bane!
Listen to me carefully!
Teemah ba na so ina miki hukunci saboda wasu dalilai amma hakan bazai hana in kin yi laifi ki amshi purnishment ba, time without numbers na sha fad'a miki bana son kina wannan chat d’in nan saboda har yanzu ke yarinya ce tunda har yau baki gama secondary ba, yanzu k'aramar ki dake har kin san ki shiga groups d’in matan aure su na bud’e miki ido kina ganin posting d’in su na zaman aure, ki bari in time yazo da kaina zan ba Ku damar chat ke da Anisa because as now you are too small, yanzu ma Allah ne ya taimake ki, ban ga alamar kina chat da maza ba, da ke da waya sai in kinyi aure ko in siyo miki k’aramar nokia in ba ki, this should be the last time da zanyi warning dinki kina ji na koh?
Gyad’a mai kai na yi saboda wani abu da ya tokare min a k’irji saboda har ga Allah yaya Faruk na matsa min, ni ban da damar yin abin da raina yake so kenan in dai yana gidan ko shi wa ya takura mai? in ban da ya mai dani wata mara class zai ce zai siyo min k’aramar nokia da haka in zauna ba wayar a hannu na mana, Shi wa ya san abin da yake yi a Abujar zai zo yana takura min, waye bai san sojoji da son mata ba zai zo yana takura min.
Kamar yasan abin da nake cewa a raina yayi wani mayaudarin murmushi yace "ki gama zagi na a ranki lokacin ki ne kin ga kin girma ne da ai baki yi ba! kin san dai hali na"

"Laifin ki na gaba shine mai ya hana ki kizo ki gaishe ni san da kika ji na shigo gidan ko ki na so ki nuna min yanzu kin wuce wannan level d’in don naga kanki na rawa.

Rasa amsar bashi nayi don haka nace " ni banji shigowar ka ba shi yasa"

ta‘be bakin shi yayi alamar bai yadda da abin da nace ba illa cewa da yayi
"Teemah manya!

Iya k'arshe yau Yaya Faruq ya kai ni saboda Magana d’aya sai ya wa ni ce na girma to da haka yake so nai ta zama don haka ban san lokacin da na d’ago kaina na watsa mai harara don kar ya gane sai na fara murza ido na alamar wani abu ya fad’a min a ido.

re-action d’in da nayi yasa ya fara dariya saboda ko da can yasan ni da tsiwa da neman tsok’ana, bai ce min komai ba ya wurga min wayar akan gado na ya fita daga d'akin.


Wata nannauyar ajiyar zuciya na saki saboda Allah ya raba ni da d’an ka’ida lafiya kuma ni jin dad’i na da bai tafi min da wayar ba, haka nayi ta zancen zuci har bacci ya dauke ni
[2/25, 21:46] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞

🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀


*STORY & WRITING*

*BY*


*MARYAM AHMAD PAKI*





*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*✍🏽



Wannan shafin naku ne

Sameena Aleeyou (Surukas)💞💞
Marubuciyar (Shak’uwa ce)

Ina jinjina miki da irin talent d’in ki na rubutu
Fatan alkhairi gare ki


Ki na raina

Jamila Sama’ila Yusuf 💖💖
Marubuciyar (A dalilin kane)

Allah ya bar zumunci


*Jinjina ga Hajara isa na amsar da ki ka bayar dadai na question of the day*.
*Amsar ita ce nana Hafsa radiyal lahu anha*

*Zanyi amfani da wannan shafin na gode wa masu kira na da kuma wanda suke min magana a pc chat, ba abin da zan ce muku sai godiya*, *pls zan jawo hankalin masu kira na ba akan novel ba ko sa da zumunci*, *duk wanda yasan dan wani nufi zai kira ni*, *ba na buk’ata saboda ba dan haka na sa numba na ba*, *saboda haka a kiyaye*, *ga masu cewa in turo musu ci gaban novel d’in*, *kuyi hakuri yanzu aka fara labarin*



DARAJAR MUTUM DA CIKAR K’IMAR SA

Ka da ka/ki damu da abin da ya wuce, don ba zai dawo ba.

Ka da yau ta sha maka/ki kai, domin gobe ma rana ce.

Yafe wa wanda ya cuce ka ni’ima ce.

Tuna abin bak’in ciki da damuwa, wahala ce

Manta alheri, butulci ne.




5&6


Washe gari na shirya cikin uniform d’ina na tafi makaranta, ko da aka tashi break, group muka yi a can k’arshen class d’in mu muna tattauna yadda graduation d’in mu zai kasance da kuma party d’in da za mu yi organizing.

A raina neman mafita kawai nake yi domin nasan zai yi wuya ne a bar ni na je partin da ‘yan class d’in mu suka had’a tun bare in wannan mugun sojan na nan don wani sa’in gwara yaya Aminu ya fishi sauk’in kai da tausayi.

Ashe kuwa za ayi drama da ni don yadda naci burin wannan graduation d’in da party d'in ina ganin ba abin da zai hana ni halartar shi sai wani ikon Allah amma ina jin duk hukuncin da yaya Faruk zai min sai naje sai dai in na dawo ya yanka ni k’arewar hukunci kenan.

Muna cikin hirar ne sai ga Anisa (k’anwar yaya Faruk) ta shigo class d’in mu kasancewar school d’in mu d’aya da ita sai dai ita tana SS3B ni kuma ina A,
bayan ta gaisa da ‘yan class d’in mu ta mik’o min hannu muka tafa, na kalle ta na ce "mutuniyar jiya ban gan ki online ba?

Yamutsa fuska tayi kana ta ce " ina na ga tayin chat, yaya Faruk ya dawo gwara in kiyaye da in ja ma kaina ya k’ara fasa min waya ta"

Kallon ta nayi da mamaki na ce "shi yaya Faruk d’in ne ya ta’ba fasa miki wayar?

Harara ta tayi ta ce "ke wani sa’in sai ki dinga yin kamar baki san halin shi ba, fasa min ita yayi sai wani daddy ya k’ara siyo min".

Dariya na fara yi na ce 'ki ce Allah ne ya taimake ni jiya nima yazo ya tarar da ni ina chat sai masifa da yayi ta min amma bai fasa wayar ba, nan na kwashe yadda muka yi dashi na fad’a mata.

Kallo na tayi ta girgiza kai tace "ke Allah yana d’aura ki akan yaya Faruk, ni da yazo ya ganni ina chat wani mari da ya min ban san lokacin da na rungume shi ba, shi kanshi sai da yayi dariya don rashin tausayi ya d’auki wayar nan ya maka min ita da bango gashi a lokacin daddy bai dad’e da siyo mana ni dake ba, ranar in gaya miki ko abinci ban ci ba sai kuka da na dinga yi, momi ce ta dinga lallashi na tace za a siyo min sabuwa sannan na hak’ura"

Ta na gama ba ni labarin na dinga mata dariya ina ce wa "gaskiya kina shan hukunci a gurin yaya Faruk"

Dariyar da naci gaba da yi ne yasa ta d’aure fuska tana cewa "ke wani sa’in Fatima kamar zautacciya, yanzu miye abin dariya kuma in dai yaya Faruk ne ba wanda ya k’yale ke ma wataran zaki fad’a trap d’in shi ne"

Na kalle ta na ta’be baki na ce "in Allah ya yarda ma bazan bari na fa’da tarkon shi ba, kar ya bani purnishiment d’in da zanyi fitsari a wando ban shirya ba"

Dariya muka yi gaba d’aya ni da Anisa muka sake tafawa.

Bell d’in da aka buga ne na koma wa class ya katse mana hirar da muke yi, mik’ewa Anisa tayi tace " in zaki tafi gida zan bi ki yau a can zan kwana na riga na fad’a wa momi"

Cikin jin dad’i na ce "yau akwai chapter kenan amma gaskiya ni ba zan tsaya extra lesson d’in nan ba na gaji gida zan tafi"

Anisa ta amsa min da ba komai sai mu tafi, in da rabon mu sha purnishment shi kenan in muka sami yaya Faruk a gidan"

Duka na kai mata ina cewa "bakin ki ya sari d’anyan kashi, in ma purnishment d’in ne ai ke zaki fi shan wuya"

Da sauri ta d’aga min hannu tana dariya ta fita daga class d’in saboda shigowar malamin physics.


Ana buga bell na closing ba mu tsaya extra lesson d’in ba muka nufi gida tunda ba d’aukar mu za a zo yi ba.

Ko da muka shiga cikin parlour, zancen yaya Faruk muka ci gaba da yi inda nake cewa "Allah ya taimake mu d'an sa ido baya nan, yanda ba na k’aunar mutuwa haka ba na k’aunar hutun yaya Faruk, don wani sa’in gwara yaya Aminu kana mishi dad’in baki zai kyale ka"

Anisa ta kar’bi zancen da ce wa "yanzu ki duba ki gani, d’an gidan k’awayen mu ba a bari muje kullum muna gida sai kace wasu daddawar d’aka"

Dariya muka yi naci gaba da ce wa 'k’yale su zan dawo da tsiwa ta, zamu fi daidaitawa, tun bare yaya Faruk d’in nan duk yafi matsa mana, haba takurawar tayi yawa"

Mintsini na da Anisa tayi yasa na ce "miye haka! zaki wani mintsine ni, kin san ba na son a ta’ba min fata"

Shirun da naji tayi ne yasa na kalle ta na ce " ke wai lafiya kika wani daskare a nan sai kace kakide"

Still ba ta min magana ba don haka nace mata "sai kiyi ta tsayuwa har tsayuwa tazo ta same ki"

Juyawar da zanyi kawai na ga mutum kwance a 3-Sitter yana danna remote kamar bai ji abin da muke cewa.

Saboda k’arfin hali irin nawa na ce "yaya Faruk sannu da gida" sannan na juya da nufin tafiya duk da k’irji na da yake dukan uku-uku.

"Teemah" ya kira ni cikin tsawa.

Tsaya wa nayi ba tare da na amsa ba.

"Ke da Anisa kuzo nan"ya fad'a cikin fushi.


A cikin mu an rasa wanda zai fara k’arasa wa gurin shi saboda tsoro.

" idan ku ka bari na k’ara muku magana sai kunyi fitsari a wando amma in kuna musu ku gwada ku gani"

Da sauri muka k’arasa gurin shi saboda sanin halin muguntar shi.

Shiru yayi kamar bazai yi magana ba can yace "zan yi maganin ku, na ga kuna tashen iskanci, zan sauke muku abin da ya ke kanku, ku yanzu har kunyi girman da zaku dinga zagin yayyin ku da gulmar su, ke Fatima har kina cewa zaki dawo da tsiwar ki, idan baki yi haka ba baki cika fitsararriya ba, dama naga kanki na rawa, zan dawo dake normal in cire miki abin da ke damun ki"

Ya juya ga Anisa wacce sai zare ido take yi alamar tsoro ya ce "ke dan uban ki har da cewa ana takura muku kamar dadawar d’aka ko? to kun ja ma kanku dan ku da fita sai in makaranta zaku, idan ko na kuskura naga k’afar ku a waje sai na cire muku ‘kafa d’aya"






*Hmmm readers nima kaina zan so in san wani hukunci yaya Faruk zai basu*
*Ku biyo ‘yar mutan paki don jin yadda dramar zata k’are*.
[2/25, 21:46] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞

🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀


*STORY & WRITTEN*


*BY*

*MARYAM AHMAD PAKI*






*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*✍🏽




*Wannan shafin na ku ne*

*Batul Adam jattako*
*Marubuciyar* (Dama ta) 💔💔💔

*Ina jin dad’in shawarar da kike bani da kuma kulawar ki gare ni, ba abin da zan ce miki sai godiya*.





*Ban manta daku ba*

*Mrs
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment