Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

TARAR ARADU DAKA
Littafi na daya 1
Na Umar Lawan
Typing:- Shuraih Usman
.
DANDANO daga cikin littafin
••••••••••••••••••••••••••••••••
Umar ya shiga gararin rayuwa
Inda ya rasa kwanciyar hankali
Sakamakon soyayya da
Yarinya mai suna Farida.
Wacce akan tane mutane uku
Suka rasa rayukansu,
Akokarin neman aurenta.kuma
Shima an gargadeshi
Amma yace yaji yagani
Kuma YATARI ARADU DA KA
Saboda fadin kai
Koya zata kasance kubiyoni acikin wannan littafi mai suna
TARAR ARADU
KunasooooTARAR. ARADU
Littafina daya 1
Na Umar Lawan
Page 1
Typing & posted by Shuraih 99%
.

Na yayi mo takarduna bayan na cika tumbina da
waina.nan da nan nafara angizo babur dina Vespa
zabuwa .zuciyata na mai dari darin dadewar da zan yi ina
bugu kafin ta tashi.
Bayan dana hada waya sakamakon gidan makullin
(ignition)da ya dade da lalacewa.
Abin mamaki yau bugu shabiyar kawai nayi ta tashi .anan
da nan wata kara ta cika wajan kamar an kunna injin
markade sabon washi, saudadama idan ina sabis acikin
gida in har na tasheta yara kanyi sallama ."Ga markade".
Ni kaina duk sanda ta tashi nakan toshe kunnena .
Lokacin kwanciyar zafi yan unguwar mu har basa so nayo
dare .
Darana kuwa matan aure basa son wuce wata wai nakan
tayar masu rigimammun 'yayansu daga barci,kuma na
kan hansu bin sallar jam'I.
Dama gababur babu gudu,kuma nakara kasheshi da kaya
.
Domin kuwa idan nabudema wajen adana kayayyakinsa ,
babu komai illa tulin fulogi wanda nikain nasan suna
ragemin gudu.
Amma inkaduba body ,mai motama sai yayi zaton zan iya
wuceshi har yagaza kamoni.
Nan da nan na dare sama mukafara kokoyi da giya na
dade ina shammatarta kafin tafada .
Aifa shigar giyar kedawuya na murdashi sai tyafiya ,kar
kaso kaga yanda nake doro ina kwambarewa .
Kullum nahau haka nake fankama naketakama kamar
sarki akan doki.
Idan na raina majalisama ko sallama banayi ahaka naita
wuta har makarantar dangiwa commercial secondry
school.
Inda anan nake koyarwa amatsayin malamin English.
Da malam sule mai gadi muka fara gaisawa "har an fito"
"Allah yayi"
Nabashi amsa .
Nakafe babur dina a inda aka tanada domin yin fakin.
@mr:-Shuraih 99%
Na nufi ofishin principle. Ko ba'a fada maka sunansa ba
zaka iya ganewa da kanka.
Domin kuwa yafi dacewa da malam Abba .akwai kwazon
aiki akwai kuma mugun son kudi na gaisheshi muka
kuma taba yar hira wadda zolaya acikinta tafi yawa .
Da fitowata na nufi wani abokin aikina kabir sabi'u. Muka
caccake na dubeshi "naga sai kyalli kake kodai kanasan ka
angoncene ban saniba?"
Yayi dariya" kaifa tsiyarka kenan baka kyale mutum haka"
Muka zauna na shiga dube dube wani lokacin har nakan
mike tsaye "wai kai me kake dubawane"
Na dawo na zauna bayan na gaza hango abin danake
nema "don Allah bakaga shigowar farida ba ?"
Na tambayeshi . Ya tintsire da dariya . "Kai mallam tunda
farida tafara aiki anan naga sai wani kankajeri Kake kana
kara kwalliya ,kodai da watane akasa?"Nace babu komai ,
don mutum ya tambayi abokin aikinsasai yazama laifi"
Ya girgiza kai
"To me isa baka tambayar su hafiz?
Kosu ba abokan aikin kabane"?
Na gyara takarduna sa'arda nake cewa
"Kaga mungama hirar ne ban tambayekasuba"
"To shikenan tunda boye-boye kake ,amma indai kuka
shirya kanku kayi sa'ar mata UMAR"
Bancemasa komaiba ,duk dacewa maganar tasa ta
kayatar dani . Bada jimawa ba na hangota tana shigowa
tana rungume da jakar takardunta .
Mace ce mai matukar tsari da kyau tana da yawan kuya
da kulawa da Addini,kai ni tunda nakke ban taba ganin
kamartaba .
Na mike tsaye kabir yabini da kallo
"To mallam ka hangota zaka gujeni ko?"
Na harareshi
"Ai kaine kake yimin wulakanci,ba gara na tafi inda inda
za'a karramani ba " ban tsaya wata wata ba nanufi inda
take da ganina ta fara murmushi ,
Murmushin da kullum in tayimin sai nadan rikice .
Na dubeta cikin sarkewar murya
"Ina kwana hajiya farida "
"Lafiya lau umar"
Tra amsa cikin daddar muryarta
To be conti......
Via:- mr:- Shuraih 99%
TARAR ARADU
Littafi na daya 1
Na Umar Lawan
Page 2
Typing and posted by Shuraih 99%
.
.
"Yau narigaki zuwa "
Nace da ita tadan kwatar da kanta
"Nadan ragewa mummy aikine saboda batajin dadi"
Ashsha Allah ya sauwake"
Nadan gyara tsayuwata "don Allah farida idan an tashi
tara ina son magana dake'
Ta kalleni da fararen idanunta sa'ar da take cewa
"Lafya dai ko umar"
Na kauda kaina domin bana jurewa kuramata ido saboda
wani kwarjini da take dashi.
"Lafya kalau akan dai maganar nan ne"
Ta sun kuyuyar da kanta kas daga bisani ta dago
"To Allah ya kaimu"
Muka juya muka tafi.
@mr:-Shuraih 99%
Tunda farida tafara aiki amakarantarnan Allah yasanya
min tsabar kaunarta , nayi kokari in yakice amma ina.
Abin yaki yiwuwa .
Wannan yasa nafara yi mata isharori amma tayi biris
kmar bta gane ba , ga misali nasha sai mata sabulai da
mayuka .
Amma sai dai tayi godiya ta kuma bini da Addu'ar Allah
yabar mutunci.
Wannan yasa nafito fili na shai da mata amma sai tace na
saurara zata tun tubeni .
Kuma shiru kakeji haryanzu taki tuntubata .
Dana tina mata saita kama noke-noke shine yau nayi
kunar bakin wake domin nasan wacce akeciki.
Ana tashi tara na nemi karkashin wata bishiya na hakimce
can jimawa sai ga farida tana isowa
"Mai yafaru ne umar?"
Ta tambayeni bayan data zauna ,nakara jingina sosai
ajikin kujerar danake kai.
Sannan na dubeta na fara dacewa
"Wai dan Allah farida mai yasa har yanzu kika ki bani
cikakkiyar amsa ?
Nidai idan kina ganin babu dama gwanda ki gayamun
insan yanda nayi.mai makon ki kyaleni kullum ina
azabtuwa da tsabar sonki, kuma ina hada ki da Allah ki
shaudamin hakikanin gaskiya "
Na dade ina sauraronta taki tace uffan .sai kawai ta
tokare habarta da hannu,
Babu tsammani kuma sai naga tafara kwalla .
Hakan ya rikitani ,cikin rudewa na fara cewa
"Maganata rai ya bata miki"
Don Allah kiyi hhakuri"
Batace komai ba taci gba da kukanta kawai
"Don Allah farida kiyi hakuri bazan sake tambayarkiba"
Ta girgiza kai lokacin da take share hawaye "umar ba
tambayr kabane ta bata min rai illa iyala wani al'amari
dabam , zan amsamaka tambayarka umar,amma saidai
in antashi kasameni agida "
Nadubeta
"Inane gidanku
Tadanyi jim sannan tacigaba 'goron dutse bayan gidan
isiyaka rabi'u gida mai kallon kudu, na biyu ahannun
dama"
*** *** ** ** ** ***
Dayin sallar la'asar na shiga wankka , nadade ina shekawa
domin kuwa awa guda na karar cur, nakarar da ruwa ya
kai jarka uku, ba'a batun sabulu wanda nakarar da fakiti
guda badon komaiba sai don na kara haske.
Aranan sabon man shafawa nasiyo saboda ji nayi nawa
nada yana wari, alhalin kuma dukranda nashafashi har
tambata ake wannan wane maine?.
Saoda tsabar kamshi, na bude kwaba nayi ta zaro kaya
ina ajiyewa gefe guda ,har nazo kan na cin yewar
,dukranda na sanyasu ka tabbatar zani muhimmiyar
ungwa ko kayataccen fati.
Nan da nan nafara jikasu da tirarena.
Na makala farin gilkashi.
Ban nufi ko'inaba sai gindin dressin mirror don duba
haduwar tawa,
Hakika nafito kamar yadda nayi tsammani, nakalli
takalmana cali-cali wayanda tuni na baiwa shushaina ya
wankeminsu harda karin kudi nayimasa domin yayi mani
wanki na musamman nan danan na zura kafata nafara
takawa cikin takama ,
Kai kace wani dokin dan sarki,
@mr Shuraih 99%
Na kulle shagon nanufi cikin gida anan na sami matar
yayana tana kokarin dora girki.
"Kai umar ina zakne haka kaci kwalliya ?"
Nagoge fuskata da hankici
"Wallahi zani unguwne ,yaya kika ganni,nafito?"
Ta kalleni daga sama har kasa
"Wallahi ka fito"
Kaga yanda kake kyalli kamar sabon kwabo"
Wata dariya ta kwacemin .
"Toh madalla dama haka nakesopn ji"
"Zanyi miki karin kudin cefane tunda kin yaba "
Tayi shewa .
"To mai gida, godiya nake,ince dai ba kishiya zakayiminba
ko?"
Na duba agogona
"Ke dai wallahi kin cika tsoron kishiya kimin Addu'a Allah
yabada sa'a"
Ta kwantar da kai
"To Allah ya taimaka "
"Amin"
Nafito nabarta .
Raina yabaci yayinda na iso soro,baodn komaiba sai don
bata min lokacin da mashin zaiyi.
Na turashi har muka zo waje.
Nakafeshi nafara bugawa nayi tayi amma ina ko amsawa
bayayi kamar wanda na cika tankinsa da ruwa .
Yara kuwa sukazo suka yanyameni,kullum haka sukemin
in har nazo fita da yamma ,sukanyi ta dariya sa'arda nake
bugawa.
Wani lokaci nakanji kaman nasa duka amma sai na daure
na rabu dasu.
Har ina shirin hakura sai naji yafara amsawa.
Wannan yasa nacigaba banfi bugu ashirin ba kuwa
yatashi.
Yara suka kaure da shewa ye !yatashi yatashi!
Nan fa suka da baya yayinda suka ga dare,badon komai
ba saidon sun san in yayi wata zabura zai iya bi takan
yaro.
Raina yakara baci dana tuna yadda zanyi fama da giya
,amma cikin ikon Allah murdawata sau uku sai fada, na
murza totur sai tafiya ahaka na ringa tuki cikin hkima da
dabara.wai ance inkana da abin hawa dolene kazama
makaryaci saboda takurawar yan aro mai zuwa yau
dabam mai zuwa gobe dabam.
To nidai nakaryata domin kuwa babur dina saudaya wani
abokin aikina yataba aronsa da uzurin gaggawa ya
kamashi,daga ranar shima bai kara araba.
CABDI WANNAN BABUR KO WAHALA DA RAI
Zamu cigaba anjima
By @mr:- Shuraih 99%TARAR ARADU

Littafina daya (1)

Written:- shuraih 99%
Page 3

Adai dai junnction din bariki yellow fifi ya tsaida mu.
Raina yabaci domin kuwa shine abin dana tsana sakamakon rashin wadataccen burki,nayi iya yina domin ya tsaya amma ina ,har nakaiwa yellow fifan sura .yayi tsalle gefe guda .
Da kyar babur din ya tsaya bayan daya tungudi ginin express, na juyo domin bawa yallaban hakuri, sai naga ashe bai dauka da zafiba ,daomin ma dan unguwar ne.
Ba'ajima ba akabamu hannu nafara kokarin sa giya ina takawa da kafa da kyar na samu ta shiga,
Wata rana ma kin shiga takeyi sai nagaji da shan zagi da horn daga masu ababen hawa .
Kai har akwai kwandastan daya taba rankwashina wai tare musu hanya .
Haka naci gaba da taifya rakakai raka kai kamar wanda yake tafiya akan jaki, sauda yawa mai keke yakan wuceni tinma ba idan na hadu da sabon jini ba.
Aje ba'ajeba sai gani a goron dutse na dudduba hakika farida tayi mantuwa wajen kwatantamin gidansu.
Domin kuwa gidan daya kamata yazama nasun sam banasu bane ba.
Saboda yadda naga tsarin gidan ko yar wanke wankensu tafi karfun tayi koyarwa amakaranta.
Sai nafara tunanin yadda ya amata nayi daga karshe na yanke shawarar in sami yaro na tambayeshi.
Haka kuwa akayi ,
Nayafito wani yaro
"Dan Allah zo mana kanina"
"Gani"
Yafada okacin daya iso gareni
"Don Allah kasan wata farida malamar makaranta"
Ya gyada kai lokacin daya ke nuna min
kerarren gidan

@mr:-shuraih 99%

"Ga gidan sunan"
Nacika da mamaki badon ita tace nazo ba da juyawa zanyi domin kuwa nakaraya lallai farida tafi karfina .
Wata kila tayimin hakanne domin innaga gidansu sai in hankalta.
Har zan juya sai natuna yakamata tasan nazo don kartakamni da laifin saba Alkawari.
Na dubi yaron
"Don Allah jeka ka kirawomin ita"
Ya zura min ido kamar maisan yafada min wani abu, da na dauka bazashi ba
Sai naga ya kada kai yace
"Amma dai"
Sai yatafi nabi yaron da kallo shin me hakan yake nufine?
Kokuwa shima yagane cika kainane?

Bai jima ba sai gashi yafito tana biye dashi tana biye dashi abaya fuskarta cike da murmushi.
Ta tsaya abakin kofa , naga ashe farida kyawunta ya wuce yadda nake gani amakaranta, yaron yazo wucewa kusa dani
"Mallam Allah yaji kanka"
Yafada yakuma zura aguje bansa abinda yake nufiba .
Na kafe babur dina na kuma nufi wajenta
"Sannu da zuwa umar"
Tace dani idanunta akaina na amsa da
"Yauwa"
"Bismillah"
Tafada sa'arda take juyawa na bita abaya ta cikin soron wanda aka shimfideshi da tayil mai kayatarwa ,
Araina ina ta sake saken abin daysa farida koyarwa.
Shin sha'awar koyarwar take ko kuma me ?.
Nidai nasan ba'ace dan tasami kudiba.
Banyi aune ba sai na ganni atsakiyar gidan aifa sai na ne mi kidimewa saboda tsabon tsari da kayatarwa.
Ta nufi wani daki dani tasa hannu ta tura kyauren na gilashi,
Ta tura kai ciki sa'arda ta kecemin shigo,
Nasa kafata nayi mamaki danaji sanyi ya dokoni alhali lokacin zafine, sai na tuna A.C babu shakka itace aka kunna ,
Na ratsa ta wani kilishi daya mamaye ilahirin dakin da a gidan nake to da babu ruwana da katifa kansa kawai zan rinka zuwa ina yin baccina.
Na dubi wasu maka makan kujerun dasuka mamaye dakin tai min nuni da daya
"Zauna umar"
Na juya nazauna sai naji nayi kasa zan nutse ,nan nafra zargin farida da laifin zaunar dani a bulalliyar kujera -kome yasa tayi min haka?
Kawai sai naji nadakata nan nagane ahe ba bulewa tayiba duk laushin soso ne.
Na jinjina kai lallai masu mura suke da tari.
Ta nufi kofa loakcin da takecewa
"Ina zuwa"
Bata dadeba ta dawo rike da farantin silverm
@mr:-shuraih 99%

Ta ajiyeshi akan wani karamin table sai naga kofa tabude wata matace ta leko.
Ita da farida tamkar an tsaga kara.
Sai nagane mahaifiyartane na sauka har kasa na gaidata tayimin kyakkywan maraba, sannan tafita na dubi farida
"Mai yasa baki kirani naje nagaishta acan ba sai ki wahalar da'ita kisa tazo nan"
Ta waiwayo gareni cike da murmushi
"Lallai bakasan momi ba umar, wani irin haline da'ita da kayi wahala dominta gwara ita ta wahalar da kanta yanzuma babu yadda banyiba akan tabari zamuzo ku gaisa tace a'a zan wahalar dakai"
Nayi murumushi gami da fadin
"Allah sarki"
Na gane mahaifyar farida irin mutanenane masu saukin kai,ta zauna akan kujerar dake kusa da tawa bayan ta gama bude tan garayen,
Dan kalin turawane wanda akahadashi da kwai aka soya sai kuma wani hadadden kosan doya.
Ta tsiya ya ruwan tatacciyar abarba akofuna sannan ta dubeni sa'arda ta ajiyemini cokali mai yatsu.
"Bismillah umar"
Muka fara gabatarwa harzuwa lokacin danaga ya kamata na dakata sannan na kora ruwar abarbar nayiwa Allah godiya.
Ta kawar da kayan gefe sannan ta fuskanceni
"To umar naga kana nema kadamu akan rashin baka amsar tambayarka ,to dayardar Allah ayanzunnan zan warwaremaka zare da abawa"
Tacigaba
"Ni da ka ganni yar wani hamashakin mai ar zikice mai suna. Alh Hashim.jigon dan kasuwane maiyin harkokinsa akasashen turai,kuma nan dakake gani dayane daga jerin gidajensa guda goma,kuma shine mafi kankanta dakuma muni"
Nakame baki jin abinda take fada
"Kwarai kuwa"
Ta tabbatar mini
"Yana da gidaje a Kaduna ,legas,Abuja kai harma da birnin london"

Zan cigaba

@mr:-shuraih 99%





TARAR ARADU
Littafina daya (1)
Written:- shuraih 99%
Page 4
Na Jin jina kai taci gaba
"To kuma matarsa biyu hajiya halima uwargidan da
kuma hajiya safiyya wato mahaifiyata, kuma ita
uwargidan yayanta hudu uku maza daya mace.
Mazan kuma sune manya kuma abokanan harkar
mahifinmu wato masu taimaksa,ni kuma ni kadiace
awajen mahaifiyata.
Ina da shekara biyu Allah ya karbi abinsa kuma yayyen
namu sune suka san kudaden mahaifinmu na banki
hakanan kadarorinsa.
Wannan yabasu damar yin rubda ciki akan
kudin,hakazalika kadarorin, gidajenma cewa sukayi uku
kawai yabari duk sauran ya sayar dasu yabiya bashin
kamfaninnuwa.
Sai suka bamu wannan gida dakuma naira miliyan daya"
Nakar kada harshe game da jijjiga kai
Taci gaba 'yanuwan mahaifiyata sunta bata shawara akan
takai kara amma tace sam wanda yatara dinma yau ina
yake? Saboda haka ta hakura
Arzikin dake tsakanin suma na 'ya ai ya isa tayi ta renona
ta sanyani a nursery kai har zuwa lokacin dana sami shiga
jami'a nai ta fama da takardu daga samari.
An kuma sha tareni fuska da fuska.
To amma ban kula ba domin alokacin burina nayi digri
na kuma sami damar tallafawa kaina da mahaifiyata.
Kamar kullum na tsaya abakin titi don samun mota
akokarina na dawowa daga makaranata.
Wata honda hala tayi fakin agabana, ahankali bakin
gilashin na kofar direba ta fara janyewa ahankali, yana
gama janyewa sai naga ashe wani matashine jibgege
bakikkirin mai jajayen idanu.
Koda acikin dodanni na tabbata baza akirashi mai
kyawuba
Ya yaye fuskarsa yazuwa abinda yake murmushine,
nikuma aganina abinda yayi yafi kama da hammar jaki
"Yan mata shigo na rage miki hanya mana"
Yafada awta muryarsa mai kama da kukan balamar
tunkiya, na kau dakai daga kallonsa domin tsoratani yake
Akuma lokaci guda nakecew
@mr:- Shuraih 99%
"Jeka abinka na gode"
Sai ya leko da kansa waje wanda ke tsugune akan
wuyansa mai guru guru
Kamar gurun diro.yaci gaba da dubana da idanunsa
wanda suke zurma zurma kamar ramin tanda ,wayanda
suka sa war ga jejen hancinsa atsakiya.
Yaci gaba da magana da bakinsa irin na kada .
"Don Allah 'yan mata kishigo mana"
Nafara matsawa
"Nagode nace dakai"
Ya biyoni yaci gaba da nacinsa. Ana hakane mota tazo
natare na shiga.
Mummunar mutumin yabini da kallo.har muka bace
masa bai motsaba , akayi tafiya har akazo inda zan sauka
nabiya kudi dana fioto.
Nakama hanya zuwa gida bayan na tako kofat gidanmu
sai naji horn din mota.
Ina waiwayawa sai naga katon mutuminnanne
"Zan dawo da daddare"
Yafada cikin daga murya kamar kwamandan sojan daya
ke bada umarni.
Bancemasa komai ba nashige gida,
Banma sake yin tinaninshi ba da daddare kuwa sai gashi
an aiko.
"Wai farida tazo inji wanda sukayi alkawari"
Na dade ina kokarin tuno waye wannan bantuna ba sai
daga baya mutuminnan yafado min a rai.
Babu shakka shine nayi tsaki na dubi dan aiken
"Kace mata waidon Allah yayi hakurin anyimata miji"
Yayi ta maido dan aiken nace masa kar ya sake shigowa.
Nama tsahi nasa sakata akofar gidanmu ganin haka sai
yatafi yayi ta zuwa gidanmu jefi jefi na ki fita har watrana
mahaifiyata tace min ya wajaba na fita banda zabi dole
hakan akayi.
Yayi ta suratansa bance masa komaiba
Sai da yagama hayaniyarsa. Wadda take bayani akancewa
wai yana kaunata ni kuwwa banga abin da zaisa na'auri
mutumin wanda yafi kama da naman daji koda kuwa
maza sun kare.
Wannan yasanya ni cewa dashi
"A gaskiya karatu nake kuma bana zaton zanyi aure sai
sama da shekaru goma"
"Indon wannanne zanyi jiranki"
Raina yabaci yanda mutumin ke kokarin likemin tamkar
kaska
"Kai kaga kaje kawai kanemi wata "
"Kece kikayi min"
Yaci gaba dafada nayi tsaki sannan nayi tahowata gida.
Washe gari yasake dawowa naki fita.
Wata washe garin sai yatareni an taso daga makaranta
yafara yimin shirme.
Nikuma kiyayyar danakeyimasa takai intaha.
Wannan yasa na kalleshi afusace
"Mallam bari infada ma gaskiyama ni dai bana kaunarka
bakuma zan kaunaceka ba , zai fima sauki kaje kanemi
daidai da kai"
Ya fashe dawata irin dariya wadda take bada amo tamkar
ana tuttule ruwa daga jarka.
Yadade yanayi har ya tsoratani ,tamkar kuma dauke
wutan nepa sai yayi shiru gaba daya.
Nan danan fuskarsa takara muni sakamakon bata rai
dayayi.
"Yarinya kinyi shirme kintafka babban kuskuren
dayakamata aganar dake"
Ya nunani da dan yatsansa mai kama da busasshen itace,
Yayi kasa kasa da murya.
"Babu duka babu zagi saidai zaki mutu babu miji"
Raina ta baci na watsa masa kasa
"Aniyarka tabika saidai kai kamutu babu mata "
Yayimin wani kallo sannan yahau motarsa yatafi.
Da ganan muka rabu da mummunan mutumin.
Baisake zuwa gidanmu bako kuma ya tareni.
Ni kuwa gani da farinjini.
Aka rinka zuwa wajena naki fita don saboda ina ganin
hanani karatu za'ayi. Don babu abinda irin da daddare
narinka nazari , ahankali na.
@mr:-shuraih 99%
Tobe conti.......
Tobe cont......
@mr:- Shuraih 99%TARAR ARADU
Littafina daya (1)
Written:- shuraih 99%
Page 5
Ni kuwa gani da farinjini.
Aka rinka zuwa wajena naki fita don saboda ina ganin
hanani karatu za'ayi. Don babu abinda irin da daddare
narinka nazari , ahankali na kammala digirina akan
mathematics .
Nakuma yi bautar kasa, sai maganar aure . Nan muka
fara soyayya da wani matashi habib , dan kasuwar kwari
ina mutuwar sonsa ana kokarin samana rana .
Watarana yazo tsallakawa titi dominisa wajen motarsa
wani mai mota yazo ya bankeshi.ko shurawa baiyiba .
Mai motar kuma yagudu"
Sai naga hawaye nazuba daga idonta .
Tacigaba
"Naci kuka har na gode Allah bayan komai yalafa sai
muka kulla da wani ma'aikacin savannah bank mai suna
isma'il soyayyar dayake nuna min hartamantar dani na
habib.
Asheshima ba rabonane ba.
Babbar motace tabi takan motarsa starlet.
Da kyar akaringa banbaro namarsa gashi kuma cikin
darene abin ya afku.
Ba'asan inda mai motar yayiba.
Hankalina yayi mugun tashi yanda kasan nayi hauka
sabida yanda nakeson isma'I'll banso habib ba,
nakasance cikin damuwa yanda samarina ke mutuwa
haka , sai natina zancen mutuminnan shkekaru biyu dasu
ka gabata.
Babu shakka shirinsane anan na shidawa mahaifiyata.
Tace saidai Addu'a tunda ba'asan inda yake ba .kuma ni
kaina tundaga ranar bansake jin duriyarasa ba.
Aifa wannan abubuwa dasuka faru suka sanya akafara
yimin son rakumin yara.
Sai dai mutum yabar kaunar dayakeyimin azuciyarsa
amma babu damar ya baiyana.
Na nesa kuwa ko mutum yafara zuwa sai naga ya janye
narasa dalili.
San dade ana haka sai wani dan'uwana yace yaji yagani
babu wani mamaci sai wanda kwanakinsa suka kare.
Saboda haka yace mahaukaci yahau kura
Sabida haka muka cigaba da soyayya abin gwanin
birgewa har ya mantar dani duk nabaya aka samana
rana.
Sai da abin yarage sati daya kawai akka tsinci gawarsa a
tsakiyar titi.
Aifa daganan sai zamto mujiya ma tafini farinjini.
Babu wani saurayi da yake fuskan tata"
Saita fashe da kuka har nayi zaton bazatayi shiruba.
Nima saida kwalla tazubo min don tausayawa taci gaba
"Wannan shine dalilin dayasa kaga naki amasa maka,
domin kuwa duk wanda ya kulla alakar soyayya dani
sunansa matacce, nikuma banso wani abu ya sameka.
Na dauki kaddara akan cewa Allah bai yi zanyi aure ba.
Domin kuwa har sai na sami wani ya dan kaunace ni
sannan zan ji sarai. Wanda ahalin yanzu abune mara
yiwuwa"
Nadaga mata hannu
"Dakata farida ni ina kaunarki"
Ta girgiza kai
"Bazai yiwuba umar banaso ka mutu sabida kaunar
danakeyi maka"
Na dubeta
"Don Allah farida da gaskene kina kaunata?"
Ta gyada kai
"Wallahi umar inayi maka kaunar da bantabayi ma wani
kamar taba"
Na mike tsaye
"To in hakane farida na daura damarar neman aurenki
koda zan mutu"
Na sun kuyo kusa da fuskarta.
"Wallahi farida babu wata wuya dazatasa na dakata"
Ta girgiza kai kuma alokacin data kirawo sunana ahankali
"Umar ,zaifi kyau kaje kasami. Wata domin samawa
kanka kwanciyar hankali"
Na bata fuska
"To ba kya kunata kenan"
Ta girgiza kai
"Bahaka bane"
"To kice kina kaunata da aure"
Tayi shiru kawai tana dubana
"To shikenan farida barinatafi tunda bakya klaunata"
Najuya cikin hanzari ,ta tare kofar na kalleta babu alamar
fara'a a fuskata
"Way or reply"
Nace da ita , murmushine yafara sauka akan lebenta
,sannan tafara fadin wasu kalmomimasu tsada
"Ina kaunarka da aure umar"
Sai wani farinciki ya mamayeni, kaunarta ya kara shiga
raina murmushi ya kubuce min.
Akuma lokaci guda dana sula le akan kujera.
Ban kula da hadarin dana ke akai ba.
"Za kiga abinda ake kira tsantsar kauna farida"
Shine abinda bakina yafara fada.
******* ********** ********
Tun daga ranar danaje gidan su farida sai ya zamo a
kowane lokaci in ina tafiya akan babur nakantafine cikin
taka tsantsan.
Kai kace mai keken daya doro ciyawa gaba da baya kuma
ya debi garke tumaki,badon komaiba kuwa saidon samun
garkuwa daga mutumin da farida tace min shine
sanadiyyar mutuwar masi neman arenta har mutum uku
Na kirga adadin makwanni cikin tafi daya.
Amma har yanzu banga abinda ya sameni ba nida farida.
Munyi matukar shiga ran juna.
Soyayya agida sannan wani salon dabn a makaranta.
Mahaifiyarta tayi matukar faribciki da soyayyarmu, baka
da baka ta fadamin
Duk samarin farinda dasuka shede bataga wabda suka
dace da juna kamar niba.
Allah yabar ku tare har abada naji dadin maganar.
Yau ranace ta lahadi da kuma muka shirya zuwa yawon
bude ido dabi da masoyiyata.
Sabbabin jacket nasiyo musamman don tafiyar ta kara
armashi
Nahadu iya haduwa. Ga wanda bai sanniba zai dauka dan
wani ne daga yayan jiga jigan garinnan nan kuwa ba haka
lamarin yakeba.
Na iso gidan su farida da misalin karfe hudu, ahalin yanzu
nazama dan gidan salllama kawai nayinashiga,
Na tarar da mahaifiyarta tana karanta wat mujallar Africa
banyi mamaki ba
Sakamakon cewa na dade da sanin cewa tan jin har shen
nasara sakamakon zama a kasar ingla na tsuguna na
gaisheta ta amasa da fara'a bisa dukkanin alamu shigar
tawa ta burgeta.
Ta nuna min dakin farida......
@mr shuraih 99%
Tobe con....TARAR ARADU
Littafina daya (1)
Written:- shuraih 99%
Page 6
Ta nuna min dakin farida.
"Tana nan inaga shiryawa takeyi"
Ba'ajimaba ta leko
"Umar shigo mana"
Na karasa ,bayau na fara shiga dakinba yanada tasari
matukar tsari.
Akalla yalunka nawa ko uku ko hudu.
Na cusa kaina

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment