Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ake Amatullah bata Sani ba domin baccin gajiya ne yayi awun gaba da ita.





Babu wani bata lokaci aka wuce da Abba Asibitin kaduna kudi sosai aka sake domin neman lafiyar sa





AFTER ONE MONTH



Amatullah ta sake da Ammy ta dauketa kamar Innar ta sauda yawa Ammy tasha gwada ta na ajiye kudi a daki sedai koda Wasa Amatullah bata dauka domin irin tarbiyyar d'ata samu.



Ta gware sosai wajan iya girki seda Ammy tayi training din'ta kafin ta fara sau Mata wasu abubuwan har wannan lokacin basu taba haduwa da IRFAN ba.





Aysha tana zaune a office din'ta tunanin takeyi irin canjin da takeji a jikinta gashi Dix month bataga period din'ta gaban'ta ne taji yayi rassssssss kardai ace ciki ne da ita inaaaaa in possible ta furta cikin karajiiii.



Handbag din'ta ta dauka babu shiri tayi gida Doctor din'ta ta Kira tace I need to see you orgent ok Ma Kawai yace.




Cikin abin. Da baifi 10 minute ba Dr Majeed ya shigo bayanin komai tayi masa gwajin farko ya nuna ciki 27 Dys zaro ido Aysha tayi murya a shake tace please Dr a zubar dashi cike da mamaki Dr Majeed yace Madam azubar Kuma gyada Kai tayi alamun haka.







Kwantar da murya Dr Majeed yayi yace Madam You Know Sins abin da IRFAN yake nema kenan Amma ace Allah ya Baku maimakon kiyi farin ciki Kuma se kice a zubar please abeg don't do this.




Masifa Aysha ta fara balbala masa tana dago ido sukayi 4 Eyes da IRFAN Yana tsaya a kanta ya zuba Mata oily eyes Dinshi da wuya ka Gane halin da yake ciki.





Wani irin bugawa kirjin'ta ya farayi tsabar tsoro domin batayi tunanin ganin'shi a wannan lokacin ba ganin haka yasa Dr Majeed fita daga parlo yaji Dadi ganin Irfan saboda shi kanshi baya son Aysha ta zubar da cikin.






Ya jima Yana kallon'ta batare da yace Mata uffan ba ya fice daga parlon site din Ammy yayi fitowar ta daga zata shiga garden kenan babu Wanda ya lura da Dan uwan shi wani irin clash sukayi tayi tagal tagal zata fadi babu shiri ya rikota ta fado kan Faffan chest Dinshi kurawa juna ido sukayi for some minutes, kallon cikin idon'ta yayi babu shiri ta lumshe Sexy eyes din'ta domin wani irin kwarjini yayi Mata cikin ranshi yace tana da kyau.





Saurin saketa yayi fuska ba walwal yace bakya gani ne Am sorry ta furta in a small tone tayi bedroom din'ta da sauri domin Tsananin bugun da kirjin'ta yake da kallo yabi bayan'ta ko wace ita oho.





Bedroom din Ammy ya shiga waye t'akeyi Zama yayi harta gama





Minert✍🏻
[23/07, 17:08] Marubuciyan Jini Daya: πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—
*AKAN MIJINA*
πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—




*NOT EDITED*⚠



Written by
Minert✍🏻
Dedicated to
Fan's Groups




Bansan Da Wace Kalma Zanyi Ampani Da Ita Wajan Nuna Godiya Ta Garekuba Sedai Allah Yah Saka Muku Da Mapipicin Alkhairi Nagode Da Irin Addu'ar KuπŸ™πŸ»





*ALJABBAR*



IT'S ALL ABOUT LUV AND CARINGπŸ’ž



Bismillahir Rahmanin Raheem


Pg 15&16


K'are masa kallo Ammy tayi tana nazarin yanayin sa cikin kulawa tace make damunka lumshe ido Kawai yayi Yana jin yadda zuciyar shi t'ake zafi danne bacin ranshi yayi.




Zama tayi kusa dashi murya a taushashe tace I'm talking to you Habibee bude manya idon'shi yayi ya zuba mata su kamar wanda ya warke makanta kamar bazaiyi magana ba yace Ammy ciki ne da ita Amma zubarwa t'ake son yi, da sauri Ammy ta kalleshi zubarwa Kuma ta furta da sauri gyada mata Kai yayi.





Shiru Ammy tayi a hankali ta fara kwantar masa da hankali domin tasan halin tilon Dan nata hukuncin dazai dauka akan Aysha bamai sauki bane, saboda IRFAN akwai Mutuwar son Yara.





Amatullah zama tayi a bakin gado tana maida numfashi wani irin kwarjini yake mata tana rufe ido shi take gani ga sassanyan kamshi turaren sa Ohhh good make shirin faruwa Dani ne dafe saitin zuciyar tayi.






Sosai hankalin Aysha yayi bala'in tashi Zama tayi turus akan kujera ta rafka uban tagumi ita dai gaskiya bata da burin haihuwa yanzu domin bata son sturucture din jikin'ta ya canza cike da damuwa tayi hanyar bedroom din'ta dole tasan abinyi.





Yana wajan Ammy har dare acan yayi Dinner tuwon semo da miyar kubewa Wanda yaji bushashshen kifi da kunun aya Amatullah tayi se farfesun kayan ciki se tashin kamshi yake tana gamawa ta shige d'akinta wanka tayi ta shirya cikin doguwar Riga maroon colour ba karamin kyau tayi ba.





Seda ta tabbatar yabar parlon kafin ta fito domin idan taci gaba da kallon'shi zuciyar'ta zata iya bugawa kome yasa oho, suna Tsananin kama da Ammy sedai yafi Ammy hasken fata da kyau hakan ya nuna cewa danta ne.







Tana jin alamun ya fita ita ma ta fito cikin nutsuwa gefan Ammy ta zauna tace Ammy barka da dare Yauwa Amatullah sannu da kokari murmushin dake Kara mata kyau tayi har dimple din'ta ya loba abinci ta diba kadan taci tayiwa Ammy seda safe da kallo Ammy tabi bayan'ta tana yaba nutsuwa irin ta Amatullah har yanzu bata son Mahaifinta ya samu lafiya ba domin Ammy bata gaya mataba.






Yana shiga parlon Aysha ta bishi har bedroom Dinshi hakuri ta fara bashi akan wallahi ta fasa zubar da cikin murmushin gefan Baki yayi yace kima zubar Mana Aysha ni Kuma sena Miki Illar da Duniya ma zata kasa ganeki.




Iya abin d'aya furta kenan ya shiga toilet.






Tun Daga lokacin Aysha ta fara laulayi bata iya cin komai tanaci se amai hatta Office ta Dena zuwa ko yaushe tana kwance ganin haka ne yasa Ammy ta fara tura Amatullah wajan ta akan ta dinga gyara Mata daki.






Yauda safe bayan ta gama gyara part din Ammy ta nufi nasu Aysha a hankali take tafiya kamar mai tausayi k'asa ita fa har yanzu tsoran Soja t'ake da haka harta shiga Babban parlon babu kowa Bedroom din Aysha ta shiga fitowarta daga wanka kenan.





Sunkuyar dakai tayi tace Aunty Ina kwana fuska babu walwala Aysha ta amsa domin tun lokacin d'ata fara ganin Amatullah taji ta tsaneta saboda tana da wani irin sirrin kyau Wanda ba kowa ne zai Gane hakan lokaci guda ba.







Dakyar ta amsa tana gama shiri tayi parlo gyaran dakin Amatullah ta fara Nan da Nan dakin ya dauki kamshi wanke toilet din tayi tana gamawa ta fito kallon banza Aysha ta wurga mata cikin isa tace ki dafamin indomie babu musu ta shiga kitchen





Please manage it mura ke damuna




Minert✍🏻
[23/07, 17:08] Marubuciyan Jini Daya: πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—
*AKAN MIJINA*
πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—



*NOT EDITED* ⚠


Written by
Minert✍🏻
Dedicated to
Hrtbeath




The I Stop Loving Yuhh Is The Day When I Close Mah Eyes ForeverπŸ’


Sakon Gaisuwa Gareku ASMEENAT XEEYAN FANS GROUP Ina Kara Jinjina Muku🀝🏻



IT'S ALL ABOUT LUV AND CARINGπŸ’ž



Bismillahir Rahmanin Raheem


Pg 17&18


Cikin 5 minutes ta kammala dafa indomie se tashin kamshi take tun kafin ta karaso parlon yawun Aysha ya gama tsinkewa a karamin tray ya kawo Mata hade da black tea se kamshin citta da kanumfari yake.




Hankalin kwance Aysha ta faraci se wani lumshe ido tsabar Dadi sedai bata nuna hakan ba domin kada Amatullah tayi tunanin cewa Food yayi mata Dadi ne Kuji Pah ReadersπŸ€”




Cikin katun kasaita da izza ya fara saukowa daga upstairs sanye da kakinsa na Sojoji As usual yayi bala'in kyau sedai Fuskar'shi babu walwala tun kafin ya karaso kamshin turaren sa ya shaida mata zuwansa, sannu a hankali bugun numfashin ta ya fara sauyawa da karfi kirjin'ta yake bugawa.




Lumshe ido tayi cikin zuciyar ta t'ake Addu ar Allah ya kawo mata dauki saboda ta rasa wane Yanayi zuciyar'ta t'ake tsawar da Aysha ta doka mata ne ya dawo da ita daga Duniyar tunani.




Keee wane irin iskanci wannan Ina miki magana kin wani lumshe wannan tsinannun idon naki Mai kama Dana Mage🀣🀣 Oya wuce ki fice daga nan, jiki ba kwari tayi hanyar fita duk abin da suke akan idon'shi Amma yayi kamar bai gani ba.





Yana fita Escort dinshi suka rufa masa baya domin suna da Metting Around 8:30am




Tun Daga wannan lokacin Amatullah kullum ita take dafawa Aysha duk wani Abu da zataci hatta panties din'ta Amatullah ke wankewa Sam bata da wani hutu idan ba dare ne yayi ba sunyi sabo da Ammy sosai.





IRFAN kuwa tun lokacin da idon'shi ya sauka a kanta ya rasa nutsuwar zuciya sedai Miskilanci ya hanashi nunawa sosai yakejin Yarinyar cikin Hrt dinsa ganin yadda Ammy t'ake kula da ita.






Koda yaushe Amatullah bata da wani zance sena Abban ta iya Hajjo kuwa bata dawo ba cikin Aysha kullum Kara girma yake wani irin so IRFAN yake yiwa cikin.





Zaune suke ita da Ammy kanta Yana cinyar Ammy cikin alamun damuwa tace Ammy tace please zan koma gida wallahi nayi missing Abba na Kuma suma nasan sunyi kewata don Allah ranar Sunday zan tafi shiru Ammy tayi har cikin ranta bata son tafiyar Amatullah domin gani take kamar ita ce Mahaifiyar ta.





Shafa lallausar sumar kanta Ammy tayi cikin kulawa tace Doughter idan kika tafi dawa zan zauna Dariya Amatullah tayi tace haba Ammy seki zauna da Yah IRFAN Mana murmushin Ammy tace to Doughter aishi ya girma da yawa,




Makale kafada Amatullah tayi alamun ita aa toki bari next month insha Allah zan kaiki da kaina zare ido tayi alamun mamaki tace Ammy bazaki iya zuwaba lakuce Mata hanci Ammy tayi tace injiwa nima ae garin mu kauye ne.





Dariya sukayi gaba daya




SU WAYE WANNAN FAMILYN



NASSER DIKKOH shine cikakken sunanshi Dan Asalin garin Yobe ne su biyu iyayansu suka Haifa Nasser shine babba se kaninshi Mai suna Yazeed Allah ya horewa DAWOOD DIKKOH Arziki sunan mahaifin su kenan.





Sun taso cikin gata da kulawa ga tarbiyyah Mahaifiyar su Hajiya Zarah macece mai Tsananin kirki rabin rayuwar su a kasar waje sukeyi.





NASSER DIKKOH a kasar Etopia yake karatun shi acan suka hadu da MOWADDAH Yar Asalin Etopia ce Class dinsu Daya sannu a hankali har suka kulla soyayya sosai suke son junan su.







Minert✍🏻
[23/07, 17:08] Marubuciyan Jini Daya: πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—
*AKAN MIJINA*
πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—



NOT EDITED⚠


Written by
Minert✍🏻
Dedicated to
Fan's Group



TUNATARWA PLX MUSAN IRIN KALAMAN DA XAMU DINGA PURTA WASU MUTA NAN SAM BASA SAWA HARSHEN SU LINZAMI MUTUM YA DINGA SAKIN MAGANA KAMAR WANI WAWA FALYAKU KHAIRAN🀫



GAREMU WRITTERS
DUK WANDA YAKE RUBUTU DOLE SEYA GAYYATO HAKURI DA JURIYA DOMIN XAKAYI SPENDING TIME DINKA KA RUBUTA MUSU NOVELS SEDAI KUMA KANAYIN MISTAKE MUTUM BAXAI IYA MAKA HAKURI BA DON ALLAH MU TARU MU GYARA ALLAH YA KARA MANA BASIRA DA KARFIN IDOπŸ™πŸ»




IT'S ALL ABOUT LUV AND CARRINGπŸ’ž



Bismillahir Rahamanir Raheem



Pg 19&20


Basu wani dauki long time ba aka daura musu aure domin ta fannin Familyn suma sun fahimci juna.




Bayan auren su Nasser ya dawo Abuja da zama sosai suke nunawa junan su kulawa shida *MOWADDAH* .




Macece kyakkyawa, akwai son dangin mijin ta.




AFTET 10 YEARS




Abubuwa da yawa sun faru cikin shekara goma masu dadi da maras dadi ciki kuwa harda mutuwar iyayan Nasser sunyi kuka sosai na rashin iyayan sedai sun mika lamuran su ga Allah domin shike bayarwa kuma shike hanawa.





Mowaddah ta haifi d'anta santalele ba karamar murna sukayiba ranar suna yaro yaci sunan kakan'shi wato DAWOOD NASSER DIKKOH /IRFAN.




Anyi wasa da naira ba kadan ba tun daga kan Irfan Mowaddah bata sake haihuwa ba hakan yasa suka bashi tarbiyyah Irfan yaro ne kyakkyawa sedai tun yana yaro miskili ne bai fiye wayan dariya ba da wuya ka gane halin da yake ciki.





Yayi sabo sosai da iyayan'sa musamman Ammyn sa bai iya boye duk wani problems dinsa sau tari tafi Daddy karantar yanayin Irfan kasancewar ta uwa mai hangen nesa da saurin nazartar halin dan adam.






Tun yana yaro yake shaawar aikin soja Daddy bai hana shiba fatan alkhairi suka masa Flight dinsu ya d'aga zuwa America.






Tun tafiyarshi bai dawo gida ba seda ya gama karatun shi inda ya cimma burin sa na zama Babban Soja wanda Duniya t'akeji dashi.





*AYSHA* Yace ga Major Muddaseer Alkali tun lokacin data dora ido akan Irfan taji duk duniya babu wanda take so kamar shi Major shine uban gidan Irfan yana mugun Girmamashi.






Irfan mutum mai tsananin kamun kai sam baida wasu friends shi kadai yake rayuwar sa tun yana America Yan mata da yawa sunsha kawo masa kansu sedai yana kyamar Zina duk da yana da feelings sosai koda yaushe yana cikin yin azumi.






Lokacin da Aysha ta samu Daddyn ta da bukatar son Irfan Major yayi murna yace ta bari seya tambayi Irfan.






IRFAN Allah ya masa kwarjini da cikar zati kamar Namijin Zaki haka yake Hatta Prisdent ya bashi lambar yabo.







Aysha macece mai son abin duniya ga shegen kishi duk da irin kudin da mahaifin ta yake dashi hakan bai ishe taba akwai son harkar karya.





Yau suka tashi cikin tashin hankali domin Daddy babu lafiya hawan jini ga ciwon sugar Hankalin Ammy yayi bala'in tashi hatta Irfan jijiyoyin kanshi sun mike domin ganin halin da Daddy yake ciki.





Likitoci sunyi iya bakin kokarin su sedai Allah bai nufa zai tashi ba mutuwar Nasser Dikkoh tayi tambari cikin garin Abuja da kewayenta dubban muta ne suka halarci sallar gawarsa Ammy yanke jiki tayi ta f'adi har aka kaishi gidan shi na gaskiya bata farfado ba.






Gaba daya duniyar tayiwa irfan zabi wani irin radadi yakeji cikin zuciyar shi sam kuka yaki zuwa masa lokaci kadan zazzabi mai zafi ya rufeshi seda sukayi 2 weeks a hospital.






Tun rasuwar Daddy Irfan ya kara zama miskili Hankalin Ammy ya k'ara tashi ganin tana shirin rasa tilon dan nata Nasiha ta dinga masa mai shiga jiki hade da lallashi harya dan saki jiki.






Dakyar ya amince da Auren Aysha da Major ya bashi Ammy ta sawa abin albarka.




Duk wani program din da sukayi bai halarci ko daya ba domin baya son hayaniya su Aysha an samu abin da ake so miji na nunawa saa.







Tun Auren su Aysha kaf ta rabu da kawayen ta domin irin tsananin kishin da take dashi *AKAN MIJINTA* zata iya batawa da koma waye.




Matsalar Aysha shine sam bata son kula da miji ba hatta gadon da suka kwanta masu aiki ne suke gyara mata ga son jiki ko abinci bata iyaba Irfan kuwa akwai kyankyami dalilin da yasa ya koma wajan Ammy dacin abinci kenan






Kwata kwata bata son haihuwa sabanin Irfan da yake son Yara duk Pills din take sha bai saniba.





Tasha korar House gal akan suna kallon mijin ta sam bata son talaka






CIGABAN LABARI




Kwance yake akan Sofa idon'shi yana lufe tunanin Yarinyar ne fal zuciyarsa ohhhhh dammmm it make shirin faruwa dani ne ya furta cikin karamin sauti shafa wuyanshi yaji an farayi sarai yasan Aysha bai kula taba.






Dear ta kira sunanshi bude lumsassun idonsa yayi yana kare mata kallo shafa cikin jikinta yayi har cikin ranshi yakejin kaunar abin dake cikin.









Minert✍🏻
Vote
Comments
Share




08068719106 Mata OnlyπŸ‘ŒπŸ»
πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—
*AKAN MIJINA*
πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—



*NOT EDITED*⚠



Written by
Minert✍🏻
Dedicated to
Fans Group




Nah Fara Ganin Comments Yana Low Plx Idan Baku Sone We Shall Tell Me Xan Iya Ajiye✍🏻 Wannan Bah Abin Damuwa BaneπŸ€·πŸ»β€β™€ And then Plx Idan Kinsan Irin Wannan❀ Xakimin Comments Dashi Ki Rike Abinki Minert Bata Bukata





IT'S ALL ABOUT LUV AND CARINGπŸ’ž




Bismillahir Rahmanin Raheem



Pg 21&22



Jikin Amatullah ya sakeyin fresh saboda hutun data samu koda yaushe hankalin'ta Yana kwance sedai da xarar tayi ido biyu da Irfan takan rasa Duk wata nutsuwar zuciya da gangar jiki ta rasa wane irin Abu takeji game dashi.




Akwai kuruciya a jikin'ta wannan dalilin yasa ta kasa Gane cewa sone yayi Mata shigar sauri yanzu ne take cikin shekara nasha biyar alamun budurci sun fara bayyana a jikin'ta.




Ita ba fara ba Kuma bazaa kirata da baka ba chaculate colour ce irin colour dake da mukatar wuyar samu tana da tsayi sedai sam bata da jiki Sexy eyes gareta wanda da wuya Mutum ya jure kallon'ta na tsahon lokaci dirin ta me kyau ne kirar coca cola gareta.




Tana da fadi ta kasa ta sama kuma babu akwai cikar kirji domin manyan Nono gareta.





Yau tun safe t'ake ciwon Mara daurewa tayi harta gama Duk wasu ayyukanta Ammy tana lura da ita cikin tace Amatullah lafiya kike kuwa murmushin karfin Hali tayi tace lafiya lau Ammy gyada kai Kawai Ammy Bawai donta yarda ba.






Bayan ta gama gyara dakin Aysha a hankali take tafiya domin hatta cinyoyin'ta ciwo suke hanyar fita tayi cikin tsawa da Rashin mutunci Aysha tace keee banxa Ina kike Shirin zuwa Baki gamamin nawa aikin ba shiru Amatullah tayi still bata juyo ba domin ta tsani irin halin Aunty Aysha kwata kwata bata dauki Dan adam da wata daraja ba.





Takai almost 6 minutes kafin ta juyo cikin sanyin murya tace kiyi hakuri Aunty Aysha banajin Dadi ne bata saurari abin da zata sake cewa ba tayi gaba abinta saboda wani irin murdawa da taji cikinta Yana Mata.





Dakyar ta iya shiga parlo zubewa tayi a wajan tana salati se yarfa hannu take da sauri Ammy tazo ta d'agata rungume Ammy tayi cikin Kuka tace Ammy mara ta cinyoyina ciwo sosai ta bawa Ammy tausayi da alamu tana Shan wahala.





Riketa Ammy tayi ta kaita Bedroom din'ta kwantar da ita tayi black tea ta hada Mata dakyar tasha tana gamawa ta fara amai.





Tsaye yake a bakin kofa ya zuba mata oily eyes dinsa har cikin zuciyar sha yakejin ciwon nata sedai bazaka Gane hakan ba.





Ammy tana dago ido ta ganshi da sauri tace please Habibee take her to hospital lumshe ido yayi as usual a hankali ya tako har inda t'ake.




Yasa dogan hanun'shi ya cirata sama kamar wata Baby waje ta fita da ita.




A bayan mota yasata Escort dinshi suka taho da gudu daga musu hanu Kawai yayi da kan'shi yayi driving har suka hospital tun kafin ya isa ya sanarwa Consultant din Yana da marar lafiya.




Juyi kawai take hanun'ta na bisa marar ta Yana parking ya dauko ta suka shiga cikin hospital.




No westing of time suka fara bata treatment din gaggawa Drip suka daura Mata hade da allurar bacci.





Cikin ikwan Allah kuwa bacci yayi awun gaba da ita Dr Junaid ne ya fito ya kalli Irfan cikin girmamawa yace Sir plz muje office.





Zama yayi Yana kallon Dr Junaid bayani ya fara masa akan Period ne Kuma Yana bata wahala saboda haka if possible kuyi Mata Aure Kawai domin shine Solution din problem din'ta.




Kura masa ido Irfan yayi for some minutes kafin yace Ok thanks ficewa yayi bayan ya karbi Drugs din'ta.





Zama yayi a kujerar dake facing din'ta se yau ne yayi Mata kallon tsaf da sauri da sauri Hrt dinsa yake beating.






Bata farkaba se wajan 1 a hankali ta fara bude ido kamshin turaren sane ya fara shiga hancinta maida idon'ta tayi luf ta lumshesu domin ta fahimci shi kadai ne tare da ita.





Sarai ya ganta Amma ya share Ammy ce ta shigo d'akin wajan Amatullah ta nufa cikin damuwa ta zauna kusa da ita bude ido tayi harta rame rike hanun'ta Ammy tayi tace sannu Murmushi tayi Mata saboda jikinta babu karfi.





Kamata Ammy suka shiga toilet da kallo yabi bayan'ta saboda yadda take bleeding fita yayi abinsa ruwan zafi Ammy ta hada Mata wanka tayi ta shirya kafin ta fito an canza bedshit din.





Tea Kawai tasha zuwa yamma akayi discharging din cuz jikinta yayi sauki





Tunda suka koma Ammy ta hanata aikin komai harsai ta gama period sosai t'ake samun kulawa ta wajan Ammy tsakaninta da Irfan Gaisuwa ce ita ma ba koda yaushe ba.









Minert✍🏻
Vote
Comments
Share




08068719106 Famale OnlyπŸ‘ŒπŸ»
πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—
*AKAN MIJINA*
πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—




*NOT EDITED* ⚠



Written by
Minert✍🏻
Dedicated to
Fan's Groups





IT'S ALL ABOUT LUV AND CARINGπŸ’ž



Bismillahir Rahmanin Raheem



Pg 23&24



Seda tayi 7 Dys bata aikin komai ranar Sunday kuwa tayi wankan tsarki.




Hankalin Aysha gaba daya ya gama tashi domin se yanzu tasan cewa girkin Amatullah shine irin abincin d'ata kauna Dan wannan kwanakin da tayi bataci dafin indomie din'ta se tashi Sam babu Dadi.





Monday nayi Amatullah ta gama shirya kayanta tsab na tafiya gida saboda gani t'ake kamar wani Abu ya sami Abban ta jikinta Duk a sanyaye cuz gefe d'aya tanajin kewar Ammy har Jikin Jini da tsokar ta.




Ga tunanin Irfan d'aya hana zuciyar'ta sukuni gara tayi nisa dashi Wala alla ta samu sassaucin abin da t'akeji.




Sanye take cikin Arabian gown Ash color tayi kyau sosai Amma sam fuskar'ta babu walwala d'akin Ammy ta shiga a hankali tayi sallama idon sune ya harke cikin na juna da sauri ya d'auke nata domin wani irin Abu taji ya soki zuciyar'ta.





Duk abin da suke akan idon Ammy ita ma basarwa tayi Zama Amatullah tayi kusa da Ammy kanta a k'asa tace Yah Irfan Ina kwana kamar bazai Amsa ba kafin yace lafiya Kawai.





Maida kallon'ta tayi kan Ammy tace na shirya da mamaki Ammy take kallon'ta tace zuwa kenan Wasa ta farayi da zoben gwal din d'ake hanun'ta wanda Ammy ce ta siya mata, Ammy gida nake son komawa wallahi Ina yawan Mafarkin Abba na please Ammy don say no.






Shiru Ammy tayi nadan lokaci rike hanun Amatullah tayi tace Doughter harkin gaji da Zama dani a hankali ta girgiza Kai domin gaba Daya kwarjinin sa ya gama cika d'akin gashi ya wani tsura mata ido.





Sosai yaji zuciyar ta karaya yanzu idan ta koma yaya zaiyi da tarin kaunar ta ita kadai yake gani yaji sanyi gashi tana Shirin nisa dashi inaa bazai yiwuba.






Kallon Ammy yayi shaye da toka yace Ammy ta bari se jibi Yana gama fadar haka yayi waje abinsa to kinje me Brother dinki yace Koh.





Kamar zatayi kuka ta gyada Kai babu yadda ta iya haka ta koma d'akinta kwanciya tayi abinta har bacci yayi awun gaba da ita.






Sosai Ammy t'ake nazarin abin d'ata hango cikin idon Irfan idan Gaskiya ne kuwa zatayi farin ciki marar misaltuwa wani tunani tayi cikin ran'ta murmushin nasara tayi.






Ranar da zata tafi ko wajan aiki Bai fitaba yake part dinsa saboda bazai iya jure kallon fitar taba sarai Ammy tasan abin d'aya hanshi fitowa shiyasa bata neme shiba.





Driver ne ya jasu harda Kawunan Irfan domin sun gama magana dasu dalilin da yasa suka tafi tare kenan.





Amatullah tana Jikin Ammy tayi shiru har suka iso Garin su a kofar Dan karamin gidan nasu Driver yayi parking sosai ta razana saboda yadda taga an canza komai na gidan ya dawo ginin zamani kamar ba gidan suba.






Kallon'ta Ammy tayi tace mu shiga Mana murmushi d'auke akan kyakkyawar fuskar'ta suka shiga gidan da sallama Abban ne ya fito d'aga daki Yana Mai amsa sallamar.






Xare ido Amatullah tayi ganin kamar bashi ba yayi kiba da kyau hutu dajin Dadi sun samu wajan xama da sauri ta rungumeshi tana Hawayen murna Anna ce tayiwa Ammy iso cikin nuna Jin Dadi.





Ita ma Ammy babu wani kyama a tare da ita tace da tare muke da b'aki a waje Abba ne ya fita yayi musu iso har parlon Abinci da drinks Anna ta kawo musu domin suma yanzu sun xama Yan Gayu Lol.





Amatullah se binsu t'ake da kallo ganin yadda komai ya canza bayan sun nutsu Abba yayi Mata bayanin komai rungume Ammy tayi cikin tsantsar kauna tace shine Ammy t''aba gayamin ba Jan karancinta Ammy tayi tace don Nayi Doughter godiya ta dinga mata.






Gidan su Ilham ta nufa cike da dokin son ganin Ilham sosai sukayi murnar ganin juna Nan Hira ta barke tsakanin su





Bayan Amatullah ta fita Ammy ta gabatar da Abba bukatarta nason hada Auren AMATULLAH DA DAWOOD NASSER DIKKOH, Abba yayi Naam da hakan Nan Kawunan Irfan suka bukaci idan anyi sallar Axahar a daura Auren.






Musa seda ya gayawa yan uwanshi ganin yanzu Yana da kudi yasa suka amince har wani rawar jiki suke.






Bayan Amatullah ta dawo Ammy janyota jikinta tace Amatullah bani hankalinki Ina so muyi magana Kuma bana son ki boyemin komai domin nima kamar Mahaifiya nake a wajanki.





Nutsuwa Amatullah tayi kafin tace Ina jinki Kina son IRFAN zaki Aure shi wannan shine kadai abin da nake so a wajanki idan bakya sonsa wallahi baxan takura Miki ba gaban'ta ne taji ya fadi saboda batayi tunanin maganar da Ammy xata mataba kenan.






Lumshe ido tayi tace har Abada bazan ki Duk wani Abu d'aya fito d'aga garekiba domin kece silar kawo farin ciki Duniya ta wallahi har cikin Raina na amince Ammy, sosai ta bawa su Abba mamaki hade da murna.





Hugging din'ta Ammy tace Allah ya Miki Albarka ameen ta furta a hankali domin tana hango irin wahalar da zata sha a wajan ganin ba son'ta yakeba ga matar Mai jarabar Kishi.





Karfe Daya aka daura musu Aure sosai muta ne suka taru.




Kanta ne taji yayi dammmmmm shikenan TA FARU TA KARE ANYIWA ME DAMI DAYA SATA







Minert✍🏻
Vote
Share
πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—
*AKAN MIJINA*
πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—




*NOT EDITED* ⚠



Written by
Minert✍🏻
Dedicated to
Fan's Group



Ina Ganin Irin Sakonku Nagode Sosai Wanda Ban Musu Reply Bah Kuyi Hkr Abin Neh Da Yawa Iya Wuya Ana TareπŸ€πŸ»πŸ’―




Gaisuwa Ta Musamman Ga Masoya Novels Dina Gsky Ina

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment