Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

Copied By
YAYA HAYAT
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
AND
Cool novel, makeup and kitchen2⃣)

WHATSAPP NO:
+2347039625239

: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
بسم الله الر حمن الرحيم

8:59 pm 01/06/2017

*A TAUSAYAWA JUNA* pg 1⃣to5⃣Na
*Aysha Ali Garkuwa*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*Ramadan Kareeeeeeeem*

*Barkanmu da shan ruwa ga dukkan 'yan uwa musulmai*

``` Barka da shan ruwa Namecy tawa Aysha Aliyu tsamiya Allah ya karbi iba dunmu Allahu rabbi yasa muna cikin bayinsa entattu zuwa cikin rahamarsa```

Zaune suke a parlon nasu mai dan girma da d'an kayan k'awa dai-dai gorgodo Bashir dake zaune kan 2 str ruggume da yarsu k'aramar Salima mai kyau cikin kula ya kuma kalli Rukayyat wace ke konce kan 3 str sai cika da batsewa take ta had'e fuskar nan kamar zatayi ruwan jini,
Babban d'ansu Salim ne ya d'an matsota cikin muryar bacci yace.
"Ummee bacci nakeji zan konta".
Kai ta d'ago cikin salon bak'ar mgn wa Uban yayan nata tace.
" wlh Salim tausayi kuke bani kai da salima sabida kun rasa ganta da duk sauran yaran jama'a ke samu a wannan wata sabida ko wanne uba mai k'aunar y'ayansa da son faran ta musu da fiddasu kunya tuni ya gama samawa iyalen sa kayan sallah Amman ku naku uban bai damu da kuba bare akai ga kaina".

Shi kam Bashir murmushin yayi cikin mmkin hali irin na rukayyat ace tsakanin ma'aurata a rasa tausawaya juna ba uzuri ita komai sai dai ayishi cikin gaggawa,
Kai ya kuma jinjinawa tare da mik'ewa ruggume da Salima ya kamo hannun Salim sannan ya kalleta cikin kula dan shi har kullum uzuri yake mata tunda ita macece mai rauni sai anbita ahankali,
Murmushi yayi tare da cewa
"Konta ki huta Baby bari nai musu wonka na kontar dasu kafin nan kin huta dan nasan kin gaji da aikin Abin bud'a baki".

Bata kula shi ba sai yatsuna fuska tai tare d'an yin kasa-k'asa da murya tace .
" jishi sai kace wani kayan azo a gani yake kawo mana na bud'a bakin"
Carab sai cikin kunneshi Amman duk da haka sai ya wuce ya shirya yaran sannan ya kontar dasu tare da musu Addu'a ya rufe musu jiki,
Sannan ya dawo parlon
Cikin k'arfin hali yace.
Baby tashi muje mu konta kar mu makara muresa tashi mu raya darenga da Ambaton Allah".
Shiru taimai sai tura baki da tayi shiko cikin danne abin yaci gaba da cewa.
"Muje mu konta dan gudun kar bacci yafi karfinmu ya sa muresa koda dare dayane a cikin wannan wata gwara mu zage damtse tunda bamu da tabbacin wanne darene na lailatul k'adir toh mafitarmu kawai mu dage mu raya dukkanin dararen da amba ton Allah ta nanne in munyi sa'a muyi muwafak'a da wannan daren na lailatul k'adir".

Cikin d'an Jan tsaki tace
" ban jin bacci".

Kauda kai yayi tare da cewa "toh muje dai"
Mik'ewa tayi ta zauna cikin kufula tace.
"Ai dama tanan kafi kauri muje dai ko? Wato kai baka da wata matsala ma ko kai dai aje bedroom ko?
Shin anya kuwa
Abban Salim kana tuna baka sayawa yaranka kayan sallah ba shin kana sane kwana kin watan nan nata tafiya yau axumi nawa muka kai amman ko k'elle banga ka shigo da shiba ko kai so kake yaran nan suyi sallah da tsoffin suturun su wlh ni har tsoro kake bani
ai kana sane da ko wanne uba ya gamawa yaran shi komai".

Gefe ya koma ya zauna cikin sanyi ya zura mata ido tare da son gano gskyar zuciyar ta a d'aya gefen kuma mmkin ta yake da kuma son ganar da ita,
cikin sanyi yace.
" Rukayyat kiyi hakuri ki nitsu ki gane halin da nake ciki ke kanki kinfi kowa sanin nauyin dake kaina tunda kina sane nike kula da gidan mu tunda mahaifina bay da karfi sannan inkula dake da yaran mu kuma kina ganin irin halin tsadar rayuwar da muke fama dashi kuma kinsan samuna bai kai yawan nauyin dake kaina ba Allah ne ke rufamana asiri Baby duk da kasawana da kike gani baki rasa ciba baki rasa shaba yaran mu ban barsu ba ilimiba na sasu a makaran mai kyau ban barsu da rashin sutura ba kuma tunda muke kema baki rasa sutura ba bare yaran mu ko ba sallah ba ina musu sutura bare sallah asheko yaci kimin uzuri ki jira har sai kinga anyi sallah ban muku abinda kuke buk'ata ba".

Tunda ya fara mgn ta kafeshi da ido har saida taji yayi shiru sannan tace.
"Kawai in bazakayi ba mu sani ai kana sane tsakanin da Allah yanzu duk cikin abokanka akwai Wanda bai gamawa iyalansa komai ba?
ai kana gani d'azu Maryam matar ya Umar na tazo nan kuma kaga dai abin da tashigo dashi kasuwa taje tawa yaran ta seyeyya komai tsap sannan ta biya gun telanta ta karb'o dinkunan ta kuma ka fini sanin Ya Umar dinne ya bata kud'in tunda ai abokin kane komai kasani,
Haka kuma Aysha ma matar Yusuf abokin naka dai har wayau itama an mata komai har tayi d'inkunan ta da salima d'azu ta turo mata,
abin kunya babanta bai mata ba,
Su suna neman yaran Allah bai basuba kai ka samu ka kasa rik'ewa".

Sosai yaji zafin kala manta toh Amman ya zaiyi da hali irin na Rukayyat sai Addu'a cikin jin zafin ya mik'e ya nufi bedroom ensu al'wala yayi sannan ya d'au k'ur ani ya rink'a karatu cikin kushi'i da k'ank'an da kai.
Ita ma d'akin ta shigo tai wonka sannan ta koma kan gado tai baccin ta tana mai ganin kasawar mijin nata,

Shiko a hankali ya fara jin sanyi bakin cikin ya rink'a gushewa a ransa a haka a wurin bacci ya d'an saceshi.

1:30 am dai-dai ya farka cikin sanyi yaje gaban ta a hankali ya tasheta tare da cewa "Baby jekiyi al'wala kizo muyi nafila"

Cikin baccin ta mik'e taje tai alwalan dan inda sabo ta saba dolene muddin Bashir ya tashi to zai tasheta.
A haka kuma sukai ta nafilfilin su sannan daga bisani sukayi ta karatun k'ur ani mai girma har zuwa lkcin Sahur sannan sukayi sahur bayan sun gama shiko yayi al'wala ya tafi masallaci dan samun jam'i asubahi,.
Itako tai tata sallan a gida.
Rayuwar gidan Bashir kenan....

*Gidan Yusuf da Aysha*

K'arfe 5 dai-dai Aysha ta kammala Ayyu kanta tsab ta share ko ina ta goge komai ta shirya musu abin bud'a bakin su tayi wonka ta shirya cikin doguqar riga mai d'an girma ta d'an yafa gyale.
tana zaune a parlon ta,
Cikin sanyi da gajiya Yusuf yayi slm hannushi rik'e da wota bak'ar leda,
Cikin hamzari da kulawa Aysha ta taryeshi hannu tasa ta karbi kayan hannushi sannan ta wuce gaba tare da cemai.
"Barka da yammah Hamma".
Ajiyar zuciya ya sauk'e tare da zama can gefen ta kan 1 str ido ya lumshe tare da cewa.
" Alhamdulillah Aysha sai dai gsky yau kam akwai rana ga k'ishi gashi na biya cikin kasuwa na d'an saya miki takalmi da mayafi".

Sai kuma ya mik'a mata hannu alamar ta mik'o mai ledar,
Cikin girmama wa ta mek'a mai tare da rabawa gefen shi ta zauna tana kallon 'yan kayyayakin da ya sayo mata ta kalmin ya dauko ya zauna a kasa kan carpet ya zura mata takalmin cikin kula yace.
"Wlh yayi miki kyau kinga yadda k'afarki ta gyara takalmin insha Allah inna samu kudi zan saya miki jakarsa "

Itama zamewan tayi ta zaune d'an nesa dashi cikin sanyi da tausayawa tace.
"Hamma meyasa kake son kashe kud'i a banza da wofi ni ba yarin yaba ka rink'a kashe min kudi yanzu ba da safe kake cewa ba kudi a hannun kaba kuma shine daga samo su ka saya min wannan tarka cen meyasa bazamuyi tattali ba?".

Kai ya jinjina cikin jin dad'i yace.
" Aysha Allah ya miki albarka Ngd da tausaya sarki gareni amman kibar korafi kar ina kashe miki kud'i dan kuwa Aysha duk wani namijin kirki toh burinsa ya faran tawa matar sa da yaran sa muddin kikaga ba'ayiba toh ba'asamu damar yi bane inko haka ta faru sai *A tausayawa juna*
d'an ba Wanda zaiso yaga iyalanshi a k'askance sai dai in abin yafi karfi kinga ko tunda na samu dole namiki tunda dama nauyi nane ai ko matata?".

Murmushi tayi cikin farin ciki tace.
"Allah ya saka da alkhari ubangiji yaa jibanci lamuran ka Allahu rabbi ya karama arzik'i da wadata Allah ya had'aka da halal d'inka ubangiji ya rabaka da haram Ngd Ngd Ngd Hamma na"

Gdy take mai cikin farin ciki da ganin girman kyautar da ya mata,
Cikin jin dad'in halin matar tasa yace.
"Nifa kin San ban son wannan godiyar kinsan irin godiyar da nake so yanzu kuma muna cikin watan Ramadan ne kuma da ranane dan haka Adana godiyar sai anjima in munsha ruwa".

Murmushi kawai tayi tare da tattara kayan sannan tayi cikin d'aki bayan ansha ruwa ne ya tafi masallaci itako tai tata sallan tare da kara kimtsa gida.
Suna rayuwar su cikin rufin asiri da tausayawa juna duk k'ank'antar abinda ya mata ita ganin shi take da girma da daraya....


*Gidan ya Umar,da Maryam da y'an yaran su Umar yayan Rukayyat ce kuwa 1 uba 1*

Tun 5 dai-dai Maryam ta gama aikinta gudu-gudu sauri-sauri da tsoron kar ya Umar ya dawo ya samu bata gama ba dan shi Umar mutunne mai gaggawa da rashin uzuri gashi,
Shi har kullum gani yake aikin cikin gida ba wuya sai dai in mace nada saib'ine,
sam Maryam bata rasa komaiba najin dad'in rayuwa ita da yaran ta sai tausaya warsa da yimusu uzuri suka rasa.

6:00 pm ya shigo cikin gidan cikin sauri Maryam ta taryeshi tare da cewa.
" Sannu da hanya Ya Umar".
Aha yace ba tare da ya tsaya ba sai Leda da ya mik'a mata cikin d'an d'aga murya yace.
"Kajine ki min gashi nan mai d'an romo-romon nan kiyi sauri fa kinga ankusa kiran sallah".

Ido ta zuba mai cikin binshi a baya a hankali tace.
" Ya Umar saura minti 25 nefa a kira sallah kuma yau jiri na wuni dashi da ker nai aikin ma wlh banda lfy".
Cikin fushi ya juyo ya kalleta tare da cewa.
"Wlh ke dai kin fiye saibin tsiya mene a cikin aikin gidan nan naga dai akwai mai wonke-wonke da shara da wonki,
girki nefa kad'ai aikin ki amman duk sai ki wani sakewa dan son jiki".
Sai kuma ya juya ya kalli 'yarsu karama da yanzu ta tashi daga bacci shiyasa kanta dake d'an tubke akan gobe za' kaita kitse.
Cikin tab'e fuska yace.
" kalli kan Ikram fa kin barta kai a tsefe ba kitso".
.sai kuma ya d'an rink'a lek'a cikin gidan da parlon dan neman ta ina zai cita gyara,
Ganin babu kuma baki ya saba mita sai cewa yayi .
"Fito min da kayan da zansa ina fito wonka sannan kuma kije ki gasamin naman nan ki kuma kitsewa ikram kantan nan".

Inda sabo Maryam Ta saba da wannan rashin tausayawar daga gun mijin nata bawai kuma son tane baiyi ba a a kawai dai baida bawa mace uzurine shi gani yake me aikin mace ai duk aikin kamar wasane.

Kayan ta fara cire mai San nan ta sawa ikram hula a kanta sai kuma ta wuce kitchen ta fara aikin ana kiranbsallah tazo ta had'a mai komi sannan ita kam ta d'an cin dabino sai kuma tayi sallah sannan ta koma kitchen din,
shiko yana dawowa masallaci ya shiga parlon ya samu su ikram da yayun ta suna wasa cikin daga murya yace.
" kai Isma,il ina Mamin Ku?".
da sauri yace .
"Daddy Mami tana kitchen ko ruwa bata shaba".

Murmushi ya d'anyi sannan yace.
" Isma,iI
Mamin Ku saibin ta yayi yawane nima yanzu yunwa nakeji amman kaga na kasa samun kulawar ta".

Da sauri yaro yace.
"Toh Daddy bari na sama Abin cin ko?".

Kai ya gyada tare da cewa "toh ya zanyi ai ya zamemin dole zo kaida Sultan muci"

Haka suka zauna sunaci yana ta mita,
Ita kuma sauri-sauri ta gama sannan tazo ta kawo musu kafin nan isha tayi sai kuma tayi sallah sannan ta kimtsa parlon tazo tawa yara wonka sukaje suka konta shima taje ta kimtsa shi sannan ta juya zata fita taje taci abinci tai wonka ta samu ta konta ta huta sai kuma tajishi yana.
"Maryama zo mana ina kuma zakije".

Cikin rawan murya tace.
" ruwa zanje insha kuma zanyi wonka gashi bacci nakeji".

Cikin rashin damuwa yace .
"Toh kiyi da sauri ina jiran ki".
Kai kawai ta gyada sannan ta fita tana mai jin zafin rashin tausayawar da mijin ta ke nuna mata .
*Gidan ya Umar kenan*

*Koya gidan Bashir kuma ke ciki*

Rukayyat ce biye dashi a baya cikin ya mutsa fuska da tura baki tace.....


*Masu karatu wanna lbrin d'an gun tune kuma nayishi kan A tausayawa juna kuma ayiwa juna uzuri mussaman a wannan marran da muke ciki mata mu tausayawa mazanmu kan samunsu da rashin su mu kasance masu godiya da abinda zasu mana duk k'ank'antar Sa mu gajarca buri da son abin duniya. lbrin 3 pages ne koma 2*

By Garkuwar Fulani 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*A TAUSAYAWA JUNA* pg 6⃣to1⃣0⃣ Na *Aysha Ali Garkuwa*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

Short story

*Ramadan kareeeeeeeem*

"Abban Salim inama mgn kayi shiru,
nacema zanje in duba Innah da jiki dan jiya Ya Umar yace min a asibiti suka wuni,
Kuma inaso mu had'u da ya Umar dan nasan zai ban kud'i zan samu nawa yara na kayan sallah,
tunda kai ba iyawa zakayi ba".

Ta kareshi mgnar cikin yanayin kai dai kaji kunya,
shi kam Bashir shiru yayi tare da tsura mata ido hak'ik'a Rukayyat ta fara k'ureshi dan tana cusa mai bak'ak'en kalamai sam duk mgnar da zata fito bakinta ba alamun tausayawa juna,
Itako ganin yayi shirun ne taci gaba da cewa,
" Na fahim ci kai baka damu da lfyar mahaifi yata ba toh ni kam dole na damu".

Cikin danne fushin sa yace.
"Rukayyat ai mahaifiyar ki mahaifiya tace,
kuma dole na damu da ciwon ta ina sone muje tare,
toh yanzu kuma ina da d'an uzuri ne kiyi hakuri gobe da safe zamuje".

Fuska ta had'e har ta bud'e baki zatayi mgn sai kuma tai shiru jin muryar mak'ocin su tare da shigo warsa cikin mutunta juna suka gaisa da Bashir sai kuma yayi shiru ganin haka Bashir yace.
" Baba Audu kayi mgn mana ba komai".
Kai ya kuma sunkuyarwa cikin sanyi yace.
"Wlh Bashiru abubuwa ne sunk'i na rasa yadda zanyi gashi bamu da ko k'wayar shinkafa a gida bare muje ga sauran buk'atu wlh ko ruwan sha babu a gidan tun safe nafita gashin ban samu komai ba gashi har yamma tayi".

Cikin tausayawa Bashir ya zura hannushi cikin aljihu ya d'ebo kud'i yan dubu-dubu guda 10 ya mik'a mai tare da cewa.
" ga wannan Baba a kai musu da wuri a samu na shan ruwa ".
Cikin farin ciki Baba Audu yasa hannu ya karb'a murya na rawa ya rink'a godiya har hawaye nabin fuskarsa,
Cikin tausayawa Bashir yace.
" Baba kabar godiyar nan kamin addu'a aini d'ane a gareka".
aiko ya rink'a gyad'a kai yana zuba mai addu'oi,
tare da cewa Rukayyat.
"'yata ki tayani gdy"

sannan ya juya ya fice.

Ita kam Rukayyat ta cika pim saura ta tarwatse.
Shiko Bashir cikin sanyi yace.
"Ki bari sai goben ko?".
ido ta tsura mai da alamar tuhuma cikin takaici tace.
" kaima baka wadatu ba shine harda yin kyauta dubu har 10 alhalin ko takalmi baka sayawa yaran kaba manya iyayen gonin ta ai mai bunu a jiki bai zuwa kolalan gobara ka rink'a tauye mana hak'k'inmu ka nawa wasu can kyautar kud'inmu".

Sosai ranshi ya baci cikin fad'a yace.
"Yar dar Allah nake nema kuma hak'k'in mak'obtaka nake sauk'ewa sannan wannan sadaka ce kuma ki sani Rukayyat bani da bbabn da zai hanani sadaka da taima ko sannan ki sani shi sadaka bawai sai mai tarin dukiya ba shima talaka zaiyi irin tasa sadakar ko dako da tsagin dabino ne ki sani wannan watan duk wani abu na alkhairi da mutun zaiyi rubanya mai ladan za'ayi,
sannan batun hak'k'in ku Rukayyat kiji tsoron Allah ni Bashir dame na regeku?
yanzu ke ko tausayi bai bakiba kici mai kyau yayanki suci mai kyau shi ko garin masara ya gagareshi shin wai me kika dauki wannan rayuwa ne shike nan ace tsakanin al'ummah ba tausayawa juna kowa kansa ya sani da yaransa".

Sosai yake mata fad'an da yafi tafiya kan gsky da abinda ke faruwa a wannan rayuwa,
Itako mita ta rink'ayi
haka dai ya fita koda ya dawo da dare ko kalon arzik'i bai isheta ba,
yanaji yana gani yana buk'atar kulawar ta amman ya rasa haka suka kwana kowa da abinda ke damunshi shi Bashir gani yake Rukayyat ta gaji da zama da shine shiyasa take ganin kasawarsa duk dako abin da yake mata na rufin asiri
Ko son zuciya ne da rud'un abin duniya ne ke cin zuciya ta
yasa a ranshi dai zaike nema mata shiriyar Allah".

Kashe garin da safe Maryam ta shirya zataje gaida Uwar mijinta itama Rukayyat ta shirya sukaje Yusuf ma ya kai Aysha ta gaida Innah tunda mahaifiyar abokin shine.

Bashir da Rukayyat su suka fara isa cikin girmamawa ya gaida Innah tare da aje mata kud'i 5000 sannan da ledan kayan masarufi cike tab Innah mace mai mutunci ta rink'a gdy tana ya bar kud'in ta gode,
Suna cikin haka Umar ya shigo cikin sakin fuska da k'aunar abokin nashi suka gaisa itama Rukayyat cikin fara'a ta gaida shi tare da cewa.
"Ya Umar Maryam fa"
Tsaki ya d'an ja sannan yace.
"Maryama sarkin saibi sam na rasa itako wacce iriyace tun safe ta kasa gama aikin niko nagaji da jiranta na fito kawai na bar ta intaga dama tazo ko zuwa k'arfe 9 ne".

Cikin saurin shi yaja Bashir suka fita a bakin gate suka had'u da Yusuf da matar Sa suma suka shiga suka gaisa sannan suka tafi suka bar matan nasu suna d'an tattaunawa Maryam da yanzu ta iso renta a bace bayan ta gaida Innah sannan ta shige dakin Rukayyat na yayin budurci suka zauna cikin kula Aysha tace "Maryam ya dai kamar ranki a abace fatan dai lfy ko ?".
Hannu tasa ta share k'ollah dake bin fuskar ta cikin sanyi da rawar murya tace .
" Aysha ya Umar zai fasa min zuciya na rasa farin ciki da kulawa bare a kai ga tausayawa juna sam ya Umar bai san yamin uzuri ba shi ya dauka mace tamkar injine ba gajiya shi baisan menene uzuri tsakanin ma'aurata ba".

Cikin mmk da tab'e baki Rukayyat tace.
"Kai Maryam yanzu fisabilillahi me kika nema kika rasa gun ya Umar ganki fa kamar sarauniya rayuwar ki cikin an nashuwa dake da yaranki a wadace ".

Ido ta zura mata murya na rawa tace.
" Rukayyat me nasa mu a gidan ya Umar inaba haihuwa ba ita haihuwar ma da rebo ke giftawa wane kula ko gata na samu wanda mace ke buk'ata gun mijin ta,
Rukayyat na rasa tausayawar ya Umar wace nake buk'ata shi bai iya lallashin mace ba na rasa kularsa ,
Rukayyat duk kud'in namiji da gatan da zai samarwa mace na banzane matuk'an bai sama mata kulansa da tausayawar saba".

Cikin sanyi murya da d'an kuka tabawa Rukayyat lbrin irin zaman da take da ya Umar d'in,
Sosai jikin Rukayyat yayi sanyi watoh abinda take ganin shirme ne Bashir ke mata ase shine babban farin cikin ma'aurata gashi rashin sa yasa Maryam zubda k'ollah duk da daular da take ciki".

Sai kuma ta kauda tunanin tare da cewa.
"Ke taki matsalar me sauk'i ce tunda baku rasa komai ba nifa Bashir bama sanin akonsa da babunshi sai dai kaga yanawa mak'ota da mabarata".
Nan ta basu lbrin irin rigimar da suke a yan kwana kinnan.

Ajiyar zuciya Maryam tayi tare da cewa
" wlh ke Rukayyat dad'ine ya miki yawa Ni in nice na samu irin kulawar da Bashir ke baki ai bani da wani bak'in ciki, Rukayyat kiji tsoron Allah fa yanzu ke da me Bashir ya regeku keda yaranki".

Shiru Aysha kam tayi tana mai zuba musu ido cikin sanyi dason tunasar dasu ta gyara zama tare da cewa...



By Garkuwar Fulani
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*A TAUSAYAWA JUNA* pg 1⃣1⃣to1⃣5⃣ Na
*Aysha Ali Garkuwa*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*Ramadan kareeeeeeeeem*

"Da forko dai zance daku abin da kukayi bakuwa mazan ku a dalci ba dan wannan sirri ne wanda ke tsakanin ku sirrin mazan Ku ne sirrin gidajen kune bai kamata ku fito kuna tad'ashi a anguwa ba,
Tabbas ba abin da zance dake Maryam sai dai nace dake Allah ya baki ladan hakurin da kikeyi kuma Allah ya fahim tar da mijin ki rabbi ya samai tausayin ki cikin ransa,
dan hak'ik'a rashin tausayawa juna da wasu maza ke gwada matan su yana jawo rashin ji tuwa".

Shiru Maryam kam tayi cikin jin sanyi na ratsata a ranta duk zafin da take k'unshe dashi ya fara tafiya a ranta kuwa godewa Allah take da ya had'ata da Aysha k'awar kirki k'awar mutunci da amana k'awarda dake bid'ar a gudu tare a tsira tare dan da wata ce sai dai ta ingi zata,
Cikin sanyi murya tace.
" Aysha ngd da tuna sarwa insha Allah zan ke tsare sirrin gidan aurena zanke Addu'a Allah ya fahimtar da ya Umar ".

Murmushi tayi cikin juyawa gun Rukayyat ta kafeta da ido cikin yanayin kinban mmk kin kuwa ji kunya har gaban Allah,
ta bud'e baki zatayi mgn kenan,
Rukayyat ta katseta cikin yin k'asa da murya gudun kar Innarta ta jisu a hankali tace.
" Ke Aysha na fahim ci bazaki gane abin da nakeji ba dan ke komai a wadace kike samun shi shiyasa kike gani kamar wani mugun abu nakeyi,
ita ma Maryam dan matsalar ta k'arama ce shiyasa bai damun ta sosai".

Cikin d'an d'aga murya Aysha

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2

Please Login or Register in order to submit comment