Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abinci" ta amsa da to ta nufi kitchen.

Hussain yana harararsa ya nufi sama,aransa yana cewa"uba da 'ya duk halinsu guda" sai da Baba k'arami ya cika cikinsa harda guzurin wani aleda wai zai kaiwa Talatu sannan,Hajiya da Hassu suka rakashi har bakin gate sannan ya musu sallama ya wuce Kujama.

Su kuma suka koma ciki Hajiya na k'ara tunanin d'an uwan nata Hassu kuma na k'umsa abinda zatawa Hussain yau tunda har ita ce wai yake so tabar gidansu.


*MORE COMMENTS MORE TYPING🤸‍♀️🤸‍♀️*

_MUJE ZUWA_
*FATIMA SUNUSI RABI'U.**HUSSAIN*
🌹 _MIJIN ALJANAH_ 🌹
*80K*

*SHORT AND TRUE LIFE STORY*

*MALLAKAR👇*

*FATIMA SUNUSI RABI'U*
*Ummu Affan*


*DEDICATED TO*
*YUSUF NUHU* _Wannan page d'in naka ne kayi yarda kake so dashi,ina jin dad'in k'aunar da kake nunawa wannan littafin,ina godiya matuk'a,kana d'aya daga cikin masu samin k'warin gwiwa domin suburbud'o muku wannan labarin ina godiya Angon Fadeelah._



*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]


_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_

*Page 13-14*

Suna shiga kuwa da ta kurma wata uwar k'ara ita kanta Hajiya sai da ta furgita,Zainab da Fatima da ke zaune parlourn suka tashi da sauri suna kallonta.

Muzurai ta fara tare da k'if-k'ifta idanuwa da zaro su,Hajiya ta kalli Fatima tace"Fatima ko dai zaki kira mana Malam Hadi ne,Malam Hadi malamin Islamiyyar su Fatima ne bashi da nisa da gidansu,Hajiya ta d'aura da cewa"abin yayi yawa kar azo a sata cikin wani halin gara a kirasa ya mata ruk'iyya."

Hassu na jin haka cikinta ya d'uri ruwa tasan idan aka kira Malami asirinta ya gama to nuwa,don haka ta fara shawarar abinyi a zuciyarta domin in har ta bari aka kira Malamin kashinta ya bushe.

Cikin mak'ak'k'iyar murya da mak'e tace"ai duk wanda ya fita nan da bakin gate akwai matsala,abu guda kawai za'ayi aljanar nan ta tafi shine a kira WUSAINI ya kai Hassu gurin masu kajin nan ya sake saya mata,idan ba haka ba kuwa yau akwai daru" Hajiya wayarta ta ciro ta kira Hussain bai san abinda ke faruwa ba ya fito.

Hajiya ta fad'a masa,d'aure fuska yayi da kallon Hassu yace"da kud'in wa?Hajiya tace"bana son tashin hankali bari na baka dubu biyar sai ka siya mata" da sauri Hassu tace"ai idan har ba kud'insa ba to a kyau fa matsala don yasin-yasin yau d'akinsa zan kwana kuma zai gamu da gamonsa" Hussain najin haka yace"a'a baza ayi haka ba muje na saya miki"

Gaba yayi Hassu ko mayafi ta bi bayansa da Sauri Hajiya tasa Fatima d'auko mata hijabi ta kai mata.

Zainab ta cika tayi famm ji take kamar ta mak'ure Hassu saboda haushi,ita tazo gidan ne domin su k'ara kusanci da Hussain ko zai sakko daga dokin zuciyar da ya hau ya fara kulata har ayi maganar bikinsu,amma ta kula wannan yarinyar Hassu tana son kawo mata matsala dole tasan abinyi kuwa,domin ita ta fara k'aryata yarinyar nan gani take ko dai aljanun k'arya take fomin masu aljanu ai ba haka suke ba,amma idan ta tuno shak'ar da tayi mata sai jikinta yayi sanyi domin tasan mutum dai ba zai mata wannan shak'ar ba.

A mota kuwa Hassu babu abinda take sai murmushi da waqe-waqenta domin fagen rawar kai da son waqa tana sahun gaba.

Wak'ar mawak'inta UMAR M SHAREEF ce Hussain ya kunna ita kuwa tana son wak'ok'insa don tana da haddar wasu da yawa,hakan yasa take bin wak'ar tana karkad'a kai kamar kad'angaruwa.
_Duk wanda yassamu gurin rabbi ya dace._
_Samu rashi na rabbi ne karda ku mance._
_D'auka kasa aranka ni taka ce._
_In munyi aure na zarcewa tsarahhhhahhhh._
Tasa tafi da dariya kamar wata zararra,girgiza kai kawai Hussain yayi aransa yace"mahaukaciya kawai.

Sun iso gurin masu kaji,tun kafin ya gama parking ta fice da gudu,mai nama yana ganinta ya washe baki domin ya ganeta musamman da yaga Hussain na binta a baya yasan zayayi ciniki da su,"Sannu da zuwa" yace da ita cikin fara'a tace"yauwa" sannan ta sami guri ta zauna tana kallon gajin nan ta fara nuna wad'anda take so,manya guda biyar,da sauri ya kalleta yace"biyar kuma wannan cen karon ai uku kika d'auka,tace"eh wancen karon nasan mutum uku ne a gidan harda ni Hajiya da Fatima wannan karon kuma an k'ara Zainab kaima gaka ai ido guba ko" da sauri mai kaji ya amshe da cewa"wannan gaskiya ne 'yan mata.

Haka ya biya ransa na suya sannan kuma tace"dole ya saya mata su lemu wannan karinma babu yarda ya iya haka ya biye mata amma yasan dole sai yayi zazza6in kud'ad'an nan da tasashi ya kashe,ransa 6ace yake tuk'i ita kuwa komai wasai sai cin Apple d'inta take tana kallonsa ta k'asan ido ta tuntsure da dariya.

*MORE COMMENTS MORE TYPING*

_MUJE ZUWA_
*FATIMA SUNUSI RABI'U.**HUSSAIN*
🌹 _MIJIN ALJANAH_ 🌹
*80K*

*SHORT AND TRUE LIFE STORY*

*MALLAKAR👇*

*FATIMA SUNUSI RABI'U*
*Ummu Affan*

_WANNAN page sadaukarwa ne ga duka masoyan wannan littafi,gaskiya ina jin dad'in yarda groups da yawa suke son wannan labari nima ina sonku FISABILILLAH kuji dad'inku page d'in nan naku ne._

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]


_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_

*Page 15-16*

Bayan sun isa gida,haka ya bita da dakon kaji yana wani kumbura kamar zai fashe,ita kuwa tana dariya k'asa-k'asa ta d'auki ledar su lemu tabi bayansa,har lokacin su Hajiya na parloun saboda ba'a kira sallah ba bare su tashi.

Da sallama suka shugo,suka amsa,gaban Hajiya ya ajiye ledar kajin,zaro ido tayi ganin da k'walan kaji har biyar tace"Hussain kana hauka ne. yace"to Hajiya ya zanyi tunda haka ta ke so" yarda yake maganar kai kanka da kaji kasan ransa a 6ace yake.

Kallon Hassu tayi wacce lokaci guda ta sauya fuska jin abinda Hajiyar tace,ganin yanayin da ta shiga yasa Hajiya tace"ok na gane hakan yayi" sai lokacin Hassu ta saki fuska tace"Hajiya kowa fa d'aya harda shi kinga daman mu biyar ne" tace"haka ne 'yar albarka" Fatima da dariya ke cinta tana daurewa ta kasa,saiji akayi ta fashe da dariya,Hussain iya harzuk'a ya harzuk'a yace"ke da ubanwa kike?bakinta a hannu tana k'ok'arin ta tushe bakinta ko dariyar zata tsaya amma hakan ya fassakara dariyar tak'i tsayawa,kanta yayi ya kai mata mari Allah ya bata sa'a ta goce ya mari iska,wani marin yake niyyar kaima da ta gane da sauri ta ruga,sai da takai k'ofar d'akinsu tace"ayya Yaya Hussain sorry wallahi dariyar kud'in da ka kashe nake nasan ko ba komai yau sai ka kwana da zazza6i sanin halinka da nayi akan kud'i."

Ai da gudu yayi kanta sai-dai kafin ya kai harta shige bedroom d'insu ta danno k'ofa,bugun k'ofar ya fara ransa 6ace da cewa"ba zaki bud'e ba sai na karya" Saman bed ta fad'a domin ta murza key tasan kuma babu yarda za'ayi ya bud'e bare har ya iya karya k'ofar,har lokacin dariya take tana cewa"gaskiya Hassu k'arshe ce,tasan salo da hanyar lagon Yaya Hussain" shi kuwa sosai ya k'ulu ji yake da zasu had'u da Fatima a lokacin zai iya karyata.

Ranar ma su Hajiya Fatima da Zainab sai oganniya Hassu haka suka sha bidirinsu na cin kaji duk kuwa cinsu kasa cinye kaji hud'u sukayi,domin an kaiwa Hussain tasa wanda saboda tsabar haushi kasa cin tasan yayi ko kallonta baiyi ba,Sai-dai kuma zuwa cen bayan ya dawo masallaci yaji k'amshinta ya isheshi kauda fuska yake kauda kai yake,amma zuwa cen dai sai gani nayi Hussain ya jawo plate da Fatima ta d'aura masa tasa akai harda su kabeji da albasa a sama sai tashin k'amshi take plate biyu ne d'ayan kuwa kayan marmari ne bayan an wanke aka yanka masa.

Yana wani tsuke baki da hararar k'ofa yace"ai idan ma naci kud'ina ne,gara ma naci na rage asara" haka yaci kazar sosai da kayan marmarin,Hassu ce tazo kawo masa abinci taga ya baje yana yagar cinya ji tayi kamar ta saka dariya ta dai daure tayi masa sallama,da sauri ya ajiye k'ashin dake hannunsa yana muzurai ta daure dariyarta tace"Yaya Wusaini ga abincinka"banci"yace da ita fuska d'aure baki duk maik'o,tace"ayya kace kazar ta k'osar da kai?yace"ban sani ba ina ruwanki kazar me ance miki ni irinki ne?,girgiza kai tayi da cewa"a'a tare da mik'ewa tana murmushi ta fita.

Washe gari Hajiya tace Hussain ya tafi da Hassu makarantarsu Fatima za'a mata jarabawa tunda tayi primary a k'auyensu sai a d'auketa JSS1 yace"Hajiya wannan k'atuwar yarinyar Jss1 ai ta wuce nan sannan kuma kin san dai babu abinda ta sani bazasu d'auketa ba" tace"Hussain mun riga munyi waya da shugabar makarantar nace yau zakazo da ita,haba ba don ransa yaso ba,yace suzo yana jiransu a mota,Zainab da Fatima ne a gidan baya Hassu a gaba,domin Zainab zata shiga Hassu tace ina bata isa ba ai idan zasu fita gaba take zama don haka yau don hardasu hakan bazaisa ta shiga baya ba,haka Zainab ta hakura ta shiga baya.

Zainab ya fara saukewa Poly inda take karatunta sannan ya wuce da su Fatima Capital School inda cen Fatimar ke karatu tana SS2,Har cikon harabar makarantar ya shiga da motarsa,bayan yayi parking Fatima ta wuce class d'inta su kuma suka nufi office d'in shugaban makarantar.

Don jin jarabawar Hassu mu had'e a page na gaba.🤣🤣🤣🤣


*MORE COMMENT MORE TYPING*

*'YAR SUNUSI JIKAR RABI'U WATO FATIMA*

*FATIMA SUNUSI RABI'U.**HUSSAIN*
🌹 _MIJIN ALJANAH_ 🌹
*80K*

*SHORT AND TRUE LIFE STORY*

*MALLAKAR👇*

*FATIMA SUNUSI RABI'U*
*Ummu Affan*



*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]


_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_

*Page 17-18*

Bayan sun shiga Office da sallama,gaisawa Shugabar sukayi da Hussain sannan ta basu izinin zama,yace"ga wacce Hajita tace na kawo miki" kallon Hassu tayi tace" 'yan mata zauna mana" Hassu wacce take ta kallon Matar ta sami guri ta zauna.

Takarda ta mik'awa Hassu bayan tace"me sunanki ne?" Hussain Hassu ta kalla domin da turanci ta tambayeta,d'aure fuska yayi yace"ba tambayarki akayi ba?" harararsa tayi tare da ta6e baki tace"ai na sani Malam ko kaji nace maka wani abu ne,ko k'auyenmu za'aje ayi tambaya kowa yasan nafi kowa k'ok'ari a cen."

Ga mamakinsa saiji yayi Hassu ta bata amsa kamar haka" My name is Hafsat Ibrahim" gyad'a kai shugaba tayi tana murmushi domin k'uruciyar Hassu ta burgeta.

Tambayoyi ta fara mata Hussain yasha mamakin jin yarda ta ke bada amsa duk da wani gurin dai sai a hankali amma sosai tayi k'ok'ari.

Takardar hannunta ta kalla wacce akace ta cike" shuru tayi tana bin takardar da kallo,kafin ta fara rubutu,kusan awa guda sannan ta bada,Hassu sai had'a zufa take,dubawa Shugabar tayi duk da wasu guraran ta fad'i wani gurin kuma taci kallon Hussain tayi tace"zamu d'auki HAFSAT kamar yarda Mahaifiyarka tace domin gaskiya yarda na kalli yarinyar da xata sami ilmi k'wak'walwarta zata bud'e sosai domin da alamar hakan."

Yace"to muna godiya" Form ta basa tace"muna so ku cike wannan azo mana dashi gobe sannan ita ma tazo cikin shirin makaranta zamu bata class,yace"da kyau muna godiya sosai" sannan suka mata sallama suka wuce.

A mota kowa yayi shuru Hussain Hassu ta basa mamaki baiyi tunanin haka daga gareta ba,koda ya sanar da Hajiya tayi farin ciki matuk'a nan take tace zata je kasuwa sayo mata uniform ta bada d'inki da kuma littattafai.

Hajiya Balaka Sunan mahaifiyarsu Hussain macece mai matuk'ar ilmi da son jama'a tana da kyirki sosai,yaranta uku Hassan da Hussain wad'anda 'yan biyu ne sannan Fatima Allah ya amshi rayuwar mijinta mutum mai dattako da fara'a yana da son mutane sosai mutum ne d'an kasuwa,bayan rasuwarsa Hassan da Hussain sukaci gaba da kasuwancin bayan dawowarsu k'asar India inda suka kammala karatunsu,ko da yake shi Hassan yana Abuja inda yake aikinsa Hussain kuma yana nan Kaduna yana kula da shagunansu.

Da mahaifinsu Hussain da mahaifin Zainab wa da k'ani ne uwa d'aya uba d'aya,ita kuma Hassu mahaifinta Baba K'arami k'ani ne a gurin Hajiya shima uwa d'aya uba d'aya suke ,wannan kenan.

Hassu ta fara makaranta boko da Islamiyya sosai ta fara natsuwa saboda ta had'u da wata k'awa Rahma wacce 'yar gidan masu dashi ce akwai wayewa a tattare da ita duk da mata cika surutu ba amma tana koyar da Hassu abubuwa da yawa don tun farko ita ta fara shigewa Hassu tana sonta da k'awance,ita Hassu kowa nata ne don d'an banzan surutu ne da ita,duka class an santa,sune group na marasa jin magana a class d'insu 'yan ajima basu ragawa ba bare malaman da suka raina kansu.

Rahma ce ta fara jan Hassu jiki inda take nuna mata abubuwa na wayewa,da farko ta fara jin Haushin Rahma amma daga baya sai ta aminta domin acewarta so take tafi Zainab wayewa da iya kwalliya domin gasa take da ita,ko gurin Hussain taga taje yanzu itama zata je ta faea surutunta na banza,ta dena aljanun k'arya amma tanama Hussain duk lokacin ta taso tsorata shi domin ta lura yafi kowa tsoran aljanu sunansa kuwa da ta sa masa MIJIN ALJANAH ya tsani sunan amma babu yarda zaiyi da ita.

Hajiya ce zaune da mahaifin Zainab yana mata magana akan su Hussain yace"ba zai yuwuba fa mu zubawa yaran nan ido sunyi karatun har sun k'oshi dashi Hussain na kasuwanci amma har yanzu baya maganar aire don haka ina mai sanar miki ki sanar masa ya fara shirin aurensa da Zainab" tace"ni kaina Alhaji ina so yayi auran nan sannan ina godiya da k'ara jajircewarka akansu xan fad'a masa yace"yauwa" sannan ya mata sallama ya tafi.

Koda ta sanarwa da Hussain maganar yace"bai san zancen ba shifa baice yana son Zainab ba.

Zainab zaune tana danna wayarta number d'in Hussain ta dannawa kira,lokacin yana kasuwa harta katse bai d'auka ba, Hassu dake zaune gefe tace"tusa kai inda ba asonka ai wahala ne,nan ta fara 'yar waqarta wacce tagaji habaici take" _Leliyar liye banyinsa la-la-la-la-lah son maso wani k'oshin wahala alalayyo._

Zainab tasan da ita take,sai bata kulata ba taci gaba da kiran number Hussain har lokacin dai bai d'auka ba.



_MUJE ZUWA_
*FATIMA SUNUSI RABI'U.**HUSSAIN*
🌹 _MIJIN ALJANAH_ 🌹
*80K*

*SHORT AND TRUE LIFE STORY*

*MALLAKAR👇*

*FATIMA SUNUSI RABI'U*
*Ummu Affan*


*WANNAN page d'in naki ne Bestiena Rabee'at Muhammad MAMAN KHALEEL kiji dad'inki dashi ina yinki over my bestie🥰🥰*

*My k'awar amana Rukayya Ibrahim Lawal UMMU INTEESAR kema kiji dadinki ina yinki irin sosai d'in nan,Allah ya bar so da k'auna🥰🥰*

*My K'anwata Maryam Ibrahim DR MARYAMAH kema kiji dad'inki ina yinki irin sosai d'in nan Allah ya bar zuminci🥰🥰*


🔚🔚🔚 _LAST PAGE_


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]


_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_

LAST PAGE
*Page 19-20*

Hassu tace"wallahi an daiji kunya babbar budurwa dake kin tsaya kina faman bin namijin da bai sonki,ko da kin auresa bakiji dadin zama da shiba tunda ke ke sonsa shi ba sonki ya ke ba sannan ina mai sanar miki MIJIN ALJANA ne,idan ma kika kuskura kika auresa wallahi kece a ciki domin Aljanar matarsa zata miki hukunci dai-dai da laifinki."

Sosai Zainab ta zubawa Hassu ido,ita kuwa ganin haka ta sake wani zaro ido da d'aure fuska tamkar dai aljanarce ke magana,ta d'aura da wak'ar " _Sabuwa ta zuma nice ban zama aibuba dani da angona sam bazamu ware ba._

Zainab tayi shuru ta kasa magana,miqewa Hassu tayi tace"idan kunne yaji jiki ya tsira,tayi wucewarta.

Zainab sosai ta tsorata da yanayin Hassu a ranar ta had'a kayanta tace zata koma gida,Hajiya ta mata tambayar duniyar nan tace"ba komai kawai yana son komawa ne" haka Hajiya ta had'a mata sha tara ta arzik'i sannan tasa direba ya mayar da ita gida.

Hussain ko da ya dawo aka sanar masa d'aga kafad'a yayi da cewa tafi nono fari.

BAYAN SHEKARA SHIDDA.

Hafsat Ibrahim ce ta fito daga zana jarabarta ta k'arshe da sukayi na waec da neco.

Sai da na k'ara bud'e idanuwana sosai ganin yarda Hassu ta dawo wata k'atuwar budurwa ta cika sosai ta k'ara haske girma sosai,kallon Rahma tayi wacce suka fito tare tace"my Rahma Allah ya kawomu mun ida jarabawarmu Allah ya bamu nasarar samun sakamako mai k'yau" Rahma ta amsa da"amin my k'awa,yanzu sai yaushe?tace"sai mun had'u islamiyya kenan" Rahma ta shige motar direban gidansu tana d'agawa Hassu hannu,dai-dai tsayuwar wani d'an saurayi gabanta "yan mata barka da hutawa,ya fad'a,ko kallonsa batayi ba ta kauda fuska,yace"haba 'yan mata magana fa nake" bata waigoba,tsayuwar motar Hussain yasa tayi saurin waigowa gurin saurayin tare da sakin fuska tace"ya kake?,sosai yayi mamakin kulasa da tayi,yayi saurin shanye mamakinsa da cewa"yauwa daman ina so na sanar miki wallahi ina sonki sosai,ina yawan ganinki Allah baisa na ta6a miki magana sai yau" murmushi d'auke a fuskarta tace"karka damu ka samu shiga don naji kaima ka burgeni matuk'a" Hussain wanda ya fito maganar Hassu karaf cikin kunnuwansa,binsu yayi da kallo bayan ya jingina jikin mota ya hard'e hannayensa saman k'irjinsa ya zuba musu ido,Hassu sai k'ara karairaya ta fari da ido da fara'a take gaban saurayin kuma duk saboda taga Hussain ne take wannan abun.

Shi kywa sosai ya k'ula da jin kalamanta,zuba musu ido kawai yayi amma ji yake zucitarsa kamar zata faso k'irjinsa saboda takaici.
Ransa ya 6aci matuqa da jin wannan kalaman nasu,juyawa yayi ya koma cikin mota,Hassu na ganin haka tama saurayin sallama yana tambayarta number wayarta da kwatance gidansu bata kulasa ba ta fad'a mota ganin har Hussain har ya tada,ai kuwa ko gama rufewa batayi ba,ya wani funciki motar da gudun tsiya abun har yabata tsoro matuqa,kallonsa tayi ganin yarda idanuwansa suka chenza kala tayi wani murmushi aranta tace''ana so ana kaiwa kasuwa,mutum sai miskilanci da girman kan tsiya to wazaka mawa?zanyi maganinka cikin ruwan sanyi.

Har suka isa gida ba wanda yayi magana cikinsu,yana parking ya fita a fusace zuwa ciki,girgiza kai Hafsat tayi da d'an murmushi a fuskarta tabi bayansa.

Hajiya zaune a parlour ita d'aya,shekaru biyu kenan da yin auren Fatima wacce ke aure acen Katsina itama Zainab tayi aurenta harta haihu domin rana d'aya akayi bikinsu da Fatima,tundaga habaicin nan da Hassu ta mata ta fara cire Hussain a zuciyarta tana kammala digirinta kuwa ta fitar da miji sukayi aure tare da Fatima ko waccensu tana zamanta lafiya da mijinta.

Hajiya tabi Hussain da kallo wanda yayi sama,Hafsat ta shugo da sallama ta mayar da dubanta gareta zaunawa Hafsat tayi kusa da ita "Hajiya sannu da gida" "yauwa ta amsa sannan ta d'aura da cewa"waccen uban 'yan zuciyar kuma shida wa?naga ya shugo a harzuk'e?nace"ina zan sani Hajiya nima haka na gansa"

Cikin ikon Allah takardunmu suka fito kuma na sami abinda ake so hakan yasa na fara cuku-cukun zana jarabar jamb da lokaci yayi.

Hajiya ta sani gaba akan ya kanata na fito da miji sai naci gaba da karatuna a gidan miji,Hussain yace"hakan shine dai-dai.nace"to badamuwa insha'Allahu" Hajiya tace"hakan shine yafi domin kina ganin dai yarda a k'auye aka sa miki ido wai har yanxu kink'i aure gani ake ma nice na hanaki wai sa'anninki harda basu yara biyu" nace"haka ne"

Tashi nayi na nufi ciki Hussain ya kalli Hajiya yace"Hajiya nifa ina ganin da Hafsat za'ayi domin yarinyar ta shamma ceni matuqa" ya fad'a yana murmushi qasa-qasa,sosai Hajiya taji dadin batun cikin ranta matuqa amma saita ce"idan ma sonta kake ni babu ruwana kaje da kanka ka nemi soyayyarta idan ta amince to komai yazo gidan sauqi idan tace a'a to ni bazan takura mata ba" Shuru yayi baice komai ba domin shi a tunaninsa Hajiyar zata ce ta amibce zata mata magana da kanta.

Haka har sati biyu bayan nan ya kasa yi ma Hafsat magana gashi yana ganin yarda samari ke kawo mata hari,haka yayi k'undun bala wata ranar juma'a ya sanar mata,kallonsa take aranta dad'i tace"sosai amma a fili tace"zanyi tunani,ka bani lokaci" tun daga ranar har kusan sati Hafsat bata ce masa komai ba hankalinsa ya tashi matuqa nan fa yaxo ya sauke girman kan nasa ya dawo ya saki jiki da ita yana mata kalaman soyayya kai kace bashi bane,ita kuwa ganin haka take ta garasa.

Wata ranar Asabar ta dawo islamiyya bayan tayi wanka tayi sallah tana kan sallaya ya shugo d'akinta abinda bai ta6a ba,murmushi tayi ta dubesa bayan ta shafa addu'a tace"Yaya Hussain da kanka,yace"eh ai zuwa da kai yafi saqo Hafsat ganin na baki duka zuciyata shine kike ta garani kamar wata kwallo ko?,tayi murmushi tace"Yaya Hussain ina tunanin ko zaka iya da halina ne saboda nasan halinka,abu na farko ni dai kasan duk abinda nake so idan baifi qarfinka ba zaka sayamin kai kuma nasanka da maqo sannan kasan dai ina da aljanu sukan tashi lokaci zuwa lokaci to ya kenan kanajin zaka iya dani kuwa?".

Yace"ni dai nasan ina sonki koma menene bai shafeni ba,maganar maqo dakike magana yanxu na dena" tace"to shi kenan ka bani kwana biyu zan sake tunani"

BAYAN WATA BIYU
Zuwa wannan lokacin soyayya mai k'arfi ta qullu tsakanin HUSSAIN 80K da Hafsat wacce yanzu har an fara maganar aurensu Hajiya da Baba K'arami sunyi farin ciki wanda har yanzu halinsa na nan amma yayi mamakin yarda yanzu Hussain ke masa kyautuka,haka ya taka har Kujama yaje ya gaishe su,tabbas yasan yanzu Hussain yanzu ya sauya sosai.

Hussain da Hafsat suna son junansu matuqa yanzu haka an bashi sauran saka rana da biki. Idan taso ta dunga tsokanarsa da MIJIN ALJANAH sai dai yayi murmushi kawai,idan suka tuna baya kuwa sin dunga dariya.

(TO MIJIN ALJANAH HUSSAIN 80K🤪🤪INA MUKU FATAN ALKHAIRI ALLAH YA KAIMU LOKACIN BIKI MUNA NAN ZUWA 'YAN AREWA WRITERS DA KUMA FANS D'IN WANN NOVEL FATAN ALKHAIRI.)

SANNAN KARKU MANTA WNN LBR NE NA GASKE AHA.

GODIYA GA Allah da ya bani ikon kammala wannan d'an gajeren labarin da nayisa don nishad'i fatan alkairi gareku masoyana ina sonku sosai da sosai.

TAMMAT BI HAMDULLAH
ALHAMDULILLAH


WhatsApp number 08104335144
*FATIMA SUNUSI RABI'U*


Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2

Please Login or Register in order to submit comment