Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA..... And Other's BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P ANNUR PAID BOOK....(20) SAKACINA PAID BOOK.... (21) SO!!! FREE BOOK... (22) FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA PAID BOOK... (23) D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU PAID BOOK...(24) RUHIN JINN PAID BOOK
loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝```

_Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken_ *RUHIN JINN💀☠️😈👹 PAID BOOK 300 ONLY*
_Ina fatan yabada darussuka dama ilmantarwa Kamar dai yarda sauran littafaina suka bayar....._




*FREE 🅿️ 21 to 30*

_SECOND TO THE LAST FREE PAGE IN SHA ALLAH_

*IDAN KINA KANA SON WANNAN LITTAFIN DAN ALLAH KU DAURE KU BIYA DOMIN FREE BOOK 300 NE KAWAI, IDAN KIKA SIYA KIKA FIDDAMUNSHI WAJE KO KIKA KARANTA BAKI BIYA BA KEDA ALLAH KAWAI ZANCE*



.......Suna had'uwa Aka kaure da Azababben Yak'i k'ara maza suke saki suna sulalewa k'asa domin karnukan Aljanu sauya kamanni kawai suke,


Hira sama karnukan suke suna kaimusu mugun Suka da Wad'annan kaifafan Hak'oran nasu Wanda dasu suke sukar mutum A wuya saiya fito tagefe,


Saidai kaga mutum ya Fad'o k'asa matacce


Al'amarin da ya d'aga Hankalinsu kenan musamman Ginbiya Yazira,


Ganin karnukan suna neman hallaka Rabin mutane Abun ya fusata Jarumi Jalal, Ta kobinsa Yasa Yasoma Ragargazasu duk inda ya nufa Saidai kaga gawakin karnukan suna bajewa matacci,



Wani karen ya daka tsalle cikin Mugun nufi daniyar hallaka sarki,


Cikin zafin nama Jarumi Jalal Ya Hira Kan dokinsa Yayi sama tare da soke Karen A wuya, Dukansu biyu Suka rikito K'asa Karen kuwa ko shurawa baiyi ba ya mutum,

Ragargazasu Ya cigaba dayi Cikin k'ank'anen lokaci ya hallaka Rabin karnukan Sauran suka gudu,




Zama Sukayi suna maida numfashi, Cikin matik'ar gajiya masu Rauni Aka soma musu d'inki, wad'an da Suka mutu Akayi musu sallah,



Zaune yake can gefe shik'ad'ai Yana tinanin ko mahaifiyar sa tana Raye?


Kowa cin Abinci yake Amma Bandashi,



Ahankali ta zauna kusa dashi Had'id'a cewa"Yakai wannan sadaukin jarumin shin meyasa kowa yanacin Abincin Amma Kai tinani Kawai kake meke damunka ne?, Shin meyasa kake b'oye fuskarsa garemu sai ceton Rayuwar mu kake Amma har yanzu basamun fuskarsa karka ba Kuma baka bamu Daman yimaka godiya ba,"



Murmushi Kawai yayi Wanda taji sautin fitar sa,

"Ni duk Abunda zanmuku Dan Allah Nayi banyi taimakon Dan ku godemin ba, watak'il Agaba Zan iya bayyana A gareku, Abinci Kuma na k'oshi ne, zaka iya tafiya,"


Daga hakan ya juya baisake magana ba Kuma baisake kallonta ba,




Al'amarin da Yayi matik'ar Bata mamaki Kenan, domin tanada matik'ar Kyau Wanda maza da yawa suke fatan Koda magana da itane balantana ta kulasu, shi Wannan jarumin waye shi? Abunda takeson sani kenan,





Safiya na wayewa suka sake cigaba da tafiya, A Yanzu shine gaba sai boka da sarki da Yazira gefe Sauran dakarun suna Baya,


Sunyi tafiya Sosai Amma Basu had'u da Komai ba,

Boka Yace"wannan Dajin da zamu Shiga fitinannen daji ne domin Yanada Aljanu kuma Akwai miyagun namun daji Kai bama Za'a rasa mutane matsafa masu cin naman mutane ba, Kuma A cikin dajin ne zamu gamu da Aljani Hardas shi d'in musulmi ne kuma da mun had'u dashi shine zai kaimu inda har Aka b'oye *RUHIN JINN* Saidai wannan Dajin dole Musa ran Abu biyu mutuwa ko rayuwa, Tabbas wasu zasu dawo wasu kuma zasu mutu, Kuma Za'a iya rasa kowa Duka mu mutu, A wannan Dajin tsafi baya Aiki domin ko Aljanun ciki basa Aiki da tsafi Saidai k'arfin dantse, basai nayi muku bayanin k'arfin dantsen Aljanu ba kuda kanku kunsan Cewar Sawun giwa Ya taka na rak'umi, Allah ya bawa Mai rabo sa'a muje,"

Yana Gama maganar Ya nausa cikin dajin, basuda zab'i Suma Dole Suka bi bayansa Amma cikin tsoro,..........................




_BASEERATA ITACE ARZIKINA😍_



WhatsApp number 07064903617

*RUHIN JINN☠️💀😈*

_PAID BOOK #300 ONLY_


_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA..... And Other's BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P ANNUR PAID BOOK....(20) SAKACINA PAID BOOK.... (21) SO!!! FREE BOOK... (22) FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA PAID BOOK... (23) D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU PAID BOOK...(24) RUHIN JINN PAID BOOK
loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝```

_Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken_ *RUHIN JINN💀☠️😈👹 PAID BOOK 300 ONLY*
_Ina fatan yabada darussuka dama ilmantarwa Kamar dai yarda sauran littafaina suka bayar....._





*1/9/2023/ First September Friday*



_last Free page in Sha Allah, Free page ya k'are idan kina so kana so ka biya ki biya 300 ne kawai, Ina K'arawa Cewa duk Wanda ya siye littafina ya fiddamun waje ko Kika karanta Baki biyaba keda Allah kawai zance....._




...........tinda Suka shiga dajin Suka soma ganin Abubuwa kala kala Wanda ko ba'a fad'a ba kasan Aljanu ne Saidai ba Wanda ya tunkaro su, Saida sukayi Rabin Dajin suna daf da Isa tsibirin Aljani Hardas, Wasu Irin manyan Halittun suka bayyana gabansu, masu kauri da girman gaske bakinsu duk jini, Hannayensu d'auke da manyan Takubba, sai wani lashe Baki suke Domin sun Sami kalacin rana suke gani,



Iya tsorata sun tsorota Kamar su ruga baya Saidai ba dama domin k'awanya suka musu,



Kansu sukayo Cikin mugun nufi,


Take A kacame da Azababben Yak'i kowa k'ok'arin kare Rayuwar sa Yake, manyan Halittun sun musu rufdugu domin kuwa d'aukar mutane suke kamar fari da sun d'auka sujefa Baki lumm d'aya su had'iye mutum Saidai su watso k'ok'on Kan mutum da k'asusuwa waje,


Wannan Abun ya d'aga Duka Hankalin su domin kuwa cikin k'ank'anen lokaci Suka Soma yimusu kisan gilla Koda suka Ankara suncinye fiye da rabinsu,


Al'amarin da ya harzuk'a sarki da Jarumi Jalal Kenan suka Soma Kai martani Cikin zafi suna kiran sunan Allah suna Yak'in


Yana zuro Hannu Yasami nasarar d'auke Yazira ya bud'e wagegen bakinsa Yana niyar had'iye ta Duka,

Ihu ta sandara Wanda ya Janyo Duka Hankalinsu gurinta,


Duka sukayo Kan wannan dodon ganinsu yasa Hannunsa ya d'auke dokin sarki Yayi jifa dashi suka Fad'i k'asa, dokin Kam ya Bugu sosai Anan ya baje sarki kuwa Ihu yasaki domin bayansa ya daku da k'asa shima Anan ya Suma,


Maida Hankalinsa Yayi gun Jalal haryanzu baicinye Yazira ba tana hanunsa Amma tsabar Rik'o da wahala sun sakata mugun laushi,


Da Hannu d'aya yake neman Kama Jalal shima ya Hallaka shi Amma Jalal sai zillewa yake ganin Yana neman wahalar da shi yasa ya bud'e Baki daniyar cinyeta, Anan ne Kuma Jalal ya Sami Daman daka tsalle yayi sama Ya fad'a Kan dodon, Yad'aga takobinsa sama ya k'walla kabbara sannan ya lumawa Dodon ita A tsakiyar Kai

Jini yayi tsartsi takobin talume cikin kanshi, wani irin Azababben Ihu yasaki yayi baya zai Fad'i tini yasaki Yazaira k'asa tayi zata Fad'i tana kurma ihu domin ba k'aramin nisa ke tsakanin dodon zuwa k'asa ba Ganin hakan yasata kurma Uba ihu,



Cikin sauri ya biyota Cikin Ikon Allah yasami Rik'o hannunta tare da kama wani reshen Icce suka mak'ale sama suna reto, Sosai ta rungume shi, shikansa yaji rungumar, nauyi sukama Rashen tini ya b'alle duka suka rikito K'asa tinkan sukawo k'asa Yazira ta sume,

Sake rungumar ta yayi tare da rik'e wani iccen duk Hannuwansa sun fashe jini Yana zuba da k'yar Yasamu ya haye iccen duka, A Hankali ya sauko da ita k'asa,

Ajiyeta gefe yayi Yasake d'aukar takobinsu Yakoma inda Sauran suka sake kacamewa Da Yak'in,


Cikin tashin sa'a d'aya daga cikin dodon Yasami nasarar lafta Masa sara A KAFAD'A ihu yasaki tareda ja baya jini ya tsartu gurin, k'arfin ihunsa Saida ya tayar da sarki da Yazira daga Suman da Sukayi,


Rigar jikinsa ya yaga da k'arfi ya d'aure Kafad'arshi tamau cikin dauriya irinta zaratan Jarumai Yasake fad'awa tsakansu A Yanzu ya fusata Cikin Ikon Allah yasami nasarar k'arar da dodannin duka,


A lokacin kuma ya zube k'asa da guiwarsa Yana maida numfashin wahala,

Cikin sauri sarki da Yazira sukayi kanshi Sarki ne ya kamashi Yana mishi sannu,


"Kada kudamu bawani Ciwo bane ai kuje ku huta kawai," mik'ewa Yayi da k'yar yanufe dokinsa ya d'auko wata jaka ya Ciro zare da Allurai Yasoma yiwa kanshi d'inki, saida ya d'inke duka Sannan ya shafa magani Akai ya Sami wata rigar ta d'aya daga cikin wad'an da suka mutu yasaka ya koma gefe yayi Zaune Abunsa Yana Jin zafin ciwon nasa,



"Abba Anya wannan mutum ne kuwa,"?
Yazira tayiwa Abbanta tanbayar



"Ni kaina tanbayar da kemun yawo A K'wak'walwa Kenan Amma na rasa mai bani ansa," Cewar sarki




Dariya boka mulkas yayi Yace"Tabbas mutum ne ba Aljani ba Amma sadaukin jarumine Shine Mai k'arfin dantse, Yasami Horo da wannan k'arfin ne duka wurin MLM Bukar, kuma taskar tsafi ta nunamin wannan Shine Zaiyi nasara A wannan tafiyar Kuma Yazo ne Dan mahaifiyar sa da Aljani marbas ya sace sama da Shekara 45 yanzu haka mahaifiyar sa tana Hannunsa, kuma shi Aljanin bazai iya Kai Jalal k'asa ba Saidai suyi ragas ko mutuwar kasko domin Yanada tsari sosai Aijikinsa,"



Duk maganar da suke tattaunawa Jalal yanaji duk da sunada tazara sosai,


Tasowa yayi Yadawo kusa Dasu Yace"Yakai wannan bokan kana nufin mahaifiyata tana Raye,"?


Duka da mamaki suke kallonsa musamman Yazira da Sarki Domin A Yanzu sun Soma tsorata da Lamarin Jalal,


Boka kuwa baiyi mamaki ba Domin yasan mlm Bukar Sarai shiyasa Sam baya mamakin duk Abunda Jalal zaiyi,



"Eh mahaifiyar ka tana Raye Amma tana kogon Israt can kusa da bangon duniya, inda take bawani mahaluk'i bil'Adam daya tab'a Shiga ciki mahaifiyarka ce kawai bil'Adama ta farko data tab'a Shiga ciki, Kan wannan kogon ko Aljanu basa iya Shiga ciki A Yanzu, ko shi Aljani mulk'as da Yasami nasarar Shiga ne Saboda Y'ar wani sarki daya yaudara ya Aura kawai Yayi Amfani da ita yashiga yakai mahaifiyarka ciki ya baro, yana fitowa ya kashe Matar, yanzu bazai tab'a iya komawa saida D'ansa Yazab Kuma shine mutanen sarki suka Hallaka yanzu shima Yana son dawoda wanna *RUHIN JINN* Domin komawa idan Kuma tada Ruhin Bai Samu ba to Lalle Yana Neman d'auke wannan ginbiya Yazira d'in domin komawa ciki, shine yake kawo Mata Hari lokuta da dama Amma kaine kake ceton Rayuwarta,"



"Yanzu boka taya Zan iya zuwa inda wannan kogon yake,"?


"Bawani dayasan Hanyar face Aljani Hardas kuma Shine Zamuje gurinsa idan munje saika masa tanbayar, kutashi mu K'arasa domin Wancan duhuwar Anan Aljani Hardas Yake,"




"Yanzu boka munkawo Amma baka fad'a muna ba," Cewar sarki



"Babu Buk'atar Dogon surutu muje kawai,"



Tashi sukayi suka nufe wannan duhuwar. Saidai Kash Rashin sani yafi dare duhu da sunsan Abunda ke lab'e cikin duhuwar da basu Nausa Haka kawai ba,


Suna Shiga sukaci Karo da Wasu Manya manyan kunamu bak'ak'e wulik girman su zasu iya d'aukar giwaye 3 A bayansu,


Cike da tashin Hankali suke kallon kunamun,

"Amma boka baka fad'amuna wanna Bala'in dake cikin Wannan duhuwar ba da munzo da Shirinmu" sarki Yayi maganar cike da tsoro



Dariya boka yasaki"kana Sarki Amma kacika mugun tsoro to wad'annan kunamun bawani makami da ke iya Hallakasu Abu d'aya gudu idan kanada gudu zaka tsira domin su wad'annan kunamun basa gani makafi ne, Saidai duk Wanda yabari suka kamashi to Wllh k'onewa zaiyi tamkar takarda domin tsananin gubar da ke jikinsu da ita suke hallaka mutum, ko daga munwuce wad'annan kunamun mun iso halwar Aljani Hardas Kenan magana tak'arewa kowa ya ceci kanshi,"


Yana gama maganar ya falfala da Azababben gudu, suma rufa Masa baya sukayi,


Aikuwa kunamun najin motsin su Suma sukayi kansu da Sunsami damar Kama mutum zasu saka K'arinsu su soke mutum take zai k'one kamar takarda Yadawo toka inda ko k'asusuwansa ba'a samu,



Wannan Abun yayi matik'ar d'aga Hankalinsu musamman sarki gashi basuci Rabin tafiyarba Yafara gajiya Kuma yana Ganin mutuwa gafdashi,

Anacikin wannan halin Ginbiya Yazira tafad'i k'asa Ihu tasaki tasadak'ar domin tasan Yau mutuwar ta tazo gashi ba damar taimako, Aikuwa wasu daga Cikin kunamun suka Mata K'awanya................




*SHIN MEZAI FARU? GINBIYA YAZIRA ZATA TSIRA KUWA? IDAN ZATA TSIRA WAZAI KUB'UTAR DA ITA? SHIN ZASU SAMU DAMAR D'AUKO RUHIN JINN D'IN KUWA? SHIN JARUMI JALAL ZAI SAME MAHAIFIYAR SA RAYE KUWA? SHIN ZAIMA SAKE HAD'UWA ITADA NE? YAYA ZASU K'ARE DA ALJANI HARDAS ZAI TAIMAKE SU KUWA? SHIN WANE IRIN GUMURZU ZA'AYI DA ALJANI MULK'AS? WAIZAIYI NASARA WAZAI FAD'I??? HUMMMMMMM NIMA DAI MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱 QUEEN OF WRITER 📝 HAUSA NOVELS 📚 BANA CEBA AMMA DAI DUK MAI SON SANIN YA ZATA KAYA TO YA KASANCE DANI DAMA BIYAN 300 D'INSA KACAL DOMIN JIN WANNAN K'ASAITACCEN LABARIN NAWA MAITAKEN RUHIN JINN☠️💀👿👹, NICE DAI TAKU HAR KULLUM MAISON GANIN FARINCIKINKU WATO MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱 QUEEN OF WRITER 📝*





_BASEERATA ITACE ARZIKINA😍_





WhatsApp number 07064904617 or 07031012948














An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2

Please Login or Register in order to submit comment