Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba.
Su Baban Tsakiya suka fara raddi, domin ba karamin gyagije wa ahalin Baban Marina muka fara ba.
Dada ta fara taka tsantsan da lamarina, tunda yanzu tana samun kayan ciye ciye da ku'di saboda ni, ga turare da atamfofi da ya kawo mata har sau uku.
Ni da kaina na gamsu ku'di suna kan gaba wajen magance tozarcin d'an-adam, haka nan suna saka wa a ga girman ka aji tsoron zuciyar ka ko da baka da siffa mai kyau.
A raina sai k'yamar wannan *BAK'AR TA'ADAR* nake yi. Domin na hakikance rashin wadata ya sanya aka mayar da ubanmu ya koma k'arami a cikin gidanmu, wai daga d'an zuwan Kwamshina har an fara raga masa, inda ace shine mai ku'din ko wani cikin y'ay'ansa fa?
Sai dai Baban Tsakiya da na Kasuwa basu sanya wa lamarin albarka ba, asalima fadi suke a ina na hadu da shi? Ba d'an gari ba? A sharholiyarmu muka ha'du kawai.
A raina bana sonsa, bana burin aurensa, amma ya zan yi?
Tunda shi ka'dai ne ya tsaya ya na sona a yanzu, sannan gaskiya na gaji da zaman Gidanmu ba dan komai ba, sai dan yadda nake shan matsin lambar na fito da miji da kuma k'iyayya da aibantawa.
Sannan tunda ake yin hassada a lamarin, sai na kudire zan sadaukar da komai na aure shi, ko dan ya zame mana garkuwa a k'ofarmu tunda mutumin kirki ne wanda ya siffantu da dabi'aun addini.
Rannan kwatsam na fito daga inda nake koyon kwalliya sai ganin Yaya J na yi a zaune kan wani dutse da alamu suka nuna dakona yake yi.
Na zo zan wuce ta gabansa tunda ba zai yiwu na koma na fasa tafiyar ba.
Sanye nake da k'aton hijabina har kasa irin wadda ake ya yi mai hula ta baya.
Ban ce masa k'ala kanzil ba, asalima ban nuna na ganshi ko na san shi ba.
Da azama ya biyo ni a fusace ya ce "Yabi ashe zaki iya ganina ki mini irin wannan wula'kancin?"
Ban ce komai ba, ban kuma fasa tafiya ta ba.
Yana bina yana fa'din "Tun jiya ban runtsa ba, ba abin da nake so irin na ganki na tambaye ki abin da ya rikita mini al'amura".
Na tsaya cak na ce "Tambaye ni Jabir, ina jin ka".
Ya zuba mini ido, nima na zuba masa tsawon lokaci, ga mamakina sai kawai abin da na binne a kansa ya nemi taso mini da k'arfin gaske.
Na yi maza na dauke kaina, tare da sake d'aure fuska.
A sanyaye ya ce "Da gaske ne Mustapha Zaki yana son ki?"
Ba ja in ja na ce "Da gaske ne".
Ya kadu amma sai ya ce "Ke nan kin amince masa?"
Na kalle shi cikin ido, na ce "ko ban amince dan ra'din kaina ba, idan kaddara ta amince masa ai shike nan kamar yadda kaddara ta amince maka zama da Maijidda".
Na yi gaba na fara tafiya, ya biyo ni yana fa'din"me kike nufi Yabi?"
Ban kula shi ba, domin gaba'daya wani irin abu ya cushe mini zuciya da mak'oshi.
Sai fa'di yake "Kina nufin zaki aure shi ke nan?"
A tunzure na juyo na ce "A a ba aurensa zan yi ba, debe mini kewa zai yi, kafin a sahale maka ka nemi aure na".
Ya girgiza kai ya ce "Wacce irin magana ce haka Yabi?"
Kai tsaye na ce "Mai da'di kuma ta gaskiya".
Ya rasa yadda zai yi, hankalinsa ya kai k'ololuwar tashi.
Ya saki gauron numfashi ya ce "To ni kuma mene ne makomata ke nan?
Na kadu na ce "Ban gane ba? Nusar da ni."
Kai tsaye ya ce "Ina nufin ya maganar tawa soyayyar, ya batun aurenmu?"
Na kafe shi da ido cikin tsananin kad'uwa.
Kawai tambayar kaina nake yi "Ko dai ya samu mental disorder ne?
Amma sai na shanye mamakina na ce "Jabir ke nan".
Da sauri ya ce "ki ha'da ki ce Jabir Badamasi Toro, ba komai ba ne watarana In sha Allah zaki dawo da yayan domin ko kin yanke alakar da ta ha'damu ai baki isa ki wanke jinin da ya cakudamu ba"
Na daure fuska ainun ban ce k'ala ba.
Ya ce "Fa'da mini inda kika ajiye ni Yabi! Ina son ki, ina son na rayu da ke, ki yiwa Allah kada ki zalunci zuciyoyinmu, ki mini adalci ko da kina mini kallon azzalumi."
Na murmusa na ce " Wanne irin adalci kake nufin na yi maka?"
Ba nauyi ya ce "ki aure ni Yabi, ki bani damar da zan rayu da ke".
Ido cikin ido na ce "To kuma ya zaka yi da Maijidda da aka baka dan ana ganin ta fini nagarta, kuma y'ar babbar k'ofa ce?"
Ya ha'de rai ya ce "Ni da ke ne anan ba ruwanki da kowa, ni nake tsaye a gabanbki, kin sani kuma ina son ki, ina kaunar ki, idan kin bani dama ina da sauran dama uku a gaba da shari'a ta bani".
Na jinjina k'arfin halinsa na murmusa na ce "zaka ha'da ni da Maijidda kishi? D'iyar attajiri irin Baban Kasuwa da ta fak'iri irin Baban Marina?"
Ya naushi hanunsa ya ce "Kina da bak'ar magana Yabi! Ki yi kokarin kiyaye harshen ki, gubar harshe ta fi ta maciji dafi".
Na yi gajeriyar dariya na ce ", Gaskiya na fa'da amma tunda ba'a sonta, to na janye"
Nan da nan ya sace ya ce "To ki yafe mini, ina son ki, idan har kika ba ni dama zan tsaya miki, ba zaki yi kuka da ni ba. Zan fafata da duk wanda ya nemi shatale farin-cikinki da iznin Lillahi."
Idona ya k'ada tsakanina da Allah ina matu'kar son Yaya J ba kowa zai fahimci hakan ba sai wanda suka yi soyayyar k'uruciya ta rikide ta zama ta gaske, irin wannan soyayyar tana matu'kar tasiri a cikin zuciyar banu adam.
Amma na sani idan zan yaudari kowa, bazan yaudari kaina ba. Ba za'a ta'ba bari ya aure ni ba. Bayan k'iyayyar ubana to ni kaina wata irin kiyayya iyayensa suke mini wanda basu ki su gan ni da abin kunya ba.
Dan haka hawaye ya b'alle mini, da rawar murya na ce "Yaya J ba kowanne Dan Adam ba ne yake nasarar rayuwa da wanda yake so.
Mata da yawa ba wanda suke so k'addara ta aura musu ba, hakan nan mazan.
Yarda da k'addara kuma sharadi ne na cikar imani. Ka sani, na sani ba za'a ta'ba barinka ka aure ni ba. Na tabbatar za'a bari ka auro ukun da kake kirari a ko'ina amma kuma ba za'a bari ka aure ni ka'dai ba, na gamsu kana sona, nima kuma har yau din nan ban so wani kamar ka ba, ba kuma zan so din ba.
Mu yi addu'a Ubangiji ya sanyamu cikin masu soyayya dominsa wanda sakamakon hakan Aljannah ce".
Idonsa ya k'ada ya ce "kin yi magana ta hankali Yabin J. Rabon da na samu aminci irin na yau, tun kafin ki juya mini baya. Abin da nake so da ke na yarda na gasgata ki, amma ki bani dama na sake jarraba wa ko za'a dace a wannan karon, zan yi iya kokarina dan na same ki, ai na yi biyayyar a farko".
Na murmusa na ce "Shari'a bata hana hakan ba, amma zan ji nauyi mai yawa a ce ina kishi da Maijidda! Sai kuka ya subuce mini na gaske".
A rikice ya ce "Wallahi zan iya rabuwa da ita matu'kar ita ce cikas din cikar burin ranmu.
Sai dai ace na aikata *BAK'AR TA'ADAH* na saki aure akan wata macen da bata zo hannuna ba".
Na girgiza kai na ce "Ba za'a kai ga hakan ba".
A hanzarce ya ce "To ki huce da ni, ki bani damar auren ki".
Hawaye na zuba na ce "Na baka Yaya J. Nan da sati biyu ka fito, idan har ya wuce baka bayyana a gaban Baban Tsakiya da Baban Kasuwa da nufin ka je neman aurena gabansu ba, ka tabbatar magana ta k'are a tsakaninmu ta soyayya har abada, na kuma baka dukkan damar da zan iya, sai dai ka sani ba zaka ha'da ni zama da ita a gida guda ba".
Ga mamakina sai gani na yi ya zube a kasa yana sujjada.
Ya dago ya ce "Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah.
Zaki ji sakona kuwa daga yanzu zuwa ko wanne lokaci. Sannan na miki al'kawarin a Bauchi zan nema miki inda zaki zauna kafin na samu halin gina miki naki gidan".
Ya tako mini har titi ya tarar mini Napep ya biya, na tafi yana d'ago mini hannu cikin matsanancin farin-ciki.
Ni kaina wani irin shauki ke fizgata mai danne dukkan bacin rai.
Na manta k'iyayyar da Baban Tsakiya yake mini azima ce.
Sannan Baban kasuwa ba yadda za a yi ya goyi bayan ayi wa diyarsa kishiya da ni.
Amma dukkanmu hankalinmu ya gushe duk da ni din gatse na yi masa, amma TASIRIN soyayyar da nake yi masa ta taso mini haik'an ta saukar mini da farin-ciki mai tsananin gaske. Har nake fatan al'amarinmu ya kasance.
Na isa gida na ci abinci na yi sallah na hau kitso tunda mutum uku na tarar suna jirana.
Da yake a cikin nisha'di nake kafin ka ce kwabo duk na kitse musu.
Hatta Gwaggo sai da ta fahimci irin walwalar da nake ciki, rabon da ta ganni hakan tun komai bai tabarbare mini ba.
Ina idar da sallar isha na nufi wajen Dada.
Na tarar ta idar da sallar ita ma tana jan dogon carbinta.
Ni da Nasiba muke hirarmu, akan makaranta.
Dada ta shafa addu'a.
Muka gaishe ta ta amsa da walwala a dalilin yanzu shiri take yi da ni tunda tana samun alheri a dalilina.
A sanyaye Nasiba ta ce "Kin daina d'ora mana karatu dai Dada".
Ta murmusa ta ce "To kuwa yau zamu yi.
Zan d'ora muku addu'ar da idan kuka lazumce ta babu ku babu yunwa ila yaumil k'iyamati, ina nufin duk tsanani, Ubangiji zai yassare muku abin da zaku ci".
Nan da nan na nutsu domin idan na ji ingancinta na d'orawa Yaya Ummi domin ita kam tana wahala kafin ta k'oshi.
Ta gyara zama ta ce " *ALLAHUMMA RABBANA ANZIR ALAINA MA'IDATUN MINAS SAMA'I TAKULU LAANA IDDAL LI AUWALI WAL AKIRI...*"
Da sauri na ce "Ai mun haddace tuni, a cikin suratul ma'ida take Ashe haka take da falala Dada".
Ta washe baki ta ce "Ai wani bajimin Malami ya tabbatar mana matu'kar zaka biya wannan addu'a to haularka ba dai su rasa abinci ba bare kuma kai da kake bitar ta".
Na 'kyal-k'yale da dariya domin ni na dakatar da ita ne saboda kurakurai da na ji a ciki. Tunda ba yarda zata yi na gyara mata ba.
Ta ce to "Kun ga ni, ni da ku ne anan zan d'ora muku wata muhimmiyar addu'a, sadakar da zaku bayar ku yiwa Annabi salati, ku nema wa Shehu karin karama".
Cikin zakuwa muka ce "To".
Ta yi kasa da murya ta ce " ku dimanci *Ya ladifu*
Idan kun yi dari ba daya a cikon na dari ku rufe da fa'din *"Allahu ladifin bil ibadihi, yar-Razaku man ya shaa'u Wallahu Qawiyin Azim*".
Karon farko da Dada ta biya karatun da babu kuskure, da haka na dage nake ta biya wa a zuwan koyo nake yi, ita kuma sai fa'di take, tana sake gyara mini".
Muka kammala tana jaddada mu ri'ke adduoin nan falalarsu ta kai matu'kar shahara.Ya ladifu kundin sirri ne, gashi babu wahalar fa'da.
Na maze domin tsokanar ta zan yi, dan na ga reactions d'inta.
Na ce "Dada ki daina jan carbi fa, babu kyau Annabi ya ce mu yi da yatsun hannunmu domin su mana shaida ranar gobe".
Ta b'ata fuska kamar ba zata yi magana ba, sai kuma ta kufula ta ce "Asiya tun kafin a haifi Ubanki nake jan jarbi, duk wani sabon addini da kuke son kawo wa na raini Wallahi ba zai yi tasiri a wajenmu ba".
Nasiba ta fashe da dariya yayin da nake jira ta tara mini gayya irin wanda ta mini watannin baya, amma na ji muk'us.
Na jijjiga kai a raina sai fa'di nake "Allah ka sake bawa Yabi tsaron da ba za'a dinga tozarta ta ba." Ta ja robar maganinta da Honarabil ya kawo mata na warwarewar gajiyar tsufa da kara kuzari. Sai kuma na daidaita siga da bugawar zuciya duka daga kamfanin G.H.T. Na murmusa ina tuna a wajen FASEELAT ba zai kai kudin da na ga ni a manne a jikinsu ba. Na Santa a littafin Guduyo.
Nemi dukkan nau'in kayan ght daga gare ta cikin RANGWAME.
*07039269802*
Muna cikin haka sai ga Yaya J.
Ya sha kwalliya da wani farin yadi, d'inkin ya zauna masa sosai.
Ga kamshin turaren Dagmar ya baibayemu.
Cikin farin-ciki Dada take fadin maraba da Jabiru angon Maijidda".
Zuciyata ta buga da k'arfi, shi kuma ya dan diriri ce.
Ya waske da ce wa "Angon Dada dai, ai ke ce ta karfen".
Ta yi dariya ta ce "Yaudara ke nan."
Ya gaishe ta ta amsa da walwala tana tambayar amaryarsa.
Ya bata amsa da ce wa"Tana lafiya a gajar ce.
Ya shige cikin dakinta yana cewa "Zo mu yi sirri Dada".
Ta rarrafa ta bishi domin kuwa mutuminta ne baya rabuwa da kawo mata tsire da turare.
Ita kuwa duk wanda zai mata ungo tana mutunta shi.
Muka ci gaba da hirarmu wacce galibi Nasiba tana fa'da mini ciwon da take ji akan sharewar da Bulkachuwa ya yi mata.
Fa'di take "Dan Allah laifina ne?
Inda ya fahimce ni, da ya k'arfafa soyayyarmu ai komai za'a mini bazan kula kowa ba, amma daga maganar fatar baki ya d'ife, ya ce kada na kuma shiga sha'aninsa. Da yana sona ba zai yi irin wannan fishin ba."
Ta fa'da k'walla na zubo mata.
Jikina ya yi sanyi ainun domin kuwa Bulkachuwa ya riga ya yi rantsuwar ya yanke hulda da ita.
Kamar daga sama na ji muryar Dada cikin karadi tana cewa "Ina! Jabiru ka zo da *BAK'AR TA'ADAH* Mai wahalar tabbatuwa, ta ya ya zaka ha'da mini jikoki kishi? Dama kuma ba jituwa suke yi ba.
Ha'kuri zaka yi da Yabi domin tuni ta samu miji ita ma, dattijon arziki irin albarka."
A sanyaye na ji yo shi yana ce wa "Idan ban samu goyon bayan ki ba akwai matsala Dada.
Kin sani Yabi nake so tun fil'azal. Amma saboda na yi biyayya ya sanya na karbi auren Maijidda. Yanzu da nake son na cike wanccan burin nawa ba sai a taimake ni ba?".
Ya dinga magiya, tamkar zai fashe da kuka.
Cikin kad'uwa ta ce "Jabiru ka zo da babban al'amarin da yafi Dutsen dala nauyi.
Bana jin iyayenku ma zasu amince maka, ka bar maganar nan tun baka tono wani bacin ran ba".
Ba shakka ko nauyi ya ce "Ba zan barta ba Dada! Domin da zan iya barinta da ko ke baza ki ji ba.
Idan ba zaki taimake ni ba, to ki mini adalci kada ki b'ata al'amarin a gaban iyayenmu".
Ta ce "ita Yabi ta gamsu zata aure ka ka had'asu da Maijidda?"
Da sauri ya ce "Ina da tabbacin soyayyarmu ba zata yi zangwayenwar da babu alfarma ko fahimta ba, ban tuntu'beta ba, amma ina da yakinin ba zata juya mini baya ba".
Tsawon lokaci sun yi jigum jigum, muma da muka bar maganarmu muka kashe kunne muna jiyosu, jikinmu ya yi la'asar".
Nasiba ta ce "Tabbas soyayyar da take ta gaskiya kuma k'arfaffa ce ake yin afuwa da sassauci a cikinta."
Na kasa cewa komai domin hausa ta yi cikin hikima. Da Bulkachuwa take.
Bansan ya aka yi ba, kawai sai ganinsa na yi ya fito ya fice a hanzarce.
Sai ga Dada ma ta fito cikin rashin sukuni.
Ta zauna jiki a sanyaye.
Ta kasa jure wa ta kalle ni ta ce "Yabi Jabiru zai ballo wani irin tashin hankali, kada ki sake ki saurare shi.
Ki rike Alhaji nan yafi miki, ina tsoron abin da zai biyo baya."
Na yi k'uri ina kallonta a zahiri gaskiya ta fa'da tashin hankali zai iya biyo baya.
Amma kuma a zuciyata sai nake ganin son zuciya ne kawai yasa ba zata goya masa baya ba. Dan kawai Maijidda d'iyar shalelenta ne, kuma mawadacin gidanmu. Dan sai yanzu na fahimci ba fa wai ku'di ne da Baban Kasuwa ba, kawai a gidanmu ne yafi kowa wadata, saboda talakawa ne mu na sosai.
Me yasa a farko bata hana a bashi ita ba, tunda tasan ni yake so?
Me yasa a wanccan lokacin ba ta yi zaton hakan zai zama tashin hankali a dalilin gaba da kullaci da zai shiga zukatan y'an gidan gaba'daya ba?.
Duk yadda nake da ba'kin jinin a cikin ya'nuwana sai da suka yi kishin abin da aka yi mini, suka yarda ubanmu aka tozarta.
Tashin hankali tuni an shige shi ai, kawai sa'ar da aka yi Baban Marina mai sassauci ne, shi yake ta tsawatarwa dan kada mu kullaci y'anuwansa ko muce zamu rainasu.
Amma iyakacin wula'kanci da kaskanci an yi mana.
Ba kuma wanda ya k'alubalanci hakan sai Baba ta Bulkachuwa ita ma kuma bata da power kamar Babanmu. Duk da a cikin rufin asiri take, dai-dai gwargwado tana dan tagazawa wajen yiwa Dada hidima. Haka nan ita ka'daice kafatalin yan'uwan Babanmu zata aiko da wani abu da sallah ta ce a bawa y'ay'ansa.
Wani lokacin sark'a da yan kunne, ko hijabai, ko y'an takalma masu sau'ki haka.
Dan ko sallar da ta wuce da hijabanta muka je sallar idi ni da Nazira.
Amma Baba Maryo uwarsu Nasiba da bata iya tsinana komai har a Dadan ma ita take zuba mulki, haka nan komai aka yiwa Dada na dangin sutura ko wani abu mai k'yau karshe sai ya zama nata ko na y'ay'anta, ita kuma saboda auta ce da ta shiga rai.
*BAK'AK'EN TA'ADODI* masu yawa na faruwa a gidanmu da dole duk kawaicinka sai zuciyarka ta motsa sa'i da lokaci.

✍️

*Ina tallata muku kayan gyara na mussaman na mutanan Sudan da chadi*.
*Saiwowin dahuwar tattabaru*
*Saiwowin dahuwar kaza*
*Saiwowin Tsumi da Zaki dafa da kanki, ki ajiye ki sha sosai ya ratsa miki jiki*
*Y'aya'n gadali na mussaman*
*Hadadden daka emergency*
*Tsumin kwakwa da zuma*
*Turaren matsi na tsugunno*
*Maganin sanyi sadidan na mara har ma da gabobi*
*Gumba*
*Goran tula syrup and fruits*
*Tsumin Goran tula na asali*
*Duk zaku same su da RANGWAME kuma na asali me ba karabiti ba.*
*Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya*.
*Tuntube ni a wannan lambar*
*08032773332*

✍️


*BAKAR TA'ADA*
*NA*
*SURAYYA DAHIRU GWARAM*
*(MRS M.I.NASHE)*

*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.}``` ✏️
____________(✪)______________
https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•



*Annur food Delicious*
*Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.*
*Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa*
*HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna*
*Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya*
*08039183880*


*Last free page*

*500regular page*
*VIP 1k twice pages*
*2384876855*
*Surayya Ibrahim Dahiru*
*Zenith Bank*.
*Ko*
*7061488065*
*Surayya Dahiru Ibrahim.*
*Opay Bank.*

*08032773332*.

19&20.
Jin na yi shiru tsawon lokaci a dalilin tunanin da nake ta yi.
Ya sanya Dada ta ce "Yabi da alama zaki bawa Jabiru ha'din kai".
Na yi murmushi na ce "A a sai dai na yi imani Ubangiji ne yake shirya komai, dan haka shi na barwa al'amurana ya yi mini zab'i.
Dama kuma ban k'ullace shi ba domin ba shine ya mini laifi ba, sannan Dada idan har auren Maijidda da aka sanya ya yi ya bar ni, bai zama abin kaico da rikici ba, ashe kuwa nawa auren da yake hak'ilon yi a yanzu adalci ne da tsantsar gaskiya".
Jikin Dada ya yi tub'us tabbacin tasan gaskiya na fad'a.
Da k'yar ta ce "Ana barin halak dan kunya Yabi".
Are yi murmushin da yake nuna ba wananan maganar.
Ta sake ce wa "Kuma yanzu wannan dattijon arzikin sai ki bar shi, duk dawainyar da yake faman yi dake da dukkan dangin ki?"
Na sake murmushi na ce "To ai aure gaibu ne, sannan Allah ne ya gadar wa maza su yi ta hidima da macen da suke so dan su ja ra'ayinta. Abin farin cikin ba rok'arsa nake yi ba, haka nan wani nawa bai ta'ba rok'arsa ba."
Ta yi shiru ta rasa me zata ce kuma.
Sai ta hau addu'a da kamun k'afa a wajen Shehu kada zuri'arta ta rikice a dalilin wannan al'amarin.
Har k'asan raina da al'amarin zai yiwu ba wani nauyin da zan ji, domin nawa ne aka k'wace mini saboda kawai zuciyar ahalin gidanmu a cike take da gilli da ba'kin ciki mai yawa.
Kwanaki biyu kullum sai na ga Yaya J ya zo gidanmu, kusan a nan yake yini, ba shi k'ofarsu ba shi a wajen Dada.
Rashin sukunin da nake ga ni a tare da shi, ya tabbatar mini kasafin ya cud'e fiye da zatonsa.
Bai kuma neme ni ba.
Kwanaki suka yi ta shud'e wa har aka samu kwanaki bakwai babu tartibiyar maganar Yaya J.
Dama na sani mawuyacin abu ne su amince, sai dai dan ya ce zai iya ha'diye gatari ne, shi yasa na sakar masa k'ota ko zai dace ya ha'diye, bayan ya sha kakarin tagwaitakar riskar ajali.
Ina cikin wannan yanayin sai ga wani b'acin ran, gidan da Bulkachuwa ya tura su Baba akai masa ku'din aure suka shafa wa idonsu toka suka ce basu san wannan maganar ba, ba zasu dauki y'arsu su bawa wanda aka bulale a bainar nasi bisa k'azamin laifi irin wannan ba, kuma marar tartibiyar sana'a.
A sanyaye su Baba suka dawo babu kuzari.
Dukkan iyayenmu ukun nan sun ji ciwon abin da aka yi musu. Amma ba wanda ya hango irin wannan tozarcin mai ciwo suka yiwa Babanmu ta hanyar hana Yaya J aure na.
Shi kuma Baban Kasuwa ya dauki tasa y'ar ya ba shi.
A gabana Baban Marina yake yiwa Bulkachuwa bayanin halin da ake ciki, cikin alhini da bacin rai.
Ba wata damuwa mai yawa ya ce "Babu damuwa Baba! Ban damu ba, domin an hana ni aure a cikin gidan nan ma. Dan haka dan waje sun hana ni ba zai zama abin kaico ko tashin hankali a gare ni ba.
Ciwon da nake ji daya ne! Da na yarda da hukuncin Allah. Na amince aka mini bulala sai kuma na zama abin k'yama a idon al'umma.
A wauta ta imani na yi, domin na yi biyayya ga abin da Allah ya zartar ba tare da bin ra'ayin turawa na yiwa hukuncin Ubangiji tawili ba.
Na sani na yi laifin da ku kanku na zubar da darajar gidanku, amma ina yiwa Allah kyakkawan zato zai katange ni daga sake aikata wa tunda na yarda da hukuncinsa, na zabi tereren duniya akan na lahira.
Matu'kar kuwa mutane zasu ci gaba da nuna irin wannan *BAK'AR TA'ADAR* Akan mai laifin da ya d'aura d'amarar taubatun nasuha ba shakka zasu dauwamar da mutum cikin b'ata, tunda idan ya dawo kan sahihiyar turba, ba zasu karbe shi ba, ba zai tsira daga yamididinsu ba."
Baba ya kasa ce masa k'ala domin jikinsa ya yi sanyi da kalaman na Bulkachuwa.
Ni kaina da nake gefensu ina wa Baban Marina wanki ba k'aramin sanyaya jikina kalamunsa suka yi ba.
Na sani gaskiya ya fa'da, hana shi aure da ake yi kuma ba shine mafita ba, illah bashi lasisin sake dulmiya cikin zunubin da ake k'yamarsa.
Baya ga hakan basu taimaki y'ay'ansu ba, tunda dukkan y'anmata nasa da aka hana shi auren su sonsa suke tamkar su bashi kyautar kansu, ashe kuwa idan ya so lalata rayuwar yaran nasu cikin ruwan sanyi zai yi hakan, tunda Ubangiji ya kyautata masa halittarsa k'warai da gaske .
Dan haka zai iya amfani da son da suke masa ya lalatasu a banza, idan kuma hakan ta faru zai yi wahalar gaske ya karbi aurensu domin komin lalace war namiji baya son lalatacciya. Cigaba aka samu ko tabarbare wa?
A wannan rana na fahimci ashe cikakken mutum ne mai nutsuwa, kawai sharholiyar ce ta yi masa k'awanya.
Ya katse shirun da Baba ya yi ta hanyar ce wa "Baba na gode sosai, zan cigaba da istigifari, idan al'amura suka sake daidaita mini zan fara sana'a, zan je Bulkachuwa na nemi aure ina da tabbacin a dangin mahaifina ko nafi hakan lalace wa zan samu mai k'arfin halin da zai bani aure tare da fatan auren ya zame mini sanadin shiriya da bud'ewar arziki."
Ya mike ya tafi yana sake godiya sosai.
Ajiyar zuciya kawai Baban Marina yake yi, na lura ba k'aramin ki'dima ya shiga akan al'amarin ba.
Murya babu amo ya ce "Yabi idan kina son Alhaji ki ce masa ya turo wakilansa, idan kuma ba kya sonsa to ki fa'da mini zan sallame shi".
Na yi k'asa da kaina na kasa amsa masa, daga haka kuma sai ya fita, na bishi da ido amma tunanin a yadda jikin Baba ya mutu murus akan al'amarin Bulkachuwa da ace Adda Nazira ba ta yi aure ba, Babanmu na iya juya wa nak'asunsa baya, ya

1 Comments On BAKAR TA'ADA
avatar
aisha-aminy

1 month ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment