Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[3/4, 22:15] 🥰Nanameera🥰: https://whatsapp.com/channel/0029VaRC69eJkK74zXhKX61n


*🌹SHEIKH HEESHAM🌹*



*Royal Star Writer's Association*




Nanameera.



01.

Yola/ Jimeta..


Tsugune take bakin kogin tayi shuru kana ganinta kasan tunani take, wata yarinya ce tazo wucewa wacce aƙalla bazata shige shekaru goma sha huɗu ba kallonta ta yi sai kuma ta ce" Jiddoh " wacce aka kirada Jiddon ta juyo sai a sannan na ƙare mata kallo farace tass amma kana ganinta kasan a cikin wahala take bazata huce shekara goma sha biyar ba tana round face da ɗan siririn hanci sai bakinta jajur dashi ganin yanda take kallonta yasa ta buɗe dara-daran idanunta masu matuƙar ɗaukan hankali. Batace mata komai ba ta juya tayi gaba abunta, sunkuyawa tayi ta ɗau ruwan da ta ɗiba sannan ta kama hanyar da ƴar uwartata tabi....



Da gudu ta shiga gidan nasu wanda bukkace kawai tana faɗin "Ammi!! Ammi " fitowa tayi daga wani waje tana kallon ɗiyar tata ta ce" lpia hanne kina yimin irin wannan kiran?" tana riƙe ƙugu ta ce" ba kin aiki Jiddoh ba?, to wlh ganinta nayi tana wasa awajen shanun arɗo bata tafi ba tana ganina ta gudu" bata rufe baki ba Jiddo ta shigo gidan da tulun ruwan akanta, ajiyewa tayi ta tsaya ganin irin kallon da take mata, ƙarasowa wajenta tayi ta murɗe kunnenta tana magana cikin gurɓatacciyar hausarta ta ce" wato ke ban isa na aike ki kije ba ko?, saboda bani na haifeki ba shiyasa kikemin irin wannan rashin mutuncin ko toh wlh bari baffan naku ya dawo yau saidai ya tsaɓa ko ni ko ke tunda ke kin gaji hali irin na uwarki" tana gama faɗin hakan ta tunkuɗata. Waɗuwa tayi tana kuka dan idan da sabo to tasaba da irin wannan, shigewa cikin bukkar sukai suka barta nan tana kuka.....



Kano State.

Ɗaukan wayarta tayi ƙirar iphone 13pro max ta zauna gefen gadonta a hankali kuma cikin isa ta fara dialing number, ganin har ya katse bai ɗagaba yasa ta ajiye wayar ta tashi ta sanya takalmknta sannan ta fito parlon.


Zaune ta sameta itada wata friend ɗinta wacce kuma daman gidan gidan zuwantane, zama tayi kusada Mami sannan ta ce" Mommy ina yini" murmushi tayi ta ce" lpia loa Shareefat ya gida ya karatun?" tana kwanciya cinyar Mami ta ce" lpia Alhamdulillah ina Nihal?" ta ce" wai yau za'a musu orientation that's why bata biyoni ba" ok tace sannan ta kalli Mami ta ce" Mami nakira Sheikh fa kuma bai ɗauka ba" Mami ta ce "maybe wani abun yake anjima sai ki sake kiran kije kici abinci Shareefat" kwaɓe fuska ta yi ta ce" wlh Mami i'm full saidai anjima" ok Mami ta ce tana kallon Hajiya Zainab ɗin ta ce" yawwa sai akayi me Hajiya?" ta ce" wlh ina baki labari kin san yaron ashe wai hacker ne to ankamashi shine take ta kuka" girgiza kai Mami ta yi ta ce" Allah Sarki Nihal Allah yasa hakane mafi alkhairi" ta ce "Ameen".......



Ganin da tayi rana ta faɗi yasa ta miƙe a hankali ta shiga inda nake zaton shine banɗakinsu, cire kayan fulanin dake jikinta tayi ta ɗebi ruwa ta watsa a jikinta sannan ta ɗaura alwala ta fito. Wata tabarmar kaba ta samu wajen ƙuda sai bi yake ta ɗauka ta shimfiɗa ta tada sallah. Tana idarwa ta tashi a hankali dan da kyar take tafiya saboda tsananin yunwar da takeji ta fita daga cikin bukkar tasu, tafiya kawai take batareda tasan inda zata jeba ita dai tasan yunwa takeji kuma abinci ta fito nema, ji tayi tafiyar na neman gagararta yasa ta nemi wani waje ta zauna ta kifa kanta kan gwuiwoyinta ta fashe da kuka, haka ta zauna wajen mintuna talatin a hankali kuma bacci ya ɗauketa.....


Sanyin asuba ne ya farkar da ita a firgice ta tashi tana kalle-kallen inda ta kwana, jiki babu kwari ta miƙe ta kama hanyar tafiya gidansu. Duk suna cikin bukkah kowa na kwance babu wanda yayi noticing bata kwana gidan ba ta shiga cikin tata bukkar wacce ita ɗaya take kwana, babu komai cikinta sai tabarmar kaba ta kwanta akai tana tunanin rayuwarta bata taɓa samun farinciki ba batasan mene ne jindaɗi ba abunda kawai ta buɗi ido ta tarar shine wahalar rayuwa, tabbas rashin mahaifiya babban giɓine a rayuwa domin da tanada uwa da tasamu sauƙin wani abun amma ita bata tadda tata mahaifiyarba dalili kuwa sanadiyyar haihuwarta Allah ya karɓi ranta dunga sanda aka haifeta har zuwa yanzu babu wani abu mai daɗi cikin labarin rayuwarta, da waɗannan tunanin bacci ya sake awon gaba da'ita.......




Fitowa tayi da shirinta na tafiya makaranta, kallonta Mami ta yi ta ce

"Shareefat kiyi sauri fa karki makara"

Toh ta ce sannan ta ajiye cup ɗin tea ɗin ta ce "tom Mami bye"

Murmushi Mami ta yi ta ce"bye dear Allah ya tsare" waje tayi tana cewa Ameen....




A firgice ta miƙe tsaye dalilin ruwan sanyin da taji an watsa mata, tsayawa tayi jikinta na kyarmar sanyi domin lokacin weathern sanyi ake tana mata wani shegen kallo ta ce

"zaki zo ki wuce ko saina bigeki" ahankali ta ratsa ta gefenta ta fita jikinta sai ɗiga yake, tulun ruwan ta ɗauka kawai tayi waje......


Tunda ta fito yake kallonta har ta ƙaraso gabansa sosai yarinyar take bashi tausayi yana kallonta ganin yanda take rawar sanyi yasa ya ce" Jiddo meyasa zaki jiƙa jikinki a wannan sanyin?" sunkuyar da kanta kawai ta yi tana goge hawayen fuskarta, ganin babu mutane dayawa wajen yasa ya ce" ina zakije?" bata kalleshi ba ta ce"

ruwa zan ɗebowa Ammi" girgiza kai ya yi dan tsananin mugunta ce tasaka wannan aiken da sassafe ya ce "toh muje na raka ki" sai a sannan ta ɗago ta kalleshi da idanunta da sukayi Ja ta ce" kabarshi kawai ngd" murmushi ya yi ya ce" karki damu Jiddoh muje" bata kuma magana ba tayi gaba yana binta abaya har suka ƙaraso kogin. Karɓa tulun ya yi ya ɗebi ruwan sannan ya ɗora akafaɗarsa yana mata murmushi ya ce" mu tafi" toh kawai ta ce ya yi gaba tana binsa a baya, tana ganin sun kusa zuwa gidansu ta kalleshi ta ce" kabani kar Haule ta ganka" bai yi mata musuba saboda yana guje mata a doketa ya miƙa mata ruwan ya ce

"kin ci abinci kuwa?" ɗaga masa kai ta yi kawai sannan a hankali cikin cool voice ɗinta ta ce" nagode Laminu" murmushi ya yi kawai sannan ya juya ta tafi........



Tana shiga ta tararda Baffa tsaye yana tambayarta da gudu ta ƙarasa wajensa ta tsaya tana kallonsa dan rabon da tagansa har ta manta, kallonta ya yi ya ce" Hauwa'u daga ina kike?" tana murmushi ta ce" Baffa na ɗebo ruwane" kallon Ammi ya yi ya ce" yanzu Hanne wannan abun ya dace da sassafe zaki aiketa ɗiban ruwa kuma ita kaɗai ina ita Haulen?" wani kallon sheƙeƙe tamasa sannan ta wani karkace baki cikeda faɗa take faɗin da harshen fulatanci " to bazan aiketa ba naga bacci Haule take kuma ba ƙanwarta bace ai dolene ta taimaka mata, har wani zakace an aiketa da safe idan yawonta ya tashi kasan inda take zuwa" girgiza kai kawai ya yi ya kalleta ya ce" jeki ki zauna" tafiya tayi kamar yanda ya ce mata ta zauna kan tabarma shikuma ya juya ya fita.....




Yana fita yayi hanya wani ɗan ƙaramin garke, yana shiga ya tsuguna jikin wata saniya ya tatsi nononta yana gamawa ya fito. Inda ya barta nan ya sameta amma banda Ammi dan tayi shigewarta bukkah, zama ya yi gefenta yana kallonta ya ce" karɓi kisha kinji" batayi musuba ta karɓa tunda ta ɗaga kanta bata saukeba sai da ta shanye nonon tass sannan ta ajiye kwaryar, kallonta yake cikeda tausayawa yasan batada kwanciyar hankali kwata-kwata kuma haƙiƙa da yasan inda zai kaita da tuntuni ta bar wajen. Kallonsa ta yi ta ce" Baffana" murmushi ya yi mata ya ce" na'am Hauwa'u " ta ce

"Ka bani labarin Ammina Baffa"



Shuru ya yi bai ce mata komai ba ta kwaɓe fuska a hankali ta ce" Baffa me kake tunani?" juyowa ya yi yana kallonta taga hawayen kwance akan idanunsa, sosai hankalinta ya tashi ta shiga goge masa tana cewa

"Dan Allah Baffa kayi haƙuri bazan sake tambayarka ba kaji" hannun da take goge masa ya riƙe yana kallonta sosai taga ya saki murmushi, tsayawa ta yi tana kallonsa dan ba ƙaramin kyau murmushin ya yi masaba kasancewarsa asalin bafulatani, ya ce


"Aduk sanda na kalleki sai naga kamar Hauwa'u ce gabana, domin babu abinda kika manta nata da baki ɗaukoshiba yanda kike da haƙuri haka take koda cutarta kake kuma tasan cutarta kake bazata taɓa nuna makaba, sannan bata riƙo a rayuwarta tana iya yafe laifi duk girmansa na tabbata Hauwa'u ƴar Aljanna ce, inaso ki ɗora daga inda kika tsaya Hauwa'u kisani babu wanda aka taɓa zalunta kuma Allah ya barshi haka ki cigaba da haƙuri kinji watarana sai labari"


Kuka kawai take ta gyaɗa masa kai a hankali ya fara goge mata hawayen yana murmushi yace" Allah ubangiji ya jiƙan Hauwa'u" ta ce" Ameen".....



Wajejen ƙarfe sha biyu tana zaune cikin garken shanun nasu bata damu da yanda jikinta ya ɓaci ba, dan babu inda takejin dadi sai wajen waɗannan dabbobin indai Baffanta bayanan. Fitowa tayi tana kalle-kalle sai kuma ta ƙaraso gabanta tana kallonta ta ce

"Kee Jiddoh kizo inji Ammi" bata jira amsarta ba ta juya ciki abinta. Tashi Jiddah ta yi ta shiga cikin gidan nasu, zaune ta sameta tana dama fura ta tsuguna gabanta cikin ladabi ta ce "Ammi gani" kallonta ta yi ta ce

"Ki tashi kije gidan Arɗo Adda zata aikeki" tashi ta yi batareda ta ce komai ba ta fita daga gidan.....



Zaune take kusada Mami tana cin abinci ta ce" toh yanzu kina ganin Sheikh zai amince ya auri Nihal kinfasan halinsa Mami" kallonta Mami ta yi ta ce


"Ai ni ce na haifi Heesham ba shine ya haifi kansaba kuws this time around dole ne ko yana so ko baya so ya yi abinda nace" taɓe baki Shareefat ta yi ta ce


"Kindai san halinsa wlh kuma abinda yakeso shi za'a yi inda Dad na nan" girgiza kai Mami ta yi ta ce " dole ne ya yi abinda na ce ko shi babanku bai'isa ya hana ba" dariya Shareefat ta yi ta ce" Hajiya Mami kenan, ai ya cemin gobe ma zai dawo Nigeria" "me zai kawoshi?"


Ta ce" maybe Dad ne ya yi kiransa amma nidai ba cemin ga abinda zai dawo yiba kindai san yaya Sheikh" sallama da akayi ne yasa suka yi shuru, zama ta yi gefen Shareefat sannan ta ce" Mami ina yini" cikin sakin fuska Mami ta ce "lpia lao Nihal ya Mommyn taki?" ta ce " tana nan klao tace tana gaisheki" murmushi Mami ta yi ta ce" ina amsawa" sannan ta tashi ta hau sama. Kallonta Shareefat ta yi ta ce " sirikarmu" dariya Nihal ta yi ta ce" kinga ranki zai ɓaci tom" murmushi Shareefat ta yi ta ce" har na ganoku ranar wow wayaga kyau da kyau" harararta ta yi ta ce" banson irin wannan rashin mutunci ina wani kyau?" tashi Shareefat ta yi ta ce "plx muje ciki".......



Kallonsa take har ya gama shiryawa ya kalleta ganin irin yanda take kallonsa yasa ya yi murmushi ya ce" mene ne Hauwa'u?" kwaɓe fuska ta yi ta ce" dan Allah Baffa karka daɗe kaji" shafa kanta yayi sannan ya ce" in sha Allah Hauwa'u, amma dan Allah ki ƙara haƙuri kinji komai zai zo ƙarshe da yardar Allah" toh ta ce sannan ta ɗaukar masa kayansa ta ce" muje na rakaka hanya Baffa" daga haka ta yi waje. Suna zuwa ƙarshen hanya ya kalleta ya ce" Hauwa'u ki koma kinji" murmushi ta yi sai kuma hawaye ya biyo bayansa ya kalleta ya ce

"Banson kina wannan kukan kamar zan mutu?" ta ce" Baffa a dawo lpia Allah ya tsare ya kiyaye" ya ce" Ameen Allah ya albarkaci rayuwarki" tana murmushi ta ce " Ameen. Tsayawa ta yi har saida ya ɓacewa ganinta sannan ta juyo ta kama hanyar gida, a hanya taga wani ɗan abun wuya ƙarami mai kyau ɗauka tayi tana kallonsa dan tabbas tasan na Baffa ne ya yardashi saboda a wuyansa yake sakawa, ɗaurawa tayi a wuyanta ta ce" idan Baffa ya dawo saina bashi abinshi" sannan ta cigaba da tafiyarta tana ƴan waƙoƙinta.....



A hanya ta haɗu da Laminu yana ɗiban kara dan kunna wuta, tana murmushi ta ce" bari na tayaka" girgiza kai ya yi ya ce " haba Jiddoh kina mace kuma ke zaki tayani" haɗe rai ta yi ta hau ɗeban waɗanda ya rage tayi gaba ta barsa wajen, murmushi kawai ya yi sannan yabi bayanta......



Hayaniyar da ya ziyarci kunnenta yasa ta buɗe idanunta a hankali, mamaki ta yi ganin har gari ya waye kuma Ammi batazo ta tasheta ba, ta miƙe jin kamar hayaniyar ƙaruwa take ta fito daga cikin bukkar tata kallon ko'ina tayi amma bataga alamar Ammi ko Haule ba yasa tayi waje dan ganin meke faruwa.....



Mutane ta hango sunyi ƙawanya sun zagaye abu amma bata ce ka abinda suka zagaye ba, hakan yasa ta ƙarasa wajen cikin tafiyarta a hankali kamar koda yaushe. Tana zuwa taji kamar ana kuka mutanen na ganinta suka matsa mata hanya, kwance ta gansa cikin jini kana ganinsa kasan kasheshi akai, da gudu ta ƙarasa wajen ta tsuguna tana sake buɗe idanunta dan tabbatar da abinda tagani, shafa fuskarsa tayi tana kallonsa kamar mahaukaciya muryarta na rawa ta ce


"Ba..Baff.Baffana" sai kuma ta fashe da wani raunataccen kuka kamar ranta zai fita ta ɗago tana sake kallonsa a karo na biyu dan gani take kamar a mafarki ta ce "Baffa ka tashi kaji kadaina irin wannan wasan kaji, nasan kana jina katashi kar nayi kuka" shuru taji babu amsa hakan yasa hankalinta ya sake tashi sai kuma ta miƙe da gudu dan kafin takai inda zata ta yanke jiki ta faɗi kasa.....




Share it plx.
[3/4, 22:15] 🥰Nanameera🥰: https://chat.whatsapp.com/LSYEkQgVkLKDQyheA6YWH4

*🌹SHEIKH HEESHAM🌹*



*Royal Star Writer's Association*




Nanameera.



02.

Farka warta kenan ta tashi zaune tana kallon cikin bukkar da take, tashi tayi ta fito tsakar gidan nasu ta tararda mai gari zaune sai Arɗo sai kuma wani abokinsu, ƙarasowa ta yi ta tsuguna tana kallonsu dan gani take kamar zataga Baffanta a cikinsu, ganin yanda take binsu da kallo yasa Arɗo ya ce" Jiddoh tashi ki tafi wajen Adda zata baki abinci" tashi tayi jiki a sanyaye tayi waje.....



Kusan sati ɗaya da mutuwar Baffa kenan kuma sai a yanzu takejin mutuwar sabuwa mussamman yanda batada kowa da zata ce wannan natane ko zaiji tausayinta babu dangin Uwa dan bata taɓa ganinsu ba dangin uban kuma su Arɗo ne dan shi kaɗai ya rage masa ɗan uwa, babu wata wacce zata bata shawara ko kuwa ta rarrasheta kullum sai dai ka ganta cikin shanu tana zaune dan sunfi ɗebe mata kewa. Haule ce ta fito tana shan fura ta kalleta dan rabonta da abinci tun shekaranjiya kallonta ta yi ta ce

"Jiddoh zaki sha?"

Gyaɗa mata kai tayi ta harareta ta ce "mayya to ko zaki mutu bazaki sha ba" tana gama faɗin haka ta juya ta koma ciki. Shuru Jiddah tayi tana tunani haka zata ƙare rayuwarta har ta mutu babu wani abun arziƙi?, haka zata zauna har yunwa tayi ajalinta?, zama ya yi gefenta ta ɗago a ɗan firgice tana kallonsa. Murmushi ya sakar mata ya ce

"Gani nayi kin zauna kinyi shuru shine na ce bari nazo na tayaki zama" shuru tayi dan ita yanzu magana sai ta kama take yinta ya ce" Jiddoh zaki aureni?" da sauri ta kalleshi sai kuma ta sunkuyar da kanta ya ce "idan har kin amince zanwa Baffana magana Jiddoh kuma nasan bazai ƙiba" share hawayen fuskarta tayi a hankali ta miƙe batace komai ba tabar wajen, kallon kawai ya yi dan shi harga Allah tausayin Jiddoh yake kuma zai cigaba da faɗa mata har ta amince ya aureta......



Wata irin azababbiyar yunwa ce ta tasheta daga baccin buɗe idanuwanta tayi wadanda ko buɗuwa sosai ba su yi saboda tsananin yunwa, fitowa tayi daga cikin bukkar batareda taji tsoron komai ba har ta fito daga cikin gidan nasu, garin ya yi tsit babu abinda kake iyaji sai kukan karnuka amma kwata-kwata Jiddah bataji tsoron wannan dare ba ta fara tafiya batareda tasan inda ta nufa ba.....


Tafiya kawai take cikin garin jimeta sai kace aljana ce, jitayi kamar ta taka wani abu hakan yasa ta tsuguna tana kallon ƙafarta, ƙaya ce ta soketa ta zauna tana cirewa sam bata lurada wadanda suka zo suka mata ƙawanyaba. Ɗago kanta tayi taganta tsakiyar maza sunkai su biyar, ji tayi gabanta ya waɗi abinda kawai yazo ranta shine ranar mutuwarta ce tazo, kasa kwakkwaran motsi tayi har sannan su kuma kallonta suke. Wani daga cikinsu ne ya ce

"Me muke jira kawai mu aikatata mana lokacifa na ƙurewa kuma munada yawa"


Batayi zaton yanda zuciyarta ta buga ba mutuwa zatayi ba amma sai taga ta samu kanta da kallonsu dukkan ninsu ƴan fulani ne kamar ta kuma duk basuda wani jiki, batayi aune ba taji sun fara janta har cikin wata bukka ƴar madaidaiciya......



Banda tsuma babu abinda jikinta keyi amma kwata-kwata ta kasa kuka sai kallonsu take dan ta tabbatar da yau zatabi Baffa da Amminta......


Fuskokinsu ɗauke da annuri suke kallonta dan gani suke sun samu nama a banza, ɗaya daga cikinsu ne ya fara cire rigarsa ɗayan ya kalleshi ya ce

"Kai bangane me kake nufi ba"

Harararsa ya yi ya ce" nufi nake ni zan fara" wani mugun kallo na ukun ya yayi masa ya ce"_ kama isa ai aradu nine nan zanfara" wanda ya tsaya daga bakin bukkar ne yazo duka ya hankaɗesu ya ce

"Tunda nine nake muku gadi ni ne wanda zai fara saina koma wajen zamana, cecekuce suka fara akan wanda zai zama na farko hakan yasa suka fara faɗa i junansu, fita sukayi daga cikin bukkar sunata faɗace-faɗace......


Zama tayi da farko sai kuma wata zuciya ta raya mata "ga dama kinsamu kawai kiyi guduwarki bai kamata ace a cikin nan kika mutu ba" da wannan tunanin ta fara kalle-kalle ai kuwa tayi sa'a daga can ƙarshen bukkar ta ɗan yage, da sauri ta ƙarasa wajen dukda batada wani kwari amma haka tayi jarumta tana zuwa ta saka kanta ciki amma inaaa bazata iya fita ta ciki ba. Fashewa tayi da kukan baƙin ciki ta haɗe hannanyenta biyu waje guda tana kuka ta ce

"Allah na roƙeka ka taimakeni nabar nan wajen da mutuncina dan darajar Annabi" ta ƙarasa maganar tana rushewa da kuka, har sannan kuma tana jiyo hayaniyarsu suna faɗa kamar ba dare ba.....


Sake gwada fita tayi amma still taji ta kasa, can wata dabara tazo mata ta zauna ta fara kakkarya karan jiki da hannunta kasancewar tsohuwar bukkah ce yasa duk inda ta karya yake karyuwa saida tayi hanya data tabbatar zata isheta ta fita sannan ta saurara. Tana ƙoƙorin zura kanta ciki suka shigo, da sauri ta ƙarasa fita suka biyota da gudu......




Gudu kawai take babu ƙaƙƙautawa kuma har sannan suma binta suke har ta fara galabaita, batasan sanda ta waɗi ƙasa sumammiya ba.........



Tsayawa Driven ya yi da tuƙun, ahankali ya ɗago idanunsa daga kan computern hannunsa juya idanunsa ya yi kamar zai yi magana sai kuma ya yi shuru da bakinsa kusan 2mins amma bai ce komai ba cikeda ladabi driven ya ce
"Sheikh motar ta samu matsala kuma gashi dare ya rigada ya yi saidai mu samu wani wajen mu zauna zuwa safiya"
Sai a sannan ya kalleshi da fararen idanunsa kuma manya, sunkuyar da kansa drivern ya yi domin duk rashin kunyarka baka isa ka haɗa idanu da Shaikh Heesham ba. A hankali ya buɗe bakinsa yana tasbihi ga ubangiji kusan mintuna biyar sannan ya ce cikin tsantar nutsuwar data gama ratsashi
"Allah ya kaimu"
Abinda kawai ya furta kenan bai kuma sake wata maganar ba ya lumshe idanunsa masu kyau. Sheikh Heesham Muhammad kenan babban malami a ƙasar saudia yankin larabawa, ya kasance kyakykyawa dan asalin balarabe ne mahaifinsa Alhaji Muhammd ɗan asalin ƙasar saudia ne amma bai rayu acan ba kasancewar duka danginsa mutanen Nigeria mahaifiyarsa ta haifeshine a ƙasar dalilin zuwa omrah. Sanda aka samu cikin Sheikh Heesham sai mahaifiyarsa Hajiya Amina ta tafi saudia dan rainon cikin jikimta har kuma ta haihu ƙasar hakan yasa shima ya kasance indigin na ƙasar saudia saboda haka sanda ya fara tasawa sai mahaifinsa ya kaishi karatu ƙasar, ya kasance ya rayu a ƙasar tun yana ɗan karamin yaro har girma shiɗin likitane gefe guda kuma babban malami a ƙasar. Wannan shine ƙadan daga tarihin rayuwarsa..

Ganin dare na ƙara yi yasa drivern ya ce
"Sheikh ko zamu samu wani gurin mu zauna?"
Ba zaka taɓa cewa da Sheikh Heesham ake magana ba dan ko kallonsa bai yiba bare ya saka ran zai bashi amsa saima cigaba da danna cazbahar hannusa da yayi..

Hadarine ya haɗo ganga-ganga kuma kana gani kasan ba ƙaramin ruwane zai sauka ba, ɗaya daga cikin securities ɗinsa dake ɗaya motar ne ya

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5

2 Comments On SHEIKH HEESHAM
avatar
ayshertul-humaira

6 months ago

Reply

Is not complete

avatar
naja-atu-8

5 months ago

Reply

Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment