Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kashekaba domin yakin baixo 'karsheba lallai kashaidama sarauniyarka cewa nida yarana munnufi Damshak damin fatauci intacika sarauniyar tamolikawa tabiyo bayana ta'dau fansar jama,anta damukashee

Yayinda Fatan yagamaba Sarauniya wannan labari saitamaida hankalinta bisa kallon tarin gawawwakin jama,anta dasu Barat sukashe tabbas ranta yabaci fiyeda kima tacika tabatse akarshe takwarara ihu har sau uku sannan taishiruuu natsawon lokaci

Cankuma sai agatakama murmushi tanamurmushi saikuma takama babbaka dariya kaikace tazarene hakan yaba dakarunta mamaki domin basusan menene dalilin dariyantaba saida taidariyar ta,isheta saitadaure fuska tadubi Sadauki fatan tacewani sakon Barat yabaka xuwa gareni Fatan yace cewa yayi shida yaransa Unaix Unaixa Farhan sunnufi Damshak domin fatauci yace inkin isa kibiyoshi domin daukan fansa dakarunki dayakashe miki, taimurmishi tace kena yanxu sarkin yakine yarage abinnin Jumki shikadai domin shima shu,uminnasu Zaffar yanacan yawon duniya sukuma suntafi fatauci saitakyakyace dadariya tace bazamubi bayansuba ammakuma zamushirya babban runduna irin wacce bamutaba shiryawaba zamunufi Jumki lallai saimunyi fatafata da Jumki saimunkashe kowa munkone binnin tayadda idan Barat da yaransa sudawo suga munshafe binnin adoron duniya zasu hadiyi rai sumutu,

Jinhaka sai Sarkin yaki Anxar yace dakyau shugabana tabbas kinyi babban tunani lallai mugaggauta aiwstarda hakan saidai dakwai shawara 'da Zaffar da yarima Ammar datsohom mijinki dakuma 'yarki Tamlika sunatare kuma sunnufi Najran domin haduws da Gimbiya binnin Najran tofa indai har su,isa Najran dakwai matsala yakamata kafinsu isa a,aikamusu dasakon mutuwa, jinhaka sai sarauniya tadubi bokanyanta alira tace gareki hatsabibiya uwarhatsabibai
take bokanya tasabi gunaguni dasambatu saigawani sarkeken aljani yabayyana agabanta yaigaisuwa yanamecewa lafiya Uwar,ifritai menene bukatanki abiya miki yanxunnan Alira tace dakwai wata 'karamar tawaga tanufi Najraran lallai babubukatan su,isa najran kamata yayi suwuce lahiraa aljani Kilaxu yace angama zankawo miki kawunansu kafin ku,isa jumkii sai yabace bata, sarauniya tace kumaxai iya Bokanya tace bakin ifritine yanda runduna metarin yawa babban abinkunyane agareshi yakasa kashe 'dan adam danhaka zaiyi iyayinsa domin shafe Zaffar datawagansa aduniiya ,jinhaka sai Sarkin yaki yacedasarauniya to yazaiyida 'yarki Tamlika datake taredasuu

Dakakkausan murya sarauniya tace adomin inceci Mutuncin 'kasata zan,iya sadaukaddarayuwata towacece kuma 'yata indai zamusamu nasara to ahada da,ita damanasani tunda sukahaduda mahaifinta tarabu damukenan

Tuni sarauniyar Tamolika molika loxar tashirya runduna medaukeda sadaukan fama miliyan Hamsin sunufi Jumki daniyar shafeta aduniyaa, to ayayin tafiyarsune Sarauniya molika tadubi bokanyanta alira tace Zaffar yama yariman daji ammar damahaifiyarsa alkawarin karbo musu Sadauki Haiman daga hannun Sarki Dusar yayalamarin yakasance

Bokanya taimurmushi kuma tai ajiyar zuciya tace aibabban labarine kuma masiface ta auku wanda jintama babu dadi domin anci rayukan yammaza anxubda jini tamkar ambaliyan teku tadubi sarauniya tace tabbas koda ace sadauki Zaffar mutunne tofa shaidanine acikin mutane kuma annobane daga annobar duniya narantse shi saukakkiyar masiface daga ubangijin sama Afusace sarauniya tadakamata tsawa tace labarin abinda yafaru nace kibamu bawai kiyabi makiyina agabanabaa Bokanya tace kigafarceni shugabana ga yadda al,amarin yafaruuuu

Todomin yadda yafaru saikujirani kuma abiyoni da Comen akalla arba,in , inko yagaza haka labarinku bazaixo dawuriba ,

Inamika Godiya gawadanda sutoromin da data wasukuma sunturamin kudii nagode Allah yabar zumunci tabbas najidadi tomin kanema abaka shine soyayya NGD ABOKAINARUFDUGHUU
047
,,,,,
Bokayan Alira tacigabada cewa raina fansane gareki shugaba Zaffar yayima yariman daji ammar damahaifiyansa alkawari cewa zaije 'kasar Dusaira domin yayaki Sarki Dusar yakarbo Sarkin daji Haiman saboda haka shida sarauniya Zarima da'yar uwansa Juraixa sudauki hanya tunfarko saida yarima ammar yacezaibisu amma sai Zaffar yace aa katsaya kakula damahaifiyarka dasauran mutanenku kawai kajira zandawo maka damahaifinka Haiman
Ahaka surabu sunyitafiya menisa harnatsawon kwanaki shatara batareda yadazango kotsayawa cin abinciba komai atafe sukeyi basawani ishashshen barci hakankuma yahaddasa musu gajiya dadumin jiki danhaka arana ta,ashirin suyada zango atushen watababban bishiyar Mesarda sufuto da abinci suci susharuwa abinkada gajiyayyu kawai saibarci yakwashesu kayya aisaida sukwashe kwana guda da uni sunakwarara barci domin biyan bashi,
Jijjigi yayinda sutashi farkawa saimamaki yakamasu sudai sunsan sunkwantane atushen bishiya amma abinmamaki saisutsinci kansu awani tsukakken 'daki maitsananin matsi 'dakin tamkar babu'kofa saidai wasu 'kananan tagogi guda biyu dagacikin 'dakin sunahango wajee sunfahimci sunatsakiyan wanikaramin kauyene wandagidajen 'kauyen basuwuce duvu ukuba, Zaffar yadubi sarauniya Zarima yace kenan munfada tarkon wasu'kabilu hakan nanufin sunfaraucemune yayinda muke barci tomezasui mana shin'barayine su kokowata mummunan mafutace garesu
Zarima tace koma menene xamugani abinsanine dolene mucika alkawarimmu damudaukama yariman daji ammar

Daidaonanne Zaffar yakama karafen da akafa atsakiya tagan danufin karyasu koma yajijjige tagar bakidaya sufuce. kayyasa tofa ananne sadauki Zaffar yashamamaki domin yakasa koda motsa karafan balle tagar Zarima tadubeshi taimurmushi tace yarona tabbas kaimayakine kuma mafarauci rayukan mazaje amma haryanxu dasauranka ashebakadasanin cewa irinwadannan 'dakuna anaginasune dazallan duwatsu kuma anakwaba ruwan gininne daruwan tsafi mekarfi sannan anatsaface dakin damanyan sirrikan tsafi tayadda koda aljani asashi acikin'daki bazai iyakubutaba jinhaka sai Zaffar yace toyanxu menena mafitarmu, caraf juraixa tace mujira jira xamuyi natabbata wadanda susamu cikin wannan tsinannen 'dakin tosune kawai zasuxo sufuddamu

Juraixa narufe baki saisuji ambusa wani'kaho buuuuu buuuu buuu har sau uku kwatsam saiga wata tawaga daga mutanen wannan'kauyen dakarune arba,in dakuma bayi arba in dakuyangi mata arba,in,
Sunsa wani mummunan saurayi atsakiya saurayin yaiwata mummunan shiga najajayen kaya akansa dakambun sarauta yanarikeda sandar girma tabbas alamu sunnuna cewa shidin yarimansune kaitsaye sunufo inda Su zaffar ketsare sunazuwa wasu dakaru goma subude wata'karamar kofa sujawo Juraixa suiwajeda ita hakanne yasa Zaffar yarika yunkurin cafkota amma tuni suiwajeda ita susake garkame 'kofar basujiraba sutafida ita

Bayan tafiyarsu sai Zaffar yadubi Zarima yace mewadannan tsinannun munanan mutanen kenufi shinmexasuima 'yar uwa narantse dagirman Allah indai sucutarda ita tosainashafe 'kauyennan bakidayansa Zarima tace nimabansan nufinsuba ammakuma dasannu zamusani, tanarufe baki saisuji muryan yariman daji amman yanacewa ninasan abindasuke nufi da,ita saigashi agaban 'dakin,Zaffar yadubi ammar yace kai yaro ya,akai kazonan meyasa kabaro mutanenka kabiyomu

Ammar yaimurmushi yace ainafadamaka wannan yafiyar dole saidani dominni nasan hanya kaikuma bakasaniba nasan duk wata masifa dake gabammu dabayammu danhaka wannan tafiyar dani za,ayita

Zarima tace munji amma wadannan wasu irin kabilune menene shirinsu akammu, ammar yace sunan kabilarsu Yaxur sudin mayune sunacin naman mutun kamar yaddasukecin naman dabba sunashan jinin bil,adama tamkar ruwa sune akema lakabi damafarautan bil,adama tabbas sunkamakune danufin cinyeku kuma yanxu hakan sunahanyasune nakai Juraixa mayankansu domin yankata sannan ananne xasu gasata surarraba namanta gajunansu kowa yaciii

Tabdijam jinhaka Zaffar yakwarma ihu tareda dakama ammar tsawa kaiwawa maza kabudemana'kofarnan don muje muceci rayuwar juraixa ,ammar yaciro wata wukar 'kashi yakama yankan 'karafannan jimkadan yayanke 'karafan Zaffar dajuraixa sufuto Ammar yace kubiyoni yawuce gaba subishi abaya tafiyar dakiku 'dari uku saisufara jiyo hayaniya gamida tashin bushin 'kahooo, ammar yace mukara saurifa domin tabbas sunadabda yanka Juraixa tafiya kadan sukayi sai suhangi ilahirin 'kabilun sunyi da,ira sunkewaye Juraixa wanda adaure hannayenta arufemata fuxka da jankyalle gawani zabgegen dakare yadaga takobi zai yanajiran umurni yadatse kanta, hohoho Zaffar yainufin afkawa caraf ammar yarikeshi yace aa shugabana karkai garaje kasani muddin kafadama mutanennen batareda kasan sirrinsuba tofa bazakai nasara akansuba, Zaffar yace menene sirrin tsinannu ammar yace kakalli makaman dake hannayensu dakyau mekafahimta gamedasu ,namfa zaffar yakurama makaman idanu natsawon lokaci saiyafahimci wani abu ,ammar yace mekafahimta game damakamansu Zaffar yace makamansu tsofaffin kayan yakine irinna mutanen farko babu 'karfe ko azurfa amakamansu nalura mafiyawancin makamannasu sassakakkune daga kaifafan duwatsu saikuma wadannda ayisu dajan itace medafi saiwadanda ayisu damugun zaren tinya meguba tabbas makamannasu nadamutukar hadari domin koyaya suyankeka dashi zaiyi wuya karayu, ammar yace tabbad zancenka haka yakr bayamma haka makamannasu tsofaffine totsafaffune domin babu wani tauri ko tsauri daxai dakatardasuuu indai sukartama yanka kosuda'bama tsini tofa shakka babu saikamutu sannan sumakansu tsafaffune tundaga ranar haihuwansu fomin kamar yadda basa amfanida 'kafee to'karfe baya tasiri akansu

Jinhaka sai Zarima tace totayaya zamugwabxa yaki dasu kenan Zaffar yace tahanyoyi guda ukune kawai zamuinasara akansu Hanya tafarko kada muyarda makaminsu yata'bemu hanya yabiyu dolene mukwaci makamansu domin damakaminsune kawai za,a,iya kashesu sai hanya ta uku mufarmakesu da'karfin dantsee tahanyar yimusu mugun duka gamida karya wuyan tsinannu ,kayyasa adaidai nanne kuma mebusa yabusa 'kahonsa aikawai sai zabgegen 'katonnan yajijjiga takobinsa yadaga sama zaixabgama Juraixa sara adokin wiyaa sukuwa 'kabilun sai ihu dahargowa sukeyi zasuci nama susha jiniii

Jijjigi alokacinne kuma yaro 'danbaiwa ammar yariman daji yajawo baka dakwarinsa yadana wata kibiya wacce asassakata da Jandutsee kurxan kankace haka yatabe bakan ya auna zabgegen katon yasakima tsinanne harbi fiuuu jikakee cassß tacaki 'kirjin 'katonnan kibiyar tahuda kirjin tsinanne tafasashi har baya tafucee abinda jar uba saida dakaren yakwarma ihu ihu merazanarwa sannan yaisama tamkar anharbashi sannan yafado timmm baburaii

Kambala,iii ahaukace tsinannun kabilun suwaigo tareka kwarara ihu ihunda yarikita ilahirin dajin bakidaya wohoho namfa 'kabilun kuxar dubu bakwai sui arbada Zaffar da Ammar dakuma Gimbiya zarimaaa

Kambala,i Sarkin kabilun mesuna Dunxara yakwarara ihu yadubi Zarima yace ketsinanniya lallai kinjangoloma kanko masifa dabala,iii narantseda jinin Gumba dakukashe yanxunnan sainamuku mummunan kisa kuma nikadai zancinye namanku hhhhhhhh Yaro ammar yakama dariya akarshe yadaure fuska yadakama sarki Dunxar tsawa cewa kaiiwawan sarki kasani kuna kujangaloma kanku masifa tundaku hada shirgi da Uban maza Namijin fama jinin sardadd Zaffar bn Hamdan yacigaba dacewa kunada zabin kumutu kokurayu immadai kubamu Juraixa mubarku kurayu kokuma kuiyunkurin kasheta madadin kukasheta saiku kuimutuwan wula'kanci ahannayemmu

Jijjigi Sarki Dunxara yaki kamar Ammar yawatsamasa narkakkiyar dalma tabbas babu wani sadauki imma mutun ko,aljan dayataba fadamusu wadannan miyagun kalamai danhaka yaji cewa kafin afara wannan yakin yakamata yajangolo babbar masifa yaga irin jarumtar yarannan

Kawai sai yaimurmushin mugunta yadubi ilahirin dakarunsa yace dakaru inaso yanxunnan kuma dukammu muhahadu muimai wannan yarinyar Dake gabammu rufdugu lallai sonake tafara mutuwa sainaga irin fushin 'yan uwanta mukuma asannanne zamununa musu iyakansu

Tabdijammm atare kuma alokaci guda dakaru dubu bakwai sukewaye Juraiza kaman abusamusu usur sudaga takubbansu atare danufin yima Juraixa Rufduguuu, kaikai tabbas tunda zaffar yake aduniya baitaba sallamawa dacewa yarasa wani nashiba kamar wannan rana domin babu abinda xai iya domin ceton rayuwan juraixa sabodahaka hannayensa biyu yadora akai yakwarara ihu yanakiran sunantaaaa JURAIXAAAAAAA

Tofa waimexaifaruneee kubiyoni daruwan Comen dominjin Bala,in dazai wakana ,shin juraixa tamutune kotarayo ohooooRUFDUHUU
048
CIGABAN
LITTAFIN
WANKAN-WUTAA
TurkashiRUFDUHUU
048
CIGABAN
LITTAFIN
WANKAN-WUTAA
Turkashi kalaman yaro ammar sunfusata Sarki Dunxara yakwarara ihu taredaba dakarunsa dubu goma umurnin suima Juraiza rufdugu kaikaikai ai,atare kuma lokaci guda azzaluman dakarun masu kamada saci babu sukwarara ihu suikan Juraiza wacce take'dure tamau gurfane abisa guiwowinta tabdijam Sadauki Zaffar da sarauniya Zarima sunyi mutukar kaduwa kuma suntsorata ainun domin sunrigada sunsallama cewa Juraixa tamutu domin babu abinda xasu,iya,

Itakanta Juraixa tariga tamikawuya tasaduda tatabbatarda cewa yauce ranan mutuwanta Hmm 'kiriss yarage dakarun su,isa kanta baifi saura taku bakwai zuwa gomaba kwatsam dakarun yarima ammar mazauna daji kimanin dubu uku subayyana akowace 'kusurwa gabas da yamma kudu da arewa kowannensu na'daukeda bakadakwari yadana kibiyar da asassakata dajan dutse kana tanacida wutaa

Batareda 'bata lokaciba dakarun yarima ammar sufara aika sakon mutuwa atare suke sakin harbi kuma atare suke'danawa ,wayyo namfa surika shimfi'darda makiya surikama 'yammaza kisan gilla kankace haka sunkashe mazaje fiyeda dubu shida tilass ragowan sujada baya domin duk sanda suiwani taku danufin cimma juraixa to mutuwace kemusu maraba
Hohoho Ran Sarki Dunxara ya'baci yakwarara ihu yazagi rana yazagi wata kana yadubi yaro ammar yace kai yaro kasani katada yaki kuma kakunno wutar fitinar dababu me,iya kasheta sai ubangiji yakaurara maganansa dacewa narantse da abar bautana Gumba yau saina hallakaku dukkanku kuma sainaji dajin Isran domin kashe mahaifiyarka daduk wanda ketareda ita, Cikin ixxa yaro ammar yataka takun 'kasaita yaje yakunce Juraixa yakama hannunta yajata hargaban Zaffar yacedashi shugabana ga'yar uwanka tadawo gareka ,sai yawaiga yadubi sarki Dunxar yace kaiwawan sarki kasani Ni mutumin dajine adaji ahaifeni kuma adaji nagirma nasan duk wani sirrina daji danhaka abune mewahala akaina ballema inatareda babban jarumi Zaffar da mamarsa sarauniya Zarima lallai zaifimaka kyau kaida dakarunka kukauce ahanyarmu muddin kunada burin cigaba darayuwa awannan duniyaa

Tabdijam jinhaka sai Sarki Dunxara yasake kwantsama ihu kana yadaga hannayesa sama yanakiran wasu sunaye marasa kan gado

Jijjigi aiyana rufe baki saiga wasu markadamarkadan dakaru suhudu sunbayyana agaban sarki Dunxar dakarun sunada mutukan girma datsayi damuni tamkar dodanni kaida ganinsu kasan masiface daga cikin masifun duniya dakarun hudu baburiguna ajikinsu domimma babu wata riga dazatai daidai dasuransu sunarikene dawasu makamakan takubba wanda tsayinta yakai tsayin wata bishiyar fadi kuwa ba,amagana sannan suna goyeda wani mahaukacin gatari wanda girman gatarin yakai girman bil,adama dakarun hudu sutsaya agaban sarki Dunxar sunawani huci gamida cika sunabatsewa cikin kakkausan murya suce Ran sarki Dunxara yadade shin wace masiface tasa atasomu tabbas kowanene yatabaka zaigummace mutuwa darayuwa cikin fushi Sarki Dunzar yace wasutsinannun hatsabibaine su addabeni nida jama,ata harma sunhallakamun dakaru samada dubu biyar danhaka nakeneman agajinku sonake kukamasu dahannayenku kugasasu daransu muci namansu nidaku

Jinhaka sai dargazadargazan dakarunnan suiwani gunji kana sujuya sufuskanci Su Zaffar sunacika sunabatsewa kamar zasu fashe

Zaffar yadubi yariman daji yace yaro wannan kuma wace masifance suwanene wadannan samudawan, yaro Ammar yace kiwatattun tsafaffun dakarune raguwane daga jinsin Samudawa arainesune tamkar yadda akerenon dabba mecin naman mutane anciyardasu naman bil,adama dana aljan kuma basuda wani abunsha face jini akoda yaushe namane abincinsu ankoyardasu farauta irinna mahaukacin zaki wanda koda akoshe yake inyaga mutun kodabba sai yafarauceta yakashe koda bazaiciba yaro ya'karisa maganarsa dacewa tabbas karo dawadannan dakaru hudu tamkar karawane dadakaru dubu 'dari huduu
Zarima takalli yaro ammar tace kenan kananufin kowani'daya daidai yakeda dakaru dubu'dari Ammar yace kwaraikuwa lallai daga dakaru dari saidai suxarce haka ,jinhaka sai Jiraixa tace lallai dakwai aiki agabammu amma zamu jarrabasu kuma zamununa musu mu jinin sardaddnee jinin Mutuwa

Alokacinne Zaffar yafara magans dakakksusan murya cewa shikenann zance ya'kare kowannemmu yafuskanci daya domin gwabxawa wohoho atare suxare takubba sukalli juna kana suiduba ixuwaga dakarunnan hudu kamar anhura 'kahon farawa

Kambala,ii dakarunnan sukwarara ihu suikan su Zaffar sunaguji dagurnani kaikace zautattun xakunane

Suma Su Zaffar sumotsa suikansu domin bambance tsakanin matattu darayayyu

Kayyasa akaiwani irin haduwa atsakiya metaken Karo dakarooo jikakee kassa kakass 'karan haduwan takubba saidai ahaduwan farko takubban su zaffar sukarerayee

Cikin zazzafan zafinnama dakare mesuna Guramm yakaima Zaffar wawan sara danufin rabashi gida biyu kayyasa wani aiki saigwani Zaffar yaibaya takobin Guram takarci wata shirmemiyar bishiya jijjigi yass takille bishiyan tafadi shirimm ,kambala,ii nanne zaffar yatabbatar borin yagirma baigama nazarinsaba Dakaren yasake kawomasa sara Zaffar yasake kaucewa awannan karon kaifin takobin yasaukane akan wani makeken dutsee kuma take dutsen yarabe gidabiyu tabdijam Zaffar nayunkurin kai sara aisaiji wawan naushi akirjinsa take yaji dum yaji kamar yamutu domin saidanumfashinsa yatsaya cik wayyo kafin zaffar yafarfado daga 'kanin mutuwan dayayi Mahaukacin dakarennan yasake kawomasa wawan sara jijjigi Iskan tahowan takobin itace tadawoda Zaffar duniya, Yayinda Zaffar yakyalla idonsa yaga tahowan sarannan saiyaiwani yunkuri yakauce takobin tasari iska afusace Zaffar yakutsa yashiga 'karkashin 'katonnan yacakumeshi yajijjigashi tareda rafka kabbara hohoho to anannr kows yasha mamaki domin saida Sadaukin maza Zaffar yaisamada dakaren yanunama sama sannan yakwantarashi da'kasa jijjigi dakarennan yadaku domin saida yakwantsama ihu yai yunkurin mikewa amma ina 'kugunshi yakaryaa bsbu abindaxai iya amfanawa Zaffar yatsaya agaban dakaren yanamasa murmushin mugunta tsananin takaici yakama dakaren kawai sai yakama kansa yamurde nantake yakashe kansaaa,,to amma al amarin Yarima ammar da dakarensa mesuna Kulkiiz sundauki lokaci suna alambaku domin shidai ammar yasan bayada wani 'karfi dazai iya karawa dawannan dakare sabodahaka yakura aransa bazaita'ba yarda suhada 'kashi dashiba sabodahaka yarika zille masa gamida kauciya har saida yawahalarda dakaren tayadda daksnsa yaja yatsaya yansmamakin shaidancin Ammar

Koda ammar yagane dakaren yagaji sai yaja yatsaya yafuskanci dakaren sukai idobiyu ammar yaima dakaren dariyar mugunta Ran dakarennan ya'baci yajikamar yaiwani yunkuri yadamki Ammar saidai yasan ko yajarraba abanxa yaron bazai kamuba zilliyanedashi kamar biriii alokacinne Ammar yazaro wani jangarin magani yazuba atafin hannunsa yabusama dakaren jan garin maganin yatashi sama yaje yasauka ajikin dakaren kambun ubannan aisai aga dakaren yakama susa yanakwarma ihu take jikinsa yafara fudda wasu maka makan kurajee kurajen surika girma sunskumbura hakashima dakaren yarika girma yanakumbura tamkar anasamasa iska jimkadan sai dakaren yatarwatse jikake darammm yafashe namansa yai'daidai

Tofa itakuwa Juraixa sunsha fama dadakarenta mesuna Zumzan sungogo yaki metaken mutu karaba tabbas dakaren yafi karfinta saugoma ammakuma tanunamasa naci irinna dakaru 'dari yaimata moyagun raunuka itakuma tafasa masa ido 'daya 'karshe tawafce takobinsa tashekamasa sara a'kafarsa nadama yass tayanke 'kafar tsinanne jikakke shirim dakaren yafadi tamkar giwa ayayin faduwansa tadaka tsalle tahaye 'kirjinsa taburmama tsinanne tsine akirji tshudashi har baya,

Kayyasa amma al,amari sarauniya Zarima danata dakaren sunkafsa 'kazamin yaki duk dacewa dakaren ysninnkata akarfi tofa tsnunamasa naci damben kuturu sunyi kare jini biri jini tayadda saida suxubda makamansu sukama dambe tabbas Zarima tadaku tasharuwan naushi suba,adadi bakidaya dakaren yakumburamata jiki daduka a'karshe yakwamusheta yadamketa yadagata sama yamannata dakirjinsa yamatse burinshi 'dayane yafasata namfa Zarima taji masifa tarika kwarma ihu saboda masifa tabbas zarima taci azaba takusa mutuwa akirjin dakaren ,wayyo yayinda tafuddarai darayuwa yayinda tafara ganin manxannin mutuwa saitatuna wani ishara damasoyinda sadauki Barat yaimata awani 'kazamin yaki dasukaf da 'kabilun abasawa awannan yakin saida akashe dakarunsu gaba'daya saiyarage daga Barat sai Zarima gakuma dandaxon tarin makiya samada dubu hamsin tabbas awannan rana zarima tafuddarai darayuwa amma sai Barat yadubeta yace yake abinkauna kisani shi yaki ba,amika wuya har sai anumfashin 'karshee danhaka koda kinjiki ahannun makiyi yashakeki yamukureki yana'dandana muki 'kamshin mutuwa tokarki sallamamasa rayuwanki kawai kinatsu kiduba sassan jikinsa tayu kisamu wani wurin kamawa koduka todazaran kinsamu kirkiyi dawasa kifarmakeshi farmaki metaken Mutu karaba

Hohoho adaidai nanne Zarima tadawo daga tunaninta tafara laluben gurin kamawa wayyo cara Fallelen kunnin dakaren yaxkan idanunta gashikuma asaitin bakinta aituni tawasa hakwaranta taiwuf takama kunnin tsinanne tagantsara masa cixo iya 'karfinta har saida jjin yacika bakinta Wayyo dakaren yaji masifa yaji kamar bakin kumurcine yacijeshi yakwarma ihu taredayin jifa da zarima taisama amma saita dire kamar wata damusa

Jijjigi dakaren yatunkareta afusace itama tadaki 'kasa dahannunta tanufi dakaren babu tsoro balle fargabaa

Mezaifarune wanene zaifadi wanene xaiyi nasara kubiyoni da ruwan Comen nikuma xambaku labariin yadda akayi
RUFDHUGUUU
O49%
Turkashi indakasan damusa haka Zarima tadire akasa taima dakarennan wani irinkallo metaken kanadab damutuwa, shiko dakaren ransane yabaci yakwarma ihu yafuta aguje yatunaki Zatima danufin sallamata yanariskanta yakaimata wawan sara daxumman rabata gidabiyu ,hohoho Zarima tazame shikuma yasari iska kafin yasake wani yunkuri taxagashi tafige wata kakkaifan wuka datake ma'kale akugunsa jikake cuss tasokamar tsini akui'bin cikinsa dakare yakwarma ihu tareda sakin takobinsa jijjigi aikafin yarufe baki Sarauniya Zarima tasokamasa tsini samada bakwai asassan jikinsa taimasa jinajina yakama watangaririya a'karshe yafadi kasa matacce

Faruwan hakanne yatsorata jama,an Sarki Darxan domin a,iya saninsu duk masifar datasha 'karfinsu indai sugayyato shaidaninnan hudu to zance ya'kare tokuma yaugashi antashesu a,aiki tabbas rana ta'baci hakankuma nanuni dacewa lokaci yayida zasusauya jagoransu dama tsarinsu kenan aduk lokacinda shugaba yakasa basu kariya to dolene yabar karagarsa kaiba,iya karagarsaba tilassne yabar yakinnan koma yabar duniyan baki'daya , Sarki Darzan yasan abinda mutanensa ketunani tabbas sunashirin yimasa tawayene danhaka sai yazaro kakkaifan wukansa yadora awuyansa zaijaaa

A,aa Zaffar yadakamasa tsawa tareda dakatardashi abin yaba sarki Darxan mamaki komai yasa yaronnan keson dakatardashi danhaka yadubi Zaffar yacekaimeyi damuwanka innakashe kaina al,hali dafari ninayi shirin kashekune nakasa
Zaffar yace nasani to amma nibanabukatan mutuwarka hasalima duk jama,arka danakashe tonakashesune bisa tilas domin inban kashesuba su zasu kasheni ,ammani sonake kaida jama,anka kucanxa rayuwanku tunda kufa asalin mutanene ba,aljannuba meyasa bazaku daina cinnaman mutaneba kudaina shanjini kukoma cinnaman dabbobi kusha ruwa kusha madara hakan zaifimuku wannan'kaxamar rayuwannaku
Sarki Darxan yakalli Zaffar yace kaico yaro kasani munarayuwane bisa ikon wata shu,umar aljana kuma mayya itace abinbautammu damugada daga kakannin kakannimmu bamada ikon sabamata dole mutafi bisa tsarinta kokuma taimana mugunyar azaban dajukkunammu bazasu iya'dsukaba ,cikin mamaki Zaffar yace to amma tunfarko meyasa kakanninku suxabeta amatsayin abar bautansu gashi batatausamuku tajefaku amasifa kunarayuwa irinta dabbobi masucinnamatane hakan badaidaibane

Sarki Darzan yace yazamemusu dolene yakai babban jarumi yaimurmushi yace kafin mutuwata zambaka tarihin 'kabilarmu yacigaba dacewa
Asalin Sunan 'kabilarmu yamama kakannimmu 'yan asalin kasar Misrane sudin karamar kabilace amisra sunkasance kabilace meson xaman lafiya gatsantseni suntsani cuta komugunta domin muddin susan kai macucine ko azzalumi tobazasu taba hada sabga dakaiba kodakai'dan kabilarsuce hakan yasa kowa acikin kabilar yaxamo mutumin kirki domin kiyaye mutuncinsa hakanne kuma yasa 'kabilun yamama suharamtama kansu auro 'yarwata kabilar kuma basubada auren 'yayansu mata aure ga kowace kabilaba,
Gashi kuma sunada kyawawan 'yammata towannan tsari nakakannimmu shine yajawo musu mugun bakinjini ilahirin mutanen misra sutsanesu har anemi adaina mu,amaladasu, hakan yatakura kabilun nayamama danhaka suka shirya hijira cikin duhun dare subar binnin misra sushiga daji basusan inazasuba suitatafiya har gari yawaye sai susami guri siyada zango domin ahuta aci abinci acigaba dstafiya
Kayya to amma akasar misra kuwa koda awayi gari ba,agansuba sai asanarda sarkin misra mesuna Adnan cewa 'kabilun yammama sunbi duhun dare subar gari hankalinsa yatashi domin aduniya inda abinda kowani sarki yatsana shine yarasa wani yanki na jama,arsa gashi yawan kabilun na yammama zasukai dubu bakwai xuwa takwass

Sarki adnan yatambaya shin me aimasu sunargari acemasa babu komai kawaidai watamummunan mafitane azukatansu shi yasa subargari babu sallama jinhaka sai sarki adnan yakasa samunnatsuwa yarika nanatawa azuciyarsa cewa mehakan kenufi shin 'kabilun yamama sunbar binnin misra har abadane koko watarana zasudawo kai sai yawaiwayi bokansa mesuna Duxara cewa yabincika masa lamarin 'kabilunnan yanaso yasan menene shirinsu

Kaico tabbas makiyi masifane to ashe shi boka Duxara babu jituwa tsakaninsa da'kabilun yamama domin yanemi auran 'yarsu sunhanashi hakan yatabamasa kimarsa kuma yakudiri aniyar fansa akansu aduk lokacinda dama tazo masa,
Tofa koda sarki yasashi binkice akansu sai yashare'kasa yakama surkulle gamida tsatsuba kwatsam yatsala ihu gamida rura ihu yadubi sarki Adnan yace kaico tabbas 'kabilunnan sunashirin cin amanarka domin sunsami sakone daga babban malaminsu cewa Suyi hijira zuwa dajin Sauzara acanne xa,a,aifi wata hatsabibiyar yarinya acikinsu wai itace zatakarbi mulkin misra kuma tabbas mafarkinsu xai,iya tabbata muddin ba,adau mataki akansuba

Jijjigi yayinda sarki adnan yaji xancan boka sai yatsaga ihu yadubi boka yaceme yakamata miyi yanxu boka yace indai kanason zuriyarka tacigaba darayuwa cikin jindadi dawalwala tofa dolene kashirya babban tawaga katurata tabibayan 'kabilun yamama su yakesu sukashesu bakidaya
Sarki yaina,am dashawaran bokansa yashirya tawagan mayaka na mazaje dubu saba,in yaturasu abinka datafiyar 'kasa aicikin uni guda dakarun sarki Adnan sucimma Kabilun yamama surutsasu sufara yimusu kisan gilla ,to awannan lokacin shugaban kabilun mesuna Zaruba tainasaran guduwa tafantsama daji tanakuka kwatsam tariski wani'katon shuri agabanta gawata zabgegiyar macijiya takewaye shurin girman macijiyan yawuce misali ,ai Zaruba naganin maciyar tasancewa shu,umace danhaka tazube agaban macijiyar tanacewa yakewannan maciya kitaimakeni kiceci mutanena daga halaka namiki alkawarin zamu bauta miki iyatsawon rayuwammu , abinka dashaidaniya koda maciyarnan taji cewa zasubauta mata saikawai taigirgiza wasu fukafukai sufoto ajikinta fuuu tatashi sama bataxame ko,inaba saigunda akecutarda yamamawa bajira macijiyar ta afkama dakarun sarki adnan tarika yimusu feshin wuta tana'konesu cikin rabin sa,a tahallakasu duka nanfa kabilun yamama sutaru aguri guda suxurama macijiyannan idanu sunamamakin meyasa taceci rayuwsnsu

kwatsam maciyar taxagayesu tasasu atsakiya sannan tairimi asama tafuskancesu tacedasu kaikusani nacecekune bisa sharadin shugabanku cewa xakubauta mini danha daga yau kunxamo bayin uwar macixai

Tofa tundaga wannan rana 'kabilun yamama sufada 'kangin bautar uwarmacixai itace kesarrafasu yadda taso itace tamaidasu suba mutaneba suba dabbobiba kuma basada ikon sa'bamata hakanne yasa abin yazama jikinsu sugada kaka dakakanni harma cinnaman mutun yazamo abin alfaharinsu daidai nanne sarki Duxara yadubi Zaffar yace tokaji labarimmu danhaka banada wani xabi dayafi kashe kaina sukuma zasu sake sabon shugaba sucigabada rayuwan salama

Zaffar yace aa lallai kanada wani zabin lallai yakamata karayu kuma yakamata kaida jama,aka kucanxa kukoma asalinku na mutane badabbobiba

Jinhaka sai Sarki Darxan yakwarma ihu yadubi zaffar yace aa yaro kasani muddin muiyunkurin sauyawa to mutuwa zamuyi dukammu kasani Wannan macijiya tawuce tunaninka takuma zarce saninka inamebaka shawara dacewa kadashiga wannan shirgin domin jarumtarka batakai hakaba jinhaka Zaffar yaimurmushi yadubi sarki Dazan yace kadakadamu dani kasani babana yafadamin cewa ni albarkane ga mutanen duniya kuma nima na yarda domin tun inakaramin yaro nake ceton mutane daga azzaluman mutane da aljannu nayi gwsgwarmaya awannan duniyan nakara da mutun kuma nakara da aljan haka nagwabxa da iblisai danhaka itama 'dayane dagacikinsu kuma zanga bayanta dayardan Allah

Zaffar yajuya yadubi tarin kabilun yace asalinku tushenku mutanen kirkine amma kunfada hannun azzaluma tacutardaku shin kunasan komawa asalinku atare suka amsa tabbas munasan komawa asalinmmu munaso muxamo cikakkun mutane muyi rayuwa mekyau munaso mubar wannan dajii mushiga cikin mutanee

Jinhaka sai Zaffar yace to inhakane kufurta abinda nafurta nikuma zammedaku asalinku kai narantse da ubangijinda raina kehannunsa sainamaidaku binnin misra domin kurayu amahaifanku ta asali,

Wayyo dadiii ilahiri 'kabilun yamama basudawani mafarki aduniya face sugansu abinnin misraa

Danhaka Zaffar yafurta kalimatushshahada suma subiyaa wayyo faruwan hakan kedawuya sai asaki wani wawan tsawa gamida walkiya take sama tarikide takoma Bakinkirin duhu yamamaye ko,ina hababu me,iya ganin waniiii

Tofa mexaifaru kubiyoni datarin Comen dominjin mekeshirin faruwane
Shin Zaffar zaicika musu alkawarinsu toyaya alkawarindake tsakaninsa da yariman daji ammar, ina labarin sarauniyar Tamolika datashirya 'kasaitacciyar runduna tanufi Kasar Jumki domin shafeta adoron duniya ,ina labarin Barat Farhan unaix da unaixa wanda sukekan hanyarsu naxuwa Darshan

Please Login or Register in order to submit comment