Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

dirje da man zaitun zakiga canji.

sannan gamai son kamshin fata
: Ki kwaba lalle da turaren ki mai kyau na ruwa wanda ake durawa ki zuba isasshen ruwa a bucket ki sa garin lalle ya jika yay já zir sai ki tsiyaye ruwan ki diga turaren ki mai kamshi ciki Bayan kinyi wankan sabulun ki sai ki dauraye jikinki dashi inkin lizimci haka to bake ba rabo da kamshin jiki in sha Allahu.

: Sannan ga gyaran duka jiki kuma zaki hada lalle da sabulun salo da Zuma kina wanka dasu duk zakiga canjin fata in sha Allah
Sannan ga Amare kuma
Kafin kiyi dilke na aurenki
: fata zatayi laushi, haske da kuma santsi.
Ki samu lalle mai kyau ki kwaba da turaren ki mai maiko, turaren gargajiya mai mai dinnan to ki jika kamar botiki ba ruwa ruwa sosai ba Kamar dai kunu, kullum sai ki shafe jikinki da hadin lallen nan duka jikin ki, sãi kizo ki saka turaren wuta a kasko ko burner ki rufu akai ki turara jikinki hayakin turaren nan ya shiga sosai sai ki fita kije kiyi wankan ki zakiga canji.

Daga karshe kuma ga masu fama da pimples, sai ki hada lemon tsami da lalle kwabi mai dan tauri amma ba sosai ba kina shafa wa a fuskaar ki, kuraje zasu mutu sannan tabo bazai zauna ba ga hasken fuska da laushi.









*_Page 7⃣._*






Kafin La'asar MA'U ta isa cikin rugar su bata zarce ko inaba sai cikin gidan iyayenta, INNAr MA'U tayi matuk'ar razana da ganin MA'U dan ita atunaninta MA'U gudowa tayi wanda tad'e batayiba, fuskar INNA ba yabo ba fallasa haka ta karbi MA'U, abinci da ruwa ta kawo mata san nan ta fara tambayar ta dalilin zuwanta, nan MA'U ta gayawa INNArta duk abinda yafaru bata 'boye komai ba, anan tasamu damar rok'onsu INNA akan su taimaka mata susaka baki acikin maganar AUREN dan itakam tana matuk'arson taga yaro/yarinya agidansu kodakuwa ba ita ta haifaba....
INNA dai shiruuu tayi tana ta tunani akan maganar MA'U takasa cewa komai..........



Sai dab da sallah maghreb MODIBO yak'araso cikin garin.......
Daga nesa yaron yagano MODIBO dan haka yakoma gida da gudu yana gayawa Umman sa cewar ga MODIBO chan yadawo, tashi tayi ta d'akko makullin da MA'U takawo ajiya tabawa yaron, da gudu yasake futowa yanufi MODIBO dake dab da k'ofar gidansa, "BABA MODIBO ga makullin gidan" cikin mamaki MODIBO ya kalli yaron yace
"waye yabaka yace ka kawo min"

"ai tunda safe ne MA'U takawo tace in UMMAna taji motsinka abaka"
Hannu yasa ya karbi makullin...
"To nagode maza ka tafi gida"
Da "to" yaron ya amsa san nan ya fellah da gudu abinsa....


Jikinsa a sanyaye yasa Makullin ya bud'e gidan san nan yashiga da sauran kayansa daya sayo a kasuwa,haka yayi alwala yanufi masallachi domin yin sallah maghreb.......



Bayan sallah maghreb ne BABAN MA'U ya shigo gida shima yayi mamakin ganin MA'U amma ko kad'an bai bayyana musu afiliba, bayan yagama cin abinci ne INNA ta shaida masa dalilin zuwan MA'U kamar yadda MA'U ta gaya mata....
"To kingadai kece mahaifiyar ta kuma ke kikasan halayen mata fiye da ni yanzu yaya kike ganin zamuyiwa MODIBO?"
BABAN Ma'u keyin maganar alokacin da INNA tagama gaya masa buk'atar MA'U.

"Hakane amma ina ganin kawai mukirawo MODIBO muyi magana dashi idan mukaji ta bakinsa sai kuma musan abinyi agaba, amma zamu nunawa MODIBO cewar yak'ara auren tunda dai ita tasakashi kaga komene yafaru ita tajawowa kanta ko?"
Inji INNAr MA'U kenan

"Shikenan in ALLAH yakaimu gobe da sassafe zan aika Akirawo MODIBO sai muyi maganar"

"to Allah yakaimu"
INNA ta amsa masa......




Washegari da sassafe saiga MODIBO ya sauka a babbar rugar tasu, kowa yayi mamakin ganinsa da wan nan farar safiyar babban abin mamakin wajen mutane shine tayaya MODIBO yasamu mota da wan nan safiyar?
Shikuwa tunda yasa kansa zai zo bai jira wata mota ba kawai hayar machine yad'akko tundaga garin dayake yakawoshi har cikin rugarsu......

kamar yadda MA'U ta zarce gudan iyayenta a jiya da sauka rugar, haka shima MODIBO kai tsaye gidan BAFFANsa yanufa.........

A k'asan bishiya ya hango BAFFANsa inda yasaba zama kullim domin kar'bar k'orafin al'ummar rugar kasancewarsa sarkin rugar garin kuma babban malami......

Tun daga nesa BAFFA yake k'arewa MODIBO kallo tareda gano damuwa k'arara akan fuskarsa, MODIBO yayi sa'a babu wasu mutane a majalissar mahaifinnasa dan haka yaji dad'in ganin BAFFANsa, bayan sun gaisane MODIBO yagayawa BAFFA abinda yagani jiya na rashin ganin MA'U agidan bayan yadawo daga kasuwa.....
Sai da BAFFA yayi shiruuu na d'an wani lokaci kafin yafara magana irintasu ta manya....

"Ehhh ni tunjiya labari ya isheni cewar anga MA'U tazo, amma saboda nasan bata zuwa ita kad'ai sai nayi tsammanin ko kana hanya kaima to amma sainaji shiruu bakaxoba harna tashi daga fada......."
Shiruuuuu BAFFA yasakeyi tsawon wani lokaci kamar mai wani tunani san nan yaci gaba.......

"To inaso kagayamin maikayi mata da har yasata tawo gida batare da kasani ba?"

Nanma yayi shiruuu yana jiran yaji daga bakin MODIBO....


"A gaskiya BAFFA nidai a jiya da shekaranjiya nikam bamu samu wani sa'bani da MA'U ba"....
Anan MODIBO yayi shiru


"A'a MODIBO basai a jiya da shekaranjiya ba koda acikin wan nan shekararne indai kasan kun samu wani sabani kagayamin, dan kasan su mata wani lokacin abu baya wucewa awajensu, kokuma dakayi wani laifin sai su tuno da wancen da wuce, dan haka yanzu katashi kashiga cikin gida abaka abinci ka karya san nan kayi tunani akai sai kazo mu k'ara maganar ko"

Bai musawa BAFFA ba haka yatashi zuciyarsa cike da tunani kala², a tsakar gida yasamu GOGGO wato matar mahaifinsa, hannu biyu ta karbeshi nan takawo masa abinci suka gaisa tareda tambayar sa iyali, sosai MODIBO yayi sa'ar matar mahaifi domin kuwa inbaka saniba zakayi tunanin GOGGO ce ta haifi MODIBO haka shima yanayi mata biyayya dai² iyawarsa.



















*_Ur's Hubbeey._*

*🚶🏻‍♀INDO K'AFAR YAWO*🚶🏻‍♀




*TRUE LIFE STORY*


*11/8/2018.*



*_STORY BY_*

*_AISHA MODIBO_*
*_(Indo k'afar yawo)._*


*_WRITEEN BY_*

*_HABEEBA IDREES(Hubbeey)._*
_________________________
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
_tσ gєt αccєѕѕ σf σur nσvєl'ѕ víα thíѕ línk tσ jσín σur fαcєвσσk grσup._
_____________________








*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHEEM.*









*ALLAHUMMA LASAHLAH ILLA MAJA'AL TAHU SAHLAH, WA'ANTA TAJ'ALUL HAZNAH IZA SHI'ITA SAHLAH.*








*KAMAR YADDA KUKA SANI WAN NAN NOVEL NA INDO K'AFAR YAWO YANA ZUWA MUKUNE AKOWANNE RANEKUN ASABAR DA LAHADI NA KOWANNE SATI DAN HAKA AWAN NAN SATIN,*
*INA MAI FARIN CIKIN SANAR DA MASOYANA CEWAR GOBE LAHADI SHA BIYU GA WATA AUGUSTA,(AUGUST) SHINE RANAR HAIHUWA TA YAZAGAYO, (MY BIRTHDAY) WANI ABIN DA'DINMA HAR DAY 'DIN DAI² YAZO RANAR SUNDAY.*



*DAN HAKA BA LALLAI GOBE INSAMU YIN TYPING EN WAN NAN NOVEL BA, AMMA INHAR NAGA DA HALI ZANIYI INSHA ALLAH.*



*SAK'ON INDO ZUWA GAREKU FANS.*

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻



*HANYOYIN DA ZAKI GYARA FATARKI CIKIN SAUK'I.*





Babu wata mace da ba ta so a ce fatarta tana sheki da yalki; babu kuma macen da take so a ce fatarta ba ta da kyau ko daukar hankali. Hakan ya sanya mata da yawa ke kashe makudan kudade wajen lura da fatar jikinsu ko ta fuska. Da yawa daga cikin mata kuma sun fada tasku sakamakon amfanin da mayukan da suke da sinadarai, wanda a maimakon kwalliya ta biya kudin sabulu sai su buge da da-na-sani. Wannan dalili ya sanya na taho miki da hanyoyin 6 da za ki bi wajen lura da fatarki ba tare da tararradin ko fatarki za ta gamu da wata matsala ba. Ga hanyoyin kamar haka:
1.    Ki samu kukumba sai ki yayyanka ta, daga nan sai ki nika ta, sannan ki ajiye ta gefe guda. Hada ruwan Rose Water da ruwan lemon tsami ko jus din lemon tsami. Bayan nan sai ki hada su waje guda da kukumbar, sai gauraya sosai. Bayan kin yi haka sai ki shafa a fuskarki ko sauran fatar jikinki, sannan ki kwanta har zuwa wayewar gari. A lokacin da kika zo wankewa, sai ki samu ruwa mai dumi. Hakan zai kara wa fatarki lafiya da kuma sheki.
2.     Hanya ta biyu ita ce, ki samu madarar shanu wacce ba a dafa ba, sai ki samu gishiri da kuma cokali biyu na ruwan lemon tsami ko ruwan jus din lemon tsami, sannan ki gauraya sosai. Bayan nan sai ki samu auduga ko tsumma mai tsabta sannan ki rika dongala kina gogawa a jikinki ko a fuskarki. Bayan nan, sai ki wanke jikinki ko fuskarki da ruwa mai dumi. Hakan zai cire miki dukkan dattin da ke makale a kofofin fatarki.
3.     Hanya ta uku ita ce, ki gauraya ruwan Rose Water da kuma ruwan lemon tsami. Ki shafa a fuskarki ko jikinki. Yin hakan zai cire tabon da yake fata ko fuska, sannan yin hakan zai sanya fata ta yi laushi da danshi.
4.     Ki samu lemon zaki sai ki yayyanka, daga nan sai ki markada. Bayan nan sai ki shafa a fuska ko a jikinki. Wannan zai sanya miki laushin fata.
5.     Ki samu karas sai ki markada, daga nan sai ki shafa a fuskarki ko jikinki. Bayan awa biyu sai ki wanke da ruwa mai dumi. Yin hakan zai sanya jikinki ya rika haske da kuma daukar hankalin duk wanda ya kalle ki.
6.     Ki samu kurkum sai ki daka, daga nan sai ki hada da dakakkiyar alkama, sannan ki hada da man zaitun. Daga nan sai ki shafa a fuskarki ko a jikinki. Bayan awa biyu ko uku sai ki wanke fuskarki ko jikinki da ruwa mai dumi. Hakan yana cire kwayoyin cutar da ke makale a kofofin fata.
Yadda Za Ki Yi Amfani Da Kurkum Wajen Gyara Fatarki


Kurkum na dauke da sinadarai da dama kamar su, bitamin B6 da bitamin C da sauransu. Kuma yana rike fata yadda ba za a sami rauni . Yawan amfani da hadin kurkum na sanya fata musamman ta fuska laushi da santsi da kuma haske. Don haka, ya kamata kada a manta da wannan kurkum idan an zo kwalliya. ta zama sakakkiya ba. Amfani da kurkum na sanya sabuwar fata fitowa da wuri a inda tsohuwar tAmina Abdullahi
•A sami garin kurkum da zuma cokali daya da ruwan lemon tsami kwatan kofi. A kwaba su sosai har sai sun yi laushi. Sannan a shafa a fatar fuska a bari ya jima na mintuna 15 sannan a wanke da ruwan dumi. Yin wannan hadin na hana kurajen fuska fesowa. Za a iya yin wannan hadin kamar sau daya ko biyu a sati domin samin ingantaccen sakamako.

•Amfani da kurkum na rage gautsin fuska. A kwaba kurkum da nono ko kindirmo. Sannan a wanke fuska kafin a shafa hadin a fuska. A jira na tsawon mintuna 10-15 kafin a wanke. Za a iya jarraba wannan hadin a kullum bayan an yi wanka.
•Idan ke mai yawan aiki a karkashin rana ce, ya kamata ki samu kurkum kadan da kindirmo mai yawa sai ki rika shafa wa a inda kunan rana ta bata fuska. kunan rana na sanya fuska ta zama kamar mai shafe-shafe don haka wannan hadin zai magance wadannan matsalolin.
•Ko kun san cewa kurkum na magance bakar fatar karkashin hammata? To! A sami zuma kamar cokali daya sai a hada da ruwan lemon tsami kamar cokula 3-4 sai a zuba garin kurkum kadan sannan a kwaba a shafa a karkashin hammata a bari ya jima na tsakwon mintuna 10-15 kamin a wanke.








*_page 8⃣._*



MODIBO Yana cikin cin abinci ne yake tuna abinda yafaru tsakaninsa da MA'U a sati d'aya daya wuce take ya ajiye abincin yafara tunanin ta yadda zai sanar da BAFFAN sa, HAJJO matar mahaifin MADOBI ta lura sarai da yadda MODIBO yashiga damuwa alokaci guda taga ya mik'e ya futa daga gidan.....


Sai Bayan sallah azahar san nan MODIBO suka samu zama da BAFFANsa, Tun kafin BAFFAN yafara magana tuni MODIBO yafara gaya masa yadda sukayi shida MA'U, shiruuuu BAFFAN yayi na d'an wani lokaci.......

"Yan MODIBO wan nan shine dalilin dayasa MA'U zatayo yaji akan kak'i k'ara aure?"




"Wllh nidai BAFFA iyakachin abinda nasani kenan, saida ko akirawo ta muji abinda zatace"

Kan MODIBO ak'asa yake Bawa BAFFAN sa amsae tambayarsa.....


"Ehhh gaskiya ne daman dole insa akirawo ta inzauna daku tare"
BAFFA ne kenyin maganan yana mai kallon MODIBO.....



Nan suka saka wata hirar, sai bayan sallah La'asar san nan BAFFA yasa aka kirawo MA'U, wan nan zaman shikuma acikin d'akin BAFFA akayishi.......

Kanta ak'asa takasa had'a ido da MODIBO ballantana BAFFA, tsawon wani lokaci babu wanda ya iya cewa komai, ganin shirunyayi yawane BAFFA yafara tambayar MA'U meke faruwa saida BAFFA ya maiamaita mata tambayar sau biyu, san nan tafara bashi amsa cikin tsananin jin kunya, ta kwashe yadda sukayi ita da MODIBO bata boye komaiba har zuwa tawo warta gida, yadda MODIBO yafad'awa BAFFA komai haka itama MA'U ta fad'a dan haka BAFFA yaji dad'in sosai babu wani bata lokaci ya yanke musu hukunci akan cewar dole MODIBO yayi aure kamar yadda MA'U take so......



MODIBO bayadda ya iya haka ya karbi maganan auren dan bazai ta'bayin musu da maganar mahaifinsaba, haka zaman yatashi MA'U tana cikin farin ciki, shikuwa MODIBO kawai yak'e yakeyi wan da hausawa suke cewa "yafi kuka ciwo".........

Washegari da wuri MA'U da MODIBO suka gama shirinsu tsaf na komawa garin su, HAJJO ta had'amusu kayan tsara ba, haka itama INNAR MA'U tayi musu tara ta arziki......


Da wuri suka sauka agarin su tunda suka tawo babu wanda yayiwa kowa magana haka har suka shiga gida itakam MA'U batada wata damuwa tunda burinta yacika dan haka kome MODIBO zaiyi babu ruwanta........



Da daddare bayan MODIBO yadawo daga sallah ne yasamu MA'U ad'akinta, alokacin ta idar da sallah tanata addu'a, saida yabari ta idar san nan tara mata magana....


"MA'U burinki ya cika mahaifina yace ink'a aure, amma sanin kankine banida wata mace da nikeso bayanke ko? Dan haka aiki yarage naki saikinemo wacce kike so ku zauna da ita nikam babu abinda yadameni inkinnemo zanyi aure kuma duk abinda yabiyo baya karkiyi kuka da ABUBAKAR MODIBO danke kika jawowa kanki, BAFFA yabani wata 2 inyi aure dan haka nikuma nabaki sati 2 kinemomin matar dazan aura"


Yana gama fad'ar haka baijira jin amsar dazata bashiba yayi ficewar sa daga d'akin, Nan MA'U tashiga funanin wadda zata nemowa MODIBO amatsayin AMARYAR sa........


Bayan kwana uku (3) MODIBO yatashi gina wasu sababbin d'akuna acikin babban gidansa, 'Dakuna yayi manya guda uku. Akayi masu rufin kwano, wanda a cikin garinsu MODIBO ne mutum na farko daya farayin rufin kwano alokacin ansha zuwa kallon gidan MODIBO saboda kyawun gidan, daga wan nan lokacin wasu suke kiran MODIBO da MAI DIGAN KWANO.




Wata yarinya BINTA mai kawo wa MA'U tallan kayan miya, itace MA'U ta fitarwa MODIBO amatsayin wadda zai aura, BINTA yarinya ce mai hankali ga nutsuwa kuma tanayin karatun boko da islamiyya saidai kuma su BINTA suna cikin tsananin talauci saboda hakanema duk wanda suka fito neman auren BINTA sai su fasa saboda yadda za'ayita d'aga auren saboda babu yadda za'ayi asaya mata kayan d'aki, dan haka MA'U take tsansnin tausayawa rayuwar BINTA da mahaifiyarta da k'annenta guda 2, wan da magaifinsu ya jima da rasuwa......


Har d'akin MODIBO MA'U tasameshi da maganar BINTA shikam Bashida wata amsa dazai bata dan tabbas yasan yadda su BINTA suke kuma yasan tarihin mahaifiyar BINTA kokad'an bata da hayaniya dan haka bai musawa MA'U ba..........





Cikin k'an k'anin lokaci BAFFAN MODIBO yaje yanemawa MODIBO auren BINTA, babu wani 'bata lokaci aka basu, aka saka biki wata d'aya, itakam BINTA ko kad'an abin bai mata dad'i ba dan ganinta taci amanar MA'U wadda kullum intakai mata tallah ko bazatayi amgani da abinba saita saya dankawai ta farantawa BINTA bayan kayan sawa da abinci datake bata takawo mahaifiyarta, dan haka ansha artabu kafin BINTA ta amince amma acewar ta saidai MODIBO yaraba musu gida dan bazata iya zama da MA'U amatsayin kishiya ba saboda yadda take tsananin ganin mutunci da k'imar MA'U.






















*_Ur's Hubbeey.😘_*



An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

DOWNLOAD
DOWNLOAD
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3

1 Comments On INDO KAFAR YAWO
avatar
jamila-3-9

7 months ago

Reply

Lovely

Please Login or Register in order to submit comment