Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Jin Dadin Yadda Kuke Comments Hrt Yuhh All




ITS ALL ABOUT LUV AND CARINGπŸ’ž



Bismillahir Rahmanin Raheem


Pg 25&26



Kudi sosai Ammy ta cire aka dinga rabawa jama'a da turamen zannuwa Gaskiya abin ne Wanda ya gani.




Su Anna Baki yaki rufuwa ita kanta Ammy ta rasa wane irin farin ciki t'ake ciki hakan Yana da nasaba ga irin Kaunar da take yiwa Amatullah da Kuma shi kan'shi uban gayyar wato IRFAN.





Sosai Jikin Amatullah yayi sanyi kanta ne taji yayi Mata nauyi kwanciya tayi jikin Ilham tana sauke Nannauyar ajiyar zuciya rintsa ido kawai tana Jin yadda aka Hayaniya a cikin gidan shikenan ta Zama mallakin Irfan sam ta kasa Gane wane Hali zuciyar'ta t'ake ciki shin farin ciki ne Koh akasin haka.





Shi kuwa Irfan se yamma lis ya fito ya shiga ciki domin duba lafiyar babyn sa totaly babu wani karfi a jikin'sa Aysha ce zaune a parlo tana kallo abinta hankalin'ta kwance kayan frut ne a gaban'ta cikin'ta ya fito sosai Kuma ba laifi yayi Mata kyau.





Zama yayi kusa da ita har suna gogar juna Dora kanta tayi a kafadarshi cike da kaunar Mijin nata tace Honey gaskiya Ina sonka please kamin Alkawarin bazaka min kishiya ba domin bazan iya jure ganinka da wata macen ba.




Shafa cikin'ta Kawai Yana lumshe ido ya matsu babyn sa ya fito Duniya koxai dinga rage kewar wani abin ganin bazai kulata bane yasa taja bakin'ta ta tsuke.






Daure Kawai yake tunda ta fara laulayi sam ta Dena bashi kanta kullum dakyar yake bacci saboda azababbiyar shaawar d'ake damunsa.






Bayan komai yayi sauki Ammy ta fara Shirin komawa Abuja tace zata turo me gyaran jiki ta fara gyara Amatullah domin se an shiryata kafin a kaita.






Flight sukabi cike da tsaraba irin na fulani suka dawo Gaskiya mutanan akwai karamci cewar Kawu Ishaq murmushi Ammy tace ba laifi kam yanzu Kuma semu fuskanci tijarar Aysha Dariya Duk sukayi saboda kowa yasan akwai daru Nan gaba






Plx Kuyi manage banida chaji




Minert✍🏻
πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—
*AKAN MIJINA*
πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—




*NOT EDITED* ⚠



Written by
Minert✍🏻
Dedicated to
Fan's Groups




IT'S ALL ABOUT LUV AND CARINGπŸ’ž




Bismillahir Rahmanin Raheem


Pg 27&28



Suna isa bayan sun huta kowa ya nufi gidan sa kana kallon fuskar Ammy zaka san cewa tana cikin farin ciki.




Bayan ya dawo daga Office site din nufa domin tun lokacin da suka sauka a airport ta sanar dashi bai samu fitowa ba se yanzu.






Tana Dining area tana cin abinci yayi sallama cikin Husky voice dinsa wanda zuwa yanzu tayi bala'in k'ara yin laushi Fuskar'shi tayi fayau kyanshi ya sake fitowa kare masa kallo Ammy tace Habibee.





Shima ita yake kallo Zama yayi a kujerar da t'ake facing tata yace well come back Ammy nah shafa beauty face dinsa tayi tace I miss you rike hanun'ta I miss you too.






Da kanta tayi serving dinsa turawa Kawai yake Bawai don Yana jin Dadin saba bayan sun gama yace bari yayi wanka da kallo tabi bayan'sa tana girgiza abu Yana cinsa Amma ya gagara gaya mata Uhm Namijin Duniya kenan.






Washe gari Anna ta fara gyara Amatullah sosai jikinta yayi sanyi komai a sanyaye t'ake yinsa Ilham ce kawai t'ake bata kwarin gwiwa.






A hankali Anna ta fara koyar da ita darusan zaman gidan Aure domin har yanzu ita din Yarinya ce bata San komai game da Rayuwar Aure ba.






Anna ta cire kunya kullum da irin darusan da t'ake koyawa Amatullah tun tanajin kunya harta saki jiki suna waya da Ammy koda yaushe tana jin lafiyar ta.






Aysha kam kazanta ta karu saboda cikin'ta ya tsufa rabon data yarda Irfan yayi Sex da harta manta shima tun abin Yana damunsa harya shareta.





Mai gyaran jiki Ammy tayi Order tun daga Etopia aka mata masauki a gidan su Anna sosai ta fara gyara Amatullah cikin kwana uku tayi wani bala'in kyau kamar wata aljana Duk inda ta gifta kamshi ne yake tashi kirjin'ta ya Kara cikowa saboda maganin gyaran Nono da Anna t'ake bata Hips dinnan ya k'ara f'adi komai dai Masha Allah.





Ita kanta ta fara Jin Canji a jikin'ta wasu lukatan Feeling's yana damunta.






Ammy ce zaune ita kadai a parlo da alamu waya t'ake zuwa can Naga Irfan shida Aysha sun shigo a hankali Aysha ta zauna akan Sofa tace Barka da dare Yauwa Aysha ya nauyin jiki Alhmdlh Kawai tace.





Gyaran Murya Ammy hakan yasa suka zuba mata ido.



Aysha Ammy ta Kira sunanta d'ago ido Aysha tayi tace Naam Ina so ki bani hankali sannan kisa Allah a Duk cikin lamuranki bana so kiyiwa maganar dazan gaya Miki da wata Mummunan fassara ki dauka amatsayin Kaddara ce.





Insha Allah Ammy babu wani dar dar Ammy tace An daurawa IRFAN Aure 2 weeks back Wanda shima kansa Bai saniba Whattttttttttttt Aysha ta furta cikin karaji Aure fa kikace Ammy wallahi har Abada abin da bazai taba yiwuba kenan kishiya Ina never.





Shima kansa maganar ta bashi tsoro sedai tsabar Miskilanci irin nasa Bai nunaba.






Ki nutsu kin Sani bake kadai bace koh cewar Ammy ko sauraran ta Aysha batayi wani irin daci zuciyar'ta t'ake mata wani shegen kallo ta wurgawa Ammy tace wallahi na sani dama ba Sona kike ba in Banda tsabar mugun...... Bata karasaba taji saukar zazzafan mari, dafe wajan tayi idon'ta yayi jaaa tace Irfan nika mara Yes be careful with your tongue karki manta ita din uwata ce zan iyacin mutuncin Duk Wanda ya nemi walakantata so ki kiyaye.






Haba haba Irfan meyasa ka mareta cewar Ammy baiko d'ago ido ba yace hakan shine daidai.





Dafe marar ta tayi tana Jin wani irin ciwon baya sunkuyawa tayi ganin tsaiwa na neman gagararta da sauri Ammy ta matsa kusa da ita tace sannu Aysha Irfan maza fito da mota haihuwa ce.






Labour room aka shiga da ita se ihu t'ake kamar wata ArniyaπŸ€£πŸ€£πŸ€£πŸ™Š Zama yayi ya dafe kan'shi dake Sara masa take it easy Habibee cewar Ammy Dora kan'shi yayi a kafadar'ta Yana jin zuciyarsa tana sanyi.






Takai wajan 4 Hour's tana labour da temakon likitocin ta haifo Katuwar yarinyar ihunta ne ya sanar dasu Ammy cewar ta iso Duniya murmushin farin ciki ne ya kufce musu.





Nurse ce ta fito da Babyn tana sanye cikin kayan sanyi na jarirai sunyi Mata kyau Rungumeta Ammy tayi tana yiwa Allah godiya shima Irfan se wani smileeeee yake t'ake yaji kaunar Babyn tana ratsashi.






Bayan komai ya lafa Duk yadda akaso akan Aysha ta dauki babyn Sam taki lallashinta Ammy ta dinga yi Amma Ina Gashi ta fara Kuka alamun tana neman abincinta









Minert✍🏻
πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—
*AKAN MIJINA*
πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—



*NOT EDITED* ⚠



Written by
Minert✍🏻
Dedicated to
Hrtbeath




I Can't Explain How Iurf Yuhh Allah Yah Barni Dake Bloody🌹




Can't Hrt Yuhh All Mah Fans Gaskiya Kuna Bani Kala Allah Yah Barni DakuπŸ’—πŸ’―



Kah Samu Kyakkyawar Fahimta Kaida Reader's Shine Abin Da Yapi Dacewa Bawai Ka Dauki Girma Ka Dorawa Kanka Saboda Kana Rubuta Novels Bah Allah Yayi Mana Jagora





IT'S ALL ABOUT LUV AND CARINGπŸ’ž



Bismillahir Rahmanin Raheem


Pg 29&30




Duk yadda Ammy taso akan ta bawa Baby Nono fir Aysha t'aki ranshi a matukar bace ya karbi Babyn daga hanun Ammy yayi gaba abinsa.






Office din Dr ya shiga yace ya Rubuta masa Madarar da zaa bawa Baby babu wani bata lokaci ya Rubuta masa fita yayi ya nufi Babban shopping Mall.





Guda d'aya Kawai ya siya saboda yayi waya za'a turo masa da China h'ade da Nanny da kanshi ya hada ya fara bawa Babyn t'ake kuwa ta farasha tana gamasha ya dorata a kafadar'shi tayi gyatsa t'ake yayi gaba da ita.






Tsura Mata ido yayi Yana jin yadda kaunar ta t'ake yawo cikin Jinin jikin'sa shima bacci ne yayi awun gaba dashi a bedroom din Ammy.






Yana fita Ammy tace yanzu Kee Aysha kin yiwa kanki Adalci kenan kin manta Manzan Allah hudu yace ayi Amma ke kin dauki bakin kishi kin Dorawa zuciyarki yanzu Ina amfanin wannan ita Kuma yarinyar da kika hanata Nono meye laifinta.






Ita Aysha babu bakin magana domin har yanzu bata wuce ba.





Da yamma suka koma gida kafin kace kwabo gidan ya cika da muta ne hatta yan uwan Ammy na Ethopia sunzo sosai kowa yake son Babyn domin babu abin data baro na ubanta.





Washe gari yayi Mata huduba da sunan Ammy wato MOWADDAH.





Lokacin da Major ya samu labari har gida yazo yayiwa Aysha tatas dakyar ta karbi AMRAH ta fara bata Nono ita ma kaunar yarta taji tana ratsata.






IRFAN bai sake bita kanta ba koda yaushe indai yana gida to Baby AMRAH na wajansa.






Ranar kuwa ansha shagali Kudi da kujerar Hajji Irfan ya dinga rabawa tsabar nuna farin ciki Baby AMRAH kuwa d'aki aka ware mata wanda ya tsara dakin shima daga China yaxo Duk wani Abu na wasan Yara akwaishi a d'akin AMRAH.





Aysha kuwa har yanzu fishi t'ake da Ammy lokacin da b'akin Ethopia zasu koma Ammy tace su bari se Amaryar IRFAN ta tare kafin domin Next week ne insha Allah.






Kayan lefe akwati set biyar aka hadawa Amatullah lokacin da aka Kai kayan sosai ya dauki hankalin muta ne kamar wata Diyar Governor tarba ta musamman akayi musu.





Ita dai Amatullah tana d'aki koh parlo bata fito ba.






Shirye shirye aka fara sosai time din da Ammy ta gayawa IRFAN wacece matarshi seda ya kusan suma tsabar farin ciki sedai bai nuna hakan ba wani irin sanyin Dadi yakeji har cikin bargwansa siririn murmushi ne ya kufce masa cuz baiyi tunanin zai sameta cikin sauki haka ba.







Yau aka dauko Amarya gaba daya Flight suka biyo Amatullah kuka Kawai t'ake saboda gani t'ake kamar ta rabu da iyayan ta kenan Nasiha sosai Abba da Anna suka mata dakyar aka cireta daga jikin'su.






Aysha fa hauka ne Kawai batayi yan uwanta sunata rarrashin'ta Amma Ina tayi nisa wajan kishin IRFANπŸ€ͺ






Duk yadda Baby Amrah t'ake kin kulata tayi tun daga harabar gidan yake jiyo kukanta da sauri ya shiga parlo Bai kula kowaba ya dauki Yarsa ya koma site dinsa da ita.






ABC ya hada mata bayan ta koshi ya farayi mata wasa se Dariya t'ake irinta Yara Nidai nace dama su Irfan ana Dariya haka.






Karfe biyar na yamma jerin motocin da suka dauko du daga airport suka shigo Estate din.





Yana jin shigowar su ya lumshe oily eyes dinsa hamdala yayi cikin ransa You Are Highly Welcome To House, ya furta cikin karamin sauti.







Site din Ammy suka shiga da ita tana rufe cikin wata tsadaddiyar liyafa Duk wajan data gifta se kaji sassanyan kamshi turaren ta.







Minert✍🏻
πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—
*AKAN MIJINA*
πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—




*NOT EDITED* ⚠




Written by
Minert✍🏻
Dedicated to
Princess Fatima Zarah




Wannan Shapin Naki Neh Idan Kinga Dama Kice Kada Wanda Ya Karanta Miki Har Kullum Ina Tunawa Da Cewa Ta Dalilin Kine Nakai Wannan Matsayin Keta Musamman Ce Allah Ya Saukeki Lpy AmeenπŸ™πŸ»





IT'S ALL ABOUT LUV AND CARINGπŸ’ž



Bismillahir Rahmanin Raheem



Pg 31&32



Liyafa ta musamman aka shiryawa yan kawo amarya kowa Yana brush da naman kazaπŸ€ͺ.





Amatullah tana bedroom din Ammy tayi luf kamar me bacci tunanin wane irin zama zatayi da muta ne biyun Nan musamman Aysha wacce t'ake tsoran kalar kishin'ta Ya Robbe ka temakeni ta furta cikin small tone.





Da yamma aka shirya gagarumar walima wacce ta hada da manyan malamai Hijabi har kasa da nikaf hade socks tasa iya manyan idon'ta Kawai ake iya gani.





Gab magrib kowa ya watse cike da tarin abin Duniya.





Aysha kuwa zaune t'ake dirshen kasan carpet tayi wani irin rama kamar wacce ta shekara tana jinya babu wanka bare aje batun Sallah tun Sister's din'ta suna lallashinta har kowa ya zuba Mata ido domin abin nata bana hankali bane.






Washe gari yan biki kowa ya nufi gidan sa.





Cike da takun kasaita ya shiga parlo fitowar ta daga wanka kenan kallo daya tayi masa ta d'auke ido Zama yayi bakin Loyal bed yace Aysha zauna muyi magana ganin yadda ya tsare gira babu alamun wasa yasa ta zauna.





Cikin dakekkiyar murya yace xan iya jure Duk wani abin da zakimin Amma Banda yiwa Amrah horan shin Kee wace irin macece a kanki aka fara kishi to wallahi daga yau se yau Duk ranta kika kuskura kika Kara hanata Nono kinji na rantse daga ranar zan baraki da ita wawiya kawai.






Kee kanki bakima San akan menene ake yin kishin ba ki gayamin tun lokacin Dana aureki wane Abu kika taba yimin a matsayina na mijinki Sam Baki damu da damuwata ba kanki Kawai kika sani.





Sosai ya Kunce mata kura ita kanta tayi mamakin ashe ya iya doguwar magana haka.





Tashi yayi ya fice bayan ya ajiye Mata Amrah toilet ta shiga tayi Mata wanka ta shirya cikin jins da farar t-shirt sosai tayi kyau se wangale baki t'ake Nono ta bata.





Bayan ta gamasha tayi bacci d'akinta ta kaita kwantar da ita tayi akan karamin Bed din'ta tayi kissing for head din'ta






Karfe 9:30pm Ammy ta tarasu a parlon ta ita dai Amatullah jiki na dar dar ta fito sanye take cikin Riga da zani sunyi Mata kyau over kamar a jikin'ta aka dinka sassanyan kamshi ne yake fita daga jikin'ta.





Tare suka shigo parlon Yana rike da Amrah akan cinyar Ammy ya direta shafa kanta Ammy tayi cike da kaunar Yarinyar.






Ciki ciki Aysha ta gaida Ammy bata wani damuba a hankali Amatullah ta d'ago ido karaf idon'su ya hadu Dana Aysha wata irin zabura Aysha tayi tana nuna Amatullah hannu na rawa tace kece wacce akayi gigin aurawa Irfan dama kina a Matsayin yar aiki na.






Tabbas kinyi Kuskure Amma zan nuna Miki bakin rijiya ba wajan wasan makaho bane.





Shut up Aysha wai yaushe zakiyi hankali ne kinsan Allah ki fita a ido'na girgiza Kai ta farayi tace har Abada bazan taba hada miji dake ba fita tayi da gudu tana toshe Baki saboda kukan d'ake Shirin kufce Mata.








Ita dai Amatullah ko motsi ta kasa sosai tsoro ya sake shiga jikin'ta tashi tayi a hankali ta nufi d'akin Ammy.






Da kallo yabi bayan'ta Yana jin yadda zuciyarshi take beating kamar ya rungumota ya gaya Mata yadda yakejin kaunar ta kabi komai a hankali cewar Ammy








Minert✍🏻
πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—
*AKAN MIJINA*
πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—





*NOT EDITED* ⚠




Written by
MinertπŸ€·πŸ»β€β™€
Dedicated to
Princess Fatima Zarah




Har Book Din Ya Kare Mallakin Kine Ina Sonki Sosai Allah Yabar Zumunci Kinyi Min Komai A RayuwaπŸ’žπŸ’―





Am Back For The Second Time Na Dawo Neh Sbd Fatima Domin Tafi Karfin Komai A Wajena Bare Kuma Novel




Tabbas Abin Da Haushi Ace Kana Abu Baa Gode Maka Lokacin Da Nace Nah Dena Wallahi I Get Some Messages More than 300 Kuna Son Abin Amma Comments Ya Gagara Ni Banji Haushin Kashe Lokacina Ba Seku Wanda Only Comment Ya Gagareku Plx Idan Kinsan Emogis Xaki Dinga Yimin Comments Dashi Wallahi Ki Rike Abinki Domin Bana BukataπŸ€·πŸ»β€β™€






Still Xaa Fara Sharhi Kofofi A Bude Suke🌹





IT'S ALL ABOUT LUV AND CARINGπŸ’ž




Bismillahir Rahmanin Raheem



Pg 33&34




Take it easy Habibee shafa lallausar suman kan'shi yayi fita yayi shima ya nufi part dinsa.




Yana tunanin irin hukuncin dazai yankewa Aysha a wannan ranar Bai samu bacci ba kamar yadda Aysha bata rintsa ba ita ma Amatullah baccin da tayi gajere ne.






Da safe bayan ta gyarawa Ammy d'aki tayi musu breakfast Duk da cewa Ammy ta hanata Amma haka tayi wanka tayiwa Amrah domin tare suka kwana tun jiya Aysha bata nemi inda t'ake ba.





Ita ma yarinyar ganin ta samu kulawa yasa ta saki jikinta sosai da Amatullah abinka da yaro tana makale da Amrah saboda tana son yarinyar sosai.





Tun Daga lokacin Sam ya daukewa Aysha wuta kwata kwata ya fita daga sha'aninta ko kallon inda t'ake baiyi Amrah kuwa tuni ta koma wajan Ammy komi nata Amatullah keyi.





Tun abin baya damun Aysha harta fara damuwa Gashi ya haramta Mata ganin Amrah sosai jikinta yayi laushi ta rame bayan sallar isha'i toilet ta f'ada tayi wanka bayaj ta fito ta cakuda jikinta da wata shuumar Humrah wata crazy night gown ta saka komai nata ana gani babu pant bare bra.





Kitchen ta shiga ta hada masa Coppe ta nufi Bedroom dinsa dakyar ya amsa sallamar ta ajiye Coppe din tayi ta nufi kan gadon cikin nuna alamun tayi Nadama tace please Honey kayi hakuri for give lumshe oily eyes dinsa yayi domin kamshin jikinta ya fara d'aga masa hankali daurewa Kawai yake.






Mata da miji se Allah a wannan daren suka daidaita kansu aka kusan kwana ana Kashe Boss saboda bata nuna gajiyarwa taba sosai ta bashi hadin Kai ya murjeta bayan komai ya kammala tare suka shiga toilet sukayi wanka saboda Sam Irfan baya kwana da Janaba a jikin'sa.







Zaune suke a parlo suna kallo cikin nutsuwa tace Ammy ina son komawa makaranta kallon'ta Ammy tayi tace ki bari a tambayi mijinki domin Wannan umarnin sane shiru tayi bata sake cewa komai ba.






Idon'ta Yana masifar kewarsa kwana biyu bata ganshi ba daurewa Kawai take Amma tana azabtuwa ta rasa wane iri so t'ake masa.






Yau ta kasance Friday shigowa parlon yayi cikin Kakinsa na Sojoji wanda sukayi bala'in amsar jikin'sa gaba Daya suna Dining Amrah kuwa tana cikin kekenta na koyan zama.






Seda ya gama wasa da yarsa ya nufi Dining din t'ake ido tayi ta bude idon sune ya sarke cikin na juna sannu a hankali suka fara aikawa junan su wasu manyan sako wanda su kadai Kawai suka San maanar sa.







Ido Ammy ta zuba tana kallon sarautar Allah da sauri Amatullah ya zare idon'ta cikin nasa a hankali ta zame daga kujerar tana gaidashi Lafiya Kawai yace Yana maida kallon sa wajan Ammy.






Ammy Morning Mrng inji Ammy tea Amatullah ta hada masa da Chip's tura masa gabansa tayi seda ya sake kallon'ta kafin ya faraci.





Bayan ya gama Ammy tace Amatullah nason a maida ita School saboda ko Secondary bata karasaba tabbas yaji abin da Ammy tace Amma yayi kamar baiji ba.





Yanzu idan ta fita wasu maxan su dinga kalle masa Mata kenan Gaskiya bayajin zai amince. Ganin baida niyyar cewa komai ne yasa Ammy tace Allah ya bada saa








Minert✍🏻
πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—
_AKAN MIJINA_
πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—



NOT EDITED⚠




Written by
Minert✍🏻
Dedicated to
Princess Fatima Zarah






IT'S ALL ABOUT LUV AND CARINGπŸ’ž




Bismillahir Rahmanin Raheem



Pg 35&36



Bayan ya fita bai tsaya a ko Ina ba sai Turkish Office din principal din yaje suka gama ya wuce office abinsa.





Karfe biyu na Rana aka kawo masa uniform din school din set goma duk wasu abu da zata Bukata dangane da school din an kawo masa check Kawai ya Rubuta ya Mika masa.






Bayan ya tashi a Office ya nufi gida part dinsa ya wuce seda ya watsa ruwa ya shiga wajan Aysha har yanzu bata dawo a Company din'ta ba hakan yasa yayi site din Ammy Duk wajan da wurga se escort dinshi sun Sara masa cikin takun kasaita ya shigo parlon hanun'shi rike da Babbar laida.





Ammy ce kadai a parlon Zama yayi kusa da ita ya Dora kanshi kafadar'ta sha kan'shi tayi cike da kaunar tilon Dan nata tace yaya aikin dai Alhmdlh Ammy Ina Amrah tana wajan Amatullah seda gabanshi ya fadi Jin kiran sunanta da Ammy tayi mikawa Ammy laidar yayi yace ga Uniform din school din'ta Insha Allah On Monday zata fara zuwa Ss 3 suka bata sosai Ammy taji tace Allah yayi maka Albarka Ameen ya Amsa.





Mikewa yayi Yana tafiya yace ta kawomin abinci Ina Jin yunwa.





Dariya ya bawa Ammy kwalawa Amatullah Kira tayi a hankali ta fito tana sanye da wata karamar top se wando pencil tayi parking gashinta Wanda ya sauka har kafadar'ta.






Mika Mata ledar Ammy tayi tace ga kayan school dinki an gama komai Monday zaki fara zuwa kin godiya Amatullah tayi Ammy tace ki shirya ki maisa Part dinsa kamar tace aa Amma babu damar yiwa Ammy musu.







Kitchen ta shiga ta jera masa komai a karamin tray Babban hijab tasa har kasa ta nufi dakinsa ta jima a bakin kofar tana tunanin shiga a hankali ta murda handling din bakin'ta d'auke da siriyar sallama kafeta yayi da ido kamar wani tsohon maye🀣🀣






A cikin jikinta t'ake yadda idon'shi yake yawo ajiye Tray din tayi a zauna zuba masa fatan Arish ne da yaji kayan Hadi se kunun aya lumshe ido yayi lokacin da kamshi abincin ya shiga hancinsa.






Komai a darare t'ake yinsa saboda yadda kirjin'ta yake lugude bayan ta zuba masa ta d'ago Kai tace Nagode Allah ya saka da Alkhairi juyawa tayi zata fice ya riko hanun'ta t'ake ko wannan su yaji sock lokacin da hanunsu ya hadu waje daya.





Kara lumshe ido cikin ranshi yace soft skin domin hanun'ta kamar audiga tsabar laushi zaunar da ita yayi kusa dashi har kafadunsu na gogar juna.






Yace waye zaiyi serving Dina shiru tayi kamar bataji meya f'ada ba ganin batayi magana ba yasa ya janyo plate din abincin diba yayi yakai bakin'ta.





Da sauri ta rike hanun'shi tace Nakoshi girgiza Kai yayi dakyar tayi spoon biyu tace wallahi xanyi amai wani skiller smile ya sake Mata tana gefan shi harya gama cin abinci.






Bayan ya kammala ya dawo da kallon'shi gareta yace Ammy ta nuna Miki properties dinki ko daga masa Kai alamun eh ok so please bana son kawayen banza sannan kada ki Manta cewa akwai aurena a kanki abin Daya kaiki Kawai xakiyi Duk lokacin danaga ba daidai ba daga ranar kinyi sallama da Boko.






Xan kiyaye insha Allah gud gal yaja karancinta Bai bari ta koma wajan Ammy ba se wajan magrib domin Sam baya son rabuwa da ita.







MinertπŸ€ͺ

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment