Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shima kanta yayi a guje ya tunkudata qasa ya zare belt din wandon jeans dinsa yace “wlh kika qara tabata sainayi miki abinda bantaba yimiki ba kashe yar mutane kikeson kiyi Sadiya me tayi miki wanne irin haukane wannan kawai don takasance matata to ki sani aurena da Umaimah hadin Allah ne haukanki bai isa ya rusheshi ba abinda yasa na boye aurannan kenan saboda nasan ke mahaukaciya ci shigowar Hajiyansa ne yasashi yin shiru da bakinsa gadan² tayo kansa kafin ya ankara yaji ta daukeshi da wani gigitaccen mari ya dafe gurin da sauri ya dago kansa yace “Hajiya...” sake zabga masa mari tayi tana kuka tace.



“dama abinda yasa ka dage sai anbaka ita kenan Hameed irin taka amanar kenan me yaja hankalinka harka lalata tarbiyya marainiyar Allah na tabbata Umaimah bazata taba banzatar da tarbiyyar da kayi mata ba saidai kai ka banzatar da taka itama ka lalata mata tata meye ribarka Hameed qanwarka ka lalata harda ciki Innanillahi wa innah ilaihir raji'un wannan wacce irin baqar rayuwace wacce irin qaddara ce Hameed da kanka da kanka ka ketama Umaimah haddi ka cucemu Hameed kaci amanar maraici bazanyi maka baki ba amma da sannu zaka girbi abinda ka shika” tunda ta fara mgnr kansa na qasa harta gama ta juya ta nufi gadon da Umaiman takekai ta ruqo hanunta cikin tausayawa tace “Allah ya isanki Umaimah Allah ya isar miki” miqewa Sadiya tayi ta kalleshi tace “zaka dawo ka iskeni har gda wlh saidai koni ko kai azzalumi”


Yanajinta amma bai iya tanka mataba harta fice zuciyarsa mugun tafasa takeyi yasan duk bayanin da zaiyiwa Hajiya bazata saurareshi ba saboda haka yaja jikinsa ya fita ya zauna a kujerar dake qofar dakin, daidai lkcn da Umaimah ta bude idonta ta saukeshi akan Hajiya ajiyar zuciya Hajiyan tayi tace “sannu kinji Umaimah” daga Mata kai tayi cikin sarqewar murya tace “Hajiya ki tafi dani gdanki Aunty Sadiya da Uncle zasu kasheni wlh Hajiya kasheni zasuyi” kama hanunta tayi tace “wa ai dama kin gama zaman tsinannen gdannan ni dama tun farko banso zamanki ba dandai wannan azzalumin ya nace ne kuma Daddyn ku ya goya masa baya yanzu ga abinda gari ya waya” kwallar dake zubo mata Hajiya ta share mata tace “kiyi hqr wlh saiya gane kuransa wannan ai zalumci ne shekaran jiya yaje yake fadamin wata shashashar mgn saboda Daddyn ku yace yabarki ki fitar da miji bayan Daddyn ku ya tashi yake cemin wai yayi miki miji ashe abinda yake nufi kenan Allah ma ya rufa mana asiri da cikin ya zube da munga ta kanmu don wannan me raayin riqau din ba bari zaiyi a zubar dashi ba macuci kawai”



Abinka da zuciyar mace duk saitaji babu dadi aibata Uncle din da Hajiya takeyi lumshe idonta tayi daidai lkcn daya dawo dakin yace “Hajiya ta farka ne?" Tsawa ta buga masa wadda tasa Umaima bude idonta tace “ban sani ba dan iska mara imani ubanka zakayi mata idan ta tashin kaga Abdulhameed idan baka fita daga rayuwar Umaimah ba wlh saina sallama ka...” kallonta Umaimah tayi taga yanda yake zubar da hawaye tace “Kayy Hajiya kibari don Allah kinga fah kuka yake don...” bige bakinta Hajiya tayi tace “eh lallai gskyr hausawa da sukace baa dan iska daya wato ke har tausayin wannan annamimin bawan kikeyi ko to zan qyaleki dashi idan ya gama daibe albarkar jikin naki a banza kya nemi tudun dafawa kuma wlh kaji na rantse saikayi dana sanin abinda ka aikata tunda kaci amana ka rubuta ka ajiye amana sai tacika"


Bai iya cewa da Hajiyan komai ba sai gaban Umaman daya matso ya kamo hanunta doke masa hanu Hajiya tayi tace “kul baka kiyayeni ba shashasha kawai babban kawai yanzu Hameed badon Allah ya duba maraicin yarinyar nan ya kawo shegen cikinnan daka kunsa mata ya zubeba daya zamuyi kenan to wlh ka fita daga idona na tsani halinka Hameed na tsani mutum maci amana baka moreba Hameed" bazai iya jure kalaman nata ba saboda haka ya juya har yakai bakin qofa ya tsaya yace “laifi nane dana boye muku gsky tun farko da ace na fada muku Umaimah mata tace da baku zargeni ba nasani Hajiya dole dama zan fuskanci wannan matsalar tunda nakasa hadiye qwalamata na sauketa akan Umaimah a lkcn da yake bai kamata ba kamata yayi ace na sanar daku matatace kafin wannan lkcn amma duk da haka inaso dake da Umaimah da Sadiya dama duk wanda yake zargina ya sani niba mazinaci bane Hajiya baki haifi fasiqi ba bantaba shuka a haramtacciyar gona ba kuma banacin itaciyar da Allah ya haramta min Hajiya koda ace ma zina nakeyi da Umaimah wannan ta faru yakama ace kuyimin uzuri nima dan Adam ne ba waliyyi bane ni inada buqatar inda zanke zuba ruwana idan na tara tun farkon aurena naso hana Sadiya aiki kukace ban isaba nasha kawo muku matsalata kuma kin kasa yimin maganinta sau nawa nazo nace muku inason qara aure amma saiku hanani kullum burinku na farantawa Sadiya wacce nine na daukota na kawota cikin family dinmu babu ruwanku da matsala babu ruwanku da damuwata Hajiya nayi hqr shekara bakwai Ina fama da matsala daya a halin inada wata matar bayan ita to me kikeso inyi idan ban nemi haqqina ba a gurin Umaimah shekara biyar tana matsayin matata ina rainonta Hajiya ko tari nake a asusun qasa yaci ace yayi cikar da idan na fasashi zai bani abinda nakeso Hajiya nasha fada miki Umaimah tanada miji kina daukan zancena wasa to ba wani bane mijinta nine matatace"



Yana fadin haka ya juya ya fice tare da jan qofar da qarfi a mugun fusace ya dauki motarsa ya nufi gdansa yana zuwa yayi parking ya nufi cikin gdan tun tsayawar motarsa tajishi saboda haka yana shigowa ta tareshi da bala'i tace “ai dama nasan dole ka dawo fasiqi la'anallahu wanda baisan Allah ba ka shammaceni Abdulhameed bantaba tunanin haka daga gareka ba saboda kaikam kwai dan akuya....” bata ida qarasawa ba ya dauketa da mari ta dafe gurin da sauri tace “kan ubancan ni ka mara Hameed tabdi wlh ka mari bala'i na rantse da Allah saika gwammace baka sa hanu ka mareni ba ihu kwarto jama'a kuzo ga kwarto Allah ya tsine maka Abdulhameed Allah ya isa tsakanina dakai azzalumi maci amana kisa tsaf saina kashe shegiyar yarinyar nan saidai idan bazata gdannan ba” murmushin takaici yayi yace.


“To dama wanne tsautsayine zai dawo da ita ta zauna dake itama ta samu yanci bautar da tayi miki a bayama ta rainon yayanki da kula miki da gdanki kina gantalin yawon aikin banza ta isa yanzu lkcn kula da mijinta ne itama da ita ta shayar dashi farin ciki tayi masa maganin matsalarsa dake kika kasa ta bashi lkcn da kika kasa bashi kinga dama jinin dake yawo a jikinta shine a jikina ita zata iya dani tunda irinmu daya bazata gaza kamar yanda kika gaza ba tana da dadi sosai" yana gama fada Mata ya shige dakinsa ya datso qofar yanajinta tana dukan qofar kamar zata balleta tana kiran sunansa harda na iyayensa tana qare masa zagi tare da tsinuwar diban albarka a haka yaran suka shigo gdan driver yaje ya daukosu suna shigowa dakin Umaimah suka nufa suna kiran “Aunty mun dawo zo kiga assignment dinmu ki kawo mana dakin ta nufa kamar mahaukaciya ta finciki charge dake jikin surket ta rufesu da duka kamar Allah ya aikota tana zaginsu tana fadin “dagaku har uban naku kutumar ubanku zanci ita ta haifamin ku tsinanniyar yarinyar da take neman rabani da ubanku to wlh duk shegiyar yarinyar dana sakejin ta kiramin sunan yarinyar nan sainaci wancan kwarton mazinacin fasiqin uban naku" yanajin irin tujarar da takeyi yasan duk dan ya kulata ne don haka ya bawa banza ajiyarta.



Sai yamma liqis ya fito daga dakin yana daura agogo bata parlourn sai yaran suna zaune sai matsar hawaye sukeyi Nihal ce ta taso ta rungumeshi ta sake fashewa da kuka tace “Uncle me Aunty tayiwa Mom take zaginta kuma yau da safe bata bamu abinci ba da zamu tafi islamiyyah sai bobbo da biscuit Uncle yunwa mukeji Maliha har kuka ta rinqayi a makaranta saida Mu'allimah ta siya mata cheese sannan tayi shiru" ransa ne yayi mugun baci wai kamarshi ace yayansa suna fita basu karya ba kawai saboda sakacin uwarsu kama hanun yaran yayi yace “kuyi hqr Auntynku batada lfy tana asibiti kuzo muje kuganta sai kuci abinci acan" murna suka hauyi da tsalle da kansa ya cire musu kayansu yasa musu wasu ya jasu suka fice daga gdan suna zuwa asibitin ya nuna musu dakin suka shiga da gudu lkcn an cirewa Umaimah roba ta biyu ta jinin tana zaune ta jingina da pillow da gudu suka nufeta suna murna suna tsalle itama taji dadin ganin yaran saboda ta saba dasu koya ta yini bata gansu ba sai taji babu dadi haurawa sukayi saman gadon suka rungumeta Maliha tasa kuka tace “Aunty shine jiya Uncle ya daukeki kika tafi kika barmu kikaqi dawowa kiyi mana break yau sai haka muka tafi bamu karya ba nayita kuka a makaranta inajin yunwa” Nihal ce me wayo tace “Aunty kin rame kinyi fark meye yake damunki aka kawoki asibiti?” murmushi tayi vta shafa kansu tace “banida lfy ne amma naji sauqi da ganinku kunajin yunwa ko?" Daga Mata kai sukayi tace “no wonder indai yarana sunajin yunwa Ina ganewa Hajiya dake zaune tana kallonsu tana murmushi tace “kaji yan jakar uba ina iyayen naku da suka barku da yunwa” kawar dakai Umaimah tayi tace “mudai ki bamu abinci yarana suci Hajiya idan sunci sayi miki bayani” Nihal ce tace “mu Mom dinmu bata sonmu yau ma duka tayi mana saboda mun tambayi ina Aunty”


Daidai lkcn ya turo qofar ya shigo tare da sallama dago kanta tayi da sauri idonsu ya sarqe guri guda yanayi mata kallonsa me narkar da zuciya murmushi yayi mata tare da ajiye kayan daya dauko mata da shopping din da yayo yace “Hajiya sannu da qoqari yame jikin?" Ko kallonsa batayi ba bare yasa ran zata amsa masa abincin ta zubo jallop din shinkafa ce data wadatu da alayyahu da kifi banda sai qamshi takeyi ta miqawa Umaimah ta karba tare da zaunar da Maliha ta fara basu abincin a baki sunata zuba mata santi itadai batace musu komai ba saboda yanda takejin qwayar idonsa na yawo a jikinta muryar Hajiya ce ta katseta tace “idan kaga dama kaje Daddyn ku yana nemanka yanzun nan ya fita zashi gdanka” amsawa yayi da “to” ya miqe yace bari naje na biyasu kudinsu na dawo dakatar dashi Hajiya tayi tace “aa aikai ka gama aikinka saura namu ubanka ya biya komai" dagowa yayi da sauri ya kalleta yace “amma Hajiya..." Dakatar dashi tayi da cewa “karkace min komai Hameed wlh da zaka yarda ma daka daina zuwa inda nake saboda idan na ganka jinake kamar na kasheka”






*UMMUH HAIRAN CE...✍🏻*




*🅱RILLIANT WRITERS* *ASSOCIATION* 🖊
( _Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers)_



*GIDAN UNCLE*
( _Love and romantic story_)


*SHORT AND TRUE LIFE STORY*



*MALLAKAR*
👇🏻
*FAUZIYYA TASI'U UMAR*
*®FAUZAH*



Wattpad👉🏻 realfauzah



[email protected]


Alhmdllh a madadina da iyalaina munayiwa daukacin al'ummar duniya barka da shiga sabuwar shekarar gogerioun calendar duk da dai mu munci wata hudu a tamu ta musulumci Allah ya hadamu da alkhairan cikinta sharrikan dake tattare da ita Allah ya kade manasu yanda muka shigeta lfy Allah yasa muga qarshenta lfy idan kuma bamu da rabon gani to Allah ya karbi ranmu muna cikin musulumci muna masu aikata ayyukan alkhairi sannan yasamu a ceton Muhammadur rasulullahi (S.A.W).



*PAGE ELEVEN*



A salube yake kallon Hajiya lallai ta dauki lamarin nan da zafi saboda tunda yake da ita ko baqar mgn bazai iya tuna ranar data fada masa ba amma yau gashi tana neman tsine masa, cikin rashin qarfin gwiwa ya matsa jikin gadon na Umaimah yace “sannu Babyn Uncle ya jikin yanzu inane yake miki ciwo?” ya fada yana dora hanunsa a saman kanta ajiyar zuciya sukayi a tare cikin sanyi muryarta tace “da sauqi” murmushi yayi yace “ok kuzo mu tafi kada ku dame Aunty kunga batada lfy ko?” Nihal ce tace “Mudai anan zamu zauna gurin Aunty da safe ta dafa mana tea tayi mana wanka" Maliha kam kuka tasa wai a dole bazata koma gurin uwarta ba.



Daqyar ya shawo kan yaran suna kuka suna komai yajasu suka fice daga dakin itama Umaimah gawayen ta share batason ko kadan taji yaran suna kuka jinshi take har cikin lakarta, Hajiya kam haushine yakusa kasheta ita a tunaninta mgnr data fadawa Hameed dince tasa Umaimah kuka.



Kwanansu daya a asibitin yazo da safe dazai tafi aiki ya dubata ya jima sannan ya tafi office a CBN Kano yake aiki, bayan tafiyarsa babu jimawa Dr Saleem ya basu sallama suka tafi gda yayar Hameed Aunty Zarah tazo gdan saboda Hajiya ta kirata ta zayyane mata komai suka hadu a parlour sukayita Allah wadarai da abinda Hameed yayima Umaimah abin takaicin harda Daddy shima ya biye musu yace “wlh badon Hameed dana bane babu yanda zanyi dashi dasai nayi qararsa an fiddawa marainiyar Allah haqqinta jiya fah tsabar ya rainamin hankali na kirashi inayi masa fadan kuskuren da yayi sai cemin yayi shifa baiyi wani laifi ba Umaimah matarsa ce laifinsa daya daya boye mana gsky danaji rainin hankalin nasa yayi yawa sai nace ya tashi ya bani guri kawai saiya fashemin da kuka waishi ba mazinaci bane idan bamu yarda da abinda ya fada mana ba mubashi dama ya gabatar da wasu daga cikin shaidun da suka shaida daurin auransa da Umaimah fada na haushi dashi kamar zan cinyeshi amma bai fasa fadamin ba shifa matarsa yayi mu'amala da ita ba wata ba har yana neman yimin rashin kunya wai gobema idan yana buqatarta zai nemeta yayi duk abinda yaga dama da ita tunda shi yasan ba zina yakeyi ba saboda haka Hajiya sai kinsa tsaro sosai akan yaronnan saboda idan kikayi sake zaa samu matsala tabbas shima mgnrsa abar dubawa ce saboda haka zanyi binkice sosai kuma nace ya gabatar min da shaidunsa nanda kwanaki uku idan ba hakaba zan sauki matakin shari'a akansa”



Yana fadin haka ya tashi ya nufi samansa itama Umaimah miqewa tayi daga jikin Hajiya ta shige dakin da idan tazo take zama a ciki ta kwanta itadai zuciyarta babu dadi kwata² batajin dadin yanda suke aibata Uncle din nata saboda koba komai yayi mata abubuwa da yawa da bazata iya mantawa dashi ba, tana wannan tunanin wayarta tayi qara ta dauka da sauri taga qawarta ce Sa'ud da sauri ta kara a kunnenta tace “Hello Sa'ud kizo gdan Hajiyata don Allah yanzu inason ganinki" tana fadin haka ta kashe wayar tananan kwance baafi 20 minutes ba taji muryar Sa'ud din suna gaisawa da Hajiya,
Shigowa tayi tare da mayar da qofar ta rufe ta zubawa Umaimah ido tare da cewa “nashiga uku Umaimah meye ya sameki haka kika rame?"



Lumshe idonta tayi tare da miqewa zaune tace “meyema bai sameni ba Sa'ud bari nayi na cikin Uncle” nan ta kwashe komai ta fada mata tace “Sa'ud nifa Ina tunanin abinda Uncle yake fada gsky ne saboda shekara daya baya munje Maiduguri lkcn dagani saishi sai yaran Aunty Sadiya qin zuwa tayi tace aiba taron family dunsu bane Ina kwance nayi matashin kai da cinyar kaka ya shigo parlourn tunda ya shigo naga yanamin kallon qurullah hankalinsa gaba daya yanakan qirjina saboda rigar jikina ba wata ta kirki bace kuma ko bra bansa ba, ashe itama kaka ta lura kawai sai naji tace “ko kana sone?” sosa kansa yayi yace “wlh kaka akwai matsala ina buqatar matata sosai” dariya tayi tace “kaida kayanka Hameed Nima na matsu a wucce gurinnan na matsu naga irin taku baiwar na matsu naga yayanka da Baby kafin qasa ta rufe idona Hameed ka fito ka bayyanawa duniya matarka ce ita ko kaima ka samu sauqin wannan banzan rayuwa ta gdanka su kansu iyayenka sunsan baka samun kulawar data dace gurin matarka amma sun kasa nema maka mafita me ake da irin wannan auran da haqqin kwanciya ma bazaa sauke ba balle akai dana kulawar yau da kullum Hameed kullum gindinka a tsaye tun bayan auranka bantaba ganin ka canza ba bantaba ganin wandonka ya zauna daidai ta gaba ba to gsky kayi qoqarin nemawa kanka mafita kafin mace ta kasheka da lfyrka da komai ka zama sorry, duk cikin yarenmu na shuwa take mgnr wlh a lkcn ban fahimci me kalaman kaka suke nufi ba kawai dai mamakin rashin kunyar kaka nakeyi.



Sa'ud sai lkcn da Uncle ya bareni ya ratsani sannan kalaman kaka suka rinqa dawomin Uncle Hameed jarababbene ajin farko tun Ina gudun abinda yakemin harna saki jiki dashi duk da wahalar da nakesha idan yana cina haka nake jurewa wlh saida ya kasance idan baya tare dani banajin dadi a zahiri banason mu'amalar mu amma a badini inaso acikin sati biyun nan naji jiki sosai a hanunsa saboda babu ragayya kota kwabo tsakanina dashi a dare saiya nemeni so uku tun a lkcn na farajin jikina wani iri ashe ciki ya dirka min bayan dawowar Aunty Sadiya saina yanke duk wata alaqa tsakanina dashi badon inaso ba saidon tsoron ranar da asiri zai tonu ashe na baro kari tun ran tubani kwana uku baya ya daukeni da zummar Daddy yana nemana kawai ya kaini wani hotel tunda mukaje nake amai a haka yayi abinda yakesonyi dani" nan ta zayyane mata komai ta kuma cewa “tunda abin ya faru kowa laifin Uncle yake gani su Hajiya sai aibatashi sukeyi nikuma banason hakan Sa'ud inason ganinsa yau amma sun hanamu ganin juna inajinsa yana roqar Hajiya yanason mgn dani ta zageshi tass dole ya bata hqr ya fice"


Ajiyar zuciya Sa'ud tayi tace “tabdi lallai Uncle yana cikin bala'i yanzu gdansa na fara zuwa ina shiga na tabbatar da ba lfy ba kayanki da duk wani abu da yake mallakinki anyi watsi dasu a harabar gdan gabana na faduwa na shiga parlourn na dauka kina ciki anan na tarar da wani tashin hankalin sababbin kayan furniture din daya zuba miki an ballesu ballar wulaqanci wadda bazasu moru ba ita da wata qawarta da wani saurayi ina tunanin qaninta ne sunata zazzaga bala'i tare da sake famfata akan kada ta kuskura ta yarda da wannan cin amanar ta daga masa hankali harsai ya sakeki wai asiri kikayi masa kika bashi yaci a abinci shiyasa idonsa ya rufe har yake fada mata maganganu akanki wai bandama jarabarsa me zaiyi dake yarinyar da yaci kashinta da fitsarinta, wlh aikine babba a gabanki idan har kin tabbatar mijinki ne cire kunya zaki ki lailaye abinki ki bashi komai kiyi masa komai ki qyale shegiya da haukanta banso cikinnan ya zube ba Umaimah naso ace yana jikinki har yanzu da ko ba aure tsakaninku nasan sai an daurashi yanzu dai ba wannan ba wanne shiri kikeyi na tarar angonki?"


Kallon Sa'ud tayi idanunta taf da qwallah tace “inajin tsoro Sa'ud nasan wace Aunty Sadiya nasan haukan kishinta wlh duk kishinmu Shuwa da ake fada Sadiya tafimu ita da take ma bahaushiya nasan zata iya kasheni kamar yanda take fada” kallon banza Sa'ud ta watsa mata tace “kaji banza kekuma tsayawa zakiyi harta kasheki kina zaune ai wannan mulkin mallakar ya wucce dole ki zage kije mata da duk yanda tazo miki idan tace kuzauna lfy ku zauna idan tace haukan zaayi ki nunawa shegiya kinfita iyawa kici uwar ubanta a hauka ki nuna Mata naki na jini ne na gadone keda kike Shuwa'arab har a fada miki kishi Allah ya tsinewa uwar wanda yaji tsoro ya fasa, wlh yarinya zagewa zakiyi ki cire tsoro ki kama dan'wanki mijinki a hannu kinji dai na fada miki"



Tunda Sa'ud ta fara mgnr take kallonta harta gama sannan tace “amma dai Sa'ud kinsan da ciwo abin ka raini yarinya kuma tazo ta zama kishiyarka gsky babu adalci a cikin lamarin” tsaki Sa'ud tayi tace “kuma fa kin fara bani haushi Umaimah da kike wannan mgnr ke kikace kada ta tsaya ta kula da mijinta ko ke kika hanata kama mijinta ai dama tasan haka zata faru tunda itace tabada qofar hakan inda tana sauke masa haqqinsa tana riritashi kamar jariri aida baiyi sha'awar wata macen ba ke bari kiji wlh mazan zamanin nan ko kana kula dasu ma saika hada musu da lahaula da yasin harda suratul Shifah don nema musu lfy ke inson samune harda suratul junnu duk ki rinqa tofa musu don wani lkcn kamar masu shafar aljanu haka suke balle ka sakeshi sasakai kamar makahon raqumi duk inda yaga dama ya cilla qafarsa ai tama godewa Allah da abin ya tsaya Mata iyanan inda wani ne ma yanda yake da lfyr nan inya rinqa neman mata harsai ya kwaso mata qanjamau yazo ya gwagwada mata su shiga uku sakaryar banza da ita kema idan kika zama lusara irinta wlh kunaji kuna gani mijinku zaifi qarfinku kuma billahil lazi kinji na rantse koni yace yanaso badakai zanyi bori ya hau dan samun miji irin Uncle Hameed a zamanin nan ba duk mace me saa ba"



Ajiyar zuciya tayi daidai lkcn wayarta tayi Ring da sauri Sa'ud ta dauka tayi murmushi tace “kinga dan halak ko dan uwarki kashe murya ki kama abunki babu komai koba aure akwai qauna ballema ni nadade da sanin mijinki ne don Yaya Yusuf ya dade da fadawa Farouq dinmu cewa yafita daga harkarki kada ya hadu da fushin Hameed saboda kedin matarsa ce" katsewa wayar tayi ta ajiye ta kamo hanun Umaimah tace “wlh Umaimah ki ajiye gidadancin nan naki ki mayar da kanki karuwa da gaske a gurin mijinki" sake shigowa kiran yayi ta miqa mata.



Hanunta na rawa ta daga tace “He...hello” ajiyar zuciya ya sauke yace “Babyn Uncle ya jikinki" a sanyaye tace “da sauqi" murmushi yayi yace “kema fushin kikeyi dani ko Baby?" Da sauri Sa'ud ta kada mata kai tace “aa Uncle" ajiyar zuciya yayi yace “har naji sanyi Babyn Uncle nasan kowa fushi yakeyi dani akan abunda ya faru tsakanina dake wanda nasan rashin sanine yasa suke ganin baqina ina cikin tashin hankali a gda Babyn Uncle gurin Sadiya basai na fada miki na bangaren Hajiya da Daddy ba kinsan komai amma duk basu dameni ba kamar naki don Allah kada kibada damar da zaa rabamu Umaimah wlh akwai matsala cikin hakan ba qarama ba inason ki bani hadin kai Babyn Uncle kinji”


Ajiyar zuciya tayi ta kalli Sa'ud daga Mata kai tayi alamar to tace “to Uncle” numfashi ya sauke yace “yawwa Baby na Allah yayi miki albarka zan kiraki zuwa dare amma jinin ya tsaya ko?" “Aa" ta fada murmushi yayi yace “shikenan shima nasan zai tsaya kafin lkcn da zan daukeki ki kwanta ki huta sai munyi waya anjima" ajiye wayar tayi tana haki kamar wacce tayi gudun famfalaqi, dariya sosai Sa'ud tayi tace “kaji banza don Allah wayar kikewa wannan hakin to ya kikayi ranar farko daya turmusheki?" Dariya tayi tace “wlh bansan komai daya faruba tun dare sai daya na rana na farka na ganni daure da drip" qara sheqewa da dariya Sa'ud tayi tace “lallai Uncle yaga mata wannan ragwanta haka" dariyarta ta qarawa sauti tace “muguwa kuma a haka don rashin imani kika bani magani ya haukatani da kaina na rinqa roqon Uncle ya gurgureni aikuwa naci naci ubana ranar naga yanda ake barin madara” dariya ta kuma sheqewa da ita tace “irin muguntar da akayimin Nima nayi miki haka Zainab tayimin washegarin ranar da Yaya Auwal ya fara zungurata ke ban fada miki wani abuba Zainab tayo ciki in fada miki Abba yanata bala'i wai mun cuceshi shikuwa Yaya Auwal yace to Abba mun fada maka aure mukeso kaqi yimana yanzu ga irinta nan shine yace ta turo Jabir din ayi mgn shima Yaya Auwal zasuyi mgn a tsayar da lkcn bikinmu amma nifa gsky banajin zan auri Yaya Auwal"



Kallonta Umaimah tayi da sauri tace “meyasa?" Murmushi tayi tace “na samu wani Guy ne sunansa Anwar wlh

Please Login or Register in order to submit comment