Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

gabatar da wasan, ga amarya nan da ƙawayenta, suma waje suka samu suka zauna suna dan taba hira, "ƙawata gafa mutumin nan yana zuwa" tsaki Zainabu tayi ganin wanda yake zuwa, "Assalamu alaikum gimbiyata" tsaki ta kuma ja a karo na biyu, "nikam Bala na tmby ka mana" washe baki yayi, ya dauka ko ta fara saukowa ne, zata kulasa, "amma dai a cikin dangin ku akwai maye ko?" zaro ido yayi jin wannan cin mutunci, "yoo in ba akwai maye ba irin wannan baƙin naci, soyayyace nace banayi dakai, ko ana dole ne, Bala","na'am gimbiyata","hohoho Bala, ka fita idona in rufe inajin kunyar ka fa, kada ka bari nayi maka abinda bazaka taba mantawa ba","nide indai zaki soni ki fadi koma miye, babu komi","kab amma dai Allah yai wadaran naka ya lalace, kinga Siyama tashi mu tafi" haka yasa suka baro wajan ba tare da sun kalli wasan ba, Siyama kuwa sai tsine mai take, yayi sanadiyar da basuga wasan da taci burin gani ba.




******

Durƙushe yake a gaban mahaifinsa, ya sunkuyar da kansa kasa, idanuwansa sun kada sunyi jajir, jijiyoyin kansa duk sun fito, jikinsa har rawa yakeyi tsabar bacin randa yake ciki, "Abee understand me plss, heyy stop I've already finished talking is either you choose us or her" yana gama fadin haka ya fice daga falon yana baza babbar riga, dama wajan aiki zaije,



"Mahammad Kareem" mahaifiyar sa ta kira sunan sa, tunda yaji ta kira cikakken sunansa yasan magana mai mahimmaci zatayi, "tunda har mahaifin ka bayason alakar ka da yarinyar nan to kayi hakuri ka rabu da ita" dogo kansa yayi ya kalli mahaifiyar sa, ita kanta saida ta tsorata ganin yadda idonsa ya kada, "Ammi I'm sorry pls it is not that I can't leave her, indan hkn kuke so I'll definitely leave her sedai this will be the reason for my passing away, xan mutu kawai Ku huta nima in huta! "Babu abinda zai same ka Muhammad Kareem sai Alkairi, ka cigaba da addu'a, nima zan cigaba dayi maka addu'a, kana tare da addu'ar mahaifiyar ka, a koda yaushe" ta fada tana shafa baƙar sumar kansa, hakan da Ammi ta fada masa yasa zuciyarsa ta danyi sanyi, "tashi kaje ka watsa ruwa, zakaji dadi a jikin ka" daga mata kai yayi ba tare da yayi magana ba,




Bayan ta gama sauraron duk abinda suke cewa, tana jin alamun za'a fito, da sauri tabar wajan tana cike da farin cikin wannan alamari, yau duniya tayi mata dadi, ji take kamar ta zuba ruwa a kasa tasha dan dadi, tashi yayi ya fito daga dakin Mahaifiyar tasa ya shige dakinsa, da kallo ta bisa har ya fice daga dakin, zuciyarta cike da tausayin ɗan nata, ta rasa wannan wace irin bakar gaba ce.











Shere fisabilillah.
✨✨ *ZAINABU ABU* ✨✨

Na

ZAINAB A BARDE



*ALƘALAMI YAFI TAKOBI WRITERS ASSOCIATION*
(A.Y.T.W.A)



Free page 7 nd 8



***


yana shiga dakinsa ya fada kan makeken gadon sa kirar royal, gaba daya duniyar tayi masa zafi, bai kamata Abee ya sako gabar su a cikin neman auran sa ba, " I will never disappoint you Abee, I will do as you wish, I will leave Shahida even if that will be the end of my last breath, ya Rab i pray with the best name of yours, Rab don't ever show me the day that I'll betray to my dad's command, ya Rab give me the effort to obey him appropriately, ya Rab i pray, ka cire min son yarinyar nan da duk wani abu da zaisa in bijirewa iyaye na" tashi yayi ya fada tiolet,



Ruwa ya sakarwa kansa, wani sanyi ya rigaji yana shigar sa, jin saukar zuwan a jikin sa, yana fitowa ya zura jallabiya, ya kwanta, dan baya jin zai iya zuwa office, saboda a zababban ciwo da kansa yakeyi, kamar zai rabe gida biyu, wayarsa ce ta fara ringing, sunan Nurul Qalb ne ya fito baro baro akan screen din wayar, kasa daukar wayar yayi, coz he couldn't disobey his dad, ganin bazata daina kira ba, shiyasa ya saka wayar a silent, tunanin yadda zai cigaba da rayuwa ba tare da Nurul Qalb ba yakeyi, a haka har bacci barawo yayi awon gaba dashi, dama yana bukatar yayi baccin, daran jiya kwata kwata baiyi bacci ba saboda tashin hankali, Ammi ce ta shigo dakin, zama tayi a gefen gadon tana kallon sa cike da tausayi, "ka cigaba da hakuri Allah yana tare da masu gaskiya da masu hakuri, soon everything will be alright" fita tayi tare da ja masa kofa.



****

"Umma! Umma! Umma! "ke Shahida what's wrong kikemin irin wannan kiran?","Umma where is Abbana?","ya fita office kema kinsan ba'a samun sa a gida a ɗai ɗai wannan lokacin, but are you really okay?","Umma I've been calling Kareem's number but he isn't picking, Umma I'm afraid of his dad kada ya hanamu yin aure","Shahida I've been telling you earlier to remove his love out of your mind , don't even let your dad to know this, in kuwa ya sani wllhi ranki zaiyi mummunan baci"," but Umm... dakatar da ita tayi ta hanyar daga mata hannu, hakan yasa dole tayi shiru, tare da fashewa da kuka, da gudu ta haura sama tana kuka, abin kwanin ban tausayi, dakinta ta shiga ta fada kan gado tana sakin wani marayan kuka, cigaba da kiran wayarsa tayi, amma still no answer, kara fashewa da kuka tayi, a haka har bacci ya dauketa with dried tears on her face.




"Saddiqa wato kece kike daure wa yaron nan kugu ko?","Alhaji nifa I don't even know what you are talking about"," ohhh dama how would you know? Let me tell you something, dagake harshi, karku kuskura gobe yaƙi zuwa office, lots of work yana can office dinsa yana jiransa saida na tmby akace min baizo ba, wato dan nayi masa fada, shine zaiƙi zuwa aiki, Allah yasa gobe kar yazo, I will show you the true colour of mine, dan Allah Alhaji ka rika sassauta wa yaron nan","ohoo wato dai maganata tana kan hanya kece dindai kike hure masa kunne","wllhi ba haka ban... ko sauraran ta baiyi ba ya shige bedroom dinsa, ransa na suya, tashi tayi ta fito daga dakin tana sharar kwalla, she don't exactly know what is wrong with her husband these days gaba daya ya birkice, ya kuma chanza mata, ita dai tasan da ba haka mijin ta yake ba, amma tana kaiwa Allah kukanta komi yayi farko yana da karshe insha Allah.



Mami na ganin fitowar Ammi ta shiga dakin, dama tana labe duk taji abinda suke cewa, shiga dakin tayi, ganin baya dakin kuma taji saukar ruwa, shiyasa ta tabbatar yana toilet, kaya mararsa nauyi ta fito masa dashi, yana fitowa ta tayashi ya shirya, cikin makirci da kisisina tace, "Alhaji are you alright? It seems as if you are a bit angry,"ki bari kawai Maimuna, abubuwan yaron chan sun fara isata, ya rasa wadda zai ce yana so, sai yarinyar nan ƴar wajan Alhaji Bukar, kuma yasan da cewa duk duniya banida makiyi sama da mahaifin yarinyar","ai ina ganin Alhaji this is so simple kallon ta yayi jin tana kiran abinda yake bakanta masa rai da abu mai sauƙi, "ni a nawa ganin ka bi duk wata hanya da zaka bi, dan ganin ka toshe duk wata kofa da kasan zata sada shi da yarinyar, sannan shi kuma Alhaji Bukar kaje kaja masa kunne akan ƴarsa ta rabu da danka, idan ba haka ba zaka dau mummunan mataki akan yarinyar","wow!! That's why I always love you , saboda duk lokacin da na shiga damuwa, kinsan hanyar da zaki bi ki faranta min rai"



Murmushi ta saki tana fadin "ba komi it is my priority,"yaran nan sun dawo daga makaranta kuwa?,"ehh sun dawo amma yanzu suna islamiyya,"to in sun dawo kice musu inason ganin su","to shknn Alhaji lemme leave you to have some rest, jinjina mata kai yayi, tana fitowa daga bangaran Abba, tana saukowa main falo taga Ammi ta zabga uban tagumi, murmushi tayi, "this is how I always want you to be, I don't want you to be damn happy "tagumi ma yanzu kika farashi a gidan nan, muddin na haifu a wajan iyaye na" zama tayi a kusa da Ammi tare da marairai ce fuska,




"Saddiqa lfy kuwa kika zabga uban tagumi haka?" firgigit tayi saboda batasan da zaman ta ba awajan, "wllhi Hajiya Maimuna, Alhaji ne ya sako yaron ki a gaba, akan zanchan naiman auransa, yace Kareem will never marry shahida because she is his enemy's daughter, dan Allah mai zaisa ya sako gabar su, a cikin neman auran yaron nan? hakane take heart dears insha Allah everything will be alright, mu bi komi a sannu, I'll talk to him insha Allah he might Change his decision,"Allah yasa to, yauwa in yaronki sun dawo yace yana son ganin su" daga mata kai Ammi tayi, saboda duniyar gaba daya tayi mata babu dadi, tashi tayi ta wuce bangaran ta, ranta fal farin ciki.





*******

Boss! Boss!! Boss!!! jiyowa wanda ake kira da Boss yayi, Masha Allah shine abinda na iya furtawa, saboda cikar haiba, da kamala, ta matashin saurayin mai jini a jiki, mai ji da kuruciya, a hankali ya dago da idanuwan sa, da suke fari tar, ya kalli wanda yake kiransa, da Boss, cikin zazzakar muryarsa ya fara magana, "Baabaa lfy kake kwalla min wannan irin wannan kiran?","Boss ka kunna labarai, gaba daya garin nan ya dauka akan fashin da mukayi jiya da daddare a Bank din nan" remote ya dauka ya kunna tashar labarai,



"Muna kawo muku labarai da ganan gidan TV A nd Z, to masu sauraran mu kamar yadda kukejin jita jita, akan wannan shaharanran dan fashin, mai suna Boss, wanda har yau babu wanda yasan kamannin sa, yauma ya sakeyin sata a shaharanran Bankin nan, dif ya kashe TV murmushi dauke a fuskar sa, "Baabaa ka bari kawai, garin nan ma bazai gigice ba, sai randa muka kaddamar da nest plan dinmu"







Shere fisabilillah.
✨✨ ZAINABU ABU ✨✨

Na

ZAINAB A BARDE



ALƘALAMI YAFI TAKOBI WRITERS ASSOCIATION
(A.Y.T.W.A)



Free page 9 nd 10



***



"Ka gayawa sauran yau zamu sake fita operation","amma Boss baza mu bari wannan zanchan ya dan lafa ba" murmushi yayi har fararan hakoransa na fitowa, "naka wasa ne kenn, kana jin tsoro ne","aa Boss, ai mu ko wuta kace mu shiga zamu shiga, balan tana wannan abu mai sauƙin" murmushin gefen baki ya kuma yi, "to kaje ka gaya musu, kuma anjima dukkan ku kuzo ku same ni, sai mu tsara yadda abin zai kasance","an gama Boss" yana fita shima ya haura sama dan ya samu ya dan huta, saboda jiya bai samu yin bacci ba.




***



Asmah da Asfah na dawowa daga makaranta Ammi ta sanar dasu saƙon Abee, uniform kawai suka cire suka tafi kiran da yake musu sallama sukayi amma bai amsa ba, basu shiga ba saida suka sakeyin sallama ya amsa tare da basu izinin shigowa, sannan suka shiga suna masu faduwar gaba, saboda basu san naiman mai yake musu ba, "Abee barka da dare" suka hada baki wajan fadin hakan, "how are you? And studies? Abee yace,"Alhamdulillah","anayin karatun ko kuwa ana wasa ne?" muskutawa Asmah tayi, "wllhi nide Abee ina yin karatu sosai, Asfah ce dai bata da aiki sai wasan banza da mazan ajinmu, and if I talk to her bataji, saboda tana ganin itace babba,




Afirgice Asfah take kallonta jin wani mummunan sharri da tayi mata, ita da ko magana bata hada ta da yan mazan class dinsu, saboda tsananin kamun kanta, har tsoran yi mata magana sukeyi, hasalima itace mai shiga cikin mazan, amma shine zatayi mata sharri, tun kafin Abee yayi magana har hawaye ya wanke mata fuska, "so this is what you are doing at school right? a haka dai gaki kamar ta Allah ashai ba haka bane, sum sum sum dake, ashai micijin tsari ka noke ce, to zanyi maganin ki wllhi, I will never tolerate this nonsense,"wllhi Abee she lied to me.



"Sharri takemin, abee wllh I don't even talk to them, kuma aje a tambayi yan class din namu" ,"wana yan class za'a tmby, shaida ta wuce wacce yar uwarki ta bayar, to tunda abin naki haka ne daga yau na haramta miki zuwa makarantar! kuka ta kara rushewa dashi, "dan Allah Abee kayi hakuri, wllhi ban aikata ba Abee, inason karutu" ta fada tana rike kafafuwansa, hankada ta yayi yana fadin "I've said mine, daga yau ban yarda ko kofar gida ki leka ba, muddin kuma kikayi haka naji labara, zakiga hukuncin da zan dauka akan ki, fita ki bani waje" da gudu ta fito tana kuka,



Wani irin farin ciki ne ya lullube Asmah, yau burinta ya cika, shknn ta yadda kwallon mangoro ta huta da kuda, no one will stop her or put eyes on her at school she will just do as she wish, dama Asfah ce mai sa mata ido, duk abinda tayi sai ta fara mata wa'azi, by now everything comes to an end"zaki iya tafiya Asmah, gara da kika fada min, kinga yanzo gashi nayiwa tufkar hanci, Allah yayi miki Albarka","Ameen Abee" daga haka ta fito tayi bangaran Mami, tana shiga ta tarar da ita, tana karanta jarida, "wash Allah, na gaji wllhi" kallonta Mami tayi, "kije ki watsa ruwa sai kizo kici Abinci, kinga wani labari nagani akan wani shahararran dan fashi, wai daran jiya ya shiga banki yayi musu mummunan sata","yeah mami this news is trending everywhere amma Mami ya naga kamar kina cikin farin ciki?"



"Ai dole ne ki ganni cikin farin ciki, ke yau ni har ruwa zan zuba a kasa na sha dan dadi, "wanchan banza ne yazo da maganar aure","wa kenn Mami? Muhammad Kareem mana" kwalalo ido Asmah tayi, so what happened then? "Do you even know who's daughter he is dating?" girgiza kai tayi, tanaso taji karshan zanchan, "it's Alhaji Bukar's daughter","na shiga uku" ta fada tana dafe kirji, "to mai Abee yace?"," cewa yayi he will not marry her kuma ko bayan ransa in ya aureta bai yafe masa ba","amma gaskiya Abee ya kyauta, that's great, Gara da ya hanasa ya auren ta","you don't even know uwarsa na chan ta shiga cikin tashin hankali, ta rasa inda zata saka kanta","Mami ai sai yanzo nema zata kuma shiga tashin hankali" nan ta bawa Mami labarin duk abinda ya faru, harda hana Asfah zuwa makaranta da Abee yayi, rungume yartata tayi, "Allah dai yayi miki Albarka, dama nasan barewa bazata taba yin gudu danta yayi rarrafe ba, maza tashi kije ki gyara jikin ki, kizo muci abinci, yau mukam kwanan farin ciki zamuyi, wasu kuwa nachan zasuyi kwanan bakin ciki"," sure Mami" ta fadi haka tana shigewa dakinta, danta watsa ruwa.




Tun daga dakin ta take iya jiyo kukan Asfah, "wannan ita kuma kukan mai takeyi" jin har zuwa wani dan lokaci bata daina kukan ba yasa tace let me go and check what is wrong with her, a hankali ta bude kofar dakin, kwance ta ganta akan gado tana kuka, ta juyawa kofar baya, a gefan gadon ta zauna tana fuskantar ta, "Asfah what's wrong, mai akayi miki da har yasa ki zubda hayawe? jin muryar Ammi yasata mikewa da sauri ta fada jikinta, kara fashewa da kuka tayi, "kiyi hakuri ki fada min abinda ya faru"nan ta bata labarin abinda ya faru, ta kara da cewa, "kuma yace bazan sake zuwa makaranta ba, yace kuma ko nan da kofar gida na leka bai yafe ba","kiyi hakuri kinji zanje inyi magana dashi, ki kwantar da hankalin ki, kuma ki daina kukan nan" da sauri ta share hawayen ta jin Ammi zataje tayi magana dashi.



Tana fitowa daga dakin darect wajan Abee ta nufa, tana shiga dakin ta tarar dashi yana kallon labarai, "banfa gane abinda kake nufi dani da kuma ya'yana ba, ka hana Muhammad auran wacce yakeso, yanzo ita kuma Asfah kace bazata sake zuwa makaranta ba, ko danka ga yaran nan suna maka biyayya ne? to kada ka bari wannan biyayyar su daina maka ita, na dai gaya maka, wannan shawara ce kyauta" tana gama fadin haka, tayi fitowar ta, "Saddiqa Saddiqa, tana ji yana kiranta, amma tayi kunnen uwar shegu dashi, ko juyowa batayi ba, balle yasa ran zata dawo, gaba daya jiyai jikansa yayi sanyi, tunda yake da Saddiqa, yau shaikara talatin da biyu kenn, bata taba daga masa murya ba, amma yauga abinda tazo tayi masa, lallai yasan he pushed her to an end.



Tunda Muhammad Kareem ya shiga dakinsa bai fito ba, ko salla a daki yakeyi, abinci kuwa ko takansa baibi ba, yanzo hakama ya idar da sallar isha, yana karatun Alkur'ani mai girma, da sallama ta shigo dakin, hannunta dauke da tray, saida yakai aya sannan ya amsa mata sallamar, "Yaya ga abincin ka, kuma Ammi tace dan Allah ka daure kaci yanzu, kallon yadda take masa magana kai a sunkuye yayi, "come here" ya fada chan kasan makoshi, ita kanta badan ta kasa kunne ba, da bazata ji abinda yace ba, zuwa tayi ta durkusa a gabansa, "gani Yaya","mai ya sami fuskar ki haka, sannan kuma kukan mai kika yi?" abinka da farin mutum gaba daya fuskarta tayi jajir, ya tabo mata inda yake mata kaikayi, nan kuwa ta kara fashewa da kuka, he didn't stop her, because he don't know the reason of her tears, shi kansa da zai samu yayi kuka, da he might feel better based on what is worrying him.




Kusan minti biyar, sannan yace "you know I don't like crying, tell me what happened that makes you to shed tears, kwashe duk abinda ya faru tayi ta gaya masa, nan fa ransa ya kara baci, duk duniya inka cire iyayan sa, bashida abinda ya fiso sama da kanwar sa, bayaso ya ganta cikin damuwa, shiyasa suke yawan samun sabani da Shahida, danme zaina nunawa kanwar sa, soyayya irin haka, shi bama sharrin da Asmah tayi mata bane ya bata masa rai, hukuncin da Abee ya dauka ne yafi komi bata masa rai, "did you pray?" daga masa kai tayi, "to kije kiyi alwalla kiyi addu'a ki kwanta bacci, gobe ki shirya kamar yadda kika saba, zan kaiki makaranta da kaina","amma Yaya" dakatar da ita yayi, "kiyi abinda nace kawai","to Yaya saida safe"



Zai iya jure komi idan anyi masa, amma bazai jure ganin kanwar sa cikin damuwa ba, zaiyi duk yadda zaiyi yaga ya sanya kanwarsa da mahaifiyar sa farin ciki koda zai rasa nasa farin cikin ta sana diyar nasu farin cikin.













Shere fisabilillah.
✨✨ ZAINABU ABU ✨✨

Na

ZAINAB A BARDE



ALƘALAMI YAFI TAKOBI WRITERS ASSOCIATION
(A.Y.T.W.A)



Free page 11 nd 12



****


Karfe daya da rabi na dare, gaba daya ko ina ji kake sitt, bakajin karar komi, sai haushin karnuka, ko wana bawa yana chan kwance yana huta, dama hausawa na cewa dare mahutar bawa, to anan ma hakance ta kasance, Boss da yaransa ne sukayiwa gidan mai girma Alhaji Murtala Chanji dirar mikiya, a cikin gidansa tare da iyalansa, ko wanne a cikin su, fuskar sa a rufe take, babu abinda ake iya gani a fuskar su sai idonsu, gaba dayan su sanye suke da bakaken kaya, hatta da hannayen su da kafafuwan su, sanye suke da bakar safa,



Koda suka shiga gidan gaba daya mutanan gidan bacci sukeyi, "ku shiga dakunan ku fito min da kowa da yake cikin gidan nan, babba da yaro banaso ku bar kowa, ku fito min dasu duka" nan danan suka cika umarnin Boss, fitowa akayi da Alhaji Murtala Chanji tare da matarsa, Baabaa ne ya hankado babbar diyar sa mace tare da karamin kaninta wanda bai wuce shaikara goma ba a duniya, "ku durkusa akan gwiwowin ku mana, Boss na tsaye kuma kuna tsaye, "Baabaa ya daka musu tsawa, aiko cikin rawar jiki da tashin hankali suka durkusa a kan kafafuwan su.




Zama Boss yayi akan daya daga cikin tsadaddun kujerun falon, ya dora kafa daya akan daya, kamar yana zaune a falon gidansa, "cikin zazzakar muryar sa ya fara magana, "inaso ka bamu kudin nan da aka kawo su cikin gidan nan dazo, wannan shine kawai abinda ya kawo mu, infa ka bamu hadin kai kenn, in kuma kace zaka bata mana lokaci, tofa baza kaji dadin abinda zanyiwa iyalinka ba","aa yallabai babu wani kudi a cikin gidan nan","owk taurin kai zaka gwada mana kenn","aa yallabai gaskiya nake gaya maka","owk ke kuma inaso ki kwaso mana gwalgwalan ki, cikin rawar jiki tace to, "gwaska ka rakata ta dauko" cikin mintuna kalilan ya rakata ta dauko su, "kai kuma tunda taurin kai zaka gwadamin, Baabaa kuyimin fata fata da yarinyar chan" ya nuna yarinyar, cikin tashin hankali ta fara ja da baya tana girgiza masa kai tana hawaye, Baabaa na binta yana murmushin wannan dama da Boss ya basa,



"Yallabai kar kuyi min haka zan bayar, zan bauar wllhi, kada ku yagawa yata rigar mutunci dan Allah","Baabaa dakata" wani bakin ciki yaji najin an dakatar dashi daga jin dadin da zaiyi, nan aka rakasa ya dauko kudin cike da manyan bags guda uku, tashi Boss yayi, "na barku lfy sai mun sake haduwa" daga haka shida yaransa suka fito daga gidan, motocin su suka shiga suka bar unguwar a dari.




****


Asuba nayi Zainabu ta tashi tayi sallah, sannan ta fara shirye shiryen dora wainar siyarwa, saboda da zarar gari ya fara wayewa za'a fara shigowa siya, "Jikata yau kece zakiyi tuyar wainar?","ehh Anna so nake yau kemah ki huta da wannan hayakin da kuma hayaniyar yaran nan, kije ki kwanta kiyi baccin ki, da zarar na gama suya zan dora miki ruwan wanka, sai kiyi wanka ki karya","to jikata" haka Anna ta shiga daki tayi kwanciyar ta, duk yaron da ya shigo yaga yau Zainabu ce take suyar waina, sai ya shiga hankalinsa ya kuma natsu, haka ba tare da wata hayaniya ba ta gama suyar wainar ta, sannan ta sallami yaran, sannan ta dora musu ruwan wanka, ta gayra gidan saf, sannan ta shiga wanka tana fitowa ta hadawa Anna ruwan wankan, tashin ta taje tayi, sannan ita kuma ta kawo musu abin karyawa, Anna na fitowa suka karya,




"Allah yayi miki Albarka jikata","Ameen ya Allah Annata","Allah kuma ya shirya min ke, ya kuma kawo miki miji na gari","nifa Anna bazan yi aure ba, ina nan tare dake" ta fada tana turo baki, "to bakiso kemah kiyi aure ki haifo min tattaba kunne, kamar yadda iyayen ki suka haifar minke","to waini Anna ba'a iya haihuwa ba tare da anyi aure bane? amma karki damu zanci tuwo da yawa anjima da daddare kinga gobe da safe sai in tashi da ciki, kinga daganan sai in haifa miki tattaba kunne" dariya ce sosai ta kama Anna jin wannan shashan cin, "toh shknn yau zan kara yawan tuwo saboda kici ki koshi kinji jikalleta","Anna ni bari naje, dama zanje gonar mai gari in tsunko mangwaro ","amma dai kinsan yayi gargadi akan zuwar masa gona a tsunko masa mangwaro ko?




"To ai wannan fadar sace, dan ya fada kuma sai mu daina zuwa? Ai indai saboda fadarsa na daina zuwa aiko ban ciki Zainabu Abu ba","to a dawo lfy jikata, kinsan duk abinda kikeso nima inason sa","na sani annata shiyasa kullum nake kara sonki, nide na tafi saina dawo","to Allah ya dawo min dake lfy" fitowa tayi tana fadin, "Allah ka hadani da abokin fada" amma har taje gonar mai gari bata samu abokin fada ba, amma mai tana zuwa ta tarar mai gari ya kawo wanda zaina masa gadin gonar sa, "kee tsaya daga nan, ina zakije?gonar da kake gadi zan
DOWNLOAD
DOWNLOAD
Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment