Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abunta.



WASHE GARI

kamar kullum da asussuba Ameenatou ke tashi dibo ruwa saboda tafiya makaranta.

Duk yan garin Ana idar sa salla suke fita diban ruwa.

Lantana da Furera ne suka biyo mata yadda aka saba.


Furera ta ce, "Goggo kiyi sauri mu tafi kin ga mu ka tsaya ba zamu samu da wuri ba."


Ameenatou ta ce, "Wallahi tallahi na rantse sai na yi kashina baku isa ku hanani kashi ba,kuma na kama layi ai tun dare dan haka wallahi sai mun diba ba wanda ya isa ya hana."


Ta karasa maganar tana shigewa bandaki


(Wannan kashin gado kenan,dan kullum goggo in ba tai kashin nan da asuba ba to ba kwanciyar hankali)


Tana shiga ji kake bututu bututu ga shegen bala'in wari da ya kaure gidan.

Ban da toshe hanci ba abun da su lantana ke yi.


Can sai gata ta fito tana nishi.

"Dilla can ku bude hanci ai gwanda nawa kashin ma akan na innoninku mai warin jaba."


Bakoti ta dauka suka bita abaya kawai.


Suna zuwa wajem diban ruwa Ameenatou tai kane-kane ta matsar da botikan mutane tasa nasu..


Adamu ya ce, "haba Ameenatoun ba ki ga layi ake bi ba ne?"

Kan ya karasa magana Washa ta ce, "kam bala'i wallahi ba ki isa ba aradun Allah in kinga su suna tsoron ki da masifar kakarki to wallahi ni na keresu."


Ameenatou ta kallesu sama da kasa ta ce, "in kuna son zaman lafiya ku bar ni na diban ruwannan ko kuwa ayi ruwan bala'i da masifa a karkarar." Ta karasa maganar tana daura dammara da dan kwalinta.


Ganin Washa bata ma san tana yi bane yasa Ameenatou kama hanya domin tasan tana kara magana zata iya domkota.



Kofar gida taje tana kwallawa kaka kira, kaka na fitowa Ameenatou ta fara kuka "Kaka kin ga wani Washa za ta ce ma munafuka jikar munafuka?"

Ta kara fashewa da kuka

"Dan kawai na....

Kan ta karasa kaka ta ce, "Jar uba!

Kara cino cinin bakin nan nata tai alamar za ayi masifar karshen zamani

"Muje na ce muje sai ta fadamun yadda akai ta mai da mu munafukan."


Suna zuwa Kaka ta bokatan kowa ta sanya na Ameenatou kan rike kugu tana, "Yawwaa gareki Washa kike ko washo? In ma masai kike to aradu ahir dinki da jikata kije ki tambayi kakar uwar kakarki da Ni Indo Sale da Ubanta mai fitsarin kwance nai munafurci ba da ku ba,yo ke har ma kuna da bakin magana daga kakannin naku har iyayen naku daga mai fitsarim kwance sai kashi awando,uwar uwarki ma yaushe yaushe ta gama cin tasono a karkarar nan?"

Ameenatou da sauran yaran wajen ban da dariya ba abun da suke.


Adam ya katse kaka da fadin, "Haba Kaka ba ki san meke faruwa ba kawai zaki fara magana haka?"


Kaka ta zaro ido can kuma ta fara shekan majina, "Adamu ni ka ke ma tsawa a karkarar nan? Ni ka ke ma tsawa to wallahi kaje ka tambaya ko uwar ubanka ba ta isa ta mun kallon banza ba bare ta fadamun magana, kaf kauyenan an sani kune kamfanin faso,kakanin kakanku ma duk fason kafa ne ya kashe su tsabar tsiro.


Adamu na jin kaka ta fara jero jawabai ya kama hanya domin inya tsaya zata iya ba da Labarin danginsu kaf.


Tana face majina da zaninta tana, "Yoo ai sa ka tsaya dan gwanda ni ban gudu ran daren aurena ba yo uwar kakanka sai da aka kwana ana nemanta dan ragwanci."


Malam Hashimu ne yazo wucewa ya durkusa yana, "lafiya kaka?


Fashewa da kuka tai tana daura hannu aka

"Wai har ni.....

. Comments din ku shine karfin gwiwata🙏


*ALƘAWARI NA NA NAN BEST 3 COMMENTERS ZA SU KARANTA FREE IN SHA ALLAH,DUK WADDA TA SAI AMEENATOU KUMA ZATA KARANTA WANI LITTAFINA NA KUDI GUDA DAYA*

24/10/2021
_LITTAFINA NA KUDINE DUK MAI SO ZATA TURO DA KATIN 300 TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN TA MUN MAGANA AWATSP TA NUMBER KO KUMA ATURA TA ACCOUNT 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Acess Bank, THANK YOU OLL,SHARE& COMMENTS FISABILLAH🥰_

_*Urs Xayyeesherthuo🤍*_
[12/1, 3:24 PM] +2348037420816: °°°°°°°°° _*AMEENATOU*_
_('Yar Kaka)_


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_RUBUTAWA_
_*Xayyeesherthul-humaerath*_

_SADAUKARWA_
_*Nura Sada Nasimat, Allah ƙara Daukaka Oga.*_

_*Domin Farincikin ki kawar arziki irin albarka Ameena Abubakar*_

_NOBLE WRITERS ASSOCIATION ABAR ALFAHARI NA,NA GAIDAKU DUKA,SON SO FISABILLAH🤍_

_*LITTAFINA NA KUDINE NAIRA DARI UKU⚠️*_



*FREE PAGE-5*


_*KADA KUCE YA YI KADAN KUCE YA YI YAWA KUNJI🥺MAI YAWA ZAI ZO GOBE IN SHA ALLAH*_

_*Kalaman Soyayya*_
_Zan so ace ko da na rana dayane kaji kwatankwacin irin son da nake yi maka azuciya,ina sonka,ina kaunar,ina fatan kasancewa da kai har karshen Numfashi na_🤍💫



"Adamu zai kalla yacewa mayya? Abun ba ma ga Jikata kadai ya tsaya ba har da ni?"

Wiwiwi Kaka ta hwara zubda hawaye kai kace da gaske ne.



Malam Hashimu ya ce, "kai Adamu dawo nan lallai ka cika mara kunya, kasan wace Kaka kuwa agarinnan? Maza ka bata hakuri."


Adamu ya ce, "Baba Wallahi ban ce mata Mayya ba,cewa na yi fa....

Kan ya karasa Kaka ta katse da

" Na yi karya ko? Na ce na yi karya ko? Dazu ka ce mun Mayya yanzu kuma ka karyatani,to wallahi ko tsohuwar kakar,kakarka ba ta isa ta karyatani ba dangin masu faso,na ga ubanka yana yaro har satan goruba suke zuwa gonar malam mudi, Amman yau ni za ka ci ma mutunci." Ta karasa maganar tana kars fashewa da kuka ana shekan majina.



Malam Hashimu ya ce
"Kaka Dan Allah kiyi hakuri yarone bai san ke wacece ba, Adamu maza bawa kaka hakuri."


Adamu ya ce, "Dan Allah kiyi hakuri Kaka."


Fara share hawayen tai tana "Aradu yau ka ci sa'ar Hashimu ne,shi ma dan dai mun sha tsallaka katangar gonar mai gari da Da Kakarsa Jummala Auduwa satan mangoro ne,amman Aradu yau da kaji ajikin ka dan kuwa tamola zan da kai, maza in kaje gida ka cewa uwarka ya akaji da hakurin Kandala mai tambotse? Ko da yake ma dakyar in ta Santa dan ko mahaifiyarta bana jin tasanta, dake Kakar, kakar ta ce."


Malam Hashimu dai ya dau hanya batare da ya ce komai ba, gudun kar acigaba da tone-tone.


Ba yadda suka iya haka suka bar Ameenatou da kawayenta suka gama diban ruwa kaf har suka gama Kaka na tsaye tana surfa uban bala'i.


Karfe takwas Sun kammala shirin tafiya boko.

Ameenatou, Lantana,tare da Furera.

Ameenatou anci gazal daga gira har kunne,jan baki kuwa saman ido da baki kamar manja ita adole yar gayu, andaga wando zuwa iya gwiwa an dago safa fara saboda Aga safarta ta yan binni,kaf kauyen ita kadaice mai safar angayu da aka kawo mata daga binni.



Tafiya take tana wani juyi da rangwada.

Kai ku dakata ma aradu fures,lantus ku bini abaya ba zai yu inyi shigar yan binni ina jerawa da ku ba,sai kusa arainani ai."

Haka suka bi bayanta tamkar boodyguard dinta.

Can kuma ta kara tsayawa tana
"ni fa wallahi sai na sha mangoro kan muje bokonnan danni bana so muje da wuri yanzu wannan malamin me *wata mie si niem* (what is your name) ne a ajin ya cika iya yi ya ce sai munyi yaren turawa."


Furera ta ce, "Aiko na ga bishiyar gonar Baba Datti ta tsiro harda wa inda suka nuka fa."



"Nima na gani wallahi, kuma manyane."


"Munahikai shine baku fadamun da wuri ba? To aradu yanzu ko can zamu kuma kadan zan sammaku."


Nan suka kama hanyar tafiya gona.

Sunci sa'a kuwa Malam Datti ba ya nan.

Tuni Ameenatou ta dane kamar tsuntsu.

Cinkowa take tana jefamasu.

"Yawwa wannan ne na biyar kenan, Aradu sai mun tsinke goma ko ashirin."


Lantana ta ce, "Ameenatou wallahi ga Malam Datti nan Shikenan mun shiga uku inya kama mu wallahi mugune."

Furera kuwa ido ya yi rudu-ruɗu an rasa abun fadi ma.

Ameenatou ta masu tsawa, "Matsoratan banza da wofi to wallahi ba zan sauko ba sai na dibi rabona yo abun da in ya nuku ba zakka ake mana ba,ai gwanda mu diba rabonmu."


Ameenatou na zuba zance su fures kuwa anga ba yi an tsere.


Ji ta yi ana, "Kambala'i aradu yau Sai kinci Kuntsin Uwarki A karkarar nan."

_LITTAFINA NA KUDINE DUK MAI SO ZATA TURO DA KATIN 300 TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN TA MUN MAGANA AWATSP TA NUMBER KO KUMA ATURA TA ACCOUNT 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Acess Bank, THANK YOU OLL,SHARE& COMMENTS FISABILLAH🥰_

_*Urs Xayyeesherthuo🤍*_
[12/1, 3:25 PM] +2348037420816: °°°°°°°°° _*AMEENATOU*_
_('Yar Kaka)_


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_RUBUTAWA_
_*Xayyeesherthul-humaerath*_

_SADAUKARWA_
_*Nura Sada Nasimat, Allah ƙara Daukaka Oga.*_

_*Domin Farincikin ki kawar arziki irin albarka Ameena Abubakar*_

_NOBLE WRITERS ASSOCIATION ABAR ALFAHARI NA,NA GAIDAKU DUKA,SON SO FISABILLAH🤍_

_*LITTAFINA NA KUDINE NAIRA DARI UKU⚠️*_



*FREE PAGE-6*

_*INA MATUKAR BUKATAR ADDU'O'I DA GA BAKU NAN KU MA SU ALBARKA MASOYA🥰🙏KOMIN KANKATA KO GAJARTA KUMIN DAN ALLAH*_

_*KALAMAN SOYAYYA🤍💫*_

_"Ina ji ajikina cewa duk randa na daina sonka to numfashi na ne yazo karshe,ka sani ka kara sani in har zanyi numfashi to sonka na cikin raina ko ince rayuwata ma gabadaya, indai ana so bayan rai, tabbas zan ci gaba da sonka har bayan raina,tare da yi mana fatan kasancewar mu atare,shin ka san mahimmacin murmishinka gareni kuwa? tamkar yiwa makaho addu'ar budewar ido ne, misalta irin Farinciki da yanayin da zai shiga,to wannan kwatane a Farincikin da nake shiga aduk sanda na ga kana murmushi,bance ni kadai za ka so ba,amman ina da tabbacin zanyi kokarin cike duk wani gurbi da ke zuciyarka ta hanyar da ba za ka taba so ko tunanin kulla alaka da wata 'ya mace ba,Ina Sonka tamkar Raina! Ko ba yanzu ba kuma ba yau ba koda kuwa bana duniya ina fatan ka so ni kwatankwacin son da nake ma hakan zai matukar kara faranta mun rai Habeebiy Da'eeman ba iya suna bane ina fatan hakan akullum in sha Allah."_
_*Fisabillah🥰duk wanda yaji dadin kalaman ya kara mun àddua*_


A firgice ta jiyo tsabar firgita saura kad'an ta fad'o, duk da yanayin tsoro da ta shiga hakan bai ta yi laushi ba.

"Kai dai Malam Dattin nan ka fiye jaraba da rashin ha'kuri, daga kawai ka ga mutum saman bishiya sai ka fara zage-zage, kamata ya yi ka samo tsafga ka ce keee uban me kike yimin a saman bishiyata, Ni kuma sai in ce bishiya ba ta uban wani ba ce tashen Allah ce sai dai mutum ya zama sanadi, na zo d'ibar zakka ce da ka gagara fitarwa, in kana iyawa sauko da Ni ka zane, sai ka kamo ni ka sauko ka fara duka, amma ka wani zo kana ta hayayaga ba."

Kamar yadda ta kawo shawara haka Malam Datti ya yi, domin kusa da shi ya samu tsafgar, yana shaud'a mata d'aya a duwawunta ,ban da ihu da tsalle, ba abun da take, sai da ya yi mata shida masu shiga jiki a na bakwan ne yana shaud'a mata ta shige cikin malun-malun dinsa, cakulkulu ta fara yi masa mai kama da yakushi, da ya kai bulalar da niyyar duka sai ta zille, kuka take wujiga-wujiga har da majina, hakan bai ya sa ta nutsu ba ta daina, ganin tana neman haukatar da shi ne yasa ya fara 'ko'karin cirota, sai da 'kyar ya cirota yana haki, ganin ta ku'buta da 'kyar yasa ta bawa wandonta iska, har ta yi nisa ta dawo ta kwashe magwonron da ke 'kasa ta kara gaba fitttttt.

Haka ta kama hanya tana tafe tana kuka harda majina tana kuma shan mangworonta kamar dole.

Lokacin da ta iso bokon an fara tarar 'yan makara, firifect d'in da suke tsarewar tsabar dariya ko tsaida ita ba su yi ba, ita d'in ma bata yi niyyar tsayawa ba, amma ta 'kuduri aniyar duk wad'anda suka yi mata dariya tun daga hanya har makaranta sai ta d'au mataki a kansu.

Tun daga nesa ta hango Malamin da ke cikin ajinsu, Malamin *wata mie is niem* ne a ciki.



Tana zuwa ta shige aguje kamar zaburarriya.

Tsawa ya mata yana, "You ba? You ba? U ar just coming now? Eheen I will deel with you in and out."

Kallon shi tai tana daura hannu aka , "Onkul Aradu I Noyin Going to bishiyar Dirimi, going to Bishiyar Mangoron Baba Datti kadai,kuma shi ma Kaka ta ce dan uwanmune Kakan kakanshi abokin makocin Kakanmune wallahi Onkul."


Uncle Ibrahim bai san lokacin da ya tintsire da dariya ba.

Can kuma ya make, kan ya ci gaba da cewa, "Oya Go Out, i said Go Out." Ya karasa maganar yana nuna mata hanyat fita da hannu.


Gatsinan Mangoron ta tai kan ta ce, "Sholly Onkul I noyin Karawa wallahi Na ce ma mangoro ne ba dirimi ba,kuma in zaka sha ma ga shi sai inje gida in karbo ma gishiri gun Kakata."


Ba yadda ya iya haka ya bar Ameenatou a ajin nan ta zauna dan inya biye mata ba za suyi karatu ba sai dai cikinsa ya kulle dan dariya da takaici.

Zama tai agefe su Furare na kallonta sai ta galla masu harara

"Onkul wallahi i no lyk botin yara,ni ka ce masu stopi kallo mie, ehee in baka haka ba na kama yara wallahi botin (bitin) din su zan kuma sai na haifosu ehee dan ina da cikinsu." Ta nuna su Lanata da hannu.


Kallon su ya yi ya ce, "Ku daina kallon mana sarauniyar turanci in ba so kuke ta kashemu da turancinnan ba."
Wani dadi Ameenatou taji adole ance mata ta iya turanci kara washe bakinnan tai tana damkar mangoro.

"Oyaa Class Wanene zai fadamun me za ace in Mutum bai da lafiya da turanci? Kun ga yanzu dai mu ka gama kuma duk wanda ya fada dai,dai zan mi shi kyauta." Cewar uncle .


Ban da zaro ido ba abun da suke suna kallon juna domin duk basu san me zasu ce ba.

Tuni Ameenatou ta daga hannu.




Uncle ya ce, "Oya Meena."

Ta tashi ta ce, "Onkul wallahi inna fada me kadai zaka ba wa kyautan ko?"


Ya ce, "Eh Go On."


Ta washa baki

"Ita Noyin Lafiya Wal."

Kallonta kawai ya tsaya yi.


"Onkul ba ka ce su tafa mun ba fa kuma na fada ai."

Dariya ya yi kan ya ce za su tafa miki amman Hausa da turanci kika hada ai.....

Kan ya yi magana aka biga bell din fita break.

Tuni suka fice suka bar sa tsaye mussamman Ameenatou da tayi wani irin tsalle.


Tsayawa ya yi kawai yana tunani duk da rigimar yarinyar shi kam birgeshi take sosai.


Ameenatou zama tai ta cigaba da shan danyen Mangoron ta kamar dole.

Furera da Lantana suka zo.

"Ameenatou dan Allah kiyi hakuri ba za mu kara guduwa miki ba."


Harara ta dalla masu kan ta ce, "e da kuka tafi kuka bari ya tsalamun duka a Duwaisatu na ba."


Furera ta ce, "Dan Allah kiyi hakuri Googo Ameenatou."



Ameenatou ta yi tsaki kan ta ce, "Banzaye jikokin masu sai da daddawa sai kuzo ku zauna ai."


Jiki na rawa suka zauna kamar iyayensu sun basu umarni.


Lantana ta ce, "Ni kam wancenn Onkul din na mun kyau yasin dama ya aureni ya kai Ni birni."


Ameenatou ta tabe baki, "tab wallahi bai kai onkul Al-ameen dinmu kyau ba Kaka ta ce fari ne sol kamar bature,ke tsaya ko son shi kike? Aradu in kina son shi mu tura mai sakon soyayya yadda na ga ni Film dinnan."






Lanatana ta rufe fuska "ni ysn ina son shi tom."


Ameenatou ta ce, "Fures dauko mana takarda da biro Aradu mun zama an binni ,zanna fada ku rubuta me za asa."


Furera ta dauko ta karda da biro.

Ameenatou ta gyara zama.

Yawwa rubuta" Salamu alaikom,dilla ma bani in rubuta ai nima na iya burutun ehee."

Nan ta fara.

_"Onkul aradu tonda nigganka nafaddarijiyar sonkkaninakefa danAllah ka sonnnikarka kacebakasona,inkakisonimituwa, zanyi,dagamasoyiyarka *lantus* kowar,fures,da,goghoameenatou,inajira,kajojjmuyi,aure,mutaibbinni._

Akayi zannen wata markadaddiyar HEART mai kama da ayaba agefe.


"Yesh wallahi ni yar binni ce yara na iya kalaman soyayya fa yanzu fures ki tashi muje mu kai,ke kuma Lantus ki tsaya amaryar onkul Ibrahim."


Suna zuwa Ameenatou ta ce....


_*BANA GANIN SHARHI FA😟KO A TSAYA NE?*_

_LITTAFINA NA KUDINE DUK MAI SO ZATA TURO DA KATIN 300 TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN TA MUN MAGANA AWATSP TA NUMBER KO KUMA ATURA TA ACCOUNT 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Acess Bank, THANK YOU OLL,SHARE& COMMENTS FISABILLAH🥰_

_*Urs Xayyeesherthuo🤍*_
[12/1, 3:25 PM] +2348037420816: °°°°°°°°° _*AMEENATOU*_
_('Yar Kaka)_


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_RUBUTAWA_
_*Xayyeesherthul-humaerath*_

_SADAUKARWA_
_*Nura Sada Nasimat, Allah ƙara Daukaka Oga.*_

_*Domin Farincikin ki kawar arziki irin albarka Ameena Abubakar*_

_NOBLE WRITERS ASSOCIATION ABAR ALFAHARI NA,NA GAIDAKU DUKA,SON SO FISABILLAH🤍_

_*LITTAFINA NA KUDINE NAIRA DARI UKU⚠️*_



*FREE PAGE-7*

_*KALAMAN SOYAYYA*_

_Kowasu Masoya Basa Da Burin Da Ya Wuce Kasancewar Su A Tare,Amman Ni Burina Ya Bambanta Da Na Su, Domin Kuwa,So Na ke Na Kasance A Zuciyarka Dukkan Bugun Numfashi, Ka Tuna Da Ni, Tare Da Sakin Murmushi A Fuskar Ka,Ina So Na Rayu Da Kai *RUHIY*_

_*SHARARRUN NOVEL GROUP,INA FARINCIKI TARE DA TAYAKU MURNA CIKE DA ALBISHIR CEWA ADMIN DIN KU TA SAI MAKU AMEENATOU DAGA FARKO HAR KARSHE ZA KU KARANCE KYAUTA🥰YO BAN MA SAN SUNAN ADMIN DIN TAKU BA FA (African Black Cofee)KUJI DADINKU KAMAR YADDA TA BUKATA*_

_______


Suna zuwa Uncle ya tsaya yana kallonsu kawai ganin Ameenatou na ta washe baki kuma ta kasa magana.

"Ah Meena Me ya faru? Ina fatan lafiya ko?"


"Uhumm uhumm Onkule dama Lantus ce ta aiko mu kawo ma wannan."
Ta mika masa.

Karba ya yi,ya bude.
Ya rasa ma ta ina zai fara karatun domin shi dama ba wata cikakkiyar hausa ya iya ba,bare kuma ta wa innan hamshakan.

Mika mata ya yi, "Karanta wannan yaren na ku ban iya ba ni kam."



Kara washe baki ta yi tana, "Wai cewa ta yi fa sonka take."


Cike da mamaki ya tsaya kallon Ameenatou kan ya kalli inda Lantana take.

Hada ido su ka yi ta yi wani fari da ido tana rufe fuska da Hannunta.


Murmushi ya yi, "owk to ki kirata kuzo office ku sameni."


Ameenatou harda tsalle ita mai hadin aure.

"Ke Lantus ta shi muje wallah yana sonki murna ma fa yake,wai kuma muje ofish ina ga ma maganar aurenku za ayi aradu."


Tuni Lantus aka tashi adole za aje gun masoyi.

Ameenatou ta ce, "Dilla mara kunya ba haka ana yi ba,tsaya ki ga nice agaba sai ke,sannan Fures a baya ,yanzu ai kin zama amarya, kuma tafiyar yan gayu za mu na yi har muje ofish din."


Tafiya suke suna karairaya kamar zasu balle,idon kowa a kansu masu dariya na yi.


Suna shiga ya kara sake masu wani hamshakin Murmushi.

"Yawwa maza ku shigo." Cewar Uncle


Ya kalli Lantana, "Ke ce ko?"


Washe baki tai tana kallon shi,ana murza ido.


Bulala ya janyo ta bayansa nan take ya bata rai.

"Maza kuyi nildon anan wajen."

Nan fa ciki ya fara durin ruwa.


Wani irin hadiyan yawo Ameenatou tai ganin zabgegiyar dorinar sai da hanjin cikin ya yi sufa..



"Onkul Wallahi Noyin Me,Lantana ce."

Lantana na kuka ta fara, "Onkul Kayi Hakuri wallahi ba ruwana, Ameenatou ce ta ce haka."


"Onkul wallahi ban da ni su biyune ka yi hakuri dan Allah." Cewan Furera.



Fara zabga masu bulalan ya yi yana, "ina ku bakwa da kunya? Wato kina sona ko? In zo muyi aure? Ke kuma meena ke ce mai hadin aure ko?"


"Onkul ka yi hakuri wallahi,na rantse ba ruwana ka yi hakuri,wayyo kwakwallar jikina zata fada, onkul kashi na ke ji wallahi zai fito,bulalar da zafi,wayyo duwawuna,wayyo jikina,kwakwalwata za ta fashe, kashina zai fito."

Ban da Sambatu ba abun da Ameenatou take tana ihu da kuka,tuni dalibai suka hadu suna kallo ban da sautin dariya ba abun da kake ji a makarantar.


Ameenatou na samun hanya a guje ta bar makarantar tana kuka,Lantana da Furera suka bi baya.



Gida ta shige ta baje a tsakar gida tana ihu.

"Wayyo Allah na Kakata na shiga uku, wallahi Onkul ya kashe ni,wayyo cikina kashin zai fito na shiga uku."



Kaka ta zaro ido tana, "wani ja'irin ya taba mun ke a karkarar nan? Tabbas yaro bai san zafin wuta ba sai ya taka yi shiru ka fadamun."


Tashi tai aguje ta nufi bayan gida sai da ta zubda kashin cikinta kaf sannan ta fito tana.


"Kaka Onkul Wata Mie si Niem ne ya dinga jibgarmu kaman sanayi taga dusar wake, wai kawai fa dan mun rubuta masa takardar soyayya Lantana na son shi.".


Kaka ta kyalkyale da dariya, "Yoo har ma kin sa na ji sanyi araina,ai ba haka ake nuna soyayya ba,zamaninmu lokacin da na ke son kakanki kin san ya nayi har ya fara sona?"


Ameenatou ta washe baki, "Aa fadamun Kaka."


Kaka ta gyara zama

"tunda na gan shi na ji cewa na fada a kogin son shi, Alokacin ina jin kunyarsa,sosai fa in fada miki,amman kawai sai Kakata ta bani shawara ta ce kullum in dinga wanka da kwalliya ina tafiyar yan mata ina rangwada aduk lokacin da muka hada ido kin san me nake masa?"


Ameenatou ta ce, "Aa yi sauri ki fada mun kaka."


"Hmm wani irin fari da ido na ke masa sai ya yi suman tsaye akwai ranar da tun da ya tsaya kallona ya kame har na tafi kwannan sa daya a haka sai da washe gari naje wucewa ya motsa,daga nan fa ya kasa hakuri sai ga Malam Mudi mahaifinsa agidanmu yana ataimaki dansa Aba shi ni in ba haka ba zai mutu,hmm Kakanki ya soni fa kamar zai mutu."



Ameenatou ta fashe da dariya.

"Kambala'iiiiiiiiiiiiiii ashe su kaka ansha soyayyar yan gayu yasin kaka yasha kallo dan yi mun inga."


Da Kaka tayi wani fari da ido sai da Ameenatou ta fadi kasa dan dariya.


Kaka ta ce, "ai wannan ma kadan na miki da na miki dayan suma zaki yi ina ga yarinya.


Ameenatou ta ce, "Aradu kaka kin iya soyayya, haka zamu na ma onkul amman wallahi yanzu sai. Mun rama tsafgennan da ya mana ba ci bulus ba."




Kaka ta ce, "Yoo ai kaf garinnan ni nake koya masu soyayya da duk wanda zaije zance sai yazo na fada masa abun da zai ce fa,bakiji wasu na ce mun Innar Soyayya ba,hhhh yarinya ni da SOYAYYA ai tamkar shan ruwa a modane,kin ga kakan me gari? Shi da babansa har dambe sukai zigidir akaina kowa sai ni,yoo ina zan iya niko nace Haliluna dan Amana kadai na ke so,ranar aurena kuwa ansha kuka gun samarin karkararnan da kam ta yi dadi arayuwa,chaaii inna tuna Halliru masoyi na kamar inyi kuka ana can."



Ameenatou ta ce, "Kaka Masoyiyar Halliru kenan."


Kaka ta galla mata harara , "Ja'ira bar ni ina kewar Halliru Masoyi Mussamman inna tuna yadda muke zuwa diban ruwa tare."



Ameenatou ta ce, "nikam na ji,yunwa nake ji kuma wallahi hum humm gobe sai Onkul ya yi bayani da larabci."


""""""""""""""

Washegari

Tare suke zasu tafi makarantar kamar kullum.


"Aradun Allah onkul bai ci banza ba,yau dinnan zaku ga me zan masa,kuma kaka ta fadamun yadda xa ayi ya soki wallahi sai ya aureki ehee."


Su dai su ka yi tsit suna binta da mamakinsu yau sune a makaranta tun karfe bakwai sun ruga kowa zuwa .

AMEENATOU ta shiga ajin ta kulle kanta tana, "kar ku shigo fa abu zanyi ehee ban ce ku shigo ba."


Sai da ta gama abun da take sannan ta bude suka shigo.

Ban da dariya ba abun da Ameenatou take,kuma taki fadin me ke faruwa kawai dariya take tana, "Walahi anjima akwai kallo."


Uncle Ibrahim ne ya shigo nan take ta bata rai ya kalleta yana masu dariyar kyeta.

"Ah yau kune da Safe haka? Kuma ba rigima? Lallai jiya bulala ta yi aiki."


Hararsa tai azuciyarta kuma tana fadin, 'aiki ma ai sai

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment