Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

komai a ciki". Da kyar aunty Hauwa ta shiga kusan sau uku tana shiga tana bazowa da gudu daga karshe dai tare muka shiga na juya baya nima tsorace tayi toilet din Habib na jiran mu a kofa sannan muk fito. Bayan mun kwanta wani irin kara muka ringa ji daga falo kamar kuka kamar dariya ba shiri na kara makalkale Habib Aunty Hauwa ta makalkale ni itama. A daren nan bamuyi barcin kirki ba. Kiran sallar fari Aunty Hauwa tace gida zata da kyar muka lalabata ta tsaya sai karfe shida Nima ban yarda an barni a gidan ba tare muka shigo mota aka kawo ta gida sannan muka koma. Wajejen karfe goma lokacin Habib tuni ya fita aikj zaune nake a Falo rike da waya ina chat da kawayena whatsapp amma sam ba a cikin natsuwa nake ba kallo daya zaka mun kq tabbar da hakan, "Salamu Alaikum" Naji ance durum! Gabana yayi mumunar faduwa Inna Indo ce ta shigo yau ma dai cikin dogon hijabinta fari har kasa. Fuskarta kam kallo daya nayi mata na kauda kai dan tsoro. Abun da ya dugunzuma hankalina shine ta ina matar nan ta ke shigowa bayan kuma yau ma na tabbata na makala kubabin gidan baki dayansu?. "Wa'alaiki salam" Na amsa sallamar hade da cewa ga waje zauna. Bayan ta zauna ne nace "Inna Indo naga na rufe gidan da kubobi ta ina kika shigo?". "Aa ni kuma ai a bude na ganshi leka ma ki gani a bude yake". Na tashi na dan rabe na wuce, abun mamaki kuma tabbas gidan a bude yake. bayan na dawo na zauna n naji tace "Ki daina barin gida a bude fatalwar nan da rana ma fa zata iya shigo miki gida". Nace "Wallahi nima na rufe". Sai ji nayi tace "Kin san me ya faru da matar da ta zauna a nan gidan ta biyu kuwa?". A dan tsorace nace "Aa". Nan take ta shiga bani labarin. "Bayan matar nan ta farko wacce aka tsorata ita da mijinta sun tashi. Sai wani mutum ya kama hayar gidan nan dan kasuwa ne shi sai karfe sha dayan dare yake dawowa gida. Yana da mata da yara biyu, Wata rana wajejen karfe sha dayan dare lokacin mijinta bai dawo gida ba yaranta kuwa tuni sunyi barci, Itama din ta kwanta har ta fara barci kawai sai taji kamar ana surutu a falo. To lokacin nepa basu kawo wuta ba. Fitila dayace kuma suke da babba. hakan yasa ta tashi ta sauko daga kan gadon ta dau fitilar nan ta nufi falo. Tana zuwa falo sai tayi curus sakamakon ganin wasu mutane biyu masu fararen kaya a zazzaune kan kujera sun juya mata baya wato bata ganin fuskarsu". Tuni tsoro ya rufe ni nace "Inna Indo kuma ba mijinta bane?". Tace "Tsaya kiji mana, Lokacin da ta gansu sai tsoro ya kamata cikin muryar tsoro tace "Su waye?". Maimakon taji an manta magana sai ji tayi su biyun sun gagabe da dariya, Tsoro ya rufe ta kamar zata ruga cikin daki a guje amma sai ta dake a tsorace ta kara furta "Su waye". Nan take taji sun kara fashewa da dariya kuma sai gani tayi su biyun sun mike tsaye a tare. Mata ne gashin kansu baki wul ya zuba kan bayansu kuma duk dogayen riguna ne farare ajikinsu. Matar nan taji sunyi shiru hakan yasa ta kara magana sai kawai gani tayi kawunan su sun juyo baya maimakon su waigo. Fuskokin su abun tsoro ba kyan gani domin sam ba irin fuskokin mutane ne da su ba. Wani irin dogon hanci ne lauyayye da shi bakin kuwa wangameme ga wasu hakora sun zuro daga ciki jini na zuba idanunsu kuwa jawur gasu da girma. Abun dai baya lissafuwa. ". Nace wayyo Allah na, basu kashe ta badai ko?". Tayi dariyar nan wacce tafi haushin kare ban tsoro hade da cewa "Ai tana ganin haka sai jikinta ya hau rawa ta koma daki a guje. Tana zuwa dakin ta iske wannan halittun a kan gado kusa da yaranta a kwance a nan wajen ta sulale kasa sumammiya. Lokacin da mijinta ya dawo ya tayarda ita kuwa ta hau rikici tace wallahi bazata kwana a gidan ba ta tashi. Ai kuwa haka akayi tun a daren ta kwashe yaranta suka bar gidan da safe sai canza gida mijinta yayi har yau bata ko yarda ta biyo ta nan kofar gida". Na sauke ajiyar zuciya hade da cewa "To ke kuma fa Inna Indo fatalwar bata taba tsorata ki bane halan". Tayi murmushi wanda ya karawa fuskar tata ban tsoro tace..................................

Zanci gaba

https://www.facebook.com/groups/1232550283531628/





↫ NI DA FATALWA! ↬

{gajeran labari}

Part {5}

@KINGBOY ISAH


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

(KU CI GABA DA HAKUR DA NI DAI. KUNSAN WAYATA BATA AMFANI SAI IN AKWAI NEPA. JIYA KUMA BA NEPA SHIYASA KUKA JINI SHIRU Autan writers ne)


Hade da cewa "Innah Indo ke kuma fa Fatalwar bata taba tsorata ki bane halan". Ta yi murmushi wanda ya fito da jajayen hakoranta waje, Fuskar ta wani yamutse abun tsoro sannan tace "Watarana ina zaune a tsakar gida bayan isha'i na gama tuwo na da miya ina jiran mai gidana kurum sai ji nayi an yi sallama. Lokacin na dai ji ana cewa akwai fatalwa a nan amma ban taba ganinta ba hakan ne ma yasa bani da tsoro a sannan. Na amsa sallama. amma sai naji shiru ba a shigo ba.Aka kara sallama na kara amsawa ba a shigo ba sai da akayi sau biyar ina tambaya wacece amma ba cikakkiyar amsa sai dai naji ance ni ce. hakan tasa na mike hade da daukar torchlight dita na nufi zaure na hahaska ko ina amma banga kowa ba har kofar gida na haska banga kowa ba. Kawai ina komawa sai naga wani abu fari kamar mutum a zaune wajen da na taso. Nan take jikina ya fara karkarwa domin nasan ba kowa a gidan kuma yanzu na ta so, Hakan tasa na bude baki a hankali nace "Mine ne a nan?". Sai ji nayi anyi wata yar guntuwar dariya. Na kara cewa miye a nan?. Sai gani nayi abu ya mike sama wai ashe fatalwar ce. Na juya a guje na shiga makwabta. Ina zuwa zauren gidan ta mukayi karo da ita itama ta fito a guje wai fatalwa ta je ta kwanta mata a kan gado. Ba shiri muka fito a guje. A ranar dai ba irin wahalar da fatalwar nan bata bamu ba tsoro kuwa har suma sai da nayi. Bayan wannan ma cikin dare in na fito fitsari na sha ganinta da fararren kaya a zaune ko a tsaye a tsakar gida. Ranar nan munje gidan biki mukayo dare wajen karfe sha daya muka taho ni da Makwabciyata muna tafe a kasai tsoro ya cika mu sai sauri muke a saitin makabartar nan a muka ga fatalwar da bakar doguwar riga abun tsoron babu kai a jikinta. Muka kara sauri ni kam dan tsoro kamar in tashi sama. lokacin fa ban tsufa sosai ba. Kawai sai ji mukayi fatalwar nan tace kai ku zo nan". Cikin duhun dare ai kuwa sai muka zabura da gudun bala'i ai kuwa fatalwar nan ta biyo mu. babu kai a jikinta tana kiran mu tana dariya". Wani motsi naji a bayana ai kuwa na daka tsalle hade da kwada ihu. domin nayi matukar tsorata. Inna Indo ta bushe da dariya ni kuwa ido wuri-wuri na kama kallonta. ji nayi tace naje na dan debo mata ruwa. nace to abun mamkin kafin naje kitchen na daukko mata ruwan ina zuwa sai tararwa nayi falon wayam. na leka waje naga gida a rufe. a guje na koma daki na kulle. Wayata na dauka na kira Aunty Hauwa duka daya ta dauka. "Hello lafiya dai Khadija ya naji kina huci? ko fatalwar ce?". Nace "Eh wallahi wata mata ce take zuwa gidana mai wani hijab fari dogo. in kin ganta abun tsoro ni wallahi inaga ma itae fatalwar saboda fa sai na kulle gida amma sai kawai na ganta a cikin gida, Kuma in ta zo ba labaran da take bani sai na fatalwa wallahi na fara gajiya". "Shegiya mahaukaciya maza dai ki tsaya a gidan nan naki fatalwa ta kashe ki. Ai ni wallahi ko a mafarki naga na sake bin hanyar gidan ki sai na tashi na yi addu'o'i da nafiloli. Wai ke me yasa ba zaki dawo gida bane? Ya zaki tsaya gida sai ke da Fatalwa". Nace "Aunty Hauwa ke kanki kinsan halin Abban mu wallahi in na zo gida a kan wannan dalilin dan banzan duka zai yi mun kuma ya koro ni. Gashi shi kuma Habib yaki fahimta ta ni wallahi addu'ah nake ma Allah yasa shima fatalwar nan ta tsorata shi nasan a lokacin zai gaskata ni". Karan kwankwasa gida naji da karfi hakan yasa na mike a firgice. daga can Aunty Hauwa tace "Miye akayi". Nace "Wallahi gida naji ana bugawa watakil ma fatalwar ce". Dull sai ji nayi wayar ta katse. Na sake kira na dauka network ne ke rawa wai ashe Jin nace ana knocking watakil ma fatalwa ce yasa auntu Hauwa ta kashe wayanta. A hankali na fito daga falo bayan na gama leke-leke kamar marar gaskiya. A lokacin dan kwakkwaran motsi zanji kawai in ara a na kare. daga bakin kofa na fara fadin "Waye? Waye?" Shiru naji ba ayi magana ba an kuma kara kwankwasa gidan. A zuciya nace yau na shiga uku wai ni me nayi wa fatalwr nan ne da bazata bar ni in zauna lafiya ba?". "Waye ne?". Na kara fada da karfi cikin fada naji Habib yace "Dallah can sarkij tsoro ki zo ki bude gida waye zai zo yanzu in ba ni ba?". Shima a tsorace na karasa a hankali na bude sai da na leka naga shin sannan na bude sauran kubobin. Dariya yayi hade da cewa "To sarkin tsoro ni wani abu na manta na zo dauka"? Nayi murmushi hade da cewa "Ba zaka gane bane habib sai ranar da fatalwar nan ta makure ka". Yayi murmushi hade da cewa "Malama ba wani fatalwa kawai dai tsoro ne irin naku in ma fatalwar ce ai ina da addu'ah". A zuciya nace "Baka san lokacin da abun tsoron ya zo ji zakayi kamar an mantar da kai duk addu'o'in ba kenan. In takaice muku labari sati daya nayi a gidan Habib cikin tsoro da fargaba wataran kullum kuma Innaa Indo sai ta zo gidan nan haka kuma kullum da kalar salon labarin tsoron da take zuwa da shi. Tsakar dare kuwa daga inga fatalwa a tsaye sai inga Fatalwa kusa dani a kwance. mafarkai kuwa gasu nan barkatai ba irin wanda banayi. na taba yin mafarkin munje cikin makabarta ni da Inna Indo wai tace in shiga cikin kabarinta ni kuwa naki shiga kawai sai ji nayi an tura ni ciki da karfi. Ni tsoro ba irin wanda ba a bani ba. Wataran inga bakar mage da jan ido tana kukan gadawaa wataran inga mage na tafiya ba kai. Yau ma kamar kullum Inna Indo ta zo ta gama zazzaga labaranta na abun tsoro ta tashi ta tafi. Ina zaune a Falo naji shigowar waya kawayena ne su uku suka ce gasu nan zuwa zasu kawo min ziyara ne.................

Hhhhh yan kawo ziyara, Allah yasa dai ku fice lafita.lol

https://www.facebook.com/groups/1232550283531628/








↫ NI DA FATALWA! ↬

{gajeran labari}

Part {8}

@KINGBOY ISAH


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


_GABA DAYA PAGE NAKU KYAUTA NA BAKU. INNA INDO ZATA ZO TAYA KU MURNA.LOL_

*✧✦✩UMMIEY ZEE✩✦✧*

*✧✦✩AUNTY ASY INDIMI ✩✦✧*
___________________________
Yanayin dariyar da take yayi matukar firgita ni bansan lokacin da n fara karkarwa ba bakina na rawa na fara ja da baya ina cewa. "Inna Indo dan Allah kiyi hakuri ki yafe mun". Wata gigitacciyar dariya ta daga kai sama tanayi jini ya fara zuba daga cikin idanunta. yayin da ni kuma naje karshen bango a lokacin da nake ja da baya din. Sai ji nayi ta daka mun tsawq duk falon ya dauka
nan take sai gani nayi ta zama hayaki al'amarin da ya kara rudani kenan, hayakin nan ya baje a tsorace na tashi na fara kokarin bude kofar falo domin dawowa tayi ta rufe da karfi. Ina cikin jan kofar da nufin in bude in gudu sai ji naji an kyalkyalewa da dariya na juyo amm banga ta ina ake dariyan ba domin ko'ina a cikin falon amsawa yake sama kasa da ma ko'ina Tsulum sai ganin Inna Indo nayi a sama kan iska kusa da fankar dake sama, cikin wata irin bakar riga mai baza hayaki na fita a karkashinta. gashin kanta ma ya mike tsaye wani irin bakin hayaki ke fita a ciki. Fuskar ta bakyan gani abun tsoro domin idanunta jawur suke kamar danja haka suke fito da wani haske ja. Hakoran ta kuwa sun kara tsayi da tsini gasu suma bakakke fuskar ta jagule ta zama abun tsoro. Magana ta fara da wata irin murya mai tsananin kara da ban tsoro "Hahahahaha Tabbas kin aikata babban kuskure Khadija da kikayi kokarin kona ni Indo Fatalwa. Kin aikata zunubin da ba zan taba raga miki ba bazan kuma taba ragawa duk wani wanda yace zai zauna a gidan nan ba". Cikin firgin ina kukan tsoro sai karkawa nake nace "Dan Allah Inna Indo ki yafe mun zan bar miki gidan yanzu". "Hahahaha kinyi kadan domin nan gida na ne dama baki isa ki fita a cikinsa ba yau sai na kashe ki. A nan aka binne gawata sadda na mutu ana cikin haka kuka zo kuka gina gida a wajen kabarina. Da kun samu ina raga muku shine har kika sama damar yunkurin kashe ni? hahahaha ko kin manta dama can ni matatta ce? Kin taba ganin gawa ta mutu? to bazan mutu ba. kuma daga yanzu ba wanda ya isa ya kara zama a cikin gidan nan ko na minti biyar gida ya zama mallaki na. don haka yanzu zan hallaka ki kamar yanda kikayi yunkurin hallakani". Tana fadar haka sai kawai gani nayi ta bace tsulum ta bayyana a gabana da hannu daya ta shake mun wuya ta daga ni sama a haka, harbe harbe na fara ina buge bug hannuwan n kokarin banbare hannunta daga wuyana amm ina kamar karfe hannun nata. In banda wata mahaukaciyar dariya ba abunda take. ni kuwa tuni lumfashina ya fara kokarin daukewa. A zuciya na yanke shawarr yin kalmar shahada domin dai yau na tabbata kwana na y kare. Nan take na fara karanto kalmar shahada tun sannan naji Inna Indo ta kwalla uban ihu. Ta kalle ni hade da kara zazzare mun jajayen idanunta. "Kiii... daki.... na... kar.. karatun... nan". Haka ta fada cikin in ina tana kara shake wuyana ni kuwa tuni idanuna sunyi jawur lumfashi ya fara daukwa. Nan take na tuno ayyutul kursiyyo. Ina fara karantawa sai ji nayi Inna Indo ta kwalla gigitaccen ihu ba shiri ta sake ni ta fadi kasa. Ina ganin hka cikin juriya da karfin hali na juya na bude kofa falo na fito a million har sannan da karfi nake karanta ayyatul kursiyyu. Na jigata sosai amma ganin na fito daga wannan gida baisa na fasa gudu ba. kafafuna ba takalmi ko dan kwali babu shi a kaina balle hijab. Ko da naga nazo saitin makabarta sai na kara kaimi wajn karatun kamar dalibar da aka karawa karatu take yi dan karta manta.
Ina karasawa bakin titi Allah ya taimake ni wani mai napep ya kawo kai na tsaida shi tun kafin ya karasa tsayawa na hau da sauri ina cewa muje muje. shima dai ya fahimci ba lafiya ba saboda irin figar napep din da yayi a guje. Muna cikin tafiya yace "Hajiya ina za'a kai ki? Da alama dai ba lafiya ba?". nace muje tawalala zaka kai ni. har a lokacin lekowa nake baya dan kar inje Inna Indo ta biyo mu. Muna karasawa tawalala a kofar gida ya faka a guje na fito na fada gida. Umma na zaune a bakin kitchen Aunty Hauwa kuma na cikin kitchen tana juya abinci. Ita ta fara ganina na shigo a guje na fada daki. Haba ai itama ihu ta kwala ta wullar da ludayin hannun ta ta fito dag kitchen din a guje kadan ta hana ta bige Umma dake zaune. Ina ban tsaya falo ba na tsallake sai dakin umm can kuryan gado na haye naja blanket na shiga. Aunty Hauwa ma na ihu ta fado ta shige cikin bargon. Banda haki ba abund nake. Umma ta fado dakin a rude "Kai miye wai? Khadija Lafiya". "Indo Fatalwa, Indo Fatalwa zata kashe ni Umma". Tambya take amma banda haka ba abunda nake cewa. kuma ban yarda na fito daga bargo ba. Aunty Hauwa kuw kar kudundunewa take. Umma ta fara addu'ah tana tofa mun da kyau na dai-daita na dawo normal. ina ji mi napep ya aiko aka karba masa kudinsa. Zaune nake gefan gado Umma a gefan damana tana mun addu'ah Aunty Hauwa a gefan hagun wai itama addu'ah tak na kuwa tabbata banda miyau ba abunda take watsa mun domin kuwa itama a firgice take. Kuka na fashe da shi na kwashe labarin duk abunda ya faru na gayawa Umma. Umma ta tafa hannu hade da yin salati. Na kara da cewa wllahi bazan koma gidan nan ba. Umma ta goyi bayan haka sai dai dady na take ji. Nima shi nak ji domin mutum ne mai tsatsauran ra'ayi. Har dare ba wani bayni bana rabuwa da Umma duk inda tayi ina biye da ita ina kuma karanta Ayyatul Qursiyyu dan ba dan itab da yau an kashe ni. Ina jin shigowar dady amma naki yardq ya ganni. haka mukaita wasan buya Umma ma bata gaya masa ba domin zai iya cewa sai na koma gidan Habib.
Misalin karfe biyar na asuba na farka sakamakon mummunar mafarki da nayi wai ga Inna Indo nan zata kashe ni ni da Habib. A gigice na tashi na yo falo a nan fa mukayi kicibus da Dady ya fito zai tafi masallaci. Salati yayi sannan ya kwalawa Umma mu kira. Tana fitowa yace "Me wannan ta zo yi gida naga alama ma a nan ta kwana da izinin wa? Mijinta ne ya kawo ta?". Cikin tsoro nace "Aa dady gidan ne da mtsala fatalwa ce a gidan shiyasa gudu zata kashe...". Tass! naji saukar mari ba shiri na hadiye maganar da ban karasa ba. Marar hankali da tunani kin dauka aure wasa ne da zaki fito daga gidan miji har ki kwana a wani waje bai sani ba? Oya shige muje ko masallaci bazan je ba sai na maidaki gida tukun kuma wallahi ki kuka da kanki in har na iske ran Habib a bace"..................................


_Kutt! Khadija ana maidaki Inna Indo zata sheke ki. Ko dan ai yanzu kin tuno da addu'ah_

https://www.facebook.com/groups/1232550283531628/



↫ NI DA FATALWA! ↬

{gajeran labari}

Part {9} *Last page*

@KINGBOY ISAH


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

_GABA DAYA PAGE NAKU KYAUTA NA BAKU. INNA INDO ZATA ZO TAYA KU MURNA.LOL_

*♡❥❥PHATEEMA ALIYU♡♡*

*♡❥❥AUNTY ZEETY♡♡*
_____________________________
Kuka na farayi ina rokon Abba yayi hakuri ya bar ni. Haka itama Umman mu tana masa magana amma kunnuwan shi kamar an toshe. Ya kama hannuna har cikin motar sa dake waje dama nan take kwana. Muna shiga yaja motar yayi gaba, Titin fayau mutane jefi jefi suke tucewa masu zuwa masallaci. Cikin dan kankanin lokaci sai gamu a kofar gida. A matukar tsorace nake har lokacin ban daina kuka ba domin nasan ba makawa Inna Indo ba zata kyale ni ba. Addu'ah na farayi yayin da dadi ya fara kwankwasa gida ya dan dade yanayi yaji shuru yana dan tura kyauren sai yaga ya bude ba a kulle yake ba. Bugon zuciyata ya karu tuni nq fara karkarwq a lokacin da Abban mu yace in shiga. Ayyatul kursiyyu na fara karantawa sannan na dan sama kwarin gwiwar shiga. Cikin sanda kamar barauniya haka nake tafe Abba na bina a baya. har muka isa falo. Abba yayi sallama kusan biyar amma ba muji an amsa ba. hakan tasa yace in je inga ko Habib din barci yake in taso shi. Tsuru nayi ina kallon dakin ina kallan dadi yayin da na fara in ina ina shirin yin kuka domin tsoron shiga nake. Sai da Abba ya daka mun tsawa sannan naci gaba da karatu na nufi dakin kirjina na dukan tara tara. tsoro ya dabai baye ni. Rufe idanuna nayi domin kar in bude dakin inga Inna Indo hankali na dora hannuna jikin kofar na murda a hade da tura kofar jin shiru yasa na bude idona ihu na kwalla da karfi na fara kiran Abba domin abunda na gani yayi matukar girgiza ni. Habib ne kwace cikin jini kamar matacce kanshi jini ke zuba haka jikinsa duk raunuka ne. Cikin hanzari Abba ya karaso da sauri ya karasa wajen shi. Kara kunnensa yayi a kirjin Habib din yaji zuciyarsa na bugawa. da sauri ya cicibe sa yayo waje ni kuwa banda ihu ba abunda nake zundumawa na bi bayan Abba. Ni na bude bayan motar ya saka shi sannan na shiga, cikin hanzari ya figi motar sai General hospital A nan Habib yake aiki Muna zuwa akayi gagawar yi da shi Emergency shi.Nan na durkushe a kofar banda kuka ba abunda nake. Abba kuwa ya rasa me ma zaiyi, Sai sintiri yake a kofar wajen da aka shiga da Habib din. Likitoci kuwa sai kai komo suke domin wasu duk abokan shi ne na aiki. Wajejen karfe shida da rabi wani dan gajeran doctor ya fito. Ni da Abba mukayi saurin tarbarsa dan jin ya jikin Habib. Ajiyar zuciya yayi sanan yace "To Alhamdulillah a gaskiya da ace kun yi jinkiri wajen kawo Dr Habib da an rasa shi. Amma yanzu masha Allah mun yi masa aiki in sha Allah ba wata matsala babban ciwon da yaji a kai ne sai dai anci sa'a abun bai taba kwakwalwarsa ba". Cikin kuka nace "Dan Allah ina so in ganshi". Dr din yace a yanzu ba halin ganin shi domin har yanzu akwai sauran likitoci a kanshi
sai nan da wani lokaci sannan. Ni da Abba mukayi sallah sannan ya kira Abban su Habib ya shaida masa suzo asbiti ba lafiya". Cikin kankanin lokaci sai gasu sun karaso a firgice Abban Habib sai Mamanshi da kuma Ibrahim kaninsa. Abban Habib ya fara tambayar Abban mu lafiya kuwa?. Abban mu ya kwashe duk abunda ya faru ya gaya masa.Da jin haka Umman Habib ta hau kuka. tana leka ciki inda Habib yake. Abban mu ya kira gida ya fadawa Umman mu sannan yace ta taho mana da kayan kari nan asibitin. Bayan mun kakarya har lokacin ba abada damar shiga wajen Habib ba. Ina jin su Umma suna hira wai a zargin su Yan fashine suka wa Habib haka.Ni kuwa ban kawo kowa a zuciya ta ba sai Inna Indo domin na tabbata ikirarin da tayi ba karya bane don nima kadan ta hana ta hallaka ni. Wajejen karfe biyu da rabi likitocin suka bada damar shiga. Muka shiga kowa kuka yake ganin irin mawuyacin halin da Habib yake ciki. Har lokacin bai farka ba balle mu san me ya faru da shi. A takaice Habib bai farka ba sai bayan kwana uku da faruwar abun. Ina zaune a gefansa Umman sa da Bintu kanwar shi suna zaune a kujeru banda tagumi ba abunda mukayi. "Wayyo Allah fatalwa". Abunda ya fara tashi da shi kenan. a gigice. ganin yana neman zare karin ruwan dake hannunsa yasa na fita a guje na kira wo doctor. har lokacin da na dawo ihu yake yana fadin fatalwa tayi hakuri

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment