Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abin musulunci ya shar'anta.



Wurin yayi tsit kowa na jiran yaji abinda Malama Hakama za ta ce, basu gama tunanin su ba suka jiyo muryar wata mata tana fadin " hakika abin da wannan baiwai Allah ta fadi haka yake domin da ba, a samu magana ba ni zanyi sai kuma gashi an samu wacce tayi bayani kmr yadda musulunci ya ya tanadar mana, hakika a zamanin baya babu wadataccen ilimi a na dora komai ne abisa tsarin *Gargajiya* wanda yin hakan ba hujja ba ne acikin addini domin ance mu nemi ilimi a duk inda yake kuma muyinamfani dashi, ni ma bazan manta da wani labari da kaka Inno ta bamu ba run Muna 'yan yara"


*Labarin kaka Inno*

Ta fara da cewa idan akayi mutuwa aka kai mutum makwancin sa, za a zo ayi mass tambayoyi kamar haka...


Baiwar Allah mai kwanciyar tsakar 'daki meye abu daya... sai tace Allah ne abu daya. Meye abu biyu... Rana da wata ne abu biyu.... Meye abu uku ... Murahun mu ne abu uku. Meye abu hudu..... Gabas da yamma kudu da arewa su ne abu hudu. To fa bayin Allah kunji labarin kaka Inno wannan dai ya na mazaunin tambayar kabari, ina hankali zai 'dauki wannan, da duk ire-iren su. Kowa ya jinjina labarin kaka Inno harda masu darawa🤣.



Hajiya Saude kenan yayar malam Ila, tunda suka ji labarin mutuwar dan uwansu suka zo garin kasancewar su a wani garin suke da ban.



Nan 'yan kauyen suka yi murna jin cewa ai takabar da muusulunci ya tanadar ba irin wacce suke yi ba ce, nan kowa ya hau tambayar abin da ya shige masa duhu kyma suna samun amsoshin su.



Ana haka har aka yi kwana bakwai, hajiya Saude ta basu gudunmawa mai yawa, sunyi kukan tafiyarta domin ba laifi sun samu ilimi a wurinta, ganin haka tai musu al'kawarin dawowa idan ta samu iko tai musu nuni da su dinga zuwa wurin Hinde domin kuwa a 'dan zaman da suka yi ta fahimci Hinde na da ilimi mai zurfi sai dai rashin mataimaki.



Nan suka yi bankwana suka wuce da al'kawarin Hinde za ta dinga basu taimako dai dai gwargwado.....



Shin kuna ganin Malan Maude da amince da haka kuwa 🤔.



Ku biyo ni a shagi na gaba.


*Sorry for the late post*



*Ummu Rahma* ✍🏻
[4/10, 7:57 PM] ‪+234 803 509 6818‬: *👳🏼👳🏼'DAN GARGAJIYA👳🏼👳🏼*

*(gargajiya ba addini bane)*


*Na*

*Ummu Rahma* ✍🏻


*Gajeren labari mai dauke da nishadi, gidadanci da rashin wayewa ta addini*


*35⚜40*


*_Sis Najer'art (YARIMA SUHAIL) tnz for the dedication Allah ya bar mu tare_*

*_Nabeela Zango Allah yasa kin fara WAYE NE lfy kuma ki gama lfy_*


*SHAFIN MASOYA*

*Billy luv*
*Humaira Shuwa*
*Dije ontop*
*Ina miko jinjina*

*Afuwan masoya 'Dan Gargajiya na rashin ganin post kwana biyu, hakan ya faru ne sanadin rashin lafiyar da na yi kwana biyu, amma na samu sauki, ina ji daku*




Hinde ce ta nisa bayan malam Maude ya gama sababin sa ta juyo ta amsa sallamar Balki (wacce ta shigo).


Malam Maude kuwa 'kin tafiya yayi ya samu gefen runbu ya ma kansa mazauni, nan Hinde ta fara yi wa gwaggo bayanin abinda Allah ya tanadar a cikin Al'qur'ani game da rabon Gado _(ayi min afuwa lokaci bazai bari muyi bayani sosai ba)_



Bayan ta gama jawabin ta ne Gwaggo tayi mata godiya sannan ta fiddo kullin Leda daga gefen zaninta ta 'mika wa Hinde


'Karba ta yi sannan ta mata godiya ta juya wurin Balki dan jin abinda ke tafe da ita.



Bayan sun 'kara gaisawa Balki ta jefo tambayar ta kamar haka, "Hinde ni kuwa ina son ki warware min wannan batu na sha'anin hakkin magidanci ga iyalan sa, shi ne ya kamata ya nemo abin masarufin gida ko kuwa matar gidan ce". Malam Maude da ya yun'kura zai fita 'kwar gida komawa ya yi ya zauna Dan jin amsar da Hinde za ta bayar.



Balki ta ci gaba da cewa mijina baya wadata mu da kayan masarufin rayuwa kama daga sabulai izuwa cefanan su kuka da daddawa, idan nayi magana sai yace ba hakkinsa bane, ai tun lokacin kakanninmu suke hidima da Kansu, kuma a wa'azin Hajiya Saude na ji ta fara bayani akan hakki na abokan rayuwa kuma banji karshen lamarin ba na tafi dauko hatsi a 'kauyen yamma.



Daga kan gwaggo har malam Maude shiru su kayi dan jin jawabin da Hinde zata sauke.



*A GIDAN BADARU*



Bayan komawar su Badaru ya ji nasihar Malama Ramatu inda ya siyo abubuwan bukata sosai ya jibge mata kuma yana kokarin kiyaye hakkin da Allah ya dora masa.



A bangaren Bahijja kuwa Ashe Malama Ramatu ta same ta kuma tayi mata nuni da cewa ita ce zata iya saita mijin ta ya dawo hanya domin kuwa mace ta na gyara mijin ta komai gur'bacewarsa kuma tayi mata alkawarin daura 'damarar saita shi in Allah ya so.


Kwanaki sun shude ana gobe suna Innar Badaru ta dira sashen 'Dan nata dan gudanar da al'adar taron suna.



Wai ya za a yi ne a 'kauyen Bandaas?



Innar Badaru wacce wainar zata toya ne a gidan sunan 'dan 'Danta?


Ku biyo ni



*Ummu Rahma*✍🏻
[4/10, 7:57 PM] ‪+234 803 509 6818‬: *👳🏼👳🏼'DAN GARGAJIYA👳🏼👳🏼*

*(gargajiya ba addini bane)*



*Na*

*Ummu Rahma* ✍🏻


*Gajeren labari mai dauke da nishadi, gidadanci da rashin wayewa ta addini*

*Jinjinar ban girma gareki NABILA ZANGO ina tayaki murnar kammala novel dinki lafiya Allah yasa a amfana da darasin dake ciki Amin*

*_Wannan shafin naki ne kyauta_*



*30⚜35*


*ASIBITI*


Malama Ramatu ce ta katse shi da cewa, duk abinda mahaifiyar ka za ta yi ba ka da tamkar ta, tunda kasan abubuwan da take sa ka aikata ba daidai ba ne sai ka guji faruwar haka.


Ka kyautatawa dangin mahaifinka, ka yi wa iyalin ka adalci ta hanyar kula dasu sai ka ga Allah ya bu'da maka.


Kayi mata biyayya kuma kayi mata addua Allah yasa ta sauko daga ra'ayin ta na baya.

Ka zamto mai riko da gaskiya a duk inda kake.....

Kukan da ta ji yana yi ne ya sa ta tsagaitawa, juyowa tayi ta kallesa cikin tausayi ta 'kara masa da nasihohi masu ratsa zuciya.


A na haka Umman Bahijja ta fito tare da nufosu, nan suka tsagaita Dan su ji da wanne uziri take tafe, nan take sanar musu cewa an basu sallama, murna sukayi gaba 'daya sannan ya nufi titi dan nemo masu abin hawa


Fitar sa kenan aka kira Malama Ramatu domin basu sallama.


Nan dai suka rabu cikin kewar juna tare da alkawarin kai mata ziyara, dimin a dan zaman su da ita ya fuskanci mace ce mai addini da amana kuma ya dauki damarar sauka daga akidar sa ta *Gargajiya*



**** ****

*KAUYE*

Assalamu Alaikum! Assalamu Alaikum! Malam Ja'e ne yake ta faman sallama a 'kofar gidan malam Maude.

Sama-sama malam Maude ya jiyo sallama lokacin yana kishingide bayan dawowar sa saga masallaci.


Mi'kewa yayi ya nufi 'kofar gida, da zuwan sa ya tarar da Ja'e tsugunne a gefen danga.


Nan suka gaisa tare da 'kara yiwa juna gaisuwar rashin abokin su Malam Ila. Tare da masa Addu'ar Allah ya ji'kan sa.

Suna cikin hira sai ga wata tazo ta shige zuwa cikin gidan malam Maude bayan ta gaisar dasu.


Shigar ta kenan Malam Ja'e yace da malam Maude "ince dai ko lafiya naga gwaggon su Mado ta bugo sammako kamar mai shirin zuwa gona" oho ni ina zan sani tunda dai tare da kai muke zaune ta wuce, to Allah dai yasa lafiya suka ce Amin sannan suka cigaba da hirar su.


*Cikin gidan Malam Maude*

Sallama gwaggo tayi taji shiru ko da ta kara shiga ta tarar da Hinde ta na sallar walaha nan ta yi wa kanta mazauni tana jiran ta ta idar.


Cikin 'yan mintuna kuwa ta idar, bayan sun gaisa ne gwaggo ta ce wurin ki nazo Hinde, naji malamar burni tace duk mai tambaya ya zo ya sameki shine na zo in miki wata tambaya.


Hinde tace to Allah yasa na Sani gwaggo, tace Amin Hinde.


Nan gwaggo tace "wai shin ya gaskiyar wannan lamarin yake, wai da gaske ne ana fitar wa da aminan mamaci ihsani kafin a raba wa magada gadon sa?

Hinde ce race a'a a cikin Al-kur'ani mai tsarki Allah yana cewa......

Bata 'karasa ba ta jiyo malam Maude yana fadin oooo Hinde abin naki har ya kai ga haka, dama tunda naga shigowar wannan matar na ga ta dade na biyo bayan ta, na San wannan sammakon ba a banza ba wallahi, yana yi yana kumfar baki........

mamaki ya hana Hinde iya furta furucin da yazo mata, ana wannan hali sai ga mace ta biyu ta doko sallama
To fa (🤣) .


Ya zata kaya ne?

Mu hadu a shafin gaba.



*Ummu Rahma*✍🏻
[4/10, 7:57 PM] ‪+234 803 509 6818‬: *👳🏻‍♂👳🏻‍♂Dan Gargajiya👳🏻‍♂👳🏻‍♂*

*Gargajiya ba addini bane*

*40⚜45*

*RANAR SUNA*

Innar Badaru ce a zaune ta hakinmce a gaban Mai yanka ta na fadin yadda za a yi da fatar bayan an Fe'de, a cewar ta ai duk na kakar yaron ce, Mutanen da ke wurin kowa yayi shiru dan gudun 'bacin ran Inna.


Bayan an kammala ta sa kanwar Badaru ta kinkimar mata sai 'bangaren su.


Ana nan zaune saiga maro'ka nan sun billo, nan fa wurin ya kaude da hayaniya, Kafina ankara Inna ta dauko jaririn ta mika wa 'daya daga cikin marokar a Cewarta me Jego ce Za tayi musu Kari (lik'i) sannan ta amshi 'danta bayan ta basu 'korai na hatsi.


Kowa yayi Mamakin wannan salo na Inna kuma an rasa me cewa komai.


Da 'kyar dai Bahijja ta yi yadda Inna ta ce saboda gudun fitina, a haka dai Inna tayi ta fito da abubuwa iri iri.


Da yammaci iyalan gidan su bahijja suka iso, ai nan da nan Inna ta tarbe su da 'korafi Akan basuyi saurin Zuwa ba dan sallamar maroka da mai yanka (bayan Badaru ya bar mata komai) a cewar ta ai haka akeyi🤔

Nan dai ta tilasta sai da ta raba su da 'dan wani abun, sun mik'e da shirin wucewa ciki sai ta tsayar dasu da cewa "ban ga Kun gabatar da abin da ya kamata ba" wata daga cikin tawagar ce tace kamar me Kennan Inna?.


Nan Inna ta karkace ta fara da cewa "na farko za a bada shaddar kakan yaro duk da ba ya raye sannan sai toshin 'kanne da yayyan mijin Nata, akwai Kuma dahuwar abincin Rana da za ta yi har tayi kwanaki arba'in sai Kuma.......... bata Ida fadin zancenta ba suka katse ta da cewa "lallai Innar Badaru abin naki 'Kara gaba yake, to mu ba za mu iya da wannan *gargajiyar* taki ba ehe, haba da me za mu ji.

Nan dai ta yi ta sababi daga 'karshe Kuma ta wucewa sashen ta tana bambami da Jiran dawowar Badaru.



*'KAUYEN BANDASS*


Hinde ce ta fara bayani cikin hikima da 'kwarewa, tace " shi dai *HAKK'I* Muhimmin al'amari ne cikin aure, hakkin miji ne ya wadatar da iyalan sa da abubuwan da suke bukata tun daga kan abinci, sutura, lafiyar, makwanci kai har da abin da shafi walwalar su baki daya


Ba tilashin mace ba ne ace ita za ta samar da wadannan abubuwa idan kuwa akai haka an tauye ta domin mata rauni ne da su, sau da dama zaka ga basu da juriya amma suna da 'dinbin tausayi da kulawa.


Malam Maude da ke gefe ya kasa kunne duk da ya ji kamshin gaskiya a jawabin da Hinde tayi sai ya basar, nan ya jefo tasa Kalmar da cewa " yanxu dai hinde in na fahimceki kina nufin ta yi wa mijin ta bore kenan ko.ya kike nufi wai"


A'a malam ni ban ce ta yiwa mijin ta bore ba kawai dai na nuna mata abin da ke da inganci ne a shari'ance. Shiru malam Maude yayi yayin da gwaggo ta mik'e da niyyar tafiya, sallama ta yi wa Hinde da Balki ta wuce, a soron gidan ta ci karo da Hajara 'kanwar Malam Ja'e da alama dai itama tana tafe da nata uzirin


Jin sallamar Hajara ya tunzura Malam Maude yana fa'din " ni fa hinde ba zai yiwu ba, da sassafiyar nan ko sanwar koko baki 'daura ba kin mayar min da gida sai kace dandali.

Allah ya huci zuciyar ka malam, yanzu zan kammala Insha Allahu cewar Hinde.

Nan ya shuri takalman sa ya nufi tirken dabbobi. Hajara da tayi sororo a tsaye tana tunanin masifa irin ta malam Maude ta ji ana cewa 'karaso mana Jaru, ga wuri ki zauna. Bayan ta zauna ne suka gaisa sannan ta fara jawabin ta kamar haka....




**** ****

A 'bangaren Inna kuwa sama sama aka jiyo hayaniya yana tashi nan dai kowa ya dunguma zuwa ganin me ke faruwa ne.


To faaa

Muje zuwa


*Ummu Rahma*✍🏻
[4/10, 7:57 PM] ‪+234 803 509 6818‬: *👳🏼👳🏼DAN GARGAJIYA👳🏼👳🏼*

*(Gargajiya ba addini bane)*


*Na*

*Ummu Rahma*


*Gajeren labari mai dauke da nishadi, gidadanci da rashin wayewa irin ta addini*



*Sorry! Sorry!! Sorry!!! Fans din Dan Gargajiya, ayi min afuwa*


*Na sadaukar da wannan shafin ga dukkannin masoyan Dan gargajiya*😘😘😘😘


*45⚜50*

Zuwa wani 'Dan lokaci 'bangaren Inna ya cika dam, kowa yana shirin jin ba'asi.


"Haba Laure ki dai ji tsoron Allah, haka mu kayi da ke, kin ci arziki kin mance shi ne kika kasa tuna abunda nayi miki lokacin bikin diyarki, to bari in tuna miki, samiru na saiti shida na kai miki da saitin silba (ci bari kallo) da hatsi na 'kwarya biyu da dubu guda (1) shine dan kinibibi kika dauko wata jemammiyar turmin zani da sabulu kwara hudu kika lallabo kika kawo min, ahayye wallahi da sake". (Inna ce ta ke yiwa kawarta Laure tijira akan biki wanda suka mayar dashi kamar ibada).


Laure ta ce kiyi hakuri Innar badaru, shekarun ne suka ja shiyasa na dab manta amma zan karo miki.


Ai dole ki mance, a zaton ki kinci lalai ko, to da sake gara dai ki yunkuro daga shi kuma mun gama buki da ke.


Mama Hansai (kawar Inna) da tun da aka fara wannan bidiri ta na gefe tana jin ikon Allah, bayan kowa ya natsa ne mama hansai tace da Inna " ni kuwa Innar Badaru ya bikin namu yake ne" yauwa 'yar gari kinji masu son zaman lafiya cewar Inna. " ai dubu uku na bhudima kacin bikin Burema da ruwa kura biyu na hudima (🤣).

To ga wannan cewar mama Hansai inda ta mika wa Inna zunzurutun kudi dubu biyar da kunun gyadar ta a cooler mai zafu da dadin gaske, nan Inna ta amshe tana washe baki da rattabo godiya.


A haka akai ta yin bikin suna gidan Inna kafin da yammaci kowa ya watse zuwa gidansa.

*_kai mata mu guji wannan al'ada ta biki da mukeyi, ace duk abinda aka baka saika ninka 🤔 idan kuwa mutuwa tazo.mana to fa mun tafi da bashi kenan, Allah ya ganar damu_*


**** ****
*KAUYE*

Kwanaki sun shude, abubuwa da dama sun faru, ciki kuwa harda sauyi da Matan Kauyen ke shirin kawowa a gidajen su da kuma tarbiyar yaransu, da juma kara zuwan Hajiya saude, wanda sai da tayi kwani bakwai kafin ta wuce, nan ta kara wayar musu da kai, sunji dadi sosai daga baya kuma Hinde ta dora daga inda aka tsaya.


Wata ranar asabar bayan malam Maude ya dawo daga masallaci ya kishingida bacci ya fara daukar sa ya jiyo kamar hayaniyar mutane a kofar gidansa bai gama tunani ba ya ji a na ta doka sallama a kofar gidansa, mikewa yayi ya fita dan ganin me ke faruwa.


Fitarsa keda wuya ya ga mutane kusan su sha biyu kowa da alama a fasace yake.


Sallama yayi musu suka amsa sama-sama kowa na muzurai, nan dai malam Maude yai karfin halin cewa "bayin Allah ince dai ko lafiya". Lafiyar kenan cewar wani murdadden mafarauci da ke tare da karan farautarsa.


Ku dakata cewar wani dattijo da ya dan fisu sassauta fushin fuskarsa, Ya cigaba da cewa munzo ne akan batun matar ka Hinde, ta juyar mana da ra'ayin Matan mu ta Billo mana da sabon tsari , wannan mafarauci ya ce to ka tabbatar ka ja mata kunne, kuma duk ranar da muka kara ganin matan mu a nan gidan sai mun mika ku kotu can cikin birni.


Suna cikin wannan sa'insar suka hango wani matafiyi da alama dai bako ne, kallin sa suke yi har ya karaso kusa da su inda yayi musu sallama tare da tambayar gidan mai gari


Kowa ya yi sakak'e kafin.daga bisani wani matashin magidanci ya ce taho muje in kai ka Allah yasa dai kai din bakon alkhairi ne, murmushu kawai ba'kon yayi yace Insha Allahu.


Nan ya raka shi har gidan mai gari sannan aka musu iso ya barshi anan ya juya Dan komawa kofar gidan malam Maude.


A hanya ya hadu da abokan tafiyar sa suka wuce gidajensu gaba daya.


Malam Maude kuwa a zuciye ya shige gida yana 'kwalawa hinde kira kamar ta ci bashi. ...........



Ya za ta kaya ne a gidan malam Maude?

Shin wannan bakon wanene kuma da me ya zo?









*Ummu Rahma*
[4/10, 7:57 PM] ‪+234 803 509 6818‬: *👳🏼👳🏼DAN GARGAJIYA👳🏼👳🏼*

*(Gargajiya ba addini bane)*


*Na*

*Ummu Rahma*


*Gajeren labari mai dauke da nishadi, gidadanci da rashin wayewa irin ta addini*


*50⚜55*


Malam Maude yana shiga gida ya fara sababi, ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba.



Ita dai Hinde shiru tayi a zuciyar ta kuma tana ayyano abubuwa iri iri dan kuwa ta 'kudiri ko da malam Maude zai dauki mataki akanta ba za ta daina bayar da tata gudunmawar ba, ganin ta yi masa shiru bata kula shi ba ya sa ya fusata ya nufi rumfar da take aikace - aikace ya sungumo randar ruwar ta ya buga da 'kasa, wannan bai masa ba ya nufi tirken dabbobi ya kunce ilahirin dabbobin ta ya kora su waje, sungumar harawar da suke ci yayi ya wulla ta bayan danga(🤣).



Duk wannan abin da malam Maude ya ke yi Hinde ba ta tofa ko kalma daya ba, nan ya shuri takalman sa ya nufi 'kofar fita Hinde kuwa ta ce malam a dawo lafiya (🤣).


Takaici ne ya kama Malam Maude ganin duk abinda yayi ba ta yi fushi ba har da masa a dawo lafiya, waje ya fita ya samu 'kasan wata bishiya ya zauna sabida takaici sai da yayi 'kwalla, yana nan zaune yaji ana shela kowa yaje 'kofar gidan mai gari akwai tattaunawa ta musamman.


Nan dai malam Maude ya mike ya nufin gidan malam Ja'e dan su tafi tare, a hanya suka hadu shima ya fito nan suka rankaya sai gidan mai unguwa.


**** ****

A gidan Badaru kuwa bayan kowa ya watse da dare Badaru ya shigo, nan Bahijja ta nuna masa abin arxikin da ta samu, nan Badaru ya ce a kaiwa Inna a ji me zata ce.


Ba dan ran Bahijja ya so ba ta kwashi kayan ta kaiwa Inna.


Inna kallon sama da kasa ta yiwa Bahijja kafin tace "lafiya dai ko na ganki da wannan tsohon dare" ta na fadi tana yatsina fuska.


Lafiya lau Inna dama kayan da muka samu ne na zo dashi in nuna miki, to ai kamar yadda kika sani a al'adar mu rabawa biyu za kiyi ki bar rabi ki tafi da rabi.


Bahijja ba dan ranta ya so ba tayi yadda Inna tace mata dan gudun 'bacin rai, ta sa 'kafa za ta fice Inna ta ce mata " yauwa kee gobe kar a fara suyar nan a bari sai na bullo ehee.

Bahijja da to ta amsa sannan ta fice zuwa sashen ta zuciyar ta a cunkushe da irin abubuwan da Inna ke mata.

**** ****

*GIDAN MAIGARI*


'Kofar gidan maigari ya cika ma'kil kowa na jiran jin jawabin maigari da dalilin da yasa aka tara su


Maigari ne ya fara jawabi kamar haka......


*Manage pls*



*Ummu Rahma*
[4/10, 7:57 PM] ‪+234 803 509 6818‬: *👳🏼👳🏼DAN GARGAJIYA👳🏼👳🏼*


*(Gargajiya ba addini bane)*


*Na*

*Ummu Rahma*



*Gajeren labari mai dauke da nishadi, gidadanci da rashin wayewa irin ta addini*



*60*

*LAST PAGE*


*GIDAN MAIGARI*


'Kofar gidan maigari ya cika ma'kil kowa na jiran jin jawabin maigari da dalilin da yasa aka tara su


Maigari ne ya fara jawabi kamar haka......

Assalamu Alaikum mutanan gari na, hakika kowa zaiyi mamakin wannan kira da nayi na gaggawa, to bana so Ku tada hankulan ku ba komai yasa na tara ku ba sai don wannan bawan Allah da kuke gani a zaune a gefena ( yai nuni da ba'kon nan), yanzu zamu ji abinda ke tafe dashi.



'Yan gari sukayi na'am da jawabin shugaban nasu sannan kowa ya maida hankalinsa dan jin da wacce ya zo.


*JAWABIN BAKO*

Assalamu alaikum, da farko dai sunana Malam Hudu ko in ce Almajiri, na fito ne daga yankin *KALLARE* wani sansani ne na Neman ilimi dake can gabas da kofar shigowa wannan gari naku na *Bandass*


Hakika na dade ina son kawo muku ziyara amma ban samu damar haka ba, kasancewar komai sai Allah ya so.


Yaa ku mutanan wannan gari hakika mafi yawan ku kuna gasgata *Gargajiya* akan *Addininku*, Ku sani cewa *GARGAJIYA BA ADDINI BANE*.


Da yawan ku kun dauki al'ada ta kakannin da wasu ma basuyi rayuwa da su ba, idan anyi magana sai ka ji ana cewa ai *tun iyaye da kakanni*🤔 ba za ka ji ance tun zamanin sahabi wane ba da sauransu.

Nan dai yai musu bayanai gamsassu cikin hikima da saukin harshe kamar yadda a ke so mai fadakarwa ya kasance.


Cikin dan lokaci ka'dan da yawa daga cikin mutanan garin sun fahimci inda malam yasa gaba sa'banin malam Maude da yake ganin kamar zai aikata wani babban laifi ne in ya watsar da al'adun iyaye da kakannin sa (🤣).


Nan fa Malam Maude ya shiga jerowa malam tambayoyi yana amsa masa cikin hikima da 'kwarewa, kafin wani lokaci malam Maude ya samu gamsuwa da jawabin malam.


Wani daga can gefe ne ya jeho tasa tambayar yana cewa, " a cikin al'adun iyayen mu akwai masu kyau Wanda bai kamata ace mun yasar da su ba, shin zamu iya ci gaba?" Malamin yace tabbas iyayen mu suna da kyawun 'dabi'un da ba zamu watsar ba kamar alkunya, zumunci, kawaici, dogaro da kai, kyauta, girmama yaro da babba da mayar da komai cikin sauki da fahimta, dukkan wadannan kuwa suna cikin addinin mu, wasu ne dai suke hadawa da canfe-canfe da sauran abubuwa idan anyi magana su ce *iyaye da kakanni*.


Haka suka kasance tare yana wayar musu da kai har zuwa azahar inda sukayi alwala ya jagoran ce su sallah, bayan sun idar ma ya kara musu nasiha ingattaciya game da Ha'kkin iyalan su, anan da yawa suka fahimci inda fadakarwar Hinde matar malam Maude ya sa gaba inda suka ba malam Maude hakuri abisa abinda suka masa a kofar gidan sa, nan yace ba komai ai duk cikin rashin Sani ne.


Sun kammala inda malam yayi musu akkawarin zaiyi watanni uku kafin ya cigaba da tafiya sauran garurawa kuma ya sanya musu lokutan daukan darasi, godiya suka dinga yiwa malam inda ya dakatar dasu da cewa Hakki ne a gareshi ya sanar tunda ya sani.

Nan kowa ya yi shirin tafiya inda mai gari ya dakatar dasu da cewa ga abinci nan za a fito dashi, godiya sukayi wa mai gari bayan sun gama cin abinci kowa

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment