Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hada jini da mutum sai kaga wani abu ya
zamo iri daya da nasa bare kuma ni da 'yar
uwata mun kasance tagwaye ai dole ne asami
kama ni da ita kamar yadda kika bani labari cewa
tamkar an tsaga kara muke. "
Nuzaira tayi ajiyar zuciya sannan tace, "nidai na
umarceki da kada ki kuskura kice zaki ce zakiyi
wannan ta fiya izuwa birnin misra kuma ina mai
gargadinki da kada ki kuskura kice zaki je kiyiwa
sarkin yaki zaihar wani abu, domin kina tabashi
mijina da sarki daksur zasu gane cewa na sanar
dake sirrin rayuwarki don haka komai zai
iyafaruwa a gareni. Yake yazila ki tuna cewa nice
na shayar dake harkika girma kika zama mutum,
ki tuna nice naci kashinki, na sha fitsarinki, kuma
nice na sha wahalar renunki idan kika bari su
sarki daksur suka cutar dani lallai kinci amanata
kuma kinci amanar zumuncin dake tsakanina da
mahaifiyarki."
Koda gama wannan jawabi sai nuzaira tayi shiru
bata kara cewa komai ba , sannan ta mike tsaye
ta fice daga cikin dakin ta bar jaruma yazila a
zaune cikin tsananin damuwa, gami da tunani
mai zurfi.Haka dai yazila taci gaba da sake-sake acikin
zuciyarta ta kulla wancan ta kwance wancen har
dare yaraba ya zamana taka sayin barci sai kai
kawo kawai takeyi acikin dakin nata tana zarya.
Bayan tayi dogon nazari da tunani akan abinda
zai fishsheta sai taje ta dakko takadda da
alkalami ta rubuta wata wasika ta ajiye a
karkashin matashin kanta sannan ta cire kayan
jikinta ta sanya wadansu bakaken sulke na yaki
ta dauki makamanta na yaki ta soke a jikinta nan
take tayi girgiza bace bata bayyana ako ina ba
sai a kofar gidan sarkin yaki zaihar da baiyanarta
sai taga masu gadi a tsaitsaye suna kan aikinsu
kai tsaye jaruma yazila ta durfafosu koda masu
gadin suka hangota sai suka cika da tsananin
mamaki bisa ganinta a cikin wannan lokaci na
tsawon dare cikin ladabi da biyayya masu gadin
suka risina suka gaisheta yazila ta dubeshi a
fusace tace kubude mini kofa da salama na shiga
dfomin naga mai gidanku idan kuma kuka yi
gardama yanzun nan takobina zata sha jininku !“.
Koda jin wannan batu sai jikin masu gadin ya
kama karkarwa cikin firgita sukayi sauri suka
bude mata kofar ta kunna kai ciki da shigar yazila
cikin gidan sai tazare takobinta taci gaba da
kutsa kai tana leka cikin dakunan gidan domin
taga inda sarkin yaki zaihar yake. Karar zare
takobin yazila daga cikin kubbenta ne yasa
sadauki zaihar ya bude idanunsa alokacin da
yake kwance tare da matarsa acikin turakarsa
dama bai dade da kwanciya ba bisa bata lokaci
da yayi wajen bincike a hallarar tsafinsa. A cikin
binciken da yayi ya ga wata gagarumar masifa
dake shirin afko masa amma sai ya kasa gane
irin masifar da kuma lokacin dazata zo masa abin
da ya saya kasa barci ke nan ya kwanta kawai
yana tunani cikin fargaba. Koda zaihar yaji karar
zare wannan takobi sai yayi wuf ya mike daga
kan gadonsa yayi sauri yasanya kayan yakinsa
sannan ya zare tasa takobin ya fita waje yana
neman wanda ya shigo masa gida cikin wannan
tsohon dare.
Lokacin da jaruma yazila ta shigo cikin wani
katon falo na gidan wanda babu komai acikinsa
face shimfidar jan kilishi mai taushi da kujeru na
alfarma sai tayi kicibus ! Da sarki yaki zaihar
tsaye ruke da takobi a wannan lokaci falon a
haskake yake dahasken fitilu tazarar dake
tsakanin zaihar da yazila bata wuce taku asirin
ba.
Koda zaihar ya ga ashe yazila ce ta shigo masa
gida acikin wannan dare sai ya cika da tsananin
mamaki kuma yaji ajikinsa cewa lallai ba lafiya ba
akwai wani abin daya faru da dai dai ba saboda
haka saiya tsaya a inda yake ya dubeta yace
yake halifata mene ne ya kawoki gidana a
wannan dare?“ Yazila ta dubi zaihar a fusace
tace ,“ nazo na dauki fansar mahaifina dakakashe
ne ya kai babban azzalumi !“
Cikin matukar mamaki zaihar ya dakawa yazila
tsawa yace ,” wannan kuma wacce irin maganar
banza kikeyi ? Shin ke ba yar mai girma barzuk
bace ? Yaza ayi kice na kashe mahaifinki alhalin
barzuk na nan araye ?”.
Dajin haka sai hawaye ya zubowa yazila tace ”
Kayi tunani izuwa shekaru goma sha takwas baya
lokacin da kabi bayan hukairu dan uwan barzuk
sa adda ya gudu tare da iyalinsa izuwa birnin
misra daf da kofar birnin misra kuka fafata yaki
kai da matarsa humaira tan goye da jaririyarta to
ka sani cewa wannan jaririr yar uwata ce mun
kasance tagyaye nida ita kuma hukairu ne ya
haifemu ita kuwa nuzaira abin data haifa mutuwa
yayi sai humaira taba ta daya daga cikin
tagyayen data haifa kuma ni ce jaririyar da aka
bata kagake nan hukairu shine mahaifina ba
barzuk ? Lallai mahaifina ka kashe , babu
makawa sai na dauki fansa a kanka kuma a
yanzu ”.
Sa adda yazila tazo nan a zancenta sai sarkin
yaki zaihar ya bushe da mahaukaciyar dariya. Ya
ce ” yake yarinya karyarki tasha karya. Ba a
zama wane a banza. Kafin na sami wannan
matsayi na sarkin yakin birnin kisra sai dana taka
mukamai masu daraja da yawa kuma sai dana
sha bakar wahala. Duk abin da kike takama da
shi a yanzu na mallakeshi tun kafin kizo duniya
saboda haka yanzu ga fili ga mai doki idan kina
ganin zaki iya daukar fansar mahaifinki ki jarraba
ki gani ina tabbatar miki da cewa kamar yadda na
kashe mahaifinki haka kema zanka sheki !”.
Kafin zaihar ya gama wannan jawabi tuni zuciyar
yazila ta fara tafarfasa kawai sai ta dag takobinta
sama ta ruga gareshi shima sai ya daga tasa
sama ya rugo gareta suna haduwa kowanne su
ya kaiwa dan uwansa mugun sara kowannensu
ya kare saran da takobinsa da takobinsa tara
tsatsin wuta ya fantsama izuwa kas. Nan fa suka
rugunzume da azababben yaki ya zamana cewa
suna kaiwa juna sara da suka cikin tsananin zafin
nama juriya da bajinta.
Wohoho ! Idan sabon hannu da tsohon hannu
akahadu a gumurzu dolene aga tsagwaran
jarumta t ban al'ajabi. Ita yazila tana ta kama da
kuruciya gami da sadaukan taka ta zamani
shikuwa zaihar yana ta kama da kwarewa da
sanin makama ne. Da dabarun yaki irin na
tsofaffin sadaukai inda aka sami babban
bambanci shine, ita yazila tafi zaihar juriya da
dadewa ana gumurzu, shi kuma yafi ta zafin
nama.
Sai da aka shafe rabin sa'a ana wannan gumurzu
dayansu bai sami na sarar komai ba, ya zamana
cewa dauki ba dadin da sukeyi yasa gaba daya
hadiman gidan sun rugo izuwa falon da suke
fafatawa a dimauce. Itama matar zaihar saita
farka daga bacci a firgice ta ruga izuwa dakin da
danta ke barci, wani karamin yaro dan shekara
hudu kawai, saita sungumi yaron a kirjinta taruga
izuwa falon da ake gumurzu tsakanin yazila da
zaihar.
Dazuwa sai ta iskesu cikin masifaffen artabu.
Gaba daya hadiman gidan sun ra kabe a tsorace
suna kallon abin dake faruwa. Nan fa itama
matar zaihar ta kasa yin komai saita tsaya ka
wai tana kallon fafatawar cikin tsananin tsoro da
fargaba da mamaki bisa ganin wacce ke gumurzu
da mijinta.
Saboda zafin naman zaihar sai ya shammaci
yazila ya yanketa acinya. Kafin tayi wani yunkuri
ya sake yankarta a damtsen hannunta na hagu.
Bisa dole yazila tayi alkafira da baya ta koma
nesa kadan da shi ta durkushe kasa bisa
guiwowinta a lokacin da ta dafe raunikan jikinta
biyu cikin jin zugi da radadi.
Koda taga jini na zuba saita fusata ainun kuma
tayi sauri. Ta daure raunikan da wani tsumma
dake daure a kugunta. Ka wai sai ta mike tsaye
ta sake zare wata takobin a kuibin cinyarta ta
hagu ya zamana cewa ta hada takubba biyu
ahannunta.
Koda ganin haka sai shima zaihar yaciro wani
gatari dake rataye a bayansa ya hada da ta kobin
hannunsa ya fuskanceta. Kawai sai yazila ta rugo
gareshi suka sake kacamewa da sabon
azababben yaki amma awannan karon sai yazila
ta sauya salon fadan ya zamana cewa tana tsalle
tana alkafira a kasa da sama. Nan da nan kuwa
ta ruda zaihar, bai ankara ba sai yaji ta dan kara
masa sara acinyarsa. Take wajen ya dare jini yayi
tsartuwa. Zaihar ya rankwala uban ihu yatafi da
baya taga-taga ya fadi
Koda matar zaihar taga abinnda aka yiwa mijinta
zaihar sai itama tarusa ihu ta fashe da kuka.
Yazila ta kara rugowa da gudu izuwa kan zaihar
ta ci gaba da kaimai sara da suka cikin iya zafin
namanta bata yarda ta bashi damar da zai daure
raunin nasaba. Nan fa jini ya cigaba da zuba
daga cinyar zaihar har jiri yafara dibarsa amma
saboda naci da juriya irinta 'YAN MAZAN JIYA sai
yaci gaba da yakin a haka. Ya yin da zai har ya
fus kanci cewa idan akaci gaba da wannan
gumurzun a haka har izuwa wani lokaci mai
tsawo zai iya gala baita yafadi saka makon jinin
dake zuba a kafarsa sabo da haka sai ya fara
amfani da karfin sihirinsa yana watsawa yazila
mugayen abubuwa kamar; masu, wuta, kibiyoyi
da sauransu. Bisa mamaki sai yaga tsafin baya
tasiri ajikinta, domin karfin sihirin nasu yazo daya
duk abin da ya watsa mata sai itama ta watso
masa irinsu sulalata juna. Al'amarin daya
dugunzuma hankalin zaihar kenan ya tabbatar da
cewa bashi da wata mafita face yayi amfani da
iyakar karfin dmtsensa da kwarewarsa ta yaki.
Bisa dole yakara ZAGE DAMTSE suka cigaba da
bakin gumurzun, yazamana cewa ta shi hankalin
komai da kowa dake cikin falon. Sai da suka
shafe sa'a biyu suna wannan gumurzu ya
zamana cewa kowannensu yasake samun nasarar
yiwa abokin gwamisa rauni. Zai har ya sami
nasarar saranta a kirji, ita kuma ta sami nasarar
sokarsa agefen kirjinsa na dama alokaci guda duk
subiyun suka kwala ihu suka ja da baya taga taga
kamar zasu fadi amma sai suka sake rugowa
suka kacame da a zababben yaki.
Hakika idan mutun ya ga irin wannan juriya, naci
da jarumta irin ta zaihar da yazila dolene ya
jinjina musu ya tabbatar da cewa sun cika
zaratan sadauki ababan misali. Bayan sun dada
kwarmazuwa bisa hadawa da naushi da bugun
juna sai suka jigata ainun ya zamana cewa da
kyarma suke kaiwa juna hari.
Duk wannan abu dake faruwa matar zaihar na
rakabe a gefe daya rungume da danta ta na
kallongumurzu cikin ta shin hankali kuma tana
kuka.
A na cikin wannan fafatawar ne duksu biyun sukA
yiwa juna wani irin mugun naushi a fuskokinsu
har jini yai tsartuwa bakunansu suka zube kasa
kafin yazila tamike tsaye sai zaihar yayi sauri ya
zaro wata wuka siririya mai kaifi da atsini ya
wurgawa yazila wutar da tafi tsananin gudu zata
cake ta cafi wukar ta maida ita inda aka jehota
nan take tsinin wukar ya lume acikin goshin
zaihar nan take zaihar ya sulale kasa matacce
koda ganin abin daya faru sai matar zaihar ta
kwala ihu ta rugo kan gawar mijinta ta ajiye
danta a gefe daya ta rungume gawar tana kuka
sauran hadiman gidan kuwa sai suka firgice suka
kama guje guje suna ficewa daga cikin gidan
gaba daya jaruma yazila ta yaka kafafunta da
kyar ta nufi inda matar zaihar take koda ganin
haka sai matar zaihar ta dago kai ta dubeta ba
tare da tsoron komai ba tace.” Yake dirkar birnin
kisra ma za ki kasaro ki kasheni ni da dana
domin na huta da wannan abin takaicin da kika
bar mini ban ga amfanin rayuwarmu a duniya tun
da kin yanke mana farin cikin rabamuda
masoyinmu. ”.
Yazila tayi shiru bta ce komai ba har ta iso kan
gawar zaihar kawai saitasa hannunta ta zare
wannan wukar wacce ta lumamai acikin goshin
zaihar sannan ta dubi matarsa a lokacin da
hawaye ya zubo mata. Tace ina bukatar alokacin
wannan wuka domin da sonki san cewa bazan
kashe kiba kuma bazawara kamar yadda uwata
humaira ta zama bazawara kuma inason wannan
da naki ya zama maraya kamar yadda ni da yar
uwata muka zama marayu ina son ki isar da
sakona ga sarki daksur cewa ni “jaruma yazila ”
na kashe sarkin yaki zaihar bisa sanin cewa shi
ne ya kashe mahaifina na gaskiya bisa umarninsa
don haka ya saurari ranar da zanzo daukar fansa
a kansa ki sanar dashi cewa na san sirrin layar
da suka rataya mini a wuya tun ina jaririya kuma
na tafi inda za ayi cire mini layar koda gama
wannan furuci sai jaruma yazila ya goge jinin
dake jikin wannan wukar daga jikinsa ta daura a
kugunta kawai sai ta juya ta fite daga cikin
gidana tana tafe tana tangadi ita kuwa matar
zaihar sai ta bita da kallo kawai cikin tsananin
mamaki bisa jin abubuwa data zaiyano mata a
matsayin sako sarki daksur.
* * *
Al'amarin hadiman gidan zaihar kuwa, dasu da
masu gadin gidan Bayan yazila ta sami nasarar
kashe maigidansu Sai suka ruga da gudu izuwa
gidan sarki daksur suka isar da labarin abinda ya
faru ga man yan hadiman gidan. Ai kuwa acikin
wannan dare labari ya riski sarki Daksur. Cikin
tsananin firgici da dimauta sarki daksur yamike
zumbur yayi shigar yaki ya jagoranci dakaru dubu
a shirin da kansa acikin dare suka bazama
neman jaruma yazila acikin birnin kisra amma sai
da suka duba ko ina basu gantaba.
Shikuwa hakimi barzuk yajin labarin abin da
yafaru sai ya ruga izuwa dakin yazila a fusace
rike da takobi. Da shigarsa cikin dakin sai ya iske
matarsa nuzaira atsaye rike da wasika tana karan
tawa tana zubar da hawaye cikin fushi barzuk ya
fisge ta kardar ya karanta jawabin dake cikinta
kamar haka.
YAke ummata ki gafarceni bisa abinda zan
aikata. Kiyi sani cewa bani da wani zabi face na
aikata hakan kuma ki gayawa mijinki da sarki
daksur abinda ya faru da sarkin yaki zaihar suma
yananan tafe garesu nan da wani lokaci a ko
yaushe kuma ina gargadinsu akan idan suka taba
lafiyarki nima saina taba lafiyar dukkanin
danginsu, sai na tabbatar da cewa na share
dukkanin zuri'arsu daga doron kasa. Idan har sun
matsu. Da son ganina su nemeni acan birnin
misra..........."
Koda barzuk yazo nan akara tun wasikar sai
zuciyarsa ta kama ta farfasa kamar zata kone.
Saboda tsananin fushi da bakin ciki ka wai sai
yasa hannu ya fyade nuzaira ta fadi kasa
sumammiya. Nan take ya kwalawa wasu hadi
mansa kira yace su dauki nuzaira su kaita can
babban kurkuku na kasar suce asamata sarka
atsareta har sai ranar daya nemeta. Nan take
kuwa wadannan hadiman suka cika wannan
umarni. Bayan hadiman sun tafi da nuzaira sai
yafita da sauri ya hau dokinsa yatafi gidan sarki
da zuwansa kuwa ya iske sarki daksur ya dawo
daga neman gimbiya yazila bai gantaba. Yana
zaune a fada shi kadai cikin tsananin fushi
tamkar zai kona gidan sarauta gaba daya barzuk
ya zube kasa gaban sarki daksur ya sunkui da
kansa kas cikin tsananin ladabi alokacin da gaba
daya jikinsa ke karkarwa don tsoro kada fushin
sarki ya kare a kansa
Bazato ba tsammani sai barzuk ya bushe da ma
haukaci yar dariya. Al'amarin daya matukar bashi
mamaki ke nan ya dago kai a tsorace yana
kallonsa.
Sarki daksur ya turbune fuska sannan yace ,
"hakika matarka taso ta watsa mana dukkan
shirimmu ta tona mana asiri bisa sakacinka na
kula da sa ido akanta. Hakika in ba don kayi
mata hukunci ba da kanka kasa ankaita kurkuku
da tuni kai da ita duk nayi muku hukuncin kisa.
Bisa bincike da nayi a halin yanzu na gano cewa
tuni jaruma yazila tayi nisa da barin wannan
birnin wannan kasa tamu saura tafiyar kwana
daya da yini daya jal ! Ta isa kofar birnin misra.
Jaruma yazila tana da matukar karfin sihirin tsafi
don haka bani da wa dansu hadiman aljanu da
zan turasu su hallakata kafin ta isa cikin birnin
misra. A cikin binciken da na yi na gano cewa
idan ta shiga cikin birnin misra bazata sami
nasarar samun abinda taje nemaba. Kuma zata
sha tsananin wahala wacce zata iya zama
sanadin ajalinta. A kwai wani lokaci da zaizo
muyi yakin karshe da sarki raihan na birnin misra
a wannan yaki ne zamu sami nasara akansa
mukama birnin nasa gaba daya a sannanne zamu
shiga har cikin birnin mukama yazila da
mahaifiyarta humaira sannan mu binciko duk inda
'yar uwarta take dabira itama mu hallakata. "
Sa'adda sarki daksur yazo nan azancenta sai
farin ciki ya lullube barzuk bai san sa'adda ya
bushe da dariyar murnaba. Nan fa duk su biyun
suka ci gaba da kyakyata dariyar kamar bazasu
dainaba.
A dai-dai lokacinne matar zaihar ta shigo cikin
fadar ita kadai rungume da danta tana zubar da
hawaye. Batare da fargabar komaiba ta iso har
gaban sarki Daksur ta risina ta kwashi gaisuwa
sannan ta zaiyana musu sakon da jaruma yazila
tabata.
Koda matar zaihar ta gama jawabi sai jikin sarki
daksur ya kama tsuma. Nan da nan zufa ta karyo
masa. Zuciyarsa ta kama bugawa da karfi kamar
zata fado kasa cikin tsananin zafin nama ya zare
ta kobinsa ya fille kan matar zaihar ta saki dan
dake hannunta ya cafeshi da hannu daya.
Gangar. Jikin matar zaihar ya sulale kasa
alokacin da dan nata ya fashe da kuka. Sarki
daksur ya yunkura zai sare kan dan sai barzuk
yace, "kayi masa rai ya shugabana ai kankanin
yarone"Sarki daksur ya sauke takobinsa kasa sannan ya
bushe da dariyar mugunta ya killata barzuk
wannan yaro ya cafe yace dashi katafida shi
izuwa gidanka ka raineshi ya taso a cikina
bayinka masu yi maka hidima hakika
mahaifiyarsa ta cuceshi data sayi ajlinta a lokacin
da yafi bukatarta a rayuwa tayi kuskure babba da
tazo gabanmu da mugun lafazi domin itace mace
ta farko datata ba zuwa gabana ta fadi mugun
sako. “ Koda gama wannan ne abin daya faru
sarki barzuk ya nufi hanyar fita daga fadar rike da
wannan yaro yana ta tsala kuka bai fasaba. “
Wannan shi ne abin daya faru a birnin kisra
tsakanin jaruma yazila dasu sarki daksur bayan
ta sami labarin asalinta. Acan birnin misra kuwa
tun kimanin shekaru sha takwas da suka gabata
wato a lokacin da sarkin yaki zaihar ya kashe
hukairu a gaban matarsa humaira saita ruga da
gudu izuwa kan gawar mijinta a lokacin da masu
gadin kofar birnin suka rugo izuwa wajen suka.
Kewayeta suna kallonta kawai cikin alamun
tausayawa domin sun fahimchi cewa mijinta aka
kashe. Kuma ga jaririya a goye a bayanta. Bayan
humaira ta dade tana kuka har ta gaji sai
wadannan dakaru suka haka kabari suka binne
gawar hukairu a gabanta sannan suka shigar da
ita mata jagora har izuwa cikin birnin misra daya
daga cikin yayi masa bayanin duk abin daya faru
ga humaira a gaban idanunsa bayan wannan
badakare ya gama jawabi sai sarki raihan ya dubi
humaira cikin alamun tausayawa yace wannan
bakuwa ina mai yi miki marhaba izuwa wannan
birnin. Namu mai albarka wato birnin misra kiyi
sani ma abota addinin musulunci ne kuma bisa
tafarkin addininmu bamu yarda da zalunci ba
saboda haka muna son kibamu labarinki iyakar
gaskiya bisa abin dake tsakanin da wancan
mutumin wanda ya biyoku har izuwa kofar
wannan birnin namu ya kashe mijinki kuma igudu
idan har kina da gaskiya akansa da iznin ubangiji
duak inda ya gudu zamu tura a kamoshi domin
ayi masa hukunci dai dai da laifin da ya aikata
kafin sannan muna son muji sunanki da kuma
sunan garin da kika fito. “
Lokacin da sarki raihan yazo nan a zancensa sai
humaira ta sunkai da kanta kas kamar bazatace
komai ba kuma taji tsoroya shigeta bisa sanin irin
tsananin gabar dake tsakanin birnin kisra dabirnin
misra amma data tuna cewa sarki raihan yace shi
mai adalci ne sai taji dukkanin tsoro ya kau daga
zuciyarta nan take ta baiyana masa sunanta da
kuma kasardata fito. Koda jin haka sai gaba
dayan jikin sarki Raihan yakama tsuma,
idanuwansa suka kada, zuciyar sa takama
tafarfasa kamar zata kone bisa jin sunan kasar
mutanen dasuka zamo sana diyar mutuwar 'yar
uwarsa guda daya jal a duniya wadda yake
matukar kauna fiye da komai a rayuwarsa.
Cikin tsananin fushi sarki raihan ya kai hannunsa
izuwa kan kuben takobinsa da nufin ya zare
takobin ya sare kan humaira amma sai ya kasa
kawai sai hawaye ya zubo masa ya kasa yin
komai ya kura mata ido kawai. Daga can sai yayi
ajiyar numfashi sannan yace, "yake Humaira
hakika kinci albarkacin adalci irinna ma'abota
addinin musulunci amma da tuni yanzu nasare
kanki da takobina. Kiyi sani cewa na tsani
kasarku, natsani mutanen kasarku domin sarkin
kasarku ne ya kashemin 'yar uwata wadda na
fiso fiye da komai aduniya a ranar da mukafara
yaki. Haka kuma sarkinku ya tsani mutanena ya
tsani addininmu. A duk sa'adda wani daga cikin
jama'armu yaje kasar ku koda da zummar fatauci
ne sai yasa a kamashi ayimasa. Kisan gilla. Ki
sani cewa mu bazamu kashekiba bisa tarbiyyar
addininmu, amma akwai sharadi mai girma a
tsakaninmu daku. Ba zamu yarda kuzauna a
kasarmuba face kun karbi addininmu idan kina
ganin bazaki iya karbar addininmu to kijuya ki
tafi izuwa wata kasar daban inda zasu iya
karbarki".
Ya yin da sarki raihan yazo nan a zancensa sai
Humaira ta fa she da kuka sannan tace, "ya kai
wannan sarki mai adalci, kayi sani cewa babu
wata kasa dazan iya zuwa na tsira daga sharrin
sarkinmu da mijin "yar uwata face wannan kasa
taka. A iya abin da na fa himta yanzu a zuwana
kasarka nagane cewa wannan addinin naku
addinine na a dalci gami da tausayi da jin kai,
domin da farko dakarun da suke gadin kofar
birnin sun kamani da karfin tsiya zasu kawoni
gabanka amma dasu fahimci halin dana ke ciki
suka an kashe min mijina kuma suka ganni da
goyon Jaririyata sai suka tausaya min suka tsaya
suka binne gawar mijina sannan suka taho dani
izuwa nan fadar ka cikin salama ba tare da cin
zarafinaba ko su taba lafiyata ba. Kaima da aka
kawoka gabana da kaji cewar na fito ne daga
birnin kisra sai zuciyarka tayi baki ka harzuka
kamar zaka ka sheni amma saboda tausayi da
adalci irin naka sai kakasa kasheni. Tabbas iya
wannan karamci dana gani daga gareku ya isa na
gamsu cewa wannan addinin naku shi ne addinin
da yafi cancanta ga bil'adama a doron kasa.
Saboda haka ni yanzu a shirye nake dana karbi
wannan addini naku mai daraja. "
Koda Humaira tazo nan azancenta sai taji gaba
daya jama'ar fadar sun rude da kabbara kuma
kowa ya kamu da tsananin farin ciki.
Shikuwa sarki rai han baisan sa'adda fuskarsa ta
fadada da murmushi ba. Nan take sarki raihan ya
biyawa kumaira kalmar shahada ta maimaita
sannan ya umarci wani hadimi nasa yace da shi
a kai Humaira cikin gidansa na sarauta abude
mata dakin matarsa marigayiya kuma a bata
sutura da duk abinda take bukata. Nan take kuwa
wannan hadimin ya tafi da Humaira izuwa cikin
gidan sarki ya cika wannan umarni.
Daga wannan rana Humaira ta tsinci kanta a cikin
sabuwar rayuwa mai cike da dumbin farinciki da
kwanciyar hankali, domin babu abinda tanema
tarasa. Haka kuma sarki yasa wata baiwa
masanar addinin musulunci ta dinga koya mata
yadda ake ibada kuma ta dinga karan tar da ita
addinin musulunci.
Humaira taci gaba da renun jaririya dabira tataso
a cikin son addini kawaici, fasa ha da jarumta.
Tsananin kyawun dabira ya dimauta gaba dayan
mutanen birnin misra, don haka tun tana da
shekara bakwai 'ya'yan sarakai da 'ya'yan
attajirai suka rinka zuwa wajen sarki raihan
kamun kafa. Shikuwa sai yarika gaya musu dabira
'yace ta amana awurinsa don haka ba shi da ikon
bayar da ita face ta girma ta zabawa kanta miji.
Lokacin da sarki raihan yaga dabira ta taso
da.matukar basirar daukan karatu da kuma
jarumtaka taban al'ajabi saiya ji ya kauna ceta
ainun tamkar hi ya haifeta. Bisa wannan daliline
yasa yazana cewa kullum sai ya tura a daukota
ta yini a wajensa yana koya mata karatu da
kansa kuma yana koyamata yaki. Hakane yasa
dabira ta shaku ainun da sarki sarki raihan ta
dauka azuciyarta cewa shine mahaifinta, don
haka tana kiransane da "abbanta". Ita kanta
Humaira bata gayawa dabira gaskiyar al'amari ba
domin kada hankalin dabiran ya dugunzuma ta
shiga wani hali. Kai a birnin ma gaba daya in
banda wadanda suka san taihi zuwan Humaira
garin da yawan matasa sun dauka cewa dabira
yar sarki raihan ce ta Cikinsa.
Wani abin mamaki shine, a tsawon wadanan
shekaru har dabira ta cika shekara goma sha
takwas sarki raihan da Humaira basu taba zama
tare ba tsawon dakika dari da sittin. A koda
yaushe duk su biyun suna gudun faruwar hakan
domin gudun kada soyayya ta shiga tsakaninsu.
A binda basu saniba shine sun makara, domin tun
a ranar da sarki raihan ya musuluntadda ita duk
su biyun suka ji suna kaunar juna.
Shidai sarki raihan tun da matarsa ta mutu a
lokacin da tazo haihuwa ya zamana cewa dan
cikin nata ma yarasu sai yaji gaba daya baya sha
awar yin aure a rayuwarsa domin a ganinsa ba
zai taba samun wacce zata maye gurbinta ba.
Tun a sannan ne yayi al'kawari a zuciyarsa cewa
bazai sake soyayya ba.
Ita kuwa humaira a duk sa'adda ta tuno da
tsohon mijinta Hukairu sai taga kamar butulci za
tayi idan ta sake yin wani auran. Abu na biyu
idan ta tuno cewa itafa ba jinin sarauta bace sai
taga babu yadda za ayima sarki raihan ya sota
har ya aureta. Bisa wannan daliline ta dunga
baya-baya da shi ta na tsoron duk wani abu da
zai jawo wata hulda a tsakaninsu duk da cewa
sautari ta kanji begensa yana darsuwa azuciyarta
domin gaba dayan halayensa suna burgeta.
Al'amarin gimbiya dabira kuwa lokacin da ta
shekara goma sha takwas, kyawunta ya kara
bayyana karara a fili fiye da ko yaushe kuma ta
zama gawur tacciyar mayakiya kuma jaruma
wacce babu kamarta akasar gaba daya. Sai sarki
yasa aka bata sarautar sarkin yaki. Tun daga
wannan rana ne dabira ta samu damar rufe
fuskarta da hular karfe, bata cire wannan hula
face tana cikin turakarta amma ko acikin gidan
sarauta idan zata je wajen ma haifiyarta ko wajen
sarki sai tasa hular sai ta shiga wajen nasu
sannan take cire hular saboda yawan kallon da
mutane suka yi mata yayi yawa bama maza ba,
hatta 'yar uwata mata da zarar sun ganta sai
kaga sun kura mata idanu baza su daina kallonta
ba face ta kule.
Allah yayi dabira da tsananin kyawu na dirin
jiki,sannan gashin kanta baki ne sidik ga kyalli da
sheki tamkar madubi ya zubo har kasan
kwankwasonta. Saboda tsananin kyallin ga shin
idan mutum ya tsaya a bayanta sai ya dinga
ganin fuskarsa a cikin gashin.
Dabira nada dara-daran idanu farare soll masu
dauke da digon baki tamkar yankan wuka. Tana
da dogon wuya tamkar na barewa. Kalar fatar
jikinta kuwa bata kasance fara ba ko ja ba, wani
irin launine na musamman wanda ido bazai iya
tantance waba saboda tsananin kyau. Kai a ta
kaice dai babu wani da namiji da zaiyi arba da
jaruma dabira ba tare da ya kamu da tsananin
sonta da begen taba.
Lokacin da samari masu isa suka yi caa ! A kan
neman auren gimbiya Dabira sai ta taka musu
birki tace baza tayi aureba har sai ta

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5

1 Comments On JARUMA YAZILA
avatar
gaskiya

1 year ago

Reply

Inajin dadinaa sosai

Please Login or Register in order to submit comment