Join Our WhatsApp Group

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

Login Register

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku

This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT

This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

*RUHIN JINN☠️💀😈*

_PAID BOOK #300 ONLY_

_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA..... And Other's BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P ANNUR PAID BOOK....(20) SAKACINA PAID BOOK.... (21) SO!!! FREE BOOK... (22) FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA PAID BOOK... (23) D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU PAID BOOK...(24) RUHIN JINN PAID BOOK
loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝```

_Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken_ *RUHIN JINN💀☠️😈👹 PAID BOOK 300 ONLY*
_Ina fatan yabada darussuka dama ilmantarwa Kamar dai yarda sauran littafaina suka bayar....._

_Monday 28/8/2023 August_

*Free 🅿️ 1 to 5*

Wata irin guguwa ta turnik'e garin, harta Haifar da ruguza wasu gidaje, itatuwa kuwa suka Soma karyewa suna zubewa k'asa, tafiya guguwar take duk Abunda ya Shiga gabanta tofa Saidai wani bashi ba,

Mutane kowa guduwa yake Yana neman tsiratar da rayuwarsa, wasu har motocinsu suke Bari suna guduwa,

K'ok'arin fitowa cikin motar Yake cikin tashin Hankali Yana Janyo Hannuwan matarsa Domin su gudu suma,

Saidai Ina domin guguwar tini ta hangosu tayo kansu,

Gudu suke d'auke da k'aramin d'an su da bazai haura Shekara 15 ba,

Cikin k'ank'anen lokaci guguwar ta rutsa su fad'uwa Kawai sukayi su duka inda Yaron ya gangara gefen titi,
Take guguwar ta lunk'umesu, Fit tacire Kan mutumin jinin Ya wasu har fuskar Yaron, wata Irin k'ara mahaifiyar sa tasaki Kuma sai suka b'ata b'at tab'ace, Haske ya gauraye garin, ba komai sai jinin da ke malala Kan titin,

Yaron kuwa Yana kallo Kuma Yana Jin Ihun Iyayen nasa Yana gani Aka halaka mahaifinsa,

Hannunsa yasa ya shafe fuskarsa sa jinin mahaifinsa Ya kalla, take Ya rusa wani Uban ihu Ya sulale gurin,.

Saida suka tabbatar Komai ya lafa garin yayi Lafiya sannan Suka soma fitowa, Wad'an da Gininsu Ya ruguje suka hau gyara,
Wasu Kuma suka fita domin Aikin gabansu,

Yana cikin tafiya Idanuwansa Suka fad'a Kan Yaron,

Cikin sauri ya K'arasa gurin ya dubashi, ganin Yanada sauran numfashi yasa ya d'auke sa, tafiya Mai nisa Yayi Kafin ya Isa bakin gari, wata Y'ar bukka nagani ya tsaya, cikin bukkar ya Shiga Ya shinfid'e Yaron Kan tabarmar sak'a dake d'akin, wasu ruwa ya d'auko ya shafa masa,

Dogon numfashi Yaron yaja Kan Yabud'e idanuwansa, k'urawa mutumin Ido yayi, Tina Abunda yafaru yasa ya mik'e zumbur Yana K'ara,

Rik'eshi mutumin Yayi tareda Masa Addu'o'i Yana tofa Masa Cikin d'an lokaci kuwa saiya natsu, zama sukayi suna fuskantar juna Mutumin Yana rik'e da Hannun Yaron,

"Waye Kai Yaro Ina Iyayenka,"? Tafiyar da mutumin ya jefawa Yaron

Hawaye Suka soma zarya daga idanuwan Yaron Yace"Ankashe su Agabana Akacire Kan babana Kuma Aka tafi da mamata bansani ba ko ita Ankasheta Yanzu,"

"Waye ya kashesu,"?

"Bansani ba wata guguwa ce kawai,"

"To meya fiddaku Cikin guguwar? Bakusan ba'a fita Ranar ba gaba d'aya saboda guguwar,"?

"Bamu sani ba Domin mu Bak'i ne muntashi daga gsrinmu ne nundawo Nan zamu zauna,"

"To Ina Y'an uwanku suke,"?

"Mu bamuda kowa sai Allah, kowa baya son mu shiyasa muka baro gidanmu, kaima waye kai"?

Ajiyar Zuciya mutumin Yayi, " Ni sunana Malam Bukar ganau, Ni shahararren malamine Kuma Ina fad'a da Aljanu Sosai Domin duk taurin Kan Aljani nakanyi maganin sa"

"Meyasa kake Zama inda ba kowa bakajin tsoro ne, Ina Ahlinka Kai,"?

Murmushi Yayi"Ni banda kowa Kamar Kai Wannan guguwar data kashe Ahlinka Nima ita takashe nawa Kuma sanadinta Yasa nadaina tsoro nake fad'a da Aljanu,"

"Itama guguwar Aljanu ce? Taya takashe naka Ahlin,"?

"Irin yarda ta kashe naka nima Haka tayi, Sosai Wannan guguwar Aljani ce Mai matik'ar k'arfin tsafi jarumtaka Wannan Itace Ake Kira da *RUHIN JINN💀☠️😈👹*"

" *RUHIN JINN☠️💀👹😈* Kuma baba,"

Shafa Kan Yaron Yayi Yana zubda Hawaye yace"Ashe zansake Samun Wanda zaikirani baba? Nacire Rai da tsammani zaka zauna dani dagaske Ni baba ka d'auke Ni,"?

"Banida kowa A Yanzu sai Kai Kaine kowa nawa idan zaka taimake Ni zanso baba, Amma waye Kai Kuma meye silar zuwan wannan Aljani har Ake kiransa *RUHIN JINN💀☠️👹😈*"?

"Hunmmmm Zan fad'a maka Komai Kafin Nan meye sunanka,"?

"Sunana Jalal, Inason nasanin samuwar wannan *RUHIN JINN☠️💀👹😈,* Domin Inason Zama silar mutuwar *RUHIN JINN💀☠️👹😈* d'in na gogeshi da zaluncinsa Ina son dawoda mamana idan Bata mutu ba Kuma na d'auki fansa Kan mutuwar babana,"

"Zaka iya fad'a da Aljanu da Gaske kana son Zama Jarumi,"?

"Eh baba Inason kaban labarin Komai kuma ka koyamun fad'a,"

Jinjina Kai Yayi Kafin Yashiga bashi Labarin....

_ASALIN ABUNDA YAFARU,. SHEKARU 40 A BAYA DA SUKA SHUD'E.........._

*SHIN SALON WANNAN LITTFIN NAWA YAFARA MUKU DAD'I? IDAN HAKANE MU KASANCE TARE DAKUMA BIYAN 300 KAWAI DAN MALLAKAR NAKA NAKI DAMA SANIN YA ZATA KAYA, WANNA SALON LABARIN NA DABAN NE.......*

_BASEERATA ITACE ARZIKINA😍_

WhatsApp number 07064904617 or 07031012948
*RUHIN JINN☠️💀😈*

_PAID BOOK #300 ONLY_

_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA..... And Other's BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P ANNUR PAID BOOK....(20) SAKACINA PAID BOOK.... (21) SO!!! FREE BOOK... (22) FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA PAID BOOK... (23) D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU PAID BOOK...(24) RUHIN JINN PAID BOOK
loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝```

_Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken_ *RUHIN JINN💀☠️😈👹 PAID BOOK 300 ONLY*
_Ina fatan yabada darussuka dama ilmantarwa Kamar dai yarda sauran littafaina suka bayar....._

*Free 🅿️ 6 to 10*

........Shekaru 40 Dasuka shud'e Abaya Ak'asar Madar Babu Addinin musulunci Sam duk wani dake garin mabiyi Addinin bautar Tsauni ne, daka shigo garin madar, Zakaci Arba dawani tangamemen dutse Wanda duk kusan Rabin garin dutsen ne, Yanada girma Fad'i tsawo nisa, ko wane sati kowa zai fito domin bauta, sannan Ranar bautar dutsen na buk'atar jini, jini nasabon jariri musamman maza, indai Agidanka Anhaife yara 2 tofa dole idan sati ya zagayo zaka bada d'aya, Wanda Kan dutsen zaka kaishi, Ana Aza jaririn zai b'ata Saidai kawai Aji kukansa da ganin jini na saukowa,

Wannan Abun yana damun mutanen garin musamman iyayensu mata,

Anacikin wannan bautar kwatsam Watarana sai ga jariri ya bayyana Kan Wannan dutsen Kuma Aranar ne Za'a gabatar da wannan bautar, batare da wani tunani ba Suka d'auke jaririn Acewarsu yau suma zasuyi bauta d'an Abun bautar tasu yau zasu Rama zaluncin da Ake musu,

Cikin Rashin tinanin Komai suka yanka jaririn Kan dutsen,

Take wani hadari ya game garin Mai matik'ar duhu gari yayi Bak'i, Koda tafin Hannunka bazaka iya gani ba Saboda duhun garin safiya ce Amma Takoma tamkar dare, wata irin guguwa ta game garin d'auke mutane take tana musu kisan gilla ihu kawai ketashi jini Yana fallatsuwa, Aranar Saida Aka rasa mutane dayawa,

Tindaga Ranar Suka daina zuwa wannan bautar, Kuma duk Wannan Ranar ba Wanda zaifita Domin kuwa Idan kafita Lalle kasheka wannan guguwar zatayi,

Suna cikin Wannan mugun halin mahaifina ya bayyana shike taimakon su Kuma dayawansu sun K'arb'e Addinin musulunci, Kuma kisan ya d'an ragu Amma muddin wannan Ranar tazo sai Anhallaka mutane, garin binciken babana ya gano Cewa wannan Yaron dasuka yanka ALJANINE Kuma Ruhinsa ne ke tashi duk Ranar yake Addabar mutane, babana Yayi k'ok'arin kawar da *RUHIN JINN* d'in Amma Ina hatsabibin Aljani ne take Ya kashe Duka Ahlin nawa, Nima da k'yar nasha da taimakon Ubangiji, Kuma har yau dana tsufa Ina Kan fad'a da wannan Aljanin Amma nakasa nasara saboda mutum da Aljan da banbanci,.

Wannan shine Asalin labarin.

*MUNDAWO DAGA LABARIN*..............

Hummmmmmm"Inason zama Ajalin wannan *RUHIN JINN* d'in,"

"Zantaimaka maka kuwa daga yau zamu fara gwaji dama sanin d'inbikan Tsafika"
..................................

_BASEERATA ITACE ARZIKINA😍_

WhatsApp number 0706490467

*RUHIN JINN☠️💀😈*

_PAID BOOK #300 ONLY_

_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA..... And Other's BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P ANNUR PAID BOOK....(20) SAKACINA PAID BOOK.... (21) SO!!! FREE BOOK... (22) FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA PAID BOOK... (23) D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU PAID BOOK...(24) RUHIN JINN PAID BOOK
loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝```

_Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken_ *RUHIN JINN💀☠️😈👹 PAID BOOK 300 ONLY*
_Ina fatan yabada darussuka dama ilmantarwa Kamar dai yarda sauran littafaina suka bayar....._

*Free 🅿️ 11 to 15*

.......Horo Yake bashi sosai ba dare ba Rana Azaba iri iri Yake bashi domin koyar dashi, b'angaren tsafi kuwa take Yayi zarra duk da tsafi ga Addini haramun ne Amma idan zakayi Amfani dashi b'angaren kare Kai to Lalle Addini yabaka dama,

Saida Suka kwashe Sama da Shekara 5 Yana horar Dashi Alokacin ya zama cikin Namiji Mai k'arfin dantse da sihiri Cikin k'ank'anen lokaci ya soma shahara sama da mlm Bukar ma,

A Wad'annan shekarun Abubuwa da yawa sun faru domin *RUHIN JINN* baida shigowa garin Yana kisan gilla wa mutanen garin ba, idanma kace had'a kayanka zakayi domin ka gudu to Lalle Kamar kabada katin gayyata ne wa mutuwarka,

Ganin mutane nayi kowa Yanata gudu sauri sauri Yana shigewa gida Domin b'oye kansa domin kuwa yaune *RUHIN JINN* d'in yake bayyana, Shikuwa tafiya Yake Hankali kwance cike da izza, Sanye Yake cikin kayan Saki Rabin fuskarsa kuwa rufe da k'aton rawanin da ya d'auka, Kirar sadaukan maza ta bayyana jikinsa k'afafunsa sanye da takalmin fata, Abayansa wata k'atuwar takobice sanye cikin kubenta, kallo d'aya zaka masa kasan yakai Jarumin Namiji, duk da fuskarsa rufe take Amma Hakan Bai hanna bayyanar kyawonsa ba, kallon mutane kawai yake suna guje gujensu Amma shikam ko Ajikinsa,

Cikin k'ank'anen lokaci guguwar ta tataso Ahankali har tasoma k'arfi, Yanajin Ihun mutane suna Fad'in "mugudu *RUHIN JINN* d'in ya bayyana tinkan Ya hallakamu,"

Bai juya, cigaba da tafiyarsa Yayi tamkar baiji Abunda suke fad'a,

Y'ar Sarki Yazira tafito rangadi Kan dokinta saiga faruwar wannna Abun dokin nata Ya tsorata jefar da ita yayi tare da zurawa Aguje yabarta k'asa tana Ihun neman taimako inda Sauran Hadimanta ma suka ranta A nakare domin tseratar da ransu,

Gadan gadan guguwar Tayi kanta, tagama sadak'arwa Kan yau k'arshen ta Yazo Domin kallo d'aya zakama guguwar ka fahimce ta Aljanu ce duk wani dabarun tsafinta sun kasa kareta daga wannan guguwar, wani Ihun tasake zabgawa domin k'iris ya rage guguwar ta sameta,

Juyowa yayi Jin Ihun yayi yawa tsayawa yayi cak tareda waiwayo bayansa, ganin guguwar tana daf da illata wannan budurwar yasa yasa Cikin zafin nama Ya ruga da Azababben gudu, cikin k'ank'anen lokaci ya Isa daf dasu lokacin har guguwar tana Neman d'auke ta, Cikin zafin nama ya sureta A Kafad'arshi ya matsar da ita gefe,

Ganin irin yarda wannan bil'Adam Yashiga gabanta Yasa guguwar tsayawa cak,

Fuskartarta gaba da gaba jarumi Jalal yayi kallon kallon suka Fara tsakaninsu Al'amarin da yabawa duk wani mahaluk'i dake wurin mamaki kenan ita kanta Yazira mamaki ya kamata,

Kallon guguwar yake tsayi ne da ita Sosai Wanda Koda mutum zai d'aga kanshi bazaiga k'arshenta ba gata bak'a wulik da munin kallo,

Kansa guguwar Tayi cikin Mugun nufi, Shikuwa Addu'a Yasoma da Anbaton Allah, Wani k'aton marfin kwano Ya d'auko Yayi kariya dashi koda guguwar tazo kansa ta rufeshi, baka Ganin komai yayi duhu, tajima tana zagayarshi yana duk'e da marfin Kafin tayi gaba tabarshi,

Saida komai ya lafa sannan ya mik'e tsaye Yana karkad'e jikinsa, ba Koda Alamun gajiya tare dashi Abun mamaki ma Wai Yafita raye,

Tafiyarsa kawai Yafara baiko waiwaye inda budurwar take ba, duk da kiransa datake hakan baisa ya tsaya ba, Yawuce Abunsa,

Tana zaune gun saiga Sauran Hadimanta sundawo sune suka taimaka Mata tamik'e,

Direct tana Shiga gida fada tawuce cikin tashin Hankali Sarki yake tanbayar ta Ya Akayi ta tsira?

Labarin Komai tabasa amma Kuma Bata ga fuskar Jarumin ba ,

Shela Sarki yasa Kan koma waye ya bayyana kansa kuma zai Masa Kyauta Mai tsoka Amma hakan baisa Jalal bayyana kansa ba,

"Naji Abunda yafaru Kuma Inada tabbacin Kaine kaceci ginbiya Yazira Amma Meyasa baka bayyana kanka ba," cewar wani tsoho dake tare dashi

"Abba Ni bana neman komai Kawai nayi Dan Allah ne, bana buk'atar komai nasu"

"D'an kayi k'ok'ari Amma kuma halwar tsafi na gawadamin Akwai gagarumin Aiki gabanka domin kuwa ba Ai nahin *RUHIN JINN* d'in bane kukayi wannan Karon kuma inada tabbacin bazai barka ba, sannan bakada k'arfin iya YAK'I dashi, dama ace zai bayyana A Asalin siffar sane ta hakan kawai Za'a iya illatashi"

"Amma Abba taya Za'a iya sa Yadawo Asalin siffar sa? Kuma taya Zan gano ko mamana tana Raye,"?

"Abunda madubin tsafi YAK'I nunawa kenan Amma dai Tabbas tana raye Bai kashe taba, Samun siffarsa Abune Mai matik'ar Wuya kuma Koda Yadawo siffar sa ba Lalle bane kayi nasarar hallkashi saidai A hallka wannan *RUHIN JINN* d'in nashi"

"Ta Ina zanga wannan *RUHIN JINN* Abba,"?

"Bansani ba bangano ba Amma Zan k'ara bincikawa, kaidai Koda yaushe kazama Cikin Shiri,".

Faruwar wannan Abun ba k'aramin Bata ran Aljani mardus, Yayi ba zaune yake cikin wani irin k'asum gumun daji Ank'awata fadarsa da Abuvuwan Alfarma

"Tuba nake ya shuga bana, wannan ba k'aramin hatsabibin Yaron bil'adama bane shine ya Hana na d'auko Yarinyar Kuma nakasa cutar Dashi, Danayi Yun k'urin ganin na hallakashi sai yazama na nine yake neman halakawa dawasu kalmomi da yake Fad'i,"

"Rufamin baki, banza ba gasharen Aljani Kawai k'aramin Yaron Bil'adama shine zai hanaka Aiwatar da aikina? Kasan me mutanen garin sukami? Jinjina Yarona durus Suka Yanka Suka barni da jininsa kawai Wanda sama da Shekara 50 yanzu Ruhin sa kawai ya ragemun, Kuma Muddin ban yanka wannan Yarinyar Yazira ba nayi Amfani da jininta d'aya bazai tab'a tashi ba, Da RUHIN sa kawai nakeda k'arfin tsafi Domin tin Yana ciki nagama mallakasa komai Indai ba Ruhin sa ba bazan tab'a iya yak'ar wad'an Nan bil'Adam d'in ba, Magana ta K'arshe kota yaya Akawo min Yarinyar Kuma shima Yaron A hallkashi, kuje da kamannu iri iri cikin garin domin halkasu,"

"Angama ya Shuga," bat wasu daga Cikin Aljanun suka B'ata,......

_BASEERATA ITACE ARZIKINA😍_

WhatsApp number 07064904617

*RUHIN JINN☠️💀😈*

_PAID BOOK #300 ONLY_

_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA..... And Other's BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P ANNUR PAID BOOK....(20) SAKACINA PAID BOOK.... (21) SO!!! FREE BOOK... (22) FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA PAID BOOK... (23) D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU PAID BOOK...(24) RUHIN JINN PAID BOOK
loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝```

_Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken_ *RUHIN JINN💀☠️😈👹 PAID BOOK 300 ONLY*
_Ina fatan yabada darussuka dama ilmantarwa Kamar dai yarda sauran littafaina suka bayar....._

_Wednesday 30/8/2023_

*Free 🅿️ 16 to 20*

........Safa da marwa Sarki Aruf yake zufa sai faman tsatstsafo Masa take, kallo d'aya zaka masa kasan Tabbas yana cikin tsantsar tashin hanakali,

"Yanzu meye mafita mlm"?

"Mafita d'aya ce A gaggauta hallaka wannan RUHIN JINN d'in domin Muddin Ruhin Yana Nan tofa saiya Hallaka Y'ar ka,"

"Kodai mu shirya runduna muje Yak'ar wannan *RUHIN JINN*,"

"Bawanda Yasan inda wannan RUHIN Yake, kuma Koda Wanda Yasani tofa Akwai Gagarumin bala'i da masifu ciki,"

"Koda Raina zai salwanta Zan iya kare Rayuwar Y'ata itace Kawai gareni Zan iya yin komai saboda ita,"

"Ashirya tafiyar Amma Kan Aje Ayi gangami domin Aje da manyan Jarumai, musamman wannan Jarumin daya ceci Y'ar ka,"

"Amma Ina zamu ganshi,"

"Bansani ba Nima domin Koda yaushe fuskarsa rufe take ba Wanda ya sanshi, Amma Inada Yak'inin zaije idan Kayi gayyatar domin Kai Sarki ne dole talakawanka Suma biyayya,"

"Magatakarda Aje Ayi shela Ace Inason ganin kowa da kowa dake wannan garin musamman maza,"

Cikin k'ank'anen Lokaci kuwa mutane suka taru k'ofar fad'a, harda Jalal

"Abunda Yasa na taraku Anan Shine, Zamuje neman *RUHIN JINN* Domin halakkashi ko masamu zaman lafiya da kwanciyar Hankali Acikin garinmu, dawa dawa Cikin Jarumanmu zasuyi wannan tafiyar,"?

Kowa shuru yayi mutane sai magana suke k'asa k'asa bawanda zai iya saka kansa cikin wanna masifar

Har sarki yacire Rai da Samun Wanda zaije, kawai saiyaga wani mutum fuska rufe da Rawani Yad'aga Hannu Alamar zashi,

Kowa kallonsa yake da mamakinsa Amma shi ko Ajikinsa

Can dai daga baya Aka sake Samun manyan matsafa da Jarumai 5

Kowa ya watse Ana mamakin wannan Sabon Jarumin,

Kowa yashirya tsaf Domin gudanar da tafiyar daga Ciki harda Yazaira domin tace saitaje,

Ak'alla Ansamu mutane sama da 100 Domin mafi yawansu Jaruman sarki ne, Jarumi Jalal ne Kawai bare, shikuwa dalilin Yarda yabisu domin Yasami damar gano mahaifiyar sa,

Tinda Aka fara tafiyar bisa dawakai Aka nufe cikin manyan dazuka boka Harus shike Nuna musu hanya domin Acikin halwar tsafinsa tana Nuna Masa inda Ruhin yake Adajin, tinda suka fara tafiyar Basu had'u da Komai na cutarwa hakan yasa suka saki jiki,,...

"Wad'annan bil'Adam d'in sun nufomu Ya Shuga kuma da niyar k'ona Ruhin d'anka sukazo muje musamesu mu hallakasu ne Yashugaba,"

"RUHIN baya ta wannan Dajin Tabbas nasan sunsan da Hakan Dan haka kuje ku Hallakasu ku kawomin Yarinyar"

"Angama Shugaba"

Firrr Aljanun Suka watse

...............

Suna cikin tafiya sukaga wasu manyan karnuka manya manya suntare gabansu ko wanne kare d'aya d'auke da Kai 7 Hak'oran su kuwa zago zago halshensu har tab'a k'asa yake,
Dukansu sun razana Amma Banda Jalal domin Yasaba Arba da Irin wad'an nan

Tsayawa sukayi Aka Soma kallon kallo tsakaninsu,

Takobbansu suka zare tareda sakin linzamin dawakansu suka nufe karnukan cikin zafin nama,

Ganin Hakan Yasa Suma karnukan Sukayo Kansu Cikin mugun nufi.............................

_BASEERATA ITACE ARZIKINA😍_

WhatsApp number 07064904617

*RUHIN JINN☠️💀😈*

_PAID BOOK #300 ONLY_

_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2

Please Login or Register in order to submit comment