Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Amma ko da wasa kada ka tako kafa ka zo in da mu ke! In ko ka kuskure ka biyo mu Baffa Mudi ko Kuma ka yi yunkurin lalata min tafiyar nan ta hanyar tsubbun da ka saba na lahira sai ya fi ka jin dadi!"

Baffa Mudi na mai jinjina kai ya ke fadi

"Na yarda Shehu adali, na yarda! Ka cika mai yafiya, in Sha Allah zan kiyaye sharadin ka"

Da haka ya tashi ya koma Rugar shehu cike da borin kunya. Usman kuwa wuta su ka sa suka kone layar da ke dauke da sunan Muhammadu Bello. Ranar wuni aka yi ana gayara makabarta, washagari da sassafe bayan Usman da Bello sun je sunyiwa Iyar su Sallama tare da addua, su ka tabbatar sun killace kabarin ta yanda ruwa ba zai taba tona shi ba, sannan su ka hada na su ya na su, kwansu da kwarkwatar su ka tasarwar barin dajin falgore. Baffa Mudi na ji ya na gani Usman ya kada duka Shanun da ya ke mallakin gidan Shehu be bar masa ko daya ba. Shanu ne masu yawa kwarai da gaske dan kuwa idan aka ce za a tsaya lissafa adadin su ace sharata ta ake. Haka kusan duka jama'ar Rugar Usman su ka bi, illa kalilan ne su ka tsaya tare da Baffa Mudi.

In da Rugar Shehu ke sauya sheka, gidan Malam kuwa auran su Halitta aka daura. Ba wani taro aka yi ba, auren kawai aka dora. Zainab ba ta halacci daurin auren ba bare ta kira amare ta mu su Allah ya sanya alkhairi. Babban bakin cikin ta shi ne tafiya Saudia da Sudais ya ke so yayi da Halitta a sakamakon aikin da ya samu a can. Zinaru kuwa a ranar aka mika ta dakin mijin ta.

Zainab sam ba ta canza zani ba, yanda ta ke rayuwa a da haka ta dora bayan ta koma makaranta, haka kuma ta sake bude saban account na Instagram bayan ta siyi dalleliyar wayar ta mai dauke da tambarin tufa ta cigaba da sharholiyar ta kamar yanda ta saba.

Satin su Usman da tawagar sa biyu suna yawo daga wannan dajin zuwa wannan dajin, su kutsa nan, su kutsa can, in da ya kamata a yada zango a yada cikin kokarin kare hakkin nomama ta hanyar kada shanun sa daga barin shiga gonaki, a haka har su ka iskewa wani daji arewa masogabashin kudu, dajin ya kasance mararraba tsakanin kudu da arewa.
Kasancewar dajin ya yalwatu da 'ya'yan itatuwa, ga ruwa da yanayi mai kyau, haka kuma aikwai wadataccan fili tuni su ka yada zangon su na zama dirshen, kwanan su uku suna gine ginan bukka, haka kuma masu ilimin surkulle su ma su ka dukafa wajan kafe dajin, suna shiga lungu da sako sai da su ka kafe dajin kaf ya zame mu su tamakar gida hatta macijan dajin sai da su ka san da kafuwar Rugar Shehu.

Cikin watanni biyu Usman ya kafa daular sa, Shehuntakar sa ta ginu sosai musammam da Allah ya hore masa ilimin da ya koya daga wajan Malam. Ganin yanda ya habaka gashi babu mata ne ya sanya magidan ta da yawa yiwa Usman tayin matar aure daga cikin yan matan Rugar Shehu, musammam yanda kowacce da ta ke ji da kan ta ke da burin kasancewar mata wajen Shehu. Amma Usman kullun cikin ba su uzurin cewa zai karba, Amma akwai wata ajiya da ya ke da shi birnin Kano, matukar ba ajiyar nan ya dauko ba toh be shirya aure ba.

Bayan wata biyu da sati daya da kafuwar daular Rugar Shehu, Usman ya shirya tsaf da shirin zuwa dauko ajiyar sa, in da ya wakilta Muhammadu Bello ya kula da Rugar su kafin ya dawo.

Komawar shi Kano ya so ba shi wuya kasancewar ba da mota su ka shiga dajin su ba, tafiyar kasa ce su ka yi mikakkiya. Da kyar da taimakon Allah ya sami motar da ta kai shi Mambila, daga nan ya sami motar Taraba, a can ne ya sami na Kano direct.

Ganin Usman da kuma yanda ya canza ya kara kwarjini kamar wanda ya sha maganin kwarjini ba karamin mamaki su Isa su ka yi ba, musammam Jauro da ya kama kan sa dan shi kan sa ya san akwai bambamci tsakanin Usman din da da na yanzu, har da yanda Ammy ta karbe shi hannu bibbiyu. Ta dawo Kano ita da Falmat bayan sun fita takaba. Bakin ta ya ke jin labarin auran Halitta wacce a yanzu haka ta na can Saudiya tare da mijin ta. Yayi murna kwarai tare da mata addua. Amma ko da Ammy ta kawo maganar Zainab, ta na mai tambayar sa dalilin da ya sa ya tafi babu sallama sai cewa yayi


"A yi hakuri abin ne ya zo min a gaggawa, shi ya sa ma na dawo na gyara, ta na nan ne?

Ya tambaya ko Zainab ta na nan ne ba dan ya na so ya ji amsar da Ammy za ta ba shi ba, abu daya da ya sani shi ne ya zo tafiya da ita, ko ta nan ko bata nan kwana daya kacal ya ba ta za ta dawo ta same shi har in da ya ke.

Ammy ce ta masa bayanin Zainab din ta na makaranta, jami'ar da ta ke yi a Yola, Amma kada ya damu ai ta ma kusa fara jarabawa, kuma da ta dawo be fi watanni biyu zuwa uku za su kara su gama makarantar gaba daya ma

'ai kuwa na ta makarantar ya kare daga gobe!'

Cewar Usman cikin ran sa, zahiri kuma cewa yayi

"babu komai ai kamar yau ne, Allah ya ba da sa'a"

BQ din nan dai da Malam ya basu nan aka sauke shi. Allah ya amsa adduar shi har lokacin akwai wasu daga cikin kayan Zainab, dan haka a daren ranar ya yanki daya daga cikin bakaken rugunan ta da ta bari a dakin, ya hada da wani ganyen turare da ya taho da shi daga Rugar Shehu. Sai da ya kulle dakin sannan ya hada garwashi ya ruru sosai yayi jajur, sannan ya dauki kyallen da ya yanka, ya hada da ganyen turare ya dora kan garwashin, yana murmushin mugunta ya ke duban yanda tufar ke konewa hayaki na ta shi, ya ce


"Kamar yanda tufar ki ke konewa haka zuciyar ki za ta na mi ki kuna matukar ba ki baro duk abin da ki ke kin zo gare ni ba Zainab, kamar yanda hayakin nan daya ke bin daya haka za ki bini duk in da na sa kafa....matata Abu"

***

Duk yanda Zainab ta so ta yi karatu daren ranar kasawa ta yi, ga shi ta na da jarabawar safiya. Washagari tun da asuba ta hado kayan ta, ba tare da ta nemi shawarar kowa ba ta na kallo kowa na shirin fita jarabawa amma ta tsallake ta dauki hanyar Kano a motar haya abin da ba ta taba shiga ba tun da ta fara karatu a Yola. Sai yamma likis ta isa Kano, wanda tun isowar ta jikin Usman ya bashi dan haka shi ma din ya fita kofar gida da shirin sa ba tare da ya bari su Jauro sun san da fitar shi ba. Be yi cakakken minti talatin da tsayuwa kofar gidan ba sai ga dan sahu ya zo ya tsaya gaban gidan Malam. Zainab ta fito sanye da bakar abaya, hannun ta rike da dan akwatin ta da ta debo kadan daga cikin kayan ta. Ta na sallamar dan sahu ta karasa gaban Usman ta tsaya, wanda tun saukowar ta ya tsura mata Ido cike da tsana. Wani farin mayafi da ya sha ado da kaloli irin na fulbe ya mika mata, Zainab ta sa hannu ta karba.

"Ki yafa shi yanzu"

Cewar Usman. Zainab ta amsa da toh sannan ta ware mayafin ta yafa.

"Sunan ki Abu...."

Cikin gasgatawa ta furta

"Sunana Abu..."

Usman ya kara da

"Ni mijin ki ne Shehu"

"Kai miji na ne, Shehu"

"Mu na hanyar komawa gida Rugar Shehu"

"Mu na hanyar komawa gida Rugar Shehu"

Zainab ta sake maimaitawa.

"Duk wanda ya mi ki magana a hanya kada ki tanka masa, matukar ba ni Shehu mijin ki ba ne ya baki umarni kin ji ko?"

Zainab ta na mai girgiza kai cike da ladabi ta furta

"Toh miji na Shehu..."

Kallan ta yayi sama da kasa ya gamsu da yanda mayafin da ta yafa ya dan ragewa rigar da ke sanye jikin ta kyau, cikin ran sa ya na mai neman yafiyar Ammy da Malam, ya ce da ita

"Biyo ni mu tafi!"

Babu musu Zainab ta bi bayan shi hanun ta rike da akwatin ta, ko waige ba ta yi ba bare ta tuna da gidan su ne nan ta bari.

*khadija sidi*Auren Shehu 2

2



Zainab na biye da Usman duk in da ya sa kafa nan ta ke dire na ta. Dan sahu ya tara ba su zame ko ina ba sai tashar Kano Line amma su ka yi rashin sa'a motar Taraba ba ta tashi sai sassafe. Direba ya dubi Zainab da gaba daya alamun gajiya ya bayyana a fuskar, a zahirin gaskiya idan aka dauke mayafin fulbe da ke yafe jikin ta, sam yanayin ta da zubin ta be nuna wani alaka tsakanin ta da Usman ba, Dan kuwa kana ganin Usman ka ga bafulatanin usul wanda babu wata alamun wayewa a tare da shi. Cikin dabarar Jin ko wacece Zainab ga Usman Driver ya kada baki ya ce

"Halan mikakkiyar tafiya ka yi tare da uwargiyar ta ka?"

"Eh mikakkiyar tafiya mu ka yi, haka kuma ita za mu tasarwa, shin ko akwai irin gidan kwana da ake biya nan kusa? Sai mu kwana washagari mu dau hanya"

Usman ya bashi amsa ba tare da ya fadi abin da Driver ke da muradin ji ba. Ganin yanda Driver ke kallan Zainab ba kakkautawa ya sanya Usman fadin

"Ni ta ita na ke ji ma, a gajiye ta ke...."

Driver na mai sosa kyeya ya ce

"Toh ka ga yanda za a yi, gida na nan kusa ne, ina da daki mai dauke da gado da katifa cikin zaure, haka kuma akwai bandaki ciki, ban fiye san saukar bakin da ban sani ba ciki, Amma ganin halin gajiyar da wannan baiwar Allah ke ciki, mu je sai na ba ku shi a kan naira dubu biyar..."

"Dubu biyar be yi yawa ba?"

Cewar Usman yayinda ya kai hannu aljihun shi domin jiyo lafiyar tattalin arzikin da ke ciki. Jin haka Driver ya ce

" Kai fullo ba dai san sisi ba, toh ai babu damuwa, kawo uku toh, ai matafiyi abin a tausaya masa ne"

"Toh babu laifi, gashi nan kirga ka gani"

Ya mika masa kudin da ya fidda daga aljihun sa. Driver ya dirga dubu uku cus sun cika. Sannan ya ce

"Toh Madallah sai ku shigo mota mu tafi nan tsallake ne ba nisa, ka ga da sassafe kafin shida sai mu fito mu yi lodi mu dau hanya"

"Abu shiga gidan baya mu tafi"

Cewar Usman cikin dakiya. Jin Zainab ta furta

"Toh Shehu mijin na"

Ya sanya Driver sake waigawa ya kalli Zainab kafin ya shiga motar ya tada cike da mamaki, ya tabbata dai wannan gabjejen bafulatanin Ruga majin wannan kyakkyawar yarinya ce, Driver ya dau hanya ya na al'ajabin yanda Usman ya tsinci dami a akala.

Kamar yanda Driver ya fada gidan na sa be da nisa da tashar. Dakin da yayi alkawarin bawa su Usman ya sauke su, babu laifi dakin be fiya dauda sosai ba, gadon gyare ya ke tsaf haka kuma kasan dakin shimfide ya ke da leda. Haka kuma akwai wutar lantarki. Daudar dai daya ne na rashin shara da dakin be samu ba. Shi ma din kafin su shiga Driver ya turo yaro daga cikin gidan sa aka share, tare da cire zanin gadon da ke shimfide bisa gadon, ya shimfida wankakken sai kamshin sabulun wanki ya ke, Sannan ya sa aka kunna mu su maganin sauro na igiyar leko, ya kuma debo ruwa ya zuba a robobin cikin bandaki. Yaron na shirin fita Usman ya tambaya ko akwai in da ake siyar da abinci nan kusa? Yaro ya ce babu sai dai akwai wajen me shayi ya na Kuma dafa indome. Usman na mai godiya ya sallami yaron da sauri saboda yanda wayar Zainab ta ishe su da kara. Ya na duban Zainab wacce ga wayar a hannun ta amma ta kasa dagawa saboda be ba ta izini ba.

"Waye ke kiran ki?"

Ko da ta duba wayar 'Ammy na' ta ga an rubuta, budar bakin ta sai cewa ta yi

"Wani suna ne wai Ammy na, haka dazu ma wasu su ka ta kira ban san su ba"

Zainab ta bashi amsa a sanyaye.

"Ki tura mu su sako na lafiyar ki lau, kada a sake kiran ki"

"Toh Miji na Shehu"

Cewar Zainab yayinda ta aikata umarnin sa. Yanayin gajiya da ta ke ciki da kuma yanda surkullen da ya mata ya kamata sam be saka tausayin ta ya tsirga zuciyar Usman ba, sai ma tsananin kiyayyar ta da ya ke ji cikin ran sa, da kuma bakin cikin da ke ziyartar zuciyar sa a duk sanda ya tuna ita ce sanadiyar rashin ganawar karshe tsakanin sa da Iyar sa.

"Ki kashe wayar kada ki sake kunna ta, zan fita na siyo abinci"

Cewar Usman cikin kokarin ficewa daga dakin, har ya kai kofa ya sake juyowa ya kara da

"Ki jawo kofa ki sa sakata idan na fita, kada ki budewa kowa idan ba ni ba ne, Ki yi wanka da sallah idan har ki na yi......."

Ya na jiyo amsar ta na

"Toh Miji na Shehu"

Ya fice zuciyar shi na tafasa na ba gaira ba dalili, shi kan shi ya san iya yan watannin nan gaba daya baya cikin hayyacin sa, babu abin da ke masa ciwo sai rashin Iya, yanayin da Bello ya shiga a sanadiyar Zainab da kuma dukan kawo wuka da aka yiwa Bello, duka a sanadiyar auren Zainab.

Bayan tafiyar Usman Zainab ta sa sakata kamar yanda Usman ya umarce ta, cire kayan ta tayi, tare da daura dan karamin towel din da ta saka cikin akwaitin ta. Cike da kyamkayami ta shiga bandakin, ba ta yarda ta tsugunna ba gudun daukar cutar bayan gida. Har ta gama wanka ta dauro alwala Usaman be dawo ba. Wata rigar baccin ta saka iya gwiwa mai dan karamin hannu sannan ta sanya hijabi har kasa ta shiga gabatar da sallah.

Idawar ta ke da wuya ta cire hijabi kan ta daure da kallabi ta ji ana buga kofa, ta karasa gaban kofar tare da fadin

"Waye?"

"Shehu"

Ya bata amsa a taikaice. Cikin rawar jiki ta bude kofar tare da fadin

"Sannu da zuwa"

Hanun sa rike da bakaken ledoji guda biyu, da kofi wanda ke fitar da turirin zafin bakin shayin da ya ke ciki ya wuce ba tare da ya tanka mata ba. Sai da ya aje ledojin da kofin shayin sannan ya daga ido ya kalle ta, tuni yayi saurin kawar da kai, cikin mummunar faduwar gaba, kan sa ya sara ganin yar rigar da ke jikin ta, da kuma yanda ya bayyana surar jikin ta duk da dai rigar ba matsattsiya ba ce, Zainab din ce MashaAllah. Cikin tsawa da fada ya ce

"Me ki ke jira a nan Abu? Ki rufowa mutane kofa ki zo ki saka hijabin ki! Kada ki sake yawo haka matukar ina wajen!"

A gigice Zainab ta rufe kofar tare da sa sakata, ta karasa da sauri hannu na rawa ta dau hijabin ta ta saka, can gefe ta sami waje ta zauna har lokacin gaban ta be bar faduwa.

Jin ta shiru ya dago kai ya dube ta, ganin yanda ta zauna ta yi shiru kamar ba tsigalalliyar Zainab din da ya sani ba, da Kuma kwallar da ta ciko idanun ta be sa yayi dana sanin ihun da ya mata ba, sai ma danasanin ganin surar ta da yayi da har lokacin ya ke masa yawo a idaniyar sa. Murya ya gyara ya na mai neman nutsuwar karfi da yaji, ya mata nuni da yatsa tare da fadin

"Ki zo nan ki ci abinci ga shayi nan shi za ki fara sha kin ji ko?"

Ya na maganar ne cikin dakiya. A hankali ta taso ta zauna in da ya umarce ta, shi ne ya bude mata ledar indomie din, yanda ya ga ta na ci hannu baka hannu kwarya ya tabbatar masa da cewa da yunwa ta wuni. Na shi ledar ya ja dan kuwa ji ya ke ya na bukatar kaÉ—aicewa a wannan lokaci, a hankali ya ja jikin sa ya fita ya bar mata dakin. Bakin kofar dakin ya zauna duk yanda ya so ya ci abinci ya kasa, tunani kala kala ke yawo cikin kwakwalwarsa, sam be da niya kuma ba zai yi danasanin tafiya da Zainab ba! Hakan shi ya fi cancan ta mutane irin ta!'

Furucin da zuciyar sa ke jaddada masa kenan har ya dan sami karfin gwiwar cin indomie din. Haka ya zauna a soro, 'ya'yan Driver na kai kawo haka na makota, har kafa ta dauke aka ma rufe gidan gaba daya. Nan soro cikin sauro ya kwana, da asubar fari ya buga mata kofa, ya ce ta tashi ta yi sallah ta yi wanka za su wuce.

Sai da aka idar da sallah sannan Zainab ta yi wanka. Ta na jiyo shi shi ma yayi na sa wankar tare da goge baki da dakakken gawayin da ya kullu tun daga Rugar Shehu. Cikin bandakin ya shirya tsaf ya fito cikin kayan saki riga da wando, haka kuma be fasa nada rawanin sa da bakin yadi ba. Ya na mai duban shigar da ta yi na bakar duguwar riga ya ce

"Ki cire kayan nan ki sanya hijabi"

Ga mamakin sa sai ga Zainab na kokarin zare ruga gaban sa, cikin tsawa ya ce

"Wai ke wata irin mara kunyar Bingel ce Abu???"

A dibirbice dan kuwa tsawar Usman rikita ta ya ke ta ce

"Ya zan yi miji na? Kai ka ce na cire rigar..."

"Mace da kunya aka santa duk da na dade da sanin ke ba ki da ita ko na miskala zarratun! Idan kin ga dama ki yi tsirara kafin ki saka hijabin!"

Ya na gama fadin haka ya bude kofa ya fice. Zainab ta yi kasake ta na kallan sa cikin tunanin laifin me ta yi har ran Mijin ta Shehu ya baci haka. Jin ya na buga mata kofa ta yi saurin saka hijabin haka ba tare da ta cire rigar ba, ta hade komai na ta cikin karamin akwatin ta ta fito.

A mota ta tarar da su, Driver ma ya fito ita kawai ake jira. Dan haka ta na shiga kai tsaye tasha su ka wuce. Nan tasha ya siya mata shayi da bredi ta ci kayan ta ba musu. Haka kuma ya siya mata silifas na roba ya ce ta cire mai tsinin da ke kafar ta, ya dau mai tsinin ya bawa wata yarinya mai tallar masara cikin tasha. Karfe shida daidai mota ta cika, su ka dauki hanyar Taraba.

Tafiya ce mikakkiya su ka sha, gashi sam hanyar ba kyau, ga checking point da yawa duk in da su ka tsaya kuwa sai sojojin nan sun tanka Zainab duk da can gidan baya su ke zaune tare da Usman. Yawanci su kance kamar sun san fuskar Zainab.

Ba su suka isa Taraba ba sai shida na yamma. Dake dama Driver da su ka kwana gidan sa ne ya ja su, Wajan kwana be basu wuya ba. Kamar yanda ya bata umarni ba ta cire hijabin ta ba, har sai da ya ce mata za ta iya cirewa ta yi wanka idan ta na so idan ya fita. Ya na ficewa ta cire hijabin ta sha iska.


Washagari da sassafe su ka sami motar Mambila. Shi ma din sai yamma likis su ka tasarwa shiga garin. Dake Mambila bisa dutse ne ko Dirobobi sai kwararru ne su ke iya hawa dutse, Zainab ba bata san sanda ta rugume Usman kam ba, ta na mai dora fuskar ta kan fadarsa sai da ya ji tsigar cikin sa ya tashi, haka kuma duk yanda ya so ya zare ta daga jikin sa ta ki, har sauran yan cikin motar suna mu su dariya. Haka babu yanda zai yi ya barta kwance jikin sa yayinda zuciyar sa ke bugawa tamkar za ta fado.

Haka tafiyar awanni ta zame masa tamkar gwale gwale. Suna Isa Mammbila ya banbare ta daga jikin sa ya fito daga motar ya bar Zainab ciki ta na mai raba idanu ta fito daga motar. Baki bude ta ke duban in da take, wato Allah mai hilitta yayi hilitta a kasar Mambila, ba ga kasar ba ba ga halittun da ke kasar ba.

Gari ne mai kyawun gaske da yalwataccen ni'ima, haka ma matan kasar don idan kaga wata ta keto daga gefan duwatsu gashi har mazauni ka ce gamo ka yi tsabagen kyau. Ganin dawowar Shehu da dama sun ga tafiyar shi ba karamin dadi su ka ji ba, sun karbe su hannu bibbiyu in da ya gabatar mu su dayl Zainab matsayin matar shi.

Daki na musammam aka ba su, haka kuma an ba su abinci mai kyau, ga fura da nono ga kayan marmari na daga 'ya'yan itace. Yanda su ke yarawa da Usman da kuma yanda ya ke musu fara'a ya sanya Zainab zuba masa idanu, ta na mamakin dama ashe Shehu mijin ta ya na dariya?

Usman ya so wucewa a ranar amma jama'ar Mambila su ka hana shi, su ka ce ya bari gari ya waye ido na ganin Ido duk da dai ba su san ainihin dajin da Rugar Shehu ta ke ba. Haka bai sa ran sa ba ya hakura su ka kwana, cikin dare matan da su ka zo su ka buga masa kofa tare da tambayar ko ya na bukatar yar tayin hirar dare Allah yayi yawa da su. Shi kuma be fasa ba su amsa da matar shi ba ta saba kwana ita kadai ba, Kar ya fito kiri kiri ya ce ba ya so wata ta kullace shi ta aikata masa wata kullalliyar. Sai ya tabbatar kafa ta dauke sannan ya fito waje ya bar Zainab ciki ta na baccin ta hankali kwance. Kofar dakin da aka bashi ya samu ya kishingida, Zainab ya ke gani cikin kayan bacci duk sanda ya runtse idanun sa, haka kuma sassanyar kamshin turaren ta da ya mamaye rigar sa sanda ta rungume shi a cikin mota. A fusace ya mike tsaye, tafiya ya ke tamkar zai tashi sama tsabagen bacin rai. Wani dan dutse mai rubar ruwa ya nufa, ya na mai cire rawanin kan sa ya tsaya karkashin sa ruwa na kwaranya bisa kansa ya na sauka gangar jikin sa. Sai da ya dau kusan minti talatin a wannan halin, zuciyar sa ta dan yi sanyi sannan ya fito ya zauna gefan dutsen. Wani irin iska ke kadawa ya na shiga jikin sa, idanun sa runtse kansa bisa dutse Allah ya kadai ya san awannin da ya bata nan zaune ya na ambaton sunan Allah. Sai da ya bushe tsaf zuciyar sa ta dan yi sanyi sannan ya tashi ya koma masaukin sa.

Da sassafe bayan sun yi sallama, an kuma hada mu su goma ta arziki na guziri su ka tasarwa Rugar Shehu haikan. Dake tafiya da mata sai a hankali duk yanda Usman ya so su yi sauri su isa Rugar Shehu ko ya rage tarayya da Zainab, abin ya gagara. Tun suna shiga dajin suna ganin yan tsirran mutane da yawancin su fulani ne masu kiwo ko mafarauta, har su ka dena ganin kowa sai bishiyu da halittun dajin da ba a rasa ba. Duk sanda lokacin sallah yayi Usman kan ce su tsaya su yi sallah, haka kuma be bar Zainab da yunwa ba duk da dukkan alamu ya nuna ta jigata kwarai da tafiyar kasa da suke duk da silifas ne kafar ta tun da su ka baro Kano.

Ko da su ka tsaya sallar la'asar nan Zainab ta kakare, tsabagen tafiya kafarta har ta fara kumburi. Amma Usman be tausaya mata ba bare ya ce su yada dogon zango, sai dai ta sami saukin daukar akwaiti, dan da tafiyar ta yi tafiya shi ya dauki akwatin.

Yana yin duhu da gari ya fara

Please Login or Register in order to submit comment