Join Our WhatsApp Group

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

Login Register

dan ta iya girki sosai.

Yana kallon Hajna ta shiga kitchen ta zubo abinci, bata ƙaraso kitchen ba, sai ma tsayawa da tayi ta ci abincin a dinning area, tashi yayi ya ce “ni zan wuce, kice wa Aunty Farwa zan yi kewar ta ", be jira me zata ce ba ya wuce ita kuma bata damu ba dan ba magana zata mishi ba.

   Abinci ta ci, sannan ta tashi ta shiga ciki, gado ta bi dan yau weekend, ba ta jima ba barci ya sake ɗaukar ta, dan Aunty Farwa ta saba musu da yin barci bayan an gama aiki, wai yana rage damuwa da gajiya.

   Da addu'a a bakinta ta tashi lokacin ƙarfe 12:50, dai-dai lokacin sautin kiran sallah ya daki kunnenta, saukowa tayi daga kan gadon, toilet ta shiga ta ɗauro arwala, sannan ta zo ta tada sallah, ta ɗauki lokaci a gurin tana roƙon ubangiji madaukakin sarki, ni kaina zan iya ganin na dama a idon Hajna,dan ba ƙaramar na dama tayi ba.

   *************************'*********
A ɓangaren Qaseem kuwa yana gurin aiki wayar shi ta shiga ƙara, kamar ba zai ɗauka ba, can kuma sai ya ɗauka, “hello" mutumin da ke ɗayan ɓangaren ya faɗa, Qaseem ya ce “hello wanene kai",   mutumin ya ce “kana magana da inspector Bala, an kama matarka da laifin, aje karuwai a wani gida, da ake kira gidan ƴanci, sannan an kamata da laifin safara miyagun magani, tare da laifin ta'addanci idan ka na kusa ka matso, muna nan police station ta gwagwalada da ke garin Abuja, an bamu damar kamata ne daga head quater ta ƴan sanda da me garin Sokoto, kiyi gaggawa, dan yanzu za'a wuce da ita Sokoto ", Qaseem ya ce “ku je da ita, a mata duk hukuncin da ya dace, sannan ka faɗa mata na sake ta, saki ɗaya, saki biyu saki uku, na datse duk wata alaƙa da ke tsanin mu ta ma'aurata" ya faɗa yana kashe waya, duk maganar da yayi a kunnen Meenat, anƙwa aka saka mata, tana ta ɗura ashar, sai surutu take “wallahi Qaseem sai ka gane da ni kayi, ni zaka saka, to wallahi sai na yi ajalinka " take faɗa, ƴan sanda sai tura ta suke tana masifa, “idan kuna ganin zaku iya maganina to muje zuwa", wata daga cikin ƴan sandan ta watsa mata sanda a baya, sai da ta gantsara, sannan ta ce “Allah ya saka min, shiyasa na tsani mata, dan mace bata kishin mace" Meenat ta faɗa.

NI KUWA NASA NAJA ALQALAMINA NAYI GEFE, INA MAMAKIN HALI IRIN NA MEENAT.

Anan zan dasa aya...................✍️

Haɗin guiwar :Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya

ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️♻️♻️♻️♻️♻️
[8/17, 09:59] Queen Nasmah✍️: ♻️HAJNA♻️♻️

Mallakin :Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya

https://www.wattpad.com/user/QUEENNASMERH08?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
PAGE 71-72
*********************
Bayan aunty ta fito ne Hajna take faɗa mata saƙon da Farween ya bar mata na cewa shi ya wuce, murmushi Aunty Farwa tayi tace “ai shi kullum haka yake, ko dai yayi zuwan ba zata, ko kuma ya tafi ba sallama, shi baya taɓa canzawa", murmushi Hajna tayi tace “kina fama da shi kam ", Aunty Farwa tace “a'a ni bana fama, dan idan ya ishe ni kora shi zanyi, ki ce da matar shi zata yi fama", wani rassss ta ji gabanta ya faɗi, Aunty Farwa tace “minene naga kamar kin yi shiru, ɗazu Farween ya faɗa miki wani abu? ", girgiza kai tayi alamar a'a, Aunty Farwa tace “to yayi kyau, kar ki damu kin ji ki saki jikinki, kuma Farween ba jimawa zai yi ba zai dawo" da sauri ta ɗaga tana kallon aunty Farwa, a ranta tace miyasa zata faɗa min, Aunty Farwa a ranta kuwa tunanin take yi Hajna tana kewar Farween ne, Aunty Farwa tace “tashi maza ki je kiyi shirin Islamiya an kusa, kuma ki cewa Aisha ina kiranta ", Hajna tace “aunty Farwa wacece Aisha kuma, ɗazu naji kuna maganarta da Ƙaninki", murmushi Aunty Farwa tayi tace “Elizabeth ita ce Aisha ", da tambaya take bin ta da kallo, Aunty Farwa tace “mun dawo cikin addinin musulunci", murmushi Hajna tayi dan sosai taji daɗin haka, “ohk to yayi "ta faɗa tana wucewa.

Ɗakin Aisha ta nufa, zaune take kan sallaya tana duba wasu littafai na musulunci, Hajna ta nufi inda take, dafa ta tayi, ɗagowa tayi idonta duk sunyi ja, alamar kuka, har yanzu hawaye basu daina bin kuncinta ba, Hajna tace “minene ya same ki ", “nayi kuskuren barin addinina, ina fatan yanzu dana gano kuskure na ubangiji ya yafe min", Hajna tace “to yanzu da kika tuba ba sai kin yi kuka ba, dan ke yanzu kuka ba naki bane, baki cancanci kuka ba, wanda yake cikin kuskure shi ya kamata yayi kuka, ke da kika gane kuskurenki ki gode ma Allah dan yana sonki da rahamarsa, ki cigaba da istigifari, Allah kareemun Raheem ne, kuma gafurur raheem, zai zama me gafara a ko yaushe, mutuƙar lokacin da kika yi tubar wuri be ƙure miki ba ", shiru Aisha tayi dan ba abunda Hajna ta faɗa da ba gaskiya ba, murmushi Aisha tayi wanda ya taho tare da wasu hawaye, hannu Hajna ta saka ta share mata hawayen, “ki daina kuka, kuma ki tashi ki tafi Mommy na kiranki, Allah ya yafe mana baki ɗaya", “ameen "Aisha ta faɗa sannan ta nufi toilet dan wanke fuskar ta.

   A parlor ta sami Mommy, gaida ita tayi, sannan ta amsa, Aisha tace “mommy gani, Aunty Hajna tace kina kira na", Aunty Farwa tace “eh dama zance ki shirya ki bi Hajna ku je islamiya, nayi magana da malaman ", sosai Aisha taji daɗi tace “to shikenan nagode sosai Mommy" tashi tayi ta koma ciki, hijab ta saka sannan ta fito, Parlor ta sami Hajna na jiran ta dan haka basu wani tsaya ba suka wuce makaranta.

A ɓangaren Meenat kuwa ta daku iya duka, dan tayi jina-jina, jini sai bi yake ta ko ina, gashi an kamata da laifin zina tana da aure, yau za'a jefe ta, dan haka aka tara yara da almajirai, Qaseem kuwa da aka kira shi cewa yayi ba sai ya zo ba, Allah ya gafarta mata, rame ake haƙawa dai-dai tsayinta, bayan an gama ne aka saka ta ciki, sannan aka rufe da ƙasa kanta ne kawai a waje, dai-dai lokacin da aka bada a jefe ta kawai ake jira sai kallon agogo mutane ke yi, ƙarfe 12:00 dai-dai har ta yi, kowa ya fara ɗibar duwatsu, “Allahu ahkbar "suke faɗa suna jifar ta, jin saukar duwatsu kake yi kawai, rass!, ƙum!, ga muryoyi nan ana ta kabbara har aka jefe ta, kanta naga ya langashe alamar ba rai a jikinta.

     A ɓangaren Farween kuwa, yana isa Kwara, direct masaukin baƙi ya nufa, wato hotel, akwatin kayanshi ya ɗauka yasa a cikin drawer, sannan ya shiga toilet yayi wanka, wasu kayan ya saka sannan yayi sallar ish'a, dan ya riga yayi sallar shi a hanya, tashi yayi bayan ya idar da sallah, kan gado ya hau tare da rufe idonshi, be ɗauki lokaci ba barci yayi awon gaba da shi dan sosai yake jin gajiya a jikinshi.

Manage plssss😪😪😪
Ina fama da aiki ga assignment.

Taku ce Queen da kanta.

Haɗin guiwar: Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya

ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️✍️
[8/17, 09:59] Queen Nasmah✍️: ♻️HAJNA ♻️♻️

Mallakin :Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya

https://www.wattpad.com/user/QUEENNASMERH08?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
PAGE 73-74
***********************
  Tunda Farween ya tafi be dawo ba, yau ya ɗauki wata ɗaya kenan, aiki sosai ya riƙe shi a kwara, yau ya ke ta shirin barin Kwara zuwa Lagos, dan haka ya gama haɗa kayanshi dan hutun da ya samu duka a gidan Aunty Farwa ya ke yin shi.

    Cikin booth ya saka kayan sannan ya shiga, tafiya ce ta yini ɗaya, dan haka ya tanadi duk abunda zai buƙata a hanya.

  A ɓangaren su Aunty Farwa kuwa yau farinciki sosai su ke yi, har Hajna da yanzu su ka fara sabawa, dan duk ya kira aunty Farwa zai gaisa da kowa, kuma ƙa'idace sai yayi awa ɗaya yana magana da mutum ɗaya, Farween mutum ne me son fira, ga mutunci, kyakkyawa ne ajin farko, dan bama za ki haɗa kyan Farween da na Qaseem ba, Farween is extra ordinary handsome, shirye-shirye kawai ake yi, Hajna ke baking snacks, yanzu ta gama baking cup cakes, yanzu meat pie ta ke baking.

  Ba su gama aiki ba sai bayan Magrib, dan haka suna gamawa suka wuce ɗaki domin yin sallah, toilet Hajna ta shiga, wanka tayi dan duk zafin kitchen ya ishe ta, arwala tayi sannan ta fito, wata doguwar riga ta saka hijab pink ya mata kyau, sallah tayi, tana cikin addu'a ta ji horn ɗin mota, haka nan kuma sai ta tsinci kanta da faɗuwar gaba, ita bata san miyasa ba ko magana Farween ya mata sai ta ji gabanta na faɗuwa, addu'a ta samu ta kammala, sannan ta fito dan basu jera abinci a parlor ba, su na kan dinning, sun aje.

    “Hello my loves, na shigo fa "Farween ya faɗa da ƙarfi, Aisha da ke shirin ɗaukar kula, da sauri ta aje kular, sannan ta rugo zuwa gare shi, rungume ta yayi shima, yace “mara kunyar ƴata ya kike na sa me ki lafiya", murmushi tayi tace “ina lafiya", kallon Hajna da ta fito daga ɗaki yayi yace “ yauwa zo ki min sannu da zuwa ", murmushi kawai tayi cike da faɗuwar gaba ta iso, “sannu da isowa, ya hanya" ta faɗa, murmushi yayi wanda ya ƙara tabbatar min da cewa Farween namiji ne cikakken namiji wanda cikin maza ake wahalar sa mu, “yauwa ƴan mata "ya faɗa yana kallon ta, Aunty Farwa ma da gudu ta iso gaban shi ta rungume shi, “am happy to see you my baby" ta Faɗa, Farween yace “wanene babynki, lallai kam, kina ganin mutum babba haka ki ce mishi baby ", dariya Aisha tayi tace “wallahi Mommy kema da wani abu ki ke, wannan ai ya wuce baby, ko ni ai ba za ki ce min baby ba", ganin suna ta fira yasa Hajna ta nufi dinning area ta shiga ƙwashe kayan , duka kan center table ta aje, juyowa aunty Farwa tayi tana magana “zauna bari mu kwashe maka abinci mu dawo da shi........, bata samu ƙarasa maganar ba sanadiyyar ganin kayan abinci da ta yi a kan centre table, “ahh ahh, wannan aikin sai Hajna ni na sa ni ", duƙar da kanta tayi , Farween yace “ ƴar albarka kenan", “to zauna ka ci abinci "Aunty Farwa ta faɗa, Farween yace “shi wankan fa?", “to kayi yadda ya fi maka, ni zan shiga ɗaki, ga su Hajna nan su taya ka fira, na gaji sosai ", “sauƙin abun ina da ƙanwa da ƴa" ya faɗa, aunty Farwa bata kula shi ba ta wuce abun ta, dan ta san halinshi da gangan ya ke mata magana dan ya ɓata mata lokaci.

  Kallon Aisha, da Hajna yayi yace “yauwa plsss ku zauna ku jira ni bazan daɗe ba zan fito ", “to shikenan" Aisha ta faɗa, already Monica ta kai kayanshi ciki, dan haka kayan jikin shi kawai ya cire sannan ya shiga toilet, be ɗauki lokaci a toilet ba, a gurguje ya shirya.

   Ɓangaren Hajna kuwa ba yadda bata yi da Aisha akan za ta je ɗaki ta dawo, amma Aisha tace mata tayi haƙuri bazai ji daɗi ace duk sun tafi sun bar shi ba, dole  ta haƙura, fira su ke yi sama-sama lokacin da ya fito, murmushi ɗauke a fuskarshi yace “na gode da ku ka jira ni ", zama yayi kan kujarar da ke kusa da su, abinci Aisha ta zuba mishi ya fara ci, sama-sama suna fira har ya gama ci, “ni dai zani ɗaki" Aisha ta faɗa, Farween yace “tare za mu yi sallah, an yi isha'i ai  ", ba yadda su ka iya dole su ka yi sallah tare, bayan sun gama Aisha ta wuce, Hajna ma tashi tayi, “ke ma tafiya za ki yi ki bar yayanki shi ka ɗai", juyowa tayi, yace “zo ki zauna mu yi fira ", bata yi musu ba ta dawo ta zauna, “miyasa ki ke tsoron magana da ni", zare ido tayi irin ni, yace “eh ke fa ", “ni fa ba tsoro na ke ji ba" to minene, rufe ido tayi tana jin kamar zuciyarta zata faɗo tsabar faɗuwar gaba, kallon ta ya ke yi yadda ƙirjinta ke wani sama da ƙasa, alamar ta kasa natsar da kanta, mamaki sosai ya kama shi, me haka ke nufi, ba dai Hajna son shi take yi ba, kamar dai yadda ya ke sonta, ya daɗe sosai yana dakon son Hajna, tun daga ranar da ya sauke idonshi a kanta, ko barci gagarar shi yayi, amma ganin tare ta ke da Qaseem shi yasa ya nisanta kanshi da ita, ko Halia da ya ke so kamar ranshi baya sonta yadda ya ke son Hajna, bayan ta samu ta daidaita natsuwarta ne ta buɗe idonta, karaf ta ji sun haɗa ido da Farween, “wai minene, duk kin ƙi bari mu yi magana, labari fa za ki bani ", shiru tayi, “to shikenan tunda baza ki bani labarin ba, bari na ki gani, ki jira ni har in gama abunda na ke yi".

Anan zan dasa aya 😪😪😪
Nasmerh loves you

Haɗin guiwar  :Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya
ALQALAMI YAFI TAKOBI
[8/17, 10:00] Queen Nasmah✍️: ♻️♻️HAJNA ♻️♻️

Mallakin :Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya
https://www.wattpad.com/user/QUEENNASMERH08?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
PAGE 75-76
**********************
Wayar shi ya ɗauka, Hajna bata ce komai jira take taji me zai ce, taɓa wayar ya shiga yi, can sai ya kara ta a kunnenshi, “hello baby ", ban ji me aka ce ɗayan ɓangaren ba, sai ji nayi yace “ina fatan dai kina lafiya, kuma tana kularmin da ke", shiru yayi dan ya jira me zata ce, sannan yace “ohk babyna ki kula sosai, kuma idan kin dawo kin tashi da wuri ki kira ni ", kashe wayar yayi yana kallon Hajna da ƙura mishi ido, bata san miyasa ba amma ranta ya ɓaci sosai, kuma ba zata iya ɓoye yanayinta ba, kallonta yake yi, a hankali yace “lafiya dai kike kallona haka, abokiyarki ce fa", cike da ƙulewa ta tashi, “Hajna " ya kira sunanta, amma bata juyo ba, dafe kai yayi, yace “Ohhh Allah me na aikata kuma haka" sai kuma yayi murmushi dan shi be ga dalilin da zai sa ranta ya ɓace tunda ita ba budurwar shi bace, sai kuma zuciyarta tace idan fa itama tana sonka, to yama zai yi ya shawo kanta bayan kishi yasa tayi fushi.

   Tana shiga ɗaki, ta shiga watsi da kayan ɗakin, bata san dalili ba, amma ranta ya ɓaci, cikin rashin sani taji hawaye su sauko mata, da sauri ta goge tace “wai me yake damuna ne ", zuciyarta tace so, Hajna tace “ina bazai yuyu na so wani ba, Qaseem ya cire min wannan kalmar a rayuwata", da sauri kuma ta rufe bakinta tana jin wani yanayi game da Farween, da wannan tunanin ta gyara makwacinta, sannan ta kwanta, ta jima tana juyi akan gado, kamar yadda shima Farween ke yi, ya rasa ganewa ba dai Hajna son shi take yi ba, murmushi yayi yace “Allah ya kare min ke Halia "addu'a yayi sannan ya kwanta, dan ƙa'ida ce kafin ya kwanta barci Halia yake fara ma addu'a sannan shi, abun ya zama jinin jikinshi.

Washe gari da safe, Hajna ta shiga kitchen ta shiga yanka naman kaza, sai ta gama sannan ta tafasa shi, bayan ya tasafa, ta zuba kayan miya da sauran kayan ƙamshi ta ƙara ruwa ciki sannan ta rufe, doyar da monica yanka ta ɗauka, soya ta tayi, sannan ta soya ƙwai, ruwan zafin tea ta ɗaura lokacin da ta sauke pepper soup ɗin, sannan ta zube a kula, itama doyar cikin kula ta zube ta, sannan ta zuba ƙwai, ruwan zafin ta duba har sun tafasa, dan haka ta juye a flask, tare da Monica suka jera kayan cikin kitchen, sannan ta koma ɗaki ta sake yin wanka, ta canza kaya, dan Aunty Farwa ta koya mata yin wanka duk ta shiga kitchen.

   Ƙamshin girkin da Hajna tayi ya daki kunnen Aunty Farwa, murmushi tayi, sannan ta ƙaraso gaban dinning ɗin ta fara cin abinci, dan sauri take zata fita, Aisha ce ta fito, itama zama tayi ta fara cin abincin.

  HAJNA ce ta fito daga ɗaki, “ina kwana Aunty Farwa "ta faɗa tana zama, “lafiya ƙalau ƴar nan ya gajiyar jiya", “Alhamdulillahi "Hajna ta faɗa tana zuba abinci, har ta gama ci su Aunty Farwa basu gama ba, kwashe kwanon da ta ci abinci da shi tayi, tana fitowa daga kitchen idonta suka yi tozali da Farween, murmushi ɗauke a fuskarshi, bata san lokacin da ta sakar mishi murmushi ba, “a zuba min abinci "ya Faɗa, Aunty Farwa tace “Hajna zuba mishi", bata ce komai ba ta shiga zuba abinci, a kan center table ta aje abinci, zata wuce yace “zauna ki taya ni fira mana", ba musu ta zauna dan bata so Aunty Farwa tayi tunanin wani abu, roƙon Allah take Allah yasa Aunty Farwa ta fita ta samu ta tafi.

  Abinci ya kai bakinshi, wani daɗi ya bugi kunnenshi, yace “ummmm wannan abinci haka waya dafa", Aunty Farwa dake iya jiyo su tace “aikin Hajna ne", gaɗa kai yayi yace “kin iya abinci gaskiya " abinci ya shiga ci hankalin shi kwance, Aunty Farwa kuma ta ɗauki jaks tace “ni zan fita, sai anjima, Aisha ki ɗaura abincin rana, Hajna tayi na dare, kice ma Monica zata iya tafiya gida idan ta gama aikinta sai gobe kuma", “to mommy a dawo lafiya "Aisha ta faɗa.

  Wayar Farween ce ta shiga ringing, kallon sunan da ke yawo kan wayar Hajna tayi, Baby taga an rubuta, wani zafi taji ranta, da sauri ya ɗaga “hello baby sai yanzu kika tashi", “eh se yanzu "ta faɗa, murmushi yayi yace “to ki ci abinci kin ji, take care" ya faɗa yana kashe wayar, tashi Hajna tayi zata wuce, taki biyu yayi ya kama hannunta, “me yake damunki ne, duk lokacin da nayi waya da Halia sai kin yi fushi ", shiru tayi, “ki faɗa min miyasa", hannunta tasa ta ture shi, sake riƙe mata hannu yayi yace “ faɗa min miyasa", “ ina sonka! "ta faɗa da ƙarfi ba tare da ta san ta furta, da sauri ta rufe bakinta, cike da mamaki Farween ke kallonta, “nima ina sonki Hajna, ina sonki" ya faɗa yana murmushi, Aisha da ke zaune tana kallon ikon Allah ta tashi daga inda take tace “kuna son juna tun yaushe ", “na ɗauki tsawon lokaci ina sonta, a taƙaice ma shekaru" Farween ya faɗa, Hajna kuwa cikin sauri ta shige ɗaki, ko kaɗan bata da niyyar faɗar haka, a taƙaice ma bata san ta faɗa ba, murmushi tayi, sai kuma ta ɓata rai da tuna da Halia, yanzu ya zata yi, tana kishin Farween sosai, fiye da tunaninku.

“ Uncle Farween miyasa take fushi da kai " Aisha ta faɗa, Farween yace “saboda Halia", Aisha tace “miyasa baka faɗa mata wacece ita ba", Farween yace “saboda bansan tana sona ba, kuma yanzu bazata saurare ni ba", Aisha tace “zan faɗa ma mommy, nasan zata mata bayani yadda zata gane, ka kwantar da hankalinka, zata haƙuri, indai akan aunty Halia ne "murmushi yayi yace “to Allah yasa, nima zan yi farinciki", Aisha tace “ni zan fika farinciki, sannan ka je gobe ka ɗauko Aunty Halia yadda Aunty Hajna zata fahimta, yanzu bazan faɗa ma mommy ba sai ka ɗauko ta ", Farween yace “har Abuja kike so naje", “eh mana ke hau jirgi zuwa da dawowa zaka yi sauri", Farween yace “gobe da safe zan je insha Allah ", Aisha tace “Allah ya kaimu", “ashe kina da hankali "Farween ya faɗa yana jan kunnenta, “hmmm naji, ni dama nayi missing Aunty Halia gashi baka barin ta yawo" , “eh so kike ta dinga yawo kamar ke, ai ƙarƙashin Farween take ba ke ba sarkin" yawo" Farween ya faɗa yana murmushi, “hmmmm amma ai kai kana yi ", yace “ni namiji ne ita mace".

Anan zan dasa aya........... ✍️
Queen ɗinku a ko yaushe.

Kar ku manta kuyi following account ɗina na Wattpad ta link ɗin da ke sama.

Haɗin guiwar :Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya

ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️♻️♻️♻️♻️♻️♻️💃🏻
[8/17, 10:00] Queen Nasmah✍️: ♻️HAJNA ♻️♻️

Mallakin :Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya
https://www.wattpad.com/user/QUEENNASMERH08?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
PAGE 75-76
**********************
Wayar shi ya ɗauka, Hajna bata ce komai jira take taji me zai ce, taɓa wayar ya shiga yi, can sai ya kara ta a kunnenshi, “hello baby ", ban ji me aka ce ɗayan ɓangaren ba, sai ji nayi yace “ina fatan dai kina lafiya, kuma tana kularmin da ke", shiru yayi dan ya jira me zata ce, sannan yace “ohk babyna ki kula sosai, kuma idan kin dawo kin tashi da wuri ki kira ni ", kashe wayar yayi yana kallon Hajna da ƙura mishi ido, bata san miyasa ba amma ranta ya ɓaci sosai, kuma ba zata iya ɓoye yanayinta ba, kallonta yake yi, a hankali yace “lafiya dai kike kallona haka, abokiyarki ce fa", cike da ƙulewa ta tashi, “Hajna " ya kira sunanta, amma bata juyo ba, dafe kai yayi, yace “Ohhh Allah me na aikata kuma haka" sai kuma yayi murmushi dan shi be ga dalilin da zai sa ranta ya ɓace tunda ita ba budurwar shi bace, sai kuma zuciyarta tace idan fa itama tana sonka, to yama zai yi ya shawo kanta bayan kishi yasa tayi fushi.

   Tana shiga ɗaki, ta shiga watsi da kayan ɗakin, bata san dalili ba, amma ranta ya ɓaci, cikin rashin sani taji hawaye su sauko mata, da sauri ta goge tace “wai me yake damuna ne ", zuciyarta tace so, Hajna tace “ina bazai yuyu na so wani ba, Qaseem ya cire min wannan kalmar a rayuwata", da sauri kuma ta rufe bakinta tana jin wani yanayi game da Farween, da wannan tunanin ta gyara makwacinta, sannan ta kwanta, ta jima tana juyi akan gado, kamar yadda shima Farween ke yi, ya rasa ganewa ba dai Hajna son shi take yi ba, murmushi yayi yace “Allah ya kare min ke Halia "addu'a yayi sannan ya kwanta, dan ƙa'ida ce kafin ya kwanta barci Halia yake fara ma addu'a sannan shi, abun ya zama jinin jikinshi.

Washe gari da safe, Hajna ta shiga kitchen ta shiga yanka naman kaza, sai ta gama sannan ta tafasa shi, bayan ya tasafa, ta zuba kayan miya da sauran kayan ƙamshi ta ƙara ruwa ciki sannan ta rufe, doyar da monica yanka ta ɗauka, soya ta tayi, sannan ta soya ƙwai, ruwan zafin tea ta ɗaura lokacin da ta sauke pepper soup ɗin, sannan ta zube a kula, itama doyar cikin kula ta zube ta, sannan ta zuba ƙwai, ruwan zafin ta duba har sun tafasa, dan haka ta juye a flask, tare da Monica suka jera kayan cikin kitchen, sannan ta koma ɗaki ta sake yin wanka, ta canza kaya, dan Aunty Farwa ta koya mata yin wanka duk ta shiga kitchen.

   Ƙamshin girkin da Hajna tayi ya daki kunnen Aunty Farwa, murmushi tayi, sannan ta ƙaraso gaban dinning ɗin ta fara cin abinci, dan sauri take zata fita, Aisha ce ta fito, itama zama tayi ta fara cin abincin.

  HAJNA ce ta fito daga ɗaki, “ina kwana Aunty Farwa "ta faɗa tana zama, “lafiya ƙalau ƴar nan ya gajiyar jiya", “Alhamdulillahi "Hajna ta faɗa tana zuba abinci, har ta gama ci su Aunty Farwa basu gama ba, kwashe kwanon da ta ci abinci da shi tayi, tana fitowa daga kitchen idonta suka yi tozali da Farween, murmushi ɗauke a fuskarshi, bata san lokacin da ta sakar mishi murmushi ba, “a zuba min abinci "ya Faɗa, Aunty Farwa tace “Hajna zuba mishi", bata ce komai ba ta shiga zuba abinci, a kan center table ta aje abinci, zata wuce yace “zauna ki taya ni fira mana", ba musu ta zauna dan bata so Aunty

Please Login or Register in order to submit comment