Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

soma cewa zaki hora kan ki da yunwa, hakan bazai dawo da Zulai ba, saidai ya sanyata cikin damuwa. Maza karbi ki ci in je in nemo miki ruwan shayi mai zafi ki warware hanjin cikin ki”.
Ta karba ta ajiye a gefe ba don zata iya ci ba, sai don so take ya fita ya bata waje, she want to be alone tayi tunanin makoma ga rayuwar ta.
Zai fita kenan yaci tuntube da manyan bagco guda biyu, ya tsaya ya bude yana dubawa, sai ya ga duk wani kayan bukatar dan adam yana cikin wadannan jakunkuna daga na ci har na amfani. Cikin mamaki yace.
“Hansai, wannan kuma daga ina?”
A hankali ta kai idon ta ga kayan amma bata ce komai ba. Domin ta gane daga inda suka fito. Jakar farko sayayyar da kai mata unity ce ya ce inji Inna, ta biyun kuma wadda yayi a Albasu ce a hanyar su ta dawowa bata san ko wa ya yi wa ba.
Ajiyar zuciya ta kwace mata, amma bata ce komai ba.
Shima Kawun sai ya gane daga inda kayan suke ba tare da ta bude baki ta gaya masa ba. Ya jinjina kai yana mamaki yace.
“Sahabi ko?”
Kai ta gyada masa. Sai ya dawo ya zauna akan karaunin dakin yana fuskantar ta yace “Hansai, me ke tsakanin ki da wannan yaron ne?”
Kai ta girgiza masa da sauri alamar babu komai. Yace “a’ah Hansai, in kin ga kare na sunsunar takalmi dauka zai yi. Ni na gaya miki akwai wani abu a kasan ran sa game dake, amma lokaci zai fada miki idan ni baki yarda da ni ba.
Saidai kuma hakan ba mai yiwuwa bane domin bazan kai ki inda zaki wulakanta ba, ke ba uwa ba ke ba uba ba, don haka na riga na yanke hukuncin da zai fishshe ki, in ya so ni ayi ta haifomin jikoki zabiyan ina kula da abuna, dama Kakar mahaifinmu ma Zabiya ce, nafi kyautata zaton wajen ta kika gado".
Yana fita Hasna’u ta lula a tunani? Ko me Kawu yake nufi da cewa ya riga ya yanke hukuncin da zai fishshe ta? Ta ji dadin abinda yace da yace ba zai kai ta inda zata wulakanta ba, wanda ke nufin ba abinda zai rude shi ya sarayar da martabar ta, koda abinda yake hasashe din ya zama gaskiya akan Uncle Saheeb.
Wunin ranar zungur Hasna banda sallah ba abinda ke tada ta daga gadon bonon Inna. Bata tashi jin sababbin hawaye sai ta yi sujjadah. Bata ci komai ba tun safe har dare, tana ji Hajjo da Kawu na fada kamar zasu yi dambe da yamma da ya dawo wai tunda ya ce Hasna’u bazata yi talla da rana ba, to dole tayi mata tallan gyada a kofar gida da daddare ko a dandali.
Kawu yace “Kinsan Allah Hajjo? In kin ga Hansai ta yi talla, to ki tabbata bana numfashi”.
Tace “da ranka da lafiyar ka, da idon ka da jin ka, sai Zabiya tayi tallan Rogo da gyada”.
Ya riga ya san halin Hajjo, bata sa kanta abu ta fasa, shi yasa yau litinin ya ki fita kasuwa ya zauna a soro yayi shimfida, ya kunna radio ya aje tum-tum din auduga ya kishingida a kai, shi bai yarda ba gadin ‘yar sa yake kada a dora mata tallan Rogo. Kawu ya ce.
"Kasuwar ma na daina zuwa kowa ya ci uban sa. Rigima uban wa ta kashe? Nima rigimamme ne".
Motsi kadan Hajjo ta leko soro ta ga ko ya gaji ya tafi? Sai ta gan shi daram-dakam ya kunno jakar magori ko taskar labarai. Hussaini wanda shi kadai ke zuwa makaranta a gidan ya dawo da azahar ya gan shi a soro. Yace.
“A’Ah Kawu yau baka fita bane?” Yace ban fita ba din, kun bani ajiya ne? Ko kuna bi na bashi? Ko a kan ku nake zaune?” Hussaini yace "Allah ya bada hakuri daga tambaya? Ai ba ni nakar zomon ba, kuma ba nina kashe uwar Zabiya ba. Na lura tunda Zabiya ta dawo hutu kake cikin bala'i da kowa a gidan nan”.
Kawu ya rarumi takalmin sa ya maka masa yana cewa "uban ku zaku ci daga ku har uwar take mai zuga ku ku min rashin kunya". Hussaini yayi ciki da gudu yana kiran Hajjo. Hajjo tace "rabu dashi, mutuwar kanwar sa ta sa ya zama kansa da motsi. Ni kuma ba mai aje min zabiya a gida, Atika tazo haihuwa ta haifo min jika Zabiya saboda yawan ganin Zabiya. Dole yasan yadda zai yi da ita.
Wajejen karfe sha biyu na rana wata mota kanknuwa 'dark-blue' ta yi fakin a kofar gidan Kawu Samaila. Kawu yaji hucin motar (don sam bata kara) amma bai kawo gidan sa aka zo ba. An dauki mintuna kafin mai motar ya fito yana rufe kofar ta da keys din hannun sa, wadanda ke makale jikin wani kyakkyawan key-holder.
Ya isa soron yana sallama da wata lallausar murya. Kawu ya amsa yana zuqar turare mai dadi a kofofin hancin sa kafin ya ce.
“Wa nake gani kamar SAHABI!”
Ya rage tsawo yadda bazai buge da gajeriyar kofar zauren ba ya shigo yana fadin “ni ne Kawu, ba fa Sahabi bane sunan, har yau ka kasa fada dai-dai, SAA-HEEB”. Kawu yace "koma menene duk abokin Manzo yake nufi, shigo daga nan kusa gare ni ka zauna, ka sha hanya”.
Ya tsugunna har kasa ya gaida Kawu sannan ya zauna a gefen sa yace. “Yaya Karin hakuri Kawu? Kuma yaya Hasna'u ta kara ji?” Kawu yace “Ai na ga boni! Kai dai akwai ka da wayo, shine ka zame ka barni da jidalin Hansai, wallahi har goshi ta fasa. Yau kwana biyun nan bana jin ta ci abinci ko loma daya ne. ban taba ganin mai son Uwa irin Hansai ba”.
Da Kawu ya san yadda maganar ta doke shi da bai fada masa ba. Kwana biyu ba cin abinci? Ta fasa goshi? That delicate and fragile skin? Murya can kasa yace.
“Zan iya ganin ta Kawu? Ni in na bata abinci zata ci, idan na bata baki zata saurare ni”. Kawu "ya ce da na ga ta fara borin nan kamar na mai iskokai sai da na tuno ka ai, na ce da na sani kai ka gaya mata". Ya kwalawa Atika kira ta fito da sauri, idon ta a kan Saheeb, yace "maza kirawo min Hansai, ki ce tazo in ji Sahabi”.
Kafin ta kira Hasna’un sai da ta fara gayawa Hajjo ga wani dan gayemai mota ya zo wajen Zabiya. Hajjo tace “dadi na da ke Atika dabbanci, waye zai zo wajen zabiya?” Ta ce “Hajjo toh? Fito da kan ki ki gan shi”. Ai kuwa Hajjo sai ta yi lullubi ta je soron kamar zata leka waje neman yaro, ta gansu suna cin rogo da soyayyar gyada shi da Kawu. Ta ce.
“Gafara dai!” Kawu ya zabga mata harara shi kuwa Saheeb sai yayi kasa yana gaishe ta.
“Samari me kake nema? Ko ka yi batan kai ne?”
Kawu ya ce “a’ah makuwa yayi, kinsan kowa makakke ne irin ki, da auren ki Hajjo? Ki fito cikin maza ba iznin mijin ki?” Ta wuce ciki tana cewa “meye laifi na don na zo in gaya masa gaskiya? Ka san Zabiya abinda yasa ake haifar su a haka, an sadu da uwar su tana jinin al’ada”.
Ba Saheeb kadai ba hatta Kawu kunya ce ba ‘yar kadan ba ta kama shi mai tattare da bakin-ciki da takaici. Yana so ya baiwa Hajjo amsa daidai da wacce ta fada yana tsoron kada su raba abin fade a gaban bako mai daraja a gareshi irin Saheeb. Duk sukayi mata shiru, sai ta wuce ciki tana fadin.
“Ni dai na gaya maka gaskiya”.
Kawu yayi ajiyar zuciya Saheeb kuma ya sunkuyar da kai, Kawu yace “wato su mata duk girman su da shekarun su tumaki ne Sahabi. Banda haka da tuni na rabu da Hajjo domin zaman nan daka ga na yi gadin Hansai nake kada ta dora mata tallan rogo, yarinya gata nan kamar ta-kitse-ta-kitse in je ta narke a rana”.
Saheeb ji yayi nan duniya ba wanda ya tsana irin Hajjo, da yana da iko yau duka zai yi mata ko ya daureta har sai igiya tai rara kafin ta dorawa Hasna’u tallah.
“A tambayeta ko nawa ne cinikin rogon zan dinga bata kullum, amma don Allah don Annabi Kawu kada a daura mata tallan nan, fuskarta zata yi dabbare dabbare in ta sha rana ko kwaro ya cije ta, sannan basa jure zafin rana ko kankani”.
Kawu yace "ai na gaya mata 'sai bayan rai na' sai dai in daina fita neman abinci in yi ta gadin Hansai har zuwa ranar da zan daina numfashi”.
“Balle ma baza a yi haka ba, a kira ta muyi lissafi, duk sati sai in din ga kawo mata kudin tallan amma dole kaje harkokin ka kuma Hasna’u bazata yi mata talla ba, in ta dage wallahi Allah zan kai ta HUMAN RIGHT”.
Atika ta shigo tana zumbura baki tace “Kawu nayi-nayi ta zo ta yi min banza, na gaya mata saurayin tane ya zo amma ko kallo na bata yi ba, ina jin fa ta zama kurma”. Kawu ya rasa abinda zai raruma ya maka mata sai ya dauki rediyon sa ya saita bakin Atika da ita...Saheeb yayi maza ya rike rediyon, Atika ta gudu”.
“Ni dai na haifi jarraba, yara duk sun biyo halin uwar su na rashin iya magana, Hussainin dana ke dan jin dadin sa shima kwanan nan ya fara daukan halin su, dazu sai da ya gwaba min magana” ya soma matsar kwallah. Saheeb yana cewa.
“Kayi hakuri Kawu addu’a zaka yi musu ba kuka ba”.
Kawu ya tashi ya shiga gidan da kansa domin ya turo Hasna’u.
“Hansai na turo kizo kika ki zuwa ko?”
Ta sake rushewa da kuka bata ce komai ba. A wurin ta ta riga ta gama yanke alaqa da SAHEEB WAMAKKO, bata bukatar komai daga gare shi tunda yayi ZARAR BUNU..... ya haura limit din da yake kai na Yayan ta. Dama alakar tasu ta Yaya da kanwa ce, tunda kuma yanzu yace ba ita bace ai shikenan, itada shi haihata-haihata....
Masu iya magana sun ce "tsuntsun da ya ja ruwa... shi ruwa kan doka, ba zata jawowa rayuwar ta tozarci ba. Wanda ta fara gani a wurin uwar sa da kanwar sa kadai ya ishe ta misali".
Shima Kawun yayi maganar duniya bata tanka masa ba, yayi lallashin ya gaji, gashi bai iya zuwa ya ce da Saheeb ta ce bazata zo ba, a karshe yace.
“Ko dai gaskiyar Atika ne kin kurumce?” Ta motsa bakin ta a hankali tace “da kunne na!” Yace “to alhmdulillahi, sakarci ne abin kenan!”. Sai ya juya ya fita.
A zaure ya tadda Saheeb yana safah yana marwa yana naushin hannun daman sa cikin na hagu, Hasna’u kawai yake son gani da halin da take ciki. Wannan wane irin damalmalallen gida ne wadanne irin mutane zata rayu da su haka? Abu daya ya rage masa damuwa da ya fahimci Kawu Samaila tsayayyen mutumne akan ra'ayinsa matar sa bata juya shi amma a yadda ya fahimta gabadaya ‘ya’yan basu da tarbiyya.
Kawu y ace “biyo ni Sahabi”.
Ya bi bayan Kawu zuwa cikin gida ta kofar shiga sassan su Hasna’u.
****






HASSAN (DA GASKE WATA KUSAN TAFI WATA?)
Tana kudundune cikin zanin Inna a can karshen gadon bonon ta, rabin gashin kan ta ya fito, wanda ba baki bane gabadaya, a kwana biyu kacal tayi mugun ramewa, ‘yan idanun sun kara kankancewa daga ‘light-blue’ sun koma ‘ash colour’. Ba zaton ta ba tsammani, kawai sai ganin Uncle Saheeb ta yi a gaban ta.
Ya tsaya hannayen sa biyu zube cikin aljihu staring at her straight in to her eyes with so much sympathy and pity, bai zauna ba daga tsaye motsa baki yace
“HASNAH!”
Saukar muryar sa ke da wuya cikin kunnen ta da gangar jikin ta, sai ta ji duk wani rauni na duniya da maraicin duniya ya rufto mata….. ‘this is indeed a shoulder to lie on’, zata so ta kwanta a wannan kafadar… tayi kukan ta mai isar ta a inda ta san za’a lallashe ta a gaya mata mai dadi, amma babu dama tunda ta san ba muharramin ta ba ne ba. Kawu sai ya kasa tsayawa tare dasu ganin sai kallon juna suke bakin sun a motsi idanu fal hawaye, ya juya ya fita.
Saheeb ya tsugunna a gaban gadon bonon Inna yasa gwiwoyin sa a kasa, cikin raunin murya yace “pls accept my heartfelt condolence, Allah ya jikan Innar mu da Rahma….”. Ai kamar jira take sai ta kifa kai a jikin bango, ta bude sabon shafin kuka.
“Hasna’u come and cry on my shoulder…..idan kukan zai sa ki ji sanyi? Amma mafi a’ala, mafi fa’ida, mafi dacewa ba kukan bane, addu’a ce a gare ta.
Hasna’u da gaske yau kwana biyu baki ci abinci ba?”
Ta soma share hawaye da zanin Inna, tana sheshsheka irin ta wanda ya ci kuka ya koshi. Gashin kanta yake kallo mai kama da na tsofaffi amma sai yaji bazai taba cewa da ita tayi dying ba koda Allah ya cika masa burin sa na auren ta, zai zauna da ita (against all odds in her natural defect and abnormality) kuma zai gaya mata bakin gashin mata ba komai bane face irin nata watarana, suma duka fading zai yi, amma akwai lokacin da zai gaya mata hakan ba yanzu ba.
Bagcon da yayi mata sayayya ya janyo sai ya tarar ko tabawa bata yi ba, ya dauko ‘juice’ din ‘exotic’ da madarar ‘hollandia’ ya dauko kofi cikin kwanukan dake gefe a wanke, Inna sarkin tsafta ta wanke ta kife abin ta, babu ko ledar tsakar daki a dakin sai karauni, amma ko’ina kalkal yake sannan gadon su babu shirgi sam sai wani kodadden zanin gado, sun shirya kayan sawar su su cikin kwandon roba mai murfi.

Ya zuba jus din cikin kofi ya bata sannan yace cikin lallashi “akwai risho in dafa miki indomie?” ta bude idanu tana kallon sa kawai, yace “Hasna bazaki yimin magana ba?” Ta juyar da kai bata ce komai ba, mikewa yayi yana duba kayan wajen don duk wani kayan amfanin su Inna bata barin shi a waje, ilai kuwa rishon ta na nan, harda ashana a kasan shi, ya dau karamar tukunya ya zuba ruwan swan a ciki ya kunna, tun ruwan bai yi zafi ba ya zuba indomin da maggin ta, shi dai burin sa ta ci wani abu koda danye ne in dai zai shiga hanjin ta.
Kan minti goma indomie ta dahu ya juye a plate ya kuma kasha rishon ya kawo mata.
“Ki karba ki ci, in kin ki ki zan yi miki dura wallahi” ya aje plate din a gabanta yana kuma nade hanun riga.
Ba shiri ta karba ta soma ci kamar mai cin dussa, loma uku tayi ta ture don daci yake mata a baki, Saheeb ya ce “Hasna ko sai na baki a baki ne?” Ta daga ‘light-blue eyes’ din ta ta kalle shi, sai aka yi sa’a shima ya dago yana kallon ta. Murmushi ya sakar mata, murmushin da ya kusa narka zuciya da ruhin HASNA’U, ya haifar da wani ‘chemistry’ mai karfi a tsakanin su, ya kuma debo abinci akan spoon ya nufi bakin ta da shi.
Sai ta kasa wofantar da wannan kulawar a karo na biyu ta bude dan jan bakin ta ya saka mata abincin. A haka sai ga Hasna ta tashi da plate din indomie tsaf batare da ta san lokacin da ta tashi da shi ba.
Ya zuba mata ruwa ta sha. Sai taji gardin ruwan hannun Saheeb ya fi na kowanne ruwa da ta taba sha a rayuwar ta.
Yasa hannu a aljihun sa ya dauko galasses guda biyu a cikin akwatin su ya ce, “ga su na karbo, will you do me a favour ta wear it for you?” (Zaki yi min alfarma in saka miki?) Ya fada yana ciro kyakkyawan glass din daga gidan sa. Yace “in rana tayi zai yi duhu, in dare yayi ya yi haske, ki kula da su sosai su zama ‘companions’ din ki, barci kadai zai raba ku, sai ko wanka. Kin dai ji abinda Dr. Turaki yace in kika kula da sanya su kina girma ganin ki na kara gyaruwa”.
Ya sa mata glass din, kada kiso ki ga yadda yayi wa karamar fuskar Hasna kyau, kuma da yake rana ce yayi duhu sosai sai ya boye kalar kwayar idanun ta, ta zama kamar baturiya, banda gashin girar da yake fari.
“Lallai kin iya zabin gilashi, inye!” Inji Saheeb, a kokarin sa na son kawo murmushi fuskar ta.
Bai yi nasarar hakan ba amma ta mike kafar ta daga tankwashetan data yi. Kafar sumul da ita fara sal kamar ta jarirai, babu kaushi ko kadan.
Yace “Hasna’u yanzu har in tafi bazan ji muryar ki ba? Kina so in kasa nutsuwa gobe ma in kamo hanya in dawo?”
A yadda ya marairace mata sai ya bata tausayi, bata taba ganin mutum irin sa ba, saukin kansa ya yi yawa, abinda bata sani ba ita kadai yake wa saukin kan, kuma in yana gaban ta ji yake bashi da komai, ba shi da kowa sai ita.
A hankali ya ji siririyar muryar Hasna’u na fadin;
“Na gode Uncle Saheeb, Na gode for all the assistance, care, and concern showed to me. My world has never meet a person like you. You are an ANGEL. I must say thank you!
Amma don Allah don Annabi na roke ka daga yau kada ka sake dawowa in dai waje na zaka zo. Ina nufin alaqar mu ta kare daga yau”.

Ta fada tana mai sunkuyar da kan ta kasa, wasu hawayen masu zafi na kwararowa.
Saheeb ya bude baki yana kallon ta with astonishment, sannan ya girgiza kai ya ce “ko zan iya sanin hujjar ki?”
“Hujjata itace our relationship has no meaning, has no direction, has no focus….” Da sauri ya katse ta da cewa “a wurin ki ba? Amma a wuri na yana da shi, haka a wurin Ubangiji yana da shi. Annabi SAW ya hore mu da mu kalli matar da zamu aura kafin a daura mana aure.
Ni Saheeb kuma neman aure nake yi, kamar yadda kowa ke yi, yau din nan ba sai gobe ba zan gayawa Mamana a zo nema min auren ki”.
Hasna’u ta dube shi da idanun tausayi, cikin ran ta tana fadin tausayi na ya sa Uncle Saheeb ya zare! Ko in ce yana gab da zarewa! Kamar ya san me take fadi a ranta yace “ki yi min kallon zararre da kyau, dama gobe zan je Zaria wajen aminin mahaifi na, in gaya masa ya zo shi wajen Kawu ya kawo sadaqi na. ana kamala SSCE a shafa mana fatiha”.

Da fadin haka ya mike tsaye, hannayen sa cikin aljihu. Hasna’u ta bi shi da kallo da ‘light blue eyes’ din ta tana tausaya masa cikin ran ta, something is really-really fishy in his brain don mutum mai hankali bazai ce zai auri zabiya ba!
Zabiya ai sai zabiya dan uwanta ba wannan sardidin lafiyayyen matashin ba, wanda ko a masu lafiya shi ajin farko ne. Tana tausaya masa don ta san ya dauko hanyar da su duka bazata bulle da su ba, ya dauko rigimar da ba zai iya ba, ya dauko fadan da yafi karfin sa….. tsakanin sa da Kawu, da tsakanin sa da Mama. Watakila har da sauran al’ummar dake zagaye da shi. Ciki har da kanwar sa ciki daya.
Har ya fita bai bar sakar mata murmushi ba, murmushin da bazai taba gushewa daga zuciyar ta ba, murmushin da ta tabbatar shine na karshe da zata gani daga kyakkyawar fuskar sa don ta san tabbas in har ya fadi abinda yake niyya ga Maman nasa, to kuwa zata taka masa katoton birki ne, watakila har daga yin aiki a ‘Unity Kachako’.


Fitar Saheeb ba jimawa Kawu ya shigo, daka gan shi ka ga wanda ke cikin rudani, yace “Hansai, saura wata nawa ki gama makaranta?” A hankali ta ce “uku” “daga ukun an gama ko?” “Eh an gama Kawu sai kuma shiga Jami’a” yace “akwai jami’a a Kachako ne? Ko ke ce zaki bude University of Kachako?” Tace “a’ah babu, dama mun yi da Inna Kano zani in yi” ya kama baki cikin mamaki “kije Kano fa kika ce, da wane muharramin?”
Hasna’u tayi shiru, ya e “to Hansai ni ba zan takura miki ba, amma dole in miki aure yanzu, auren da hankali na zai kwanta da shi.
Don haka tun kafin Sahabi ya furta neman auren ki gara in miki aure, don bazai iya neman wata alfarma a gareni in hana shi ba, har ga Allah ina son yaron nan, kuma ina miki sha’awar aure sa, domin kika aure shi kin gama samun soyayyar miji.
Amma ki sani, muddin kika aure shi to fa shi kadai kika aura jinin sa da dangin sa har abada baza su so ki ba.
Sannan bazaki taba yin daraja a idanun su ba, ba zasu taba son abinda kika Haifa ba, musamman in ya zo a ZABIYA, ban kuma isa in tsawatar ba in wani cikin su zai taba mutuncin ki.
A bisa hakan, da wasu dalilai da dama, na yanke shawarar aurar dake ga dan uwan ki HASSAN gobe-goben nan ba sai jibi ba, kafin Sahbi ya sake dawowa da kokon alfarmar da bazan iya maida masa alkhairin sa ba, kin ga hakan ya fi dan dama-dama tunda yana dan zuwa makaranta yanzu, kuma yana dan jin Magana ta ba kamar da ba.
Idan kika auri Hassan dukkan ku kuna karkashin iko na komai zai zo da sauki, sanna ‘ya’yan ki suna tare da jinin su iya wuya iya zabiya ana tare.
Amma me kika gani? Don ko shi Hassan din ban gaya masa ba sai na fara neman amincewar ki tukunna. Ba zan yi miki auren dole ba, ‘yan zuqe-zuqen nan da yake yi duk dainawa zai yi da zarar nauyin aure ya hau kan sa”.
Hasna’u ko motsi ta kasa. Mutuwa mai tonon asiri!” Anya Kawu da gaske yake kaunar ta yake yi ko son kan sa? Da sanin sa zai aurawa dan wiwi ita? (MARIJUANA)? Kawai don Allah ya yo ta ZABIYA ana neman yadda za’ayi da ita? Ba gara-gara Hussaini ba shi da baya shan komai kuma yana zuwa makaranta?
Amma ai ya fi ta sanin akwai Hussainin ya zubar mata lalataccen don su taru su rufawa juna asiri.
Ta yarda da duk abinda ya fada akan Saheeb gaskiya ne, ta yarda bazata iya zuwa jami’a ba tunda babu Inna, wannan burin ya zagwanye! Ta san da Inna na raye koda jan gindi sai ta kai ta Kano jami’a ba tareda ta ji koda darr ba kuma ba tare da ta nemi taimakon kowa ba sai aikin karfi da lafiyar ta.
Wasu hawaye suka gangaro daga idanun Hasna’u. Hawayen da ta tabbatar har abada bazata daina zubar da suba har zuwa karshen rayuwar ta, idan ba har Inna ce ta dawo duniya ba.
A wannan gabar da Kawu ke son jin ra’ayin ta na eh ko a’ah zata auri lalataccen dan sa Hassan bata da zabi, bata da wani hope, bata da wani sauran buri a rayuwa bayan na fatan cikawa da imani.
Dama karatun karatun shine kadai burin ta, Kawu ya ce bazai taba yiwuwa ba tunda ba’a Kachako bane. Bai san cewa Annabi SAW y ace ku nemi ilmi ko da a birnin Sin ba, kuma bai iyakance mace ko namiji a wajen neman ilmi ba.

Ta dubi Kawu, da rinannun idanun ta, wadanda ke cike taf da hawaye, yayi zuruuu! Yana jiran hukuncin ta…… Kawun ta mai fada da kowa har da ‘ya’yan cikin sa a kan ta, Kawun ta da baya bari a nuna mata yatsa bai karya shi ba, Kawun ta daya da ya rage mata a duniya don an ce Kakar ta ta Kabo ma ta rasu da jimawa, shi da bai kyamaci hada jinni da ita ba bai kira haihuwar ta mummunar haihuwa ba, so yake ma ta haifo Zabiyun shi ta kawo masa.
Kawunta shakikin Innarta guda daya a duniya ya kyautu tace masa bazata iya auren dan sa ba don yana shan wiwi? Ai ana barin
DOWNLOAD
DOWNLOAD
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment