Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

AMANI




Littafin






SUMAYYAH ABDULKADIR (TAKORI)
takorikabara@gmail.com

AMANI
TARE DA NI, SUMAYYAH ABDULKADIR

SHIMFIDA
Safiyar yau wadda ta kasance Lahadi, an wayi gari da lullumin hadari mai hade da sassanyar iska mai dadi a gidan su Amani, wanda ke cikin rukunin gidajen GRA a birnin Katsinan Dikko. Kasancewar lokacin ya kasance lokaci ne na tsakiyar damuna, kada ka so ka ga yadda shuke-shuken dake harabar gidan suka bude ganyayyakin su suka yi korra sharr, suna bada kamshin furanni da bishiyu kala-kala, musaman da bada jimawa ana iskar sai yayyafi ya soma sauka, don haka iska ce mai dadi kawai take kadawa a gidan mai sanyawa alummar gidan nishadi, ciki harda Amani dake can upstairs, ta bude tagogin dakin ta iskar na tadda har cikin toilet din da takw wanka.
Dai dai lokacin da aka tsuge da ruwan saman kamar da bakin kwarya. Amani ta fito wanka, daure da towel a jikin ta, ta karasa ta rufe tagogin ta don dakin ya soma jikewa, ta zauna gaban mudubin kwalliyar ta dan kasar Mexico mahadin furnitures na gogaggen katakon kasar waje dake dakin kamar dakin matar aure. Kamar yadda yake a aladar ta kullum, daga fitowa wanka sai ta bata lokaci tana kwalliya a zaune a kan stool, kamar mai shirin tafiya beauty contest in ka ga yadda take bata lokaci wajen tsantsara kwalliya kullum.
To yau ma hakan ce ta kasance, Amani ta kwashe kusan mintuna talatin tana gyara fuskar ta da serene make-up, bakin nan ya dauki maikon wet lips na Elizabeth Arden sai sheki yake kamar ka sace bakinka gudu irin wanda ake kira kissable lips, ta shirya cikin wani dan shafal din swiss lace ruwan gwaiduwar kwai da feshin golden a jikin sa, duka wannan adon na karshen mako ne bana zuwa wani waje ba, koda-yake dama tun filazal ita maabociyar ado ce da son kyale-kyalen mata irin wanda ya wuce kima, musamman a renaku irin wadannan na karshen mako da take wuni a gida, don ita bata yawace-yawacen gidan kawaye ko bukukuwa don basu ishe ta kallo ba.
An yi mata wani kyakkyawan dinki na zamani na doguwar riga wadda ta kama ta daga sama ta bude daga kasa sosai kamar (A shape). Kai da ganin dinkin nata kasan na yayan gata ne kuma ya ja kudi a jikin sa.
Amani tana sakkowa daga matattakalar bene inda dakin ta yake a cikin gidan su, wata irin tafiya take yi kamar hawainiya, kamar bata son taka kasa, kuma kamar tsinin takalmin ta bai dame ta ba. Sakkowa take daga benen cikin takun ta na kasaita da rangaji irin na yan matan da ke cikin lokacin su, suka kuma yi katarin samun rayuwa ta gata da wadata, dai-dai da yadda suke buri ko suke son samun ta a duniya.
Daga nesa sai tayi maka kama da matashiyar macen Dawisu saboda iya ado da iya baza tafiyar kasaita, koko zangarniyar dabinon da iskar hunturu ke kadawa sabida yadda ilahirin kyakkyawan jikin ta ke rangaji tana zuba kamshi. Kai Amani karshe ce a class da gayu karshen duk inda zaka iya kwatanta ta. A haka ta isa babban falon gidan su, inda ta tadda mahaifin ta yana aiki cikin wasu muhimman takardu da naura mai kwakwalwar bisa cinya (laptop) a gaban sa.
Tun kafin ta gama sakkowa daga benen hankalin mahaifin ta Hon. Usman ya kai gare ta sabida karar takalmin ta mai tsinin dunduniya. Ya daga ido ya dube ta, sai ya sunkuyar, yana cigaba da danna naurar gaban sa cikin kwarewa, ita ta san baban ta Guru ne a computer da lissafi bay a taba yarda kwandalar sa ta bata cikin lissafin sa, in ma ka sace ta don kana maaikacin sa zai gane, kuma sai ka yi aman ta.
Cikin sigar kirari kamar ba mahaifin ta da ya haife ta ba, sai ka yi tsammanin wani saan ta ne koko abokin wasan ta, Alhaji shiga fadin TA-FISU YAR GIDAN BABAN TA! Ya saki dariyar farin cikin ganin ta ba tare da ya dago ba, hankalin sa na bisa lissafin sa don kada ya bata kwandala, ya ce Ta-fi-sun Daddy an fito?.
In ji Alhajin cikin kulawa, sai yanzu da ya kammala kirgen sa kaf! Sannan ya dago ya dube ta, ya kuma bata hankalin sa, bayan ya kashe naurar gabadaya, cikin murmushin kauna da kulawa cikin yan kananun firi-firin idanun sa masu kama dana yan China.
TA-FISU-KIN FI SAURAN MATA! Ya kara fadi cikin kambama yar tasa, wadda a kullum ya dube ta surar mahaifiyar ta Jalan ke masa gizo, har kullum yana godewa Allah da wannan kyakkyawar halitta da ya bashi a matsayin diyar sa, yana godewa Allah da ta debo komai na Jalan bata ko dauko farcen sa ba, ji yake kamar ya lika ta a goshi don So da alfahari, banda Allah sarkin hikima da tsara halitta yadda yake so, wa zai iya hakan? Mai sanya mummunan mutum bakikkirin kamar sa ya haifi irin wannan kyakkyawar halitta? Ai sai Allah Al Khaliqu Sarkin kaga halitta a yadda ya ga dama, Ubangijin sammai da kassai. Mai sanya mummuna ya haifi kyakkyawa. Shi da kan sa Uban yau da ya dube ta sai da ya ce tsarki ya tabbata ga sarki Allah!
Domin gani yayi gabadaya ta rikide masa ta koma mahaifiyar ta Jalan, sau tari har gizo take masa da Uwar ta, shi yasa har kullum yake kara kaunar ta, duk soyayyar da yake wa uwar ta kan ta ya koma. Har gobe bai auri macen da yake so yake darajjawa irin Jalan ba. A yau ganin ta yayi replica din Maman ta, wato kamar Jalan ce gaban sa shekaru ashirin a baya.
Amma Amani har ta fi ta sheki da daukar ido, don nata kyan ya hadu da gyara da kyale-kyalen zamani mai tsada.
Alhaji Usman Faskari, baki ne wuluk, tittirna, gajere, kuma mai dagaggen hanci da kananun idanu mitsi-mitsi kamar na yan birnin Sin. Kai babu wata suffa a jikin Alhajin da zaa kira kyakkyawa, a cewar sa shi yasa Jalan ta ki zama da shi duk arzikin sa. Jalan mai kama da matan Hurul-eeni don kyau. Ta sha ce masa firgita ta yake cikin dare, ya daina shigo mata daki in dare ya yi, ya dinga bari sai gari ya waye. Ta fannin halayyar Alhajin ma sai mu ce sai a hankali, domin dai a zahiri shi mutum ne mai mammako (marowaci) kuma mai son kan sa da yar sa kadai. Ya mallaki mahaukaciyar dukiya da shi kan sa bai san adadin ta ba, wadda ya mallaka ta hanyoyin duka yaki halaal, da ya ki haraam, tunda kuwa gogaggen dan siyasa ne na jiya ba na yau ba, wadanda suka dade suna ci da tada kai hadi da birgima cikin dukiyar alumma da sunan siyasa da cigaban alumma.
A halin yanzu yana rike da shugabancin jamiyya mafi karfi, mafi shahara da farin jini a wurin alummar kasar Najeriya. Wato jamiyyar AC da aka fi sani da (Action Congress) ta kasa bakidaya. Ya iso ga matsayin shugaban jamiyya ne bayan ya rike manyan mukaman Siyasa da baza su lissafu ba, tun daga karamar hukumar sa ta Faskari, har zuwa matakin jiha, wato jihar sa ta Katsina, har zuwa halin da ake ciki yanzu da ake damawa dashi a Gwamnatin Tarayya.
Cikin manyan mukamai na karshe-karshe da Hon. Usman Faskari ya rike har da Sanatan Katsina ta kudu sau biyu.
Idan ka cire harkar siyasa da yafi bada karfi da yin kaurin suna a kai, don da ita aka san shi, da ita yayi ficce, har ila yau, shi din kuma babban dan kasuwar ketare ne (International Business Man) wanda koda siyasa ko babu ya riga ya haye tudun mun tsira.
A can baya tun kafin ya haifi Amani har kasuwancin fidda Iron ore da aluminium ore yayi, wato exporting natural resources da ake hakowa a kasashen Afrika daban-daban irin Saliyo da Madagascar, yana da shahararrren kamfanin sa na kan sa a Katsina mai reshe a birnin tarayya, Abuja wato FASKARI INVESTMENT amma rayuwar sa tafi yawa a garin Katsina.
Daga baya bayan Amani ta tasa ya mayar wa da kamfanin suna Amani Faskari Investment, kamfani ne na komai da ruwan ka a harkar shigo da kayan ginin gidaje dana sakawa a gidaje, ba irin kayayyakin da basa shigowa da su da suka shafi wannan bangaren daga kasashen ketare musamman kasar Faransa da kasar Mexico inda ya zuba mafi rinjayen hannayen jarin sa, har ta kai ta kawo rabin rayuwar Usman Faskari ya zama na yawo tsakanin Najeriya da Faransa da Mexico, komai na kamfanin sa kowa ya san daga kasashen nan France ko Mexico yake kawo su, wato daga makerar su sai kamfanin sa kadai, shi yasa baa fiya samun irin kayan sa a Najeriya sosai ba, abin nufi, kayan ginin kamfanin AMANI FASKARI INVESTMENT LTD sun fita daban. Kama daga kofofi, tagogi, tiles, marbles, da duk abubuwan ceramic da ake amfani dasu wajen ginin gidaje. Masu ginne-ginen estates da gidaje a Katsina da Abuja yawanci duk a kamfanin sa suke order.
A halin yanzu, Alhaji Usman Faskari, wanda alumma ke kira Hon. Faskari, yana da shekaru hamsin da biyar amma in ka gan shi arbain zaka bashi sabida jin dadi da kula da lafiyar sa, bashi da wani buri da yasa a gaba yanzu irin diyar sa Amani da rayuwar ta, babban burin sa kullum shi ne farin cikin ta, jin dadin ta da walwalar ta. Hon. Usman ya wadata Amani fiye da kima, tun a kananan shekarun ta Amani ta san tafi sauran tsararrakin ta gatan aljihu dana Uba, ya kuma fifita ta ya sangartata wanda hakan ya shafi tarbiyya da muamalar ta da mutane, saboda ya jika ta da komai na jin dadi da bukatun rayuwa ba tare da ta yi maraicin mahaifiyar ta ba, wadda Amani bata taba gani ba ko a hoto, alhalin tana raye ba wai ta mutu ba.
Iyayen ta sun rabu tun tana tsumman haihuwa, a cewar sa saboda munin sa ne Jalan ta ki zama da shi, wanda kullum take cewa yana firgita ta, a zahiri shi yake tunanin hakan, amma dalilai da yawa ne suka hana Jalan iya zama da shi, ciki har da halayen sa na kankamo da rowa, dama kuma auren dole iyayen ta suka yi mata da shi a dalilin ya saye mahaifin ta da dukiya.
Tunda ta koma kasar su (Sierra Leone) bata kara dawowa Najeriya ba, wai da sunan ganin yar da ta Haifa ta tafi ta bari bata ko shayar ba, shi kuma bai kara bin bayan ta ba, bai ma san tana raye kota rasu ba. Sai ya maida hankali a kan rainon kyakkyawar diyar data bar masa wato AMANI, ya kuma maida kafatanin soyayyar da yake yi wa Jalan a kan ta, bai yarda ta nemi wani abu a rayuwar ta ta rasa ba, komai darajar sa, bai yarda ta yi kukan babu ba, ba ya ko tunanin ya dace ya aurar da ita haka, kullum kallon yar kankanuwar yarinya yake mata, yadda take shekaru ashirin a baya sanda yake goya ta da kan sa a bayan sa.
Shi kan sa bai san iya son da ya kewa yar sa Amani ba, ko iyakar adadin abinda ya mallaka, kuma komai nasa da sunan tilon yar sa AMANI yake rubuta hakkin mallakar sa. Wato ita yake sanyawa hakkin mallaka a rubuce gaban lauyoyin sa.
Wannan ne kuma babban abinda ya assasa bakar kiyayya tsakanin Amani da matar sa Hajiya Rabi, saboda ita bata taba haihuwa da shi ba. Kafin Hajiya Rabi ya auri mata kusan tara yana sakin su, duk ba a kan komai ba sai a kan rikon Amani, don sun kasa yi mata irin rikon da yake so na gaskiya da amana, kankanin laifi zasu yi, ya basu takardar saki in dai a kan yar sa Amani ne, da ya sakawa suna TAFISU. Yake mata kirari da Kin fi sauran mata.
Haka masu aiki ma basu tsira ba, kullum cikin canzawa Amani su ake, saboda a cewar sa basa kula masa da ita yadda yake so. Wannan yasa Amani ta tashi yarinya sangartatta, hamshakiya, mai girman kai, mai yawan alfahari, mai raini ga mutane, kuma mai izzah da dagawa da son a bata girma koda kuwa mutum ya haife ta.
Ga rashin tauna magana da kowa take Magana, har shi mahaifin nata kuwa wani lokacin bata masa magana da girmamawa, ka yi mata magana ta mayar maka da harara. Yadda duk magana ta zo bakin ta haka take furzar da ita ga kowa cikin raini da gatsali, bazata yi laakari da yawan shekarun da ka bata ba zata iya marin ka ko ta tofa maka miyau a fuska muddin ka shiga gonar ta.
Sabida girman kai irin na Amani ko kawaye cikin tsararrakin ta bata da su domin ta raina ajawalin kowa, da an fara kawancen zaa babe, saboda ba kowa ke jure halin ta na raini da dagawa ba.
Kawar ta daya ce da suka yi karatun sakandire tare a (Ulul Albaab Science Secondary School Katsina) wato Hamida Balewa wadda itama Baban ta tsohon dan siyasa ne, da ya rike har mukamin gwamna a jihar Baucin Yakubu.
Hamida ta iya da ita da halin ta, don ta fi ta hankali da hakuri kuma tana son Amani kamar yar uwar ta, shiyasa suka rayu tsayin lokacin nan basu rabu ba, har zuwa yanzu suna tare a shekarar nan da suka kammala karatun Jamia tare a jamiar Tafawa Balewa.
Har zuwa lokacin da mahaifin ta ya auri Haj. Rabi, ita da kan ta Amani ta roke shi ya rufe aure-aure daga kan Haj. Rabi saboda mutuncin siyasar sa, da kuma kasancewar tana son ya zama akwai mace tare da su, duk da dai in ya saki baya jimawa yake kara aurowa, kafin ya auri Haj. Rabi ya dade babu mata, don ta karshe ta kusa kashe Amani da duka don haushi sabida ta tofa mata miyau a fuska, ita kuma Haj. Rabi ganin inda raunin Alh. Usman yake wato (son a taya shi kula da Amani da taya shi soyayyar tilon diyar tasa), sai ta saka kaimi a kai, ta kama Amanin ta rungume a farkon zuwan ta, har fiye da kima, da ta gan ta zata hau rawar jiki da hidima da ita a gaban Alhajin, irin yadda Hon. Din yake so matar duk da ya aura ta yi wa Amani, Haj. Rabi ta shiga nuna mata soyayya har fiye da shi. Hakan yasa ta shiga ran Alhaji. Amma ba haka abin yake a zuciyar ta ba.
Wannan ne yasa tayi dan nisan zango a gidan Hon. Usman, domin a kalla zuwa yanzu tayi shekaru kusan hudu a gidan su Amani, sauran matan da ya aura a baya babu wadda ta rufa shekaru biyu. Amma a zahiri Haj. Rabi ba wanda ta tsana data bude ido ta gani a duniya irin Amanin.
Babban tashin hankalin ta ranar data fahimci cewa komai na dukiyar Alhajin sunan Amani yake bearing, mai nufin ya gama mallaka mata komai nasa, duk wadda zata zo sai dai ta jira dan tumunin takaba (idan ma ta yi nasarar dadewa a gidan kenan). Musamman hankalin ta ya kara tashi da likita ya tabbatar mata shekarun ta sun wuce na daukar ciki wato ta isa menopause ba matsalar haihuwa ce da ita ba yadda take zato.
Haj. Rabi tana da yara biyu mace da namiji da tsohon mijin ta na baya. Ta aurar da macen, namijin kuma yana jamia yana hannun mahaifin sa a garin su Minna jihar Neja.
**** ***** *****
Amani ta karasa saukowa daga matattakalar benen, ta karaso ta zauna a jikin mahaifin nata yadda ta saba duk girman ta, kai ka ce yarinyar goye ce a yadda take masa magana cikin shagwaba.
Daddy, saboda Allah ba zaka daina kira na da sunan tsofaffi ba ko, bana son wannan Tafisun da kake kira na da shi, kullum sai na gaya maka ka bari bana so, amma ba dama ka ga na yi ado sai ka sake kira na da Tafisu-Tafisu. Amani ta fada cikin zumburo baki, tana kallon takardun da ya kammala sakawa hannu, sakamakon ganin sunanta baro-baro a kan takardar shaidar mallakar boutique na kayan sanyawa na mata mai suna AMANI COLLECTION.
In bata manta ba tun shekarar data gabata Daddy yake shirye-shiryen bude mata boutique din nan, wato sai yanzu Allah yasa aka kammala kenan.
Alhaji ya ce ba sunan da ya dace da ke irin Tafisu, saboda ai kin fi sun ne da gaske, ina nufin kin fi tsararrakin ki gata, kin fi sauran yaya gatan Uba, kin fi su komai tunda kina da Uba iri na, wanda ke tsaye a kan duk abinda kike so, da son tsaya miki kan duk mai son shiga hancin ki. Ya fada babu wasa a maganar sa, ita ta san Daddy yana nufin abinda yake fadi, a shirye yake ya tsaya mata a kan kowa da komai. Shi yasa itama bata hada kaunar sa da ta kowa a rayuwar ta.
Hon. Usman Ya mika mata takardun yana fadin amshi ki duba Tafisu. Boutique din ki da na dade da yi miki alkawarin bude miki a nan Katsina ya kammala, yana nan a jerin shagunan Goruba Road, gobe sai kuje da MUKHY ki gani, idan da abinda bai yi ba, ko baa kawo ba, ko zaa canza cikin kayan da kika bada list aka yi odar su, sai ki fada masa, in ya so sai a kara yin sabuwar order, don yana da wata tafiyar dama nan da watanni biyu zuwa Mexico, ina saka ran zai shigo min da wasu samfurin marbles, sai ya karo miki abunda babu din.
In yaso sai ku je tare ki gani, kina dubawa kina fada masa yana rubuta min komai a tsanake.
Ai kuwa nan da nan fuskar Amani ta yi kicin-kicin, ta zama kamar hadarin da ya nausa ya yi gabas, ta yi mugun bata rai kamar bata taba fara a rayuwar ta ba, ta kirne kyakkyawar fuskar nan tata ta wani irin yamutse ta, fuskar ta a wannan lokacin sai ta koma masa exactly ta Jalan, wato mahaifiyar ta, idan kiyayyar ta ta motsa a kan sa; wata kwayar mace guda daya da ya taba so a rayuwar sa, kuma daga kan ta bai kara son kowacce mace ba, yanzun da Amani tayi hakan sai ya ga ta rikide ta koma masa Jalan har sai da gaban sa ya fadi sosai. Yanayin ta a irin wannan lokacin yafi kama da na yayan nan da baa kwaba, baa hantara, wadanda saidai iyayen su su bi abinda suke so ko basa so, fadi take cikin shagwaba, hassala da zumburo baki.
Allah ya tsare ni hada hanya da shi, Allah ya raba gatari da saran kuka, shin Daddy sau nawa zan gaya maka ka manta ne? Magana ta gaskiya ka daina hada sabga ta da ta wannan mai cunkusashshiyar fuskar da halin sumumu-kasau din.
Ina dalili mutum kullum yana faman kirnewa mutane fuska kamar malaikan daukan rai, alhalin da bazar su yake rawa? Mutum dan siriri da shi sai kafirin girman kai da bakin hali kamar na mutanen farko.
Daddy yayi kasa da murya duk da yana son yin dariya amma ya hadiye, saboda yadda ta fitittike tana furzar da maganar zaka san an tabo fushin Tafisu, cikin lallashin yar tasa yake cewa.
Uwa ta. Kullum ina gaya miki ki daina damuwa da yanayin fuskar Mukhtar cikin shaanin kasuwancin mu ko muamalar mu ta yau da kullum da shi, kowa da kika gani a rayuwa, yana da damuwa, mai yuwuwa damuwa ce a kasan ran sa take bayyana a kan fuskar sa, yanayin walwalar sa ko rashin ta ni ba zai shafi alaqa ta da shi ba, o neman kobo na because its obvious I cant do without him (a fili yake ban iya rayuwa sai tare

1 Comments On AMANI
avatar
nafisa-adamu

9 months ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment