Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dari biyu akudin da Alhji badama yaturo min jiya nasa kati.

Suka kwashe dadariya harda tafawa badee tatashi tadauko ruwa afreg tada wo taxauna

"Ayya anty sumy ko yanxu kawata huru Insiyya tana Ina oho kwanaki nakejin madam suna Shira da wannan kwarton nata Alhji Amjad din Nan wai suma basace gawanda yasiyetaba halama shima yasiyarwa da turawa ita,

Sumy tajinjina Kai
"Ai wadan Nan mutanen axxalimaine wlh kiga yarinyar Nan Babu ruwanta Amma sun lalata Mata rayuwa ,koke batislas akamiki ba domin unnarki tasani kuma da yardar ta akataho dake,itakuwa fa wlh wayo sukama kakarta suka sato Mata jika Nima natabajin suna wannan maganar shiyasa naji,kuma itanan ala dole aurenta takeso abokin shedancin nata yayi ,hummm ajaka yake kallonta Mara amfani,fa

Badee tace

"Wlh hakane sato ta sukayi domin alamu ma sun nuna haka,

Sannan tayi dariya "ai insha Allahu anty sumy rayuwar huru baxata taba lalacewa ba, domin bansan meyasaba ajikina nakeji batacikin mummunan yanayi.

"Allah yasa ,ke bakisani ba mutumin madam fa Anna ciki ana rage xafi da faree

Badee tayi shewa tana ba sumy hannu suka tafa
"Dakyau madalla dama wai inba shashanci irin na madam ba me alhji Amjad xayyi da tsohuwa irinta bayan shida kwarinsa har yanxu ,hammm kainaji dadi wlh

"Kemadai kyafada.

"Munafukan banxa algun gumai ,tsinannu ,tanbadaddu ,kwashashshu,wadanda basu da albarka ko kadan,aunixaku xauna kunaima diban albarka sbda ku din bakaken la anannune,toh yau duk sainaci tsinin bara ubaku,wlh agidan Nan 'yan isaka tanbadaddu. Gantalallun asara.

Madam fanna tagame xaginta tana karasowa falon takwashe badee da Mari tana nunata dayatsa tayikan sumy tamike dasauri tana direwa bayan kujera cike da futsara takama kugu

"Bafa xaki dakeniba domin Baki haifimeni ba ,dakin haifeni da baxaki bani lasisin karuwanciba

"Toh asararriya, kinmanta dai Amma alalace atanbade naganki,anaba 'yan biyu sha biyar na 'yanta ki ,nabaki 'yanci,vutulun banxa butulun wofi ,dama ni nace nahaifekine,Ina ni Ina haifar watsatstsiyar 'ya irin ki ,ai wannan sai dai uwartaki ,shegeya 'yar tsiya dama Ina kula tsaf da take taken ki kuma wlh dagayau saikin fara nadamar rayuwarki wlh.ku kitattara kibar gidan Nan Don bana ubanki bane,

Sumy tayi tsalle ta dire tana fadin
"Shege kafasa Dan halak sai yanka madam gidakuma xama daram domin dama muke biyan hayarsa bawani shegeba ,Baki Isa kimin goriba domin ko ficika bakiyimin kyautartaba ruwa wannan danasha abaya acikin aljihunki saidana biya toh saikuma me da harkike kirana butulu,umhum

Faree da alhji Amjad suka fito shida gajeran wando itakuma da daurin kirji, madam fanna tagama kamewa kam a inda take.

_______________________________
Lokacin da Sultana ta isa fada kaitsaye tanemi iso akabata umarnin shiga Papa King ya sallami bakinsa suka tafi yarage daga waxiri sai sauran'yan fada yabata Umar nin fadin uxirinta Amma takasa tasaki Kuka me ciwo hakan yasa Papa King ba bafade daya damar Kiran prince awaya..

Saida aka Kira sau biyu kafun yagani yadaga

Ba ajuma ba yashugo fada dama Papa King yabada umarni aje Akira momi da Ammi ,dakuma yayyensa biyu prince Ekbal dakuma prince Naheed.

Saidakowa yahadu sannan Papa yakalli Sultana

"Masarautar mu Mai albarka tanason Jin damuwarki matar prince meke tafedake haka ciki harda kuka munasonji fatan mu yaxama alkhairi.

"Yayi kyau yayi Mai martaba Allah yaja kwana ,da tsawon Rai ga adalin sarkinmu , ke yake saurare 'yar mutan omo,ke yake saurare sarkin adalai .

Fadawan sarki suka hada Baki wajen isar dasakon sarki ga princess sultana tareda kirarashi
Cikin kuka da hawaye masu xafi tasanar da fada abunda yafaru ,tundaga lokacin data ga huru har Kama magan ganun dasuka gudana atsakaninsu.

Sarki har jijiyoyin hannunsa inka kalla suntashi sbda bacin Rai, domin kallo daya yayima prince yatabbatar da maganar Sultana gaskiyace sbda yadda prince yadukar dakai xuffa ke karyo Masa tamkar wanda aka watsa Masa ruwan xafi adukkan jikinsa.

"Shin menene gaskiyar lamarin daga gareka Ammar??

Jin maganar sarki tahautsina ma prince ciki Amma dayake namijin duniyane yakara da mugwayen 'yan uba ma irin su Ekbal da Naheed,basudauki komi ajikinsa basa kaunarsa tunda sukaga Papa King yafi sonsa,jarimine shidin kwata kwata bayada tsoro kokadan ko papa King suke magana baya dauke ido,yanada tsayawa kwarai.akan diga digansa.

Dago kansa yayi yakalli momi takwada Masa harara tareda wornning dinsa da ido akan karya amsa.da eh. Yajuyar dakansa yakalli Papa King saikuma yajuyardakansa yakalli sultana tabbas baitaba xaton xata jawo wannan rigimar da wuri har hakaba yaso ace dakansa cikin nutsuwa da salama yaxo yasami iyayen nasa da wannan maganar.

"Ina magana dakai ne fa Ammar amsa ,.

Batareda shakkar komi ba yafara magana.
"Hakane Papa,inasonta kuma inaso a auramun ita, Papa na kaidin adaline Dan Allah karkaki maganata da beauty, sannan sunanta HURU INSIYYA kuma 'yR nageria ce,Babu ruwanta Papa rayuwace takawota har inda nake Allah yajarabceni da ita baxan iya rayuwa Babu ita ba.

Ba Papa King ba har momi takulu haka Ammi datake son Ammar kamar danta data haifa. bataji dadin abunba itabama tasan wacce kasa bace nageria.

Kusan minti goma fada tayi shuru bakajin komi sai karar fanka dakuma numfarfashin su.kowa jiran hukuncin sarki yakeyi.

Papa King ya yunkura cikin dacin Rai yafara magana,

"Raina yayi xafi sosai idan nayanke hukuncin nidaya baxai dadiba ,kafun Nan Fatima kinji abunda ya faru ko yakike ganin Abun.

Mome tawatsawa prince mugun kallo
," Mai girma ban amince ba ,adomin wannan din xubar dagirma da darajane ga masarautar mu.auren bare baren ma ,barara wacce bamuda sani game da tabbatar asalinta.

"Hakane Ulaitu fa mekikace kinada hakki akan wannan

Takalli prince tareda gyara xamanta
"Duk hukuncin daka yanke yayi Amma ayima yarona hakuri yayi kuskure,sannan idan baxaixama xafiba abamu dama nagaba domin samun wata alfarma shi abun dake damunsa din baya kwankwasa kofa balle yaturo sako

"Amma daraja da kaskanta,basa jerawa amatsayin kawaye ulaitu

"Hakane maigirma Amma,shidin jaririn mune,mundorawa ruhi da xuciya kauna,har yasa jaririyar xuciyar Dana, sakankance wa darainon mu,akan xaisamu alfarmar mu takowacce hali,ko tsanani ,inta xo, kar mukaryamar xuciya me girma ,ayidai bincike xaifi kafun komi.

"Ulaitu,korafin ki Yana baya ,bayanxuba dubasa domin baxantaba hada wannan gambixar ba,saidai darajar tausasawar kalami,xatasamu saukin mu.

Yakalli prince Ammar

"Ammar Duk dakamin biyayya a auren Sultana,hakan baxai hana in hukuntakaba ,sannan ita ma yarinyar mutkar ba 'yar gidan sarauta bace toh dagayau xanxuba jami'ai aduk inda akasameta akawota domin ta amshi hukunci,irin na gidan sarauta, domin,tatsallake iyakarta kuma inajiran yaki daga kasarta sbda kwatarta, mutkar tashigo hannu hukumarmu.

PRINCE ya xaro ido hukuncin yayi tsauri kwarai makuwa domin yasan irin hukuncin su,kurkukun cikin masarautar kanta abar kallo da tausaice, yadda akaraya axaba da bunkasa wahala,sukagirma,kokadan basauki inka tabbata Mai laifi.

Papa yakalli waxiri
"Akiramin minestan tsaro xanmagana dashi,sannan ayanxu basai gobeba arufe masarautar Nan bashiga ba futa mutkar ma aikacine ko bawa. Natsawon kwana uku, kawo lokacin ansan mafita. Kaikuma Ammar kaje kanemo diyar sarauta aduk indayayi maka xanbarka, ka aura ,ko yaune.
Wannnan shine adalcin mu.

Yakalli shugaban hidima da fada
"Anemo kwararren me xane domin axana fuskarta .

"Angama maigirma sarkin adalai angashsheka .

Yafuce.

Ba ajimaba shugaban hidima da fada yashigo tareda maixane dama akwaisa na musamman acikin gidan sarautar.
Sultana tanafadi Ana xanawa cikin ikon Allah saiga fuskar HURU ranga dadau, tafito tas duk Wanda yasanta xaiganeta.

"Allahamdulillah nasallami Kowa atashi atafi nagama yanke hukunci.,

PRINCE yaxube kasan kafar Papa King Yana Kama kafarsa hannu bibbiyu.

"Aa Papa AA Papa xaka illata xuciyata dakanka,Papa nine fa danka Ammar,kaikacemin dakanka xakaso duk abun dana keso

"Ammar kaxo da Al amura masu rikitarwa sannan kuma mutuncin masarautar mu xaitaba,kaje kararrashi xuciyarka ,karkabari fushina yatabaka, Fateema kitaushesa domin hukuncina baxaitaba tashiba

Damugun xafi Ammar yabar fadar momi da Ammi nakiransa yafuce dasannu kowa yakama gabansa akabar Papa King da tawagar sa. Cikin jimami da mamakin wannan Al amari daya faru kamar amafarki.

Bayan sunyi waya da minestan tsaro nakasa yaturo jama arsa suka amshi xanen fuskar huru Insiyya sukafuce sannan aka karowa masarautar Jami ai sbda bince kotana cikin gidan.

PRINCE kuwa tunda yasan batacikin garin ma ,hanklinsa kwance,kuma yasa aransa ko mun Bala e saiya auri huru Insiyya kowa yayi yagama yabada Naan da wata biyar komai xai setu.
___________________________
Madam fanna takalli alhji Amjad tsam dagashi sai gajeren wando halakoshi baikula ba ,takalli faree saikuma tanunasu da yatsa

"Menene haka kuma Amjad mekakeson nunamin kana bin fareeda kenan sabda kaidin tsinanne watsatstse.ummm
Kema tsinanniyar kike bude Masa ata yanadiba sbda karuwanci yakai intaha.
Amjad yawatsamata mugun kallo

"Ina kedin ba uwata bace ko matata,balle naji kunyarki, saime barikice kema wayasan mutane nawa kike mu ammala dasu,inkika fuce, ,karki kuma xagina sbda Kinga kingirmeni aiba haifata kikayiba faree komaciki inaxuwa .

Lokacin dafanna tadaka tsalle tashako faree ma batasaniba saijin naushi tayi yasauka afuskarta gefe guda.alhj Amjad yasauke Mata hannunsa.

Badee da sumy suka kwasheda Dariya suna fadin

"Wash sannu madam Ayya

"Allah yatsine maka albarka Amjad wlh saikaci bara ubanka la anannen duniya fasiki,najadu kawai.saikasan nikadaka afuska Dan tsininn........ Babanka Dan wahala saina tonamaka asiri aduniya saika toxarta wlh.

Ko saurarenta baiba yabi faree daki Yana fadin

"Idan tafita ku rufemana gidan domin tuni nayimagana damai gidan hayarnan.cewa yadawo hannuna ,inkuma xaki iyacigabada xama bamatsala kisa abunki akasuwa kema,

Madam fanna kadan kadan take gani sbda naushin yataba idaninta.

"Xama daram mako asararre Dan iskan duniya wlh saikayi birsin tadalilina xakaganine.

Yawuce yabartanan su sumy ma said Dariya suke shekwa,takallesu

"Tsinannu duniya uwar wa kukeyiwa Dariya Dan kan uwarku

Badee tatabe Baki tana fadin
"Wayasani

Sumy tace
"Uwar bariki mukeyiwa Dariya ganin yadda takwabemata Kinga saimuyi takanmu tunkafin Abu yaxo kanmu,wooo yau su madam ansha hannun maxa kingakwa yadda fuskarki tafara tashi.

Suka fashe da Dariya ganin xasu haukatata yasa talallaba kafarta taja jikinta tashiga dakinta takira Dr AA yadubamata fuskar,domin kuwa tadaku wlh,kawai tadaurene sbda karsu ga gaxawarta.

😘INDIA😘

❀️❀️😘MUMBAI 😘❀️❀️
Love story
Hot Love
Hot πŸ˜‹πŸ˜‹πŸ˜‹πŸ˜‹
Zanba cikin Amin ci😭😭

Yamarasa Wanda irin bayani xaiyima mAh tun ajirgi yake kokarin harhada karyar daxaiyimata duk Daba karya atsakininsu Amma yau tadalilina prince xaimata karya,

Donhaka yatakarkare yake fadamata cewa,πŸ‘‡πŸ‘‡

Har kasa huru taxube tana gaida mAh cikin fara ah mah tariko hannunta tana fadin
"Kyakkyawar yarinya ykk Axad inakasamo wannan budurwa kuma,

Huru ta sunkui dakai Raxeena kuma takurama huru Insiyya ido,Dama tana ganinsu tare aranta tace shikenan tafaru takare yadauko matsalar tasa yataho da ita yaushe Axad yafara soyayya toh, jin maganar sa yasa ta maida hankli.

"mAh itadin alhakin prince NE, domin yafadamun.cewa sunxo Dubai tareda iyayenta wani uxirin saikuma tabata an nemesu ba asamesu ba tsawon lokaci tana gidan su prince amatsayin ajiya Ana neman iyayenta gashi lokacin batakai haka girma har bbc ansa labarin batan nata Amma shuru,yanxu kuma prince wata matsala tafaru agidan saarautar shine suke so sukoreta daga ciki,kinsan dai yadda suke da karanci yarda ,yarokeni alfarmar intaho da ita Nan India murikemasa ita nawani lokaci kafun komi yalafa asan abunyi.

mAh ta tausayawa huru itakuma huru jin wannan karya ta Axad saita tuna Mata da Annan ta,lokaci guda hawaye yawanke fuskarta

Tsaki Raxeena tayi kasa kasa tana barin falon domin tagano karyar Azad kaitsaye kuma xata xamemusu ciwon ido wlh.

Yakalle ta aransa Yana fadin.
Tadau hannu 'yar renin wayo kowayasnma asalinta oho.har dawani hawayen munafunci

"Ayya my son nidama prince din xaikyaleta anan din gabadaya sbda karma watarana takoma rikicin yatsara da ita,meyasa mutane kehaka Axad shifa da na kowane Inka taimaki Dan wani kaima watarana wata uwar xata taimaki naki Dan.

Huru tace aranta mahaifiyarsa mutumniyar kirki bakamar Shiba axxalumi har karyani yakusayi.

Axad Yana daddana waya yace
"Um um abari kawai yadda yace mAh din xaifi

"Shikenan saita xauna adakina

"AA mAh xa abata dakinta kawai tunda ga dakuna Nan ascound falo. Aibadamuwa ko.

"Yayi my son Allah Yama albarka

"Amin yabar sashen domin xuwa nasa yahuta yadan gaji ,

Raxeena ce tabisa tana hango futowarsa

"Bro

Yadakata
,"Bro yanxu fa yakakeji gameda xuciyarka dakuma jikinka gabadaya

Yatabe Baki

"Normal

Yanafadin haka yashige mota kamees yaja sa xuwa sashensa don bakasafai yakeson tafiya akafaba komin rashin nisan guri.sai dai in motsa jiki yafito yi. Akwai gurin motsa jiki na musamman daya idar da sallar asuba yake xuwa yamotsa jikinsa sannan yayi wanka yakoma bacci.

Lokaci da ruwa ke sauka ajikinsa wata nutsuwa keratsa shi ta ko Ina yanajin kwanciyar hankli nashigarsa,yanajinsa yacika yanxinkan baida ajiya ako Ina ,sannan wani nishadi ke shigarsa yanajin farinciki haka siddan. Agaggauce yashirya yafuto falo ya ci abunci yafuta Shan Isa sbda jikinsa yasaki sosai.


AFTER 2 WEEK'S

mAh najin dadin xama da huru sosai data tambayeta sunanta huru tace huru Insiyya Amma prince Yana cemin beauty shikenan mAh ke kiranta da beauty shiyasa duka ma aikatan gidanma suke kiranta da beauty sbda tasaba dasu batada kiwa ko ganda haka take tayasu yin aikin gida sosai ko mAh ta hanata Saifa tayi saidai tabata hakuri suyi Dariya kawai.

Shiko baida aiki sai xarya sashen abukadan yace shiya kawosa atakaice yanxu anan yake breakfast, ranar da ba office yayi lunch, yayi dina.har mAh tafara mamakin Abun Amma tana alakatanwa da ko sbda raxee yake xama .itakuma huru ganin haka yasa tadaina xama afalon ma duka takexama asashen su Janbi chatanya,ko dakinta.duk abundake faruwa Raxeena na sa ido.

Sunayin waya da prince sosai kuma tafara sakewa dashi ,wayar hannunta lokacin da Raxeena taganta saidata Sara sbda saitasayi tata sau uku.

Baisan meyasa ba yakejin kunci inyashigo sashen mAh baigantaba yau sati biyu kenan baikuma ganintaba meyasa kodai shitake boyewa mAh nata magana baijiba sai data tabashi.

"Sorry mAh

"Dama kwana biyu kabi kacanja meyasa kaki fadamun komi kodai kana boyemin wani Abu my son?

Ya sunkui dakai
"Babu mAh kiyarda

Da gudu ta iso gaban mAh konkuladashi batayiba tana xama kusada dama takama hannunta

"Xanraka aunty Janbi kasuwa yanxu mAh

Xaxzakar muryarta tadoki dodon kunnensa yadago aikwa yanakallonta lokacin taluradashi takallesa saikuma takomar da idonta kanma tana jin ansarta

"Banason yawo fa beauty Amma kifadamata karku Dade sannan tasai Miki duk abundakika gani kina so akasuwar tana murmushi tace

"Tanx my mAh
Tafuce tana tsale tsallenta

Yabita da kallo yamakasa dauke idaninsa daga kanta itama mAh tana kallonsa yanxu kuma tafara gane damuwar Dan nata.don haka tayi murmushi kawai tana fadin.

"Ayya beauty kenan akwai hankli yarinyar sosai

Sannan ya waske Yana Dan gyara xamansa.

"Amma meye nayawon mAh kuma kina kallo fa riga da wando ne jikinta Kika kyaleta yakamata murike ajiyar prince dakyau mAh

Dariya takusa kwacewa mAh ta dake tana fadin

"Yarona kenan ai yaune kawai tafitan.kasani ma kotayo maku siriki amata aure kawai basai Tama komaba,Dubai din .

Tamkar tatsira Masa allura ya Mike xaimasifa kuma yatuna toh menene nadamuwarsa Dan ance haka

mAh takallesa da mamaki eh lallai Axad yafada soyayya

"Lafiya kuwa Axad??

mAh ta tanbayesa tana tsaresa da ido

"Banga gilmawar Raxeena ba yau kuwa mAh tana lafiya

mAh tace.
"Kuma tana ciki hala wani Abun takeyi,Niko yamaganar mudakai gameda tsakaninku da Raxeena Ina so mutsayar da magana nida 'yR uwata salama.

Gabadaya yaji ransa yabaci ,dama tunda tace ko huru xatayo saurayi yaji baiyarda da futar ba hanklinsa ke tashe.

"Kibar maganar nan mah akwai yuwuwar samuwar matata tawani barin.maganar sista kibari karma abunyayi xafi pls.

Yabar falon mh tayi dariya tana Kara gasgata xatonta.

Raxeena kuma dake labe akofa taji komi takoma daki tana sa kuka bashiri takira mamanta tafara sheda Mata duk abindayake faruwa.

Bansan metafada mataba Naga tayi dariya tana fadin

"Tabbas wannan shine mafuta mama.

Sannan ta aje wayar tana Dariya.

Game da Axad Yama rasa nutsuwa kawai yaxari key nadaya daga cikin sabbin motocinsa dayayo odar ,yafuce agidan sucuiritys nabakin kofa ne kadai suka ganesa , baida numbar Janbi amma wanna kasuwa xasu super market ko old kasuwa dai.


_______________
Ah kuxo kuga πŸ˜‚πŸ˜‚ huru Insiyya akasuwar India irin wacce take gani afina finan fassara,ai tun yaushe tafara nishadi tana daukar hotuna domin tanunawa nuwaira idan takoma nageria tunda prince yace xai maidata.,Janbi tabiye Mata sai hotuna sukeyi.
Suna nishadi

Awani shago tahango sari kala kala tacema Janbi tanaso suje

Aikwa suka shiga tunda suka shiga wani saurayi yake kallonta har suka gama siyaryar tashiga wani daki tareda Janbi tanadamata sari din Jane anyi layinin Baki abakinsa ,tayikyau sosai duk da tasa hula tarufe kanta Amma gashin yasauko tagadon bayanta sosai gaban goshin Tama yakwakkwanta,sosai tamkar fa yar can Amma irin 'yan Pakistan din Nan haka tafito tayikyau. Saida kwata kwata daga turanci batajin kowanne yare sai hausarta.

"Aunty Janbi yamin kyau sosai Dan Allah kimin video kamar afilm nikuma xanyi actin sosai fa.

Janbi tayi dariya
"Badamuwa Amma kinsan mAh tace karmu Dade kibari idan muka koma sainamiki sbda canma akwai fili ga gurare masu kyau xaifi.

"Shikenan xantafi daikam dawannan ajikina Naga nayikyau irin afilm din Nan

"Sosai mako kedin kyakkyawace kina masifar kamada jaruma, kajol

Sunje biyan kudi akace ai anbiya xasu wuce saurayin Nan yabisu yanafadin

"Dama xaki daure kisani awannan film din naki Dana baki gudunmawar wani Abu.

Huru takallesa tana kallon Janbi yadage Mata gira

"Hhhh 'yan Mata hadaddiya ,sunana fahad inaxaune new a new step

"Itadin bakuwace mungode dahidimarka

Janvi ta fada tana Kama hannun huru

Huru takallesa taga kamarsa sosai da jarimi Ajey debgan itakuma duk duniya tana masifar yinsa ,hakama tana son Fina finansa.

"Yayi sunanka medadi nikuma beauty sunana,idan akaga video na da hadadden saurayi ba India irinka bakaramin shankai xanba kayi mutkar Yi wlh.

Fahad yashafa sumarsa jin wannan yabo yana fadin

"Muje muyi videon agurin mota ta saina saukeku agida kawai,Kinga daga lokacin kinxama kawata beauty.

Huru tace
"Muna yin sauri ne Amma da dikkan alama kaidin Dan uuwan jarimi Ajey debgan ne ko ? Ai inayinsa sosai kodan shi xamuyi k................ab ab.........

Hango Axad jingine da motar yasa bakin ta yin bam tana raba idanu ,tamakasa cigaba da maganar.

Fahad kuwa yanakallonsa yabar gurin.dasauri Yana wai waye.

Janvi Kam dasauri tanufi motar da aka kawosu huru tabita , Axad yadakamata tsawa, direaba yaja motar yabar gun janvi na tunanin laifin me beauty kuma tayi.

Afurgice ta dawo inda yake jikinta natsuma sari na xamewa tana kwasosa idaninta yaciccika da kwalla iyasaninta babu abundaya hadata da shi toh metayima. Sane. Harhaka yake hura hanci.

Yaja hannunta yacilla amota yashiga yabar gurin me huru xatayi inba kuka, ba, takankame jikinta sosai guri guda dama back sit yajefata,hakan yasa tadan dago kanta tana kallonsa ta glass yadda yahade rannan kamar hadari., Hawaye nacigaba da xuba a idaninta.

Wayartane tafara Kara ,yayimamaki domin baison tana dawayaba kodai dama prince yabata wayane? Kafun yagama tunaninsa yaji tafashe dakuka maicike da shagwaba da munafunci tana magana.

"Dan ALLAH prince kaxo katafi Dani yaukam xaidakeni da alama ransa yabaci sosai bansan menai masaba yake tsanata.

Tacigaba da shashheka
"Nifa Babu abundana Masa kuyimagana dashi

Tadanyi shuru alamun rarrashinta prince din yakeyi.saijan majina takeyi tana fadin
"Tohm Bari nabasa Amma inajin tsoro sosai

Tamikawa Axad wayar tana Dan dari dari

Doke wayar yayi tafada gabansa daidai kafarsa yasa kafar yatake ta tafashe huru takara fasa kuka tana fadin

"Wayata ce fa me wayata tayimaka wlh saina fadawa mAh nibaxan yadda ba , prince NE yabani,kullum MUNAYIN waya yabani hakuri ya lallasheni,meyasa baka kaunata meyasa katsaneni ,do me xaka rinka takura rayuwata nifa banada alakar komi dakai xan...........

Basan lokacin daya saki sityarin motar yajuyo

Yawanke fuskarta dawani shu'umin mari harsaidata tafi hutun wucin gadi dakyar yakama kan sityarin din sbda yakwacemasa yagangara damotar yayi pakin.

Kishi da masifa kecinmasa rai.yaganta dawani tana baje Masa hakora yanxuma kuma tana waya da prince dama sunayi kenan baisani ba saiyau.

Dafe take da kuncinta wasu mahaukatan hawayene ke kwararamata wannan mutumin meyake nufi meyake nufi Dani aikwa yau koxan Bata asaceni 'yan mafiya suncinye namana baxan koma gidansuba nagaji.taballe murfin motar tafuce da axababben gudu tana kuka iyakar iyawarta. Tagaji dakomi gwara tamutu kota huta.

Axad sai lokacin yadawo hayyacinsa,buguwar mufin motar dajikin motar , amilyan yataka motar yabita duk houn din dayake Mata Bata ko juyo ba sai gudu take tika tana kuka xuwa yanxu tasabe sari din ahannu daga ita sairigarta da wando duk gashinta yagame fuskarta sbda kuka har wani duhu duhu take gani,

Shiko ganin baxata tsayaba yafuto yasabeta ehu take tana dukansa Amma Saida ya sata amota,ko ajikinsa tamkar yadauki 'yR tsanar roba shiyama Raina rashin nauyinta.

Dukan glassdin take tana kuka fuskarta tayi kaca kaca da hawaye da majina.

Yadakamata tsawar dasaidata nutsu Kam tahade jikin ta guri daya tana tsuma,

"Karki kuma min haukar kin Nan ,gobe xa amaidake inda kikeso din inkin kuma min kukan kin Nan xanmiki duka wlh kiyi Mai dalili ,

Shuru Bata motsaba yafigi motar bai tsayaba sai agida asashen mAh yafaka tafuce dagudu tana Kara sautin kukan ta mAh ko tunda taga janvi afujajan tasan xa arina ,tariko hurun

"Lafiya menene me yamiki

Raxeena nagefe tana nishadi sbda tagama gasgasata cewa duka yayimata

"Dan Allah amaidani Dubai mAh kitaimakeni yafasa min wayata yamareni yadokini acikina yadoki ni abayana yagwaramin kaina ajikin mota nashiga uku nidai baxan xaunaba .xai kasheni.

Duk abundata fada akunnesa domin yataho shigowa tun kafun mAh takirasa,don yasan xata kirasa din

Bursusuwa take yi akasa rike daciki,koba komai saiyagane ita ma din ta iya sharri,

Mugun kallo mAh kebinsa dashi shikuma Yana sinke Kai,duk da hankalinsa nakan huru,ganin kukan datake yi tamkar maishirin barin duniya. Yana mamakin yadda takulla abota da kuka.

"Duk meyasa hakan Axad wannan shine amanar da abokin ka yabaka.yanxu kakyauta kenan toh kanutsu kajini dakyau wlh kaje kasiyomata wayarta sannan kakira Dr taduba ta kakuma kiyaye harkarta dagayau kafadawa shi prince din amanar tadawo hannuna ,kafuta asabgarta tunda ba mutunci kasani ba

Yasunkui dakai

"mAh karyafa takeyi niban daketa ba kumafa kula maxa Naga tanayi itakuma janvi tabiye Mata sai hauka sukeyi atiti

"Rufe min baki da Allah Ina ruwanka wayace Kama bisu tohm dasauri kakira Dr yaduba min jikinta Inka targadata asani dawuri kargurin yayi Mata tsami.

Jinhaka huru takuma sa kuka tna Dan jujjuya kanta

"Wayyo kaina mAh inagama shine yagoce domin kuwa asama sama nake jinsa

mAh tarikota tana fadin

"Kakira Dr nace Axad kana daukar Abun wasa komi wlh wani Abu yasami beauty saikaga bacin Raina.

Axad haushi yagama kulardashi yakira Dr din nasu xaibar falon mAh tace yakoma yaxauna agabansa xa ayi komi,aishi yajawo koma menene yasameta.

"Hummm. mAh kidaina lallaba ta shiyasa gashinan tana kokarin rabaki da danki

Fadin Raxeena tana tabe Baki
mAh ta ce
"AA ataki fahimtar kenan ,Amma watarana xaki ffahinta de de

"Shikenan dama nasan haka xakice

Dr yayi sallama yashigo yagaida mAh suka gaisada Axad Wanda keta wani daddaure Rai .

Dr yadubatadakyau baiga Rauni ba yasanar ma bakomi naciwo ajikinta,mAh tabashi ixinin tafiya,tana kallon Axad

"Bakin ku daya dashi Amma duba fuskarta shatikan marikan daka xaxxabga mata Kinga Raxeena mikamin ita wani hospital din.

"Basai anje waniba banajin komi mAh

"Allah ma yakyauta yarinya nabata lokacina akanki.

"To ainice nasakaki Raxeena meyasa bakida kunyane ke

"mAh nidin yanxu dama wata xata iya shiga tsaakaninmu bro kagani yadda take kokarin rabamu da mah ko

Ya buga Mata harara tareda daga Mata hannu

Dagudu tabar falon tana kuka mAh tatashi tana taimakawa huru tamike taji wayarta nakuka abedrom

"Kije dakinki kisamu kiyi wanka Bari nadaga wancan Kiran kiwanta kihuta fa xanrama Miki dukanki.

Sannan kaikuma kaje kanemo Mata wayarta kamayar Mata da sim card dinta kabata ,domin bakai kabataba bakada hakki akan ta ,nafadamaka.

Huru tajinjina Kai tana dangasawa tana Kara tattare sari dinta Dan duk wannan badakalar da akasha tana rike da sari dinta.kam.

mAh nabarin falon takara sauri sbda taga yadda yake jifanta da wani irin kallo Shiba hararaba Shiba kallo Normal ba,majority prince taga yanamata irin wannan kallon.

Tashige dakinta xata rufe yadanno yashigo sakin Baki tayi taga yadanna sakata , aikwa tabare Baki xata yi ehu ko mAh xataji takawo dauki.

Yadora hannu abakinsa alumin taimar shuru.aikwa tafara ja baya,baya tana matsar kwalla da mur mur da ido, har yakaraso daf da ita suka dangane da bango.

Yaxin yatabbar dason tafa yakeyi Amma Yana kuma chalanjin din kansa ,duk lokacin daya Sami kusanci da ita yanajinsa cikin kammaluwar jiki da nutsuwar ruhi, yafahimci bakaramin son kukan Nan nata yakeyi ba kamar tafi kyau idan tana kuka. Ma

Ganin xai matseta dabango yasa ta tokare kirjinsa da hannunta bibbiyu,sai lokacin yakalleta ta turo Baki gaba yaja yatsaya tajanye hannuta,tana sunne Kai sbda Abun yaxo Mata bako kirjinsa taji ko motsawa baiba lokacin data tokaresa yakaramata kwarjini,da cika ido awani muryarshi daya gama shiga shauki yamata magana.

"Kinmin sharri na dokeki ko

Ta cono Baki tana turbune Rai tareda wasa da yatsun hannunta

Shikuma yaxuba Mata ido haryanxu ba Dan kwali akanta Amma tatura gashin baya.,bakaramin kyau gareta ba yarinyar fa ,jibanta kawa aljana

Taxaro ido ,saiyanxu yakula afili yayi maganar

Tabar gabansa tana kun kuni xata shige bathroom yadanko hannunta .

" Eh Mana yanxu tunda kinmin karya na daddakeki saikinunamin gurin naduka shikenan bakarya kikayiba

Abunma Dariya yabata aikwa tasa Dariya tana rike ciki tareda janye hannunta sbda shocked din dataji

Shima yaji Amma yafaske duk da yanayin yayimasa dadi

Cikin karfin hali tace Masa.

"Kamar yafa duk xalina dakaci bai ishekaba saika karamin

Please Login or Register in order to submit comment