Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

*HUSSAIN*
🌹 _MIJIN ALJANAH_ 🌹
*80K*

*SHORT AND TRUE LIFE STORY*

*MALLAKAR*👇

*FATIMA SUNUSI RABI'U*
*Ummu Affan*


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]


_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_

*Page 1-2*

Zaune ya ke cikin mota ya bud'e murfin,ya zuro k'afafuwansa k'asa,hannunsa d'auke da wayarsa yana dannawa,zuwa cen naga ya kara wayar a kunne da alama kira yayi.

Zuwa cen naji yace"Hello,ina k'ofar gidanku",sai naga ya ajiye wayar yana ci gaba da karkad'a keys d'in motar,yasha wani mur,kai kana kallonsa kasan bashi da fara'a,sai wani d'aga kai yake tare da murtuke fuska,sa'arsa d'aya yana da haske da ba k'aramin muni zai yi ba saboda sam bashi da fara'a.

Cikin yanga da yauk'i ta fito daga gate d'in gidansu,kai tsaye wajen motarsa ta nufa,cikin fara'a tace"sannu da zuwa",a hankali ya d'ago ya kalleta cikin isa da miskilanci,(Ko da yake miskilancin nasa na ganin dama ne,sai wanda yaso yakewa🤪).

Yace"yauwa" yana sake tamke fuska,cikin sanyin murya tace"kazo mu shiga daga ciki mana" da sauri ya d'aga mata hannu yace"kinga Zainab ba wannan ya kawo ni ba,kinsan ba don Hajiya ta takura nazo na ganki ba,babu abinda zai kawoni don haka ki iya takunki."

A sanyaye tace"amma Yaya Hussain mai nene matsalata anan ko don kawai nace ina sonki" yace"eh ita ce babbar matsalarki",yana gama fad'a ya ja murfin motarsa ya rufe,ba don ta matsa ba da sai ya mugeta,yawa motarsa key ya bar gurin da gudu.

Bin motar tayi da kallo kafin taja numfashi cike da k'aunar d'an uwan nata tabar gurin tana waiwayen motarsa.

Kai tsaye gidansu ya wuce,yana zuwa yayi hune mai gadi ya bud'e masa ya zura hancin motarsa ciki,guri ya samu yayi parking tare da fitowa ya nufi ciki.

Hajiya zaune a parlour ya shugo,kai tsaye kujerar da take zaune yaje ya zauna kusa ta ita,cikin murmushi ta shafa kansa"my son ka dawo da fatan dai kun dai-daita,d'an turo baki yayi gaba da d'aga gira irin na 'ya'yan gata yace"no Mum wannan yarinyar fa batayi tsari da ra'ayina ba kawai ki hak'ura zan sami dai-dai da ra'ayina" tace"haba my son mai nene matsalar Zainab yarinya natsatstsayi ga tarbiyya kai-dai kullum zaka sami dai-dai da ra'ayinka kuma har yanzu shuru" Zaiyi magana k'anwarsa Fatima tace"Rabu dashi Mum kullum maganarsa kenan ina ga fa baya son aure ne kawai,bari nazo na rigasa sai muga tsiyar kuma fa ya girme ni da kusan shekaru goma sha biyar" da sauri ya katseta cikin d'aure fuska yace"wallahi ki kiyayeni kafin yanzu kisha duka kin rai nani koni sa'anki ne?,ta 6e baki tayi dacewa"ni ina ruwana kar kayi basai kayi ta zama ba",kanta yayi da duka da sauri ta tasha ta ruga sama data masa dariya,sosai ya shak'a da hakan yace"Mum kina ganin yarda yarinyar nan ta rainani ko?tace"barni da ita yanzu dai ya maganar Zainab yace"mum mubar wannan maganar ni zan kawo muku mata wacce zakuyi fahari da ni."


To muci gaba ko mu tsaya?🤪🤪


HUSSAIN 80K MIJIN ALJANA idan kuna so naji ruwan comments hakan zaisa ku sami posting kullum.

More comments more typing,idan naji comments na k'ara muku yawansa akwai chakwakiya kuma labari ne na gaske aha🤣🤣🤣🤣🤣


Ummu Affan.✍️
*HUSSAIN*
🌹 _MIJIN ALJANAH_ 🌹
*80K*

*SHORT AND TRUE LIFE STORY*

*MALLAKAR👇*

*FATIMA SUNUSI RABI'U*
*Ummu Affan*

*Dedicated to*
_Hajiya Maryam Sakatare_
_Aisha Galadima_
_Wannan page naku ne,kuyi yarda kuke so dashi_ 😂

*Special Thanks*
_Ga masu goyan bayan ci gaba da suburbud'o wannan littafi,karku damu yanzu aka fara._ 😂

*Da k'yau 'yan Fcbk gaskiya kun burgeni musamman MIJIN KWAILA FANS gaskiya iya wuya ana tare.*


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]


_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_

*Page 3-4*

Hajiya ta kallesa tace"to Allah yasa haka dai" yace"hakan nema domin ni matar da zan aura sai kowa yayi mamakinta" Hajiya tace" *HUSSAIN* Ba dai cika baki ba kar azo ayi za6en tumun dare" yace"haba Mum fatan alkhairi dai."

Murmushi tayi tace"a kullum muna cikin yi muku *HUSSAIN*",Kamar mai tunani sai tace"kai amma nafa mance da d'auko Hafsat kuma kai nace zan aika" *HUSSAIN* Wanda har ya fara danna wayarsa yace"haba Mum wacece kuma hakan?,tace"bana son shashancin banza har ka mance da Hassu 'yar wajen Baba k'arami dake k'auye?da sauri ya zaro ido kamar zasu fad'o yace"Haba Mum yanzu saboda Allah a rasa wanda zaije d'auko wannan mahaukaciyar yarinyar saini,bayan ga direba" tace"to ba direban da zashi kasan dai Baba k'arami da fad'a,idan ba kai kaje ba haka zai dunga mita ka sani" Kallon Mum yayi zai magana tace"kar kace komai kaje ka d'aukota duka tafiyar batafi awa guda ba zuwa KUJAMA."

Ba don yaso ba haka ya tashi tare da mata sallama,yana tafe a mota yana tunani,sarai yasan halin yarinyar bata da hankali sosai,matsalarsa d'aya da ita ALJANUNTA domin tana da Aljanu abin tashin hankalin babu abinda *Hussain* yafi tsoro irin aljanu.

Haka yana tafe yana tunanin nan har ya kai Kujama,kai tsaye gidansu Hassu ya nufa,kafin ya kai ya hango wasu matasan mata biyu suna fad'a,parking yayi tare da fitowa yana masifa"Ke!Ke!!,bazaku bari ba?,wacce ke kimar d'ayar da alama tafi k'arfi da rashin kunya ta taso da cewa"to Malam ina ruwanka sa'ido sana'ar banza" k'arasowa yayi cike da bala'i yace"ke wa kike fad'awa magana?d'aga hannu yayi zai mareta,ai da ta kurma wani uban ihuww tuni jikinsa ya fara rawa,wani mutum ne ya k'araso da gudu sai da ya iso gurin *Hussain* ya gane ashe Baba k'arami ne,ita kuwa yarinyar nan tana ganinsa ta k'ara sautin kukanta tace"Baba k'arami kaga wannan mutumin ko?cike da masifa ya juyo yana cewa"wanne mutumin?sai ganin Hussain yayi tsaye kansa yana mazurai,k'ara bud'e ido yayi yace"wa nake gani kamar *USAINI*?da sauri bakinsa na d'an rawa yace"eh Baba k'arami ni ne."

Baba k'arami ya fara tafa hannu yace" ehye USAINI kaine kake mugun Hassu,yanzu Hassun kake bugu?, *Hussain* aransa yace"kuji wannan tsohon kamar yaji ance ya daketa,nai sani ba ashe maganar zuciya ta fito fili saiji yayi Baba k'arami na salati yace"eh lallai USAINI ka girma ni kake fad'awa magana eh lallai wuyanka yayi kauri."

Girgiza kai da Shafa sumar kansa yayi tare da fad'in "matsala", muryar Hassu yaji tana cewa"Baba wai daman wannan Yaya WUSAINI ne?(Su wusaini manya😂😂🤣🤣🤪)yace"shine fa bakiga ya kawo girma ba abinda yake fad'a mini",turo baki tayi tace"Baba dama kace zaizo mu tafi binni ko?bari na ruga gida Iya ta had'a min kayana a leda,kafin ya bata amsa tuni har tasa gudu har tana take k'afar Hussain saboda sauri,ina ta sani ita dai tayi gaba da gudu,da sauri ya janye k'afarsa yana gogewa da fad'in "wash kai-kai yarinyar nan bata da hankali fa.

Baba k'arami ya tasa shi gaba har gida,suna isa k'ofar gidan sai ga Hassu ta fito da leda hannunta da tsummokaran kayanta tace"mu tafi,daga Hussain har Baba k'arami suka bita da kallo.


*MORE COMMENTS MORE TYPING*

*COMMENTS*
*AND*
*SHARE*

*MUJE ZUWA*
_FATIMA SUNUSI RABI'U._*HUSSAIN*
🌹 _MIJIN ALJANAH_ 🌹
*80K*

*SHORT AND TRUE LIFE STORY*

*MALLAKAR👇*

*FATIMA SUNUSI RABI'U*
*Ummu Affan*

_Wannan shafin naki ne Maman Imam comment d'inki na burgeni matuk'a_

_Hahhhhh_🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣 _Yau ake yinta fa,wasu sunce wai ya zata kasance da Hussain da Hassu_ 🤣🤣🤣🤣🤣 _Ku biyoni muje zuwa._


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]


_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_

*Page 5-6*

Hussain yace"wannan wanne irin hauka ne,ke haka ake tafiyar?. Da sauri Baba k'arami yace"tofa ni fa matsalata da kai rashin hakuri abun magana bai wuya agareka,yanzu ita Hassu me ta sani wallahi idan har masifa zaka dunga mata gara ma a hakura da zuwan."

Hussain aransa yace"da hakan yafi" sai ji sukayi Hassu tace"a fasa zuwa ina taf wallahi sai naje,Kai Baba kasan yarda nake mafarkin binni kuwa tabbb",Baba k'arami yace"tunda tana son zuwa ya zanyi,sai ka shiga ku gaisa da Talatu ka fito ku wuce" ciki ya shiga bayan sun gaisa ya fito,ya shiga mota Hassu ma ta shiga,Baba k'arami yace"uhmmm kai dai Hussain baka da halin k'warai yanzu kazo k'auyen nan ko 'yar tsaraba nan babu sannan kuma zaka tafi babu ko kyauta,ni kam wannan rowa taka da yawa take",sai lokacin yasa hannu aljihu ya zaro dubu daya yace"ayi hakuri Baba k'arami ga wannan" amsa yayi yana jujjuya gudar dubun yace"yanzu dubu guda zaka bani saboda tsabagen rowa irin taka to me 'yar uwata tace ka kawo min" a hankali Hussain ya furta"wallahi mutumin nan ya cika matsala,a fili kuwa cewa yayi"tace zata aiko maka saboda ina sauri yasa ban tsaya amsar sak'on ba" Zaro ido Baba K'arami yayi yace"amma kai USAINI anyi shiryayye bazan fad'i d'ayan ba,yanzu saboda Allah ni kakewa bak'in ciki saboda tsabar bak'in ciki irin naka ka tsaya ka amsa shine kak'i saboda saurinka na banza da wofi to na gode kace mata zuwa jibi zanzo da kaina" yace"to" tare da jan motarsa yabar gurin yana mita.

Sam ya mance da Hassu dake rashe gaban mota yana da mita da cewa"Baba K'aramin nan matsala ne" Sai ji yayi an kece da dariya da sauri ya juyo Hassu ke dariya ba sassautawa kallonta yayi kafin yayi magana yaga ta kalli saman motar tana cewa"Eh mana haka ne fa" sai ta saki dariya,cikin d'aure fuska yace"ke lafiya?bata kallesa ba taci gaba da surutunta.

Sun shugo garin Kaduna,zasu wuce ta gurin wasu masu kayan marmari tace"Yaya Hussain don Allah tsaya ka sayamin" yace"ni ba mahaukaci bane irinki" ganin bashi da niyyar tsaya ta fara k'ok'arin rik'e sitiyarin ai da yaga tana niyyar sa su fara layi a titi ba shiri ya tsaya yada daka mata tsawa,ina ta sauraresa ai da gudu tayi ta fita sai gurin masu kayan marmari,tana zuwa ta zari ayaba ta 6are ta fara ci.

Mai kaya ya bita da kallo cike da mamaki,gani yayi ta zauna saman benci tana cinye waccar ta zari wata tare da d'aukar lemu wanda aka fere ta dasa masa hak'ora,yace"Malama lafiya?tace"ka had'a komai da komai na dubu d'aya" jin ciniki da sauri ya fara had'awa domin da farko ya d'auka mahaukaciya ce.

Hussain ya fito yana wani takon isa,ya k'araso ganin abinda take ya zaro ido yace"ke baki da hankali ne" wai lemu ya fara washe baki yace"ashe tare take da Yayanta wannan yarinyar da gani 'yar gata ce" Mik'a mata yayi tace"yauwa ashe dai ka gane" gashi nan shi zai baka kud'in" ta nufi mota,mai lemu ya juyo da fara'a yace"oga na 1k ne kawai aka had'a" Zaro ido yayi yace"1k kai baka da hankali zaka bata kayan 1k ina laifin na d'ari biyu" yace"ranka ya dad'e ai ita tace a had'a mata" tsaki yayi yana mita ya basa domin shifa ya tsani kashe kudi ba gaira babu dalili.

Dawowa yayi mota,amma babu Hassu sai dai ga kayanta da lemukanta a ciki,yace"wannan mahaukaciyar kuma ina ts nufa" d'aga kan da zaiyi ya hangota gurin masu kaji,tana ci hannu baka hannu k'warya,da mugun tsoro ya zaro ido,ganin ana had'a mata guda uku cikin leda rik'e baki yayi da sauri tare da zaro ido.

Mota ya nufa da sauri domin ya yajin zai iya biyan wannan kudin sai dai idan basu gansa ba za amsa na ledar su yafe mata wanda taci ko su jibgeta babu ruwansa.

Yana k'ok'arin shiga har sun iso,amsar ledar tayi tare da cewa shi zai biyaku,ta shige ciki,suka ce"Alhaji dubu biyar ne" cikin masifa yace"ni kunga na muku kama da Alhaji ne?ko kuwa tsabar rashin mutumci?,mutumin yace"Allah yabaka hakuri Malam",cikin tsawa yace"waye Malam?kai kafa kikayeni",mutumin yace"koma dai menene fara biyana kud'in kazar na wuce" yace"ni naci da zakace na biyaka?,Hassu ta lek'o daga mota tace"wai Yaya Wussain ka basa mu wuce mana" wata harara ya buga mata tare dasa hannu aljihu aransa yana cewa Wallahi sai nayi maganin yarinyar nan tunda ta sani asara ba gaira babu dalili.

Biyansa yayi,mutumin na magana bai kukasa ba domin ji yaje kamar ya makesa wai ansashi asarar dubu shida lokaci guda me yakai wannan takaici🤪🤪🤪(Don a gurin Hussain dubu shida kamar Dubu dari shida take🤣🤣🤣🤣).

Shiga mota yayi yana mita da haka suka isa gida,yana parking ya fita cike da k'uluwa Hassu tace"Yaya WUSAINI kazo ka d'aukar min kayana mana.

🤣🤣🤣🤣🤣

*MORE COMMENTS MORE TYPING🤸‍♀️🤸‍♀️*

*COMMENTS*
*AND*
*SHARE*

_MUJE ZUWA_
*FATIMA SUNUSI RABI'U.**HUSSAIN*
🌹 _MIJIN ALJANAH_ 🌹
*80K*

*SHORT AND TRUE LIFE STORY*

*MALLAKAR👇*

*FATIMA SUNUSI RABI'U*
*Ummu Affan*


*Marubuciyar👇*
*UWANIN QAUYE*
*CIKIN WAYE?*
*NIDA YAYA LAMEER*
*KAINE SANADI*
*NAYI GUDUN GARA...*
*IZGILI*
*K'URUCIYAR SAPNAH*
*MAHAD'IN RAYUWATA*
*SANDAR MAKAUNIYA*
AND NOW👇

*HUSSAIN*
_MIJIN ALJANAH_


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]


_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_

*Page 7-8*

Wani kallo ya mata da cewa"waye d'an dakonki?sakkowa tayi tare da dire basa ledar kayanta gabansa sannan ta d'auki ledar kazinta da su lemunta tayi gaba.

Tsuwww yaja tsaki tare da d'aukar ledar yace"wallahi Mum ta kawo mana matsala gida" domin shi fa gani ya ke Hassu ba kanta guda ba.

Kasancewar Hassu ta ta6a zuwa gidan yasa ta gane hanyar domin duk idan Baba k'arami zaizo wato mahaifinta tare suke zuwa,hakan yasa kai tsaye parlourn gidan ta nufa HUSSAIN na biye da ita.

Fatima da ke zaune parlour tana ganin Hassu ta tashi da murmushi tace"Laaaah Hassu sannu da zuwa" tace"yauwa tare da dire kayanta tsakiyar parlourn ta zauna,Hussain da ya k'araso ya jefa mata kayanta kusa da ita ya haye sama,yana mita,Fatima ta dunga dariya k'asa-k'asa.

Fatima ta jata zuwa bedroom d'inta,tana cewa"Hassu wannan kaji haka ba dai daga k'auye aka saki ki kawowa Hajiya ba?cike da shiririta irin tata tace"Yaya WUSAINI YA sayamin a hanya" sosai Fatima ta zaro ido tace"kai da gaske Yaya Hussain mai mak'o wanda d'ari biyar kafin yabaka aiki ne shine ya saya miki kazi har uku?Sosai Hassu tayi dariya sai-dai bata ce komai ba.

Fatima tace"bari na d'auka a sake d'umamawa lallai yau zamuci tafarrakin uban 'yan mak'o,zata d'auki Kajin taga su lemu tace"wannan kuma fa?sosa kai Hassu ta fara tare da rank'washin kan kamar mai kwarkwata tace"duka duk ya sayamin. Fatima bakinta ya kasa rufuwa sosai take mamaki sai tayi murmushi ta had'a dasu tace"bari a wanko" sannan ta fita zuwa kitchen.

Ko da Hassu tayi wanka,wasu ko d'ad'd'un kayanta ta saka riga da zani da kallabi irin mai santsin nan,ta zana ja gira da wani jan gazar nata da ta taho dashi ta ranbad'a kwalli tayi d'igo-d'igo a kumatunta da goshi.

Sannan ta fito,lokacin Hajiya ta fito Hussain ma shugowarsa kenan ya dawo masallaci,gurin Hajiya ta k'arasa tace"ina wuni Inna" Hajiya tana murmushi tace"Hafsat lafiya k'alau,kun shugo ina sama na shiga sallah fatan kun sauka lafiya,ta washe hak'ora"lafiya k'alau Inna sai-dai Wallahi tallahi kinji na rantse kuwa wannan Yayan Wusainin yayi ta min fad'a wai zai dake ni"

Hussain wanda tun tahowarta yake harararta yace"nayi miki fad'an damma ban faffasa miki baki ba asarar da kika sani" da sauri tace"yauwa Inna kinji ko?,Hajiya da Fatima da babu abinda suke sai dariya Hajiya tace"kiyi hak'uri 'yata Yayan ne naku da bak'ar zuciya kamar tsohon kuturu" Kallon Hajiya yayi fuskarsa babu walwala yace"abinda zaki ce kenan Hajiya bayan na sanar miki duk kan abunda ya faru tun zuwana Kujama har dawowarmu" Hassu ta d'aure fuska tare da zama tana harare harare.

Hajiya tace"ni kuna rud'ani na rasa bayan wa zanbi to duka kuti hakuri yarana",tashi Hussain yayi ya wuce ciki Hajiya tace"Hassu haka yake da zuciya ga saurin fushi halinsa haka yake don haka ki iya zama dashi" Hassu aranta tace"ai kuwa haka wallahi zai ganene,bayana min kallon bagidajiya ba 'yar k'auye da wannan zanyi amfani na gyara masa zama.

Fatima ta kawo naman sukaci gaba d'aya suka k'oshi suka sha kankana lemu da ayaba sannan suka kora da ruwa mai sanyi,Fatima tace"yau wace rana munci ta farrakin Yaya Hussain sarkin 'yan mak'o.

Hajiya tace"wallahi babu ruwana idan yajiki ke da shine",Ranar basuci wani abinci ba saboda sun k'oshi da naman nan.

Washe gari da safe,Hussain ne ya sakko cikin shirinsa na fita kasuwa,kasancewar babban shago ne garesu na sayar da atamfafo shadda yadi les kai duk wani abu da ya shafi kayan sawa suna sayarwa shagon Yayansa ne (HASSAN ATK)Kasancewar shi Hassan yana cen k'asar India to shi Hussain ke kula da shagon🤪🤪🤣🤣tare da sauran amintattun Hassan d'in.

Hassu wacce tun lokacin da ya fara bud'e k'ofa ta fito da sauri daman tun asuba da tayi sallah taje kitchen ta kad'a omo da ruwa da mai kad'an cikin k'aramar roba,jin yana bud'e k'ofa yasata saurin sakkowa tazo saitin k'ofarsa ta juye ruwan omon sannan ta shige cikin labule,

Fitowar da Hussain zaiyi cikin shirinsa ya d'au wanka sai tsantsi ya jamesa timmmm ya fad'i k'asan tass saboda wahala sai da ya saki k'ara,Hassu ta fito daga cikin labure tana shek'a dariya da cewa"wohwohwoh ya fad'i kuzo kuyi kallo,Fatima ce ta fito da sauri tana tambayar lafiya?ganin yarda Hassu ke tun tsura dariya ta kalli gurin da take kallo zaro ido tayi ganin Hussain 80k zube a k'asa ya kasa tashi,gaba d'aya jikinsa ya 6aci.


*MORE COMMENTS MORO TYPING🤸‍♀️🤸‍♀️*

*Yasin,Yasin WhatsApp ku gyara ina son jin comments idan ba haka ba kuji d'if ato.**HUSSAIN*
🌹 _MIJIN ALJANAH_ 🌹
*80K*

*SHORT AND TRUE LIFE STORY*

*MALLAKAR👇*

*FATIMA SUNUSI RABI'U*
*Ummu Affan*

_DEDICATED TO_
_My k'awar amana Rukayyat Ibrahim Lawal (Ummu Inteesar) Allah ya bar amana,Ya kaimu ranar bikin amin,Sannan ya bawa jinin jikinki lafiya mai d'aurewa yasa kaffara ne,ina yinki over my K'awata_🥰

_SPECIAL GIFT TO_
_Hauwa S Zaria_
_Anty Hauwa Mmn Uswan,Alkhairin Allah ya kai miki har gadon barcinki,ina yinki over my Antyna._🥰


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]


_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_

*Page 9-10*

Hussain wanda ji yake kamar ya karye k'ugu ya d'ago fuska murtuke yana dubanta,dai-dai fitowar Hajiya wacce ke cewa"K'arar me naji kamar abu ya fad'i?ganin Hussain k'asa warwas ta yi saurin k'arasawa da rik'esa"Hussain lafiya?saboda tsananin takaicin da yakeji ya kasa magana ma.

Tuni Fatima ta dena dariya,Hassu kuwa tasha wani mur kai ka rantse da Allah ba ita tayi ba.

Da k'yar Hajiya ta iya kaisa saman kujera,tasa Fatima ta d'aura ruwan zafi domin dole sai an masa gashi idan ba haba kuwa zaiji jiki,babu abinda yake sai hararar Hassu.

Zainab ce tayi sallama,rik'e da akwatinta a hannuta tana ja,duka suka zuba mata ido bayan sun amsa sallamarta,da sauri ta saki akwatin tare da k'arasowa gurin Hussain tace"Laaah Yaya Hussain lafiya?me ya sameka?,harara ya zuba mata murya ciki-ciki yace"me ya kawo ki gidanmu harda akwati?,k'asa tayi da kai tace"na cewa su Mama ni dai zan dawo nan gidan kuma sun amince" yace"amma baki da hankali" Hajiya tace"to meye a ciki don ta dawo nan gidan karka manta da mahaifinta da mahaifinku wa da k'ani suke don haka Zainab je kikai akwatinki d'akinsu Fatima"tace"to Hajiya na gode."

Fatima ta kama mata zuwa ciki,Hassu ta bisu sa harara.

Bayan ruwan ya tafasa,Hajiya da kanta ta saka towul tana matsa masa bayan ya cire riga,me Hassu zatayi ba dariya ba ganin yarda yake rik'e hannun Hajiya da cewa"don Allah kiyi a hankali da zafi fa" tace"dole a gasa maka kar wajen ya suntuma. Zainab tace"don Allah Hajiya ki masa a hankali,wacce dawowarsu kenan da Fatima da tashiga da akwatinta ciki.

Cikin d'aure fuska yace"wai ina ruwanki ne?,cike da tausayi tace"Allah ya baka hakuri" tsuww yaja tsaki,ita dai Hajiya girgiza kai tayi tana ci gaba da matsa masa da haka har suka gama yana raki da cewa ta bari.🤪

Misalin k'arfe,shidda na yamma suna zaune a parlour dukansu,Hassu ta saka k'ara da ihu,kafin kace kwabo dukansu sukayi kanta da tambayar lafiya?ganin yarda idanuwanta ke juyewa yasa Hussain farayin baya aransa yana cewa"daga gani wannan ba ita bace gara na gudu",ai saiji yayi cikin wata siririyar murya tace"karda ka sake d'aga k'afarka daga gurin" a mugun rud'e ya juyo yana dubanta tashi tayi ta kalli Hajiya Fatima da kuma Zainab tace"ya naga kun zuba min ido?da sauri dukansu suka maida idanuwansu k'asa cike da tsoro.

Tace"Yanzu abinda nake so shine dukanku ku runtse idanuwanku,babu musu suka runtse domin duk tunaninsu aljanin ne ke magana ita kuwa a gurin Hassu tsabar shak'iyanci ne irin nata take son basu tsoro da sunan aljanu,tace"Tana so Hussain ya hau bene da rarrafe idan ba haka ba kuwa yau za'ayi mamaki a gidan nan" Zainab tace"haba ke kuwa ya za'ayi kice hawa bene da rarrafe ai abun da kamar wuya,tsawa ta daka mata tace"ke dakata kinsan ko ni wacece kuwa?to nice Aljanar Hassu ba Hassu bace sannan wannan da kike gani shine HUSSAIN MIJIN ALJANA mijin aljanar Hassu,ai daga Hajiya har Fatima suka bud'e idanuwansu,batse baki tayi da zazzaro ido kai idan ka kalleta a lokacin tsaf zakace mai aljanu ce,tace"ko yayi ko yanzu na juya gidan nan,ai Hajiya da sauri tace"Hussain kayi don Allah,da sauri ya nufi bene gar yana tuntu6e,Hassu ta kusan sakin dariya ta dai daure,haka HUSSAIN yayi rarrafe ya hau saman bene,gwiwowinsa babu abinda suke sai rad'ad'i(Wayyo cikina🤣🤣🤣🤣).

Hassu tace"to kowa ya runtse idanuwansa Aljanar Hassu zata wuce" da sauri suka rufe idanuwa,kallon inda Hussain yake tayi wanda babu abinda yake sai numfashi ya jingina da garo tace"kaima ka rufe idanuwanka da sauri ya rufe."

Dariya tayi k'asa-k'asa sannan ta koma gurin zamanta,saiji sukayi ta fara wak'a" _Cikin raina na sanyoka ka bani guri kaima in shugo naka_ duka suka bud'e ido Fatima tace"Hassu" kallonta Hassu tayi irin bata san abinda ke faruwan nan ba tace"Yaya Fatima me ya faru" Hajiya najin haka ta tabbatar aljanar ta tafi sai tayi saurin isa gurin Hussain tana masa sannu haka Zainab.

*MORE COMMENT MORE TYPING*

_MUJE ZUWA_
*FATIMA SUNUSI RABI'U.*


*COMMENTS*
*AND*
*SHARE*

_MUJE ZUWA_
*FATIMA SUNUSI RABI'U.**HUSSAIN*
🌹 _MIJIN ALJANAH_ 🌹
*80K*

*SHORT AND TRUE LIFE STORY*

*MALLAKAR👇*

*FATIMA SUNUSI RABI'U*
*Ummu Affan*



*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]


_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_

*Page 11-12*

Ranar dai haka Hussain ya wuni a gida babu batun zuwa kasuwa,da ya kalli Hassu yaji kamar ya shak'eta saboda haushi gashi ba hali domin yanzu mugun tsoranta yake musammanma aljanarta.

Hassu kuwa tunda ta gane hakan ta tsiro da wulak'anci kala-kala da sunan aljanarta ce wacce tace"matar Hussain,sosai Zainab ke jin haushinta gashi da tayi magana yanzun Hassu ta tada aljanun,kamar jiya abinda ya faru,suna zaune bayan sun kammala breakfast sai Hassu tasaka dariya ganin yarda Hussain ke d'ingishi saboda fad'uwar da yayi,tace"ayya Yaya Wussaini na lura jiyan nan fa kaji jiki.

Tun kafin yayi magana Zainab tace"waike Hassu meye haka ? Wallahi zanci mutumcinki akan rashin kunyar da kikewa Yaya Hussain. Harara Hassu ta jefa mata tare da zaro ido tace"eh daman harda ke ciki. Sai Hassu ta mik'e ta nufi hanyar k'ofa sai kuma ta dawo sai gani akayi ta shak'e wuyan Zainab akayi-akayi taqi sakinta da qyar Hajiya ta qwaci Zainab ai kuwa tasha baqar azaba,tun daga lokacin ta dena sa mata baki a cikin abunta,sai dai ido da harara domin sosai take jin zafin abinda Hassu kewa Hussain.

Baba k'arami ne yau yazo gidan,Hassu tayi farin ciki da zuwansa haka Hajiya,Hussain yana ganinsa yace"yauwa Baba k'arami kazo tafiya da Hassu ne ?, wata harara ya banka masa yace"nazo tafiya da ita ko dai na kawo mata ragowar kayanta ai ita kuma ta sami gurin zama." Hussain yace"a'ina ? " Baba k'arami yace"kai bana son shaqiyancin banza fa yo a ina take ba cikin gidan nan ba."

Hajiya tace"hakan na da k'yau daman ina son na mayar da ita makaranta naji dadi da kamar min ita ko ba komai zata san wani abu ilmi na da dadi sosai" yace"yauwa 'yar uwata na gode sosai. Ya d'aura da cewa daman Hussain yace kin basa saqo ya bani saboda baqin cikinsa da rowa irin tasa bai amsar min ba wai saboda yana sauri shine nazo amsa."

Hajiya ta kalli Hussain shima Hussain ya kalleta yana k'if-k'ifta ido,kai da ka kallesa kasan ya zubowa Hajiyarsa k'arya ne,tace"eh haka ne,bari na kawo maka" domin bata so tace"Hussain ya mata qarya ne a gabansa" tana shiga d'aki ta zage jaka dubu ashirin ta irga ta dawo ta basa,Baba k'arami ya dunga godiya da cewa"Allah ya raya miki zuria yaji k'an magabatanmu tabbas Hajiya ke ta gari ce" ita dai ba abinda tace"bayan amin.

Hassu wacce ke zaune kusa dashi tace"To Baba yanzu mai zakayi da kud'in nan?yace"ke kinci k'aniyarki ni sa'anki ne har tambayata zakiyi abinda zanyi da su. Tace"Allah ya baka hakuri Baba" cikin maqe murya yace"Hassatu sai-dai naga tunda nazo ko ruwa ba abani ba bare nasa ran abinci.

Hajiya wacce zurum a kunnanta ta kalli Fatima tace"ki kawowa Kawunku

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2

Please Login or Register in order to submit comment