Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

UMMUH AMANIH
By
Hafsa. Umar dangoro yarmutan
BAKIN RAFEE

漏锔� JARUMAI WRITAR's ASSOCIATION 馃摎馃摎鈿滐笍 J. W. A馃枊锔�




Godiya ,


Dasunan Allah mai rahama mai jin kai tsira da amincin Allah sutabbata ga shugaban halitta annabi muhammad S,A,W da iyalansa da sahabbansa baki daya.




Sadaukarwa.
Na sadaukar da wannan littafin mai suna UMMUH ga kanwar mahaifiyata fatima saleh yusuf (binta) wadda take zaune a naibawa "yan lemo.


Fatan alkawari zuwa ga dubun dubanar masoya na kusa dana kewaye,ina muku Fatan alkairi dafatan Allah yasa kugama lafiya , inagodiya da gudummawar da kuka bani har nakawo wannan kan matsayin danake kai ayanzu,ina godiya ga uncle usama,Allah ya bar zumunci,ina godiya musa baffa,Allah ya baka abinda kakeso duniya da lahira,ina godiya ga mahaifiyata abarkaunata,Allah ya sanya ki a aljanna madaukakiya, daduk wanda bansamu damar ambaton sunan shi/ke ba suma ina matukar godiya Allah ya bar zumunci.



Wanan littafin mai suna UMMUH AMANIH narubutashine badan komai ba saidan gera ga al,ummar musulmai,domin fadakarwa , nishadan,ilimantarwa,duk acikin wanan littafin mai suna UMMUH AMANIH,mar yadda rayuwa,da duniya , ta juyawa UMMUH AMANIHBaya, alokacin da bata da kowa sai allah.



Wannan littafin kirkirarran labarine,ban rubutashi dan na muzan ta wani ba kodan na bayyana sirrin wataba, no ba hakabane, littafina kirkirarsa nai kuma nasan hakan tana faruwa, amma duk wadda taga yayi shige da labarin rayuwarta, arashin sanine.

Gargadi,

Ban yarda wata tajuyamin littafinaba, ko kuma adinga siyarmin da littafi batare da saninaba, banaso, banyarda wani ko wata sukarantamin book ba ,batare da iziniba ,ngd.





Pages 1

******** ********************Tafe suke akan hanyar islamiya ,yamma tayi likis, domin har an fara kiran sallar magriba, UMMUH wai nikam can"ba ibrahim nake ganiba,kai haba indo bashi bane ba wallahi kin fiye sa ido,sa'ido sana ar banza, cewar UMMUH,harara UMMUH ta watsawa indo,kinganki ko wai kema kingirma, wallahi ni bazan tsayaba, umma tahanani kula samari, to meyasa zatace bazaki kula samariba,zaro ido UMMUH tai tace,umma tace ban isah zanceba, tace karatu zanyi ba aureba,tabe baki indo tai tace niko aure na zanyi, kinsan dai akauyannan idan yarinya ta huce shekara 8 batai aureba ,haka ake cewa tayi kwantai,to balle mu kuma yanzu munkai shekara 10 daker zamu samu mijin aure,tun wuri ummuh ki canza shawara, ,oho ai aure lokacine idan zakiyi ni ban hana kiba amma dai ni dinan karatu zanyi shine burin ummana,to shikkenan ummuh tunda baki daukar shawara kije kiyi karatun,idan kin tashi ki zama likita,mukuma zamuyi auren"kigani in damu da ke wanene, rayuwarsa zatafi "in ganta,nidai bance ba,Kinga tafiyata ,ummuh taka ma hanya tai tafiyarta tabar indo a tsaye sake da baki tana bin bayanta da kallo,

Ibrahim ne ya karaso "inda yaga indo a tsaye, aslmualaikum, amin wa, alaikumussalam,indo yanaga ummuh tatafi tabarki, babu komai dan sa ido kawai,ta galla Masa harara ta wuce ta barshi atsaye a gurin.

Dagudu tanimu ya karaso inda yaga ummuh ta bullo,har yana tuntube tsabar gudu ,agaban ummuh ya tsaya yana maida numfashi, nan take kirjin ummuh ya fara bugawa,tana jin faduwar gaba ,daker ta iya cewa tanimu, lafiya meyafaru ne, babu komai ummuh zo mu tafi gida, yaja hannunta suka nufi gidan, tunda ga kofar gidan ummuh ta fara ganin mutane a tsatstsaye sunyi cirko cirko, ahaka harta karaso kofar gidan zata shiga,kowane mutum dake gurin kallon ta kawai sukeyi suna jijjiga kai,nan danan jikin ummuh ya kara sanyi ,kamar mara lafiya,shiga gidan sukai da ita da tanimu,tundaga soron gidan ummuh take jin koke2",nan danan taji kafafuwanta sun mata nauyi daker take iya daga su, tana saka kafarta cikin dakin ummah taga ,makara har guda biyu,kowacce dauke da mutum aciki an lullube su da farin lukkafani, innalillahi wainna ilaihirraju,baki na rawa ta dubi wata mata dake zaune a gurin tace, in in inna " ina ummana, wannan matar da takira da innace ta nuna mata daya daga cikin makarar ,aikamar zatayi hauka ta durkusa, a gaban makarar ta bude,da sauri ta dauke kanta,tana furta kalmar innalillahi wainna ilaihirraju un ,nashi ga uku nan fa tashiga jijjiga ta tana cewa, umma ki tashi kada ki tafi ki barni,dan Allah kitashi, wayyo Allah na ummana nashiga uku ta na dora hannu aka, can kuma kamar an tsikareta ta mike ta fuce ,waje mazan dake wajen ta kalla,daya bayan daya, amma bataga baban taba,daya daga cikinsu ta kalla tana kuka tace,"ina babana yake ,ammadai besan ummana ta mutuba ko, naga ban ganshi a gurinba, ita kadai sai sumbatu takeyi,suko mutanen gurin ko wanne kallon yarinyar yake cike da tausayi,innace ta biyo bayanta ta kama hannunta, tashiga da ita cikin gidan,tana bubbuga bayan ta, daker ummuh ta iya dagowa ta kalleta tace inna!! "Ina babana yake ,dakamar bazata gayamata inda yakeba, saikuma wata zuciyar tace kifada mata,hannunta ta sake rikewa ta dagata tsaye taja hannunta, har gaban makarar tagaban ta ummanta tace,ummuh ga mahaifinki,wani mahau kacin ihu ummuh ta yi yayinda ta daka tsalke ta dure tana fadin, innalillahi wainnailaihirraju un allahummah ajirni fi musibati wa aklifni kairu minha, innalillahi wainnailaihirraju un nashiga uku, shikenan narasa ummana narasa babana,narasa duk wani gata na duniya, komai ya kare, banida sauran gata, babu uwa babu uba, babu yaya, babu kanne,nashiga uku ni ummuh ina zansaka rayuwata innalillahi wainnailaihirraju un,kawai tafuta tasulale agurin sumammiya,



Misalin karfe 12 na dare ummu ta farfado daga sumar da tai, fitowatai tashiga inda gawawwakin iyayanta suke ta zauna a tsakiyarsu ko tsoro bataji,ta hada kai da guga sai rusa kuka take kamar ranta zai fita,ahaka har bacci barawo ya dauketa,anan tsakiyar gawawwakin iyayanta,to kasan cewar su umman ummuh da magariba Allah ya musu cikawa,yasa dole sai washegari za akaisu a bunnesu,domin sai sunyi kwannan keso.

To washe gari da safe aka dau gawar iyayan ummuh aka tafi kaisu gidan su na gaskiya daker aka banbare ummh daga jikin gawar iyayanta, haka yarinya karama kamar ummuh "yar shekara10 tazauna babu uwa babu uba,ko abinci tadainaci ,har akai sadakar ukun iyayanta,

Azaune tasamu inna tana cin abincinta hankalinta kwance,zamatai a gabanta ta tsuramata t. Ido tana kallonta,ke lafiya kike kallona haka kamar ni na kashemiki iyaye,lafiya kalau inna ,daman sonake natambayeki, garinya akai iyayena suka mutu,hhhhhh inna ta kwashe da dariya takalli sauran "yan uwanta da suke zaune tace,kunji wai tambaya ta take meyasa iyayanta suka mutu , to dan ubanki iyayan naki sunfi kowane dabaza su mutuba, kobata amsa yaya atine,wadda aka Kira da atine ce tace,ta sana diyyar haihuwar kanwarki uwarki ta mutu, shikuma ubanki waishi sarkin soyayya, sai ya bita suka tafi tare,tabe baki inna tai ta amshe zancen,shegeba tsohon banza ai daya hakura da soyayyar ya tsaya kodan ya kula da rayuwarku da ke da kanwar taki,amma saiya biyewa soyayya yabi tsohuwarki lahira, nan kuma sunbarki da rainon jaririya,dan wallahi daga ke har ita kanwar taki da aka haifa babu wacce zan rike,hhhhhh atine ta kwashe da dariya tace to balle kuma mu, kunga ni tafiya tama,cewar inna, duk abinda suke cewa ummuh tana zaune aganansu tanajin cinmutuncin da suke yiwa iyayanta, kuka takeyi sosai tana tunanin yadda zata iya taimakon kanta, haka suka dinga tafiya daya bayab daya,saida gidan ya kasance babu kowa sai ummuh kadai,tana zaune tana rusa uban kuka ,jitai kamar kukan jaririya takeji agefenta, waigawa tai ta hangi jaririyar nannade acikin zani,nandanan gaban ummuh ya fadi, tashiga furta innalillahi wainnailaihirraju un,wai dama dagaske inna take bazata iya rike kanwataba nashiga uku,to ni kenan yazanyi da ita ni kaina bukatar kulawa nake, ballantana ahadani da wata jaririya,wayyo Allah ni ummuh,ina zansa rayuwata da ta kanwata, hannu ummuh tasa ta dauki jaririyar ta fara rarrashinta can kuma saitai shiru, zama tai tana tunanin yadda zata I da jaririyar,kawai sai ta yanke shawarar ta cillar da ita kawai, yafi sauki ,


UMMUH AMANIH
By
Hafsa. Umar dangoro yarmutan
BAKIN RAFEE

漏锔� JARUMAI WRITAR's ASSOCIATION 馃摎馃摎鈿滐笍 J. W. A馃枊锔�




Pege 2


Bakkon kayan ta tanufa, tadakko hijabi tasaka ,sannan tadurkusa ta dauki kanwar tata, tafuce daga gidan ,tafiya takeyi sosai saida tai tafiya mai nisa ,sannan ta isa wani jeji babu kowa sai kukan tsuntsaye, ajiye jaririyar tai a bakin wata bishiya ta juya zatatafi,kamar a mafarki taji taruko shijabinta,abin mamaki UMMUH taja hijabin amma takasa fincikewa daga hannun jaririyar, kuka UMMUH tasaka tazauna a gaban jaririyar tafara magana kamar wata tababbiya, tace dan Allah"yar, uwata ki cikani natafi, wallahi bansan yadda zanyi dakeba,kina bukatar kulawa bazan iya shayar da keba, idan kuma natafi na barki anan gurin zaki samu wanda zai taimaka miki, dan Allah karki kuka,hannunta tasa tana jijjiga jaririyar tana cewa, kiyi shuru kanwata banison kinayin kuka, nafiso ki dauwama cikin farinciki da walwala,ina bukatar rayuwarki ta inganta,abin mamaki saitaga jaririyar tadai na kuka tanata yimata dariya,Inda kasan wadda ta shekara ba sabuwar haihuwaba,nanfa UMMUH ta fara tsorata da lamarin jaririyar,yaza ai ace jaririyar tana dariya, tana tsaka da Wanan tunanin taji an dafa kafadarta,a tsorace ta juyo indo tagani kawarta,zaro ido UMMUH tai tace indo taya akai kikazo gurinnan waya kawoki nan,indo ce tace,tundaga lokacin da kika fito daga gida ina binki abaya naga me zakiyi, saikawai naga kin zo kin tsuguna anan kina ta surutu kekadai,uhm UMMUH tai murmushin takaici indo kenan dama kin taba ganin mutum yana surutu shikadai,indai ba mahaukaci bane, bani kadai nake yiba nida kanwatane, kanwar ki kuma ?indo ta zaro ido, eh kanwata ,

Muganta indo ta zaro kwola2 idanuwanta tanabin jaririyar da kallo, "kai ummuh kallifa dariya takeyi, anya kuwa ba aljana BACE?uhm kemadai ke fada,ashedai ba "idonane yake nunamin dariya takeyiba" to wai ke ummuh me yakawoki jaji? Nazo ne nayar da jaririyar nan, kiyar da "itafa kikace indo ta zaro"ido, "eh indo amma dai yanzu nafasa, meyasa kika fasa ummuh? Sabida inason zama da "yar uwata, ayanzu itakadaice ahalina, bani da kowa sai "ita , itace wadda zan gani nadinga jin dadi a zuciyarta, tunda su inna da atine sun gugeni,ta fashe da kuka,

Kiyi shiru ummuh ,dolene ki nisanci wannan jaririyar,ummuh ke karamar yarinya ce bazaki iya rikon jaririya ba, kema kanki kulawa kike bukata, ya isa haka indo, dakatamin" saiyanxu kikasan ban girmaba, sai yanzu kika gane nidin yarinya, ce sai yanzu zaki gane kulawa nake bukata, hmm kin manta mekikacemin rannan, nidin na yi kwantai,sabida nakai shekara 10 ba ayimin aureba, to idan har maganarki gaskiyane "nacewar na isa aure,to zan iya rainon kan wata, zan tsayamata tayi ilimi, zan tsayawa rayuwarta da tarbiyyarta zan zamar mata bango da jigo narayuwa ,kingane,a tsorace indo tace nagane, dan ko giyar wake tasha bazata yarda ummuh ke furta wannan kalmominba, bata gama tunanin ba,ta tsin kayo muryar ummuh tana cewa,indo lokacin da muna maganar aure a aji" mema nace miki sunan "yata,muryar indo tana rawa tafurta,amanih,amanih kikace zakisawa, "yarki, murmushin ummuh tai sannan takalli indo tace, daga yau sunana, UMMUH AMANIH,karda ki kara kirana dasuna, ummuh gatsar kikirani da UMMUH AMANIH,

Hannu ummuh tasa tadauki jaririyar tafara mata wasa tanacewa, amanih baiwar Allah,Allah ya rayamun "ke "yata,sannan ta kalli indo tace muje ko,!!!! "tafe suke indo nabin ummuh abaya,zuciyarta cike da tunani kala2 don gaba kidaya tagama tsinkewa da lamarin ummuh, ko tayaya zata iya rike jaririyar ,bayan itama dakadan tafi jaririyar,sai kawai indo tace bari inzuba na mujiya insha kallo.

Nimako nace aradu zanyi kallon "yar shekara10 da rainon jaririya sabuwar haihuwa.




Indo ,na am, nafuskanci AMANIH tana jin yunwa, dan Allah ko zamuje gurin ummanku, ko da taimakon da zata "iya yiwa kanwata,
Eh muje to, amma UMMUH ina dada jaddada miki ,ki hakura da rukon AMANIH, kinga da allah malama ki rabu dani, kar ki dagamin hankali,idan da kanwar kice zaki "iya jefar da ita,meyasa indo baza ki fahim ceniba, kinyi hakuri"UMMUH nafahim ceki, Allah ya taimakeki akan rukon AMANIH,Ameen haka nakeson ji,

Dai,dai lokacin da su ummuh suka iso kofar gidan su indo, sallama sukai, aslmualaikum, amin waalaikumussalam barka da hutawa umma, cewar indo, barkadai, toh yau kuma ummuh ce a gidan namu,e wallahi,umma,ah to karaso ga guri ki zauna, zama ummuh tai sannan tashi ga gaisheda umman indo, bayan sun gaisane, ummuh ta fara magana, umma daman tambayar ki nakeso nayi,toh "ina jinki ummuh Allah yasa nasani,uhmm umma ai kin sani dama sonake~~~~ natambayeki, kanwata tana jin yunwa ina so na bata abinci taci amma ban san me zan bataba,ayya Allah sarki "yar nan, to amma ina su atine da innar taki,ai nazata suntafi da ku,aa umma ,sunce dagani har kanwata ba zasu zauna da muba,ummh tafashe da kuka, umman indo ce ta shiga rarrashin UMMUH,tan cewa ki yi hakuri UMMUH nasan damn haka zata kasance amma inaso kiyi,ta addu,a karda ki damu,da duk wani abu da za ayimiki, kedai kawai kiyi tawakkali ga annabi muhammad (S,A,W) sannan "inason ku dawo gidan nan da zama",don nasan yanzu bakuda kowa babu wanda zai taimakeku, gashi bakusan dangin mahaifin kuba ,asanin da naiwa mahaifinku shidin ba dan cikin karkaran nan bane,yazo neman ilimi daga wata kasar,bekoma garinsuba haryasamu mata annan ya aura amma bayannan bansan wani abu dan gane da mahaifin kuba,inason ki barmin wann jaririyar zan riketa agurina"har dakema,a,a umma ki barshi kawaii,nafison na dan danawa "yar uwata irin soyyar da MAHAIFIYATA ta nuna min ,ina son tatashi da kaunata acikin ranta,sanan ina bukatar na ga nasata amakaranta da kudaina,na biyamata kudin cin abincinta,da kudin makarantar ta da kudin kayan sawarta,da komaima duk ya kasance da gumina zan mata duk kan wadannan abubuwan,inason na dan dani zafin da mahaifiyata taji alokacin da take wan kemin kayan kashi da fitsri,ina son na ji yadda takeji alokacin da nake tsalamata kuka, tabar duk abin da take tazo ta rarrasheni,inason naji wuyar da tasha daga sanda ta haifeni zuwa yan zu da tatafi tabarni,tabbas ta barmin amanar AMANIH,kuma wallahi sai dai in babu raina, amma sai na cikawa ummata burinta na karatu datake so nayi, koda ni banyi karatuba,zan nema da karfina nabiyawa amani tayi,dan gin mahaifiyata"sun gujeni ,sabida haka bani bukatar taimakon kowa,akan rikon AMANIH,nidinnan zan rike "yar,uwata da kaina,umman indo ce tazubawa ummuh "ido tunda tafara magana harta dasa aya ,tana mamakin karfin hali irin na UMMUH"uhmm idan banda abinki ummuh ta ina zaki iya rainon jaririya,ai wanan aiki saimu manya,jibe ki fa kota2 nawa kike"kedinfa yarinyace karama,kidai yi hakuri ki bari na rike ta agurina.

****,umma? Na,am umma?na,am umma? na,am,so nawa nakira sunanki,?sau 3, UMMUH shin na isa aure, eh UMMUH kin isa aure "harma kin wuce lokacin da akewa yara aure a kauyannan , Alhamdullah,umma kin bawa kanki amsa, muddum na huce munzaliin aure,to zan iya rikon AMANIH,umma ,menene auren ne, daga aure sai samun ciki,sai laulayi,daga shi sai nakuda,sai haihuwa,sai shayarwa, da raino da aikin kayan futsari da na kashi, to nikuma haihuwa ce kawai banba amma kuma ni zanyi raino.
UMMUH AMANIH
By
Hafsa. Umar dangoro yarmutan
BAKIN RAFEE

漏锔� JARUMAI WRITAR's ASSOCIATION 馃摎馃摎鈿滐笍 J. W. A馃枊锔�




Pege 3
**** ,umman indo ce ta dubi UMMUH da mamaki, kana takai hannu ta tabata domin taji ummuh ce kokuma aljanna ce,dan wallahi ta yi imani ba ummuce take wanan maganar ba,magana tafarayi ummuh anya kuwa kece,itadai indo tana gefe tana binsu da "ido,caraf ta cafke zancen,umma daman ni tunda muka taho dani da ummuh na san ba iya bace gamo kurum nayi, eh to zata iya yuwuwa gamo mukayi gaba "dayanmu,nidai ummuh dana sani ,bahaka takeba,yarinya ce me kunya,da hankali,da kuma girmama na gaba da ita, amma yanzu naga sabanin haka.


********************hadiye yawun bakinta tayi ji kake kuku kut..... Sanan tace ummuh mekike bukata yanzu,umma sonake ki fadamin mezan bawa "yar uwata yunwa takeji,to ,bari akawo miki, indo dakkomin kudi adaki muttala,biyar,kije gurin rabi,u me kanti ki sayowa,ummuh madara,to indo tace kana tashiga dakin ta dakko kudin ta fuce daga gidan,ummace ta dubi UMMUH tace ummuh na amince kirike kanwarki,Allah ya baki hakuri ,ya isa haka umma baniso kidaina bani hakuri,kuma zan fadamiki wani abu,da ga yau karki kara cemin ummuh,kikirani da UMMUH AMANIH shine sunana,sanan abinda na tambayeki bakibani amsataba,menene zan dinga bawa kanwata,? UMMUH AMANIH,na am umma?yanzu kika fadi sunan dai dai ina jinki, UMMUH AMANIH abun da zaki dinga bawa amanih shine, kudin ga bata madara,ko kuma ki damamata karmu,kina bata tana sha ,insha Allah "yarki zata dinga sha sosai tana koshi,

Aslmualaikum indo tai sallama ta kawa madarar, tabawa umman ta,kar ba umman indo tai ta shiga damawa da ruwan dumi,bayan ta gama damawa ne ta mikawa ummuh ,"ummuh ta karba ta shiga bawa amanih,amma taki karba,nan umma tace indo tashiga daki ta dakko mata fidar fahat,tunda an yayeshi, haka ko ta dakko fidar ta kawowa umma,sannan aka zuba madarar aciki, aka bawa ummuh, karba ummuh tai tashiga bawa amanih tana sha, ummuh ganin tai amani tanashan madarar sosai ,da alama yunwa takeji, sai taji hawaye yana zubo mata daga "cikin "idonta bakaramin tau sayin amanih take jiba,amma ita din ta kuduri niyyar baza ta taba barin amanih tayi kukan maraici ba, sannan tasa azuciyarta duk saitayi maganin su atine da inna,.********************godiya ummuh taiwa umman indo sannan tai musu sallama, ta goya amani ta tafi gida.


************to a hanyarta na zuwa gida ta hadu da tanimu,sai gudu yake yana bin ta ina kolla mata kira, ummuh? ummuh!!? ummuh dan Allah ki tsaya mana, cak ummuh ta tsaya sabida ya hadata da wanda yafi kowa matsayi aduniyar nan wato ubangiji sammai da kassai,"assalamualaikum, Amin waalaikumussalam, ummuh ya kike? Ban saniba, iyayan nakane suka aikoka kaji mun mutu ko muna raye,to inaso kasanar musu, dacewa munanan da ranmu, subahanallah, ummuh ni kike fadawa wannan maganar, ummuh yaushe kika zama mara kunya haka,wallahi ummuh kin canza,? Rufemin baki idan ban can zaba mutuwa,kuke so nayi ko kuma sokuke,kuganni ina kuka,daga kai har iyayanka, bamu bukatar ku acikin rayuwar mu,daga ni har amani,nidin nan zan zamar mata uwa da uba sannan ummuh tai shaki ta huce,


Shiko tanimu tsaye yayi yana bin ummuh da kallon mamaki, to meyake faruwane? Yanaga ummuh haka ? Meyasa tacanza haka, yarinyar da nasani ko magana bata dameta ba,menene ya can zamata halaye haka,"? Kai ya jijjiga sannan ya nufi hanyar gidan su, yana shiga yashiga kiran,inna,inna !!! Inna!!! Na,am,"wai menene hakan sai kirana kake kamar naci bashinka, gani menene, inna! Meke faruwa da ummuh ne, naga ta canza, mekagani cewar inna? Najene ina kiranta taimin shiru, dana karasa shine nake tambayar lafiyarta, saita dawomin da bakar magana, wai kun turonine nagano muku tamutune ko tana raye,hhhhhhh inna ta "kwashe da dariya ,tace shegiyar yarinya yaushe tai baki haka, hhh? Bangane mekike nufiba inna ki fahim tardani ,naji kuma tana kiran da ita da kanwarta sannan tace ta yafemu acikin ahalinta, daman ummuh tanada kwanwa ne,ban saniba, hava yaro sai surutun tsiya ,to sai me dan ta tafemu acikin danginta, kafin tafara ciremu mu mun cireta ,"dama mahaifiyarta itace "yar, uwata ba suba ,kuma wallahi daga ita har kan war tata babu wadda zan rike,tai tsaki ta shige daki tabar tanimu tsaye zuciyarsa, cike da tam bayoyi kala2, bashida zabi dole hakan ya juya yanufi gidansu ummuh, sallama yayi ya shiga ,tana zaune a tsakar gidan tana yiwa AMANIH rawa,karasawa yayi,yasamu guri gefen ta ya sauna"ummuh dan Allah kifadamin me ke faruwane,meyasa ni bazaki min uzuri ba,ina me baki hakuri a matsayina, "na 'dansu, kiyi hakuri da duk abinda sukaimiki,"ya isa haka tanimu!!!!! Nace bani bukatar ku acikin rayuwarmu, dan Allah na rokeka kafuta daga lamarin mu,dani da "yar, uwata,ni nayarda na amince zan zauna da "ita na kula da "ita,na nuna mata soyayya irnta iyaye,zanyi aiki tukuru somin na tallafi rayuwarta, haba ummuh kidaina fadar haka,shin dama laifin wani yana shafar na wani, ummuh ce ta ajiye AMANI agefe ,ta mike cikin tsiwa tace"tanimu kafuta daga cikin gidannan tunkafin nayi maka ihun kwarto,

********Nashiga uku ummuh,yau "ni tanimu kike kira da kwarto,wai ummuh meyake damunkine,haka, !tanimu,tanimu, naran tse da ubangijin da ya halicci, aljanu da ,mutane,"idan na irga uku baka mikeba sainasa an mun ragaraga da kai a gidannan, a,a ummuh abin bai kai zafi hakaba, zan tafi na barmiki gidan, tunda dama ai gidan kune, babu wanda ya "isa yayi muku I'ko da shi,amma kisani ko natafi zan dawo,bazan barki ke kadaiba,

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment