Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

SAHLAH, WA'ANTA TAJ'ALUL HAZNA IZA SHI'ITA SAHLAH.*



*KARKU MANTA*

*🚶🏻‍♀INDO K'AFAR YAWO🚶🏻‍♀ZAI DINGA ZUWA MAKUNE ARANEKUN ASABAR DA LAHADI INSHA ALLAH.*


*SAK'ON INDO GAREKU*
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

*DOMIN RAGE TUMBI CIKIN SATI BIYU:-*

*1-BAKING POWDER*
*2-KHAL TUFFA*
*3-RUWAN ZAFI*

*YADDA ZAKI HA'DA*

*KIFARA ZUBA RUWAN KHAL TUFFA MURFI 'DAYA A CUP SAIKI KAWO BAKING POWDER TEA SPOON KISHARE SAMAN DA 'DAN YATSANKI KODA BAKIN GOGONIN SAIKI RABASHI 1/⁴ SAIKI ZUBA 'DAYA CIKIN WAN NAN KHAL TUFFA EN ZAKIGA YAYI KUMFA TSAMIN KHAAL TUFFA EN YAFITA KENAN TA YADDA HAR MAI OLCER ZATA IYA SHA, SAIKI ZUBA RUWAN 'DUMIN KI CIKA CUP EN 'DUMIN YAZAMA DAI² YADDA ZAKI IYASHA KAMAR TEA KISHA DA SAFE KAFIN KICI KOMAI SAI KISHA DA RANA BAYAN KINGAMA CIN ABINCI SAI KUMA KISHA DA DADDARE KAFIN KI KWANTA.*
*INSHA ALLAHU ZAKIGA YADDA TUMBINKI ZAI KOMA.*







*_page4⃣._*






Gaba d'aya hankalin GOGGO baya jikinta kawai dai tanayin aikinne kamar mara lafiya,
hakan nan ta d'ora murhu biyu na tuwo daban na miya dantayi saurin gamawa kafin BAFFA yadawo, har aka fara kiran sallah maghreb INDO bata shigo gida ba anan hankalin GOGGO ga k'ara tashi, tunanin ta d'aya kar BAFFA yace tayi watsi da AMANAR da yabata, Tana cikin wan nan tunani ne yaro yayi sallama bayan GOGGO ta amsane yaron yafara sanarwa da GOGGO sak'on innarsa.....

"Wai inji INNA tace idan BAFFAn INDO yadawo daga kasuwar wai yabata sak'on"
Cikin rashin fahimta GOGGO ke kallon yaron "itakam wanne sak'o ne?" GOGGO ta tambayi kanta cikin zuciyarta jin shiru ba ansa ne yasa ta tuna cewar azuciyarta take maganar, shikuwa yaron jira yake tabashi yatafi... "kace BAFFAN bai dawo ba inyadawo zangaya masa, kace ina gaida INNA mai koko kaji?"
Yaron ya amsa da "to" san nan yayi ficearsa, nan GOGGO ta tashi tayo alwala ta shiga d'aki.......


Da gudunta ta nufi inda mai machine d'in yasauke saurayin duk inda cikakken d'angayu yake to wan nan saurayin yakai awancen lokacin, rataye yake da wata jaka wadda daga gani kasan kayan sawarsane aciki saikuma wata Bagco a hannunsa, tana k'arasawa wajen yana gama sallamar mai machine d'in, kallonsa kawai INDO takeyi da Alamun wan nan saurayin yayi matuk'ar burge ta....
"Ai daga gani daga wani garin yake gashinan ya banbanta da jama'ar garin nan lallai dole inbishi gidansu kodan yabani labarin inda yaje kuma yagaya min nawa ake zuwa ALLAH dai yasa mata ma suna zuwa karyace min mazane kawai suke zuwa"....
yayin da INDO tayi nisa cikin tunanin ta batasan lokacin da wan nan saurayin ya d'auki kayansa yayi gaba ba sai farkawa tayi kawai taga baya wajen, zazzare ido tashigayi ganin babu kowa sai d'ai² kun mutane dake k'ok'arin shiga massalaci domin yin sallah, wani irin tsaki INDO taja kafinta wuce ta nufi gidansu.............



Da sallama ta tura kai cikin gidan alokacin GOGGO ta idar da sallah tana ta addu'a, kamar daga sama tajiyo muryar INDO a tsakar gida godiya tasakeyi ga Allah saboda jiyo sallamar INDO datayi, cikin sand'a kamar wadda za'a kama haka INDO ta shiga d'akin GOGGO takalminta ne rik'e a hannu tana k'ok'arin bud'e fantekar GOGGO zata ajiye aciki, dafarko GOGGO batayi niyyar yi mata maganaba saida taga INDO nashirin ruguzo mata da jeren d'akin akanta san nan tacewa wa INDO takawo takalmin ta ajiye mata, ba musu kuwa INDO ta mik'awa GOGGO takalmi mamakine yakama GOGGO sanda ta kalli sabon takalmin da INDO ta mik'o mata....

"INDO yaushe BAFFAn ki ya sayo maki takalmi?"

Nan fa INDO ta yashewa GOGGO baki da farin cikinta take magana....

"Wllh GOGGO d'azune bayan kintafi duubo malam AUDU sai inna mai koko ta aiko da kud'i wai BAFFA ya sayo mata gero akasuwa saboda ta rainamin BAFFA shi zata aika kasuwa? nikuwa nayi maganinta na kar'ba kud'in na tafi kasuwar nasayo takalma daman BAFFA yace zai sayo min to kinsan halin mantuwar BAFFA shine kawai na kar'ba kud'in naje BABBAR KASUWA nasayo harguda hud'u".....
Jin ta ambaci BABBAR KASUWA ne yasa GOGGO saurin sakin takalmin ak'asa sai alokacin ta tuna da yaron inna mai koko da yazo d'azu "INDO BABBAR KASUWA fa kikace, kedawa kukaje?"
GOGGO take tambayar INDO
"Lallai ma GOGGO nid'in sai da wani zan iya zuwa BABBAR KASUWAR?"


"HAZBUNALLAHU WANI'IMAL WAKEEL kai jama'a anya kuwa INDO k'alau kike? To nawane kud'in inna mai kokon?"

"Oho mata ni iya lissafinnayi? Naji dai yaron yace kwano uku za'a sayo mata geron, nikuma danaje wajen mai takalmin saina bashi kud'in gaba d'aya sai yabani chanji"....
Nan tsahiga laluben inda ta d'aure chanjin amma batasamu ba....
"To GOGGO kingama nazubar da chanjin da mai takalmin yabani, daman ke zankawo wa kozaki sayi wani abun"
INDO tafad'a tana turo baki kamar zatayi kuka.

"Haba INDO kin kashe su dai kawai"

"a'a wllh GOGGO ban kashe su ba kinsan bana kashe kud'i"

Dan dole GOGGO tayi shiruu saboda tasan tabbas INDO bata kashe kud'i ko kad'an barta dai da shegen yawo ko yunwa bata ji inhar tana yawonta, k'arkashin gado GOGGO tazuba takalman san nan tafito waje ruwan wanka ta had'awa INDO mai d'umi takai mata bayi, san nan tadawo d'aki "INDO tashi ga ruwan wanka chaan na had'a maki daganan sai kiyo alwala kiyi sallah"
Ba musu INDO tacire kayanta ta tafi wanka....



Kamar yadda BAFFA yayiwa malam AUDU alk'awarin zai dawo yadubashi haka kuwa yana dawowa daga kasuwa ko gida baijeba yabawa almajiri kayansa yakai masa gida shikuwa BAFFA yanufi gidan Malam AUDU, BAFFA ya jima awajen malam AUDU har bayan sallah isha san nan BAFFA yanufi gidansa........



Alokacin da BAFFA yashigo gida INDO kam tajima dayin bacci, har k'ofar d'akin GOGGO yazo yana kiran AISHAn sa sai GOGGO ce tace masa "tayi bacci" sosai BAFFA yayi mamaki Anya kuwal lafiyar INDO k'alao zatayi bacci yanzu? Kai saidai in tayi yawo tagaji gaskiya, duk azuciyar sa yake maganar bayan ya koma d'akinsa...

Sallamar GOGGO ne ya katse masa tunanin sa, saida ya amsa mata san nan ta ajiye tray d'in abincin da ta kawo masa.....
"GOGGOn AISHA yau kam mai kikayiwa AISHAn ki tayi bacci haka dawuri?"
Fuskarsa d'auke da fara's ake tambayar GOGGO....
Itakam GOGGO tarasa amsar dazata bashi, ko kad'an GOGGO batason abinda zaisaKa BAFFA cikin damuwa Amma bayadda ta'iya yazama dole tasanar dashi kodan ya gaggauta biyan inna mai koko kud'inta saboda bayyada zatayi ta biya mai koko kud'in kilama har zancen yadawo kunnen BAFFAn batare da ta biya mai kokonba, dan haka kawai ta yanke shawarar gayawa BAFFA komai....

"Ina magana kinyi shiruuu kodai AISHAn bata da lafiya ne"

"Hmmmmm a'a lafiyarta k''alau gajiya ce kawai take damunta dan yau har BABBAR KASUWA taje"...

Da sauri BAFFA ya tashi zaune yana mai² ta maganar da GOGGO tafad'a.


"BABBAR KASUWA fa kikace maitaje yi?"

Anan GOGGO ta kwashe yadda komai yafaru ta gayawa BAFFA...
Hawayen data gani yana sauka daga kan fuskarsa shiyafi komai tayar mata da hankali, matsowa tayi kusa dashi tana share masa....

"Dan ALLAH MODIBO kadenayi nata kuka, kukan ka agareta bashine zai shiryar da itaba addu'a ce mafita kawai"


"Ko kad'an ba AISHA nakewa kuka ba ina tunanin wanne laifi nayiwa Allah ne da yabani AISHA mai k'afar yawo"

"subhanallahi MODIBO bantabajin wan nan mummunan maganar daga bakinka ba kaifa musulmine kuma mai tawakkali dan Allah karka sake fad'ar haka".














*_Ur's Hubbeey._*
[04/08, 21:53] Hubbey Frd Ameena Kn: 🚶‍♀ *INDO K'AFAR YAWO*🚶‍♀



*TRUE LIFE STORY*



28/7/2018.



*_STORY BY_*

*_AISHA MODIBO_*
*_(Indo k'afar yawo)._*


*_WRITEEN BY_*

*_HABEEBA IDREES(Hubbeey)._*
_________________________
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
_tσ gєt αccєѕѕ σf σur nσvєl'ѕ víα thíѕ línk tσ jσín σur fαcєвσσk grσup._
_____________________




*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHEEM.*






*ALLAHUMMA LAASAHLA ILLAH MAJA'AL TAHU SAHLAH, WA'ANTA TAJ'ALUL HAZNA IZA SHI'ITA SAHLAH.*



*SAK'ON INDO ZUWA GAREKU
FAN'S*

*DOMIN MAGANCE NANKARWA (STRECTH MARKS).*

Da farko dai shi Nankarwa wasu tabbai ne layilayi da suke fitowa mace a jiki musamman wacce ke dauke da ciki zuwa haihuwa Wanda idan anyi maganin sa da wuri wato daga fitowar sa zasu iya bacewa gaba daya amma barin shi ya dade kan hana sa bacewa gaba daye sai dai zai dushe ya zama dan kadan kadan ake iya gani
suna fitowa ne a wurare kamar haka :-

Cikin mace daga kasa (mara)
Cinya 
Saman mama 
Mazauni 
Saman hannu ta wuraren hammata 
Da sauran su.
*ME KE KAWO NANKARWA ?*
Akwai abubuwa da dama da suke sa nankarwa kamar:-
1-daukan ciki zuwa haihuwa (wannan shine babban abinda ke kawo nankarwa)
2-ramewa tashi daya (ga mutum mai qiba)
3-yin qiba tashi guda (ga mutum mai rama)
4- gado daga mahaifiya 
5-jinya na tsawon lokaci 
6- damuwa mai yawa da makamantar su

*MATAKAN NANKARWA*

Yana da matakai guda uku gasunan kamar haka:-
1) farko fitowar sa zaki gansu sirara yana da pink kala sannan yakan yi kaikayi wannan matakin bashi da wahalar magani
2) zai zama ja ko ruwan bula sannan girman su zai karu yanzun kam babu kaikayi sai lokaci zuwa lokaci zai iya bacewa ki ya ragu ya danganta da yanayin jikin mutum
3) zai zama fari ko ruwan silva wannan kam yana da matukar wahalan magani sai an jure shima din sai dai ya ragu ba wai ya bace baki daya ba.











*PAGE 5.*







Tun sanda Malam *AUDU* yasamu karyewa *INDO* ko sau d'aya bataje ta/dubashi ba,kullum idan Malam *AUDU* ya tuna hakan yana 'bacin rai saidai kuma yanayi mata uzirin k'uruciya da shirme dasuke tare da ita........

Kamar kullum yanda tasaba ficewar ta yawonta babu ruwan ta da cewar dare ne ko safiya itakam duk sanda yawonta yatashi kawai kama hanyarta take yi sai dai idan *GOGGO* ce ta kulle mata k'ofa shine za'a samu lafiya, dayawa mutanen garin suna danganta cewar *INDO* tana da Aljanu sune suke sakata wan nan shegen yawon.........

Yauma tasamu sa'a *GOGGO* bata rufe k'ofar ba dan haka tasamu damar fellawa da gudu daga d'akin *GOGGO,* *GOGGO* tana kwala mata kira amma inaaa zakara yabawa *INDO* sa'a, *GOGGO* tsayawa tayi kawai tana kallon k'ofar soro ta inda *INDO* ta felle addu'a tashiga yi mata cikin ranta kafinnan takama aikinta.....

Tana fita tanufi k'aramar kasuwar dake cikin garin nasu,babu mutane sosai a kasuwar saboda safiya ce dayawan mutane basu firfito ba amma hakan bai hana *INDO* samun wani itacen bishiyaba tayi zamanta tana kallon d'ai² kun mutanen da wuce domin sayen abinda zasuci.........

Daga nesa ta hangoshi cikin shigarsa ta burgewa,daganin sa kasan ba rayuwar garin k'auyen yasaba ba, cikin fara'a tanufi inda yake ta washe fararen hak'oranta tafara gaidashi, shima yasaki fuska sosai ya amsa tareda yi mata 'yan tambayoyi ciki harda tambayar waye babanta acikin garin?...

Bayan yagama jero mata nasa tambayoyin itama tashiga tambayarsa.

"Amma kai ba d'an garin nan bane ko?"

Saida yayi wani irin murmushi san nan yabata amsa...

"Ehh nazo gidan k'anin Abbana ne"

Yabata amsa cikin kulawa

"Aidama tun ranar da na ganka ka sauka a mahin nasan kai ba a nan garin kake ba"

Dariya yayi sosai an nan ya tambayeta...

"To mene da mutanen garin dazakice banyi kama da mutanen garin ba?"

"Hmmmm zangaya maka amma sai mun sake had'uwa, zan tafi ni sai anjima"

Bata jira amsar dazai bata ba kawai *INDO* tayi gaba abinta......


Sai da akafara kiran Sallah Azahar san nan *INDO* tashigo gida alokacin *GOGGO* tagama aikin cikin gidan duka, Abinci *GOGGO* ta d'akko wa *INDO* ta mik'a mata amma abin mamaki sai *INDO* tace ita ta k'oshi bazata ciba, *GOGGO* kam har cikin ranta bataji dad'i ba gashi zuciyarta tana sak'a mata abubuwa kala² ita kam bataso taga *INDO* tak'i cin abinci ko kad'an bata jin dad'in hakan.

" *INDO* mai yasa bazakici abin cin ba?"

" *GOGGO* sai anjima zanci yanzu kam bana jin yunwa"

Badan ran *GOGGO* yasoba haka ta hak'ura ta k'yale *INDO*, fitowa tayi taje ta kulle k'ofar gidan ta 'boye makullin.






*TUNA BAYA*


*WANENE MALAM MODIBO?*



*MALAM ABUBAKAR MODIBO* shine cikakken sunan Mahaifin *MALAM MODIBO* baban *INDO* wato *MODIBO* na yanzu, *BABAN MODIBO* cikakken bafulatani ne kuma sun kasance fulanin tashine basu zama ako ina sai jeji tareda dabbobinsu dasuka had'ar da shanu tumaki zabi da kaji *MALAM ABUBAKAR* shine sarkin rugar garin kuma babban Malmi ne wanda mutanen rugar suna ganin girmansa sosai duk rugar da suka zauna dazarar mutane sun fara cika wajen sai sukuma su tashi suk'ara shiga jeji suda jama'ar su, sun zauna a garuruwa da dama har Allah yakawo su cikin garin kano k'aramar hukumar *AJINGI* ananma ba'a waje d'aya suka zauna ba dan ko kad'an basu son rayuwa cikin jama'a dan haka ne suke yawan tashe² daga wan nan jejin sukoma wanchen...

*MALAM ABUBAKAR* ya jima Allah bai bashi haihuwa ba dan saida sukayi shekaru 15, shida matarsa *SAFIYYA* basu ta'ba haihuwa ba,duk inda *MALAM ABUBAKAR* yaji maganar magani sai yaje yanemo musu ahaka har Allah yasa suka dace tasamu ciki murna sosai awajen *MALAM garnets* tareda jama'ar sa, bayan watanni 10 ne Allah yasauki *SAFIYYA* lafiya tahaifi yaronta namiji ansaha bikin al'adun fulani a wancen lokacin yayin rad'awa yaro suna, *MALAM ABUBAKAR* ya rad'awa jariri suna *ABUBAKAR* wato ya maida sunan sa akan yaron kenan saboda haka sai ake kiran yaron da *MODIBO.*

Shekarun *MODIBO* k'arami goma sha bakwai (17) Allah yayiwa maifiyarsa rasuwa, alokacin saura kwanaki kad'an a d'aura masa aure da *AMINA* mahaifiyar *INDO* kenan.

*SAFIYYA* tagamu da jalinta yayin da *MALAM MODIBO* mijinta yakawo wani k'ato sa wanda babban abokinshi yabashi kiwo shikuma yakawo cikin gidan ya had'ashi da saura shanun dayake kiwo agidansa, tun ranar da aka kawo wan nan *SA* d'in hankalin SAFIYYA yakasa kwanciya dashi saboda yana da matuk'ar fad'a kuma a lokuta da dama idan *MODIBO* k'aramin bayanan itace take basu abinci, kamar kullum yauma *MODIBO* K'arami yauma yatafi kasuwa hakanne yasa *SAFIYYA* kaiwa shanun abinci har cikin garken su, shigarta keda wuya wan nan bak'on *SAN* yayo kanta gadan² kafin ta ankara ya soka mata k'ahon sa a cikinta atake tafad'i sumammamiya tanan wajen har Allah yayi ikonsa ta amsa kiran mahaliccinta babu wanda ya ankara da abinda ke faruwa...

Saida aka kusa yin sallah maghreb sannan *MODIBO* k'arami yadawo daga kasuwa d'akin *INNAR* sa Yanufa amma ga mamakin sa sai yaga batanan wanda a dai² wan nan lokacin yasaba samunta cikin d'akinta tanajira ayi sallah maghreb, fito wa yayi yafara nemanta inda aka kewaye dabbobin nan ya nufa yana zuwa cikaro da *INNA* sa a kwance zuwa lokacin ma tuni tafara sandarewa, fad'awa yayi kanta yana kuka yana salati..

mak'ocin sune yajiyo ihun MODIBO K'arami cikin garken shanun da sauri shima yashiga yana zuwa yaganewa idon sa gawar *iNNA SAFIYYA* kwance ahankali ya janye MODIBO daga jikin *INNA*, saida yak'ara duba ta sosai yatabbatar da cewar rai yayi halinsa san nan yakoma yasanar da sauran jama'a.


*ALLAH YA JIK'AN INNA SAIYYA KAKAR INDO.*



*_Ur's Hubbeey._*
[04/08, 21:54] Hubbey Frd Ameena Kn: *🚶🏻‍♀INDO K'AFAR YAWO*🚶🏻‍♀




*TRUE LIFE STORY*



*1/8/2018.*




*_STORY BY_*

*_AISHA MODIBO_*
*_(Indo k'afar yawo)._*


*_WRITEEN BY_*

*_HABEEBA IDREES(Hubbeey)._*
_________________________
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
_tσ gєt αccєѕѕ σf σur nσvєl'ѕ víα thíѕ línk tσ jσín σur fαcєвσσk grσup._
_____________________







*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHEEM.*







*ALLAHUMMA LAA SAHLAH ILLA MAJA'AL TAHU SAHLAH WA'ANTA TAJ'ALUL JAZNA IZA SHI'ITA SAHLAH.*



*WAN NAN PAGE EN NA RANAR LAHADI NE WANDA NAYI BANSAMU DAMAR YIBA KUMA NA 'DAUKI ALK'AWARIN ZANYI MUKU KAFIN NA RANAR ASABAR.*
*ALHAMDULILLAH*
*NAJI DA'DI DA ALLAH YABANI IKON CIKA WAN NAN ALK'AWARIN.*

*MUCH LOVE MY FANS*


*_Page6⃣._*









Kwanan INNA SAFIYYA arba'in da biyar(45) da rasuwa aka d'aurawa MODIBO K'ARAMI aure da kyakkyawar matarsa ASM'AU wadda agarin suke kiranta da MA'U, ASMA'U tana da matuk'ar kyau ga gashi anyi matuk'ar artabu tsakanin masu neman aurenta cikin su kuwa MODIBO baban INDO shine yayi nasara dasamunta a matsayin matar aurensa, bayan SHA'DI da akasha ayayin neman auren wanda awancen lokacin kowa yashaida tsawon shekaru a rugar tasu ba'a tabayin SHA'DI da gwagwarmaya kanneman aure ba sai akan MA'U wadda kowa yashaida tabbas MA'U mai kyauce..........
Ansha shagalin biki irinna al'adun fulanin asali nawancen lokacin Amarya da ango kowa cikin tsananin farin ciki, A Al'adar garin bayan angama biki ba alokacin amarya zata tare ba, saita tasamu kamar wajen wata biyu agida koma fiye da haka, hakama bayan ankaita sai anyita artabu da ita kafin ta zauna agidan mijin dan kusan kullum sai ta gudo gida komai nisan garinsu haka zata gudo sai bayan wasu kwanaki sai amaida ita ahaka harta tasaba da gidan mijin san nan ta zauna.....
To hakanne yakasance akan MA'U maman INDO amma itakam nata haryayi yawa dan harsai da aka had'a mata da rok'on Allah san nan akasamu tazauna a gidan MODIBO, duk nisan da ke tsakanin garin da Akakaita hakan baya hana MA'U guduwa wuyarta MA'U tasamu 'yan kud'inta tofa zata biya ta hau motar garinsu..........
Hakama idan tasauka daga motar wata muguwar tafiyar ce kafin akai ga dajin da rugar su MA'U take................

Soyayya da shak'uwa mai tsananin sun samu wajen zama a zuk'atan MODIBO da MA'U kullum kafin MODIBO yatafi kasuwa sai ya tabbatar da yagama komai na aikin cikin gidan kafin yafita, haka suke rayuwarsu gwanin ban sha'awa duk dacewar suna k'auye ne amma hakan bai hanasu yin soyyayarsu yadda suke soba.....




Yau kimanin shekaru goma shabiyu (12) kenan da auren MA'U da MODIBO amma har wan nan lokacin MA'U ko 'batan wata bata tabayiba hakan kuwa yana matukar damun MODIBO......
Haka itama MA'U abin yana damunta amma saboda tsananin kunya haka take daurewa bata nuna masa gashi duk sa'anin aurenta duk suna da "ya"ya..............

Wata rana bayan MODIBO yadawo daga sallah maghreb ne suna hira shida MA'U cikin jin dad'iq kawai sai MA'U takawo wa MODIBO magana akan cewar tanaso yak'ara aure, wan nan magana tayi matuk'ar 'batawa MODIBO rai kuma saida yanuna mata afili saboda ko kula ta baiyiba haka ya saka takalmin sa ya bar gidan.....

Sai chaaaan bayan sallah isha yadawo, baiko nemi inda takeba ya nufi d'akinsa yayi kwanciyarsa...

itakam MA'U tarasa inda zata saka kanta dan ko kad'an bataso taga mijinta cikin 'bacin rai ballema ace ita ta haddasa masa, amma ita aganinta idan MODIBO yak'a aure ai zasu samu farin ciki idan amaryar ta haihu, dan haka ta tsaya akan cewar saitayi yadda tayi dan ganin yak'ara auren......



Juyi kawai MODIBO yakeyi yakasa bacci, ganin baccin ya gagareshi ne ya tashi yanufi d'akin MA'U, ga mamakinsa itama sai yasameta a zaune takasa baccin sai tunani takeyi, kusada ita yazauna.......

"Haba ASMA'U gaskiya banji dadin maganarki da kika yi minba d'azu, yanzu ASMA'U kina tunanin akan bamu samu haihuwaba zan k'ara aure?, sam hakan bazai yiwuba muyita hak'uri har mujira lokacin da Allah zai yanke mana dan Allah kicire damuwa daga ranki kinji?"
Tunda yafara magana MA'U batace komai ba kuma bata d'ago kanta ta kalleshi ba, hannunsa yasaka a fuskarta ya d'ago kanta, hawayen da yagani suna sauka daga idanunta sunyi matuk'ar tayar masa da hankali, da sauri ya jawota jikinshi cikin tashin hankali yake tambayarta MENE DALILIN HAWAYENTA? shiru tayi takasa bashi ansa, shima shiruuu yayi da tambayar ta haka yayita rarrashinta har bacci mai nauyi yayi gaba da ita, sai da ya tabbatar tayi nisa cikin barcin ta san nan yatashi, Alwala yayi yazo yafara jero sallolin nafila kamar yadda yasaba yi duk dare...........

Haka rayuwar MA'U da MODIBO tacigaba da tafiya kuma harzuwa wan nan lokacin MA'U tana kan bakarta kullun cikin rokon MODIBO take akan yak'ara aure amma fuurrrr yak'i Amincewa da buk'atar ta..........


Yau Laraba MODIBO yagama shirinshi tsaf dan tafiya kasuwa k'ofar d'akin MA'U yazo danyi mata sallama kallo d'aya yayi mata yaji gabansa yayi wani mummunan fad'uwa, anan yadafa k'ofa yanata ambaton sunayen Allah cikin ikon Allah kuwa atake yasamu sassaucin bugun zuciyar tasa, itakam MA'U kawai kallonsa take dan tasan abinda tagama shirya masa, Sallama yayi mata itakuma tayi masa fatan dawowa lafiya tareda addu'a, jikinsa babu kwari haka yafito yakama hanyar kasuwa......


Saida ta tabbatar dacewar tsawon lokacin da MODIBO yafita ya isa yakaishi kasuwa, san nan ta mik'e tashiga had'a kayanta bata d'auki wani lokaci ba tagama had'a kayanta a kanta ta d'ora faggon kayan wanda ta d'auresu a acikin wani tsohon d'ankwalin ta, mak'otan ta tashiga a soron gidan ta ajiye kayanta tashiga cikin gidan, sak'o ta bayar na kuubar data makulle gidan, cewar idan sunji motsin MODIBO shibashi, matar gidan taso ta tambayi MA'U inda zataje amma ganin yadda tale saurine yasa tafasa tambayar ta.........


Ta bayan gari MA'U ta d'auki hanya sai faman sauri takeyi, tafiya ce mai matuk'ar nisa kafin tasamu ta futo babban titin dake garin AJINGI cikin nasara tasamu mota kasancewar ranar kasuwar LARABAR ZANGO keci ba'ayin wahalar mota.











*_Ur's Hubbeey._*
[04/08, 21:54] Hubbey Frd Ameena Kn: *🚶🏻‍♀INDO K'AFAR YAWO*🚶🏻‍♀





*TRUE LIFE STORY*






*4/8/2018.*







*_STORY BY_*

*_AISHA MODIBO_*
*_(Indo k'afar yawo)._*






*_WRITEEN BY_*

*_HABEEBA IDREES(Hubbeey)._*
_________________________
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
_tσ gєt αccєѕѕ σf σur nσvєl'ѕ víα thíѕ línk tσ jσín σur fαcєвσσk grσup._
_____________________




*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHEEM.*





*ALLAHUMMA LAA SAHLAH ILLA MAJA'ALTAHU SAHLAH, WA'ANTA TAJ'ALUL HAZNAH IZA SHI'ITA SAHLAH.*


*BRR ALEEYAH*
*NA*
*AUFANA*

*HAK'IK'A INA MAI MATUK'AR TAYAKI MURNAN KAMMALA WAN BAN SHAHARARREN NOVEL NAKI MAI 'DAUKE DA ILMANTARWA,FA'DAKARWA TAREDA NISHA'DANTARWA ALLAH YAK'ARA 'DAUKAKA DA BASEERA.*



*SAK'ON INDO ZUWA GAREKU FANS.*


👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
*AMFANIN LALLE GA MATA*




Lalle dai da farko wani sinadari ne mai dauke da alfanu iri iri, kuma addini ya kwadaitar da mata su yi lalle akwai sirrika acikin sa.
Nafarko dai lalle Kariya ce daga sihiri, Kariya ce daga aljanu sannan kuma Kariya ce daga cututtuka da dama, yin lalle a kafa na zuqe cutar dake kafan sannan yana kula da dumin mace, bi ma ana yana kiyaye. ni imar mace ba tare da ya gushe ba, innace lalle wasu zasu dauka zanen henna nake nufi ko, to lalle dai na gargajiya wanda muka rabu da yinsa yanzu shi nake magana akai:

Ga kuma sadaqa ga duk mai infection ta tafasa lalle inyadan huce sai ki dinga zama a ciki na sati biyu, in Allah yayarda za ki warke.

: Saboda maganin da lalle keyi ma akan iya shan ruwan lalle cokali daya don wankin dattin ciki amma banda masu ciki, to yanzu dai zamu dauki bangare daya daga cikin amfanin lalle muyi magana akai, wato shine amfanin lalle da kuma yanda ake amfani da shi don gyaran Fata.

Lalle dai ba karamin tasiri yake dashi wajen gyara fata ba, domin shi natural toner ne ba bleaching yake ba amma yanasa haske mai kyau kuma yana goge dattin fata, in kina son gyara fuska tai kyalli, laushi da haske to ki kwaba lalle da ruwan Kwai amma banda kwaiduwar kwan ki kwaba ruwa ruwa amma ba sosai ba ki lizimci shafa shi kullum minti talatin kafin wanka, za ki sha mamaki in sha Allah:

Ga masu son hasken fata, ki kwaba lalle da ruwa, ki shafe a jikinki inya bushe ki
DOWNLOAD
DOWNLOAD
Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3

1 Comments On INDO KAFAR YAWO
avatar
jamila-3-9

7 months ago

Reply

Lovely

Please Login or Register in order to submit comment