Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

halas ko don kunya. Masu iya Magana suka ce “Naka sai naka…. sannan in ta saki Kawu da iyalin sa wa za ta kama???
Abu daya ta iya tambayar Kawu a wannan lokacin da yake zake da jin amsar bakin ta. “Kawu karatu na fa na Unity saura wata uku in gama shi?” Yace in don wannan ne da auren ki ki je ki karasa ki dawo ki tare a dakin ki. Hassan bazai hana ki ba, in ya hana zan saka kafar wando guda da shi”.

Bayan wannan bata kara tambayar shi komai ba. Sai da yace.
“Kin amince ko Hansai? Ki duba hujjoji na da idon basira, bana nufin son kai ko yi miki dole cikin lamarin nan sai don an ce ko me zaka yi kayi shi da tsinkaye”.
Hasna’u ta ce “Kawu duk hukuncin da ka yi a kaina, daidai ne”.
Tana gama fadin hakan ta rufe ido kamar mai barci, Kawu yayi ta sanya mata albarka. Ya ce gobe ta tashi da wuri tayi wanka karfe goma za’a daura aure.
Yana bada baya taji cikin ta ya hautsine, da gudu ta sakko daga gadon, ta amayar da girkin SAHEEB tsaf, sannan ta samu sa’ida.
Ta kwanta a dandaryar kasa tana maida numfashi a hankali, tana rokon ubangiji da ya dauki ranta kafin wayewar garin.
Domin ta tabbata Hassan dan uwan ta ne amma bai dauke ta a mutum ba, balle akai ga zancen kauna ta aure, Kawu kadai ke son ta cikin gidan nan, daga Hassan har babar shi Hajjo da kannen sa babu mai kaunar ta.
In comparison to SAHEEB BELLO WAMAKKO wanda ke son ta da dukkan zuciya da ruhi soyayya ta fisabilillahi daga indallahi, ‘yan Uwan shi ne kawai da Maman shi baza su so ta ba, in haka ne ‘challenges’ na auren Hassan da ‘challenges’ na auren SAHEEB duk daya ne babu banbanci, so it was da duk wani miji da zata aura. Gara ma na SAHEEB akwai soyayya da gatan miji (wanda shi ya fi komai dadi da muhimmanci ga mace) idan babu na wadanda ke zagaye da shi.
Duka wannan tunanin ta na yi ne kawai ba don tayi wata hobbasa ta ceton kai a kai ba. Ta tattara komai ta mikawa sarki Allah, amma zabi ko jayayya da Kawu Samaila ba nata bane, ta bar wa Allah komai yayi duk yadda ya ga dama da rayuwar ta………
SUMAYYAH ABDULKADIR.
*****






MAMA (DAGA BAKIN UWA)
Tuki Saheeb yake amma hankalin sa ba ya jikin sa, a kan titin da zai mai da shi Kano bayan ya baro Hasna’u a kauyen Kachako, tunanin ta ina zai fara yake yi, yayi alkawarin zama bango abin jinginar Hasna’u. Hakan ba zai taba dorewa ba ba ta hanyar aure ba. Idan a da tausayin Hasna ya ke ji to yanzu son ta yake yi, so guda daya mai tsayawa a zuci, soyayya daga indallahi daga inda bai zata ba. Mama is such a kind of person da dosar ta da maganar da bata gamshe ta ba sai mutum ya shirya. Amma kuma dole itan zai fara dosa, in ya so in ta ki, sai ya nemi Barr. Dalha wato aminin Alhaji Wamakko dake zaune a garin Zaria. Ya soma shirya duk kalaman da zai yi amfani dasu wajen lallashin Mama, yana yi yana rehearsal don kalaman su zauna sosai a kwakwalwar sa.
Hasna’u will become his wife no matter what…. Mother of his children, koda kuwa su duka zasu zamo albino ko rabi su zamo albino, he will take care of them to the rest of his life by becoming a DERMATOLOGIST. Amma dole ya nemi albarka da yardar Uwa, Mama ba daya take da sauran iyaye ba ta fannin kula da su da nuna musu soyayya she is super excellent, and also a sacrificing mother, duk wahalar siyasa da fadi-tashin da take a rayuwa don ta nema musu farin ciki ne da rayuwa mai kyau shi da kanwar sa.
Amma kuma ya jima baya son halin Mama, domin kwata-kwata ta hana su alaqa da ‘yan uwan Alhaji da ke Wamakko, ba don komi ba sai don su din talakawa ne, gata dai ‘yar siyasa, wadanda kowa ya san talaka shine tinkahon su, amma a wurin Mama talaka ba komai bane face hanyar samun shugabanci, tsakanin sa da ita amfanin sa lokacin zabe ne kawai, ta yi amfani da shi ita da ‘ya’yan ta su ji dadi, shi kuwa ya cigaba da shan ranar sa.
Tunda uban su ya rasu bata kara barin su sun je Wamakko ba, sai shi ne da yayi hankali bayan gama jami’a yake zuwa jefi-jefi a boye yana taimaka musu yana musu ihsani.
Ta yaya zai yi ta karbi Hasna’u shine abinda ke damun sa, bayan ya san ta dade da yi masa mata wadda ta ke ganin itace daidai da shi, Fa’izah ce diyar aminiyar ta Senator Ladi, duk wani aure sun fi so su yi a junan su ‘yan siyasa, ko ba jam’iyyar su daya ba don duk inda ta fada ya zamo sha. Shi kwatakwata tarbiyyar yarinyar bata yi masa ba domin kuwa rainon Lagos ce, ita kan ta Mama uban Fa’izah ya fi ta kudi domin har deputy Gov. Yayi can da jimawa na jihar su Taraba. Amman kuma duk inda ake neman kyau to akwai shi a Faiza tunda babanta dan Taraba ne Maman ta ce ‘yar Kano.
Ya karbi Faiza ne a kan cewa bashi da zabi domin kuwa a lokacin yana final year yana karatu a jami’a, a cewar shi a lokacin shi bai da idon kallon mata he’s a goal oriented. Maman ta zabo duk wacce ta yi mata tunda ta takura da y agama NYSC zai yi aure.
Yanzu kuwa ba idon shi ne ya kyallo mace ba, zuciyar shi ce da ruhin sa. Ba kuma ya jin akwai abinda zai sa ya fasa auren Hasna’u, idan a da tausayi ne tsakanin su yanzu ya tabbata soyayya ce. Ko Hasna bata son sa, shi yana son ta zai aure ta a haka, in ya so a hankali ya koya mata soyayyar. Babu abinda zai dorar da dangantakar su ya cigaba da tallafawa rayuwar ta idan ba aure ba. Bai taba jin ma yana son yayi aure ba sai yanzu, ji yake kamar yayi fiffike ya gan shi gaban Mama su yi duk wacce zasu yi.
Bai iso gida ba sai yamma lis, cikin sa’a da ‘Rolls-Royce’ din Mama ya fara cin karo a ma’adanin ta tabbacin ta dawo gari. Da yayi parkin sai da ya tsaya ya karanta addu’a, addu’ar neman rinjaye. Ya kara rehearsal kalaman lallashin Mama. Sannan ya fito ya shiga cikin gidan.
A falo ya tadda su ita da Nusaibah suna kallon tashar MBC3. Mama da glass din ta a idon ta, kullum ya dube ta sai yayi tazbihi a ransa sabida kyawun ta da kuruciyar ta da har yanzu suke tattare da ita, kuma ta ki aure don kada a kira su agola. Shi kan da zata yi auren sai ya fi masa kwanciyar hankali sabida mazan dake karakaina a gidan su da sunan siyasa suna damun sa. Ya kudurce sai ya raba Mama da siyasar nan in har don su take yi, da zarar ya gama karatun sa ya samu aiki mai kyau, in Nusaiba ce ai ta gama sakandire ta tsaida wani cikin masu zuwa wajen ta tayi aure, itama Maman ta yi, shima yayi, a rufe harkar siyasa, in ta kama a rufe gidan Wamakko ne bakidaya a rufe kowa yaje ya tara nasa iyalin. Yayi bautar Allah.
Da wannan tunanin ya shiga gida.
Yana shigowa Nusaiba ta sulale ta bar wurin don ta san ta gama hada masa bom din da zai tashi da shi yanzun nan.
Yayi sallama Mama ta ki amsawa. Ta dai juyo ta dube shi sama da kasa ta gan shi a gajiye kuma da alama doguwar tafiya yayi. Shaddar jikin sa ta yi sqeezing, ta kara gasgata abinda Nusy ta fada mata cewa budurwa yayi a kauye kuma Zabiya, har gidan ya kawo ta tana Abuja, in zata iya tunawa itace Zabiyar da ya baiwa abinci a Unity Kachako ranar visiting.
Lokacin da Nusy take gaya mata Mama ta kusa yin sabo bayan ashariyar data dankara, don haka yanzu da ya shigo ya zauna a gefen ta da sauri ta matsa gefe.
A kyamace (disgustingly) ta ce.
“Ka je ka yi wanka da soso da sabulu da Dettol, sannan ka wanke hannu da sanitizer, sannan na amince ka zo inda nake” kallon rashin fahimta ya yiwa Mama, yau shi ake cewa ya je yayi wanka tamkar wani karamin yaro?” Mama ta buga masa tsawar data kara ruda shi,
“kaje ka yi wanka nace Saheeb! Sannan ka zo ka gaya min daga ina kake?”
Babu alamun wasa cikin sautin Mama, don haka ya mike zuwa bangaren sa, yana fadi a ransa Nusy ta jika masa aiki, kuma da sannu zai sa kafar wando daya da ita, sai ta gwammmace bata san shi ba.
Yayi wanka ya sanya farar jallabiyya ta zaman gida ya fesa turare sannan ya dawo falon, Mama na nan zaune inda ya bar ta har zuwa lokacin, sai cika take tana neman wanda zata batse da shi. Saheeb ya zo ya zauna a kujerar dake fuskantar ta, politely yace.
“Na yi yadda kika ce Mama”
“Daga ina kake?|” Ta tambaya da sauri tana zaro manyan sparkling idanun ta irin nasa.
Kai tsaye babu ko darr, yace “Kachako”
“Ba an yi hutu ba?”
Saheeb yayi shiru. Mama ta yi kwafa tace.
“Sannu da dawowa daga wajen Zabiya ‘yar kauyen Kachako, Saheeb ashe baka da hankali? Ashe karatun ka na banza ne? Tunda kuwa bai gaya maka hereditary and genetic ba? Kafin ma in yi zancen Fa’iza kenan da kasa aka kaiwa kudin aure.
Yo ko babu Fa’iza ni Muneera meye hadi na da Albino? Kai ni tunda nake ma na taba jin wani mai lafiya ya aure su? Haihuwa mai jaye-jaye, yau haihuwa zata janyomin bala’I cikin gida da cikin jinina, to ka sani Saheeb over my dead body!”
Tunda ta fara Saheeb kan sa ke sunkuye, har ta dasa aya, ta kuma nuna shi da dan yatsa “nayi waya yanzun nan da Perm.sec na NYSC, Kano, an canza maka PPA (Place of Primary Assignment) zuwa asibitin Nassarawa Kano. Dama ai tun farko sai da nace bazaka je kauyen nan ba kace in na bari ba komai taimako ne, kai ga ka waliyyi sarkin taimako, daga taimako ka kashe ni ina tsaye, a haifomin albino cikin gidan Wamakko, idan na kara jin ka je garin Kachako ma ba gidan su Zabiya ba ALLAH YA ISA BAN YAFE MAKA BA!”
SAHEEB. Ya dago idanun sa cike da hawaye yana duban Mama. “|Mama kada ki yi min haka, kada ki yanke hukuncin da zaki zo kiyi nadama, ba’a yiwa Da baki, idan ana so ya bar abu. Mama kiyi min alfarma ki saurari kalaman baki na, ki bar ni nayi wanna JIHADIn nikuma na amince ki aura min duk wadda kikeso su zama su biyu. Don Allah Mama ki taimake mu ni da Hasna’u.
Mama daga ni har Hasna marayu ne amanar Allah a hannun ki. In ta haifi zabiyan ni ina so ko bazaku rike min ba, in yaso wadda kika aura min ta Haifa miki masu lafiya”. Maama ta lailayo ashar ta yarfa masa (abinda bata taba yi masa ba) tace “ko kai ne Romeo don soyayyah, ko kai ne kafi kowa tausayi da taimako bazaka auri yarinyar nan ba, na fada na kara fada over my dead body zaka auri Zabiya ABUBAKAR (Karo na farko data ambaci sunan sa na hakika tun daga lokacin da ta haife shi ta yi masa laqabi da Saheeb.
Tana gama fadin haka ta mike tayi daki. Nusaiba dake make bayan labule tayi maza ta futo zata shige dakin ta sai ya gan ta, da mugun sauri ya bi bayan ta, tana shiga yana shiga ya maida kofa ya kulle, yasa key din dake jiki ya murda ya cire ya zura shi a aljihun wandon sa.
A kasan jallabiyar da yasa dogon wandon jeans ne baki, sai ya fara zaro belt din shi jikin sa har rawa yake ya soma dukan Nusaiba, ya riga ya tsara duk abinda zai gayawa Mama ta amince masa ba tareda bacin rai da tashin hankali ba, Nusaiba ta lalata komai da tsugudidin ta bayan sai da ya gargadeta kan ta fita batun sa da Zabiya.
Nusaiba ta soma ihu tana kiran Mama, amma kofar dakin da windows duka masu karfi ne Mama bata ji ta ba, sai da yayi mata lilis yaga tana neman shidewa sannan ya yarda belt din ya bude kofar zai fita, (feeling somehow relieved) ya rage bakin-cikin sa. Suka ci karo shi da Mama wadda sai a lokacin ta ji kukan Nusaibah ta shiga dakin da gudu shi kuma ya fice da sauri, ya zari mota ya bar gidan da wani mahaukacin gudu, saura kadan ya take maigadinsu.
Gudu yake shararawa na fitar hankali akan titin zuwa Zaria, ya manta ko karfe nawa ne lokacin, duhu ya riga shigo sabida hankalin sa ba ya jikin sa, gudun da yake yi sai da motocin gaban sa da bayan sa suka rika aiko mai da fitilun zagi. Burin sa ya isa Zaria wajen aminin mahaifin sa, ya san shi kadai zai iya tankwara masa Mama ta bar shi ya auri HASNA’U. Hasna’un da bata shigo rayuwar sa da sauki ba ta shigo ne da karfin gaske, ta dusar hasken sauran mata daga idanun sa. Daga uwar sa sai ita a wadanda yake so yanzu, yake burin kasancewa da su, baya jin in duk duniya zata taru a kan sa zai fasa auren ta…..
Iya abinda zai iya tunawa kenan, sai bude ido yayi ya gan shi a ambulance ana dawo da shi Kano. Mummunan hadarin ya faru a daidai garin Kura ta jihar Kano tsakanin miotar sa da wata karamar peogeot504 da ya bugawa.
Allah ya so kusa da jami’an tsaro ne aka kira ambulance nan take aka kwashe su jina-jina zuwa asibitin Malam Aminu Kano wanda shi ya fi kusa akan na koyarwa na Zaria.

LABARIN HASNA’U ‘YAR NAJERIYA YANZU ZAMU FARA SHI. BA MU TABO KOMAI BA HAKA BAMU FARA KOMAI BA. HASNA’U HAS A LONG JOURNEY AHEAD KAFIN CIKAR BURIN TA NA ZAMA CIKAKKAR MUTUM KAMAR KOWANNE DAN ADAM DESPITE HER ABNORMARLITY\DISABILITY.
AL’UMMAR NAJERIYA NA BUKATAR ‘COUNSELLING AND ENLIGHTENMENT’ A KAN ‘DISABILITY AND INCLUSION’ WANDA SAURAN KASASHEN DA SUKA CIGABA TUNI SUN YI ADOPTING MUHIMMANCIN NAKASASSU A CIKIN AL’UMMAH A TSARIN KUNDIN TSARIN MULKIN SU DA DOKOKIN SU. BA’A ISA A TABA MUTUNCI DA LAFIYAR MAI NAKASA BA.
NI SUMAYYAH ABDULKADIR (TAKORI) A YAU ZAN YI WA AL’UMMAR NAJERIYA WANNAN ENLIGHTENMENT DA HARSHEN HAUSA IN FORM OF STORY WRITING, DON A SAMU FAHIMTA KYAKKYAWA TSAKANIN NAKASASSU DA MASU LAFIYA A HULDA TA AURATAYYA. KOWA YA DAINA KALLON KOWA DA MUGUN IDO (MASU LAFIYA NA KALLON NAKASASSU BA MUTANE BA, NAKASASSU NA KALLON MASU LAFIYA A MARASA TAUSAYI DA RASHIN ADALCI). TA YADDA AURE YANZU YA KOMA SAI TSAKANIN NAKASASHSHE DA NAKASASHSHE DAN UWAN SA.
DA GASKE ZABIYA MA MUTUM NE KUMA ZABIYA ZAI IYA AUREN MAI LAFIYA KAMAR KOWA? IN ZAI IYA WHAT ARE THE OBSTACLES? WHAT ARE THE HINDRANCES? WHAT ARE THE CHALLENGES? KUMA WHAT ARE THE POSSIBLE RECOMMENDATIONS?
MAMA KO SAHEEB WANENE KE DA NASARA A KAN KUDIRIN SA? DA GASKE KARATUN HASNA’U YA KARE A UNITY? HASSAN FA? ZAI YARDA YA AURI ZABIYAR SHI KAMAR YADDA KAWU KE SO? DA GASKE WATA KUSAN TA FI WATA???
NI DAI TAKORI NA SAN SAU-TARI BARE ZAI IYA SADAUKARWAR DA DAN UWA NA JINI BA ZAI YI MAKA BA. AMMA ANYA HASNA’U ZATA IYA TSALLAKE AUREN HASSAN???
YANZU NE ZAMU SHIGA LABARIN HASNA ‘YAR NAJERIYA GABA-GADI. OUR THEME IS “GREEN WHITE GREEN, ONE NATION BOUND TOGETHER….. NO DISCRIMINATION ON DISABILITY”.
N500
3094856450
SUMAYYAH KABARA
FIRST BANK

FOR COMPLETE STORY

SHAIDAR BIYA

07030137970
An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
DOWNLOAD
DOWNLOAD
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment