Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sabon mamaki 'kyadamasa kai tayi alamar eh

'Agidan ba'a san bakida lafiya bane'

Shiru tayi danbatasan mezatace masaba ganin hakan yasa yayi parking ɗin motar yamayarda hankalin sa kanta Maryam!

Yakirata cikin sanyin murya tace ansamasada

''Na'am'' bawandake yin aikenne saike? ''Eh '' ta amsa masa tambayar cikeda ƙosawa shiru yayi naɗan wani lokaci yajuya akalar motar zuwa kasuwar habu bene wata sassayar ajiyar zuciya tasauke batare data kalleshiba tace

''Nagode, Allah yasakamaka da mafificin alkairi, yabiyamaka buƙatun kana allkairi yasakagama da duniya lafiya''

Sosai yaji daɗin waɗanan addu'oin nannata ammakuma yayi mamakin yadda tajidaɗi ganin yakama hanyar kasuwa

Parking yayi sannan yadubeta yace 'dame dame zakisaya '' kifi kilo ɗaya, madara ma kilo ɗaya''

Jintayishiru yasa yace shikenan kyaɗa masa kai tayi alamar ''eh''.

F🌹A🌹K Batool Kamba

More comments more typing

{🖤Batool kamba 🖤}✍️✍️🏃💋*SON KI NE ƘADDARA TA*💋
{🌹Your love is my destiny🌹}


STORY & WRITING
BY
FATIMA ABDULLAHI

Batool kamba

LAFAZI ASSOCIATION

Kyakkawan lafazi acikin rubutu
yanadamɓarene dabin ƙabidar adabin Hausa

Page



___________________✍️Jintayi shiru yasa yace shikenan kyaɗamasakai tayi alamar ''eh''

''Jirani'' abinda yace kenan yafita daga mota baiwani jimaba yafiti hannun sa riƙeda ledoji yabuɗa from sit yasa sannan yazagayo amazauninsa yasauna tare da tayarda motar taredasake nufar hanyarda zatasadashi da banda bari

Shidai mamaki yake saboda yasan akwai kasuwa akusa to amma meyasa dole sai habubene?

Kasadaurewa yayi tajuyo yakalleta karona barkatai yace 'maryam meyasabaki je yantalaba? nagatafi kusa Murmushi maiciyo tayi kafintace

''Canɗin akace naje shiyasa naje''

Cigaba yayi da draving ɗin harsaka kawo indasuka ganta ayashe inane gidan? Yatambayeta batare daya kalle taba, nuna masa hanya tafarayi har suka iso ƙofar gidan buɗe marfin motar sukayi atare ''kiramin babanki''

''Bayanan''

' A' ina zan gansa'

Kallonsatayi Kamar tace wani abu kumasaita fasa ''baya garine yayi tafiya''

'To kiramin mamanki '

''Mezatayimaka''?
Kedai nace kikiramin ita
Sumsum hakatashige gidan mamma nazaune gefen ɗakin hannun tariƙeda wata shar ɓeɓiyar bulalar doki

Sunahaɗa ido da maryam tadumfaro ta, sanindatayi tabbas duka zataci yasa takwasa aguje takoma bakunya mamma tarufamata baya

Ganin tafito aguje yabuɗabaki daniyar magana saikuma yafasa ganin wata babbar mace tabiyota

Bayansa yakoma tana sharar kwalla Mamman naganin sa taja birki cike damasifa tafara magana

dama kaine kadauketa saida kuka gama shashan cinku kamayarda ita ko kunya babu maganar tabashi mamaki amma saiya danne yace

Mamman kiyi haƙuri kisaurareni maryam dafarko nidai sunana shafi'u nandai yagaya mata yanda akai amaimakon yaga tanuna alhini saiyaga tajawani mugun tsaki tamkar zata tsinke harshen ta tashigegida tana ɓaɓatun itazaa rainawahankali zakizo kisameni ai

Kallon sa yakomaga Maryam waddake faman sharar hawaye yace itace mamanki? Cikin Muryar kukatace ''eh''

Jinjina kai kawai yayi yaɗaukimata ledojin yamiƙamata tare dayimata kashedin kartasake zamata yunwa

Karɓatayi yahaɗamata da ledar maganinta tayimasa godiya tashige

Lokacin har anfara kinran sallar magariba hakanyasashi tsayawa awani masallaci yayi sallah sannan yaƙarasa gida

Itakuwa tana shiga tagabakowa atsakar gidan hakanyasa taje harɗakin mamma ta'ajiye ledojin tafito dantana gudun takai su kichin

Tayi wani laifin har akayi sallar isha'i batajimotsin kowaba hakanyasatayi kwanciyar ta amma fa gaskiya tafarajin yunwa rabontada abinci tunwanda taci a asibiti lokacin kosallar la'asar ba'ayiba

Tananan kwance har ƙarfe goma nadare barci yaƙi ɗaukanta jitayi kawai an yaye labulen kifito kiɗauramin farfesu kifinnan inada buƙatarshi muryar kursiya ce kewannan maganar cikeda wulaƙanci

''Kinga kursiya banida lafiya kibari gobe idan Allah yatashemu lafiya zanyimiki''

Wata gundu memiyar ashar kursiya tamaka mata

Sannan tabar ɗakin kocikakken minti biyar batayi dabarin ɗakinba saiga Mamma dashar ɓeɓiyar bulalar ta bawani magana kotambayar ba'asi tahau jibgar baiwar Allah ganin tanada sauran ƙarfi ajikinta yasa tagudu tabarɗakin


Tasan waƴannan bayin Allah watarana sune ajalinta

Cikin ɗaga murya mamma tace ''wallahi yau inhaer bakiyi mata farfesunnanba saikinbar gidannan tunda bana ubanki bane shegiya karuwa'' jinhaka yasa tanufi kichin nantaga amma fara aikin da'alama ƴar aikin gidance tafara akadakatarda ita nandannan tagana takaimata harɗaki

Alwala tajetaɗaura tashigaɗakinta tafara nafil fili tana kuka 😭maiban tausayi kodata gama ƙarfe biyun dare yayi saita kwanta tanasauke ajiyar zuciya Allah yasani yunwa takeji amma ko karen mahaukatane yajijeta bazataje tace subata abinciba

Washe garima bata samu abinciba tunwanda mutumin daya taimaka mata ne yasiya mata shine acikinta


Fitowa tayi kamar yanda tasaba ta kammala aikinta, lokacin yunwa takeji sosai, yauma aiken nata Mamman tasakeyi bawani cefanen arziƙi bane domin papa yana siyo komai ya ajiye, amma saboda anason awaha larda ita kullum saitaje kasuwa aƙafa.

Ahaka rayuwa ke tafiya kamar juyin agogo saida papa yashare wata ɗaya baidawoba, izuwa yanzu maryam tafifita ahayyacinta

Itama iya tunzuwanta doso batadawoba.

"Tunsafe tatashi da zazzaɓi sosai ajikinta hakan bai hanata yin dukwani aikin gidanba adadsafe tsgama, tashige ɗaki, kominti biyar batayiba Mamma tashigo a masifance takeya mata magana

dakyar ta iya ɗagokanta yakalli Mamma tace

"Mamma dan Allah kibawa ɗan aiken gidannan banada lafita yau sosai"

Taƙarasa maganar tana mai kokawa da numfashita 😢

Cikin rashin imani da tausayi Mamma tace

Kozaki mutu baishafeniba aikennan saikinje tawulla mata kuɗin awulaƙance tajuya tafita

"Waini banada mahaifiyane? Kodai tarasune? Ya akai bansantaba? Ina papana? Suwaye ƴan uwana? Wacece kakata? "Tayi wa kamta waƴannan tamba yoyi ne ka tasan batada sar su.

"Waɗannan tambayoyin kullum dasunake kwana nake tashi, rasa waye zai amsaminsu"

"Idan papa yadawo zantambayeshi hala inane yaganni yaɗaukoni, kumafa innayi haka makar nayi masa haka zaiga tkar naga gazawarsanr nanuna bangode da karamcin dayayiminba zaiga rashin haƙurina yayi yawa'' to amma yazanyi''

Duk acikin zuciyarta take waɗannan maganganu.

Saukar bubala dataji ajikinta neyasa taɗago dahanzari dukane kesauka ajikinta tako ina batamasan waye keyimata wanna dukanba, ihutake tananeman temako amma ina tuntanayi daƙarfi har muryanta yadushe,tsaban azabarda takeji batako iya ɗaga yatsanta.


Wato ke kangararriya na aikeki kiyi kwanciyarki tsabar kin rainani , Mamman kewannan maganar cikeda rashin imani da tausayi


Kinsan Allah duk nadawo nasameki
adakinnan saina kasheki kowa yahuta tsinanniya gantalalliyar yainya

Wanisbon kuka tasake fashewa dashi! ''Ya Allah shikaɗai takekira tasanibawanda zaikawo mata ɗauki inhar bashiba

Zazzaɓin dakejikinta yaƙaru sosai
gawani irinciyonda kantakeyi sakamakon kukanda tasha sanin halin Mamma duk abinda tafaɗa zata aikata shiyasa tayi ƙarfin halin miƙewa

Ta Ashirin fita sukacikaro da papa abakin ƙofa wani sanyin daɗi yashigeta kobakomai tahuta da shintirin hanya.

Saukar sakenanyahigo gida kaitsaye yanufo ɗakin yarasa sukuni baisan meyasaba yana matuƙar son yayinyar ko ƴaƴansa bayayi musu wannan soyayyar kuma yarasa dalinlin hakan .


Kallonta yatsayayi ganin yanda duk tafita ahayyacinta tayibaƙi tarame manyan idanunta sunsake girma

inar Isah bakinda lafiya ne?

kaita kyaɗamasa alamar Eh

Mekedamunki manar Allah wasuhawayene taji sun zubo mata


''Bakomai papa zazzaɓi nekawai daciyon kai''

jinjina kai yayi badan yayar daba


Muje abindayafaɗakenan taredajuyawa yanufi inda motar satake

Mamma cetafito daga ɗakinta ganin papa yasa takalleshi damamaki akan fuskarta tace malam yaushi kadawo?

'bataredaya kalletaba yace yanzu' baijira jin abinda zatasake faɗiba yashige motar Maryam ma shiga tayi kaitsaye asibitin da abokinsa ke aiki yakaita nan akashiga dubata

Lokacin da akafaɗamasa abinda ke damunta baƙaramin ɓaci ransa yayiba yanada daidai rufin asiri komai aikin gidansa yunwa batakamaba sai wadda yakewa kallon ƴarsa

Godiya yayiwa likita sukafito da isarsu gida yanemi ganin Mamman nan ya balbaleta damasifa

''Kinga hadizatu inkingaji danine kifaɗamin azatona ko kare nakawo zaki bashi kulawa bale mutum ''


Ran Mamma baƙaramin ɓaci yayiba akan wannan karuwar yarin yar malam kemata wannan tijarar

Haƙuri tabashi tabar ɗakin ranta namata suya

Wani abun mamaki tun ranar papa yamanta dawata ƴa mai suna maryam mamma kuma tashiga galllazawa maryam son ranta yau kusan wata ɗaya amma abu kullum haba yakeyi, papa dakansa yake cewa inhar Mamman tanason farin cikin sa tadaina ragawa maryam shiyama tsneta

*******Washe gari tundasafe mamma tabar gidan batadawo daworiba hakanyasa baya maryam ta gama aikinta tayi kwanciyar ta


Bayandawowar mamma dakamar minti goma papa yafito yana kwalawa maryam kira, kirane wanda baitaɓayimata irinsaba, hakan yasa taji gabanta nafaɗuwa

Ƙarasowarta keda wuya yafara balbaleta da masifa bayan itadai batayi masa wani laifin ba jin kansa nasarawa yasa ya kulle kunnen sa jiyayi tamkar ana yimasa magana kamar umarnine akebashi.

Yaso yadaure amma ina hakan yasa yabuɗebaki yafara magana cikin rawar harshe


Kita --tta--ra naki ya naki kibarmin gida nagaji da ciyarda karuwa mara asali

Arazane take kallon papa kicin tsanananin mamaki

''Papa! Takirashi cikin raunin murya dawani irin firgaci maihaɗeda tsoro damamaki bai ko sauraretaba yafice

Tsayawa tayi sororo kunnentane baijiya mata daidaiba kome

Kamarfa papa korarta yayi

''menayiwa papa yakorena nashiga ukuna ina zanje? ''


Mamma ce tawani kyalkyale da dariyar mugunta🤣 tace kinga bara nakira wata hajiya ta ɗaukeki tasamar miki aikatau ko bakiso?


Cikin baƙi ciki daraahin madogara tace

''Inaso mamma''

Ta amsacikin kuka indan matace batason temakin ina zata

korufa mintuna talatin ba'ayiba saigawata babbar mace tashiga gidan

Ciniki yafaɗa kenan? Matar tafaɗa cikeda suniyanci eh wallahi hajiya kinganta zatayi saurin kawo kuɗi

'Gaskiya kan yarinyar akwai kaya'

Duk abinda sukefaɗi agaban maryam amma batawani fahimci komaiba tashi muje matar tafaɗa tare da kallon maryam tashi tayi tanajin dama ace mafarki take

Wai papane dakansa yakoreta tometayi masa hartakusa shiga ɗakinta mamma tace hijab kawai zaki ɗauko


Masukaratu inane za'akai Maryam? Meyasa papa yakoreta haka siddan?
Meyasa mamma tahaɗata da wannan matar?
Koyaya makomar rayuwar maryam zatakasan ce inhar tabar gidan papa?

Anya basa hannun mamma akorarda papa yayiwa Maryam?
Ina labarin marwan?

Amsoshinku nanan acikin littafin
Your love is my destiny

Kubiyoni domin samun waɗannan amsoshin.

{🖤Batool kamba 🖤}✍️✍️🏃



💋*SON KI NE ƘADDARA TA*💋

{🌹 Your love is my destiny 🌹}

STORRY & WRITING

BY
FATIMA ABDULLAHI

{Batool Kamba}

Dedicated to my lovely mom ALLAH yaƙara tsawonrai 🌹🌹


___________________________✍️wai papane dakansa yakoreta tome tayi masa hartakusa shiga ɗakin mamma tace hijab kawai zaki ɗauko

Batareda ta amsaba tashige ɗakin wani kukane yasake kufcemata

Kukane irin wandake fitowa tun ƙasanrai , kukane maihaɗeda ƙunar zuciya

''Inna lillahi wa'inna ilaihirra ji'un! ''
''Inna lillahi wa'inna ilaihirra ji'un! ''
Inna lillahi wa'inna ilaihirra ji'un''

''Alhamdu lillahi ala khulli halim ''
''Alhamdu lillahi bini inatihi tati mussalihun ''
''Alhamdu lillahi wakhhafa ''

''Alhamdu lillah ''

''Alhamdu lilah''

''Aljamdu lilah''

Abinda take nanatawa kenan afili jinzuciyarta take tamkar zatafashe

''Wayyo! Allah nashiga ukuna ni Maryam inazansa kaina Allah yakawomin agaji nibaiwarkace mai tsananin rauni Allah natuba ''😭

''Astaqfi rullah ''

''Astaqfi rullah''

''Astaqfi rullah wa'atubu ilak''


Jin anfara kwalamata kirane yasa tayi saurin fitowa bayan ta ɗauko hijab ɗin kallon motar papa tayi kasancewar atsakae gidan suke, nufar motar tayi cikin sanyin jiki papa naganinta yayi saurin ɗauke kai durƙusawa tayi agaban papa bayan ta isa wajan cikin murya mai rauni tafara magana

''papa bansan dawacekalma zangodemakaba, bansan dawane harafi zan godemakaba, haƙiƙa kazamomin wani jigo arayuwata , wanda bazan taɓa mantawaba, kazamomin bangon jingina alokacinda narasa majin gina, kazamomin tudun dafawa alokacin da narasa madafa papa Allah yabiyaka bazan gushe dayimaka addu'a ba, zantafi kamar yanda kabuƙata nabarmaka gidanka amma kasa aranka bazan taɓa mantawa dakai ba arayuwa katallafeniii ''

Kasa ƙarasawa tayi saboda wani irin kuka daya tasomata, dasauri tamiƙe tayiwaje mamma takalli matar tace kuɗinfa? Murmushi matar tayi sannantace Hadiza bakida sauƙi akan kuɗi

Kallon bakida hankali mamma tayi mata tace ke awannan zamanin kuɗi ai sune rayuwa malama kibaninkawai

Buɗa jakarta tayi taɗauko damen kuɗi tamiƙawa mamma washe baki tayi kafintakarɓa tanafaɗin yanzun naji zance hajiya sa'ade karki manta ƙasararda nabakifa maitsadace dan Allah kisamomata gurri mai gwaɓi kindaigane taƙarasa maganar tanamai kashe mata ido

Murmushin ƴan duniya hajiya sa'ade tayi, karkisamu damuwa Hadiza wannan yarinya aisai manya kumanasan baƙananun kudi za'a samu akantaba .

Nandai sukayi sallama papa najikuma yana gani amma yakasa cewa ƙala shifa acikin ransa tausayin Maryam yake amma yarasa dalilin dayasa yace tabar masa gidansa shidai yasan bahakane aranshiba , jiyake bakinsa yayimasa nauhi hakanyasa yakasa magana har matar tabar gidan wani abin haushima lokacinda Maryam keyimasa magana yasu yaceda Ita wani abu amma yakasa

Fitarsu daga gidan kaitsaye sukaɗau hanyar barin garin neimey Maryam tatsorata sosai dan itadai bata taba ganin irin wannan tafiyaba gashi kuma ba'itakadai bace sunfi su talatin amotar kuma duk mata bawanda yakulata itama bawanda takula saikuka datake matar dake gaban motarce ta juyo amasifance tafara magana

Ke Malama kiyimana shiru kowaye kikaga yana kuka a nan dazakidami mutane

*MARWAN*



Guduyake shararawa titin garin abuja kaidaganin wannan kasa tuƙin gangancine dubada yanda yake draving baya damuwa dawanda ke kan titin burinsa kawai yakai inda yake jamil dake gefensa duk atsirace yake Allah ne sheda yayi danasanin biyosa dayayi yasan waye marwan bai iya fushiba cikin shakkar sayace

''please, marwan come down mana karka kashemu abanza naga ai gaskiya suka faɗa da tana sonka aibazata gudu ajajibirin ɗaurin au.....'' Wani irin birki dayajane yahana jamil ƙarasa maganar

Cikin wani maɗaukakin ɓacinrai yace ''stop Please jamil ''yafaɗi atsawace wandayasa jamil ɗin jan bakinsa yayi shiru

Yashiga bashi haƙuri kosau raronsa marwan baiyiba yafita daga motar yana huci Allah mayasa lokacinda zai jabirkin yagan gara gefe da anyi ɓarna, tsaye yayi yamarasa mezai yiwa jamil dasu Khalid yahuce

Shima jamil fitowa yayi
''please marwan kafahimta ada inagoyon bayanka kaci gabada son yarin yarnan amma ayanzu nadawo daga rakiyar ka dama ai anfaɗa tsintacciyar mage aibata mage ''

Baikula dayanayin dayashigaba yacigabada cewa

"Marwan sanin kankane bawanda zai ɗauke hotu nanta inhar ba itaba wamaysan inda suke? Kuma aiii''

Wata muguwar shaƙa marwan yakai masa, nan yafara dukansa baji bagani Wani ikon Allah jamil baya ramawa saidai yana ƙoƙarin kare kansa da dukkanin hanna yensa wani mai motane yatsaya ganin abinda ke faruwa nan yafara rabasu dayake shi Jamil baramawa yakeyiba faɗan yayi saurin rabuwa kallon marwan yayi cikin zaro ido da maɗaukakin mamaki yace marwan!

Haba yallaɓai dagir manka meyayi zafi? Ko kallonsa marwan baiyiba yagiftashi yashiga mota A 360 yabar wajen kallonsa mutunan yamayar kan jamil yace yalla ɓai meyahaɗakada yallaɓai baka gudun abinda zaije ya dawo kasan masu kuɗin nan basada mutunci

Barinma wannan shakwa ɓaɓɓen yaro waye bai san shiba? Kab garin abuja dakaceee

''abokinane'' Jamil yakatse shi

Yanafaɗin haka yabar wanjen Allah mayasa ba mutane ke yawan wucewa kan titinba hanyace hara hayaniya

Kaga inazakije tunda shi yawuce loko ESTATE jamil yafaɗa kaitsaye

Muje na saukeka Allah ya ki yaye gaba

Bamusu Jamil yabishi ganin yakama hanyar ganinzasu wuce gidansu yasa yadakatar dashi fita yayi

''Nagode ɗan uwa ''
Jamil yafaɗa haɗida juyawa yashige gida

Marwan tun barinsa wajen yake jinsa wani iri magan ganun Khalid da jamil ke faɗomasa arai

Shifasam bayaganin guduwa my soul ɗinsa tayi yafi yarda da saceta akayi kowani abun badai guduwaba duk cikin kalaman jamil bawanda yayiwa marwan ciyo kamar tsintacciyar mage kenan ma gori yake mata


''No never wallahi my soul bazatayimin hakaba mema zaisa tayimin haka, tana sonafa haba kai bazai yiyuba ''

Shikaɗai yaketa magana tamkar wani zararre harya isa bakin gate ɗin katafa ren gidansu hone ɗaya yayi saiga gateman yazodasauri yabuɗe

Kaitsaye parking space yanufa ko parking arziƙi baiyiba yafito direct yanufi part ɗin mom

''Mom!
Mom!!
Mom!!''

Yashiga kwalamata kira tamkar zaifasa gidan


Mom dake farlou tamiƙe tanafaɗi lafiya dai? Wani irin rungumeta yayi tare dafashewa da kuka tamkar ƙaramin yaro

Sosai mom hamkalinta yatashi ,zaunardashi tayi sannan tamiƙe taɗauko masa ruwa maisanyi a freg saidayasha sosai

Yafara magana ''mom wai dagaske my soul batasona shiyasa tagudu mom dagaskene dan Allah kigayamin? Yanamagana hawaye na tsiyaya a idanunsa

Daman tatsuniyar gizo ai bata wuce ƙoƙi sosai ran mom yaɓaci

Kaga bstason wannan tayar da hankalin dayake

A'a bagaskiya bane kamanta dawacece my soul ɗinkane? Yazakayimin wannan tambayar Please ka kewanyar da hanka lin ka kaji

Shiru yayi yana sauke zazzafar ajiyar zuciya

Miƙewa yayi yanufi part ɗinsa kaitsaye haban wadrop yanufa yaɗauko wani allon zane wani irin zaro idanu yayi waje 👁️👁️ cikin tsananin tsoro yajefarda allon yana ja da baya tamkar wanda yaga mala'ikan zare masa rai

Too masukaratu aganinku me marwan yagani dahar yabashi tsoro haka?

Amsarku nanan a page 14 & 15

Inhar banga ruwa comments ba sainan da One monch zakusa ke gani post inkuwa kun shirya nima ashirye nake


💋SON KI NE ƘADDARA TA 💋

🌹your love is my destiny🌹

STORRY & WRITING
BY
FATIMA ABDULLAHI
{Batool Kamba}

Wannan shafi kyau sadaukar wane ga duk wata marubu ciya dake faɗin duniya ina sonku writters


___________________________✍️ma gana yake son yi amma yakasa
''Mom!''
Yakwala wa mom kira afir gice yana mai miƙewa yanufi fita waje yana mai mai ta kiran mom

Tun aharabar gidan yadinga faɗi yana tashi abun mamaki securiti's zuba masa 👁️sukayi dan basu taɓa ganinsa ahakana gashidai bai daɗe dashi ga part ɗin nasaba mom dafe kai tayi ji kiranda yake yimata, lamari marwan nabalain bata mamaki mutum kamar ba namiji ba

Mom! Yasake kiranta lokacin daya shigo part ɗin akiɗime

Lafiya marwan? Ta tambayeshi ganin yanda yake zaro ido kamar tsohon kwarto😂

''Mom dan Allah wa yashigar min part ɗina daba nanan? ''

Kallon mamaki tayi masa cikin halin ko inkula tace

Wakasan yana shigar maka part ko wayasan password ɗinka?

''Mom dan Allah zo ki gani Please yafaɗa out of control''

Ganin kamar baya hayyacin sa yasa mom binsa , koda suka isa part ɗin bedroom ɗinsa suka nufa kaitsaye gurin allon zazen yakaita ɗagoshi yayi

''mom kinga sauran maganarce tamaƙale saka makon ganin wayam .

Menene?

Kasa maga yayi saboda ɗimauta saida yaɗau dogon lokaci sanan yaja numfashi

"Mom kinsan menazana?

A'a

Mom face ɗin my soul nazana amma natarar yakoma kwaran kwal☠️🙄

Yanzukuma bakomai Please mom meke shirin faruwa ne?

*MARYAM*

Sunyi tafiya takai ta 5 hours suka huta sannan suka cigaba daga nan bazatace ga abinda yasake faruwaba saida ta buɗa ido taga duhu yamutsa fuska tayi ganin suna ƙoƙarin tsayawa yasa duk jikinta yayi sanyi

"Niyanzun inane za'akaini gunsuwa zan zauna Allah kajikaina ka agazamin Allah karkabarni na wulaƙanta aduniya 😭"

Tsawarda aka dakamatace tadawo da ita hayyacin ta

Fito malama kinwani zaunawa mutane amota inajin bakitaɓa shiga motabane

Wasu zafafan hawayene suka wankemata fuska jin irin tsawarda yakemata aka

"Yihaƙuri" tafaɗa cikin muryar kuka

Tsakiyaja kafin yayi gaba abinsa,
Shin yanzun ita menene makomar rayuwar ta

"Ya Allah kajiƙaina "

Wani gida tagani da alama nanne masaukinsu domin sauran yanmatan duk sun shige ragiwar kuma suna ƙoƙarin shiga itama hanyar tanufa.

Gidane da ɗakuna ajere barandace doguwa yawan ɗakunan mayasa bansan adadin suba

A tsakar gidan suka tsaya, wasu ƴan mata kusan su goma wasukoma suka shige ɗakunan da'alama sunsan yanda gidan yake wata matace dafito dagawaniɗaki dake gefe ɗaya, hannunta ɗauke da sigari tana busawa, jan sigarin take irin nakwararru kuma ta tattun ƴan bariki, kallon wula ƙanci tayimusu tareda yatsina baki

Kune baƙi annan dafatar kunsan meyaka woku nibana ɗaukar iskanci dole gobe kufara aiki danbazan baku ɗakuna kushare kuzaunaba .

Cire glas ɗin idanun tatayi tabisu da kallo ɗaya bayan ɗaya idanutane yasauka kan Maryam saida taƙre mata kallontsaf yafito ta da hannu

Cikin ɗari ɗari dajiki tanufi inda matar take sake kallon sauran tayi bangaya muku sunanaba ko?tatambaya cikeda iskanci

Taɓebaki tayi da alama hakan yazame mata ɗabi'a

"Zaku iya kiranada uwar gida ko anty kundai gane ?"

Jinjinakai sukashigayi itadai Maryam duk atsorace take kasan cewar bata sababa. kallon Maryam tasakeyi cikin iskanci tace my love yasunanki?

"Mar r y a m" tafaɗa cikin rarrabewar harshe murmushin ƴan duniya tayi

Dagayau sunanki qutty kinji? Kyadakai tayi alamar Ehm


Nan akashiga bawa kowa ɗakinsa har maryam ɗin ɗakine maiɗaukeda madaidai cin bad, Waldrop sai mirror dakujera two sitter, da bathroom .

bathroom ɗin tashiga taɗauro alwala cike da damuwa tafara sallah.

Harta idar taci gabada tunanin makomaer rayuwarta, taɗau alƙawarin dul wuya bazata sayar da mutuncin taba, danta soma gano wani abu dangane da wannan gida
amma zata bi ahan kali tagani har Allah yasa tasamu hanyar gudu.

Washegari tundla tayi sallar asubahi tarinƙajin hayaniya dataso tayi zamanta saigawata matashiyar yarinya taahigo waitafito waje inji Uwar ganta lalli hijab ɗinta tasanya
tafito ganin gidan yacikada mutane daban daban yasata fara tambayar kanta "wannan wane irin gidane? "

Muryar Uwargida ce taji tafara magana. qutty zonan. Dakar kartaje saikuma tanufeta, matsawa tayi ta zauna cikin ladabi tace "ina kwana " lafiya cewa uwar gifa

Sannan tace da alama ke bakisan wannan inaneba amma zakisani naga kowa ya fahinta kece kawai kikeson bamu problem amma You don't worry qutty zaki gane, yanzun jekiyi wanka natanada miki costomer yananan zuwa zaki tayashi kwana baƙone kisaki jikinki kikwashi rabonki karki kuskura kimai musu komaiyace

Saurin katseta Maryam tayi dacewa "hajiya kiyi haƙuri ban fahimtaba , wani kuma? A ina yasanni nida nazo jiya wana sani, waya sanni dahar zaizo wurina . kuma naji kince costomer nida bana kasu wanci meya haɗani da costomer?"🤣

Sosai wurin akashiga dariyarta ciki kuwa harda waƴan dasukazo jiyan

Kumin shiru cewar uwar gida kinga qutty aiki bata ƙananun mutane bace so karkidami kanki cos kinada abinjan hankalin ɗa namiji karkiyi wasa da damar ki wanna dakike ji nace zanhaɗaki daahi babban mutunne a Nigeria so kiyi amfani da damar ki wajen sa

Kan Maryam yasake kullewa itafa bagane wannnan kurman zance takeba "Please hajiya let me go to the streat point zanfi ganewa " tafaɗa cikin yatsina tana son tabbatar wa dagaake wannan gidain karuwai ne

Cikin ɗanjin haushinta uwar gida tace jeki kiyi wankan zan aiko miki da kaya idan kunje zaki gane nufina ok yamutsa bakitayi kamar tayi magana kuma tafasa

, kamar yanda uwar gida ta, Umar ceta wasu ƴan isan kaya takawo mata taso taƙisakà kayan amma saita tuna karfa tayi ƙoƙarin ja inja da ita takoreta Allah mashaidane wani abu takeji maikama samun freedom, wato ƴanci .

sosai kayan yakarɓi jikinta kasancewarta Black beauty kayan kuma golding colour kamar dan ita akayisu the best colour ɗin ta kenan .

Ridane dawando rigar iya gwuiwa shimadai wandom baikai ƙasaba.

"zuwa yanzu tacire komai daga ranta zatata fuskanci rayuwarta tayanzun.

Motsin mutum taji dasauri tajuya ganin wani tayi atsaye yana mata wani irin kallo data kasa ganesa, tarigada taranfo uwar gida zata yarda tabishi daganan zatasan abinyi..

More ✨comments ✨ more ✨ typing

F🌹A🌹K 🖤BATOOL KAMBA 🖤}forever ✍️
🏃🏃





💋 SON KI NE ƘADDARA TA💋

{🌹 Your love is my destiny🌹}

STORRY & WRITING
BY

{🖤 Batool Kamba 🖤}

Wannan littafin kacokan sadaukar wane ga mahaifiyata abar alfaharina
Allah yabani ikon kyau tatamiki ameen


_______________________________✍️

Ganin baiyi mata sallamaba yasa tacigaba da sabgo ginta,

baƙarya taji haushisa sosai, ƙato dashi bai iya sallamaba.

mtsuu taja

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment