Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

?"..

"Nima ,mota zanje na jira shi" murmushi yayi, yace Soon insha 'Allah"...

"Allah ya kaimu "cewar,Basmad..

Hajar kam bata, sake cewa komai ba ,

Mota Dr ,ya koma basmad kuma ta shige ciki ,suka bar Hajjo da Captian..


Gyaran murya Captian yayi ,yad'an jingina da jikin motar,Basmad "Hajjo haryau baki ,bani amsa ba kince kuma zaki sanar da ,Dady duk abunda yace zaki sanar dani, Hajjo ina so ki sani ,ina son ki tsakani kuma da 'Allah komai naki yamin , soyayyar da na keyi miki tamkar tafiyace mai nisa da na fara yinta wadda bata da lokacin yankewa har abada.na san burina zai cika matsawar ina tare da ke domin kuwa dukkanin burina yanzu bai wuce na samun ki a matsayin matata uwar ya'yana ba. Ina son ki fiye da gwal ko kud'i"..

Tsaki hajar taja cikin zuciyar ta, tace sai kuma kaje kayiwa ,wasu dad'in baki amman bani ba ,don ko nariga da nagama sanin halin maza ,na gama sanin dad'in bakin su, duk wannan kalaman banzan da kakeyi jinka ,kawai nake don ko Akram ya rigaka fad'an su, kuma 'Akram ya gama b'ata duk wani d'a namiji a gurina, da mutun d'aya na yarda 'a yanzu shin ma bawai nayarda, dashi duka bane, azahiri kuma tace..

"Ina sane da zance kad'an bani lokaci zakaji amsa ta ,na kuma gode , da wainan kalaman duk ni kadai".

"Tow ina nan ina jira ,ai kad'an ma kikaji matsawar ina tare dake zakiji ,kalamai masu kwantar da hankali don , ko ina son ki ked'in kamar hasken wata kike mai hasken da ke haske idaniya ,haka kuma kalaman ki tamkar sugar suke ma'abocin zaki, tabbas kinyi kama da kan ki hakan ya sanya naji ina son ki, don haka bazan tab'a gajiya dake ba gurin ganin ,nasaki cikin farin ciki ,koda bazan samu hakan daga, gurin kiba"..


"Tow nagode Allah ya mana me kyau ni barin shiga ciki, gara kaje ka samu Doc...kar yayi ta jiran ka babu d'ad'i"..

"Tow habibty na ki kularmin da kanki, ki shafa min kan beby na "...

"Tow zataji sai anjima" nan sukayi salama..


******

Yau jumu'a yau ne aka d'aura 'auren Basmad k'arfe biyun narana bayan sallar jumu'a...

Mutane sai shirin tafiya Kano kai amarya suke, motar da za'a kai amarya har tayi gaba tare da k'awayen amarya da su Hajar , iyaye ne kawai basu fito ba ,suma suna shirin fitowar ne...

***

Kano

"Ummi kinji yanda mukayi da ita ,ban samu lokaci bane shiyasa ban miki zancen ba, sai yau kuma ta shaida min cewa ita kanta bata san inda yake ba 'a halin yanzu don tabaro shi a india ,gadai pic d'inshi ta bani "..

Karb'an pic d'in tayi ,ta fara kallo kamar shi d'aya da mahaifin su, Samir kamar anyi kaki "Allah Sarki Malan har ka mutu Allah besa ka cika burin kaba, wannan d'a bashi da maraba da Malan, insha 'Allah mun kusan cika maka burin ka , Samir duk yanda za'ayi ka samu lokaci kaje indian pls ".

"Tow Ummi duk abunda kika ce shi zanyi ,farin cikinki nake so, amman Ummi ina so ki bani lbrn su meyasa tunda nake arayuwa ban san ,suba se yanzu ?"..

Dafa 'Doc...Ummi tayi ,tana hawaye wannan ,wani sirri ne wanda mukayi alk'awarin bazamu tab'a bud'e shiba, bazan iya fad'a maka ,komai ba Samir kuma ina me umartan ka da, karka sake tambaya ta matsawar ,kana son farin ciki na , da kaje ka nuna mata cewa kai d'an Malam ne?"..

"A'a ban ,nuna mata ba ,naji ance gobe za 'ayi shara'an k'arshe anan kotun dake jahar kano daga, nan kuma zata, zauna ,anan gidan yarin kano"...

Ummi ,na kuka tace "meyasa baka sanar da ita kokai waye ba Samir , idan sunzo ina so zanje na ganta , yanzu baka ganin akwai hanyar da zata iya fita?"..

"Duk yanda naso da ta gane waye ni ta kasa ganewa dalilin dayasa kawai na rabu da ita kenan, na nuna zan taimaka mata idan ta sanar dani 'inda ,d'anta yake, gsky babu wata hanya da zata iya fita 'Allah nekawai ya isa fitar da ita sai kuma wanda ya had'a mata wannan mugunta ...

"Ni 'idan ,naje zata ganeni zata san wacece ni duk da munyi shekaru da, dama bamu had'u ba, Allah yasa had'uwarmu yayi kyau Allah yasa ta cenza hali ".

"Ameen Ummi don kince karna sake miki zancenne amman da zanso jin labarin ta koda ,d'an kad'anne "...

"Hmmm Samir lokacin Sallah yayi barin tashi, idan ,nace zan baka labari babu 'abinda zai haifar min sai tuna Malam aduniya kaf rayuwa ta babu ,labarin dana tsani tunawa irin lokacin da mukayi zama da Lubabatu , "tana gama fad'ar haka ta mik'e tayi dakin ta .....

K'arfe bakwai na magrib yan abuja suka isa kano , gidan su mijin Basmad aka ,kaita nan zata kwana da k'awayen ta washe gari a mik'a ta gidan mijin ta,.

Su Hajar na zuwa basu jima ba suka tashi 'ita da Khadee zasu tafi subar sauran k'awayen tare da Basmad ,babu yanda Basmad batayi dasu akan subari sai gobe ,ba 'amman suk'i suka tafi Khadee tayi gidan su Hajar ma tayi gida tare da wasu yan uwan su da zasu kwana cen gidan....

Suna isa tun daga bakin ,kofa Jawahir tayi kan Hajar ,tana murna ta rungume ,maman ,nata, tsam tsam kamar zata koma ciki , itama Hajar rungume tan tayi ,ta d'auketa suka shiga ciki.

"Beby na bani lbrn abubuwan da yaya Kalifa yayi maki bayan tafiya ta"..

Jawahir dake ,kan ciyar mamanta ,tana shan ice cream d'in data siyo mata ,tace" kullum ya dawo daga office yana fita dani ya kaini park ya dinga siyamin abun dadi , kuma idan dare yayi , shida Grandfather kafin su kwanta bacci sai sun tabbata nayi bacci ,da grand f ze tafi London ,nayi ta kuka, kuma 'Ancle Kalifa ma yazo ya tafi abuja ya barni dagani sai me aiki shima nayi kuka, Mummy na dan Allah karki sake tafiya ki barni".

Murmushi Hajar tasa ta kuma matseta 'a jikin ta, tana shafa gashin kanta "naji Beby na bazan sake ba kow , sauka ,ki zauna kijirani ,nayi wanka saina baki tsaraban ki"....


Washe gari

"Doc...nannane gidan yarin ?gsky duk da banshigaba tukun ,nasan mutanen ciki suna cikin ukuba " Eh Ummi nanne saima kin shiga ciki zakiga mutane abun tausayi muje"...

Suna shiga suka fad'i sunan wacce suke son gani aka musu 'umarni da suje gurin da idan bak'i suka zo, suke zama, bayan minti k'adan saiga wani ya fito da wata mata, matar na ganin Ummi sai tayi k'okarin komawa ciki tana, "wlh bansan taba wlh muguwa ce kufitar da ita nashiga uku wlh muguwa ce nashiga uku idan baku fitar da itaba ,harku zata kashe"..


Muje zuwa




*BY Dija_Waziri*πŸ’‰
[18/12 7:33 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
*DOCTOR HAJAR*πŸ‘©πŸ»β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰



Chapter 29

Wanda ya taho da ita ne ya daka mata tsawa "ke bama son haya niya da rashin hankali, kin gane kow idan zaki 'iya ganunsu ga wuri ki zauna idan kuma bazaki 'iya ba wuce muje ,don kina b'ata man lokaci ". Tana daga k'ofa ta rik'e kofa kamar wata mara hankali "ni bazan jeba ,ban san suba wlh mugaye ne kasheni zasuyi". Nata maganar tana shirin komawa, jin muryan Ummi ne ya dakatar da ita.

"Lubabatu ina son kid'an bani lokacin ki, ni ba nazo nayi miki wani abu ,bane ,nazo ne don in sanar dake abu". Jiki a sukwane ta dawo ta zauna tana kuka duk ta rame ta fita hayya cinta 'Amman hakan besa 'Ummi kasa gane taba don ko a mafarki taga fuskar ta zata gane.

"Hajiya kinga yanda 'Allah ya dawo dani kow? Nayi nadaman rayuwan dana,jefa kaina ,abunda na shuka yau gasu ina ta girbewa, Malam yayi gsky da yace nabi duniya a hankali hak'ika na cuceku na cuci rayuwa ta kuma na cuci d'ana tilo na jefashi wata gurb'a taciyar rayuwa, najima ina ,neman ku ,keda malam na rasa inda zan samo ku sai yau gani gaku shekaru da ,dama don Allah kuyafe man ".

Wani d'aci da k'una zuciyar,Ummi keyi ,"ba wannane ya kawo niba Luba, cuta kam da zalunci kin man shi sai dai nace miki Allah ya saka man kuma, mu had'u a lahira ba komai bane ake yafewa, Malam kuma ,ki bari 'idan kinje cen kunyi shari'a don ko ya rigamu gidan gaskiyi kuma bak'in cikin da kika cusa masa yana d'aya daga cikin abunda ya mutu dashi cikin zuciyar sa "..

"Inna lilahi wa inna ilaihi raji'un Hajiya karki cemin Malam ya rasu ? Na shiga uku ni Luba ya zanyi da hakkin bawan Allah ya zanyi da Hakkin shi, Hajiya ki taimaka, ki yafe man ko na samu sassauci a rayuwa ta, ".

"Hmmm yau kuma Luba ko kin manta kece Lubabatu ko ,kin manta irin cin zarafin da kika man ko kin manta cutar da kika man arayuwa ,yanzu kinyi wa kanki adalci bakiji kunyar cewa na yafe maki ba? Yanzu duk irin duniyar da kika nema ina riban shi? Jibi yanda 'Allah yayi dake yanzu dama 'Ai Allah baya barin wani don wani kuma duk wanda ya hau motar kwad'ayi tow ,wlh sai ya sauka 'a tashar wulak'anci ,kinga yau naga riban hakuri na daman ,Malam yana ,nusar dani akan duk abunda ze saman ,na zama ,me hakuri da juriya ,yau gashi hakurina ya kaini matsayin da banyi tunanin zanje ba tun randa kika zalunceni, Abunda ya kawoni daman shine wannan yaron kin san shi? Ta mata nuni da, Dr Samir ,kanta dake ,k'asa ta d'ago takai ,idon ta kan Dr Samir"Eh na san shi, shine wanda yace ze taimaka man ,naga d'ana ". Yawwa tow ,wannan yaron ba kowa bane sai Samir wanda kike ikirarin baze tab'a arziki ba ko bayan ya girma kuma ze wulak'anta 'a duniya idan kina raye sai kinga bayan shi, yau gashi dai shine wanda ze taimakeki ,kuma wanda ,duniyana tasan da zaman shi ina fatan kin tuna shi ?"..

Girgiza kai tayi tana, nunashi tana kuka" nayi kuskure arayuwa ta ki dena tunamin rayuwan da yariga ya wuce ,na zalunci wannan yaron yana k'arami na zalunce shi, hak'ika ni butulu ce ni ,nasan hakan Amman don Allah kuyi hakuri ku yafe man ". Murmushi Ummi tayi tace "a halin yanzu babu wannan zancen kin makara 'dama ni bani da burin daya wuce naga kin wulak'anta 'a duniya kuma nagode Allah daya nunan wannan rana ina raye Samir tashi muje" tad'au jakar ta zasu fice .

K'afar Samir Luba ta kama tana kuka tana cewa "don Allah ka rok'i mahaifiyar ka da ta yafe man ko zan samu sassauci ,cikin ziciyata ,Hakika na kasance yar adam 'Amman butulu wacce ba'a mata 'Alkairi ta kyautata, na kasance mace me son duniya fiye da komai a rayuwa na kasance mace mara juriya da hakuri mace wadda bata, tab'a yarda ,da k'addara ba mara zuciya , Hak'ika na citar da iyayen ka fiye da kowa 'a duniya na jefasu cikin halin k'unci da, damuwa musamman mahaifiyar ka nafi cutar da ita , nasan bata 'tab'a sanar dakai wacece ita ba, tow yau zan baka labarin zamana da ita tun daga farko har k'arshe ,Amman ina neman Almarman ka da karka gujeni ko bayan ka sani ka tayani rok'on ta da tayi hakuri ta yafe man"..

Ummi da takai bakin ,kofar fita ,taji muryan Samir "Ummi karki manta kece kike yimin nasiha 'a kullum akan na zama mejin k'an yan uwana musulmai na zama ,me yawan yafiya na zama ,me hakuri akan duk wata damuwa ko bak'in ciki da hakurin abinda ina iya ramawa ko d'aukar fansa. "

Juyowa tayi ,tana kuka tace "Samir wannan matar ta cutar dani arayuwa bazan iya ,yafe mata ba" tabbas ,Samir na zalunce ta na cutar da ita batayi k'arya ba zauna ,na baka lbrn koma " karki yarda na fad'a maki karki yarda wannan maganar sirrice danagi sai ke sai Malam sai Allah , sai kuma wainda mukayi rayuwa dasu a lokacin su kad'ai suka sani don haka, ki barshi 'iya nandin". Bazan iya ba Hajiya gara duniya tasan wacece ni gara na gaya masa irin zaluncin da nayi wanda yanzu nake nadama " komawa da kallon ta kan Samir tayi , Samir ni kishiyar mahaifiyar kace ni Malam ya fara'aure kafun ita"..

LABARI
shekaruna biyar da Malam ban tab'a haihuwa dashi ba, kuma bawai haihuwar ce banayi ba 'a'a duk sanda na samu cikin zubarwa nakeyi saboda bani da niyan haihuwa dashi kuma badon komai ba sai don shi talaka ne, kuma ni a rayuwata babu wanda na tsana, sama da talaka na tsani talauci saboda nima 'a cikinta na tashi,

Babu yanda Malam beyi dani akan ,nadena shan maganin zubar da ciki ba sai ,na nuna masa be isaba idan har nabari na haihu dashi me yake dashi da zai rik'e yaran , haka yaci gaba da hakuri yana zama dani ,yaki sakata ne saboda yana jin ,nauyin mahaifina don shine yayi sanadin samun aikin shi, tow ana tafe ana tafe ya bijiro man da zeyi aure babu yanda banyi ba 'akan kar auren ya, yiwu Amman da 'Allah ya tsarawa Hajiya shan wahala saida ta shigo gashi yar babban gidace ita, tafito daga family d'in manyan mutane masu karamci da mutunci ,

Mahaifin Hajiya babban malami ne a k'asar nan kowa yasan da zaman shi kuma babban atajirin me kud'i ne ,ita kad'a ya haifa , bayan ta girma Allah yayi masa rasuwa ya barmata dukiya masu ,yawa ..

Shigowanta, gidan Malam yasa komai ya cenza nadaga rayuwan mu , muka koma katon gida ci da sha babu wanda yake gagaran mu ,kuma duk ba dukiyar kowa bace muke wadak'a dashi face nata duk iya kyautatawa da girmamawa Hajiya naban ko ,kaya ta siya sai ta sayoman irinshi idan ta dawo daga 'aiki duk motar data cenza nima irinta zata cenza man , idan ta d'auki albashi takan samman ,nasamu na kashewa tunda ni banyi karatu ba , ta d'aukeni da zuciya d'aya amman ,ni ba haka na dauke taba don ko duk abunda take man ban tab'a son taba, burina 'a kanta shine ,nasan yadda zanyi na mallaki dukiyar ta, kud'in gadon ta kuwa Malam ta baiwa tace ya dinga juya mata su..

A kwana 'atashi Allah yasa ta ,samu ciki, alokacin hankalina yayi dubun tashi don kuwa nayi alk'awarin yanda ban haihu ba itama bazata haihu ba , saboda tunda rayuwan mu ta cenza nake neman haihuwa ido rufe ,Allah be ,ban ba Hajiya ta fuskanci bana k'aunar ta 'Amman hakan besa ta dena mun duk wani abu da take man ba ,tsakanina da ita habaice habaice maganar banza zagi kai ,k'arshe ma ciki dake jikinta cewa nayi bana Malam bane awaje ta samo shi, amman ahaka take hakuri dani, hajiya ta kasance me zurfin ciki da hakuri duk abunda nake mata be tab'a damun taba ko ,tanunan taji haushi, ni kaina ,nakan zauna, nace wace irin matace ita wacce bata fushi.

Ko ,kad'an Malam be tab'a nuna mana banbanci nida ita ba ,Amman ,ni kullum a korafi nake , yafi sonta a kaina don ita mekudi ce kuma suna cutar dani shida ita basa ,sona, cikin ta yana wata biyu nasan yanda nayi da wayo nabata wani ruwa tana sha bayan awa 3 cikin ya zube..

Ba k'aramin bakin ciki sukayi ba ita da malam haka suka d'auki ,kaddara sukaci gaba da addu'a , niko nayi farin ciki da gud'a.

Tow haka na dinga yi mata saida na zubar mata da ciki uku ana ukun nne suka gane , ranar da suka gane Malam ji yayi kamar ya kasheni ,don bak'in ciki har yayi niyar sakina 'Amman Hajiya tace karya sakeni ya barni da 'Allah ze saka masu , tow tundaga wannan lokacin muka fara samun ,matsala da malam ta b'angare Hajiya kuwa babu abinda ya cenda komai tanamun kamar da..

Bayan shekara uku Allah ya kuma bata wani ciki, shima babu hanyar da banyi ba ,Akan naga ya zube amman da rabon sai kazo duniya ,cikin yak'i barewa , haka tayi ta rainon abunta har Allah yasa kakai wata ,tara ta haifo ka , Malam ya soka kamar babu gobe soyyar danaga yana yimaka ,kaida mahaifiyar ka yasa nace saina rabaku dashi.

Dalilin dayasa naje wajen boka yamin aiki akanku , ku ,kenan yazama duk ,dukiyar mahaifiyar ka ya dawo hanuna ,nike juya kujeran kud'in gidan, Malam kuma ya zama yana tafin hanuna sai abunda nace yayi zeyi ,kuma nasa ya tsaneku , ko ganinku baya son yi , nakuma sa 'aka, kori Hajiya daga, gurin aiki nasa boka yamin aiki akan duk inda taje neman aiki ,karta samu



Muje zuwa



*BY DIJA_WAZIRI*


TEAM AKRAM😜
[18/12 7:33 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
*DOCTOR HAJAR*πŸ‘©πŸ»β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰



Chapter 31

Ya zama Hajiya ta shiga matsananincin kuncin rayuwa ,ta rana 'abinda zataci ma gagaran ta yakeyi, Malam kuwa ko damuwa dasu bayayi don ko na hanashi zuwa inda ma suke.

Haka rayuwa taci gaba min cikin daula da walwala ,cikin jin dad'i duk wannan abunda 'akeyi mahaifina besan komai ba, bayan shekara hud'u , lokacin kana da shekaru hudu da wasu yan watanni Allah yasa na samu ciki dad'i kamar ya kasheni , mahaifiyar ka , kuwa na dawo da ita kamar baiwa 'a cikin gidan itace girki gidan wanke wanke ,wankina dana Malam duk ita keyi , duk irin cin zarafi da wulk'ancin da nike yi mata babu wanda ta, tab'a gayawa cikin dangin ta haka tayi ta hakuri dani a kullum dai takan ce Allah ze saka mata ba kuma zata ,tab'a yafe man ba nakan ce da ita gaba ta kaini karta yafe d'in dama 'ae ban tab'a neman tayafe man ba...

Kaiko tsakanina dakai duka zagi hantara cin fuska , haka Hajiya tayi ta hak'uri da, dukkan wani hali nawa har Allah ya saukeni lfy na haifo san talelen d'ana ,namiji ,yasha gatan da bako wani d'a bane ze samu irin shi a lokacin gashi Malam yanaji dashi..

Bayan yarona ya cika wata ,takwas a duniya ,kwatsam sai ga k'anin mahaifin Hajiya ,yazo gidan ,namu ranar wata 'asabar da yamma ,zuwan bazata yayi mata ,a farfajiyar gidan ya sameta, tana tik'an wanki ,kai kuma kana gefen ta kana wasa , ganin halin da take ciki ba k'aramin d'agawa kawunta hankali yayi ba , ita kanta saida ta ,tsorata da ganinshi bata so yazo ya ganta haka ba, don kuwa batayi niyar,kowa yasan halin da take ciki ba ,tayi niyar barina da 'Allah ne idan munje cen yayi mana hisabi,

Kawun Hajiya ,dak'er ya shawo kanta, ta fad'a masa halin da take ciki tare da cin Amanar da mukayi mata, ni da Malam, da ita 'alokacin batasan shima ba'a hayacin sa yake ba, kawunta bece komai ba, ya tashi ya tafi ,tare da sanar da ita zed'au mataki.

Ni kuwa duk maganar da sukeyi inajin su, jin kawun ta yace zed'au mataki yasa na tsorata dashi ,don ko naji mutane,na cewa bashi da mutunci ko ,kad'an kuma 'asiri bata kamashi cikin sauk'i, Hakan yasa na yanke hukuncin guduwa da ,dukiyar gabaki d'aya tun kafun me afkuwa ta 'afku...

Bayan ,nabar najeriya ban tsaya ko ina ba sai ijif anan ,na baza koli na, wata gobara ce da 'akayi wanda yayi sanadin mutuwar mutane da yawa na wannan yankin da muke yasa na tattara na koma, indian anan na yada zango na,na nemi had'aden gidan haya na kama nida ,d'ana..

Ina wada k'a, da dukiya son raina da naga kud'in sun fara k'asa kawai na zuba rabin dukiyar a wani gidan karuwai da'ake ginawa ya zama gidan nawa ne da na wani babban mutun d'an kasar ,bayan angama ginin ya zamana mice babba 'acikin gidan karuwan , gidana kuwa daga wannan ,namijin ya shiga yau sai wani sabo gobe, yaro na kam yana kallo ,tun yana d'an karami yake ganin maza na shigowa gidan mu, har ya fara wayo ,tunda yake ban tab'a sa shi yayi sallah ba, na maidashi arnen dole ,don ,nima tunda na koma cen ,na shiga wata sabuwan rayuwa na manta, menene musulunci (wa'iya zubillah).

Sunan da malam yasa masa na cenza ,masa, suna ya koma 'akram ,.

Bayan mahaifina yaji labarin ,abunda na 'aikata ma su hajiya, ciwan shi ya tashi dalilin hakan yayi sanadin rasuwan shi Amman kafun ya rasu saida ya tsine man," ta k'arashe maganar tana kuka, gatan da, nasan ,nayiwa 'Akram shine besa na manta da koyar dashi yaren shiba, kuma dukiyar da nake tak'ama dashi wannan mutumin ya zalun ceni ya gudu, da, duk wani abu dana tara ya zamana duk wani abunda nasa gaba sai ya lalace" Samir wannan shine labarin da mahaifiyar ka bata son ka sani, don Allah kuyafe man".

Mutumin daya kawo tane yace "ke lokacin ki ya k'are ki tashi mu tafi " tow malam d'an jirani pls " kallon wulk'anci yayi mata ,yace "kinga nayi kama dame jira, ae wlh ke baki cencenci a yafe miki ba ,don ko ,ke acikin butulun ma za'a iya saki a sahun farko, dama tsiyar tala kawa kenan, ka d'aukesu da zuciya d'aya su kuwa su d'aukeka da zuciya biyu, dallah ni tashi muje" yaja hanun ta..

Shi dai Samir be iya cewa komai ba ya mik'e ya fice, koda ya fita be samu Ummi ba don ta, tafi..


*BAYAN SATI BIYU*

Hajar ce zaune a kan wata farar kujerar, k'arfe cikin lambun gidan su mai d'auke da korayen ciyayi da ni'ima mai dad'i ,wajen da ya zamo tama wajen hutawar ta kenan duk lokacin da ta dawo daga 'aiki bayan tayi aiki ta gaji nanne inda ta saba zuwa ta zauna don tasamu nutuwa cikin zuciyar ta, jin muryan Jawahir na dariya harda shewa ne yayi saurin dawo ,da hankalin ta jikin ta, kara, sowar sune yasa ta saurin mik'ewa tana gera gelen jikin ta daya koma gefe daban, sanye take cikin riga da siket na kanti, rigan shara shara me k'aramin hanu ,har ana iya hango rigan ciki.

Fuskar ta 'a d'aure ta dakawa Jawahir tsawa"bana hanaki kawo man kowa nan gurin ba Jawahir koba ,nace maki ,idan anzo nema na kizo, ki fara sanar dani ba?" Sorry Hajjo ba laifin ta bane laifi nane, saida tace zata, zo takira man ita nace a'a barin biyota muzo tare mun yi kuskuri kiyi hakuri" Caotian ya kama, kunnen sa yana bata hakuri..

Murmushi kawai tayi, tace "ba komai ya wuce, wuce kije ki d'auko hulanki, kisa bana hanaki fitowa ba d'an kwali ba?" Mami ne tace nazo na gaya maki Dady ,yazo " tayi saurin barin gurin da niyar zuwa saka hula, kamar yanda Hajar ta umarce,ta shiko Captian guri ya nema ya zauna "Maman Beby sannu da hutawa ya 'aiki ?".

"Lfy qlau Alhamdullih ya office?".

"Office lfy qlau ".

"Masha 'Allah ina 'abokin ka, kwana biyu ,ya dena zuwa hospital karb'an magani, kuma yasan sarai ba'a tsalakewa idan ,anfara Khadee sai fad'a takeyi kow miye dalili?".

"Hmm kinji ba wlh ban san meyake damun gayenan ba, kwata kwata nakasa gane masa cikin kwanakinan tunda 'aka saka ranar auren shi ,shi besan ba'a wasa da cutar daji ba".

Ji tayi gabanta ya fad'i jin cewar ansa ,ranar Dr Samir, duk yanda taso ta b'oye damuwar da tashiga 'a lokacin amman ta kasa , innalilahi wa inna ilaihi raji'un ,shine abunda kawai take iya furtawa cikin zuciyar ta, yanzu Dr Aure zeyi ,ya barta duk irin dakon sonshi da tayi, yanzu ya tashi a banza , anya tayiwa kanta 'adalci da tak'i sanar dashi abundake ranta ,yanzu ga wata, tariga ta, dole ta jenye duk wata ,soyayya da take yi mishi koda hakan ze ,zame mata, matsala kuma dole ta nisan ceshi don kuwa had'uwa dashi wani babban tashin hankali ne a rayuwan ta dole ta gujewa duk wata hanya da ze had'asu dashi zatayi blockin .

"Hajjo tun d'azu fa nake magana kinyi banza dani lfy dai kow" da sauri ta dawo hankalin ta, wani yak'en da yafi kuka ciwo tayi , "lfy qlau Captian wlh na tuna wani abune , kace abokin ,naka 'aure zeyi ashe kuna da babban biki Allah ya sanya 'Alkairi".

B'ata fuska yayi"ae harda ke ,kune ma kan gaba wajen d'aukar amarya kuda kuke ,k'anne". Yak'en da yafi kuka ciwo ta kuma saki 'a karo na biyu "Allah ya kaimu dai tukun darai da lafiya".

"Ameen" tun daga Ameen d'in da yace be

Please Login or Register in order to submit comment