Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

JARUMA YAZILA
Littafi na daya
Na Abdul'aziz sani madakin gini
Created and design by:- Shuraih Usman
Publishing shuraih Usman
From http://shuraih.waphall.com
.
A wani zamani
can baya mai tsawo da ya shude a kasar kisra
an yi wani karamin kauye mai suna himsarul
aswad ya wanzu a yammacin birnin kisra
kuma shi ne gari na karshe wanda yayi iyaka
da birnin rum. mutanen birnin himsarul aswad
manomane wadanda suka sami albarkacin
kasa domin agaba daya garuruwan dake kar
kashin birnin kisra babu inda ake da arzikin
noma kamar himsarul aswad acikin wadannan
kauye akwai wani mutum da ake kira hukairu
wanda asalinsa dan uwan hakimin garinne
amma saboda bambancin ra'ayi da halayyarsu
sai hukairu yahakura dazama tare dan uwansa
hakimi yakoma daji inda yayi gidansa kusa da
gonarsa yaci gabada rayuwa a wajen tare da
matarsa guda daya jal wacce akekira humaira
shidai hakimin kauyen himsarul aswad wanda
ake kira da suna barzuk yakasance azzalumi
kuma make taci mai danne hakkin talakawa
kamar yadda sarkin kisra ya zamo na wannan
lokaci dalilin dayasa kenan ma yadade akan
mulkin yana tayin abinda yakeso
Hukairu da barzuk sun kasance hassan da
usaini kuma suna matukar kama da junansu tamkar
antsaga kara wani abin mamaki shine matansuma
yan'uwan junane kuma suma hassana da usainane.
Sunan matar barzuk nuzaira. Humaira da nuzaira sun
shaku da juna ainun kuma har aka yimusu aure basu
rabuba tunda agidadaya suke zaune lokacan da
hukairu da humaira zasuyi hijira subar cikin kauyen
himsarul aswad da kyar hukaira da nuzaira suka rabu
domin kankame junayi suka fashe da.matsanancin
kuka A wannan lokaci shima Hukairu kuka yake koda
yakama. Humaira yana kokarin banbareta daga jikin
yar uwarta nuzaira saita dubeshi alokacinda Fuskarta
ta jike sharkaf da hawaye tace "yakai mijina saboda
me zaka rabani da yar uwata alhalin tunda aka
haifemu Bamu taba rabuwaba Nikam da dai ka
rabamu gwara ka barnina zauna anan gidan koda
kuwa zan zama baiwar sune. ". Sa 'adda hukairu yaji
wannan batu saiya dada kamuwa da tausayin
Humaira "yace yake matata ki sani cewa ba a
sonraina zan raba ki da 'yar uwarkiba, sai domin
mugayen halayen mijinta Nassey ke magana Tabbas
bazan iyaci gaba da kallon irin rashin imani da yake
yiwa talakawaba tunda banida IKon Hanashi. Ni a
rayuwata bantaba marin wani mutumba bare ma
muyi kace nace amma shi dan uwannan nawa ba a
kwana ba kwai sai yasa ankewa wani hannu kokafa.
Sannan yana kwacewa mutane dukiyarsu ko matansu
ya maishesu bayinsu. Kituna cewa ahalin yanzu kina
da ciki tsawon wata hudu yaza ayina tafi nabarki
acikin wannan hali alhalin ina son nakula da lafiyarki
da kaina kuma naga abin dazaki haifa. " Sa adda
Hukairu yazo nan azancensa sai hukaira ta kara fashe
da matsanancin kuka da kyar tayi shiru sannan tace
yakai mijina kasani cewa itama 'yar uwata nuzaira a
halin yanzu tana. Dauke da juna biyu tsawon watanni
hudu dai dai da nawa. Ita haihuwa abuce mai hadarin
gasKe. Zan iya rasa rayuwa yayin haihuwar itama zata
iya zata iya rasa rayuwarta saboda haka bana son
rabuwa da 'yar uwata awannan lokaci, zan so naga
ranar da zata haihu. Don haka ina rokonka daka barni
na zauna tare da ita har izuwa ranar haihuwarta"
Har Hukairu ya budi zaice
wani abu sai nuzaira ta tari numfashinsa ta
dubi.humaira taceyake 'yar uwata kada ki guji mijinki
saboda ni domin shima ba shi da kowa face ke, idan
babu ke akusa dashi zai iyashiga mugun hali. Ina son
ki bishikutafi tare, kada kidamu dani naayimiki
alkawarin komai rintsi bazan haihu ba sai agabanki."
Koda jin wannanbatu sai farinciki ya lullube humaira
takara kamkame nuzaira tafashe da kuka. Haka dai ta
hakura sukayi bankwana suka rabu. Tun da hukairu
da humaira suka koma daji basu kara ganin
mutumba daga cikin Himsarul Aswad saboda sunyi
nesa da garin kimanin tafiyar sa'a bakwai, saidai suna
ganin tafiyar fatake. Wani iko na allah yanzu Hukairu
da Humaira sunsami tsawon wata hudu A wannan
daji inda shi dakansa yagina musu wani narkeken
gida. Harda garken dabbobinsu dasuke kiwo da
rumbu na ajiye kayan amfanin gona amma ko sau
daya 'yamfashi. Ko 'yan sumame basu taba kawo
musu hariba. Dalilikuwa shine akwai layar sihiri da
wani boka yabashi. Wadda ya binneta a tsakiyar
gidansa. Duk wani mugu idan yazo gidan bazai
ganshiba koda daranane tsaka. A ranar da cikin
Humaira yacika wata takwas ne laulayi yayi mata
yawa har ya zamana takasa yin komai. Ka wai saita
zauna. A tsakar gidan tana kallon hukairu alokacin da
yake baiwa dabbobi acikin garkensu. Koda ta dan
jima tana kallonsu sai idanunta suka ciko da kwalla,
Hawaye ya fara zuba. Yayin da Hukairu juyo yaga
halin da take ciki sai hankalinsa ya dugunzuma yabar
garken da sauri yazo gareta ya tsuguna ya rike
hannunta yace matata ina dalilin kukannan naki shin
jikin kine yake ciwo. Kokuwa ninayi miki
badaidaiba ?"Lokacinda humaira taji wannan
tambayar sai ta gyadakai tace Ba wani abubane yasa
kaga ina zubar da hawaye ba face tunanin cewa
abune mawuyaci na sake ganin ranar dani kaina zanyi
I rin wannan aiki dakakeyi yanzu domin ina ji ajikina
abune mawuyaci na rayu daga hadarin wannan ciki
danake dauke dashi." Kodajin haka sai Hukairu yayi
murmushi yace. Ki daina wannan tunanin naki kisani
dawowatanan bisa umarnin bokanane domin ya
tabbatarmin dacewa idan kika haihu acikin gari
zamurasa abinda zaki haifa kuma zamurasa duk
abinda muka mallaka. Saboda a shekarar daki
haihune za ayi mugun fari da cututtuka acikin garin
amma mu damuke anan wannan annoba bazata
shafemuba. Koda jin haka sai Humaira tayi
murmushi cikin karfin hali tace "idan zancenka ya
tabbata haka ina fatan "yar uwata nuzaira tazo ta
haihu tare dani domin kada annobar ta shafi abinda
zata haifa." Hukairu yayi ajiyar zuciya yace "nima ina
fatn haKan tafaru duk da cewa nasan halin "yar
uwarki macece maicika alkawari. Lailai zata zonan ta
haihu tare dake cikin kowane hali. Da gawannan rana
hukairu yaci gaba da kulada humaira har cikinta ya
tsufa sosai harma ranar da nakudarta tazo. A wannan
ranane hankalin hukairu ya dugunzuma ainun domin
basu da makota bare yasamo mace wadda zata karbi
aikin ungozoma. Amma dayake dama can Yasami
cikakken bayani a wajen wata tsohuwar mace
tunkafin subaro cikin gari sai yayi sauri ya shigar da
Humaira cikin daki ya kwantar da ita akan shimfida ya
shiga taimakamata. A wannan lokacine hadari
yagangamo aka fara walkiya da tsawa kafin ajima
ruwan sama ya kece kamar da bakin kwarya kuma
asannane humaira tafara kwalla ihu sakamakon
nakudar data zomata. Duk da cewa Humaira nacikin
tsananin shan wahala duk sanda ta kwala ihu tayi
shiru saita kuma kirawo sunan "yar uwarta nuzaira.
Al'amarin dayayi matukar dugunzuma hankalin
Hukairu kenan domin yana tsoron cewa idan nuzaira
bata zoba har bayan haihuwar Humaira zata iya shiga
cikin wani mugun halin dazata zamo sanadin
salwantar Hankalinta ko rayuwarta.
Kwazam bazato ba
tsammani sai hukairu yajiyo sukuwar doki a wajen
gidansa kuma adai dai lokacinne kan jaririn yafito
daga jikin humaira. Namfa Hukairu yarude yarasa
abinda zaiyi shin zai rabu da humairane. Ya ruga
waje
yagano ko nu zairace tazo. Kokuwa zai tsayane har sai
yaga humaira ta haihu lafiya. Yana cikin wasu
wasinne
yaji humaira ta damki hannunsa da kyar, tace ya kai
mijina maza ka ruga izuwa.kofar gida domin ina ji
ajikina 'yar uwata ce ta iso kuma na tabbata kodai ta
haihu kukuma tana cikin i rin halin da nake ciki. Karka
damu dani zan iya kara sa haihu wa da kaina. Cikin
matukar damuwa hukairu yace menene tabbacin
hakan? Humaira tace shinna taba maka karyane?
Hukairu ya girgi za kai yace baki tababa kuma ina
gasgata maganarki kamar yadda nake gasgaga
maganar ma haifiyata marigayiya. " Koda gama
maganar sai ya mike da sauri yaruga da gudu yana
fita
ya arba da keken doki. Kwance acikin keken dokin
nuzairace kaca-kaca da jinin haihuwa gefe kuma ga
jaririn data haifa ko motsi bayayi. Itama a kwai a
lamun dogon suma tayi cikin razani hukairu ya ruga
gareka ya dauki jaririn ya girgiza shi kuma ya kara shi
akunnuwansa yaji ko numfashi bayayi. Sai tausayi
yakamashi. Adai dai wannan lokacinne kuma yajiyo
kukan jarirai acan dakin da ya baro humaira nantake
nuzaira tabude idanunta tayi arba da gawar jaririnta
data haifa kuma taga hukairu tsaye akanta. Saita fa
she da kukan bakin ciki amma da ta jiyo kukan jariri
adakin humaira. Sai ta fashe da dariya cikin hanzari
subiyun suka ruga izuwa cikin gidan. Da shigarsu
cikin
dakin da humaira take kwance saisukayi arba 'yan ta
gwayen jariranta mata. Guda biyu suna ta tsala
kuka.kuma ita humaira ta kasance cikin Koshin lafiya.
Fuskarta cike da murmushi. Koda humaira taga
nuzaira babu juna biyu kuma babu komai ahannunta
sai ta yunkura donta mike tsaye. Nuzaira ta ruga
gareta da cikin hanzari ta kwanta tace "kwanta ki huta
tukunna yake yar uwata kiyi sani cewa kin zubarda
jini
mai yawa ajikinki. Kafin nuzaira ta rufe bakinta
humaira tatari numfa shinta tace ina abinda kika
haifa
nuzaira ta kalli hukairu takasa cewa komai sai
humaira tayi murmushi tace "yake 'yar uwata ai baki
da damuwa tunda 'ya'ya biyu na haifa saiki dauki
daya
ki barmin daya. " Koda jin wannan batu sai nuzaira ta
cika da tsananin mamaki ta dubi hukairu shima sai
yayi murmushi yace "yar uwarki tayi gaskiya domin
abinda ta haifa nakine koda kuwa guda dayane zan
iya
amincewa ta mallaka mikishi domin zakiyimishi
komai kamar yadda zata yi mishi da kanta. Nuzaira
tayi murmushi ta dauki daya Jaririyar ta zauna ta
shayar da ita. Bayan dukkaninsu sunnu tsu sai
hukairu
ya dubi nuzaira cikin tsananin damuwa yace yaya akai
kika baro mijinki kika tahonan ba tare da yasaniba
shinkin tabbatar baisa abiyo bayan kiba? Nuzaira ta
gyada kai tace aidama kun kafi ranar naku dar nayi
kyaky kyawan shiri domin na hada baki da kuyangina
tuni suntanadi wancen keken dokin danazo dashi.
Acan bayan gari kuma acikin dare muka saci jiki
muka
sulale muka bargarin banyarda wani daga cikin masu
tsaro yagammuba kuma suna dorani akan keken
dokin na umarcesu dasu share sahun keken dokin
don
kada aga alamar komai kafinna baro gida kuwa
nabarwa mijina wasikar cewa nibazan haihuba acikin
garinsa acikin irin wannan lokaci nafari da annoba
tun
satin jiya gari ya hargitse da wadannan matsaloli.
Saboda haka ninasan cewa mijina bazai biyo
sawunaba
idan yaga wannan wasika. Nikam na zabi na karasa.
Sauran rayuwata tare da ku anan har izuwa karshen
rayuwata. Sa'adda nuzaira tazo nan azancenta sai
hukairu ya jawo kwauran numfashi ya ajiye sannan
yace yake Nuzara kiyi sani nasan halin mijinki fiye da
kowa aduniya. Tabbas sai yabiyo bayanki danhaka
zamanki anan abune mai hadarin gaske. Aduniya
babu
abinda mijinki yakeso sama da samun magaji. Hanka
linsa bazaitaba kwanciyaba idan baiga abinda kika
haifaba idan yazo nan ya iske.cewa abin dakika haifa
ya mutu. Zai iya hallakamu nida matata da dukkan
abida muka haifa. Yazama dole ki dauki wannan
jaririya guda daya ki tafi da ita kikoma wajen mijinki.
Nayi imani cewa a halin yanzu ya baro gari yataho
nemanki. Idan baki tashi kin tafi tafi yanzuba
kintareshi ahanya. Tabbas zaizo har nan ya riskemu
abinda nake gudu ya faru sai ya faru.
Kodajin wannan batu sai
nuzaira ta fashe da kukan bakinciki saboda jin cewa
zata sake rabuwa da yar uwarta. Cikin tsananin
damuwa Humaira ta dubi hukairu tace yakai mijina
shin gidannan na dauke da sihirin mugu bai isa yagan
shiba? To ai koda dan uwanka Barzuk yazo.nan bazai
ga gidan ba kenan. Hukairu ya gyada kai yace ai
shima yanaa da irin wannan sihirin nawa kuma yana
da makarinsa domin tunmuna yara boka saibur
yabamu shi sa'adda mai haifimmu yakaimu gurinsa.
Nuzaira bamu da ishashshan lokaci dan haka dole ne
ki tashi kiyi shirin gaggawa ki koma cikin gari. " Koda
jin sai Nuzaira da Humaira suka fa she da kukan
bakin ciki kamar bazasu dainaba nan dai hukairu da
humaira suka raka nuzaira wajen keken dokinta suka
bata abinci da kayan marmari. Nuzaira ta goya
jaririyar da akabata ta rungume humaira suka sake
fashewa da kukan bakinciki suka kamkame juna. Da
kyar suka rabu har nuzaira ta sa kafarta guda cikin
keken dokin saita waigo ta dubi hukairu tace. "Yakai
mijin 'yar uwata shin baka tsammanin wannan farin
da annoba bazai shafi wannan jaririyar da kuka
baniba". Hukairu yayi murmushi yace karki damu ba
abinda zaisameta kuma ina tabbatar miki nan da
kwanaki kadan wannan fari da annuba zasu kau. "
Nuzaira tace wana suna zan sawa ya rinyar?" Caraf
humaira tace "kisamata suna YAZILA mukuma zamu
sawa tamu suna DABIRA. " Nantake nuzaira ta shiga
cikin keken dokinta ta kada linzamin da wakanta tayi
gaba. A can birnin Himsarul Aswad kuwa
lokacin.Hadari ya gangamo a ka fara walkiya da tsa
warnan sai Barzuk yatafi dakin nuzaira domin ya ga
halin da take ciki saboda sanin lokacin haihuwarta
yayi a ko yaushe zata iya haihuwa. Da shigar Barzuk
cikin haraba bankaren nuzaira saiyaga abin mamaki.
Bakomai yaganiba face.dukkanin kuyan ginta akwakw
kwance suna ta sharar barci al halin lokacin baccinsu
bayyiba. Sannan ya ji warin banju yacika gurin gaba
daya. Cikin firgici Barzuk ya toshe hancinsa ya ruga
izuwa cikin dakin Nuzaira dazuwa yaga dakin wayam
babu Nuzaira babu alamarta. Cikin tsananin fushi ya
fita daga dakin da sauri ya kwalawa Dakarunsa kira
nan da nan kwa dakarun suka rugo gare shi sai ya
dubesu yace "maza kuje ku shirya hawa za afita
neman matata lallai anzo an saceta batare da bata
lokaciba kuwa barzuk yayi gagarumar shigar yaki mai
matukar kwarjini. Daban tsoro ya hauwani farin
ingarman doki ya jagoranci dakaru dakaru dari biyu
suka fice daga cikin birnin. Babban abinda yatayarwa
dasu barzuk hankali shine kokadan ba suga sawon da
wakaiba bare su san hanyar dayakamata subi. Koda
ganin haka sai barzuk yaja linzamin dokinsa ya tsaya
cak, suma dakarun nasa sai suka tsaya a bayansa.
Nantake barzuk ya dauko madubin tSafinsa ya
shafashi da hannunsa take barzuk yagano hanyar da
yakamata yabi amma bisa mamaki saiya kasa ganin
hoton komai acikin madubin tsafi face hanya kawai
al'amarin daya matukar bashi mamaki kenana domin
asaninsa gaba daya kasar kisra inbanda sarki Daksur
babu wanda ya fishi karfin sihirin tsafi wanda zai i ya
hada kafada da shi sai dai dan uwansa Hukairu.
Hukairu kuwa ya dade dayin hijira gabarin gari gaba
daya to wane ha tsabibinne haka yazo har cikin garin
sa ya sace masa mata. Nan dai barzuk yakada
linzamin dokinsa. Yayi gaba, dakaru suka bishi abaya
duu aguje sai da su barzuk suka shafe tafiyar wajen
sa'a hudu sannan suka hango wani keken doki yanufo
garesu aguJe cikin mamaki su barzuk suka yi tur jiya
kuma suka zare maka mansu suna jiran isowar keken
dokin.
Tun daga nesa kadan
barzuk ya shaida keken dokin yagane na matar sane
Nuzaira dan haka sai jikinsa yayi sanyi ya maida ta
kofinsa cikin kube ya sauko da gakan dokinsa ya ruga
izuwa keken dokin. A gabansa keken dokin yayi turjiya
yayi arba da matarshi Nuzaira rike da linzamin
dawakan fuskarta cike da annuri kuma tana dauke da
goyan jariri abayanta al'amarinda ya matukar bashi
mamaki kenana. Cikin tsananin farin ciki ya kama
nuzaira ya sauketa dagakan keken dokin ya
rungumeta sannan ya karbi jaririn dake baynta ya
kura mata ido yana dariyar farin ciki daga can kuma
ya turbune fuskarsa ya dubi nuzaira yace "bani
labarinki yake matata wanene yazo ya saceki har cikin
gidana, kuma ai na kika haifi wannan tsaleliyar
jaririya mai kama dani ainun haka?" Sa'adda Nuzaira
taji wannan batu saitayi murmushi tace "yakai mijina
kayi sani bansan meya faruba ina cikin turakata sai
naji anrufe mini fuska an shaka mini banju ahanci. "
Kawai sai farkawa nayi naganni a tsakiyar dokar daji
kuma babu kowa a kusa dani sai wasu mutane masu
shigar bakaken kaya kuma duk sun rufe fuskokinsu i
danunsu kadai ake gani suna rike da muggan
makamai. Adadin mutanen yakai dubu. Babban
cikinsu ne kawai da Jajayen tufafi bisa jan doki koda
naga wadannan mutane sai na firgita abin da jawo
tasowar nakudata kenan cikin kankanin lokaci na haifi
wannan jaririyar dake hannunka acikin keken doki
shugaban wa dannan mutanen ya matso kusa dani
yakura min ido sannan ya bushe dadariya. Yace yake
matar babban abokin gabata kisani cewa kinyi babbar
sa'a da yazamana cewa kina dauke da juna biyu da
tuni na hallakaki amma saboda ganin kina dauke da
juna biyu shiyasa muka fasa dalili kuwa aduniya bana
tausayin kowa sai mace mai juna biyu. Narasa matata
ne alokacin da take nakudar haihuwar dana kuma
tamutu tabarmin dan, har yau har gobe ina tausayin
dan saboda ba shi da uwa. Bisa wannan hujjane zan
kyaleki kikoma wajen mijinki wannan karankan kun
tsallake harina amma baza ku tsallake na gababa.
Koda gama fadin haka sai ya doki daya daaga cikin da
wakan keken dokina take suka zabura sukayi tatafiya
dani har na hangoku akan hanya wannan shine iyakar
abin da zan iya tunawa ya faru gareni ya kai mijina.
Lokacin da nuzaira tazo nan azancenta sai barzuk
yacika da tsananin mamaki kuma yakamu da matukar
farin ciki yace tabbas babban makiyin mune sarki
Raihan yaturo aka daukeki domin ya dauki fansar yar
uwarsa da na kashe amma bai sami na saraba lallai
yazama wajibi naje na sanar wa sarki daksur wannan
al'amarin domin mu dauki matakin gaggawa saboda
nayi mamakin yadda abokin gabarmu ya shigo har
cikin kasarmu ya sace min mata batare da
munsaniba yake matata ki sani yau shekara goma
dayin auranmu amma bamu taba samun haihuwaba
sai yanzu lallai acikin farin ciki nake mara misal tuwa
dan haka yanzu da ganan birnin kisra zamu wuce
nanunawa sarki wannan kyakykyawar 'ya" dakika
haifa mini kuma na gaya masa maganar makiyammu
Sarki raihan koda gama fadin haka sai barzuk ya
shiga cikin keken dokin ya zauna kusa da nuzaira
sannan daya daga cikin yaransa ya hau gaban keken
dokin ya fara sarrafa dawakan aka cigaba da tafiya
aka nufi hanyar da ta nufi birnin sin.
Tunda aka fara wannan tafiya zuciyar nuzaira ta fara
bugawa da karfi domin ta tabbatar da cewa da zarar
sun isa gaban sarki Daksar asirinta ya tonu bisa
karyar data shirgawa mijinta cewa yaran sarki
raihanne suka saceta domin shi sarki Daksur ka sur
gumin ma tsafine wanda ka iya ganin duk abinda
yafaru tun gabannin su isa fadar tasa har aka iso
cikin kisra hankalin Nuzaira atashe yake bata da
sukuni al'amarin dayasa barzuk ya dubeta kenan yace
yake matata lafiya naga kamar kina cikin damuwa?
Tunda muka fara wannan tafiya bakice uffanba kuma
babu walwala da annu shuwa afuskarki koda jin haka
sai nuzaira tayi murmushi tace yakai mijina kasani
cewa ban taba shiga fadar sarki Daksur ba da
girmanaba saboda tun ina yarinya wata rana sa'adda
mahaifina ya je dani naga an sare kan wani mutun a
gabana saina firgita ainun na tsandara ihu tun daga
wannan rana kullun sai nayi mafarkin wannan abu
ina firgita acikin barcina saida ma haifina yanaimi
taimako awajen bokansa sannan na daina wannan
mugun mafarki yanzu dakace zamu fadar sarki
daksur sai mafarkin ya fadomin arai saboda haka
nidai bana son shiga fadar sarki Daksur ka samomin
masauki agari kafin mu isa fadar. Sa'adda Nuzaira
tazo nan azancenta sai barzuk ya bushe dadariya yace
kadaki damu yake matata lallai bazanje fadar sarki
batare dake.
Kamar yadda barzuk yayi alkawari haka abin ya
kasance wato da shigarsu birnin kisra sai ya kai
nuzaira cikin wani ka sai taccen gida irin na sarakai
wan da ke dauke da komai na jin dadin duniya harda
baruri da kuyangu masu hidima. Al'amarin daya
matukar bata mamaki kenan domin bata ga lokacin
da
aka biya kudin hayar gidanba kuma da zuwansu kofar
gidan ta ga masu gadin gidan sun tsube kasa sun
kwashi gaisuwa har nuzaira ta bude baki zata
tambaye
shi batun wannan gida sai yace saboda me zakiyi
mamakin mallakar wannan gida agareni ? Shin kin
manta ina daya daga cikin makusan tan sarki?
Nuzaira
tayi murmushi ta ce bana mamakin mallakar wannan
gida agareka amma ina mamakin dalilin da ya hana
ka
sanar dani labarinsa Barzuk yayi murmushi yace
sonake na shamma cekine nabaki mamaki kinga
kenana zamu tare a sabon gida nuzaira tace yanzu
idan katare anan birnin ya zakayi da wakilcin sarki a
kauyen Himsarul Aswad? Barzuk yayi dariya yace aiba
tarewa zanyi ananba kece dai zaki tare a cikin birnin
nan domin na fison 'yarmu tataso da wayewa ta zama
cikakkiyar 'yar birni mai waye war kai in yaso duk kar
shen mako nazo nata fi daku tare kubi yun.
Bayan barzuk ya nunawa Nuzaira bangarenta a cikin
wannan gida harta shiga ciki ta kwanta tana hutawa
kuyangi suka fara mata shidima sai barzuk yayi shiri
yata fi izuwa fadar sarki daksur.
Fadace kasaitacciya wadda aka kawatata da kayan
alatu
iri iri tamkar aljannar duniya sarki daksur na zaune
bisa wata kerarriyar kara gar mulki ta ka saita fadawa
sun kewaye shi a tsakiyar fadar ga wasu tsala tsalan
'yammata sai tikar rawa suke cikin mummunar shiga
mai baiyana tsaraicinsu.
A kaida duk sa'adda sarki ke kallon wadannan
'yammata yayin da suke tikar rawa yana dariya da
murmushi amma a yau sai sarki ya tur bune fuska
babu annuri atare da shi koka dan kuma tun da ya
fito
fadar haka ya ka sance cikin rahin walwala da sukuni
kallo daya mutum zai masa yasan yana cikin tsananin
bacin rai.
Al amarin daya matukar dugun zuma hankalin
fadawa
kenan domin sun sancewa fushin sarki ba karamin ta
shin hankali bane agaresu gaba daya. A na cikin
wannan haline akaga hakimi barzuk ya shigo fadar
cikin farinciki kamar wanda aka yiwa albishir din
mulkin duniya cikin sauri har da hardewa barzuk ya
isa gaban sarki Daksur ya zube kasa ya kwashi
gaisuwa
ya dago kai domin yayiwa sarki baya nin abin farin
cikin da ya sameshi sai sarki yayi farat ya tashi tsaye
kawai sai ya dubi barzuk yace kabiyoni izuwa cikin
dakin gani ina son magana dakai a sirrance. Koda
gama fadin haka sai sarki Daksur yanu fi dakin gani
nanfa Barzuk ya bishi da sauri aka bar fa dawa da
jama'ar gari a zazzaune sun yi tsurutsuru da
idanuwansu suna mamakin abin da ke faruwa. Yayin
da sarki Daksur da Barzuk suka shiga dakin gani sai
sarki ya tsaya a tsaye maimakon ya zauna ya juyo
suka fuskanci juna shida Barzuk yace kazone kayi
mini
aibishir bisa cewa matarka ta haifi "ya" mace koba
hakaba? Cikin muryar rawar murya burzak yace
hakane ya shugabana Daksur yace tokasani kasani
wannan "ya" data haifa ba "yar ka bace "yar" dan
uwanka ce Hukairu amma ita matarka "da" na miji ta
haifa kuma a mace yazo duniya hakika matarka ta yau
dareka kuma karya ta shiryama domin ka jaddada
magana ta yanzu zan nuna maka duk abubuwan da
suka faru azahiri. Kagani da ida nuwanka. Gama fadin
hakan ke da wuya sai sarki yayi nuni da hannunsa
izuwa ga jikin bango take hoton al'amarin suka rinka
gudana tun lokacin da Nuzaira tayiwa 'yar uwarta
Humaira alkawarin cewa lallai awajenta zata haihu
har
lokacin da aka bata jariri yarnan koda ganin wannan
al'amari sai barzuk ya kwarara uban i hu cikin
tsananin bakin ciki jikinsa gaba daya ya kama tsuma
ka wai sai ya zare ta kofi ya juya da nufin yaje ya sare
kan Nuzaira amma sai sarki daksur ya daka masa
tsawa ya tsaya cak ya juya ya durkusa bisa gui
wowinsa a gaban sarki daksur ya mayar ka takofinsa
bisa kubenta ya sunku yar da kansa kasa alokacin da
hawayen ta kaici yake zubo masa yace ya shugabana
yanzu me ya kamata nayi? Sarki dak sur yayi ajiyar
numfa shi sannan yace ya kai Barzuk kayi sani bisa
bin
ciken da nayi idan muka ka bar matarka da wannan
"ya da aka bata wannan fari da annoba da muke fama
dasu a gari zasu kare nan da sati biyu kacal gari zaiyi
lafiya amma inda masifar take shine wannan jaririyar
da matrka ta zo da ita idan har ta girma zama gawur
tacciyar jaruma kuma maya kiya fiye da sarkin
yakinmu sadauki Hauzar bin Mausus duk yakin da
muka taro sai ta sami nasara amma fa duk sanda ta
san sirrin tsafina mun

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5

1 Comments On JARUMA YAZILA
avatar
gaskiya

1 year ago

Reply

Inajin dadinaa sosai

Please Login or Register in order to submit comment