Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

shiga in tsunko mangwaro, ko kana da dumuwa da hakan? "banida damuwa, amma fa karki manta abinda kikace, gonar da nake gadi, kinga kuwa baki isa ki shiga ba" dariya ta fara tana nunasa, "yanzo kai har kana tunanin ka isa ka hana Zainabu Abu abinda tayi niya ne? ai ko sama da kasa zata hade banga wanda ya isa ya hanani shiga gonar nan ba" tahowa tayi zata shiga ya kankane wajan, dutsan da ta gani a kasa, ta dauka ta kwala masa a ido, nan take ya fara ihu yana birgima saboda radadin azabar da yakeji, sallake sa tayi ta shige gonar, bata wani sha wahala ba ta debo mangwaron ta fito daga gonar, har lokacin mai gadi na birgima a kasa na azaba, ko takansa bata bi ba ta tsallake sa tayi wucewar ta.




Kamar yadda yace tayi, haka tayi, safiya nayi ta shirya saf cikin uniform dinta, darect dakinsa ta nufa, shima ya shirya yana kokarin fitowa ta shigo, "Yaya Good Morning","Morning how are u? am fine Yaya","muje ko? Fitowa sukayi ta bude mota ta shiga, shima yana kokarin shiga yaji ance, "gidan ubanwa zaka kaita?"










Shere fisabilillah.
✨✨ ZAINABU ABU ✨✨

Na

ZAINAB A BARDE



ALƘALAMI YAFI TAKOBI WRITERS ASSOCIATION
(A.Y.T.W.A)



Free page 13 nd 14



****



"Abee I'm taking her to school, dan Allah Abee yarinyar nan batada burin da ya wuce tayi karatu, ina rokon ka dan Allah Abee don't destroy her future, Abee yau dai ina rokon ka wannan alfarmar a matsayinka na mahaifina" kallonsa kawai yakeyi tunda ya fara magana har ya dasa aya, shi kansa yasan yana matukar son yaran nasa kuma bayason bacin ransu, amma baisan maiya shiga kansa ba kwana biyu yakejin tsanar su, kuma yake musu wadan nan abubuwan,



"Tunda harka roke ni, kuje ka kaita amma fa ka sani duk abinda ya faru da ita it is non of my business, don't even mention my name, kuyi kuka da kanku and that your mother, kuma in ka gadama yauma karka zo company kaga yadda zan bata maka" yana gama fadin haka ya shiga motar sa driver yaja suka tafi, ajiyar zuciya mai karfi Muhammad Kareem ya sauke, ko babu komi shalelan kanwar sa zata cigaba da zuwa makaranta, "get in, it's getting late" shiga tayi suka bar gidan zuciyar ta fal farin ciki, tama rasa wace addu'a zatayiwa yayan nata, cikin matukar bakin ciki Mami ta saki labulan window din ta koma ciki, zama tayi akan kujera tana huci, "banso ka barsu suka tafi ba, tayaya bayan kace bazata sake zuwa makaranta ba amma kuma ka barsu suka tafi, dama nasan muddin wanchan dan banzan na raye bazai taba bari ta daina zuwa makaranta ba, in ko ta daina zuwa to he is not breathing anymore, amma ai inkunsan wata bakusan wata ba, zanyi maganin ku ne"



"Asfah" ya kira sunanta cikin natsuwa, "na'am Yaya" saida ya nunfasa sannan ya cigaba da magana, "nasan cewa ke yarinya ce mai nasuwa, kinji dai abinda Abee ya fada" daga masa kai tayi, "to all I need from you is to take a very good care of your relationship at school, ki tsare mutuncin ki a matsayin ki na diya mace kinji, kuma inaso ki zama yarinya mai natsuwa, mai ladabi, sannan kuma mai girmama na gaba da ita, kinji yar kanwata","insha Allah yaya I will not disappoint you insha Allah I'll did all as you said","yauwa yarinyar kirki, Allah yayi miki Albarka, Allah ya kare min ke a duk inda kike","Ameen Yayana" da wannan hirar suka karaso school din, har zata fita ya dakatar da ita, chocolate ya dauko a back seat manya guda biyu ya mika mata, cikin murna da farin ciki ta amsa, "nagode sosai Yaya" mayar mata da murmushi yayi, "study hard kinji"insha Allahu Yaya" ta fada tana daga masa hannu, saida yaga ta shiga sannan ya sauke ajiyar zuciya yana fadin "Alhamdulillah" sanan yaja motarsa yabar wajan, bai zarce ko ina ba sai company.




Lokacin da ta shiga aji har malamin english ya shiga, "Good Morning Sir","Morning my dear, you are late","am sorry Sir","ok have a seat, and bring out your book" zama tayi tana ciro littafin ta, tunda ta shigo take hararar ta cike da bakin ciki, kamar idon ta zai fado kasa, "amma kikace mana Abee dinku yace bazata sake zuwa ba","Safiya ta tambayi Asmah murya chan kasa kasa, "I don't know what happened, amma jiya haka Abee yace she will never come again" tabe baki Safiya tayi daga nan babu wanda ya sake mgn har malamin ya gama darasin sa ya fita, tana ganin malamin ya fita, ta tashi taje wajan Asfah, dama ta matsu ya fita, ji take kamar akan kaya take, "how comes da abee ya barki kikaxo?, bayan yace baza ki sake zuwa ba?" murmushi mai ciwo Asfah tayi, amma sai tace "nima ban sani ba, kawai dai yace min in shirya, dana shirya shine muka taho tare, ya ajeni shi kuma ya wuce office","wai kina nufin Abee nai ya kawo ki","yes of course, let me even show you what he gave me, chocolate din ta nuna mata, jitai ranta na suya, "and where is mine?,"nima dai bansani ba, amma zaki iya bari in mun koma gida ki tmby sa" a fusace ta tashi daga wajan ta koma wajan zaman ta, ranta a matukar bace.




Assalamu Alaikum! Assalamu Alaikum! ya kwada sallama har sau biyu, niko jikata sallama akeyi a waje jeki gani wana gantalallan neke kwada mana sallama da ranar Allah haka, kamar munci masa bashi","yoo Anna ba'azo da rana ba, da daddare ko da asuba kikeso azo","kinga tashi kije kigano min" jin an kara kwada sallama yasa Zainabu bata sake magana ba ta tashi ta fito, "Malam lafiya zaka rinka kwada mana sallama haka, bashi ko tara" ta fada tana turo danƙwali gaban goshi, " ba wajan ki nazo ba, wajan anna nazo dan haka yimin magana da ita","amma lallai Malam kai dan rainin wayo ne, ai in aka ganni a waje kamar anga Anna ne, to wai tsaya ma, maiyasa kake naimanta?" jin shiru shiru Zainabu bata dawo ba yasa Anna fitowa, "jikata mai yake faruwa ne","gashi nan wai wajan ki yazo dan rainin hankali kawai" shidai baice komi ba, "lafiya kake naima na","dama mai gari nai yake naiman ku, yace inzo in tafi daku","iyye sai kace wasu ƴaƴan ka"," rabu dashi Anna, kaje kace masa munci dubu sai ceto, baza muzo ba","aa jikata mai gari fa akace","yoo mai garin fa","aa hanyar lafiya a bita da shaikara, kaga bawan Allah kaje kace masa ga munan zuwa","aa cewa yayi in taho kafata kafarku","amma fa mutumin nan ka cika dan rainin hankali, bar mana kofar gida akace ko bakaji bane" ta yunƙuro kamar zata dakesa, babu shiri ya karawa wandonsa iska, "nifa Anna da zakiji magana ta, to da babu inda zamuje","aa jikata muje dai muji wacce karar tamu aka kai masa, dan in kaji kiran mai gari, to billahillazi karan mu aka kai masa" da haka dai ta lallabata suka tafi.





Suna zuwa Zainabu tasha jinin jikin ta saboda ganin mai gadin da ta fasa wa ƙai, amma da yake yar rainin hankali ce saita maze, zama sukayi tare da gaisar da mai gari sukayi ya amsa, bayan gaishe gaishe mai gari ya fara magana kamar haka, "Zainabu kin gane wannan mutumin" ya nuna mai gadi, "aa ni sam ban sansa ba, hasalima ban taba ganin sa ba, ni ko mai kama dashi ban taba gani ba" ta fada tana babbata rai, "amma shi yace kece kika fasa masa kai da dutse, ko ba haka akayi ba" ya fada yana kallon mai gadi, "hakane rankaidade, wllhi itace","Zainabu nifa fitinar nan taki ta fara isata, Anna kiyi mata fada in ba haka ba, wllhi na kusa korarku a garin nan, haba gaba daya jikar ki ta fitini kowa a garin nan, duk abinda takeyi ina samun labari","ayi hakuri rankaidade, hakan bazata sake faruwa ba insha Allah","zaku iya tafiya"




Sun fara tafiya Zainabu sai faman cika take tana batsewa, "jikata lfy kuwa naga kina babbata rai","Anna ai kece kika bata min rai, mai yasa zaki basa hakuri, aida kin bari ya kore mun mana saimai inya kore mu, dama ni wllhi na gaji da wannan dan iskan ƙauyen","kiyi hakuri jikata dama nima na gaji da kawo min karar ki da akeyi, duk sun takura maki wllhi, so nakeyi na tara mana kudade mu koma birni da zama","da Allah Anna da gaske" ta fada tana rungume Anna, "da gaske jikata, ƙauyen nan na kula an fara takura maki, ni kuma banason abinda zai takura maki, in sha Allah mun kusa barin garin nan, ina nan ina mana tarin kudi" da wannan hirar farin cikin suka dawo gida.













Shere fisabilillah.
✨✨ ZAINABU ABU ✨✨

Na

ZAINAB A BARDE



ALƘALAMI YAFI TAKOBI WRITERS ASSOCIATION
(A.Y.T.W.A)



Page 15 nd 16


****

Da wannan hirar suka karaso gida, ko zama basuyi ba Zainabu ta kwaso kayan wankin su, ta fara wanki, itako Anna girki ta dora masu, tana masifar an takura wa jikar ta a cikin garin nan, "daga yau zan fara mana tarun kudi wllhi, danni ba gantalalla bace da zan zauna inda ba'ason jikata","ni dama Anna na jima dason mu bar wannan banzan garin","karki ji komi jikata, aini duk abinda kike so shi nakeso, karki wani damu, kisa aranki gari kamar mun barshi ne","yauwa Annata shiyasa a koda yaushe nake kara sonki.



Zaune yake a kan kujerar dake cikin office din shugaban gidan marayun, "yallabai, bamu da bakin yi maka godiya da wannan dawainiya da akeyi da marayun nan, saide muce Allah ya biya maka bukatun ka na Alkairi" kayataccan murmushi yayi, wanda hakan ya kara fito da tsantsar kyawun sa, saboda ba kasafai ya ciki yin murmushin ba, gyara zama yayi akan kujerar ya dora kafa daya kan daya, magana ya fara cikin daddadar muryar sa mai dadin sauraro, cikin natsuwa yace, "na dade da fada maka, ka daina kirana da Yallabai, call me with my name, MUHAMMAD KABIR, dani dakai duk daya muke a wajan Allah, babu wanda yafi wani, sai wanda yafi bauta masa","ayimin afuwa, zanji nauyin kiran sunan ka kai tsaye ne shiyasa","babu komi ka fada kanka tsaye ba wani abu bane","To Muhammad Kabir muna godiya sosai, Allah ya saka da alkairi","babu komi nidai abinda nakeso daku shine, ku cigaba da rike amanar da Allah ya baku","insha Allahu"



Mika masa hannu yayi, yana mikewa tsaye, har bakin motocin sa ya rakosa, da sauri masu tsaron lafiyar sa suka bude masa mota ya shiga ya zauna sannan suma suka shiga tasu cikin azama suka hau titi, duk inda suka wuce motocin ake kallo, saboda tsabar haduwar su, motoci ne jere guda goma ko wacce mota tinted ce, baka iya ganin na ciki, tafiya suke cikin natsuwa, saboda baya son ya shiga hakkin mutane, kowa yaga lambar dake cikin motocin wato *MK* saiya masa fatan Alkairi saboda taimakon sa ga Alumma, ko ina suka wuce hannu kawai ake daga musa, a haka har suka karaso gida, gida ne daya amsa sunan sa gida, bawai muna gida ba, kaida ka kalli gidan kasan mamallakin sa ya tara, motocin na tsayawa da sauri bodyguards dinsa suka fito suka bude masa kofa, fitowa yayi, ya nufi kofar shiga gidan, da sauri daya daga cikin yaran nasa ya ruga ya bude masa kofar, har ya shiga ya dawo, "kuje ku samu wannan mutumin daya kwace wa wadan nan marayun gidan su, tell him that I want to see him, and if he refused, ku dauko min shi ta karfin tsiya","an gama Sir" daga haka ya shige ciki.




Yana zuwa Company ya tarar da uban aiki jiya kawai da baizo ba, PA din Abee ne ya shigo, "Sir Muhammad Kareem yazo office, shigowar sa kenn ma, nace bari na sanar maka" nannauyar ajiyar zuciya Abee ya sauke, yaji dadin shigowar Muhammad Kareem office, duk da cewar yasan bazai taba fada masa magana ba yakiyi masa biyayya, yasan tunda yace masa lallai lallai yazo Company yasan zaizo amma mutum yana iya chanzawa a koda yaushe, "nasan cewa Muhammad Kareem shine bangon wannan Company, muddin kuwa ya daina zuwa, to abubuwa zasu tabar bare, Company zai lalace","gaskiya ne Sir, Muhammad Kareem yana matukar kokarin ya jajirce akan yaga wannan Company yaci gaba, kuma ya samu daukaka","na sani PA, Allah yayi masa Albarka","Ameen ya Allah","ka shirya yanzo zamu fita","owk sir" ya fada yana fitowa daga office din.



Shima fitowa yayi, da sauri PA ya bude masa bayan mota ya shiga, shi kuma ya shiga wajan mai zaman banza, driver yaja suka bar Company, saida suka hau kan titi sannan ya tmby Abee ina zasuje, "ma'aikatar Alhaji Bukar zanje" ta cikin mudubi PA ya kalli Abee, maiyasa zaije chan, bayan bakar gabar dake tsakaninsu, ko sun shirya ne banida labari, yayi zanchan a cikin zuciyar sa amma babu mai basa amsa, wayarsa ya dauko ya turawa wata lamba test massage, akan gasu nan zuwa ma'aikatar su, ni kaina bansan number wane ko wacece ba, babu jimawa aka dawo masa da reply, ashai yau muna da manyan baƙi, murmushi PA yayi ganin abinda aka rubuta, kashe wayar yayi ya maida ta aljihu,




Suna zuwa da sauri PA ya fito ya budewa Abee kofa, tunda suka shigo ma'aikatar ake kallonsu bare ma wandan da suka san baƙar gabar dake tsakanin Alhaji Bukar da kuma Abee, bai jira an masa jagora ba, ya fara tafiya, ko tsayawa a basa izinin shiga baiyi ba, ya bude kofar office din, dagowa Alhaji Bukar yayi, murmushi dauke akan fuskarsa, shi duk a tunaninsa Abee yazo ne dan suyi sulhu, su cigaba da tsohuwar abotar su, shiko indai da hakan yazo, to ya shirya tsaf da irin wulakanci, da kuma korar karan dazaiyi masa, zama Abee yayi dan bashi bukatar a bashi izinin zama kafin ya zauna,



"Nazo ne in fada maka, kajawa yarinyar wajanka kunne akan ta rabur min da ɗana, if not, zan maka ku a kotu, no need of having any relationship da Wanda bashida tsoran Allah, kuma macuci,maha'inci, kuma Azzalumi","kaga dakata Malam, bangane abinda kake nufi ba, what the hell my daughter will do da wannan gunkin dan naka, she is not his mate anymore God forbid, kaidai zaka jawa danka kunne bani ba, kama je kaja masa kunne tun dare baiyi muku, okayyy is that what you said? "Yeah ni Alhaji Bukar haka nace" Abee bai sake cewa komi ba ya fito daga office din ransa na suya, sai baza babbar riga yakeyi, mota ya shiga yana fadin "let's go home"



Yana fitowa shima Alhaji Bukar ya shiga mota, ya nufi gida, yau sai yaji dalilin da yasa Shahida zatayi soyayya da dan makiyinsa, kuma uwarta ta sani amma basu sanar dashi ba, suna zuwa gida ko parking bai bari driver sa ya gama ba ya fito, yana kwala kiran sunan, Shahida! Shahida!! Shahida!!! Umma ce ta fito tana fadin Abban Shahida lfy kuwa, kake kwala mata irin wannan kiran","ki kyale ni tukunna I'll get back to you.














Shere fisabilillah.
✨✨ ZAINABU ABU ✨✨

Na

ZAINAB A BARDE



ALƘALAMI YAFI TAKOBI WRITER'S ASSOCIATION
(A.Y.T.W.A)


*LITTAFIN ZAINABU ABU NA KUDI NE, AKAN FARASHI MAI SAUƘI #200 KACAL, ZAKU TURA KUDIN TA WANNAN ACCT DIN, 0599919281 ZAINAB ADAMU, GT BANK, SAIKU TURO SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER, 07048614405, FREE PAGE SUN KUSA KAREWA, SAIKU HANZAR TA KAR AYI BABU KU*




Page 17 nd 18



****


A firgice Shahida ta fito daga dakin ta, har tana naiman yin tuntube da step, zuciyar ta sai lugude takeyi saboda ganin yadda fuskar Abban ta yake, ransa a matukar bace, "Abbana gani","ashai bakida mutunci ban sani ba, duk gatan da nake nuna maki, ashai da abinda zaki saka min kenn, yin soyayya da dan makiyi na","ba Shahida kadai ba, hatta Umma saida gabanta yayi mummunan faduwa, ko ina ya jiyo wannan labarin ohoo, "to hankalin ki ya kwanta, uban yaron yazo har office dina yaci min mutunci a bainar jama'a, to ki sani nan da wata biyu zan aurar dake, dan bazaki jamin abin kunya ba","Amma Abban Shahida bai kamata ka yanke wannan hukuncin ba, wata biyu sai kace auran yartsana","masha Allah dama kinsan da soyayyar da sukeyi amma baki fada min ba, to kin kyauta, yayi miki kyau, ke kuma tashi ki ban waje kafin na hada ki da bangon nan" da gudu ta tashi tana kuka mai ban tausayi, da kallon tausayi Umma ta bita, "dan Allah Abban Shahida ka sassauta mata wannan hukuncin, karka yanke hukunci cikin fushi, kar yarinyar nan ta shiga cikin mawuyacin hali","kee bari kiji in fada miki, ko mutuwa zatayi bazata auri wannan banzan yaron ba, kuma ku shirya nan da wata biyu zan aurar da ita","amma abb.. daga mata hannu yayi, na riga na gama magana" shknn Allah yasa hakan yafi zama alkairi a gare mu" "alkairin ne ma" ya fada yana hayewa sama, bayansa tabi, dakin Shahida ta shiga, a kwance ta tarar da ita, tayi rufda ciki, tana kuka mai ban tausayi, with a very low tone ta kira sunanta, dagowa tayi tana ganin Umma ta fada jikin ta, tana kara rushewa da kuka, bayanta Umma ta rika shafawa a hankali alamar rarrashi, "Umma dan Allah karki bari Abba ya rabani dashi, wllhi Umma I can't live without him, Allah ya jarrabe ni da soyayyar sa, badan haka ba sai in rabu dashi kamar yadda Abba yakeso, amma ban iyawa Umma I can't, wllhi bazan iya ba" ta karasa maganar kuka nacin karfin ta, tari ta fara da karfi da sauri Umma ta riketa tana kiran sunanta, amma ina tarin yaci karfin ta, da sauri Umma ta dauko ruwa tana kokarin bata, amma mai zata gani, gaba daya jini ya batawa Shahida gaban riga, har lokacin kuma bata daina tarin ba, ga aman jini da takeyi, a rikice Umma ta fito daga dakin tana kwala kiran Abban Shahida! Abban Shahida!! harta shiga dakinsa, a firgice ya mike ganin tana hawaye kuma tana nuna masa kofar fita, she guarded all her courage dakyar ta iya janyo sunan "Shahida","maiya samu Shahidan?" ganin bazata bashi amsa ba sai kuka take yasa shi rabawa ta gefenta ya fita, biyosa tayi a baya, yana shiga dakin ya tarar da ita a kwance bata ko motsi ga jini duk ya bata mata baki da riga, cikin sauri ya karasa kan gadon yana kiran sunanta amma bata ko motsi, "shknn ka kashe min ƴa saboda wata banzar gabar ku, wllhi indai ta mutu bazan yarda ba sai nayi karar ka" shi bama yajin abinda Umma take cewa tsabar rudewar da yayi, cikin tashin hankali ya dauki Shahida, da sauri da sauri yake sallaka matakalar benen, wani gurin ma bibbiyu yake tsallakewa, da sauri itama Umma ta biyo bayan sa, hannun ta rike da mayafi tana kuka, Driver sa ya rika kwalawa kira, a gigice shima ya fito jin irin kiran da mai gidan nasa yakeyi masa, kuma dai yasan baice masa zasu fita ba, amma ganin karamar Hajiya a hanunsa, ga jikinta duk jini yasa shi kara gigicewa, "take us to hospital inji Abba" da sauri driver ya shiga mota, shima shiga yayi ya kwantar da Shahida akan kujera, ya dora kanta akan cinyar sa, da sauri yaja motar suka fita a gidan, gudu kawai yake shararawa, Abban shahida kuwa gani yakeyi kamar motar bata gudu,




Umma na karaso wa taga har sun fita, motar ta ta shiga ta rufa musu baya, da yake tana iya hango su a gabanta, ikon Allah ne kawai ya kaita asibitin lfy, suna zuwa da sauri aka kawo kujerar tura marar lafiya aka dora ta akai, dakin taimakon gaggawa aka shiga da ita, Abba na kokarin shiga aka dakatar dashi, kusan awa uku suka dauka akanta kafin su samu nunfashin ta ya dawo dai dai, bugun zuciyar tama ya dawo dai dai, fitowa da ita akayi, dakin hutu aka kaita, Doctor ne yacewa Alhaji Bukar ya samesa a office, Umma kuwa dakin da aka kai Shahida ta tafi, a kan gadon ta zauna tana kallon ta, har lokacin idonta bai daina zubar da hawaye ba, bin Doctor din yayi a baya har zuwa office din, wajan zama Doctor ya nuna masa zama yayi, "Doctor ka fadamin maike damunta","mene alakar ka da marar lafiyar?","ni mahaifinta ne","to a gaskiya ƴar ka ta kamu da heart attack, da dukkan alamu tana cikin damuwa mai tsanani, kuma idan har ana barinta cikin damuwa to zuciyar ta zata iya bugawa" ajiyar zuciya Alhaji Bukar ya sauke, yana mamakin har son da takewa tsinannan yaron nan yakai haka, ai kuwa ko mutuwa zakiyi bazaki aure sa ba, gara inga mutuwar ki akan inga auran ki da wanchan banzan yaron, "gashi a siya mata wadannan magungunan" maganar Doctor ta dawo dashi daga duniyar tunanin daya lula, karba yayi yana masa godiya, yana fitowa ya wuce permercy ya siyo magungunan sannan ya shiga dakin, ko kallonsa Umma batayi ba ya aje ledar maganin, tare da zama akan kujerar da take kallon gadon, "yanzu kai ka gwam maci kaga yarka a wannan halin akan ka bata wanda takeso?","wllhi saide ta mutu amma bazata auri wannan yaron ba, kinji ma na fada maki, gara ma ki fada mata she should better remove him out of her mind, tun dare baiyi mata ba, kuma nan da wata biyu babu fashi zan aurar da ita" yana gama fadin haka ya tashi ya fita daga dakin, da kallo ta bisa tana mamakin wannan wana irin uba ne, irin wannan taurin zuciya haka.




Karfe biyu ɗai ɗai driver yaje dauko su asfah, a cikin mota babu wanda yayiwa dan'uwansa magana, ita Asfah ma littafinta ta dauko ta fara karantawa, itako Asmah sai cika take tana batsewa, sai faman jan tsaki takeyi, a haka dai suka ƙaraso gida, ko wacce daga cikin su tayi bangaran mahaifiyar ta, babu ko sallama haka ta shiga falon, kuma maimakon Mami tayi mata fada sai cewa tayi, "yau kuma waya tabo min Asmah ta, shalele ta?" zunburo baki tayi, "Mami kisan wachan mayyar yarinyar taje makaranta, kuma fa harda chocolate ya bata ni kuma bai ban ba"," to saime in bai baki ba, are you going to die ne in baki sha chocolate ba?","girgiza kai tayi, "ki barni dasu zasu gane shayi ruwa ne, kemah kinsan bazan gyalesu haka ba","yauwa Mami na sanki da mugunta da makirci, indai a wannan fannin ne banida matsala" kuji fa wai ƴace take gayawa mahaifiyar ta haka, murmushi Mami tayi, "kije kiyi wanka kizo kici abinci yanzu zakiga lokacin islamiya yayi","ni wllhi Mami banason islamiyar nan, dan babu yadda zanyi ne, nasan Abee bazai taba bari na daina zuwa ba","tashi kije karki makara" tashi tayi ta fada dakin ta, da wani irin kallo mai cike da ma'anoni Mami ta bita dashi, tana sakin wani munafukin murmushi.



Da sallama ta shiga falon, Ammi ta tarar a zaune tana kallon TV gaishe ta tayi, tana zama a kusa da ita, "nikam ya akayi kikaje school, sai shiga dakin ki nayi na tarar bakyanan, dana tmby mai gadi, sai cewa yayi kin tafi school","wllhi Ammi Yaya ne ya kaini, kuma ya bawa Abee hakuri yanzo zan cigaba da zuwa school","masha Allah, nide nasiha ta a koda yaushe a gare ku shine, ku dinga yin hakuri a duk halin da kuka tsinci kanku a ciki","insha Allahu Ammi, bari naje nayi wanka, yanzu zakiga lokacin islamiya yayi","to maza kije ki shirya, Allah yayi muku Albarka","ameen Ammina, Allah ya kara miki lfy da nisan kwana","Ameen Ammi ta fada murmushi dauke a fuskar ta, tanason yaranta so mai tsanani, gasu da tarbiya da hankali.


****

kawo masu mutumin akayi kamar yadda ya bukata, yaso yayi musu gardama, amma
DOWNLOAD
DOWNLOAD
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment