Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

DUNIYA MAKARANTA

1
(Hikimomi 1-250)

Rubutawar
Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto

1

Bugawa da Yadawa:
Bugu na biyu 1437H/2016
Haqqin Mallaka @ Mawallafi

[email protected]
isbn 9960-49-972-3

2

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Gabatarwa
Yabo da godiya da’iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama su dawwama ga
fiyayyen halitta, shugaban Annabawa kuma jagoran Manzanni Annabinmu
Muhammadu, da iyalansa da Sahabbansa baki xaya.
Waxannan kalmomi na fito da su ne daga cikin Alqur’ani da Hadisai da
maganganun masu ilimi da basira da fahimtar rayuwa na da, da na yanzu. Na kuma
rubuta su ne musamman don amfanin kaina game da darussan da wannan rayuwa
take xauke da su. Kuma tasharmu mai farin jini ta Wisalhausatv ita ce take da
yaxa su a kullum safiya ta Allah domin amfanin jama’a. Haka kuma ana yaxa
waxannan kalmomi masu amfani a shafinmu na Minbarin Malamai wanda yake
group ne na faxakarwa a Whatsapp wanda ya qunshi darussa da fa’idoji masu
amfani.1
Babu shakka, wannan littafi ya samu karvuwa a fitowar sa ta farko wanda ya sa har
aka yi ta maimaita buga shi sau da dama, wasu kuma suna raba shi a wuraren
tarurruka da bukukuwan aure da makamantansu. Wannan ya daxa ba ni qwarin
guiwa wajen ci gaba da fito da waxannan Hikimomi masu amfani. Ga shi yanzu
wannan bugu na biyu zai fito a tare da littafi na biyu. Bayan haka kuma in sha
Allahu za mu buga littafin “Abokin Fira” wanda yake bayyana darussan “Duniya
Makaranta” a cikin qissoshi na tarihi masu ban sha’awa da sa nashaxi da ban
al’ajabi.
Baban Ramla
A Sakkwato
27 ga Safar 1437H

1

Waxanda suke son shiga wannan zaure za su iya aika lambobinsu ta Whatsapp
zuwa ga 08064661666. Haka kuma masu buqatar wannan littafi suna iya bugawa
ko su aiko saqo zuwa ga wannan lamba: 09030606028
3

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

1. Sauqi yana tare da tsanani. Mai haquri yana cim ma daxi. Mai kyauta ba ya
rasawa. Kowa ya ji tsoron Allah, Allah zai yi ma sa mafita. Manta da
damuwa ka fuskanci rayuwa. Kowa ka gani a duniya akwai abin da ya dame
shi.

2. Idan za ka yi alheri ka gaggauta shi, ka sirranta shi, sannan kada ka yi gori.
Wannan shi ne halin mutanen kirki!.

3. Idan ba ka iya yin sadaka daga abin aljihunka to ka yi sadaka daga cikin
haqoranka. Murmushi ga fuskar xan uwanka shi ma sadaka ne.

4. Ba kowane aiki ne qarfi yake yi ba. Wani aikin haquri ne yake yin sa!

5. Yaro akwai lokaci da qarfi amma babu kuxi. Dattijo akwai kuxi da qarfi
amma babu lokaci. Tsoho akwai kuxi da lokaci amma babu qarfi. A rayuwa
in ka samu wani abu ne za ka rasa wani. Cikakkiyar ni'ima kawai tana
aljanna. Ya Allah ka ba mu aljanna.

6. Maqiyanka mutane uku ne: Mai qin ka, da mai qin masoyinka, da mai son
maqiyinka. Mai son uwa dole ne ya so xanta.

7. Macce ce ta haife ka. Macce ce ta yi rainon ka. Macce ce kuma
uwargidanka. Ta ya ya za ka raina macce?

4

8. Uwa ita kaxai ce take manta kanta a addua, ta shagaltu da yi ma xanta. Mu
so iyayenmu.

9. Abubuwa uku ne su ke kawar da bala'i: Sadaka da Addu'a da Sada Zumunta.

10. Abubuwa uku idan sun tafi ba su dawowa: Magana da Lokaci da Mutunci.

11. Mutane iri uku ne: Wasu kamar guba suke, gudun su ake yi. Wasu kamar
magani suke, akai akai ake buqatar su. Wasu kuma kamar abinci suke, a
kullum dole ne a neme su. Yi qoqari ka zama wanda a kullum ake neman sa
saboda amfaninsa.

12. Idan ka kwanta ba ka sani ba wane ne zai tashe ka? Iyalanka ne ko
Mala'ikan mutuwa?! Zama cikin shiri a kullum don kada a riske ka.

13. Ana yin da-na-sani ne a kan magana, amma ba a cika yi a kan kawaici ba.
Kama bakinka duk lokacin da ba ka tabbatar da amfanin magana ba.

14. Kada ka damu da masu qulla ma ka sharri, duk iya qoqarinsu ba su wuce
zartar da qaddarar Allah a kan ka.

15. Alamomin tsoron Allah guda biyar ne:
a. Fadin gaskiya
b. Cika alkawari
c. Riqon amana
d. Jin tausayi da
e. Kyautata ma mutane.

5

16. Rayuwa kamar kasuwa ce. Ka zagaya ka tsinci duk abin da ka ke so. Idan
ka zo fita za ka biya duk abin da ka xauka.

17. Wanda bai iya karatu da rubuta ba jahili ne! Amma wanda ya fi shi jahilci
shi ne wanda ya san gabas amma kuma ba ya salla!!

18. Idan ka mutu an rufe labarinka, amma abubuwa uku suna rayuwa a
bayanka:
a. Ilmi da
b. Haifuwa da
c. Aikin alherin da ka shuka
19. Abokai iri uku ne:
- Mai son ka don abinka.
- Da mai sonka don kanka.
- Da mai son ka don kansa. Irin wannan yana tare da kai ne idan ka samu.
Idan ka rasa zai yi ko-sama-ko-qasa.
20. Idan ka yi fushi ka kama bakinka. Domin ba kai ne za ka yi magana ba a
lokacin, Shexan ne!

21. Kada ka bar aikin yau ka ce sai gobe. Gobe ai ta mai rabo ce.

22. Kada ka zolayi masu aikata zunubi. Dukanmu muna cikin suturar Allah ne.
Amma ka yi ma su nasiha da lafazi kyakkyawa. Duk masu laifi ba su kai
Fir'auna ba, kuma duk masu wa'azi ba su kai matsayin Annabi Musa (Alaihis
Salam) ba. Amma Allah ya ce da shi: Ka gaya ma Fir’auna magana mai
laushi, wataqila zai karvi wa'azi ko ya ji tsoron Allah.
6

23. Huda-huda tsuntsu ne da ya kawo rahoto, ya isar da saqo, ya nuna kishin
addininsa. Kada ka bari tsuntsu ya fi ka son Allah da kishin addininsa.

24. Abu Jahali cikakken Balarabe ne, mai kuxi, kuma Baquraishe. Amma yana
wuta. Bilal talaka ne, kuma bawa ne, baqar fata. Amma yana tare da Manzo
a aljanna. Aikin kowa shi yake fisshe shi.
25. Idan namiji bai ji daxin aure ba zai yi tunanin qara mata ne don ya samu jin
daxi. Idan kuma ya ji daxi zai yi tunanin qarawa don ya qara jin daxi. Mata
ku yi haquri. Qarin aure xabi'a ce a cikin mazajenku.

26. Ba zaka iya yin hukunci na gaskiya a kan mutum ba, sai idan ba ka da
buqata zuwa gare shi. Wanda ya miqa hannu bai miqe qafa! Idan baki ya ci
dole ne ido su ji kunya!!.

27. Maganar gaskiya ba lalle ne ta zama mai daxi ba, amma tana da kyau da
amfani.

28. Duk lokacin da zunubinka ya fara damun ka to, ka riga ka kama hanyar
tuba.

29. Zuciyarka ita ce adireshinka. Harshenka shi ne ma'auninka. Gyara zuciyarka
sannan ka kula da harshenka.

30. Haquri iri biyu ne: Haqurin abin da kake so idan ba ka same shi ba, da
haqurin abin da ba ka so idan ya same ka.
7

31. Idan kana tafiya babu takalma watarana za ka gamu da wanda yake tafiya
ba qafafu. Kalli wanda ka fi shi a kullum sai ka gode ma Allah!

32. Rana a cike take da wuta mai zafi a cikin ta, amma haskenta ne take ba mu.
Ba abin da kake da shi ne yake da muhimmanci ba, abin da kake bayarwa.

33. Yana da kyau ka yafe idan aka yi ma laifi. Abin da ya fi haka kyau shi ne ka
manta da laifin da aka yi ma ka.

34. Ba za ka sauka tashar nasara ba sai ka hau motar haquri da qoqari da
sadaukarwa.
35. Wani ya iya karanta komai amma bai iya fayyace abin da ke cikin zuciyarsa
ba. Yana gane aibin kowa amma bai iya ganin nasa. Laifi tudu ne, sai ka
take naka ne kake hango na wani.

36. Wanda duk ya yabe ka da qarya watarana sai ya zage ka.

37. Namiji ba ya raki! Jarumi ba ya ja da baya!! Fara ko ta mutu akwai idanu!!

38. Da yawa na nesa da kai zai amfane ka, na kusa da kai ya cuce ka. Kusancin
zuciya shi ke da amfani ba na gangar jiki ba.
39. Duk qofar da ka gan ta a rufe tana da mabuxi. Kada ka saki baki kana jiran
ta buxe da kanta!

8

40. Komai a duniya yana da mabuxi. Mabuxin ilimi shi ne tambaya. Mabuxin
nasara haquri. Mabuxin arziki tsoron Allah. Mabuxin zaman lafiya adalci da
gaskiya.

41. Hattara da mabuxai guda uku:
- Fushi, mabuxin azaba.
- Tsoro, mabuxin fitina.
- Kwaxayi, mabuxin wahala.

42. Babban mabuxin alheri shi ne Istigfari. Idan ka yawaita shi matsalolinka za
su kau, damuwarka za ta gushe, sauqi daga ubangiji zai zo maka.

43. Kafin ka yi tambaya ka yi tunanin amsar da za a ba ka.

44. A cikin mutane akwai wanda ya cancanta ka jira shi komai daxewar sa.
Wani kuma sam bai cancanta ko da ka waiwaye shi ba.

45. Komai ya fi kyau idan yana sabo amma ban da imani. Shi kam ana qara
daxewa yana qara kyau da qwari.
46. Duk yadda ka yi sai wani ya zage ka. Manta da mutane ka yi komai yadda
ya kamata!

47. Mutane da yawa ba su iya bayyana uzurinsu. Rinqa ba su uzuri ba sai sun
faxi ba.

9

48. Duk abin da za ka yi ka yi shi da zuciya xaya.

49. Kowa ya iya haquri ya iya komai.
50. Idan Allah ya ba ka lafiya ya ba ka komai.

51. Kada ka damu da abin da ya wuce, don ba zai dawo ba. Kada yau ta sha ma
kai, domin gobe ma rana ce.

52. Yafe ma wanda ya cuce ka ni'ima ce. Tuna abin baqin ciki da damuwa
wahala ce. Manta alheri butulci ne.

53. Babban zunubi ne ka ci naman wanda ya mutu. Ba za ka iya gaya ma sa a
nan duniya ba, shi kuma ba zai yafe ma ka ba a gobe qiyama!

54. Kafin ka roqi Allah abin da ba ka da shi, ka fara gode ma sa a kan abin da
kake das hi, don shi ne ya ba ka.

55. A da can mutane ba su da asibitoci amma suna da lafiya. Ba su da yawan
kuxi amma suna da arziki. Ba yawan makarantu amma akwai ilimi. Ba
hanyoyin sufuri da na sadarwa amma akwai sada zumunci. Ba su da yawan
ni'imomi, amma suna da jin daxi. Ko ka san dalili? "Albarkar abu ta fi
yawansa".

56. Babbar alamar girman kai ita ce ka raina mutane ko ka ki karvar gaskiya.
“Mutakabbiri ba ya shiga aljanna”.

10

57. Ba kowace faxuwa ce matsala ba. Da yawa wanda zai faxi amma idan ya
tashi ya sheqa ba ka iya cim ma sa.

58. Idan ka saka kuxi a account ko ka cire kana samun alert na abin da ya rage
ko ya qaru a cikin jarinka. Ina ma ace duk lokacin da ka yi qarya ko sata ko
ka ci naman xan uwanka za ka samu alert na yawan zunubinka? Ko kuma
idan ka yi sallah ko azumi ko sadaka za ka samu alert na yawan ladar da ake
ba ka? A kullum ka aikata savo ko xa'a haka tana faruwa, amma Mala'iku ne
suke lissafa ma ka suna rubutawa, kuma za su haxa rasitinka gaba xaya a ba
ka gobe qiyama, a buga total, a fitar da sakamako, sannan a yanke hukunci.
Allah ka sa muna shiga aljanna.

59. Kada ka cuci wanda ya cuce ka. Sharri kare ne, ko ya yi nisa sai ya dawo
ma mai-shi.

60. Abu mafi sauqi wajen tunkuxe cuta shi ne ka manta da an cuce ka.

61. Idan ka ga mutum yana tsarguwa da shiga cikin jama'a, shi maha'inci ne.
Idan ka ga mutum yana fushi a wurin jayayya to, maras hujja ne. Idan ka ga
mutum yana faxa, ba shi da abin faxi. Mai gaskiya ba ya tsoron jama'a. Mai
hujja ba ya fushi. Mai abin faxa ba ya faxa!

62. Fulawa tana koya mana fara'a da murmushi. Tururuwa tana koya mana aiki.
Zuma tana koya mana tsari. Zakara yana koya mana sammako. Kowace
halitta da tata gwaninta.

11

63. Wanda ya fi kowa jin daxi a cikin mutane shi ne wanda bai damu da
sha'anin mutane ba.

64. Ba duka wanda ka ke so ne yake amfanin ka ba. Ba kuma duka wanda ka ke
qi ne yake cutar ka ba. Wuqa ko tana da laushi yanka take yi, magani kuma
tare da xacinsa ana samun waraka a cikin sa.

65. Da zarar ka ji qarar wayarka ka san wani yana son magana da kai ne. Kamar
haka ne da ka ji kiran sallah ka san ubangijinka na neman ka. Kada ka sanya
karva kiran mutane ya fi ma ka muhimmanci a kan kiran Allah.

66. Sirri kamar dafi yake a cikin zuciyar Macce. Idan ba ta fito da shi ba sai ya
kashe ta. Yana da kyau ka san inda za ka voye asirinka!.
67. ‘Yan uwan Annabi Yusuf sun yi niyyar kashe shi, Allah bai kashe shi ba.
Sun so su qasqanta shi, Allah ya xaukaka shi. Su ka vatar da shi don
mahaifinsu ya manta da shi, ya daina son sa, amma sai Allah ya qara masa
son sa. Aka sayar da shi a matsayin bawa amma ya zama Sarki. Kada ka
damu da sharrin xan Adam. Allah gatan Bawa.

68. Akwai miliyoyin halittun ubangiji waxanda ba su da aljihu, ba asusun ajiya
a gida ko a banki. Amma ba su daina cin arziki ba. Kwantar da hankalinka.
Arzikinka yana nan ba zai wuce ka ba. Nemi halaliya, don ba ka wuce
arzikinka. Saurin nema ba ya kawo samu.

12

69. A Hotel ake rubuta cewa, "idan mun burge ka ka faxa ma duniya. Idan mun
vata ranka ka faxa mana". Wannan shi ne yadda ya kamata ka yi hulxa da
kowane musulmi xan uwanka.

70. Abu xaya ne kyakkyawa wanda ko makaho yana iya ganin sa. Shi ne
kyawon hali. Ka zama mai kyawon hali ba sai ka faxi ba mutane da kansu za
su yabe ka.

71. Da dare kowa yana rufe qofarsa ne don tsoron mutane. A lokacin ne kuma
Allah ya ke buxe qofofinsa don karvar mutane. Ko kana qwanqwasa qofarsa
ta hanyar salloli da zikiri da addu'oi da tilawa a wannan lokaci?

72. Kada jin daxin wani ya tsone ma ido. Ba ka san abin da ya rasa ba kafin
Allah ya ba shi ni'imar da yake cikin ta. Kada damuwarka ta tada
hankalinka. Ba ka san alherin da za ta jawo ma ka ba. Haquri maganin
zaman duniya.

73. Idan ka makara a wajen aiki kana jin kunyar shugabanka. Idan ka makara
zuwa masallaci ko kana jin kunyar Allah?

74. Idan yaro ya yi wayo kyawonsa a sa shi makaranta. Idan ya girma kyawonsa
a gan shi a masallaci. Macce ita kuma kimarta idan ta girma tana a gidan
mijinta.

75. Kamilin mutum shi ne wanda ya tara ababe guda uku: Ga kyauta, ga dadin
zama, ga kuma yawan ibada.

13

76. Rinjayar mai qarfi ba shi ne gwaninta ba. Gwani shi ne wanda ya iya
bakinsa, ya rinjayi zuciyarsa, sannan ya ji tausayin na qarqashinsa.

77. Idan ka ga tururuwa ka xage qafarka don kar ka take ta, za ka gamu da
rahamar Allah don ka ji tausayin wata halitta daga cikin halittunsa. To ya ya
ka ke ji idan ka tausaya ma xan Adam mai daraja a wurin Allah? Ina kuma
ace wanda ka tausaya ma musulmi ne mai fuskantar gabas ya yi sallah?

78. Zunubi da savon Allah suna cike da shu'umci. Sukan sa ka da-na-sani, ko su
ja maka hasara, ko su hana ka riba, ko su mantar da kai wani alheri, ko su
zubar da girmanka, ko su bayyana aibinka, ko su jawo rinjayar maqiyinka a
kan ka, ko su tozarta dukiyarka. Ga shi kuma suna ja maka fushin Allah da
tozarta a cikin jama'a. Nisanci zunubi don ka zauna lafiya.

79. Matsalolinmu a yau guda biyu ne: Mu yi aiki kafin mu yi nazari, ko mu yi
ta nazari ba aiki.

80. Idan ka taimaki wani saboda Allah kada ka jira ya yi maka godiya. Yardar
Allah ta fi yardar mutane.

81. Yana da kyau ka damu da damuwar xan uwanka. Abin da ya fi wannan shi
ne ka taimaka ma sa domin ya fita damuwa.

82. Kyau iri uku ne: Akwai kyan jiki, akwai kyan hali, akwai na zuciya. Kyan
zuciya shi ke sada ka da Allah. Kyan hali yana sada ka da mutane. Kyan jiki
kuwa a kullum sai ya ja ma ka fitina. Duba tarihin Annabi yusuf Alaihis
Salam.
14

83. Abin da ka koya da farko a cikin addini shi ne abin da za a tambaye ka a
cikin qabarinka. Ba tarin ilimi ke da muhimmanci ba. Amfanin ilimi aiki da
shi.

84. Magana tsuntsu ce. Idan ta fita ba a iya kamo ta. Ka iya bakinka don kada
ka kwana cikin da-na-sani.

85. Wanda ya fi kowa girma shi ne wanda bai ganin girman kansa. Wanda ya fi
kowa xaukaka shi ne wanda yake amfanin mutane.

86. Mace ta gari tana neman yardar Allah da biyan buqatar mijinta. A gidanta
ba qazanta, a jikinta ba cuta, a waje ba a jin muryarta. Daga nesa idan ka
hango ta ba ka gane ta saboda kamalar suturarta da kwarjinin hijabinta.
Muguwar mace ita ce mai yawan kiran ciwo, mai gajiyar haquri, mai
kaushin magana, mai dogon harshe, mai kukan qarya, mai tona asirin gida.

87. Mutum yakan qosa da quruciya, amma idan ya girma zai dawo yana begen
ta. Yana qarar da lafiyarsa wajen neman kuxi sannan ya sa kuxi yana neman
ta.

88. Wahaltattun mutane a duniya su biyu ne: Wanda Allah ya kawo lokacin abu
ya ce ba za ayi shi ba, da wanda Allah bai kawo lokacin abu ba ya ce sai an
yi shi. Ka yarda da hukuncin Allah, shi ne zaman lafiya a gare ka.

89. Babbar hasara a lahira ita ce ka samu ladarka a cikin littafin wani, ko ka
samu zunubin wani a cikin littafinka. Kada ka zalunci mutane. Kada ka
15

shiga cikin haqqinsu. Idan ka yi haka za su washe ladarka ko su lafta ma ka
zunubinsu.

90. Masoyinka shi ne wanda yake kare ka idan aka aibata ka. Maqiyinka a
kullum fatar ya ke yi ka tozarta.

91. Rayuwa taqaitacciya ce. Kada ka cika ta da damuwa. Kada dogon guri ya
xauke hankalinka daga mutuwa. Aikata alheri a kowane lokaci wataqila shi
zai zamo mabuxin aljanna a gare ka.

92. Sau da yawa mu ke kuskuren fahimtar mutane. Ma'aunin da ba ya kuskure
shi ne ka ajiye kanka a matsayin wanda kake yi ma hukunci.

93. Idan ba ka son a soke ka kada ka ce komai, kada ka aikata komai. Duk
wanda ya motsa dole ne sai an soke shi.

94. Mafi hankalin mutane shi ne wanda ya bar duniya kafin ta bar shi, ya gyara
qabarinsa kafin ya shige shi, ya yi sallah a cikin jama'a kafin su sallace shi,
sannan ya yi ma kansa hisabi kafin a gurfanar da shi a ranar hisabi.
95. Ba ka sanin daxin lafiya sai idan ciwo ya same ka. Ba za ka san daxin
zaman lafiya ba sai ka gamu da tashin hankali. Ana sanin daxin haxuwa ne
idan rabuwa ta zo.

96. Idan kwalba ta fashe za a ji kukan fashewarta ne sau xaya amma za a taka ta
sau goma. Haka mummunar magana ta ke idan aka faxe ta, za a ji ta sau
xaya, amma za ta daxe tana zungurar zukata.
16

97. Aboki guda xaya ne zai taya ka kwanciyar qabari. Shi ne aikinka. Aikata
alheri don ka samu aboki na qwarai a wannan kogo da ba shi da makawa.

98. Abu uku su na vata lokaci ne: Da-na-sanir abin da ya wuce kuma ba zai
dawo ba, da neman yardar mutane gaba xaya kuma ba za ta samu ba, da
haxa kanka da wanda ya fi ka kuma ba za ka cim ma sa ba.

99. Wanda ya fi ka wadata ba lalle ne ya fi ka arziki ba. Wadatacce shi ne
wanda yake samun biyan bukatunsa.

100.

Idan ka ga mutum yana sukar xan uwansa bai lura da nasa laifin ba.

Ko sukar xan uwanka da ka ke yi shi ma aibi ne.

101.

Wani aboki yana bin ka don ya koyi alherinka. Wani kuma yana bin

sawunka don ya kama laifinka. Rinqa hattara da abokai.

102.

Wani mutum idan ka yi ma sa alheri zai saka maka ne da sharri. Idan

ka amfane shi zai cuce ka. Idan ka sa shi inuwa zai jefa ka a rana. Kada ka
damu. Ka ci gaba da yin alheri, kowa halinsa ya ke yi.

103.

Da yawa mutanen da muka san su, muka yi hulxa da su a yau sun riga

mu gidan gaskiya. Idan yau mu ne, wata rana ba mu ne ba.

104.

Idan ka ga mutane suna tururuwa zuwa gidanka abin buqatarsu ne

Allah ya ajiye a wajenka. Idan ka rasa shi kowa zai kama gabansa. Kada ka

17

nemi hutu daga taimakon jama'a. Xaukakarka ita ce buqatuwar su zuwa gare
ka.

105.

A wuri uku ake sanin halin mutum: Idan aka ba shi aure, ko aka yi

ciniki da shi, ko aka yi tafiya mai nisa a tare da shi.

106.

Ba kowane lokaci ne mutane za su fahimce ka ba. Qaramar

qwaqwalwa ba ta gane manyan kalamai. Babban kifi sai babbar gora.

107.

Ana sanin darajar mutum ne ta hanyar halinsa ba ta hanyar matsayin

gidansu ba. Gina kanka da kanka. Ka daina gadara da matsayin gidanku.
108.

Da yawa waxanda ke ce ma 'ya'yansu: "Ina son ka zama Likita" ".. Ka

zama Injiniya" ".. Ka zama Malami". Mutum nawa ne su ke ce ma xansu: "
Ina son ka zama mai albarka, mai taimakon jama’a"?

109.

Kada ka damu da cewa qarya ta miqe qafa. Tabbas qarya za ta gushe.

Kada ka damu da tambayar yaushe ne gaskiya za ta bayyana? Lalle za ta
bayyana komai daxewa. Abin da ya kamata ya dame ka shi ne, mine ne
matsayinka; a kan gaskiya ka ke ko a'a?

110.

Rayuwa a kullum cikin canji take. Yaro zai girma, babba ya tsufa, mai

lafiya ya yi ciwo, wani mai ciwo ya warke, rayayye kuma ya mutu. Lokacin
da ka samu sannan wani zai rasa. Idan ka faxi wani ne zai tashi. Rungumi
hukuncin Allah a cikin amincewa da yarda.

18

111.

Alamun mai riya guda uku ne: A fili yana sallah, a voye yana wasa.

Idan an gan shi an ga mumini, idan ya kevanta ya koma fasiqi. Bakinsa ya fi
zuciyarsa qarfi. Allah ka kare mu daga sharrin riya.

112.

Abu uku ba a wasa da su: Addininka, da qasarka, da mutuncinka. Abu

uku ba a faxar su: Arzikinka da Iliminka da yawan shekarunka.

113.

Ba kowace magana ce ake ba da amsar ta ba. Ko shiru magana ce.

114.

Sana'arka arzikinka. Annabi Dawuda maqeri ne. Annabi Zakariyya

kafinta ne. Annabi Idris maxunki ne. Annabinmu makiyayi ne. Nemi na
kanka. Zaman banza babbar cuta ce. Arziki kuma zomo ne. Zomo ba ya
kamuwa daga kwance!

115.

Yi murmushi idan ka ga mai son ka, zai ji daxi. Yi murmushi idan ka

ga mai qin ka, zai ji tsoro. Yi murmushi idan ka ga wanda ya bar ka, zai yi
da-na-sani. Yi murmushi ga wanda ka sani da wanda ba ka sani ba.
Murmushi kwarjini ne ga namiji, ado ne ga

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment