Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

don ba zan yadda wannan dukiyar da na ke gani ta tafi a tutar babu ba,ayi duk abinda za'ayi ko nawa ne zan biya matuƙar dai nima zan samu abinda na keso."

wa wa keken bakinsa ya buɗe ya ce"ni boka tsidau na yi miki alƙawarin haihuwa a gidan multibuloniya Ammar,akwai abinda zamuyi miki matuƙar kika yi to tabbas za ki samu Haihuwa don haka ki saka aranki ma kin samu". sai ya bushe da wata irin dariya mara daɗin sauraro.

"Tashi ki biyoni kin samu Haihuwa kin gama".

dariya ce ta kama ƙawar Sakinat wato Falmata don tasan abinda bin boka tsidau ya ke nufi,ɗan jiyowa Sakinat ta yi ta kalli ƙawarta da ayar tambaya a bakinta sai dai babu ikon yin maganar don boka tsidau tuni ya yi gaba cen ƙarshen dutsen inda wata ƴar ƙaramar bukka ta ke.

Wa iya zubillah wannan boka aranar sai da sukayi alfasha da Sakinat kuma ya tabbatar mata cewa buƙatar ta kamar ta biya ne.
Masha Allah Ammar shirye ya ke cikin wata tsadaddiyar shaddarsa ruwan arsh ya gyara gashin kansa wanda ya ƙwanta luf luf irin na asalin fulanin usul,fatarnan sai walƙiya ta ke yasha agogonsa na rolex ya yi matuƙar ƙyau,wani irin nishaɗi ya ke ji don ayau zai ga Amminsa bayan shekara 5cif ba tare da sun haɗuba.

Yana shiga motar dieban yaja sauran motocin suka biyosa ya rufe idanunsa kamar mai jin bacci daman kuma aƙidarsa ce kuma haka Allah ya halicce sa baya mintina ba tare da ya yi hakan ba,hakan baƙaramin ƙara masa ƙyau ya ke ba,ga waɗanda basu sanshi ba sai suce iyayi ne.




Wata muguwar harara Sakinat ta bugawa ƙawarta Falmata ta ce"gaskiya Falmata baki da mutunci da ki ka haɗani da wannan bokan gashi yanzu ya haɗa jiki dani in banda wari da hamami babu abinda ya ke,ni wallahi Allah ya isa kawai kuma yanzu ba sai
Anjima ba Zamu je hospital a dubani".
Dariya Falmata ta yi bata ce komai ba suka cigaba da tafiyarsu har suka kai bakin titi suka tari mota suka tafi,duk jikin Sakinat ciwo kawai ya ke.

Ko da aka duba ta lafiya ƙlau babu wata cuta sai anan taji wani babban abu ya wuce a maƙogoranta ta amshi ruwan sanyi ta kora,suka hau mota Falmata ta wuce gida ita kuma Sakinat ta wuce Adamawa wajen mahaaifinta.



Jiniya ce ta cika titin baki ɗaya ko da ba'a gaya maka ba kasan wani mai babban muƙami ne zai wuce don haka sai matsawa a ke.


Salati Sakinat ta yi ganin motocin mijinta G.A M wato general Ammar Muhammad.





*Ummu Maher ce*
*🌈DARASI!!🌈*


BOOK 1

✨Rabiatu Bashir
Ummu maher(miss green)🍀💚


*@Wattpad link*

https://www.wattpad.com/user/Rabiatu333?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_campaign=invitefriends


*@Arewa book link*

https://arewabooks.com/chapter?id=62a48949772e179ad6e54443


*SIRRINKI👂🏻*

Shan kayan marmari yana taimakawa wajen bunƘasa lafiyar jiki.
----------------------------

04/05


. . . . . Sakinat aranar ta koma Abuja Don firgici da tsoro,duk hatsabibancin Sakinat tana matuƙar jin tsoron Ammar don shima hatsabibin kanshi ne,wannan asirin da ta yi mishi ma da wani babban jigo ta haɗashi har aka samu abinda a keso.


Har gudawa Sakinat ta yi don ta tsorata da ganin Ammar a Adamawa,to yaushe ma ya dawo ba tare da ya sanar mata ba?kuma me yaje yi Adamawa?abin tambayar ta shine ba dai gidan mahaifiyarsa yaje ba?da sauri ta tashi daga zaunen da ta ke,tana girgiza kai tana cewa"no.no.no ba zai yiyu ba ace yaje wajen mahaifiyarsa ba,don tafi kowa sanin cewa farraƙu ta saka aka yi musu a tsakaninsa da mahaifiyarsa.


Har dare Sakinat tana sukuku gashi ta kira aminiyarta Falmata ringing yafi goma bata ɗaga ba,ƙarshe ma taji an kashe wayar wayar.

"Wato ma kada in dame ta shiyyasa ta kashe wayar ko?shegiya mayya kawai ai nasan tunda ta ce baƙo za tayi to lallai tana cen tare dashi"ta yi wurgi da wayar hankalinta a tashe,ga ta da tarin tambayoyi amman kuma babu mai amsa mata.
Sai kusan ƙarfe uku sannan bacci ya ƙwashe ta daman babu halin yin sallar asuba don Sakinat sai taga dama ma take yin sallah,wa iya zubillah.


Sai kusan ƙarfe uku sannan bacci ya ƙwashe ta daman babu halin yin sallar asuba don Sakinat sai taga dama ma take yin sallah,wa iya zubillah.




Ammar kuwa yana isa Adamawa ya kira Aliyu babban abokinsa mazaunin Adamawa amman wani lokacin yana Abuja Babban gidan da Ammar ya sai mishi,yana kiransa bugu ɗaya ya ɗaga yana tsokanarsa da angon sakinat,"mlm bar wannan tsokanar kana cikin gari ne?kazo zaka yimin jagora wajen AMMI."

"Welldone aboki na ina yiwa Allah godiya da ya karkato da hankalinka akan mahaifiyarka,insha Allah yanzu zanzo.

Sai da Ammar ya jira yazo sannan suka tafi suna ta hirarsu ta abokai,daman su uku suka tashi Amir,Ammar,sai Aliyu,ana kiransu da first A.
Khalisat tana tafe tana bitar karatunta na hadda alokacin ta fito kenan za taje islamiyya,sauri ja da baya ta yi don ganin motoci kala sunfi goma a bakin gate Ɗin gidan kana ganin motocin ba sai an gaya maka ba kasan sun haɗu sosai.

Aliyu ne ya fara fitowa yana kallonta cikin murmushi,itama murmushin ta mayar masa tana sake kallon motocin gabanta yana faɗuwa.

Ƙafar sa ya fara sakowa kafin ya fito,da sauri Khalisat ta ja da baya kamar za ta faɗi badon tsohuwar motar Ammi ta tare ta ba da tuni ta faɗi.

Ya.ya.ya.ya.sai kuma ta zunduma da gudu ta yi cikin gida tana kiran Ammi!ammi!!Ki fito kiga wani abu,kafin ta gama rufe bakinta tuni Ammar ya shigo shi da amininsa Aliyu.

Kusan daskarewa Ammi ta yi a tsaye tana kiran sunan Allah tare da godewa Allah daya dawo mata da farin cikinta wato ɗanta Ammar.


Da gudu ya rungume Amminsa yana kuka yana kiran"ilove u my Ammi na ki yafe min don Allah,na tuba bazan sake ba ya haɗa hannayensa alamar neman yafiya.

Ita ma kukan ta ke tana "son na yafe maka Allah na gode maka da ka dawo min da farin cikin raina".


aranar waɗannan Familyn suna cikin farin ciki sosai,ya yiwa Ammi alƙawarin sai ya yi sati biyu kafin ya koma don ya samu hutu,sosai Ammi taji daɗi tana ƙara saka mishi albarka,don tasan duk abinda ya yi ba da sanin sa bane asiri ne.
Tunda Ammar yaje bai kira Sakina ba,hankalinta ya tashi sosai ta dinga kiransa a waya amman yana gani yaƙi ɗaukar wayar ƙarshe ma ya kashe wayar.


Suna zaune da daddare suna cin abinci Khalisat ta kalli yayanta,ta ɗauki ruwa ta fara sha ai Ammar yana ganinta ya yi saurin ƙwacewa yana ce wa"inye lallai Khalisat kin samu sarari yanzu ruwa ki ke sha kina cin abinci?.
"Wallahi Yaya" ranƙwashi Ammar ya kai mata yana ce wa"me ɗan ƙaramin baki kawai.

Murmushi Ammi ta yi tana kallon ƴaƴan na ta cikin so da Ƙaunar su,tana roƙon Allah ya bar maya ƴaƴanta guda biyu da ta mallaka a duniya.







*** *** ***

Amma ta ƙara matsamin sosai yanzu don talla na ya ƙaru yanzu inyi na safe inyi na rana inyi na dare,bani da lokacin hutu Baba na babu yadda zaiyi don yanzu ma har ya fara shiru da bakinsa,tunda ita dai amma ba dai na wa za ta yi ba,don haka ya tattara ta ya watsar da ita don rashin kunyar da ta ke mishi abin yana damunsa.

Ni daman ba a zancen arabi ballan tana boko kullum ina yawo a gari gayyar talla.




Rannan da daddare ina tafe tsoro fal a ciki na don ban taɓa yin dare irin na yau ba,don nasan idan na koma gida sai Amma ta yi gunduwa2 dani.


Wani kango nazo wucewa naji wari kamar nawiwi,na toshe hancina ina kakarin amai,kawai sai naji wani yana ce wa"kai Ba-ba waccen yarinyar me ta ke toshewa hanci ne?".

"oho bari muje muji me ta ke toshewa hanci. . . ...




Anan zan tsaya don rashin comments.
*🌈DARASI!!🌈*


BOOK 1

✨Rabiatu Bashir
Ummu maher(miss green)🍀💚


*@Wattpad link*

https://www.wattpad.com/user/Rabiatu333?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_campaign=invitefriends


*@Arewa book link*

https://arewabooks.com/chapter?id=62a48949772e179ad6e54443


*SIRRINKI👂🏻*

Ki yawaita yiwa ƴaƴanki addu'ah yin hakan zai taimaka miki wajen shiryuwar ƴaƴanki.
-------------------------------
06/07


. . . . .har nazo ƙwanar layinmu sai naji kamar ana bina a baya,ga warin taba dana wiwi ya haɗe waje ɗaya suna bada wani irin ɗoyi me wari,sauri na fara yi ina waiwayansu don tun ina hangosu daga nesa yanzu kurkusa na ke hango su.


Gudu sosai na fara yi amman kun san gudun mace dana miji ba iri ɗaya bane dai gashi sun cimma ni,kuka na farayi ina basu haƙuri amman ko sauraro banga suna yi ba,don ko ɗigon tausayi babu a fuskarsu,abinda naga ɗaya daga cikinsu yana shirin aikatawa ne yasa na buɗe bakina na taƙarƙare na rusa uban ihu,yana zuge ta zugen wandonsa yana lasar
Baƙin bakinsa wanda ya gaji da shan tabar wiwi.


Wata shaƙa babban nasu ya kawo min tare da duka na akai nan da nan na daina ganin komai sai duhu,saurin ɗaukata suka yi da ya ke dare ne babu wanda ya gansu suka shiga dani wani kango.
"Kai ba-ba ya zamuyi da wannan yarinyar kada fa a kamamu".?


"au tsoron kamen ka
Ke kai" ?,kawai mu ƙwashi rabonmu mu mu wuce mu bar ƴar talla masu son kuɗin jaraba ai daman ƙarshen son kuɗi kenan",ya faɗi hakan yana lashe bakinsa.


"Haba Amma ta ya ya zaki ƙwanta ki yi ta bacci amman kuma ƴarki bata dawo ba har yanzu?ki duba agogo ƙarfe goma na dare fa?gaskiya Amma wannan mummunar ɗabi'ar da ki ka ɗakko ba za ta haifa miki ɗa mai ido ba",yana faɗar hakan ya yi hanyar waje yana cigaba da mitarsa kamar zai cinye ta,amman matar nan Ƙara juyawarta ta yi tana baccinta har da minshari,Haruna ma da ya ke ƙarami kuka ya dinga kuka ganin Fahima bata dawo ba,don ya saba ita ke kaishi ya yi fitsari.

A hankali ya ke tafiya yana ɗan duba lungu2 na layinsu,ƙwatsam ya hango wani lungu,ci ke da ƴan daba suna shawarwari a tsakaninsu akan su aikata mata ko kada suyi.

Shahada ya yi yaje wajen ya haskosu da babbar fitilarsa,da sauri suka jiyo dukkansu kana ganinsa kasan shine mahaifin yarinyar nan don har hasken da ƙyau irin na fulani duk na shi ne.

"Aha kace kazo ne ka karɓi ƴar ka ko"?.

sai suka tuntsire da wata mahaukaciyar dariya suna nuna baban Fahima.

Kukan kura ya yi ya bige mutum biyu Alokaci guda da ya ke sun bugu sosai suka zube a wajen,saura mutum biyu,da sauri ya yo kansu suma suka fita da gudu,ya tsugunna yana hawaye har sun fara yagawa Fahima kayanta abin tausayi.

Kawai sai yaji saukar wani abu a bayansa tun daga nan bai ƙara sanin inda ya ke ba.





*** *** ***

Da wuri Sakinat ta dira a garin yola babban birnin adamawa,tana sanye da glass baƙi no respect wanda ya gaji da haɗuwa yana sheƙi da walwali.

Ta saka ƙananun kaya komai na jikinta ana gani ita daman ƙirar slindium ne da ita babu cinya babu sharaɓa sai fari wanda har yawa ya yi mata saboda bleaching.

Chewin gum ne abakinta tana taunarsa yana ƙara ƙara ras-ƙara ras,alamar za ta yi rashin mutunci kenan .
Bata sha wahalar gane gidansu Ammar ba don rabonta da zuwa shekara shida kenan,kallon gidan ta ke tana ya mutsa fuskarta,taja trolley ɗinta tana wani yauƙi da yanga kamar mutanen gidan suna kallonta.

Hanan tana sama tana hango ta,da sauri ta sauko don ba ta son Ammi tasan abinda zai faru don wallahi ba za ta bari wannan matar ta shigo musu gida ba,suna cikin farin cikinsu ta kawo musu baƙin ciki.

"Ke makira ina zaki"?.

Hanan ta faɗi hakan tana ɗaga mata gira tare da tare hanya.

Wani banzan kallo Sakinat ta yi mata ta cire gilashinta tana kallonta ta ƙasan glass ɗin, sannan ta ce"Hmm Hanno ki ke ko wa?to ma dai ko me ye sunanki?,ko wannan siririyar bafulata na bata isa ta ce za ta hanani shiga wannan ruɓaɓɓan gidanba wanda ko albarkacin fenti ba ya samu.

Idanun Hanan suka yi jawur jin zagin rashin mutuncin da Sakinat ta ke musu,da sauri ta nuna Sakinat da hannu ta ce"Hmm da ba asan asalin balbela ba da sai ta ce daga misra ta ke,ke kin manta gidan na ki uban ko albarkacin siminti bana tunanin ya samu"?.

"kuma kinga gidannan kaf babu siriri sai wannan makauniyar uwar ta ki wacce har ta mutu bata gani saboda baƙin cikinki dana wannan baƙin basa muden uban na ki,kuma kaf gidan na mu babu wanda ya fito ba ta hanya ta halak ba,wani kuwa sai da a kayi cikinsa sannan aka yi aure. . .


Cikin matsanancin fushi Sakinat ta kaiwa Hanan wani mari,Hanan ta shafa wajen da hannunta ta ce"ko yanzu Sakinat na fiki cin ribar zance tunda gashi har kinyi mari saboda fusata,amman fa baki mari banza ba don ba a marin wannan ƙyaƙyawar fuskar tawa a zauna lafiya ko mijinki ne kuwa ballan tana ma ke."

wani mari Hanan ta kaiwa Sakinat wanda sai da yasa ta riƙe hannun ƙofar shiga farlon,wata shaƙa Sakinat ta kaiwa Hanan,ta kama maƙogoron ta Hanan ta kama kararin mutuwa,Ammi ta fito za ta gidan barka ta hango abinda ya ke faruwa.

Da sauri ta ƙaraso tana rabasu tana mamakin ƙarfin hali irin na Sakinat,sa ƙer Ammi ta ɓanɓare Hanan ta ƙwanta luf a hannun Ammi kamar ba ta numfashi.

Sakinat tayo kan Ammi za ta haɗasu duka,suka jiyo sallama Ammi na kallon tsinanniyar shigar da Sakinat ta yi wai a matsayin matar Aure matar ɗanta tilo.

Amir ne da matarsa har da ƴaƴansa biyu,sosai sukayi mamakin ganin Sakinat a gidansu Ammar don sun san takun saƙar da ke tsakaninsu.

Amir ya ce"Ammi lfy me ya samu Hanan ɗin?wani abu ne ya same ta?."

gaba ki ɗaya ya tambayeta,Ammi ta shaida masa duk abinda ta gani a lokacin da tazo,bata gama ƙarasawa ba me gayya me aiki ya fito yana sanye da kayan motsa jiki don bai san abinda ya ke faruwa ba,yana zuwa Sakinat ta saki kuka ta faɗa jikinsa kamar ƴar yarinya.
*** *** ***

A wajen mahaifin Fahima ya faɗi baya motsi,ƴan patrol suka zo wucewa suka hango ƴan daban nan suna Ɗaukar Fahima,da sauri suka zo wajen suna zuwa suka arce da gudu amman an kama guda ɗaya.

Aka kai su Fahima asibiti aka fara yi musu taimakon gaggawa,sai dai mahaifin Fahima har yanzu bai farfaɗo ba amman Fahima ta farfaɗo.



Allah sai kun fara comments zan fara yin sa da yawa.




*Miss green ce*
*🌈DARASI!!🌈*


BOOK 1

✨Rabiatu Bashir
Ummu maher(miss green)🍀💚


*@Wattpad link*

https://www.wattpad.com/user/Rabiatu333?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_campaign=invitefriends


*@Arewa book link*

https://arewabooks.com/chapter?id=62a48949772e179ad6e54443


*SIRRINKI👂🏻*

Kada ki bari kishin mijinki ya kaiki ga halaka,ki yi kishi na sunnah wayo da dabara,yawan kishi yana kaimu ga halaka ƙarshe kuma kibar mijin saboda kishi.
-----------------------------
08/09


. . . . .har yanzu mahaifina bai farfaƊo daga suman da ya yi ba,sai dai yana numfashi,hankali na ya tashi sosai don likitoci sun faɗamin Mu biyu aka kawo mu ni da mahaifina,kuma tunda aka kawo mu ƴan sintirin da suka kawo mu sune suke biyan kuɗin.



Amma tana gidan goggo mahaifiyarta sai faɗa ta ke mata na rashin mutuncin da ke yi,gashi yanzu daga ni har mahaifina babu mu babu labarinmu,sharce hawaye ta yi da majina ta ce"wallahi Goggo ni fa ban san yadda a kayi yarinyar na neme ta na rasa ba,daga tura ta talla tun jiya bata dawo ba,idan zubarda kuɗin tallan ta yi ta dawo mana,shi kuma Malam da karan baninsa ya tafi nemo ta,gashi yanzu babu labarinsu su duka".sai ta cigaba da kukanta.


Tun da ta fara maganar Goggo ke yi mata wani banzan kallo,sai da ta gama sannan ta ce"wai ni kuwa Amaturrahman kina da kirki kuwa?"cewa fa ki ka yi wai mahaifinta ya yi karanbani?shi da ƴarsa sai yaƙi fita nemanta saboda sakaci da kuma rashin hankali?,ke irin wannan riƙon na yi miki a rayuwarki?tambayar ki na ke yi?".kamar za ta daki Amma ranar ta yi suna cikin wannan halin ne a kayi sallama a ƙofar gida.


Kallon banza Goggo ta yiwa Amma sannan ta ce"w/kslm waye?".ta ɗauki mayafinta ta leƙa.


Salati ta fara yi tana kiran sunan Allah tana cewa"to shikken Mlm Bashir yanzu zamu taho insha Allah",da sauri ta dawo tana faɗawa Amma wai ƴan sintiri ne jiya suka kai su Fahima da mahaifinta asibiti,kuma tunda safe akaje cen gidan Amma ba a sameta ba,shine Bashir ya ce yasan kina nan gidan.


Bakin Amma bai mutu ba da abinda ya faru da mijinta da ƴar ta ba sai cewa ta yi"Hmm su Bashir an riƙa wajen iya gulma yanzu har yasan nan na taho?".

lokacin har Goggo ta saka hijabi ta ɗakko kuɗi ta ɗaure a bakin zaninta"ta ce to maras tunani idan kin gama gulmar mutane ki tashi mu tafi?wa wiya kawai mara tunani,har a wannan halin da ake ciki bakin ki bai mutu ba".
*** *** ***

abin mamaki Sakinat tana fara kuka hankalin Ammar ya tashi,ya kalli Khalisat da ke jikin Mahaifiyarsa tana kuka ya daka mata wata uwar tsawa ya ce"shut up!ki yiwa mutane shiru munafuka wato daman bakya son matata ko?to wallahi ko waye zai ƙi matata ko waye wallahi tallahi saina rabu dashi".ya faɗi hakan cikin yaran fillanci ya riƙe hannun Sakinat suka yi wuce warsu,Sakinat harda wani la fewa ajikin Mijinta tana yiwa su Ammi gwalo.

Ni kuwa na ce oh Sakinat kamar abin arziƙi haɗa ɗa da uwa,Duniya ina zaki damu😭.ya Allah ka haɗa mu da surukan arziƙi Amin.


Sororo Ammi ta yi tana kallon bayan ɗanta Ammar,shi kuma tasa ƙaddarar kenan mace,jiya i yanzu yana tare da ƙanwarsa suna hira kamar abin arziƙi,amman yau daga zuwan matarsa har komai ya watse.

Wasu zafafan hawaye ne ya fara zubowa Ammi a ƙwarmin idanunta, bata san sanda Khalisat ta saka hannu ta fara share mata hawaye ba,ita ma Khalisat ɗin kuka ta ke na tausayin kansu"Ammi ki yi haƙuri don Allah kinji,komai ya yi farko yana da ƙarshe kada ki saka wannan abin a ranki kinji?".rungume junansu sukayi suna tausayin kansu dana Ammar.


Har sun manta da tsayuwar Amir sai da sukaji yana cewa"haƙiƙa Sakinat ba ƙaramar butulu ba ce da ta manta,da duk abin arziƙin da ki ka yi mata ta butulce miki,ta zaɓi taci miki mutunci ta kassara miki rayuwaɓ,ta zaɓi hanyar musguna miki ta hanyar mallake miki ɗanki,amman babu komai aƙwai Allah."

Matar Amir ma har kuka ta yi don ganin abinda ya faru,tana yawan ji a littafin hausa da sauran kafofi yadda ƴaƴa suke wulaƙanta iyayensu, amman bata taɓa gani da idanun ta ba sai yau.


a ranar Sakinat ta saka mijinta a gaba kamar mayya suka tafi Abuja,shi kuwa Amir saboda haushi daman alokacin ya tafi gida,saboda takaicin hali irin na Ammar ace ka rasa wanda zaka ƙunta tawa a rayuwarka sai mahaifiyarka wacce tasha wahala a rayuwarta don rayuwarka ta ginu?gaskiya abin aƙwai lauje cikin naɗi.
Ranar gidan Ammi kamar ana zaman makoki,gidan shiru don ɗan wannan zuwan da Ammar ya yi komai sun ƙara shaƙuwa sosai,ranar kusan raba dare Ammi da Khaisat sukayi suna kaiwa Allah kukansu ta hanyar yin nafilfilu.




Abin mamaki ranar Amma ta saka rigima wai mu koma gida alhalin har yanzu mahaifina bai farfaɗo ba,aranar na sake tabbatar da rashin tausayin Amma,Goggo ce tace mata idan ta gaji a yini ɗayan da ta yi,to ta tafi gida ita za tayi jinyar sa tunda shima ɗanta ne,jin wannan da Amma ta yi yasa ta zauna amman ba don ranta yaso ba don biyunnan da ta yi bata yi sana'a ba abin yana matuƙar damun ta sosai.


Hmm kuji fa rashin tausayi irin na wasu matan,mijinki yana ƙwance bashi da lafiya,mijin da ki ke saka ran samun aljanna ta ƙarƙashinsa amman ace kina nuna masa rashin tausayi haka?😭.



Innalillahi wa inna ilaihi raji'un.

A ranar likitoci sukayi bincike wai mahaifina ya. . . .



Yasin idan kuna comments da yawa zan ƙara yawan tyiping oh.




*Miss green ce
*🌈DARASI!!🌈*


BOOK 1

✨Rabiatu Bashir
Ummu maher(miss green)🍀💚


*@Wattpad link*

https://www.wattpad.com/user/Rabiatu333?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_campaign=invitefriends


*@Arewa book link*

https://arewabooks.com/chapter?id=62a48949772e179ad6e54443


*SIRRINKI👂🏻*
Ki yawaita yiwa ƴaƴanki addu'ar ƙwanciya bacci yin hakan zai tsaresu daga dukkanin sharri.
--------------------------------
10/11


A ranar likitoci suka yi bin cike suka gano mahaifina ya kamu da ciwon ɓarin jiki,kuma suka rubuta magani da allurai masu tsada wai saboda idan aka yi mishi zai samu reliep kuma idan yana samin kulawa zai warke baki ɗaya,magani da allura shine ya tashi dubu sittin da biyar,kai tsaye Amma ta ce wai mu tafi gida ba sai anyi masa ba,wataran idan Allah ya kawo ayi aikin.


Hankali na dana Inna ya tashi sosa ta fashe da kuka tana cewa"oh Allah sarki Abu kin bani amanar Ɗanki yanzu gashi na kasa riƘewa",,sai ta fashe da wani kuka mai cin rai.
Fahima tana gefe itama tana wani irin kuka wanda harda amai sai da tayi kamar ance mahaifin ta ya rasu ne.




Ƙwanci tashi asarar mai rai yanzu watan Baba na huɗu da samun matsalar ɓarin jiki wataran ma har yamma baya samun abincin da zai ci,ya rame ya zama wani kamar tsoho ɗan shekara sittin abin dai gwanin ban tausayi.


Rannan na fita talla ina tafiya ina hawaye bana ganin gaba na ballan tana baya na,kawai sai ga wata mota ta yi saurin yin ribas don ashe ina tsakiyar hanya kuma motar tana ta yimin horn amman ban sani ba.


A hankali na cikin motar ya fito yana cewa"haba beauty ya zaki fito kan hanya kina tafiya bakya kallon hanya,me ya yi zafi haka shi ba wuta ba?".

a hankali nima na kallesa hawaye yana zuba a idanuna nace"yi haƙuri ban gani ba ne".na faɗi hakan cikin ƙaguwa don na matsu in siyar in koma in ga Baba na.
Handcachep ya ɗakko sai naji kawai hannayensa yana gogemin idanuna,cikin sanyayyar murya na ce"na gode".

"Dont mentioned beauty".

kallonsa na yi don ban san me yace ba,ya fuskanci hakan don haka ya ce"nan gaba ki dinga kula da hanya kinji don ke haryanzu girl ce".


da ɗan sauri na wuce ina ƴan dariya don rabon da inyi dariya har na manta,amman ban san abinda ya sakani dariya yau ba,ammn ni dai nasan tunda na kallesa naji wani abu ya tsaya azuciyata ko meye hakan oho".


Biyoni ya yi ya ajjemin kuɗi da yawa akan farantin sanman yace"idan kinje gida ki yiwa almajirai sadaka".kamar bazan amsa ba ammn dai na daure na amsa don tuno da masifar Amma idan na koma gida.
Abuja


Sai da Ammar ya ƙarasa hutunsa a Abuja sannan ya koma Tunesia don ƙarasa aikinsa,Sakinat kuwa kamar ta zuba ruwa a ƙasa tasha don tsabar farin cikin ta raba ɗa da uwa,Sakin duniyar nawa ma take baki ɗaya wataran mutuwa zamuyi.


Tana zaune tana waya tana cewa"am gaskiya yakamata kazo don tun jiya general ya koma,kuma kasanshi Ɗan ra'ayi ne ba ko da yaushe muke kasan cewa ba,don ɗan ra'ayi ne kuma gaskiya ina buƙatar zuwanka,ta faɗi hakan cikin shagwaɓa,a ɗaya ɓangaren kome aka oho?tace oky sai na jika ta kashe wayar tana ƴar dariya.


Sai kuma ta gimtse fuska tana cewa"aikin banza ko ta yaya ma mutum zai samu ciki oho".


duk abinda ta ke faɗa Raliya tana jin ta mai yi mata aikin sashenta tace"Hajiya na gama aikin nawa in tafi gida ne"?.


Ai wata Uwar ashar Sakinat ta ƙundu mawa Raliya ta ce"gidan uwarki zakije da zakizo ki tsayamin akaina munafuka shegiya ƴar talakawa,kuma wallahi ina fatan ko kinji me nake cewa kika nemi tona min asiri wallahi sai na saka an ɓatar ɓin dake".


tana faɗar hakan ta yi gaba abinta,Raliya ta bita da idanu,tasha kama Sakinat tana kawo maza amman har yau bata taɓa ganin fuskar wanda ya ke zuwa ɗin ba ballan tana ma ta bada shaida.

Ko wadda ta turo ta don ta ɗaukar mata rahoto amman har yau bata fara ɗauka ba don Sakinat ta iya takun ta sosai.




Kuyi haƙuri bani da lfy ne👏🏻.



*miss green ce*
*🌈DARASI!!🌈*


BOOK 1

✨Rabiatu Bashir
Ummu maher(miss green)🍀💚


*@Wattpad link*

https://www.wattpad.com/user/Rabiatu333?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_campaign=invitefriends


*@Arewa book link*

https://arewabooks.com/chapter?id=62a48949772e179ad6e54443


*SIRRINKI👂🏻*
Ki guji ha intar mijinki wajen fita ba tare da ya sani ba,Allah ya tsaremu da cin wuta Amin.
------------------------------
12/13

. . . .Ina zuwa gida na miƙawa Amma cinikin duka harda ɗoriyar kuɗin da wannan bawan Allah n ya bani,murna harda rawa Amma ta farayi ni kuwa kallonta kawai na ke yi ta ɗoramin talla na ɗari biyar,na kawo mata kusan dubu uku amman bata nemi ba asi ba,sai nice na ce"Amma wannan kuɗin baki tambayeni

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment