Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Oummi da hannu daya ya kalli Alhaji yace" Dan Allah ayi hakuri ba zata saké ba Insha Allahu" mikewa Alhaji yayi tsaye yace" k'warai ba zata saké ba kamar yanda ba zata k'ara koda Awa daya ba a gidan nan ba" kallan ta yayi ya daka mata tsawa" wuce mu tafi" raba ido tayi dan bata san inda zata wuce ba duk ta rud'e" zaki wuce ko sai'' na sa ya d'auko min ke?" da sauri ta d'auki hijabinta jiki na rawa duk zugi ta keji a jikinta saïda ta kai bakin k'ofar d'akin ta juya ta kalli su Abba cikin kuka tace" Abba ku yafemin dan Allah, La mamma kiyi hakuri" da sauri ta bar wajen suna fita K'ofar gida Alhaji yace ma Salman " d'auko motar ka na kai ta gidan ta" mamaki yasa Salman yin tsaye amma daya mashi tsawa saiya wuce babu shiri ya d'auko mota, basu tsaya ko ina ba sai sabon gidan Salman da duka jiya ne aka kammala gyaran shi.
Yana iza k'eyar ta yace Salman ya maida shi gida suna tafiya Ummi ta fad'i a tsakar falon ta fashe da kuka tare da k'ara kamar ta kashe kanta take ji.
27/02/2019 à 17:30 - Mamar Latif💃: 💑 AUREN HA'DI 💑

_Samira Harouna_

🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_ 🤜🤛

*page*


2⃣1⃣-2⃣2⃣



Koda Salman ya shigo ya sameta nan bai tankata ba ya wuce d'akin shi, Oummi kam bata farka ba sai da aka gama sallah asuba tana tashi zaune tayi akan kujera tana tinanin inda zatayi alwala tayi sallah, zazzab'i ne ruf ya rufe ta da k'yar ta fito farfajiyar gidan ta samu panpo tayi alwala ta dawo falo tayi sallah ta koma ta zauna.

Har saida gari ya waye sannan Salman ya shigo gidan daga massalaci lokacin har bacci ya saké d'aukar ta saman kujera, kallanta yayi ya kalli agogon dake mak'ale a bango dab da ita yazo ya kama kafar ta ya fizgo har saida ta fad'o k'asa, a tsora ta bud'e ido ta sauke a kanshi, gyara zamanta tayi cikin muryar da tasha kuka tace" miye haka dan Allah?" cikin fad'a yace" Dallah malama tashi kiyi sallah kin wani saki baki kina bacci har safiya tayi" hararan shi ta murgud'a baki tace" amma ai nayi sallah" tsayuwar sa ya gyara yace" to naji abin karyawa fa, ko shima harkin gama?" tashi tayi tsaye tace" haba dan Allah wane irin abin karyawa kuma, ni ban dafa ba kuma gaskiya ba zan'iya ba" tana rufe baki ya kama kunnenta ya murd'e yace" karki saké bari saina maki magana akan abin karyawa, ki tashi kiyi abinda nasa ki idan kin gama zan fada komai a kaina dan bana san shirme" ganin batada niyar tashi yasa ya d'aga carbin shi zai tsula mata da gudu ta shiga cuisine kin ta fara had'a abin kari.

Dak'yar ta kammala sabida zazzab'i gashi duk jikin ta ciwo yake sabida dukan da tasha, falo ta same shi zaune cikin shiri a jiyewa tayi ta juya zata koma cuisine tunda har yanzu bai bata d'aki ba," ke zo nan" a hankali ta dawo zaune tayi hankalin ta a tv, cikin b'acin ray yace" miye wannan kika dafa?" wani banzan kallo ta masa tace" aw kai bakasan ko miye wannan ba?" tassss ya kwashe ta da mari yana fad'in" ke dan kin raina ni na zauna ina jiran abinci tsawon minti ashiri, amma a k'arshe ki kawomin wannan abar a matsayin abinda zanci na fita, to bari kiji ni ba haka nake kayana ba komai ina yinshi da tsari ki buda kunnuwanki kiji abinda zan fad'a maki" ganin gaba d'aya hankalin ta na kan tv yasa ranshi ya k'ara b'acewa da k'arfi ya fizgota ta fad'o k'asa kusa da shi yana kallan idanta yace" ki nutsu idan bâ haka ba wallahi jikin ki zai dinga fad'a maki kinji na fad'a maki sakarya kawai."

Kuka ta fara haka shi kuma ya fara zana mata sharad'an shi da k'a'idojin shi kamar dai....,

" ki tabbatar kowace safiya ina samun abun Kari na da missalin k'arfe 08:00, 08:01 tofa bazan d'aga maki k'afa ba, sannan k'arfe 14:00 na rana ki tabbatar abinci ya kammala kafin na shigo, haka zalika da k'arfe 20:30 na dare kiyi k'ok'arin gamawa kafin minti d'aya ya hau sama"

"Sannan ya zama wajibi gareki da kin idar da sallah asuba kije har d'aki na ki gaishe ni, sannan kowane dare kafin ki kwanta bacci sai kin tabbatar kin kaimin Tea mai kayan kamshi a ciki sannan ki kwanta."

"Sannan ba komai nake ci ba, da safe inasan karyawa da abu mai nauhi,da rana kuma inasan abu mai romo,da daddare kuma zaki iya kawomin komai naci amma banda kifi,Kwaï,tuwo,wake, bana cin su da dare."

"Sannan kowane sati ina azumin litinin da alhamis, dan haka kowane bud'a baki ina bukatar salade, lemon zob'o,kayan marmari, haka kuma duk juma'a zaki dinga dama min fura da rana ina sha, sannan kowace juma'a ina yanka dabba sabida sadaka dan haka zaki dinga sarrafashi ta hanyar data dace sai ayi sadakar, sannan kowace asabar ina gayyatar abokaina suna zuwa muci abinci dan haka zaki dinga dafa abinci mai yawa."

"Sannan kowace juma'a zaki dinga wanke min kaya na kanana sannan ki gogemin su,sannan kowace safiya idan nafita dole zaki gyaramin d'aki na kafin na dawo, wannan shine tsari na kibi ki zauna lafiya, ki k'i bi kisha wahala dan nidai ba zan gaji da dukan ki ba, sannan ki d'auke wannan abar dan bata daga cikin tsari na wannan saike jaka."

Wani kallo ta watsa mashi tace" jaka kuma, ni d'in?" e ke d'in koba jakar bace?" kauda da kai tayi gefe ba tare da yanda zai jita ba tace" jakuna dai" mikika ce?" girgiza kai tayi ta mike tsaye tace" to Malam naji dokokin ka amma kasani ba zan'iya ko d'aya ba, kaji mutum sai kace wani shiya haifeni ko ya hallice ni da zaka zauna ka zana min dokoki" sa'ar cabko hijabinta yayi ya zaunar da ita ya rik'o hannayenta duka biyu, saidai zafin da yaji a jikinta na zazzab'i yasa yace" kar Allah yasa kiyi ko daya d'aya daga cikin abubuwan da na zayyana maki kigani saina lahira yafiki jindadi shashasha kawai mai k'wak'walwar kifi." tsallaka ta yayi ya wuce da sauri tace" to ina zan zauna ni kuma, ko d'akin naka zan dinga kwana?" juyowa yayi yasa hannu aljihu ya ciro makullin ya jefa mata, tayi saurin cab'ewa kamar masu jira a tare suka aikama juna harara Oummi harda tukwicin murgud'a baki, wucewa yayi ya barta nan, d'akin ta ta shiga dak'yar tayi wanka sabida ciwon dake jikinta ta shirya cikin riga da wando ta kwanta kuka ta dinga rerawa sabida takaicin abinda aka mata gashi shi kuma ba imani ne da shi ba.

_Tofa wannan zama_
27/02/2019 à 17:30 - Mamar Latif💃: 💑 AUREN HA'DI 💑

Samira Harouna

```Dedecated to My Meelat``` 😘

🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
( _Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛


*Page*

2⃣3⃣-2⃣4⃣



Komawa tayi ta kwanta dan ko zai kasheta ba zata yi abinda yace ba, yana fita gidan su ya nufa ya fad'awa Mahaifiyar shi duk abinda ya faru a daren jiya, ta tausaya ma Ummi, ta kuma k'ara jaddada mashi ya rik'eta amana, d'akin shi ya shiga ya ida harhad'a sauran kayan shi yace zai aiko azo a d'aukar masa.


Haka ma daya shiga gidan su Ummi ya gaishe da su La mamma ta had'a mata sauran kayan ta yace zai aiko a d'auka anjima.


Tana bacci a d'aki taji bugun k'ofa, cikin magagin bacci ta taso ta bud'e, matashin saurayi ne ya kawo kayan su, karb'a tayi ta koma d'akin nata tai masu wajen zama, nashi kuma ta bar su nan kafin ya dawo, kwance tayi tana tunani shikenan ta rabu da gida kenan har abada sai in taje da ziyara, tunda take bata taba jin labarin wacce aka kai gidan miji kamar ita ba, kuka ne ya kwace mata ta nayi tana ajiyar zuciya har bacci ya saké d'aukar ta.


Ummi na gama sallah azahar ta shiga cuisine ta dafa indomie, badan ita take so ta ci ba saidan k'iwa, tana ci ta koma ta kwanta nan saman kujerar bacci ya saké d'aukar ta, ruwa da taji an watsa mata yasa ta tashi a tsora ce tana piki piki da ido, ganin Salman yasa ta fashe da kuka tana fad'in" ni dama nasani wallahi dan ka dinga min mugunta ne yasa ka aure ni, haka kawai ina zaman zama na an wani had'a ni da kai, gashi kana neman kashe ni" tsaki yayi kafin ya zauna idonshi a tv yace "kawo min abinci na," wata harara ta galla masa tare da juya baki tace "ban dafa ba, ai dama na fad'a maka ba bauta nazo yi ba."
Mik'ewar da tayi tsaye tana ta kakkabar riga, hakan yasa ya tashi tsaye cikin had'e rai yace "durk'usa" wani kallo ta mashi, hakan yasa ya d'auke ta da mari yana k'ara maimaitawa "ki durk'usa nace" zubewa tayi tana kuka ci gaba yayi da fad'in "ki saurare ni da kyau kiji, karki saké bari na dawo gidan nan ban samu abinci shirye ba, sannan daga yanzu karki sake tashi tsaye in har ina zaune, ko ina zaune ke ma kina zaune, dole ki girmama ni a matsayi na na mijin ki kuma wanda yake gaba da ke, kina jina.?"


Cikin turo baki ta d'aga kai, zaune yayi yana kallonta yace "ki tabbata Kin kawo min ordevre nan da minti talatin, idan kuma ba haka ba to rai zai b'ace," ganin babu alamar wasa a al'amarin yasa ta tashi dan gabatar da abinda yace d'in, awa d'aya ya d'auke ta kafin ta kammala ta kawo masa ta koma ta d'auko ruwa ta aje masa, tana turo baki ta koma d'akin ta tana gunaguni.

Yana ida wa ya mik'e tsaye yana k'walla mata kira "ke! ke!! ke!! ko ba kiji ne.?"

Cikin gadara ta fito tayi tsaye tana kallon k'ofa, bugu ya kai mata a kai yana fad'in "me na gaya maki yanzu?" kamar zata fashe haka tana ji tana gani ta durk'usa gaban shi yana fad'in "saura ki kwanta bacci tsiya ki k'iyin abinda na saki, wallahi da kinga k'ask'anci a gidan nan dan sai na k'arya ki" kallan shi tayi tace "wai yaya Salman me kake nufi dani ne, wannan fa ba daidai kake yi ba, haka kawai kayi ta wani samin doka kamar kai ka halicce ni ko kuma siyo ni kayi. ?"
Waige waige da ya shiga yi ne na neman abun bugu yasa ta arta a guje ta shige d'aki ta Kulle tana fad'in "wallahi saidai ka kashe ni amma ba zanyi ba, haka kawai daga zuwa na zaka wani ce wai abokanan ka zasu zo dan bak'ar jaraba."
Jin abinda take fad'a ya santa farin sani ba zata yi bâ, dan haka ya fita ana idar da sallah la'asar ya dawo gidan ya sata aikin dole hannun shi rik'e da tsumagiya, harta gama aikin tana kuka shiko ko a jikin shi tunda ta mashi abinda ya ke so wannan ba matsalar shi ba ce ko kukan jini zata yi.
Tana idar da sallah isha'i tayi wanka ta shirya cikin riga da wando na bacci tunda babu wani abun daya rage mata daya wuce ta kwanta tayi kuka bacci ya d'auke ta, Salman ne ya k'wank'wasa k'ofar d'akin a hankali ta bud'e tana kallan shi tace" ya dai Malam?" tun daga sama har k'asa ya kalleta kafin yace "ki fito ku gaisa, amma ki sanyo hijjab." Wuce wa yayi ya barta ita ma ta koma ciki ta d'auko hijjab tasa sannan ta fito.

Oummi ta d'auka wasu bak'i ne ashe ma su Khamis ne da sauran y'an uwan nasu, cikin farin ciki suka gaisa Oummi ta zuba masu abinci ta aje a gaban kowan ne, Salman ta zuba ma tana dariyar mugunta da gangan ta zuba masa abincin a jiki, da sauri ya mik'e yana fad'in "ke! ke!! wai ke wacce irin sakarya ce baki gani ne?" juya baki tayi ta wuce tana rera waka ta barshi nan, hakuri Khamis ya bashi suka ci gaba da cin abinci suna hira cikin nishad'i.




_Yan Uwa ance tuna baya shine rok'o, amma ance waiwaye Adon tafiya_
27/02/2019 à 17:30 - Mamar Latif💃: 💑 AUREN HA'DI 💑

_Samira Harouna_

🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S* _
( _Gidan zaman lafiya da_ _amana_ insha Allah)_ 🤜🤛

*Page*

2⃣5⃣-2⃣6⃣


*Alhaji Usman mai Dala* Tshoho mai ran k'arfe haka jikokin shi suke kiran shi wani lokacin, ya nada mata hud'u, *_Hajia Salamatou_ _Hajia_ Zeinab* *Hajia Hawa'ou Hajia* *Mariya* , ya nada yaya ashirin da takwas jikoki da dama, mutum ne mai kakkausan ra'ayi mai tilasta iyalen shi akan duk wani abu da yake so koda basu san shi, ya d'auki turbar had'a tsakanin yayan shi da yayan yan uwa aure dan k'arfafa zumunci, duka yaran sa babu wanda ko wacce ta kawo zabinta duka *AUREN HA'DI* ya masu.

Zaman da matan shi suke sai san barka zama ne da kowace take girmama abokiyar zamanta, sabida tsari da tarbiyar gidan yasa kowane yaro bai san ainahin wacece ta haife shi ba, kowa mama ce kuma kowace tana d'aukar d'an yar uwar ta amatsayin d'anta, da haka ne Alhaji Hamidu ya saka ma yar shi sunan Zeinab duk da bâ ita ta haife shi ba.

Ba iya nan abin ya tsaya ba har jikoki haka yake tsitar su da dai daya yana had'a su aure, sannan auren kaka manu kamar auren zobe ne babu saki saidai ya yarda duk wanda aka ma ba daidai ba ya kawo kara, amma ko yaji kayi to take za'a d'ora maka kayan ka aka ka koma inda ka fito.

Sabida rik'o da addini yasa babu d'à ko jika da ya kai shekara goma sha takwas ba tare da ya aura da shi ba, sai Oummi tayi wannan sa'ar sabida k'wak'walwa da Allah ya mata harta sauke Alkur'ani ta nada shekara goma sha hud'u sannan ta samu( BEPC) ta nada shekara goma sha shida, hakan yasa ya barta ta ci gaba da karatun Alkur'ani harta samu harda lokacin ta nada shekara goma sha takwas, Oummi dai ba wata kyakyawar yarinya bace face abu biyu da Allah ya bata, jar fata da manyan ido masu kyan gani sai dinple wanda ko d'umi take yake k'ara mata Kyaou.

Salman shi ne na farko a duka iyalen da kaka manu ya fi so, dan haka yake daga mashi k'afa harya haura shekarun da ya ke ma mazan aure, amma ba dan yana so ba, dama yana cewa idan lokaci yayi zai bashi mamaki to gashi ya mashi aure babu shiri.


_Kwana hud'u kafin d'aurin_
_auren___ *Salman da Oummi*


~Ku ja muje👌~
27/02/2019 à 17:31 - Mamar Latif💃: 💑 AUREN HA'DI 💑

_Samira Harouna_

_Cette page ce pour toi mon macho *Meelat AHK,* tu auras la bénédiction da Dieu insha, que Dieu te bénisse. Bizou_ 😘

```dedecated to```

🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛

*Page*

2⃣7⃣-2⃣8⃣


Kamar yanda ya zama al'adar gidan yake idan ya rage saura sati d'aya a d'aura aure to amare su kan dawo da zama gidan Alhaji har a d'aura auren.

Ummi ma ta dawo tare da amaren dan bâ zata iya zama babu su ba sune k'awayenta ita ce k'awarsu kuma yan uwan juna, yaou tunda safe suke takura Ummi akan taje ta karb'o sauran dinkin su daya rage amma sabida san jiki irin nata taki tafiya har saida marece yayi ta fara shirin tafiya amma kuma hajia Babba tace ba zata ba tunda babu wanda zai kaita kuma Alhaji ya hana su shiga adaidaita dan haka ta zauna jiran Allah ya kawo wanda zai kaita.

Zaune take tana jiran taga wanda zai shigo, kwatsam Khamis da Salman suka shigo cikin farin ciki suna hira,saida suka gaishe da su hajia suka fito zasu tafi hajia Babba tace" yaran albarka ina zaku haka?" Khamis ne yace" hajia yadai ko ba kisan mu fita ne?" tsaki tayi tace" kai tafi can ina ruwana da ku dan kun fita, wace uwar zaku bani idan kuna gidan ma, ina so inji inda zaku ne dan ku biyamin da wannan yarinyar" to ina zataje ita?" wajen tailleur kin su karb'o sauran dinkin su" to ai ba damuwa dama wajen aski zamuje yanzu, taso muje Ummi" Salman ne yace" kaga karfa ka d'auko mana yarinyar nan kasan yanzu raina zai b'ace" kafad'ar shi ya dafa yace" haba karka damu wannan fa k'anwarka ce" maida kallanshi yayi ga Ummi yace" taso muje".

Haka suka d'auki hanya Khamis da Ummi nata hirar su, Salman kuma ko tanke bai kula su ba har suka isa wajen, ta samu ana cikin dinke na k'arshe dan haka ta zauna ta jira Khamis kuma yace Salman ya kaishi wajen askin saiya dawo ya d'auketa, haka kuwa akayi ya dawo d'aukar Ummi amma na second d'aya bai jira ba haka ya fara zuk'a mata oder dole ta fito a hargitse tana saka kayan a leda ta shiga mota suka wuce, suna bisa hanya hadari ya taso aka fara iska gari yayi jawur harda baki ga k'ura da k'yar kake ganin gaban ka.

Salman ne yayi tsaki yana fad'in" wannan jaraba har yaoushe da irinta, gashi kinja min na rasa aski sabida bakin halinki kod'an saurayi ma ba kida shi wanda zai maki anfani idan irin haka ta taso, murgud'a baki tayi tace" e d'in banada ai kai naga kanada budurwar, kuma duk bakin halin mutum ai baya rasa massoyi saidai in hali baizo d'aya ba" da k'arfi yasa hannu ya bige bakin Yayana fad'in" yimun shiru kona taka ki yanzun nan marar kunyar banza" rufe baki tayi tace" wallahi saidai mu taka juna, haka kawai zaka takuramin" cikin d'aga murya yace" ke ni kike fad'awa haka, Allah saina sauke ki a nan naga abinda zai faru" cike da tsiwa Ummi tace" yo ka sauke ni mana saime inada wanda zai maida ni idan ma ka sauke ni" OK haka kika ce, to sauka ya fad'a lokacin da yayi parking kamar wasa ya sauke Ummi a nan ba tare da wani tinani ba, ganin yanda gari yake yasa har saida tayi kuka sannan ta matse kayanta ta d'auki hanya a k'afa.

Tafe take tana share hawaye tana tinanin abinda zata ma Salman idan taje gida, oder taji Daga bayanta wata tsaleliyar mota ce ke biyar ta amma bata tsaya ba har saida ya tare gabanta sannan ta tsaya, wani santalelen saurayi ne ya fito daga ciki yana fad'in" haba hajia inata oder amma kinki tsayawa" hararanshi tayi tace" to lafiya?" kinga yanzu dai ba wannan ba ki shigo dan Allah na rage maki hanya inba damuwa" sabida bacin rai yasa tace" da damuwa malam, dan Allah ka wuce ka barni" zata wuce taji anyi tsawa mai k'arfi alamar ana ruwa a wani wajen, abar da tafi tsoro kenan dan haka ta bud'e motar da sauri ta shiga tana k'ilu k'ilu da ido, dariya yayi ya shiga saida sukayi nisa yace" yan mata ni suna na JAMAL, ke kuma fa?" bata fad'a mashi ba sai kwatancen gidan su ta mashi dan ya sauke ta.

Dak'yar ya samu ta bashi number wayarta, tana fitowa yayi dai-dai da kawowar Salman dan haka tabi bayanshi dan ta sauke ruwan bala'i, Jamal kam bin bayanta yayi da kallo yana lasar leb'e yace" ina san faran mace amma fa badan na aureta ba, kema zan latsaki kad'an duk da naga akwai tsiwa da jan aji a tare da ita, amma ba komai naga wanda suka ninka ta so dubu dan haka zan fara shawo kanta kafin nan sai in abka mata" kara lashe leb'en yayi yaja motar ya wuce.

K'ofar gidan ta tsayar da shi tace" to dan ciki bakin nazo gida lafiya babu abinda ya sameni sai ka mutu tsabar takaici" tana fad'i ta wuce gidan su Alhaji a tinanin su kuma Salman ne ya dawo da ita, tana shiga su Khairat suka karb'i kayan suka fara dubawa, ba bata lokaci saiko aka keto da ruwa mai k'arfin gaske.

_To bari muji wai wannan Yar tsama yaoushe ta fara tsakanin Ummi da Salman ne?🤔_
27/02/2019 à 17:32 - Mamar Latif💃: 💑 AUREN HA'DI 💑

_Samira Harouna_

```Mommyn Khadija``` ( ma Belle)
```Mommyn Sultan```
```Mommyn Labyb``` (Mamien mu)
```My Heenat``` (Raheenat)
```Choukoura``` (Chouk Beby)
```Halima```
```Maman samha```

( *Cette page ce pour vous)*

~Luv u😘~

🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
( _Gidan zaman lafiya da_ _amana insha Allah)🤜_ 🤛

*Page*

2⃣9⃣-3⃣0⃣

__A fahimtar Salman shine k'arshen rainin da mace zata ma namiji to ta harareshi ko tsaki had'e da murgud'a baki, dan ko a film yaga haka to ya tsani wannan matar kenan dan ko miji da matar shine ta_ _ma shi haka to ta gama raina shi dan haka ya tsani abin sosai._

__Tunda Ummi ta tashi tana k'arama ya zama in dai Salman zai mata magana to sai tayi abinda ya tsana harta girma, bayan ta mallaki_ _hankalin kanta sai ta gane Salman baya so ita kuma sai ya zama d'abi'arta hakan, duk lokacin da yake mata fad'a ko ya dake ta akan ta raina shi sai Mahaifiyar shi tace, kawai dai dan ya sama ransa ne shiyasa ko d'umi tayi sai yaga kamar tayi abinda baya so, Mahaifiyar Ummi kuma tana cewa, da gangan ta keyi dan tasan baya so, to haka_ _dai ya zama kowa da bayan wanda ya ke bi, kasancewar su mak'otan juna dan Ummi bata wanka ta bushe sai a gidan wajen k'awarta Khairat, haka ma Salman ya fi wuni gidan akan gidan su sabida k'annan Ummi da Mahaifiyar su yana jin dad'in zama da su._
_
_Rayuwar Iyalin tana da ban sha'awa dan Ummi da su Jawahir duk lokacin da babu école ko makaranta to suka_ _zab'i gidan da zasu je su kwana biyu a can, haka zasu dinga farin ciki suna d'aukar photunan junan su sabida_ _tarihi shiyasa suka shak'u sosai ba su tab'a samun sab'ani ba._

_In dai Ummi zata ma Salman_ _abinda baya so to ya kan dage ya tumurmushe ta san ransa kuma hakan ya samu asali ne sabida la mamma tace duk sanda ta mashi to ya daketa har sai ranar da ta daina dan kanta, burin Iyayen nasu bai wuce suga an had'a auren su ba to amma yaran ma sunki jituwa tsakanin su duk da dama ana had'a_ __auren ne ba sai wanda ka ke so ba ko ku ke fahimtar juna._
_
```Wannan kenan``` 👈

_
Washe gari amare suka shirya zuwa wajen kitso,Salman da Khamis ne su ka kai su a mota ma saida aka samu matsala tsakanin Ummi da Salman sakamakon..., sorry dear wayar ta gaji😞.
27/02/2019 à 17:33 - Mamar Latif💃: 💑 AUREN HA'DI 💑

_Samira Harouna_

*(Yan uwa ku gafarceni a bisa kuskuren da nayi wajen saka num page, kamata yayi wannan ta zama 27-28)* 👏

🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛

*Page*

3⃣1⃣-3⃣2⃣


Salman da Khamis ne a gaba, yayin da su Jawahir ke su biyar ke baya Ummi kuma tana bisa k'afafun Jawahir a bayan kujerar da Salman ke tuk'i, saboda rububin da yayi yawa da ramuka dake wurin yasa Salman shiga wani rame da baisan da shi ba hakan yasa kowa saida ya girgiza Ummi da ke k'afafun Jawahir saida tayi kamar zata fad'i da sauri ta rik'e kafad'un Salman duka biyun tare da fad'in" Inna Lillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un, malam kashe mu kake so kayi ne?"da k'arfi Salman ya fizge hannayenshi yana fad'in" ke wannan wani irin abu ne? muguwa kawai" mugu dai, kaji mutum kamar makaho da ba zaka kalli inda zaka saka mu ba" ke rufa min wannan banzan bakin naki kinji ko" idan kuma naki fa saime ya faru?" sai kisha dan banzan duka kuwa mahaukaciya kawai" turo baki tayi ta harare shi kallanta yayi ta madubi dan haka ya zuro hannu ya mazge kanta, haka suka kai suna

Please Login or Register in order to submit comment