Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nake ji a cikin nan da k'unci." ta fad'a tare da d'ora hannu a k'irjinta b'angaren zuciyarta.

Wani irin murmushi Salman yayi najin dad'i yayin da yake fad'a a zuciyarsa "lallai wannan so ne kuma Ummi tayi nisa, kawai dai ta kasa fad'a kamar yanda nima na kasa fad'an komai."

Da hannu ya mata alama ta zauna kusa dashi, tana zaunawa ya kalleta yace "Ummi da gaske kike fad'an maganar nan?"

Cikin kuka tace "wallahi da gaske nake yaya Salman, ba zan sake maka rashin kunya ba."

Shi kam kamar yayi dariya amma ya rik'e, cewa yayi "ok tunda kince haka na yarda, amma a bisa wani sharad'i."

"Na yarda koma wane iri ne in dai zai hana ka k'ara aure."

"Ok ba zan k'ara aure ba in dai zaki dinga jin magana ta, amma ki sani duk sanda kika min ba daidai ba to tabbas a satin nan k'anwarki zata shigo gidan nan a matsayin amaryarki."

Saida ta harareshi ta gefen ido tace "na yarda, kuma wallahi idan nayi abinda kake so kuma kace zaka k'ara aure to wallahi...." mik'ewa tayi danta had'a mashi abin karin, da sauri ya rik'e hannunta yace,

"Wallahi me?"

Saida ta nuna shi da yatsa tace "saina kashe ka, dan ba zan had'u ni da wata a kanka ba." Fak'at 😳

Wucewa tayi Salman ya bita da ido "anya yarinyar nan ba zata kashe ni ba kuwa in ina maganar auren nan?"

_Ah to koma dai miye ni dai ina daga nan_


Haka ta wuni ita d'aya a gidan jikinta yayi sauk'i sosai shi yasa ma babu wanda yazo gidan dubata saidai kiranta a waya kawai, har dare haka ta kammala 'yan aikace aikacenta kafin Salman ya shigo gidan, kai tsaye d'akinshi ya shiga yayi wanka yana fitowa ya shafa mai, tsaye yayi yana kallon kayan da zaisa kafin daga bisani ya yanke wata shawara.

"Abule, Abule, wai Abu bata jine?" Salman ne fa ke kiran Ummi haka, Ummi dake zaune falo tun kiran farko taji tasowa tayi tana fad'in "haba wallahi saina maka rashin mutunci in kana kirana da wannan sunan."

"Gani" ta fad'a a tsaye, kallonta yayi dan bai san da shigowarta ba hankalinshi na kan sak'on daya shigo wayarshi yanzu, ba tare daya kalleta ba yace "fiddo min kayan da zansa."

Kallon ba kada hankali ta bishi dashi har ta bud'a wadrob d'in ta d'auko wasu bleue noir rigar kamar singlet saidai hannuwan suna da fad'i sai dogon wando.

Aje masa tayi tana kallon wayar dake hannunshi, tashi yayi ya aje wayar dan yasa kaya, sai kawai idonta ya sauka kan chart d'in da suke da mai wannan sunan *Reine*, da sauri ta d'auki wayar tana kar'ema photon Nuseiba kallo wanda ga dukan alama yanzu ta aiko shi, a k'asa kuma ta rubuta,

__kana da girma a wajena yaya Salman, ba zan iya had'a ido da kai ba koda a photona ne._"

Jin hawaye sun taho mata ne yasa ta aje wayar tana kallonshi, kallonta yake shima kafin yace "ya dai lafiya?"

"Allah zai saka min in har kaci amana ta, kuma wallahi zanje na samu Nuseiba har gida sai naji dalilin da yasa take kula ka, azzalumai macuta kawai."

Zata fita ya rik'o hannunta tare da fad'in "ke kina hauka ne, wai mi yake damunki ne?"

Cikin b'acin rai ta fizge hannunta tace "lâche moi (sake ni)"

Tana fita d'akinta ta shiga ta fad'a saman gado ta fashe da wani kuka mai cin rai da ban tausayi.

*Kishi kenan, zama da kishiya sai dole amma idan a kayi hak'uri to komai ya kan zo ya wuce kamar bai faru ba, mu dinga saka hak'uri tare da tausar zuciyar mu da kuma addu'a, dan ba kowace mace bace zata iya hak'urin ganin ta had'a miji da wata.* _Allah kasa muyi kishi mai tsabta irin na matan Annabi (S A W)_


Yana saka kaya ya d'auki wayar yana kallon Nuseiba kafin yace "kiyi hak'uri ba zan iya juran ganin hawayenta ba, in dai har a kanki ne take shiga k'unci to daga yau ba zata sake b'ata ranta ba, ina son aurenki ne saboda kashe wata matsalata, amma idan maganar so ake to Ummi ce a cikin zuciyata dama birnin raina, bana jin wata ko wani abu kamar yanda nake jinta a cikin zuciyata dan haka daga yau komai ya k'are, ba wai zumuncin mu ba saidai daga yanzu ba zan sake maki kallon wacce nake so na aura ba, daga yanzu kin koma k'anwata kamar yanda kike a da, Ummi kuma zan ci gaba da k'ok'arin sakata farin ciki da yardar Allah."

"Dole na guji b'acin ranta in dai har a kaina take kishi haka, ban san me take ji ba amma da zan iya kwatantashi da abinda naji jiya lokacin da tace min wannan likitan ya rik'eta, to tabbas ba k'aramin b'acin rai da tashin hankali take ciki ba."

Yana fad'a ya canja sunan Nuseiba daga Reine zuwa Cousine Nuseiba kamar yanda yake a sauran numbobin 'yan uwa, d'akin Ummi ya shiga sosai ta bashi tausayi ganin ta dage tana kuka dan taji sauk'in abinda ke damunta.

Zaune yayi tare da d'agota ya d'ora kanta a k'irjinshi yana fad'in "haba Ummi duk wannan kuka dan kinga photon Nuseiba ne? amma ai ni na maki alk'awarin na fasa ko?"

D'agawa tayi daga jikinshi cikin kuka tace "yaya Salman me yasa, me yasa nake jin haka? wallahi ji nake na tsani 'yar uwata? "

Kai ya girgiza mata ya k'ara janyota ya rumgume yana cewa "shhhh, kiyi shiru kinji ya wuce ba zan sake ba"

Cewa tayi "yaya Salman ba wai na hana ka k'ara aure bane, ni kawai bana so ne ka auri kowace mace, ina ji da ina da iko a kanka to dana hana ka auren kowace mace a duniya, yafi muyi zaman mu haka koda ma za kayi ta duka na wallahi ba zan gaji ba."

Ji yayi duk ya k'ara jin haushin kanshi in dai har tana jin haka a kanshi, to miye zaisa ba zai zauna da ita ba ya kuma k'ara sonta fiye da yanda ita take sonshi.

Rarrashinta yayi tayi har tayi shiru kafin suka komo falo ta bashi abinci yaci, dare nayi kowa ya kama hanyar d'akinshi, suna kaiwa k'ofar d'akunan suka kalli juna Salman ne yayi murmushi yace,

"Kiyi bacci ba sai kin kawo min tea ba."

Shiru tayi tana kallonshi dan haka yace " kina buk'atar wani abu ne?"

Nan ma babu amsa dan haka ya matso kusa da ita yace "ko zaki kwana d'akina ne?"

Tana jin haka ta bud'a d'akinta ta shige, dariya yayi ya shiga d'akinshi shima yana fad'in "tsoro kamar farar kura, ko taya zata fuskanci daren farkonta.?"

```Wannan aiki kuma ai ya rage naka ```😍
05/03/2019 à 19:30 - Mamar Latif💃: 💑AUREN HA'DI 💑

_Samira Harouna_

_'YAN K'UNGIYATA INA JI DAKU_

```MY HEENAT, MY BK, MY SEEYA, K'AWALLIYA CEYMER, HAPSY, QUEEN BK, MY LISSA```😍❤😉

🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛

*Page*

7⃣7⃣_7⃣8⃣


Yau Ummi ita d'aya tayi break dan yau alhamis Salman na azumi, tana kammalawa ta fara sharar falo da goge goge tana cikin goge dinning Salman ya fito cikin bleue shadda, d'inki ya masa kyau sosai gashi sun dace da k'irar shi, tsaye yayi yana k'arewa Ummi kallo data sha dogon wando da k'aramar riga, sun kamata sosai kayan gashi kuwa Ummi dama dai bata da kyau na nunawa amma k'ira kam ko a mujjala za'a iya bugata, tsaf rigar ta tsaya a k'ugunta daram wata hula ce a kanta irin mai maganin sanyi sai dai tsakiyar kanta ta tsaya sai gashinta daya kwanta a bayanta.

Daf da ita ya matso yana ci gaba da kallonta, k'amshin turarenshi da Ummi taji ne yasa tayi saurin juyowa karaf idonsu suka had'u, k'asa tayi da kanta tace "ina kwana"

Yanda rabin k'irjinta ke waje wuyanta hannayenta gaba d'aya sun d'auki hankalinshi, hannunshi yasa a hankali ya shafi wuyanta har damtsenta, jin yanda yake wani latsa fatarta yasa tayi saurin janye jikinta tana kallonshi, kallon idonta yayi da suka fara tona asirin abinda ke zuciyarshi cikin wata irin murya yace,

"Ummi bana so ki sake saka irin wannan kayan a gidan nan."

Kallonshi tayi cikin mamaki tace "saboda me, me yasa zan daina? naga ko a gidan mu ina saka kayan da raina ke so bare kuma gidana."

Cikin mamaki shima ya kalleta yace "gidanki fa ki kace? inama laifin kice gidan mijinki."

"E mana gidana, domin kuwa in da babu ni ba za'ace danan gida ba, haka da baka da ni da ba za'a kiraka mai gida ba."

Gaf da ita ya matso yana mata wani shu'umin kallo yace "amma ai a zahiri ne mutane ke ganin haka, amma a bad'ini har yanzu ke k'aramar yarinya ce baki cika cikakkiyar mace ba."

Ummi kam kallon jikinta ta fara tun daga sama har k'asa sai dai bata fahimci komai ba, kallonshi tayi tace "a hakan ne ban cika cikakkiyar mace ba? ina haka dani?"

"Murmushin gefen labb'a yayi yace "cikakkiyar mace bawai tana nufin mai k'iba ko kyau ko ilimi ko iya gayunta da sauransu ba."

Rik'e k'ugu tayi tace "to kenan me yake nufi?"

Gashinta ya janyo yana wasa dashi kafin yace "zan fad'a maki ranar da kika cika babbar mace, amma ba yanzu ba dan ba zaki fahimce ni ba."

"Ka fad'a zan gane ina da fahimta sosai."

Sakin gashinta yayi ya nufi hanyar fita, da sauri Ummi tace "in dai ban cika cikakkiyar mace ba, to kaima baka cika ba..." shiru tayi saboda yanda ya juyo yana kallonta, saida ya matso kusanta yace "ban cika namiji ba kike so kice?"

Shiru tayi tana kallonshi dan haka yace "ok muje na nuna maki ni namiji ne kuma na gaske."

Hannunta ya kama zuwa cikin d'akinta, tana ganin sun doshi d'akin ta fara k'ok'arin kwace hannunta, rik'eta yayi sosai yace "muje saina nuna maki"


Zubewa tayi k'asa tana bille bille tana kuka tana fad'in "a'a wallahi bana so dan Allah kayi hak'uri wallahi kai namiji k'arya nake dama."

Ganin zata b'ata masa lokaci yasa ya kimkimeta sai d'akinta ya zubdata akan gado, ganin yanda take kuka tana bashi hak'uri yasa ya rik'e dariyarshi wutar d'akin ya kashe tare da dawowa wajenta yana kallonta yana cire ma b'allan rigarshi yana fad'in "to wai miye na kukan? naga ke zaki zama babbar mace ni kuma zan zama babban yaro."

Cikin kuka Ummi tace "ni d'in banza wallahi bana son na zama dan Allah ka k'yaleni wallahi cikina ke ciwo ga baya na ma rik'ewa yake, ko kana so olcerta ta tashi ne?

Baya ya bata dan ya samu damar dariya tare da cire rigarshi har da singlet d'in duka ya aje a gefen gado sannan ya mik'a mata hannu yana fad'in "zo nan"

Da gudu ta nufi toilet dan neman tsira, da hanzarinshi shima ya bita tare da rik'ota, baiyi wata wata ba wajen wurgata saman gado yayo kanta gadan gadan, runfa ya mata da k'irjinshi yana k'ok'arin had'a bakinsu waje d'aya, ganin idon Ummi duk sun canja bakinta bud'e tana k'ok'arin maida numfashi amma ta kasa dan ji take kamar ya danne mata ma shak'ar iska ne.

D'agata yayi ya koma gefe ya kwanta yana dariya yana fad'in "matsoraciyar kawai, ashe bakinki na rufuwa, ashe akwai lokacin da kike rasa abin fad'a.?"

Ummi na tashi k'ofa ta nufa ta kunna wutar d'akin, juyowa tayi tana kallonshi tsaki ta masa tana shirin fita yace "zo nan."

Daga jin amon muryarsa babu wasa dan haka ta dawo tayi tsaye tana kallonshi har yanzu kuma kwance yake, "wa kike wa tsaki?"

Shiru tayi ta kasa magana dan haka yace "ok kimin tsaki san ranki kafin amaryata ta shigo gidan."

Tana jin haka ta zube k'asa tace "dan Allah kayi hak'uri wallahi ba zan sake ba daga yau."

Ba tare daya kalleta ba yace "to naji, tashi ki fita ki barni zan kwanta a nan."

Tab'e baki tayi ta yunk'ura zata tashi idonta suka sauka akan wani abu, gabanta ne ya fad'i sosai mik'ewa tayi tare da nuna wajen tace "yaya Salman miye wannan, meya ji maka ciwo anan wurin?"

Da sauri ya dafe wurin tare da tashi zaune amma bai tanka taba, a hankali Ummi tace "yaya Salman dan Allah miya ji maka ciwo a wurin nan mai hatsari, ko kaima kayi k'in ji irin na yara?"

"Ke bana san wannan tambayar kinji ko,wuce kije in da zaki"

Wucewa tayi jiki a sanyaye tana tunanin wannan wane irin ganganci ne ciwo a kusa da mara ko tsoro ma baya ji, to wai mima yaji masa ciwon ne?"

Tashi yayi yaje gaban madubi yana k'ara kallon ciwon dake k'asan cibiyarshi wanda shekara d'aya kenan daya same shi, kayanshi yasa ya fito daga d'akin tana zaune yace "saina dawo."

"A dawo lafiya" ta fad'a a takaice shi kuma ya fice daga gidan.


Tana zaune rana ta fito sosai taji ana bubbuga k'ofar gida, cike da mamaki ta saka hijab ta fito ta bud'e tana kallon mai buga k'ofar mamaki k'arara a fuskarta, MANNIR ne tare da Alhaji gefe ta matsa tana fad'in "ku shigo ciki".

Ciki suka shiga Ummi har yanzu jikinta a sanyaye yake dan bata san da wacce Alhaji ya zo ba, wuri suka samu suka zauna saida suka gaisa da Mannir sannan ta kalli Alhaji a tsorace tace "ina kwana"

"Lafiya lau, kun tashi lafiya?"

"Lafiya lau muke, yasu Hajia suna lafiya?"

"Lafiya lau suke, amma basu san zan zo nan ba"

Shiru Ummi tayi tana sauraran abinda zai fad'a, shiru ne ya ratsa wajen na dak'ik'u shabiyar kafin Alhaji yayi gyaran murya yace "Ummi na san kinyi mamakin ganina a gidan nan ko?"

Cike da ladabi ta jinjina kai dan haka yace "ba abun mamaki bane, nazo ne dan naga jikinki nima, sannan na shaida maki na daina fushi dake yanzu."

Murmushi ne ya bayyana a fuskarta tana fad'in "na gode sosai Kakana"

Da hannu ya mata alama ta matso kusa dashi tana zuwa kanta ta d'ora akan gwiwarshi tana hawaye tace "Alhaji ka yafe min, wallahi ranar ma babu abinda ya faru kawai dai...." bai bari ta k'arasa ba yace "ya isa haka Ummi, nima nayi kuskure matakin dana d'auka akan ki bai kamata ba ko kad'an, domin kuwa na sanki farin sani dan rayuwar da ki kayi a gidana, tafi wacce ki kayi a gidanku yawa kiyi hak'uri kinji ko."


Haka suka jima suna hira kafin suka tashi tafiya Alhaji ya k'ara mata nasiha akan ta kula da mijinta sannan ta zama mai ladabi da biyayya ga mijinta.


Ummi taji dad'in yinin nan fiye da sauran yinin da 'yan uwa ke zuwa mata, haka ta wuni cikin farin ciki da annashuwa.


*A GURGUJE*
11/03/2019 à 17:51 - Mamar Latif💃: 💑AUREN HA'DI 💑

_Samira Harouna_

🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛

*Page*


7⃣9⃣-8⃣0⃣


Haka zaman nasu yake tafiya ba yabo ba fallasa, har yanzu babu abinda ya canja daga zaman nasu sai dai abu d'aya shine yanzu Ummi tana yin duk abinda Salman ya sakata, har yanzu Ummi ba tada sarau dan kuwa ko yanzu Salman yace mata kule to kai tsaye za tace masa cas.

Amma tana mayar masa da yace zaiyi amarya kuma zata fara bashi hak'uri, haka Salman ya samu yana wasa da Ummi son ransa ta hanyar k'ara aure, kullum soyayyar junansu ce ke k'ara k'aruwa a tsakaninku sai dai har yanzu kowa baya yarda d'an uwansa ya fahimta, haka suke zaune sai dai wani lokaci daga kallon da suke aikawa junansu ya kan tona sirrin zuciyoyinsu.

Salman yayi niyyar ba zai fara fad'awa Ummi kalmar so ba,saboda sanin Ummi da yayi zata iya watsa masa k'asa a ido idan ya fad'a mata, shi kuma a yanda yake jinta a zuciyarshi dama sauran sassan jikinshi baya tunanin zai iya jurar rasata ko jin rashin amincewarta daga bakinta.

Ummi ma haka ta zab'i ta b'oye ta barwa kanta ita kad'ai ba tare data fad'a masa ba, tunda ta fahimci bata gabansa ko kad'an shi yasa ma zata ci gaba da b'oyewa har lokacin da shima zai fara jin irin abinda take ji sannan ya fad'a mata.



A haka kuma warin auren su Ummi suke ci gaba da kula da cikinsu, Khairat, Nadiya suna fama da laulayi mai tsanani su Jawahir kuma alhamdulillah za'a ce.

Har yau har gobe idan Ummi ta kira La Mama dan su gaisa, sai La Mama ta k'ara jaddada mata akan ta kula da mijinta sannan saita fad'a mata wani abu da zata k'aru da shi ko dan rayuwar gaba.

*WATA BIYU*

A lokacin ne su Jawahir suka fara shirye shiryen komawa makaranta, in da Ummi ita ma ta nemi izinin Salman akan ya barta ta koma makaranta, sam Salman yak'i amincewa yace sai tayi hankali sannan zata fara fita ma daga gidan.


Ummi tayi kuka tayi magiya tayi rarrashi amma sam yak'i yarda, dole Ummi ta hak'ura ta shafa ma kanta lafiya, yayin da su Jawahir suka fara karatu sai dai suma suna kewar Ummi sosai duk da tana gaba dasu a ajin, amma dai koba komai zasu dinga had'uwa.

Tun lokacin sai Ummi ta sauya gaba d'aya ta daina walwala ba kamar da ba, yanzu duk abinda Salman zai mata bata kula shi sai dai ta bishi da ido kawai, hakan ba k'aramin tab'a Salman yayi ba dan kuwa farin cikinta shine nashi, amma yanzu gashi ta daina gaba d'aya, dole Salman ya nemi mafita daga matsalar dan a ganinshi koda ace ba abinda yake da iko a kanshi bane ai zaiyi k'ok'arin ganin ya sata farin ciki, bare kuma yana da iko.


Ummi na zaune a falo tana kallo tare da uban tagumin data rabka Salman ya shigo da sallama, kallo d'aya ta masa ta kau da kanta tana amsa sallamar, zaune yayi kusanta yana kallonta, ledar dake hannunsa ya mik'a mata ta karb'a tana kallonsa ta aje ledar dan a tunaninta irin kayan k'walam d'in da yake siyo mata ne.

Kallonta yayi yace "miye haka kuma? ya za'a baki abu amma ba zaki duba ba ki gani, kawai saiki aje."

Ko kallonshi ba tayi ba ta d'auki ledar ta fara dubawa, take farin ciki ya lullub'eta saboda ganin d'inkakken tenue (uniform) da sauran kayan makaranta da duk abun da d'an makaranta zai buk'ata.

Fiddo kayan tayi ta mik'e tsaye tana gwadasu a jikinta bak'ak'e (tenue 'yan lycée ne na moufida), riga iya gwiwa wacce ta bud'e sosai da gajerun hannuwa sai dogon wando mai forme d'in slim da kuma hijab daya wuce rigar, sannan da nik'ab, cikin mamaki tace,

"Wannan fa yaya Salman na miye?"

Murmushi yayi yana kallon tsantsar farin cikin dake kan fuskarta yace "naki ne"

Bud'a baki tayi cike da farin ciki tace "wow, yaya Salman amma naji dad'i sosai, hakan kenan na nufin zan koma makaranta nima?"

Da ido kawai ya mata alamar Eh, cike da farin ciki ta k'araso wajenshi ta zube k'asa tana fad'in,

"Kai amma yaya Salman naji dad'i sosai, Allah ya saka maka da alkairi, Allah ya k'ara bud'i na alkairi, Allah bar min kai, Allah ya saka maka son...."shiru tayi ta kasa k'arasawa.

Mamaki ne ya bayyana a fuskarshi tare da fad'in "ya saka min son mi?" kai kawai ta girgiza alamar ba komai, mik'ewa yayi ya nufi d'akinshi ita ma haka, suna kaiwa k'ofar d'akin Ummi tace,

"Yaya Salman yaushe zan fara tafiya?"

"Gobe mana"ya fad'a yana bud'a d'akinshi, murmushi tayi wanda ya bayyana hak'oranta tare da dinple d'inta sosai, Salman dake k'ok'arin shiga d'akinshi ne tsaya tare da dawowa yana kallonta, a hankali yasa d'an yatsarshi akan dinple d'inta ya latsa, ita kam k'ura mashi ido tayi tana kallo yayin da shi kuma kasa had'a ido da ita saboda tartsatsin da yake ji idan yana kallon idonta ma abota girma da fari.

Bai bar latsa kumatunta ba yace "Ummi na barki ki koma makaranta ne saboda tabbacin da nake da akan ki, na san zaki kula da kanki sannan zaki karemin mutunci na dama mutuncinki."

Ajiyar zuciya ta sauke tana kallon cikin idonshi tace "insha Allah yayana, ba zan tab'a baka kunya ba, sannan ba zanyi abinda zai shafi mutuncin ku ba, zanyi iya bakin k'ok'arina wajen ganin na kare maku hakk'inku da yake kaina musamman ma kai."

Murmushin jin dad'i yayi yace "me yasa musamman ma ni?"

K'asa tayi da idonta cikin jin kunya tace "saboda kai mijina ne." tana fad'a ta k'arasa shigewa d'aki tana dariya, Salman ma haka d'aki ya shiga yana jin wani sanyi na ratsashi yana ji ina ma ace Ummi ta fad'a mashi kalmar so a matsayin godiyar abinda ya mata.


Tun asuba Ummi da tayi sallah bata kwanta ba, tana gama had'a abinda kari ta d'an gyara abinda zata gyara a d'akinta da falo dama cuisine, tana kammalawa ta shiga wanka tana fitowa tsaf ta shirya cikin tenue d'inta.

Jakarta ta d'auko da hijab da nik'ab ta fito falo ta ajesu saman kujera sannan ta nufi d'akin Salman dan ta tashe shi, da sallama ta shiga amma shiru bai amsa ba alamar bacci yake, saida ta k'arasa har gabanshi ta k'ura mashi ido tana kallo yana baccinshi cikin kwanciyar hankali.

Rumgume hannayenta tayi a bayanta a hankali tace "ina sonka yaya Salman, sai dai ba zan iya fad'a maka ba, dan na san kai baka sona kuma ba zaka soni ba, amma zan ci gaba da jiran lokaci na san zai zo."

Lek'a fuskarshi tayi taga sosai yake baccinshi dan haka ta sunkuya daf da k'eyarshi ta sumbata, mik'ewa tayi tare da zura hannunta ta rufe hancinshi, da sauri ya juyo da kanshi yana bud'a idonshi yana ganin Ummi ya tashi zaune yana ci gaba da kallonta, murmushi kawai take masa kafin yace,

"Wannnan kuma wane irin tayar da mutum daga bacci ne?"

D'aga kafad'u tayi tare da d'aga gira sama alamar ba magana, saukowa yayi daga kan gadon yana fad'in "saina ji kamar an sumbace ni a kaina ko?"

Bud'e baki tayi cike da mamaki, lokaci d'aya kuma tayi k'asa da kanta tana wuru wuru da ido, gaf da ita ya matso yace "kece ko, ko dai akwai abinda kike b'oyewa ne ban sani ba?"

D'ago ido tayi suka kalli juna, ja tayi da baya tana fad'in "haba dai sumbata fa? sai kace wani jariri."

Toilet ya nufa yana fad'in "banyi mamaki ba dan kince haka, amma ki sani wani lokacin ma miji yafi jariri buk'atar kulawa."

Kallonshi tayi tace "to, ni dai na san ana cewa namiji kamar k'aramin yaro ne, duk in da kayi dashi can zaiyi."

Tsaye yayi yana kallonta kafin yace "kuma ke kin yarda da abinda aka fad'a d'in?"

Murmushi tayi tace "me zai hana ko, tunda mune ke jan ragamar."

Ganin ya tun karota yasa tayi saurin ja da baya tana fad'in "dan Allah ni dai kaje ka shirya kar nayi late a zuwan farko."

Sai lokacin ya lura da kayan dake jikinta dan haka yace "oh, hakane fa, ok ki bani 5 minute ina zuwa."

Kallon agogon dake gefe gadon tayi tace "ah bon, 5 minute? Ok je t'atend."

Ciki ya shige ita kuma ta dawo falo ta zauna jiranshi, kallon agogo take lokaci na tafiya amma Salman shiru bai fito ba, ido Ummi ta fiddo tare da mik'ewa tsaye tana dafe da k'irjinta ganin 07:45, kukan shagwab'a ta saka tana fad'in,

"Shikenan zuwan farko zan fara da late."

Hijabinta ta saka ta goya jakarta ta d'aura nik'ab, d'akin Salman ta nufa sai kuma suka ci karo da juna, ido ya fiddo waje yana k'are mata kallo sama da k'asa kafin ya nunata da hannu yace "ke kuma wannan shiga haka bak'a k'irin kamar wata 'yar wuta."

Turo baki tayi duk da baya gani sannan tace "yaya Salman ka dubi lokaci fa ya wuce, wallahi nayi retard."

Lokaci ya duba ya k'ara zaro ido yana fad'in "kai kai kai, lallai kam, to wuce muje ina fatan dai kin karya?"

"Ni ban karya ba, kawai idan naje naci wani abu."

Wucewa sukayi bayan ta rufe d'akin, tunda suka kama hanya tayi shiru tana kallon gari, Salman ne ya kalleta yace "ina fatan dai ba zaki cire nik'ab d'innan ba idan kinje can?"

"Haba yaya Salman dole zan cire mana dan nasha iska, lokacin zafi ne gashi yanzu ba'a ruwa sosai."

Hararanta yayi yace "bana so, karki bud'e fuskarki kowa ya gani."

"Amma yaya Salman akwai takura fa, kai baka san nik'ab ba wallahi tana hana mutum kyakyawan shed'a."

Kallonta yayi irin ba wasanan yace "wallahi idan naji labarin kin cireta, to daga ranar bake ba k'ara

Please Login or Register in order to submit comment