Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shine ya mayar da ni mai son zuciyar, kamar yadda kika mayar da ni banza ko wacce magana zaki fada mini babu fargaba.
Kin ta'ba jin na yi magana akan yadda yaranki ke ka'dai suke nufa da tallafinsu, ai saboda nasan uwa mafi uba ce ko da kuwa uban sarki ne".
Ban sake jin harshenta ba, na wuce a raina ina ta murnar Babanmu ya fara gwada k'arfin halin taka mata burki, duk da a yanzu ma babu garantin ba zai lallabata ba. Domin ta riga ta jarraba shi ainun.
Washagari asabar da wuri na tashi na ha'da kayan wankin dakinmu gaba'daya.
Na aiki Anas ya siyo mini sabulu da omo tun daren jiya dama.
Na fara wanki, yayin da shi kuma yake janyo mini ruwa a rijiyar bayan shashinmu.
Kafin karfe takwas din safe na kammala na shanya su reras.
Tuni kuma Inna ta kammala abin karin kumallo.
Na karbo mana namu dumamen tuwon da Nazira, ga kuma kokon a jug da kullum Gwaggo sai ta bawa duk wanda yake son sha a gidan.
Kusan kullum sai na tambayi ko ribar nawa take samu?
Yadda bana gajiya da tambayar itama bata gajiyawa wajen cemin "Wanda ake sha ne ribata".
A duk sadda ta fa'di hakan ban cika fahimtar rufin asiri ba ne sai kawai na kalli ita din mace ce mai yin hidima a inda ba'a ganin darajarta.
Kafin Nazira ta gama wanke baki na k'osa domin indai na yi wanki to bani da jarumtar ri'ke yunwa sai na ji tamkar an mini yasa a cikina.
Ta tarar tuni na fara cin tuwon.
Ta zauna tana fa'din "Yabi sark'a, yanzu da ni ce na fara ci ban jira ki ba, sai kowa ya ji kwakwazon ki"
Na rausayar da kai tare da fa'din Ayyah Addah Nazi kinsan bana shiri da yunwa ko kadan.
Muna karyawa ina bata labarin yadda ta kaya a tsakaninmu da Yaya J.
Ta murmusa ta ce "Yabi duniya! Yanzu Yaya Jabir din ma ba zaki dinga raga masa ba?
Na dan daure fuska na ce "Ai matu'kar zai tsokano ni tabbas zan ajiye komai na yamutsa shi inta kama a rabu ma shi kenan.
Ba zan dauki wula'kanci ba ko ka'dan.
Ta girgiza kai tare da cewa"Allah ka shirya mini Yabina".
Dai dai lokacin Baba ya fito da nufin fita.
Muka gaishe shi ya amsa yana cewa Nazira da Asiya albarka ta kewaye mini ku".
Cikin farin-ciki mai yawa muke fa'din ameen Babanmu".
Amma sai na sake cewa "Babanmu Asiya fah?"
Ya murmusa ya ce " Ho Yabi! Da ikon Allah sai kun sauke farali daga ke har y'ar-uwarki. Sai kin zama Hajiyar ta sosai".
Cikin karadi na ce "Ai kuwa dai Babanmu "Dawafi na mussaman zamu yi maka!"
Ya fice yana dariya.
Babanmu wani irin uba ne da yake wasa da raha a tsakaninsa da y'a'yansa, babbar matsalarsa kawai Mama ce, domin yanzun nan sai ta saka ya ci mutuncinka ko na uwarka akan idonka dan ma an yi sa'a abin ya dan fara sau'ki, na sani kuma karfin addu'ar da muke yi ne mu da Gwaggo".
Kwanaki suna ta shude wa har muka yi jarabawar zangon karatu na uku.
Muna tafe kowa da sakamakonsa a hannunsa, Nasiba da su Firdausi sai murna suke yi a dalilin sakamakonsu ya yi kyau.
Nazira ma babu laifi domin ta sha biyu ta zo.
Amma ni kam sakamakona ba zai nunu ba domin kuwa ta arba'in da takwas na zo a cikin mu hamsin da bakwai.
Kowa ya nuna sakamakonsa a tsakaninmu. Amma ni na boye nawa kamar yadda na saba.
Muna tafe Maijidda sai fa'di take "Akan me za ki dinga ganin results dinmu amma ke ba zaki yarda a ga na ki ba?"
Na gallah mata harara na ce "Saboda mahaifina bai fara gani ba, ba kuwa wanda yafi cancantar ya fara gani sai shi".
Ta tunzura ta ce "Kins an Allah yau sai na ga ni, ai na sani ta karshen aji kike yi.
Ban da class master din ajin naku saurayinki ne ai demotion ne ya kamace ki Asiya".
Na fusata kwarai da gaske na ce "Tabdi jam! Yabi kika je fa wa wannan maganar?"
Ba shakka ta ce "An fa'da miki Asiya. Kin dauka ina jin tsoron ki ne? Idan ba jakar aji kika dauka ba to miko mini sakamakon ki kamar yadda na baki nawa kika ga ni".
Na girgiza kai da tare da yin k'wafa mai tsananin gaske.
Nazira kuwa sai fa'di take "ba ruwanki da al'amarin Yabi fa Maijidda".
Ta ce "Na shiga komai zata yi, ta yi ina daidai da ita".
Ban ce komai ba sai da muka isa zauren Gidanmu ba zato na shake Maijidda da dukkan k'arfina, ina kai mata duka ko ta ina.
Kafin ta yi yun'kurin ramawa na jibge ta sosai, sannan kuma muka ci gaba da gwabza wa.
Aka rasa mai rabamu domin duk wacce ta ta'ba ni kanta fa'dan zai koma sun san haka dabi'ata take.
Nazira sau fa'di take Yabi sake ta, amma bata ri'ke ni ba, domin ta san ce wa zan yi bata taya ni fa'da, ta taimake ni ba tunda bata kishina, akan me zata ri'ke ni?
Na turmushe ta ke nan na debo k'asa ina shirin cika mata bakin da ya yi mini izgilanci sai ga Bulkachuwa ya shigo.
Ya hau fa'din ke Asiya Toro wanne irin abu kike yi haka ne?"
Ganin na fara kokarin danna mata a baki ya sanya shi iso wa garemu, bai jira komai ba ya saka hannunwan sa ya cira ni cak kamar y'ar tsana ya yi wurgi da ni.
Na yi sa'a na dire akan sayyadata.
Da yake a hassale nake sai na durfafe shi ina cewa "To kai ma din ai ba tsoronka nake ji ba, ka zo ka zaune mana a gida ka uzzira mana haba.?"
Na kalli yadda ya harzuka amma ko gezau ban yi ba, duk da ban fi iya cikinsa ba.
Ya kalli Nazira ya ce "Me ya ha'da su?"
Ta tsara masa yadda aka yi ba ragi babu kari.
Ya juya ga Maijidda da take hawaye ga jini a hancinta tabbacin habo ne ya goce.
Ya ce "Dube ki gansamemiya da ke amma wannan y'ar tsakon ta lallasaki haka, wanne irin mutuwar zuciya ce ta same ki?"
Na galla masa harara tare da murguda baki na ce "To ni komin girman gardi ma ba zai hana na zubar masa da jini ba, bare kuma mace yar-uwata".
Ya nuna kansa ya ce "Asiya Toro ni kike tunanin zaki buga?".
Na ce "Ba dan ha'da jiki da kai sai ballagazaye ba, ba abin da zai hana na zage mu gwabza y'ar k'ashi Wallahi".
Ya nuna ni da yatsa ya ce "Asiya Billahillazi zan sumar da ke, yar iska marar mutunci kawai.".
Yana rufe baki na ce "Ga ka nan babban dan-iska mai shiga fa'dan mata, yabi bayan wacce take da abin da zai lallaba ya cuce ta."
Ya yo kaina yana fa'din ashe "Izgilancinki mai girma ne haka?"
Ga mamakinsa sai kawai na yi shirin kai masa naushi tamkar bacaniya.
Wannan dunukule hannu da saitin da na yi, ya yi matu'kar bashi dariya da tu'ajjibin k'arfi halina.
Ya tsaya ya ce dambe zaki yi da ni?
Na ce "Allah suturu bu'kui na yi dambe da mai daudar zunubi irin ka, kuma ni ba ballagaza ba ce, kawai zan kare kaina ne daga cutarwar ka".
Ya jima bai ce komai sai ya kalle ni ya ce "shahsa da bata iya komai ba, sai fa'da da rashin kunya a aji kuwa ita ce dalkiya".
Ba'kin ciki ya mamaye ni, idona ya ciko da hawayen takaici na ce "Na gode wa Allah da na yarda ina zuwa makarantar, wani ma tsabar akuyanci korarsa aka yi daga karatun nasa. Me za'a yi da mai halin bunsuru?"
Ya rasa yadda zai yi da ni sai kawai ya shammace ni ya dauke jakata yi wuf ya zaro takardar sakamakon da take a farko farko.
Ya juya zuwa waje ya bu'de ya ga yadda jan biro suke mamaye sakamakon.
A karshe ya ga ta yadda na zo sannan ya mayar ya shigo ya kalli yadda na tumbatsa ya ce "Anya Asiya ba dusa kike ci ba kuwa?
Ace har kin doshi hamsin?
Gaskiya ina taya Baba ba'kin cikin asarar ku'din taran da ya wanzu yana baki".
Cikin rawar murya na ce "Bulkachuwa Yadda ka tozarta ni a gaban wanda suke son na tozarta in sha Allah sai an tozarta budurwarka fiye da yadda ka mini, da ikon Ubangiji sai ka ha'du da sharrin mace, sai ka muzanta a idon duniya".
Ya make kafa'da alamun ko a jikinsa tare da cewa "Yabi yanga mai kwakwalwar kifi".
Ganin hakan ya sanya Maijidda ta mike tana jin karfi yana shigar ta tunda ta ji abin da take son ji.
Ta mini gwalo tare da cewa "Na ji dai, dama nasan baki tsinana komai ba".
Ta shige wajen Dada da saurin ta.
Yayin da ragowar suke fa'din "Yi ha'kuri Yabi, ai kin nuna mata ruwa ba sa'an kwando bane. Ba gashi ta tsere ba".
Na jijjiga kai na ce
"Ai dan ta ga Bulkachuwa ya tsaya mata ne".
Yayin da shi kuma ya ce "Ba dole na tsaya mata ba, tunda ke din karfinki na aljanu ne, na tabbatar ba ke ka'dai kike fa'da ba, kina samun tallafin aljani mai kilabo da gwaigwai".
Duk wajen aka fashe da dariya illah ni dana sake fusata na daga murya "Ina ce wa "Allah ka dora wa matar Bulkachuwa aljanun da zata dinga daga shi sama tana danfara shi da k'asa".
Ya wuce yana fa'din "Duk bala'in aljani ba zai shigo mini gida ba, domin hafiza zan aura mai hazakar gaske a ilimin boko da na addini.
Safiya da marairaice ta yi ta tofe mini gidan da azkhar, idan kin ga aljanu sun yi tasiri, sai a gidan wanda basa mayar da
kai a wajen bautar Allah irin ki".
Na wuce shi zuwa shashin Dada.
Na tarar da Maijidda tana ta kuka yayin da Dada take sakacen hakori da tsinken zabori hankalinta a kwance.
Na bu'de baki na ce "Dada sannu da gida, mun dawo".
Ta amsa ba alamun damuwa a tare da ita.
Na juya na tafi sai na ji kukan Maijidda ya karu tana cewa "Kin bar ta tafi baki bi mini kadina ba?"
Na yi tsam dan na jiyo amsar Dada.
Kamar ba zata tanka ba sai kuma na ji tana ce wa "Na k'i na yi mata maganar. Yar kankanuwa a gabanki, sannan kin bata kwanaki arba'in cif amma kin kasa kwatar kanki a hannunta sannan dan asaranci ki ce na tare miki fa'da?
Ai kinsan fa'dan ta baya mutuwa akan me zaki tsokano abin da yafi karfinki?"
Maijidda da bata yi zaton haka Dada zata ce ba, domin mun saba yin fa'da da yan k'ofarsu ta basu gaskiya ko da kuwa ni ce mai gaskiya.
Dada ta ja tsaki ta ce "Sadda nake cikin shekarun kuruciyata haka nake nima duk girman mace bata bani tsoro, haka nan duk wanda ya mini kan ice sai na yi masa na kara.
Sai yanzu na fahimci wannan tijarar ta Yabi sawuna ta biyo domin komin sharrin mai sharri ba zai ce ubanta mafadaci ba ne ko kuma uwarta.
Dukkan iyayenta sanyin kalau ne, dan kuwa inta sune kiyama ba zata tsaya ba."
Kukan Maijidda ya tsananta ta dinga yi tana ce wa "Ai dai kinsan bata isa ta kai ni k'asa ba, dunbular mini kirji ta yi ta yakushe ni a wajen."
Salati Dada ta dauka tana cewa "Ikon Rabbani, tarihi na maimaita kansa ni Fadimatu.
Wallahi Maijidda sadda aka mini auren fari ina kankanuwa aka kai ni babban gida, matar wan miji ta saka ni a gaba, duka, kyara zagi.
Har na fara girma a cikin fargabar wannan baiwar Allah na ke.
Ai kuwa da tura ta kai bango na fara rama abin da take yi mini.
Har muka kai jallin da muka fara dokuwa, sai dai kashi take bani da yake ta fini sosai, ai sai kawai nake fakar ido idan muna damben ina mintsinin nonuwanta ko na na cije su. Shi kenan na yi maganin gallazawarta, ta shiga kiyayata.
Yau ga Magajiyata na samu a haulata".
Ta fa'da tana tafa hannu tana sake jan salati.
Na wuce ina son yin dariya amma ba'kin cikin Bulkachuwa ya dabaibaye ni.
Na wuce shashinmu ina jaddada wa kaina ko a gaban Baban kasuwa ne Maijidda ta tsokano ni sai mun sake cire raini, bare Dada.
Bamu jima da dawowa ba sai ga mahaifiyar Maijidda da kanta ta kawo togaciya.
Fadi take "Tura ta kai bango kullum Yabi sai ta yi mini sanadin bacin rai jiyan nan ma sai da ta dakar mini Kaltume akan sun samu sabani da Ismail, akan me zata tisa mini yara a gaba irin haka?"
Ha'kuri kawai Gwaggo take ta bata, Inna da ta rage tsananta gaba da ni a dalilin ina yiwa yaranta hidima tamkar yan dakinmu, sannan ba mai tab'asu a waje matu'kar ina wajen sai hakan yayi tasiri, ta rage daukar zugar Mama.
Dan haka sai ta ce "Ban da ke ma Abu da shiga shirgin yara ina ce Maijidda ta girmi Yabi ne?
Sannan idan kinsa ha'kuri anjima ka'dan zaki iya ganinsu tare".
Nan da na ta harzuka ta ce "To Yabi ni kaina ai sai ta dake ni tunda fa'dan yan-iska take yi, ban da dai ta riga ta rik'a ta yaya zata dinga dumbular kirjin y'anmata, tabbas dayan biyu ne, ko dai niyyar kisa take yi ko kuma ta shiga sahun masu *Bak'ar Ta'adar* neman mata."

*Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko kuma kina sha'awar yin register da su. Ki tuntubi babbar dealer din su Aisha lame*
*Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea*
*Akwai pop corn mai kore dukkan kwadayi*.
*07036662633*.

Gwaggo ta ce "Dutse a tsakaninmu da duk masu wannan al'amarin, muna neman tsarin Allah da su, muna kuma nema musu shiriyarsa."
Ta ce "ASMA'U Wallahi kin siffatu da agwagwa, ace wai baki isa ki sarrafa y'ar cikinki ba, ta gallabi kowa a gidan amma ba k'ya yi mata fa'da, saboda tana samun ku'di shiyasa ta gagareku?
Sai ayi ta fankamar ku'din kitso da na lalle ne, alhalin munsan samarin da suke mata layi ne suke bata. Wallahi idan ba sa'a kika yi ba sai Yabi ta hana ki shan ruwa kamar yadda ta fitine mu".
Na fito na ce "Umma ya isa haka nan, ba zai yiwu fa kizo k'ofarmu ki zagi Gwaggo ba".
Ta mini dakuwa ta ce gidanku tabbataciyar yarinya marar albarka".
Tana rufe baki na ce "yarinya tana bayan uwarta Wallahi, albarka kuwa da ikon Ubangiji sai na yi ta".
Gwaggo ta yo kaina na ki guduwa tasan kuma matu'kar ta kawo mini duka ban gudu ba, na riga na shiga yanayin da nake bu'katar a kashe ni kawai na huta.
Inna ta yi maza ta karbe itacen hannun Gwaggo tana fa'din "Wannan ai sai ki sabauta ta".
Yayin da Umma Abu ta juya tana fa'din "Zaman babban gida ko masifa, ba dama a ganka da haske sai an tisa ka a gaba da ba'kin ciki da hassada tamkar dai kai ofne ka tare wa mutum nasa arzikin".
Tana fita Gwaggo ta kalli inda nake a tsaye kik'am tana fa'din "Kin ji da'di ai da wannan wula'kancin da kika janyo mana".
Ban ce komai ba, sannan kuma ban ji a raina cewar zan koyi ha'kurin dole idan an ta'ba ni ba.
Wannan rikicin yana cikin al'amura masu tsananin gaske da ya faru.
Domin da daddare babu kunya bare kawaici Baban kasuwa ya gurfanar da mahaifina a gaban Dada yana ta sababin ya gaji da yadda na takura wa ya'yansa amma ubana ya kasa tsawatarwa.
Da yake Dada bata iya tsallake umarninsa sai kuwa tabi bayansa.
Ta dinga fa'din ai tsoron zuciyata yake yi.
Cikin rishin kuka Baban kasuwa ya ce "Ki gafarce ni Dada! Wani satin zan koma gidana dana kammala gina wa tun bara, amma na kasa tashi saboda ke, to yanzu kam zan tashi na gaji da wannan masifar Wallahi".
Dada ta ce "Wallahi ko ubanta ba zai tashe ka ba tunda matsayinku guda a cikin gidan bare kuma ita.
Share hawayenka ita ce zata bar mini gidan".
Na sake kasa kunne domin tunda aka aiko cewar Babanmu ya zo in ji Dada nasan karata za'a kai sai na bi bayansa ba tare da yasan ina binsa ba.
Na makale a soron Dada ina addu'ar kada Allah ya kawo Bulkachuwa tunda dakinsa a cikin soron yake.
Ta ce "ka fa'dawa Yabi ta tsayar da miji da dukkan yaran ma.
Na umarce ku, ku aurar da su nan da watanni biyu".
Baban kasuwa ya ce "Shi kenan"
Ya fice ya barta da Babanmu."
Ganin zai fito ya gan ni sai na yi maza na fice daga soron na tsaya a bakin k'ofar shashinmu.
Ya zo wuce wa ya dallaro mini ido da sabuwar tocilayit dinsa da alamu suka nuna yau ya zuba mata sabbin batira saboda tsananin hasken ta.
Na dauke kai tare da saka hannunwana na rufe fuskata dan rage wa kaina kaifin hasken da ya dauke mini ido.
Takaicin rashin gaishe shi ya sanya ya ce "Asiya ce?"
Na dauke kai a shak'e na ce "Yabi ce?"
Ya kuwa bu'de murya ya ce "Ja'irar yarinya mai mugun y'anci dama nasan ke ce zaki gan ni ki mini irin wannan iyashegen. Na ce ba, zaki yiwa ubanki Sani hakan?"
Na dauke kai ina kunkunin fa'din "Ai kai ma ba zaka yiwa su Maijidda irin hakan ba".
"Me kika ce? Bude Baki sosai ki fa'di abin da kike ce wa shedaniya."
Ganin Baban Tsakiya dawo ya nufo mu dan ya shiga wajensa ya sanya Baban kasuwa ya d'auki k'arfaffan salati.
Ganinmu hakan ya sanya Baban Tsakiya ya dakata ya ce "ya ya ne Iliya?"
Ai kuwa ya hau rattab'a masa bayanin da aka yi masa na karya akan fad'anmu da Maijidda.
Wani abin mamaki a gabana ya lauya zance yana fa'din a gabansa ma, na zage shi yanzu nan. Da kunnensa ya ji ina zaginsa.
Baban Tsakiya yana bu'de baki sai ce wa ya yi "Tuni fa na d'iga alamar tambaya akan yarinyar nan domin wacce ta saba cudanya da maza ne take irin wannan dibar albarka."
Gabana ya yanke ya fa'di wacce irin magana ce mai muni ta fito a bakin kanin mahaifina kuma uban wanda nake burin aure?"
Na yunkura da nufin mayar masa da zazzafar magana sai kuma na tuna girman aika aikar da zan janyo wa kaina da uwata.
Na sani mahaifina ba zai d'auki al'amarin da sauki ba, domin kuwa zai ce tunda na iya zagin dan-uwansa shima zan zage shi, hukuncin da zai biyo baya kuwa na tabbatar zai zama mai tsananin gaske.
Na ha'diye maganar na juya na tafi na barsu dan kada na yi subutul kalam.
Sai na sake juyo muryar Baban kasuwa yana sake cewa "Na kagu a samu mai tsautsayin daukar kara da kiyashi ya zo ya kwashe ta, ko zamu sarara da musibarta domin ta riga ta zame mana tamkar annoba" .
Baban Tsakiya ya ce "Lallai kuwa kara da kiyashi daukar marar sani, na tausaya wa ahalin gidan Sarkin gida q tunda ina ganin d'ansu a wajenta"
"To namu d'an fa? In ji Baban kasuwa.
Baban Tsakiya ya yi wata irin dariya ya ce "Ta yaro ai kyau take yi bata k'arko, yaushe kana ganin kashi a jikin mutum, za kuma ka yi kuskuren bari naka ya dauki abin nan?"
Kai-tsaye dakin Gwaggo na fa'da na zauna akan tabarmar da take shinfide, yayin da take zaune gefe daya, yanayinta ya nuna a takure take ma'ana tana cikin zullumin kiran da aka yiwa Babanmu me zai haifar mata.
Na sassauta murya na ce "Gwaggo ki yi ha'kuri dan Allah"
Ta muskuta ta ce "Idan ban yi ha'kuri ba ya ya zan yi ne Yabi?
Ai a gabanki aka tabbatar mini ni agwagwa ce akan ki.
Kinsan me hakan yake nufi kuwa?"
Manufa kina gaba ina bin ki a baya, saboda gudun zuciyarki da nake yi.
Ace yanzu kullum a cikin d'aukar wa kanki baki kike, sai ka ce ke kad'ai ce a gidan?
Ga yar'uwarki nan ban ta'ba jin an kawo togaciyar Nazira ba.
Amma ke idan ba'a kawo k'ararki ba, sai idan baki fita ba, ko kuma kin ha'du da masu alkunya, anya Yabi kina ganin kin hau turba mai b'ille wa?
Jikina ya yi sanyi sosai na ce "Duk fa'dan da nake yi kowanne takala ta ake yi, ba wanda nake yin sa na rashin gaskiya, amma ki yi ha'kuri zan yi kokarin koyo ha'kuri idan an nemi ganin rikicina".
Ta kafe ni da ido tana cewa "koya ma zaki yi Yabi?
To fa'da mini zuwa yaushe zaki fara bita?"
Na yi kasa da kaina na ce "Addu'a zaki tsananta yi mini a sanya ni cikin bayi masu ha'kuri da kawaicin cutarwar mutane. Amma a zahiri saboda ke zan yarda na zama mai kawaicin tunda abin da kike so ke nan.
Domin ni dai har yau ban ga ranar da ha'kurinki ya miki ba, ban ga kuma ranar da kawaicin Babanmu yayi masa ba, tunda yau an kai dan-uwansa ne mai kirana da lalatacciya mai bin maza".
Na fa'da hawaye na kwace mini ba tare da na shirya zubarsu ba.

*Annur food Delicious*
*Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.*
*Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa*
*HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna*
*Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya*
*08039183880*


*VIP 1k, regular 500.*
*2384876855*
*Surayya Ibrahim*
*Zenith Bank.*
*Shaidar biya ta*
*08032773332.*


*BAK'AR TA'ADA*
*NA*
*SURAYYA DAHIRU GWARAM*
*(MRS M.I.NASHE)*.

*Marubuciyar*
*Halin Yau*
*Sabo da kaza*.


*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.}``` ✏️
____________(✪)______________
https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•


*Annur food Delicious*
*Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.*
*Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa*
*HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna*
*Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya*
*08039183880*


11&12.

A ki'dime Gwaggo ta ce "Baban Kasuwa ne ya fada miki hakan Yabi?".
Na girgiza kai na ce " A a Baban Tsakiya ne".
"Tirk'ashi"
Gwaggo ta fa'da a hautsine.
Na sunkuyar da kaina k'asa ina jin wani irin al'amarin tashin hankali na ratsa ni. Da kaina nake jin shekaruna sun yi k'aranci na dinga fuskantar irin wannan rikita rikitar.
Na rasa dalilin da ya sanya nake da ba'kin jini a cikin gidanmu.
Hatta a k'ofarmu mak'iyan da nake da su sun wuce misali.
Domin kafatalin y'an d'akin Mama Nazira ce take sona fisabidillahi, sai ko Yaya Salamatu ita ma kuma ba yadda za'a yi alheri ya samu ta doshe ni da shi, sai dai Nazira, tana dai bani kuncen kayanta da suka sha ruwa ainun.
Ni kuma murna nake yi domin tafi sauran yi mini adalci da sassauci.
Mama kuwa da tana da ikon da zata kore ni a gidan da tuni ta yi hakan tsabar yadda ta washi ta bude ido ta gan ni, mussaman yanzu da sana'ata take sake kafuwa.
Y'an dakinmu ne bana fuskantar adawarsu sai dai muna yawan haura wa sama da su a dalilinsu na ce wa ina daga wa Gwaggo hankali tunda kusan kullum sai na janyo mata bacin rai.
Inna kuwa tare wa yaranta fa'da da nake yi ne ya sanya na kubuta daga nata kaidin.
A hankali ta ce "Ai kuwa ribar ha'kurina gashi nan a bayyane tunda ban yarda na tafi na barku kun yi rayuwar ni y'asu a dalilin rashin uwa ba.
Kina gani ina nan din ma ya ya kuka kare ne, bare kuma na zubar da ku na tafi?
Ashe yanzu yadda yayunki suke dawainyar rike gidan nan bai isa abin alfaharina ba?
A bayyane yake kafatalin ya'yan gidan nan ba wanda Babanku yake mora irin yaran dakin nan. Ai kuwa ko iya hakan na ga ni ba abin da zan ce da Allah sai godiya. Domin wasu da yawa yaran nasu basu amfani kansu ba bare waninsu ya amfanesu.
Ubangiji ba abin da bai yi mini ba, na gode masa, kema na hore ki ri'ke ha'kuri ba abin da hakuri ba zai baki ba.
Ta ri'ke kaina ta ce "Àllah ya miki albarka, ya sassauta miki al'amuranki.
Ina fatan Ubangijin da yake sarrafa zuciya, ya sarrafa taki ta zama mai sassauci da afuwa".
Kuka ya k'wace mini sosai ina cewa "Ameen Gwaggo".
Ba komai yake sanya ni d'imuwa ba irin maganar Baban Tsakiya.
Maganarsa ishara ce akan aurena da Yaya J ba zai yiwu ba.
Zuciyata ta yi nauyi ainun. Na shiga rud'ani mai yawa, na sani idan har zan yi aiki da lura kamata ya yi na nisanci d'ansa tunda har yake neman maraba da ni a cikin gidanmu, ina kuma ace na zama cikin ahalinsa?
Mutumin da bakinsa yake ambaton jaje da alhini ga ahalin wanda d'ansu zai kwashe ni.
Bansan yadda aka yi ba na tsinci kaina

1 Comments On BAKAR TA'ADA
avatar
aisha-aminy

1 month ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment