Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

*ƘASAITA BOOK 1*


*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*


Page 1


Mota ƙirar ƙasar (South Korea) ce ta tsaya a dai-dai ƙofar wani kanti, wanda zamu iya kiranshi da suna na tailoli, ma'ana shagon ɗinki kenan,Mai suna Almansir Tailoring and Fashion Design Company. Mutumin ƙofar shagon shi ya nuna mana cewa mata da maza na iya kai ɗinki a shagon. Ruwan toka ash colour shi ne fentin motar, wanda zamu iya kiran motar da suna KIA Saloon.

Farar yarinya ce,za mu ce ko budurwa, ita ce matuƙiyar motar, wacce ta fito sanye da riga da wando zubin (Suits) irin na ƙasashen tsallake (Abroad) amma na mata, kenan mai shimi mai babban maƙwancin hannun kafaɗa, sai doguwar riga ƙwat ta ɗora a sama, wacce ta kai mata har wucewar gwiwa.

Maɓallin tsakiyar doguwar rigar ƙwat ɗin ne kawai ke maƙale da rigar, ruwan toka ne ash colour kalar kayan nata. Takamin ƙafarta kuwa baƙi ne, tare da farin gilashi manne a saman dogon hancinta, wanda mafiya yawan likitoci ke sanya irin shi.

Babu komai a hannun ta sai kan wayar zamani ta Ipad,gashin kanta kuwa a sake yake wanda za mu iya cewa ya kai tsakiyar bayanta,babu wani alamar ɗanƙwali balle mayafi a saman kanta, kallo ɗaya za ka yi mata sai ka maimaita goma a lokaci ɗaya baka sani ba.

Tabbas yanayin yanda take kulle motar ta kawai zai iya nuna mana mace ce mai taƙama da ƙyan da Allah ya bata, zan iya cewa kuma ita kanta ta san duk inda ta gifta sai ta tsayar da ayyukan mutane, shi yasa na fahimce ta mai jiji da kai.

Doguwa ce, amma ba shal ba, yanayin kiran zubin jikinta kuwa,za mu iya kamanta shi da na Pretty Zeeta, ƴar ƙasar India. Kai kallo ɗaya ma ka yi mata za ka iya ce mata ba ƴar ƙasar Najeriya ba ce, saboda yanayin zubinta ya fi kama da na ƴan (Miss World),Sarauniyar ƙyau ta duniya.

Yatsun hannunta kuwa zara-zara suke, waɗanda suka sha fentin ƙwalba (Lamp paint) a saman faratanta, shi ma ruwan toka, faratanta sunyi tsayi kamar ƴan kanti, ta saka a yatsun ta. Sai da ta ɗan ɗauki sakan biyar, sannan ta sa makulli ta rufe motarta.

Ɗagowar da zata yi kuwa, sai da ta rausaya da gashin saman kanta da ya zubo mata a fuskarta,a lokacin da take kulle motarta, sai da ta duba hagu da damarta, sannan ta tsallaka titin da ke a gaban,MONAK STORE, shi ta shiga.

Tsayin minti talatin da baƙwai na yi ina dudduba kayan ƙwadayin da ke kaini duk wata (Super store), cakulet (chocolate) dasu Chingam (Chewing gum) sannan biskit (Biscuits), irin waɗanda na mayar abinci na,kayan ƙwalliya kuwa sai dai in dinga ɗaukar kala-kalar jam baki da man leɓe (Wetlips).

Leda ce a hannuna wacce aka cika ta da rubutun sunan kantin da na fito,ƙarar wayar dake hannuna, ita ta ɗan ɗauke mini hankali,a bisa tafiyar da nake yi.

"Ka san dai bana magana a titi, sai dai kayi haƙuri bayan mintuna arba'in ka bugo,a wannan lokaci na isa gidan Aunty,okey, thank bye."

Maganar da nayi a waya kenan da (Proposed) ɗin da na tsayar a matsayin wanda zan aura nan da ɗan lokaci ƙanƙani, don ma ina ja masa rai, saboda tunanin barin gida, wannan yake ɗan tayar mini da hankali.

Zamu iya cewa yanayin da muke ciki na sanyi duk da dama mun san Garin Jos gari ne mai ni'imar gaske, dalilin haka ne ma Turawa da sauran fararan fata,sun fi yawa a can, saboda sabo da suka yi na jin sanyi a ƙasashensu.

Wannan yanayi na yau ya sha bamban da na kullum,tun da yau sanyin da sauƙi, sai dai iska da ake hurawa a hankali mai ratsa jiki, wadda za ta iya saka nishaɗi. Na ɗaga kaina sama ina kallon giza-gizan sanyi na tafiya cikin natsuwa,gashin kaina kuwa iska ke yi mini wasan ball da shi, ina faman buɗe fuskata.

Tabbas na hango motoci a tafe, amma ganin nesa suke da ni yasa na kalli ɗaya gefen nawa, na tsallaka titi, iska ta watsar mini da gashin kaina wanda ya watsu a fuskata, ina ƙoƙarin buɗe fuskata ne na ji mota ta kai mini zungura, take na faɗi zaune a ƙasa tsakiyar titi.

Ƙarar jan birki ita ta sa na ɗora hannayena a saman kaina, ina jiran ƙarfen Nasara ya bi ta saman kaina. Tsawa na ji an daka mini da ƙarfin gaske, wannan yasa na yi saurin ɗago kaina, haushi ya kama ni a take da na ga ashe daga motar baya ce ma ake yi mini wannan tsawar, ta gabana kuwa mai zubin (Cardillale Lemousine) wacce ta banke ni kenan doguwa mai ƙofa uku.

Baƙin gilashi ne daɗe da ita,babu alamar zugewa, balle in samu tabbarakin ganin ko naji ciwo, wannan ya ƙara tunzura mini zuciya,na miƙe da sauri na sa hannuna na daki gaban motar, daga sama suka faɗo,ko ko ta ƙarƙashin ƙasa? Oho ƙartin mutane ne masu kaya layi-layi, wanda na ga layin ya ƙunshi kala biyu. Dogarawa kenan, waɗanda aka fi saninsu a gidajen masarautu.

Ko gama gane su banyi ba, cikin dishi-dishin idanuna na ga wani ƙato daga cikin su ya ɗaga hannu zai kai mini mari,cikin zafin nama na riƙe hannunsa, duk da sai da hannuna ya yi kamar zai karye biyu,tsayawar shi kuwa kusa da cinyata, saboda yafi ƙarfina.

Ƙwanƙwasa baƙin gilashin muka ji anyi daga cikin motar nan ta gabanmu, shi yasa gaba ɗayanmu hankalinmu ya koma ga gilashin da yake sauka a hankali. Ƙyakkyawan mutum ne,sanye da manyan kaya na alfarma,ƙwance a kusurwar mota (Owner's Corner) zan iya ganin gashin bakin fuskarsa mai suna ƙwata miliyon (Quater Million) farin gilashi ne manne a fuskarshi, duk cikin sakan ɗin da bai wuce uku ba na karanto hakan.

Sai da ya yatsina tamkar mace, sannan ya motsa jikinsa da ƙyar, ya ƙara gyara ƙwanciyarsa a kusurwar motar, da ƙyar ya ɗaga hannunsa ya cire gilashin fuskarsa. A tunanina magana zai yi, amma sai naga ya yi masu alama da kai, ma'ana ya girgiza kai,hannunsa mai gilashin nan ya ɗan ɗaga ya yi masu alamar su koma cikin motocinsu. Daga wannan kuwa sai dai na ga baƙin gilashin motar nan na komawa sama mazaunin sa a hankali, har gilashin ya kusan rufewa, sai na ga an cillo bandir ɗin ƴan ɗari biyar-biyar ƙwaya ɗaya,an ja motar an tafi.

Ban san lokacin da na kaiwa bayan zumɓutun motar nan duka ba da ƙarfina, amma ko tsayawa ma bata yi niyyar yi ba. Wucewarsu ke da wuya mutane suka taru a kaina suna yi mini sannu, a cikin su ne wata mata,ɗaure da zani da riga masu buɗaɗɗen hannu ta kama ni, da ganin ta kaga yare, da harshen Turanci ta yi mini maganar sannunta.

"Sorry wooo!"

A nan ne take gaya mini wai na ci arziƙi, saboda ina da ƙyau, da yau sai an ɗaure ni nasha dukan ƙarti,ban san ko waye ba a cikin motar,wai ɗan Egwe ne mai jiran gado a hausarmu kenan Yarima,yaren da ta faɗa kuma He is the Prince,ta dinga rawarsu ta yare cewa take.

"You Are very luck woman." Wai in yi sauri in ɓace daga nan kada a aiko a ɗauke ni. Wani mugun haushi da baƙin ciki ya kama ni a take.

Su kuwa sai miƙa mini kuɗin nan sukeyi, sai cewa suke Allah na sona, na waiga na kalli mutanen da ke zagaye da ni dukkansu ba mai rigar da ta wuce dubu ɗaya, na kalli matar nan, sannan na karɓi kuɗin a hannun wani namiji wanda ke ta faman miƙo mini su,na miƙawa matar nan, sannan na ce.

"Madam go and share it. Na ɗauki ledata na isa ga motata,ni kaina sai fadanci suke yi mini wai Allah ya taimake ni.

"Good bless you."

Gidanmu na nufa kai tsaye, saboda haushi na fasa isa gidan Auntynmu. Get ɗin gidan da motata ta tsaya ina yin horn mai ruwan jinin kare ne (Maroon colour) fentin gidan kuwa fari ne da ratsin ruwan Maroon colour. Maigadin gidan bai wuce ɗan shekara arba'in da biyar ba,ƙaton yare maji ƙarfi da shi, shi ya leƙo sannan ya buɗe mini ƙofa da rawar jikinsa.

Da gudu ya iso ga motata, kamar yanda ya saba, amma yau ban tsaya saurarenshi ba,ko rufe murfin motar ma ni ban tsaya yi ba, balle ledar kayana ko wata waya can.

Da gudu na haye matattakalar,benen da ke ƙofar shiga gidanmu, wacce zata kai biyar. Ƙofar gilashi ce mai ƙwarin gaske, amma da hannu ɗaya na tura ta na shiga,ban tsaya ko'ina ba sai (Set room) ɗin Babana,ɗakin shaƙatawa, da ƙyar na iya yin sallama, na shiga yana kishingiɗe a saman lallausan kafet ɗin tsakiyar falo, wanda musamman aka saka shi a gefe ɗaya na falon, wanda ƙasan shi katifa ce mai laushin gaske, inda yake ɗora hannu kuma tuntaye ne na fatar damisa har guda huɗu a zagaye da shi.

Kujeru ne ƙwaya uku kacal, masu zubin irin na teburin cin abinci,a gefenshi zagaye, wanda in kazo gaishe shi,ko ya yi baƙi,yana wajen za su zauna a kai su gaisa,ko wacce kujera da ɗan tebir a kusa da ita da jarida (magazine), a saman shi,in za a kawo ruwa ko lemu,a sama za a ɗorawa kowa.

Ya fi yin wannan kishingiɗa daga bayan sallar la'asar zuwa ta magriba, daga nan kuma sai wajen ƙarfe taƙwas da rabi na dare idan har yana gida. Ina shiga na zauna ɗaya daga cikin kujerun alfarmar da suke a tsakiyar falon, cikin sigar shagwaɓa nake kukana.

Babana ya saba da shagwaɓata, saboda haka sai ya yi dariyarsu ta manya.

"A'a Yasmin yaya? Ko wani ne ya ɓata miki rai ne? Taso in ji,taso inji autar Daddy. Come and tell me my dear."

Na tashi na isa na durƙusa a gabanshi, kafin in yi magana Mamata wacce muke kira da Mamee ta shigo, Babanmu kuwa muna kiranshi Dad.

Tana shigowa ta fara faɗa, "wallahi My Dear,kai ke ƙara shagwaɓa yarinyar nan, shi yasa kullum take ganin ta kamar ƙaramar yarinya, ta ƙi tsayawa ma ta ƙwantar da hankalinta ta fito da miji a yi mata aure ma mu huta, ina dalilin sakarci irin wannan? Wallahi na kusan gajiya zan haɗa kanki in auna da ke Syria in huta,ko bakina ma ya gajarce."

"Dad kaga Mamee ko bata so na, yanzu da Aunty ce dakaga sun shige ɗaki sun koro ni waje, amma ni kullum ta dinga yi mini faɗa."

"Ki yi aure ki gani in na ƙara yi miki haka."

"Dad..."

"Ke sorry ƙyale ta,ban ma san wanda ya kira ta ba, fita My Dear kada in taso miki nan."

"Allah ya huci zuciyarka duk dai son da ake mata,ni dai wajena ba shi da amfani, tunda an ƙi yi mata aure shekara ashirin da uku. Ni kuwa tawa ɗiyar tun da sha taƙwas nayi mata auranta."

"Fita na ce ko!" Ya faɗa har da ɗan tashi daga kishingiɗar da ya yi.

"Na yi shiru sorry."

"Nayi nima, dawo nan to ki zauna." Ya nuna kusa da shi kaɗan ta taso ta zauna, sannan ya ce, "Okey, talk my daughter."

*Dad,dama da na fita ne wani ya bankeni da mota."

"What?" Ya faɗa har da tashi zaune.

"Wa ye shi?"

"Nima ban san shi ba na faɗi kuma wai sai yasa wasu za su dake ni."

"How is that senseless man?" Ya tashi zaune sosai.

"Okey, tell me."

"Dad,kuma ya ja motarshi ya yi tafiyarsa,wai don raini ma har da jifa na da kuɗi. Dad ko magana fa ba ya yi, da kai da hannu yake ba su duka (Instruction)."

"To waye ubanshi a garin nan?"

"Oho,ni dai na ji mutanen da suka zagaye ni bayan ya tafi suna cewa wai ko ɗan waye ma, oho,fa don haushi ban tsaya tambayarsu ba. Dad da ƙyar fa yake motsi,ƙwance yake a bayan mota."

"Zaki iya gane shi in kin ganshi yanzu?"

"Eh Dad."

"To duk lokacin da ki ka ganshi ki ɗauko mini lambar motarsa da sunanshi kawai ma sun isa, zan haɗa shi da hukuma tunda haka sukeyi wa mutane sakarci a gari."

"Haba My Dear, ya za ka biyewa zancen yara ka je kaji kunya."

"A'a zan sa a koya masa hankali, ba wai don ya taɓa ƴata ba, illa saboda nan gaba, tunda da gani haka suke yi wa mutane,don suna taƙama da iyayensu na da kuɗi."

"Wallahi Daddy da gaske ne,ka ga ma kayana yanda suka koma,ƙafata ma sai ciwo take yi."

"To anji Allah ya bada sauƙi, tashi ki je ki sha (Panadol) fanadol.)"

"Dad ka ga Mamee ko?"

"Ke ƙyaleta,je ki abin ki ke dai ki yi mini aikin da na saka ki kinji ko?"

Na ce, "To." Na tashi na tafi.

Ina isa falo na samu Katung a tsaye. Katung mutum ne mai ban dariya, ga iya bin hanyoyin da zai saka ka cikin farin ciki,ko da ranka a ɓace yake. Ai kuwa nan ya dinga bin hanyoyin shi da ya saba, har sai da ya saka ni dariya a dole. A nan ne har ya samu damar tambayata, na ƙwashe duk abin da ya faru na gaya masa.

A nan ya ce in har na gane ko waye, to shima fa zai bayar da gudummawarsa, ya ɗan ba ni ƙwarin gwiwa, sannan ya miƙo mini kayana,har da makullin motata, waɗanda na manta da su ƙwata-ƙwata, sannan na haye ɗakina, na jefa kayana saman gado na wuce banɗaki kawai, saboda in shiga ɗan ruwan ɗumi ko naji ɗan daɗin jikina.


**** **** ****

Plateau State,wacce jama'a suka fi kira da suna Jos. Jos gari ne wanda Allah ya yi masa ni'imar sanyi da duwatsu kala-kala, ga wajen ƙwanciyar ruwa yana dashi. In kayi la'akari da Jos,za kaga yanayinta ya fi kama da ƴan ƙasashen tsallake (Abroad), ire-iren wannan ne ya sa garin kullum tamkar ana damina.

In kuwa lokacin sanyi ya zo,....

*ƘASAITA BOOK 1*


*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*


Page 2


In kuwa lokacin sanyi ya zo, sai ka ga har ƙananan dusar ƙanƙara ke zuba wasu lokutan (Snow), amma saboda sabo wannan duk baya hana mutanen garin yawonsu da hidimomin su. Wannan kuma yasa yawancin Turawa da sauran ƴan ƙasashen duniya ke zama a Jos. Asali ma ƴan garuruwa da ƴan ƙasashe daban-daban sun fi yawa a garin.

Sai dai mutanen garin Jos, yawancinsu sun fi baiwa (English wears) mahimmanci, ƙananan kayan turawa. Wannan dalili ne ma yasa ko a tarihin Jos, shi ne garin da aka fara kawo kayan gwanjo daga ƙasashen duniya, shi yasa har yau kuwa ita ce kasuwar duniyar Gwanjo ga wuraren da shagunan siyar da sababbin kayan turawa (Boutiques) sun yi yawa.

Jos gari ne wanda ya saba da jama'a kala-kala, wasu in ka samu tarihinsu sun daɗe sosai a garin, wasu ma ba su san asalin inda garin iyayensu da kakanninsu yake ba. Wannan dalilin ma ya haddasa samun harshen yare da dama a garin, wanda a iya ɗan ƙiyastawa za a iya samun harshen yare ya kai kusan ɗari biyu a garin, wannan yasa suka ɗauki Hausa Central Language ɗinsu. Sai dai sun ɗan fi amincewa da Turanci,ko da kuwa irin turancin da aka fi sanin ƴan Legas ko kuma mutanen Ibo,wato (Broken English).

Yanzu haka sana'o'in masu kuɗin ba su wuce shigo da motoci, da kayan sawar turawa da Gwanjo, amma za a ga masu kuɗinsu na yawo da ƴar ƙaramar sanda mai lankwasashen masa. Ni kam garin na burge ni, saboda wuraren shaƙatawarsa, amma fa sunayen Hausawansu duk irin sunayenmu ne. Wannan kuma bai hana su yin karatun zamani ba, wato makarantun boko, ga shi akwai Islamiyoyi a garin, kamar yanda aƙwai wajen bautar yawancin wasu yare Choci.

Mahaifina kuwa ɗan asalin ƙasar Najeriya ne,a jahar Adamawa, wacce take kusa da jahar Taraba. Suna wani ƙauye wai shi Gembo. Iyayenshi duk ƴan asalin can ne, amma duk Allah ya yi musu rasuwa, tun yana ɗan yaro,a hannun Yayan Babansa ya girma. Mahaifinmu bai yi karatun boko ba, a lokacin da yana garin Gembo.

Saboda a lokacin ba a waye sosai da karatun ba. Asali ma abin da ya hanashi karatun mariƙinshi talaka ne sosai, sai dai sun yi karatun allo, wanda har sun yi sauka. An taɓa yi masa aure a ƙauyen Gembo wanda dalilin auran ne suka yanke shawara shi da abokanshi su fita neman kuɗi.

A lokacin yana shekara sha takwas kaɗai. Sun fara tsayawa Kano tsawon shekara ɗaya,a inda ya fara sana'ar siyar da rake a ƴar kura (baro), shi ma ta haya ce ɗaya daga cikin abokansa,ko in ce abokin wasanshi, saboda ɗan mace da ɗan namiji suke, shi ne ya kama sana'ar Gwanjo a kasuwar Ƙofar Wambai.

Tun yana tsaro ana biyanshi, har ya fara ɗan sarar nasa yana yawo da su a hannu, ganin yana samu yasa ya janyo hankalin mahaifina da ya daina sana'ar rake ya koma ta Gwanjo, da ƙyar ya amince.

Ganin sun ɗan bunƙasa kaɗan yasa suka yanke hukuncin zuwa Jos su dinga sarowa. Zuwansu uku,ana huɗu ya yi shawara da yayan Babanshi ya amince suka koma Jos da zama, shi da kanshi bai san ya bar matarsa da ciki ba,sai dai haihuwa aka aiko masa.

Saboda ya ce mana sukan yi wata baƙwai,taƙwas ba su je gida ba. A ranar da ya isa gida, a daren matarshi mai suna Huraira ta rasu, lokacin ƙwananta uku da haihuwa,ana gobe sunan yarinyar da ta samu, ita ma ta ce ga garinku nan.

Shi ne tun da ya baro Gembo bayan an gama makoki da sati uku, daga shekara sai shekara yake komawa garin, domin gaishe da wan Babanshi Alhaji Tsalha. Har yau kuwa yana nan da rai, sai dai ya tsufa.

Ikon Allah yasa suka shiga makarantar yaƙi da jahilci,su wai don saboda su iya maganar ciniki da yaran garin,a haka kuwa suka yi fice wajen iya komai, aka sa su, suka zama zakaru a ajin.

Wannan yasa aka tura su Sakandire ta garin da suka gama, aka dinga bin su da aiki. A lokacin neman masu karatun ake ba kamar yanzu ba. Cikin ikon Allah Daddy na har digiri ya yi inda ya haɗu da mahaifiyata kenan ita ma tana digiri ɗin ta a kan Education, shekararta ta farko.

Shi kuwa yana shekarar ƙarshe ta kammala digiri ɗinsa,a lokacin yana ɗan shekara talatin da biyar kenan. A shekara sha ɗaya ya je Jos, ya yi shekara ɗaya ashirin kenan, suka yi yaƙi da jahilci shekara biyu, Sakandire shekara shida, shekara biyu sharar fagen shiga jami'a, Diploma kenan, sai haɗa digiri shekara uku, sai kuma kammalawa da bautar ƙasa ya ɗauke shi shekara biyu.

Tunda Allah ya haɗa Momeena da Dad ɗina, Mahaifinta ya nema masa aiki a ma'aikatar (NNPC) ta Jos, ya kama masu wajen zama. Mameena gidan Dad ta kammala karatunta na digiri, da tana aiki a ma'aikatar Ilimi (Ministry of Education), amma daga baya Dad ya hana, saboda maza da suka dame ta. A hankali har Allah yasa komai nasa ya bunƙasa, amma har yanzu sana'ar shigo da kayan Gwanjo tana nan Dad na yin ta,irin tasu ta manya-manyan ƴan kasuwa.

Saboda yanzun haka, ba ya aikin gwamnati, sai dai siyar da motoci da harkar Gwanjo da ta safarar kayayyaki ƙasashen duniya. Amininsa abokinsa ɗan uwansa, wanda suka fara harkar tare shi ne Alhaji Kabir babansu Aminiyata ƴar uwata Fatima Kabir.

Mahaiyata Mamee, wacce sunanta na gaskiya Sharifat,iyayenta ƴan asalin Syria ne,mahaifinta ne yazo aikin wakilcin Syria a Nijeriya (Ambassador) ya zo da su Mamee suna ƴan mata,a inda Mamee ta gama makarantar gaba da Secondary a Najeriya ta fara karatun digiri ɗin ta a jami'ar Jos.

Mahaifin Mamee ya zo Najeriya tun shekara ta 1973, a lokacin mulkin Gen.Gawon, a inda ya ji daɗin zaman Najeriya, ya yanke hukuncin zama a cikinta,a lokacin da ya kammala aikinshi. Su Mamee su biyu ne a wajen iyayen su, ita da ƙaninta Saifullah.

Shekarar iyayenta goma sha ɗaya kenan da komawarsu Syria,a lokacin kuwa ina da wayona sosai, saboda ina ƴar shekara sha biyu a inda suka tafi da Yaya Habib can ƙasar,a wata jaha wacce take mai albarkar noma da kiwo. Kenan zan iya cewa kakannina Fulanin Larabawa ne, yanzun haka su kan zo lokaci-lokaci,mu ma mukan je masu ziyara.

Mu uku ne kacal su Mamee suka haifa,Aunty Salwa ita ce yayarmu, shekara biyar ta baiwa Yaya Habib. Ni kuma shekara biyar Yaya Habib ya bani, kenan Aunty Salwa shekararta talatin da uku,Yaya Habib ashirin da taƙwas, sai ni ƴar auta ashirin da uku.

Dukkanmu mun yi digiri, amma Aunty Salwa a gidan mijinta ta yi shi,tana ƴar shekara sha takwas aka yi mata aure, ta gama makaranta da shekara ɗaya kenan, yanzun haka ƴaƴanta uku. Shekarar ta sha biyar da auran Uncle Abdulƙadir,amma suna zamansu lafiya.

Ɗan ta na farko shekararsa shida, sai ƴar yarinyarta mai shekara biyu Haulatu, har yanzun kuma shiru, amma Uncle ya hana ta yin aiki, sai dai tana yin kasuwancin siyar da injinan saƙa da na keken ɗinki, da na hawa, kuma mijinta Uncle yana da abin hannunsa sosai.

Yaya Habib yanzun yake digirinsa na biyu a jami'ar Syria,wanda ya yi karatunsa ne gaba ɗaya a can ƙasar,wajen iyayen Mamee. Yana karantar (Agronomy) karatun fitar da tsiro daga cikin ƙasa.

Alhaji Fahat shi ya zaɓa masa wannan fannin,wato mahaifin Mamee kenan. Yaya ba mazaunin gida ba ne, sai dai in yazo hutu.

Ni kuwa na yi primary ɗi ta a Al-Imam School of Science nan Jos,na yi Sakandire ɗina a Minna,amma nan Jos na kammala makaranta ta, inda a can

2 Comments On KASAITA 1
avatar
khadijat-6-8

6 months ago

Reply

Thanks

avatar
khadijat-6-8

6 months ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment