Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya fita kiran Doc... Yana fita kuwa yaci kara da Khadee, hankali a tashe yace.

"Khadee pls muje ki taimake mu Hajjo ta fad'i ".

Wani yawu me d'aci Khadee ta had'iya cikin tashin Hankali tace

"Ta fad'i kuma, meya sameta".

Ita dai tasan tabar ta lfy qlau tow meya sameta kuma, kar tarihi ya ,maimaita kansa fa 'Allah sa ba wani abu Captian yayi mata ba ,shine addu'ar da take tayi.

"Wlh nima ban sani ba Khadee".

Ta ,tsinci muryar shi da fad'in haka


Bata iya k'ara kula Captian ba tayi saurin k'arasawa cikin d'akin.

Abunda ta gani ba k'aramin d'aga mata hankali yayi ba.

Wani abu taji yana mata yawo tun daga d'an yatsan k'afar ta har zuwa tsakiyan kanta. Lokaci d'aya jikin ta ya d'auki ,k'erma .

"Ya 'Allah ,huma 'ajirni fi musibati ".

Shi kad'ai ta iya furtawa ita ,tasan shikenan duk wani farin cikin da k'awar ta ke ciki ya tarwatse , basu tab'a tunanin zasu ,kuma ganin akram ba

"Lfy Khadee".

Cikin fargaba Dr Samir ya tmby.

Fuskar Khadee ,d'auke da hawaye tace , Dr waye ,wannan ?"

Ta masa nunu da 'akram.

Babu wata fargaba Dr Samir yace

"k'anina ne ".

Sai alokacin Khadee ta fashe da kuka me sauti .

"Pls Khadee kibar kukanan ,ki sanar damu ,meke faruwa".

Dr Samir ya kuma tambaya.


Cikin ,kuka ,Khadee tace .

"Sh......shi....ne....wlh shine Akram ,mahaifin Jawahir".

"innalilahi wa inna ilaihi raji'un".

Dr Samir yake ambato ,lokacin dayaji wani ,irin bugun zuciya.

Nufashin sa yake ,kokawa dashi wurin fita saboda tsabar tashin hankali da yake ciki.

Yana jin yanda zuciyar shi ke zafi,kanshi na wani 'irin juyawa.

Wani 'irin ,nishi yake fitar wa me zafi kansa nayi masa wani 'irin ,nauyi , lokaci guda fuskar shi ta sauya ta koma jawuri jiri ne kawai ke d'ibar shi.

Jikin shi sai b'ari yakeyi, Khadee ,da Captian ,na shirin fitar da Hajar basu ankara ba kawai suka jishi a k'asa.

Wani 'irin k'ara Ummi ta saki tana wani 'irin kuka me sauti.

K'aran da tayi ne yasa 'akram farkawa .


*DIJA_WAZIRI*πŸ’‰
[18/12 7:33 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DR HAJARπŸ‘©β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

*ina jin dad'in yanda kuke biye dani cikin wannan novel d'in ba tare da wani k'orafi ko gajiya ba, comments d'inku shi ke sani son naji kullum naturo muku ,kuma shike sa nasan kuna biye dani*

*Rashin comments d'inku shike sa naji k'in son yin typing da wuri* *Allah ya barmun ku*


Chapter 42

Bayan su Khadee sun kai Hajar wani d'akin sun saka mata Drip .

Da sauri Khadee ta dawo takira wasu nurses maza ,suka ,kama Dr Samir suka shigar dashi wani d'aki, har alokacin ,wani 'irin nishi yakeyi.

Wasu manyan likitoci ta kira guda biyu kasan cewar Dr Aiman baya, nan suka had'u da ita su uku suka rufu a kanshi.

Oxgyen suka ,sanya masa tare da wasu na'urori da suka jajona masa ,sanan suka saka masa roban ruwa.

Captian yana d'akin Hajar ,addu'a yake ,kawai Allah yasa ta, tashi.

Ji yake zuciyar shi kamar zata fito daga k'irjin shi tsabar b'acin rai, lokaci guda yaji wani tsanar Akram na ,ratsa ko ina ,najikin shi.

Yaji baze iya sake ganin shiba ,wani kishin shi ya lulub'e shi , ko d'akin da 'aka kwantar da, Dr Samir ma kasa shiga yayi.

Khadee tayi tunanin ta kira su Mami ta sanar dasu Halin da 'ake ciki amman ta fasa ,tana ganin hakan ze iya haifar musu da matsala.

Basmad takira ,ta sanar wa halin da'ake ciki,

Babu yanda Basmad batayi da mijin ta ya barta, taje asibitin ba'amman yace tayi nauyi baya son wani abu ya faru da ita, hakan yasa ta hak'ura ta rabu dashi.


Hajar bata jima da sumaba 'Wani daga cikin yan asibitin har ya kira Dady ,ya sanar masa babu wani b'ata lokaci Dady ,ya sanar da Mima ,suka d'ugun zuma ita da 'Aunty Asma'u suka tafi tare da ,addu'ar Allah yasa ba wani abu, bane ya same ta.

****************
A hankali take bud'e idon ta , d'akin taga yana juya mata ,tana gama bud'esu bata sauke su kan kowa ba sai kan Mami hanun ta, taduba taga d'aure yake da roban ruwa hakan yasa tayi sauri mik'ewa 'a firgice .

Mami ne ta k'arasa inda take da sauri ,ta rik'e ta, tana share mata hawayen dake zuba daga idanun ta.

Don tunda sukazo Khadee tariga da tasanar dasu duk abunda ke faruwa.

Mik'ewa 'Aunty Asma'u tayi ,taje dab da Hajar ta k'ura mata idanuwa tana rik'e da hanun ta jin hanun Aunty Asma'u cikin ,nata yasa ta sakin nufashi.

Muryan ta na wani irin Sama sama ta k'ara damk'e hanun ta cikin na 'Aunty Asma'au tana wani 'irin kuka tace.

"Aunty ban san randa wainan jarabawan zasu...."

Saurin dafe mata baki Mami tayi ,

Juyawa tayi ta kalli Mamin Sosai ,itama ta jawo hanuta ta damtse ,zuciyar ta na k'ara dokawa kamar ze fasa k'irjin ta ya fad'o tace.

"Mami yazanyi na gaji da wanan rayuwan mutuwa nake so".

Wani jiri ke d'ibar ta ,take fad'in.

"Ganin Akram ya sosa min ciwuka da, damana dana samu suka dena min zafi".

Shiru tayi tana jin yanda duniyar ke juyawa mata.

"Ki dena fad'in haka Hajjo komai yazo k'arshe yanzu haka yan sanda mahaifin ki yasa'aje a d'auko , yau ze biya duk cin zarafin dayayi miki, yau zai fara girban abunda ya shuka.

Yau zamu rama ,miki abunda yayi miki shekaru masu yawa, yau zeyi nadamar ,zuwanshi duniya ,yau zesan cewa ko wace mace tana da gata ."

"Mami bazaki gane halin da nake ciki ba ,Mami bakisan yanda nakeji cikin zuciyata bane".

Hajar tayi saurin k'atse Mami.

"Akram k'anin Dr Samir ne Mami ,".

Cikin bacin rai Mami tace.

"Tow ina ruwam mu Hajjo ko Baban shine wlh sai an hukun tashi ,kamar yanda yayi miki, ke ,kinfi kowa sanin waye mahaifin ki.

Shekara nawa yana ,neman shi ,ko kin manta".

Jin yanda 'aka banko ,k'ofar d'akin da k'arfi yasa duk hankalin su ya koma, kan guri.

Ummi suka gani fuskar ta chab'a chab'a da hawaye ,idanun ta sunyi jawuri har sun kun bura.

Takowa tayi ,ta k'araso cikin gurin ba tare da tabari tashin hankalin da take ciki ya bayayyana ba.

Tsintar muryan ta Hajar tayi tana cewa.

"Sanu y'ata yajikin ,naki ?".

D'ago ido Hajar tayi ta sauke su kan Ummi ,murya 'a dashe tace.

"Da sauk'i ya jikin Samir ?".

Ummi bata iya bata 'amsa ba kawai ta ce da ita.

"Allah ya k'ara sauk'i ".

Sannan tadubi Khadee tace.

"Doc....pls kizo ki salame ,mu Samir yace baze iya zama anan ba pls kizo ki cere masa roban ruwan da kika sa masa tare da na'urorin da kuka saka ".

Tana gama fad'ar haka ta fice.

Kallon Hajar Khadee tayi ta gyed'a mata kai alamun taje amman kar tayi salamar .

Khadee na fita bata ,tsaya ko inaba sai d'akin da ,Dr Samir ya ke.

Tana shiga abunda ta gani ba k'aramin d'aga mata hankali yayi ba.

Shi kad'ai ta samu cikin d'akin yana aman jini guda -guda lokaci guda idanuwan shi suka sauya daga fari zuwa jawuri .

Ko ina najikin shi b'ari yakeyi shi kad'ai yasan abunda yakeji.

Ayanzu sunan Allah kawai yake kira da fatan cikawa da kalmar shada .


Tana ganin haka tayi saurin toshe bakin ta ,tafice.

Duk wanda yaganshi acikin halinan idan yana da imani tow dole yaji tausayin shi , tana fita suka had'u da Ummi na shirin shiga hanun ta d'auke da ruwa.

Yanayin yanda taga Khadee yasata saurin tmby.

"Lfy Doc....".

Khadee bata iya ce mata komai ba sai girgiza mata kai da tayi ,ta wuce da sauri.

Office d'in Dr devid tashiga ta sanar dashi halin da ' Dr Samir yake ciki.

Cikin sauri suka had'a kayan aiki suka ,koma d'akin dak'er Captian ya iya b'an b'are Ummi daga jikin gadon da Dr Samir yake, ya fita da ita waje.

Su Khadee sunyi wa Dr Samir gwaje gwaje sosai, sannan suka k'ara saka masa ruwa sunfi awa d'aya 'akan shi.

Ko da suka fito su dukan su babu wanda yake walwala , da sauri Captian ya tsaida Khadee da fad'in .

"Khadee ya jikin ,nasa lfy dai kow?".

Girgiza masa kai Khadee tayi ,kawai tana kallon Ummi tausayin ta, takeji bata iya cewa dashi komai ba sai.

"Kubiyo ni office "

Tana kaiwa nan ta wuce.

Captian babu yanda beyi ba da Ummi akan tabari yaje shi kad'ai ba' amman tak'i yarda .

*********

D'akin, ne yaji yana juya masa duk yanda yaso da ya tashi 'Amman ya kasa don wani 'irin zafi da zugi yakeji.

Hanun damar sa me karaya ,ya d'aga dak'er ya shafa k'afar shi ta dama jin babu komai yasashi ,zaro ido.

Hawaye kawai yake fitarwa masu zafi, be tab'a tsamanin zai shiga halin da yake Ciki a yanzun ba, yanzu ne ya gane ainahin abubuwan da yake shukawa ya fara girbewa,

Yanzu ne ya fara 'ainahin ,nadamar abubuwan daya 'aikata ,a rayuwan shi.

Babu 'abunda ke motsi a jikin shi daga kanshi sai hanun shi tsaya, wa duba d'akin yayi ,yaga babu wanda yake tare dashi.

Wasu zafafan hawayen ,ne suka ,kuma wanke idon shi.

"Allah ya isa Mama kin cucene kin b'ata min rayuwa ta kece silar duk wani hali dana shi ,bazan tab'a yafe miki ba".

Afili yake furtawa yayin da yake wani 'irin ihu yana, neman agaji ,duk yanda yayi, da yatashi ya zauna 'amman ya kasa.


*DIJA_WAZIRI*πŸ’‰
[18/12 7:33 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DR HAJARπŸ‘©β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

Chapter 43

A hankali Ummi ke tafiya ba tare da tasan inda zata ba komai yayi mata zafi, duk yanda taso da hawaye ,ya zubo mata 'amman ta kasa.

Captian daya fito daga office d'in Dr Khadee yana binta ,da sauri don yasan komai ma ze iya faruwa da ita 'a halin da take ciki yanzu .

"Ummi pls kitsaya".

Kiran ta yake amman bata jin komai sai furucin Khadee dake mata yawo cikin kwanyar kanta.

Samir yana d'auke da kedney cancer kuma yana daf da rasa rayuwan shi matsawar ba'a cire kednye d'inshi an cenza masa ba.

Tunani daya fad'o mata shine meyasa ,Samir ze b'oye mata ?.

K'afafuwan ta ,taji sun kasa d'aukar ta .durk'ushewa tayi a dade kofar da ze sadata ,da dakin Dr Samir tasa fuskar ta cikin tafin hanun ta, tana sakin wani 'irin kuka mara sauti.

Matsawa kusa da Ita Captian yayi ,ya dafa kafad'an ta yana rarashin ta, a haka Salma tazo ta same su.

Ummi ko d'aga ido ta kalli Captian batayi ba , ta mik'e tashige d'akin .

Gefen inda yake ,kwance ta nema ta zauna idon shi a rufe hanun shi ta kama jin yanda zuciyar ta ke bugawa da sauri da sauri.

"Na d'an dana zafin mutuwar iyaye ,na kuma d'an d'ani zafin mutuwan miji.

Tunda natashi nayi wayo nayi aure a wahala nake ban san miye dad'i ba , kaine silan farin cikina kaine gatana 'ayanzu kai kad'ai nakeda.

Bazan iya jure ganin ka haka ba, Samir ban tab'a sanin ya akejin zafin mutuwar d'a ba , idan har nabari ka mutu bayan inada ,da 'abunda 'ake buk'ata wanda ,ze iya ceto rayuwan ka ban kyauta ma kaina ba.

Gara ni ,nasha miya 'aduniya koyau na mutu nasan ,nabar memin addu'a.

Zan sadaukar da rayuwata saboda kai, farin cikin ka shine ,nawa babu abinda bazan iya bakaba nawa matsawar hakan be sab'a 'adini ba ,da 'ana iya cire zuciya 'a bayar dana cire nawa na baka.

Bana so kowa yayi maka wannan abun saboda ni kad'ai ya cen -canci nayi maka haka shine kad'ai gatan dazan mata kuma shine kad'ai ze iya gane irin soyayyar da nake maka ".

K'asan mayafin ta, tasa tagoge kwalan dake shirin zubo mata ,kafun ta k'ara da cewa.

Zan baka kodana sabo......"

Kafun ta k'arasa taga Samir ya mik'e dak'er yake tashi ya jinguni da jikin gadon hanun sa nakan bakin ta daya toshe saboda karma ta k'arasa zancen ta.


"Ummi ,taya kikayi tunanin ko ,kin bani zan rayu?.

Idan ,narayu mezanyi kuma 'aduniyar babu ke?

Kokin manta kidney ,d'aya gareki? Ummi soyayyar da zaki min kawai shine kimin addu'a da fatan cikawa shinafi buk'ata 'ayanzu".


Duk ,k'arfin halin da Captian yakeyi na danne hawayen da baya so ,suzubo saida suka zubo masa.

"Samir ya mukayi dakai?".

Captian ya tmby.

Lumshe ido ,Dr Samir yayi ,ya sauke su kan Captian tare da fad'in.

"Junaid na 'amince maka 'alokacine sobada, bana son magana .

Kayi hak'uri junaid nasan kamun komai arayuwa kuma duk irin halacin dakamin bani da 'abunda zan ce maka sai fatan 'Alkairi , wannan shine karo na farko dakayi min kyauta ban k'arb'a ba".

Captian bece dashi komai ba ya fice.

Kallon shi Ummi tayi tare da wani tausayin shi tace.

"Idan baka ,karb'a ba Samir wlh sai dai aci....."

Kafun ta k'arasa yayi saurin tareta da fad'in.

"Bana son rantsuwan ki Ummi na 'amince ".

Ajiyan zuciya ta saki ta kalli Salma tace taje d'akin da 'Akram yake ,kow ya farka.

****
Roban ruwan dake hanun ta, ta cire ta kalli su ,Ummi tace

"Mami ku, koma gida naji sauk'i zamu taho da Khadee idan ta gama".

Kallon ta Mami tayi lokaci guda ta kuma burkicewa kamar ba Hajar d'in taba.

"Kin tabbata ?".

Ummi ta, tambaya.

Murmushi tayi wanda iya kacin sa fatar baki ,ne amman zuciyar ta bak'i ,kirin ,ne komai ya dawo mata sabo kamar ayanzun yake faruwa .

Da ,da hali ma gidan zata bisu don jitayi shi kanshi asibitin ma ta, tsane shi.


"Kune Mami babu komai".

Mami ta barta ne kawai badon ta yarda ba suka ,tafi.


Tashi tayi ,tasa mayafin ta da takalmin ta ,tafice office d'in Khadee ta shiga ,yanayin yanda taga khadee yasa ta k'arasawa ta zauna tana .

"Lfy Khadee?".

Sai lokacin Khadee ta ,d'ago ta kalli Hajar d'in , mamakin k'arfi Hali 'irin na Hajar taji, bata ,tab'a tunani 'idan ta ,tashi zata dawo dai-dai ba.

Bata san sanda ta furta.

"Hajar kece kuwa?".

Murmushi Hajar tayi, tace .

"Nice mana Khadee lfy".

Girgiza kai Khadee tayi tace.

"Gsky na jinjina ma k'arfin halin ki, ban tab'a kawowa zaki iya walwala haka ba".

Girgiza kai ,Hajar tayi ,tace.

"Tow ya zanyi Khadee kashe ,kaina zanyi ko me, shekara nawa najima ina jin ciwan shi.

Bawai yanzun ma bana ji bane wlh ganin Akram ya miyar min da komai sabo kamar ayanzu suka faruwa.

Amman yanda naji rayuwan shi ta kasance a yanzun ma kawai yasa na sare ,ko a yanzu wlh Al lah ya bimun hak'ina Khadee ko haka 'Allah ya barshi ,shi kad'ai darasi ne ".

"Haka ne".

Khadee ta fad'a yayin da take sauke numfashi.

Tablet d'inta ,ta mik'a, ma Hajar tana mata nunu da 'abun dake jiki.

"Miye wanan d'in kuma Khadee?".

Hajar ta ,tambaya , sai da Khadee ta sauke wani ajiyar zuciya sannan tace .

"Hajar Dr Samir yana buk'atar taimakon mu , yana cikin wani hali " .

Nan ta kwashe duk halin da ,Dr Samir yake ciki ta fad'a ma Hajar.

"Kuma gsky mu bazamu iya, yi masa wannan aikin ba ,bamu da yakan su ,shine nadubo wani hospital a new delhi aikin su kenan ".

Murmushi Hajar ta saki ta kalli Khadee tace.

"Meyasa kika ce mu bazamu.iya, yi masa 'aikin ba Khadee?

Wai meyasa ne mu yan najeriya bazamu had'a k'arfi muma ,muga munayin aiki kamar yanda su cen k'asashe waje keyi ba?

Meyasa da zarar munga cuta, tayi tsanani ajikin mutum sai muce zamu turashi k'asar waje?

Me suka fimu ne wai da....."

Kafun ta k'arasa Khadeee ta katse ta da fad'in

"Hajjo kema dai kin san akwai ban ,banci sosai .

Na d'aya sun fimu kayan aiki ,mu shine babban abunda yake tauye mu kuma sun fimu abubuwa da,da 'ama".

"Khadee tayaya 'ake samun kayan aiki? Ina ce dai abun kud'ine ? Tow mu zamusai komai inaso mu kafa tarihin da ba'a tab'a kafawa ba 'a wannan asibitin insha 'Allahu muma zamuyi amfani da ilimin mu kuma zamuyi 'iya k'ok'arin mu na ganin komai ya tafi daidai.

Koda 'ace Dr Samir be rayuba gurin wannan aikin da zamuyi masa, dama 'Allah ya rubuta iya lokacin daya d'iba masa ne ya ciki, bawayon muba kuma ba dabaran mu ba ".

Kalon Hajar kawai Khadee keyi tasan duk wani abu da takeyi a yanzun k'arfin haline kawai.

Kamo hanun Hajar tayi tace

"Kinyi gsky Hajjo insha 'Allah zamuyi 'iya bakin k'okarin mu na ganin anyi masa komai cikin lfy Amman gsky ina tsoro Hajjo".

Murmushi Hajar tayi ta kuma damtse hanun Khadee cikin ,nata ,tace .

"Karki damu insha 'Allah babu wata matsala, tashi muje d'akin ,nashi".

Babu musu Khadee ta mik'e suka fita.

*

kwance ta sameshi 'idanun shi alumshe ga dukkan alamu ba ,bacci yakeyi ba, Ummi kuwa na gefen gadon shi kan carfet ,tana zaune.

Har gefen shi ta, taka ta ,ta nemi kujera ta zauna, tana zama sai ga Captian ma ya shigo d'aki .

"Sanu Dr Samir ya jikin ,naka ".

Muryan ta da'alamun tana sonyin kuka tayi maganar, don tausayin shi taji ya kama ta, barin ma Ummi dataga ta d'un kule guri d'aya tana kuka mara sauti.

Sai a lokacin ya sauk'e jajayen idon shi kan ta, itama shid'in take, kallo ,kallo d'aya, yayi mata ya sauke idon shi daga nata

A raunane yace

"Jiki da sauk'i Hajjo, inajin zuciyata kamar zata fasa k'irjina ta fito Hajjo, inajin gabaki d'aya duniyar ta isheni bana jin dad'in komai Hajjo.

Ina jin takaicin ,cewa 'Akram k'anina shine sanadin wargajewan duk wani farin cikin, ki, kuma ina jin d'acin cewa shine Mahaifin Jawahir.

Inaji dama'ace ba uba d'aya muka fito dashi ba , wlh da 'ace kisa 'abune mekyau dana k'arasa 'akram yabar duniya ,kaico ,wannan wace irin rayuwa ce".

Tari ya farayi jini ,na fita, ta hancin sa da sauri Ummi ta mik'e ta rik'oshi tana goge masa jinin da Hanki.

Hajar kuwa ,wani kuka takeyi me sosa zuciya, gabaki d'aya taji komai ya tsaya mata, fari ya koma, mata bak'i haske ya koma, mata duhu , ko d'an yatsan ta ,ta kasa d'agashi don ta daskare akan kujeran da take zaune sautin kukan tane kawai ke fita .

Khadee ce tanufo inda yake don ta, taimaka masa yayi saurin tsaida ita, sannan ya maida kallon shi ga Hajar.

"Na jima ina,neman wanda ya miki wannan d'an yan aikin don ,na hukun tashi Allah bebani dama ba,

Yau danaji d'an uwana ,ne yayi miki wannan aika 'aikan wlh nayi girgizan da ko sanda mahaifina da matata, suka rasu banyi 'irin shiba.

Mahaifin mu, mutumin kirki ne har bayan ransa mutane suna yaban halayan sa, Mahaifiyar Akram itace silar tab'ar b'arewan tarbiyyan Akram.

Wlh duk ,da 'akram d'an uwanane badon ya nakasa ba, wlh da 'ashirye nake da hukun tashi dede ,da 'abun dayayi miki Hajjo"

Dak'er ya mik'e daga kwanciyar da yayi, ya had'e hanun shi.

"Hajjo don Allah kiyi hak'uri nasan baki son ko ganin mu ayanzu, nasan muma ya shafa mana bamu k'ad'ai ba duk dangin mu ya shafa mana.

Ya tozar tamu ya tona mana'asiri, ya zubar mana da mutunci .

Da wannan ,nake rok'on ki da kiyi hak'uri , k'adaddara ce kowa da irin tasa, ke taki d'adaddaran ce haka".

Joyawa yayi da kallon shi kan Ummi yace.

"Ummi ki yafe min ba lalle nakai gobe, ba ,bakuma lalle nakai anjima ba,

Captian Hajar kuyafe min kuma, haka , kawai yau nake kwad'ayin naga yayi muku wasiyya.

Ka rik'e Hajjo da hanu biyu don Allah kad ka watsa mata k'asa'a ido , nasan baka da mak'iyi ayanzu daya wuce Akram ,don Allah ka dubi girman Allah albar kacin annabi muhamad kad ka wulak'anta Jawahir.

Ka rik'eta 'amana yarinya ce batasan komai ba,"

Ummi na hawaye ,ya dafa kafad'an ta yace.

"Ga mahaifiyata Captian amana bata da kowa saini ,nima bani da kowa sai 'ita don Allah kad ka bari ta wula k'anta 'aduniya kad ,kabari tayi kukan rashina.

Hajar ga 'amanar Ummi na, nasan zaki ,kula min da'ita ,

Shine Kad'ai Alfarman da nake nema 'agare ku bayan raina, ku, kulamin da mahaifiyata, da kuma Jawahir ,".

Gabaki d'aya, yan d'akin ,kuka sukeyi ,kamar ba gobe, Captian duk yanda yaso da k'arfin halin shi, saida yayi hawaye.

Ummi kasa jurewa tayi tabar d'akin tana wani 'irin kuka , babu wanda ya iya tsaida ta harta fice.

"Captian pls zoka d'agani ,ina son akaini d'akin akram zan....".

Kafun ya gama rufe bakin shi Salma ta shigo 'a guje.

"Lfy Salma?"

Captian ya tmby

A firgice Salma tace yan sanda, ne sukazo tare da wata mata, wai kuma zasu tafi da'akram, ".

Sai a lokacin Hajar ta d'ago ta kalli Salma, bata ce dasu komai ba ta mik'e tayi d'akin da Akram ,ke ciki, zuciyar ta na wani 'irin bugawa da sauri da sauri .

Dad tagani tsaya tare da wasu yan sanda, da kuma wata datijuwan mata bak'a.

Muryan da bazata, tab'a mancewa dashi 'arayuwan ta bane taji yana magana.

"Ku tafi dani, wlh bani da baki magana na cencenci fiye da hakan ma, yanzu na fara girban abunda na shu-shuka.

Wlh da zakuyi min gata'ayanzu shine kawai ,kukashe ni bani da sauran amfani aduniya , kaico na, kaico da irin wannan rayuwan tawa.

Nagode Allah daban haihu ba, don wlh bazanso ayiwa,y'ata 'abubuwan da nayi ba, kuma bazan so d'ana ya d'auki halaya irin tawa b.....".

Kafun ya k'arasa ida zancen sa Dad yayi saurin katseshi da cewa rai 'a b'ace.

"Dama zakayi tunanin baka da, y'a mana saboda lokacin daka b'ata min y'ata bakayi tunanin komai ba.

Tow kasani Hajjo katafi ka barta da ciki, kuma ta haife maka, don haka baka fara girban 'abunda ka shuka ba sai nan gaba.

Zan ,nuna maka cewa ka tab'o ni kuma zakasan yar wa ka tab'a"

Rai a b'ace Dady yace wa yan sanda ku ,kamashi ku tafi dashi, daga nan har birnin sin sai munyi shar'a dashi".

D'aya daga cikin yan sandar ne yace .

"Alhaji bazamu iya tafiya dashi yanzu ba har sai ya warke zade mu cigaba da tsare shi".

Cikin zafin ,nama Dad yace .

"Bade a hospital d'ina ba ,kufita min dashi bana son ganin shi".

Saurin tsaida shi Hajar tayi da idanun ta da suka, koma jawur.

"Dady kayi hak'uri ka barshi ,ko ayanzu ya koyi darasi, kafa kaleshi amfanin me ze sakeyi nan gaba? Duk abubuwan da yayi abaya wlh be isa ya sake yin suba ".

D'ogo kai Akram yayi, ya sauke su kan hajjo, be tab'a tsamanin ze sake had'uwa da ita ba..


*BY DIJA_WAZIRI*πŸ’‰
[18/12 7:33 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DR HAJARπŸ‘©β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰




*Duk naji k'orafe k'orafen ku, dakuma ra'ayoyin ku ,kuma naji dad'i sosai da kulawan da kuke nunawa ,wannan litattafi.*

*Amman 'abunda nikeso ku gane ,shine karku damu da ,komai dayake faru cikin littafin ,nayi muku alk'awarin akwai happy ending ,abunda nafiso ku fahimta, shine darusan dake ciki*

*Ina fatan zaku bini sanu a hankali, har Allah ya bani 'ikon kawo k'arshen sa*

Chapter 44

Wannan karon kwala yaji sun kwaranyo daga cikin idanun sa , yanaji wani abu tun daga tsakiyar kanshi har cikin ,naman jikin sa.

Babu abinda ya razanashi, sai furucin da yaji Dad yayi na cewa yana da y'a, har cikin ransa beso hakan ba' amman ta wani fanin yaji dad'i .

Zuciyar shi ce ke wani 'irin bugawa da sauri da sauri, farkon had'uwan su kawai ya tuna, da kuma k'arshen rabuwan su.

Wata ,nadama ce ta daban ta ziyar ceshi, da za'a iya maida hanun agogo baya da yamayar ,ya gyara duk wani kuskure daya 'aikata 'a rayuwan shi,

Kasa kod'a motsa bakin shi yayi, sai kallon ta yake tana magana da, Dad

"Dad yaki hak'uri ka barshi acigaba da jinyar sa'anan din rama 'Alkairi ga azalumi 'ibada ce, badon shi zamuyi ba, kuma badon halinshi zamuyi ba, zamuyi ne don Allah da kuma girman Annabin mu, ae Allah yana sane da, duk irin cin zalin da yayi mun".

Dad be iya cewa da Hajar komai ba don ranshi a matuk'ar b'ace yake, fita kawai yayi daga d'akin shida yan sandar, da suka zo.

Su Dr Samir duk suna d'akin sunyi cirko cirko Salma ce ta, turo shi a keken marasa lafiya, Ummi ,ma tashigo d'akin.

Juyawa Hajar tayi zata fice tana hawaye, kawai taji muryan Akram yana kiran ta.

"Hajjo pls ki bani minti d'a ya don Allah".

Tsayawa tayi chak ba tare da ta juyaba kuma ba tare da tace komai ba, zuciyar ta na suya, don ko muryan shi bata son ji.

"Hajjo nayi kuskure arayuwata, sosai nayi wasa da, damata 'alokacin daya kamata 'ace na more ta.

Nayi shuke shuke da, dama wanda ban samu damar girbe suba sai yanzu, Kinga yanda 'Allah ya dawo dani kow , nasan ina da lefi sosai Amman laifin Mahaifiyata yafi yawa, itace sulan shigana cikin matsala, itace silar komai nawa.

Nuna ta yayi da yatsa yace kin cuceni Mama "

Mahaifiyar Akram bata iya cewa komai ba sai kuka da take tayi tun shigowan su da yan sanda.

"Na tashi a wulak'ance ,na tashi cikin k'azan taciyan rayuwa, na tashi bani da uba don kuwa Mahaifiyata, ta samoni a yawon ban...."


Kafun ya ida zancen sa Dr Samir ya d'aga masa hanu da jajayen idanun sa , zuciyar shi nayi masa wani irin rad'ad'i da k'una , kanshi na wani 'irin juyawa .

"Kana da Uba kuma kai d'an halak ne, ni dakai ubanmu d'aya ,

Mahaifiyar ka ita ce

Please Login or Register in order to submit comment