Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

SARKIN SARAKAI 1
Littafi na daya 1
Abdulaziz Sani M gini
Made:- Shuraih Usman
Daga:- http://shuraih.waphall.com

SARKIN SARAKAI
Littafi Na Daya (1)
Part A.
.
Ina yima daukacin musulmai murnan zuwan Azumin
watan Ramadan, Allah ya bamu Alkhairan cikinsa
.
Marubucin littafin
Abdul Aziz Sani M/Gini
AA Misau Ke Magana
.
Labari ya isowa AA Misau Cewa..
.
A WANI ZAMANI can baya mai tsawo da ya shude anyi
wani mashahurin sarki a birnin misra mai suna SAHIBUL
HAIRI
Shidai wannan sarki ba a tabayin talakan sarki ba
kamarsa a duniya saboda yawan kyautarsa da taimakon
talakawa
akarshe da talauci ya isheshi sai ya shirya ya tafi wajen
wani boka AWANI DAJI WAI shi HAZARIL DALFUR
a yammacin misra Daga cikin birnin misra zuwa wurin
wannan boka tafiya ce ta s'a biyu kacal sarki Sahibul hairi
bai tafi wannan daji ba sai da dare ya raba kuma saida ya
saci jiki yayi bad da kama ya tafi a kasa ba tare da ya hau
doki ba ko rakumi
Bayan tafiyar sa'a biyu ne dai dai ya iso kofar gidan boka
HADIMUL ASUR
Wanda aka ginashi da zallan itatuwa bisa kan wani godon

dutse faffada mai tsawon gaske
lokacin da sarki Sahibul hairi yazo gaban dutsen sai ya
tsaya yana tunanin hanyar da zaibi ya hau kan dutsen ba
zato ba tsammani sai yaga boka Hadimul Asur ya bayyana
a gabansa yana mai murmushi
hadimul asur yayi sujjada ga sarki Sahibul hairi yace Lale
marhaban da SARKIN SARAKAI na duniya baki daya kaine
sarkin da zaiyi arziki da daukakar da ba a taba yin kamar
su ba nan gaba idan har ka sami nasarar samo abubuwan
da zan gaya maka yanzu
muje zuwa cikin turakata domin mu zanta a tsanake kafin
sarki sahibul hairi yace wani abu tuni boka Hadimun Asur
ya dafa kafadarsa take suka bace bat sai gashi sun
bayyana a cikin turakar boka hadimul asur Wadda akayi
mata ado da fatun manyan dabbobin dawa da
kwarangwal din kawunansu
nan take hadimul asur ya yiwa sarki nuni da wata
shimfida mai taushi shi kuwa sai yaje ya zauna a kai
zamansa keda wuya saiga wata zabgegiyar budurwa ta
fito daga cikin
wani daki dauke da tambulan na ruwan inibi da kofin
zinare a hannu
tun da sarki sahibul hairi yazo duniya bai taba ganin
budurwa mai kuruciya da kyau kamarta ba duk da cewa
sarki sahibul hairi yayi alkawarin cewa ba zai taba yin
aure ba saida yaji yayi sha awar wannan budurwa
budurwar tazo gaban sarki ta tsugunna sannan ta zuba
ruwan inibi a cikin kofin zinare ta mikawa sarki ya karba
kofin yana mai kura mata ido da murmushi
ita kuwa saita sunkuyar da kanta ta fice daga cikin turakar
fitarta keda wuya sai sarki ya bude baki da nufin yayi
magana amma sai boka hadimul asur yai masa nuni da
yayi shiru
yace dashi wannan 'yata ce ita kadai gareni a duniya
kuma babu abinda na ke so sama da ita ka bar batunta
yanzu zamuyi shi nan gaba
ya kai wannan sarki mai daraja kayi sani cewa tuni na san
abindake tafe dakai kuma kamar yadda na gaya maka
cewa bukata zata biya idan harka sami nasarar samo
abinda na umarceka da samowa
Sa'adda boka hadimul asur yazo nan a zancensa sai sarki
ya dubeshi cikin kokwanto da mamaki yace yakai wannan
boka hakika nayi mamakin jin yadda kake bayani tamkar
kasan sirrin xuciyata
amma duk da haka ina so ka fada mini ainihin bukatar da
nazo da ita gareka domin na kara samun natsuwa dakai
koda jin wannan batu sai boka hadimul Asur ya tuntsure
da dariya sannan yace yakai wannan sarki na gani cewa
kwanaki bakwai da suka shude
sarakai bakwai sun aiko maka da wasika A cikin wasikar
sunyi bayanin cewa tunda ka zamo almajiri zasu rinka
taimaka da sadaka domin kada ka dinga zubar da kimar

sarakai a duniya kuma sunyi maka gorin baka da lafiya
tunda baka da aure
lokacin da ka sami wannan sako saibakin ciki ya turnuke
ka har ka shiga cikin turakarka kayita shara kuka a boye
ba wanda ya sani bayan kayi kukanka ka gaji ne kayi
rantsuwa da girman karagar mulkinka cewa
saikafi dukkan sarakunan duniya mulki dukiya da mata to
ka sani cewa idan har kana so ka sami wannan matsayi
dolene ka nemo wadansu 'yan mata guda uku ka aura
mace ta farko utace 'ya ga wata mace wadda duk duniya
babu mai iliminta yanzu ita dai wannan mata tana jin
yare guda dari ba daya haka kuma ta kasance malama a
cikin addinai guda dari ba daya shekarunta dari ba daya
cif-cif kuma ta boye kanta tare da 'yarta a inda babu
wanda ya sani a halin yanzu in banda wannan 'ya tata duk
duniya babu mai iliminta
mace ta biyu babu wanda yafi mahaifinta yawo a duniya
mahaifinta bai mutuba saida ya ziyarci kasashe dari tara
da casa'in da tara inda ya cika dubu da ya sami matsayin
da kake son samu yanxu 'yar wannan mutum yanzu haka
ta ziyarci kasashe dari takwas da sittin a cikin shekaru
bayar kacal baisa taimakon wani Aljani waishi KALBURA a
matsayin abin hawanta
wannan budurwa ta lashi takobin cewa saita ziyarci
kasashe dubu dan cika burin mahaifinta wanda ajali ya
hanashi cikawa duk kasar data ziyarta saita debo irin
kasar da aka gina gidan farko a nahiyar idan ta kammala
tara kasar guda dubu shine zata sami wannan daukakar
budurwata uku itace 'yaga wani mutum wanda yafi kowa
sanin tarihin sarakunan duniya da mulkinsu itama
wannan budurwa mahaifinta ya mutu kuma ta gajeshi A
halin ynx itace kadai tasan adadin sarakan duniya da
tarihin mulkinsu tun daga farko har karshe
wannan budurwa kwakwalwarta kamar littafi yake domin
tarihin a rubuce yake a kanta zata iya baka lbrn shekara
dari baya......
YAKAI WANNAN SARKI kayi sani cewa idan har kana son
kafi dukkanin sarakunan duniya mulki dukiya dolene ka
nemo wadannan yan mata uku ka auresu
sa adda boka Hadimun Asur yazo nan a zancensa sai yayi
shiru ya kurawa sarki idanuwa kawai cikin tsananin
damuwa sarki Sahibul hairi yace yanzu a ina zan ga
wadannan yan mata kuma waye zai iya samo minsu
boka Hadimul Asur yace tambaya ta farko tafi karfina
domin banida amsarta amma tambaya ta biyu itace a
halin yanzu duk duniya babu wanda zai iya samo ma
wadannan yan mata face wani jarumi saurayi kuma
mafarauci wanda ake kira SADAUKI AWAISU
sadauki awaisu na zaune a can nahiyar kasar Hindu a
cikin wani birni da ake kira HALRALI awaisu ya kasance
matsafin gaske kuma yana da wani Aljani wanda ake kira
SARMUDA

aljani sarmuda ya kasance matashi mai karfin gaske
kuma a cuk cikin jama ar aljanun duniya babu kamar sa
a fagen karfin gudu da sauri yayin tafiya a sararin sama
Aljani KALBURA ne kadai ke iya yin rabin tafiyar sa a gudu
sadauki Awaisu bazai taba yarda ya samo maka
wadannan 'yan mata uku ba face ka samo masa 'yarsa
guda daya wata karamar yarinya yar shekara bakwai
ALFILA
WACCE aka saceta a shekaru uku da suka gabata babu irin
neman da sadauki awaisu bai yiwa wannan ya tasa ba
amma ya rasa inda take da yayi bincike a cikin tsafinsa sai
ya gano cewa yarinyar na can hannun wani mashahurin
bokan Aljanu ne a cikin wani gida dake tsakiyar tsibirin
tekun BAHAR ZAILUS
sunan wannan boka SHAMZUBUL AZWAS ba komai bane
yasa bokan ya sace Alfila ba sai don ya kwashe sirrikan
tsafin dake jikinta guda dari tara domin shi yana da guda
dari nasa da kansa idan ya hada da wannan sirrika zai
zamo babu wani matsafi kamarsa a doron kasa
Shamzubul Azwas ba zai iya kwashe wadannan sirrikan
tsafin ba daga jikin Alfila har sai izuwa tsawon shekara
biyar A halin yanzu saura shekara biyu kawai ya kammala
debe sirrikan tsafin su kuwa sirrikan tsafin ainihinsu na
Sadauki awaisu ne duk duniya babu mai irinsu face shi
bayan rasuwar mahaifiyar Alfila da shekara daya sadauki
awaisu ya zuba wadannan sirrikan tsafi guda dari tara a
cikin jikin Alfila domin burinsa a duniya shine ta gajeshi a
fagen tsafi
lokacin da sadauki awaisu ya gano inda aka boye masa
'yarsa sai yayi shiri ya hau kan aljani Sarmula suka durfafi
tsuburin bahar zallus daga birnin Hindu zuwa bahar
zallus tafiyace ta shekara goma sha daya akan rakumi ko
doki amma cikin wata uku aljani sarmuda ya isa can
koda suka sauka a kofar gidan boka shamzubul azwas sai
suka iske cewa gidan an ginashi ne da zallan bakin karfe
kuma bashi da kofa ko taga wacce za a iya bi a shiga
cikinta kuma koda mutun ya shiga gidan ba zai iya kashe
dakarun Aljanun dake ciki ba guda dubu dari wadanda
suka kasance manyan zakwakuran mayaka masutaurin
kai da dakakkiyar zuciya
nan da nan sadauki awaisu da aljani sarmuda sukayi ta
kokarin shiga wannan gida ta hanyar amfani da karfin
sihiri da kyar suka gano wata kofa guda daya wacce
akayita da karfen lu u lu u nan take suka fara kokarin
bude ta da karfin tsiya domin shiga
amma sai abu ya faskara saida suka kwana uku a wajan
suna saran kofar da makamai iri iri amma kofar taki
buduwa
tabbas inda kofar ta bude to sai sunsami nasarar shiga
gidan kuma sai sun kashe dukkan dakarun ciki sun
hallaka boka shamzubul azwas sannan su dauki Yarinya
alfila

Yakai wannan sarki kayi sani cewa bincike ya nuna mini
cewa akwai wani gatari guda daya a duniya wanda zai iya
sare wannan kofa ta gidan boka shamzubul azwas shidai
wannan gatari ya kasance mai girma da nauyin tsiya
domin sai karti sittin sun taru suke iya daga shi sama
kuma anyi shine da zallan lu'u lu'u bincike ya nuna mini
cewa kaikadaine mutumin da zai iya sarrafa wannan
gatari sbd sadaukantakarka tafi ta kowa a wannan zamani
A yanzu haka wannan gatari na can a ajiye a cikin fadar
sarki BARUSA na birnin ASKANDARIYYA cikin mummunan
tsaro Ainihin wannan gatari na sarkin farko ne na kasar
don kowanne sarki zuwa yake ya tarar dashi a matsayin
abin gado kai sbd ganin darajar gatarin ma har takai
cewa mutanen kasar sun camfashi a matsayin indai yana
nan ajiye a cikin gidan sarautarsu to har abada ba za a
cisu da yaki ba bisa wannan dalili ne kullum dare da rana
aka zuba dakaru dubu uku suke gadinsa
wadannan dakaru dubu uku sun kasance karfafa
mayakan kwarai wadanda ake takama dasu a birnin
Askandariyya yakai wannan sarki ya zama wajibi a gareka
kayi shirin yaki ka tafi izuwa birnin domin ka dakko
wannan gatari na sihiri ka dawo gareni sannan na
kimtsaka ka tafi izuwa fadar boka shamzubul azwas don
ka dauki Alfila yar sadauki awaisu idan ka daukota saikazo
da ita nan mu ajiyeta har sai yaje ya samo mana
wadannan yan mata uku wadanda sune bukataka zata
biya
sa adda boka hadimul Asur yazo nan a zancensa sai sarki
sahibul hairi yace to yanzu idan sadauki Awaisu yazo yaga
'yarsa baka tunanin cewa zai iya karbeta da karfin tsiya ba
tare da ya biya muna bukatarmu ba?
KODA jin wannan batu sai boka Hadimun asur ya
tuntsure da dariya sannan yace ai kowa a gidansa sarki ne
ina tabbatar maka da cewa indai kazo da Alfila cikin
wannan gida nawa babu wanda ya isa ya tafi da ita face
da yarda ta
da wannan kalmomi nake maka sallama dan haka sai ka
tafi kayi shirin zuwa fadar sarki Barusa na birnin
Askandariya don dauko gatarin sihiri zan kasance mai
sauraronka a nan
kuma ina yi maka tuni da cewa shima wannan gatarin
sihiri karka barshi a can fadar boka Shamzubul azwas
lallai ka taho da shi nan gareni tare da yarinya Alfila
koda gama fadin wannan batu sai boka hadimul asur ya
sake dafa kafadar sarki sahibul hairi nan take sarki
sahibul hairi ya tsinci kansa a wajen gidan boka hadimul
asur kuma a kasan dogon dutsen nan kawai sai sarki
sahibul hairi ya juya ya tafi ya nufi cikin birnin misra yana
mai tafiya da sauri don ya isa gida kafin fitowar Alfijir
kashe gari da sassafe sarki sahibul hairi ya tura aka
kirawo masa dukkanin fadawaLabarai farko sunyi
tsammanin cewa wani abu zai nema a hannunsu don

haka sai wadannsu suka noke suka ki zuwa da wuri suna
karyar fadin cewa suna nan tafe
koda ganin haka sai sarki ya fusata yace a gaya musu
cewa duk wanda baizo ba a yanzu a bakacin ransa koda
jin haka sai yan majalisar suka rude nan da nan suka iso
fadar suna masu rawar jiki bayan sun hallara sai kowa ya
nutsu yayi shiru baka jin motsin komai a dakin face
sautin numfashi
daga can sai sarki sahibul hairi ya mike tsaye fuskarsa a
murtuke babu alamar fara a Al amarin da ya kara firgita
fadawan ke nan gaba daya suka sunkuyar da kawunansu
kasa don gudun fushinsa sarki yace dasu
''yaku yan majalisa kuyi sani cewa raina ya baci bisa
halaiyarku ta kina da guduna sbd halin da na shiga na
babu wannan ya nuna min cewa babu soyayyar gaskiya a
tsakanina daku kuma kuna tsoron kada ku talauce ne
shiyasa kuke guduna? To ku sani cewa daga yau bana
bukatarkomai daga hannun ku kuma nayi muku Alkawari
cewa ba zan sake neman komai ba a wajenku
kuyi sani cewa ba wani abu bane yasa na taraku a nan ba
sai don na gaya muku cewa zan tafi yaki izuwa birnin
Askandariyya domin dauko gatarin nan na sihiri wanda
suka baiwa kyakkyawan tsaro zanyi amfani da wannan
gatari ne don kawo karshen wannan talauci da nake
famda dashi kunga kuwa idan na rabu da talauci kuma
kun huta da fargabar komai
kuyi sani cewa bayan na sami wannan gatarin kuma zan
wuce izuwa tsibirin zallus inda boka shamzubul azwas
yake domin na dauko wata karamar yarinya wacce ya
saceta shekaru uku da suka gabata wadda ta kasance
yaga babban matsafi sadauki Awasisu
a kalla zan sami shekara guda kafin na kammala wannan
tafiya na dawo sabo da haka yanzu ina son ku zabi wanda
zai rike mini kasa daga cikinku kafin na dawo koda jin
haka sai gaba dayan suka kidime suka haukace nace kowa
na cewa shine zai rike kasar shikuwa sarki sahibul hairi sai
yai shiru ya zuba musu idanu kawai yana nazarinsu ya
fuskanci cewa gaba dayansu babu abin yarda a gareshi
yayi da sarki yaga sun kaure da gardama sai ya daka
musu tsawa nan take suka kame kamar gumaka kowa ya
yi tsit sarki ya kira wani barde dake can kofar shigowa
dakin da suke ciki barden ya rugo da gudu ya zube kasa
gabansa sarki yace da barden maza kaje dakin ajiya ka
debo mini akwatunan karfe iya adadin fadawan nan nawa
barden ya mike da sauri yace an gama ranka ya dade
koda ficewar barden sai cikin yan majalisar nan ya duri
ruwa domin a zatonda suke shi ne sarki zaisa su a cikin
akwatunan ne ya kulle domin akwatunan sn kasance
darma darma baisa wannan daliline jikinsu ya kama
kyarma gaba daya kamar ace kyat su fita da gudu
barden ya dinga shigowa da akwatunan daya bayan daya
yana saukewa da jerawa a waje guda har saida ya gama

tara guda taran koda ya gama ajiye akwatunan sai sarki
ya dubi yan majalisar yace gaba dayanku ku fita su rufe
kofar kuma su tsaya a bakin kofar cikin rawar jiki suka bi
umarni fitarsu keda wuya sai sarki ya dauki kwagirinsa na
sarauta ya saka a cikin daya daga cikin akwatunan bayan
ya bame akwatun saiya yiwa yan majalisar nan izini su
shigo cikin hanzari suka shigo suka tsaitsaya a jere waje
guda sarki ya dubesu a natse yace
yaku yan majalisa kuyi sani cewa kwagirin sarautata na
cikin daya daga cikin akwatunan nan guda tara daya
bayan daya zakuzo ku zabi akwati dai dai ku budeta
wanda ya dauko kwagirin sarautata shine zai rike mun
kasata har na dawo daga doguwar tafiya
koda jin wannan batu sai gabadayansu hankalinsu ya
dugunzuma wazirin Akiyanu ya dubi sarki sahibul hairi
yace ya shugabana ni a tunanina bai kamata ayi haka ba
ni da nake a matsayin wazirinka nine na dace na rike
maka kasa
koda jin haka sai sarki ya yi murmushi yace na sani cewa
ka dace ka wakilceni to amma fa ka sani cewa ban taba
yin tafiya irin wannan ba kuma gaba dayanku babu
wanda hankalina ya kwanta da shi don haka kawai sa'a
naga mai rabo dole ne abi wannan tsari nawa....
KAFIN WAZIRI ya kara cewa wani abu tuni Sarki sahibul
hairi ya dubi yan majalisar na farko ya umarceshi da yaje
kan akwatunan ya zaba hannayensa na karkarwa sai ya
tsaya ya kasa zabar akwatin da zai bude sai da sarki ya
daka masa tsawa sannan yaje ya bude akwatin farko
aikuwa yana budewa sai yaga wayan babu komai ciki
koda ganin haka sai kwalla ta ciko idanun dan majalisar
ya fara kukan zuci don takaicin rashin samun nasara daya
bayan daya suka rinka bude akwatunan har akazo kan
mutum na tara shine wanda na kashe wanda ake kira
AMINUL HAS
Aminul has ya kasance shine galadiman sarki kuma duk a
cikin yan majalisar shine wanda baya gajiya da yiwa sarki
hidima duk sa adda sarki ya aika masa da bukatar abinci
ko sutura take yake aiko masa har saida takai cewa sarki
sahibul hairi ya kure Aminul has ya talautar dashi duk ya
siyar da kadarorinsa
wani lokacin ma idan aka turo da bukatar sarki sai yayi
rance sannan ya aika wajan yaransa da suke tafiya fatauci
a kawo masa kudi ya biya bashin gaba daya yan majalisar
mutum takwas babu wanda ya sami nasarar dauko
kwagirin sarautar kuma duk su takwas din babu wanda
bai zub da hawaye ba da fargaba lokacin da ya zo bude
akwatinshi
Shikuwa Aminul has cikin nutsuwa ba da fargabar komai
ba ya zo ya bude akwatin ta karshe wadda ba a bude ba
bisa mamaki sai shima yaga babu komai a cikin akwatin
yan majalisar suka dubi sarki sahibul hairi waziri Akiyanu
yace ranka ya dade yazaka yaudaremu kace akwai

kwagirinka a cikin daya daga cikin akwatunan nan alhali
babu?
Koda jin haka sai sarki sahibul hairi ya bushe da dariya
sannan yace hakika na yaudareku amma ba dan komai
nayi hakaba sai don na gane wanda ke kaunata a
tsakaninku gaba dayanku nan kun sani cewa wannan
tafiya da zanyi mai hadarin gaske ce kuma na tabbata
cewa duk kuna ganin cewa idan natafi ba zan dawo da
raina ba don haka duk wanda ya hau kan karagata ya
haukenan
gaba dayanku takwas din nan babu wanda baiyi kukan
takaici ba a nan da fargabar rashin samun nasara face
Galadima kuma a cikinku shi kadai ne bai gajiya da
bukatata lallai yanzu na dad gamsuwa cewa Galadima
masoyina neh na kwarai tunda baya harin kujerata
batun kwagirin sarautata kuwa hakika da farko na sanya
shi a cikin akwatin tsakiya amma kafin ku shigo sai na
sauya shawara na dauke abina sakamakon wannan
hikimar da tazo cikin gaggawa koda gama fadin haka sai
sarki sahibul hairi ya fiddo kwagirin sarautarsa daga cikin
alkyabbarsa ya baiwa aminul has ya karba sannan yace
dashi
daga yau kaine sarkin misra kafin na dawo daga tafiyata
ko shakka babu zan dawo kuma na umarceka da kayi
adalci a cikin harkokin mulki kamar yadda na sabayi
nan take sarki ya sallamesu gaba daya suka tafi cikin
bakin ciki galadima ne kadai ya zamo a cikin dumbin
farin ciki mara misaltuwa domin dama yana da wani
babban buri a zuciyarsa wanda ba zai taba cika shiba face
ya zama sarkin misra
bayan sarki ya sallami yan majalisa sai yasa aka shirya
masa doki da guzuri amma sai bawan dake wannan aiki
ya sanar dashi cewa guzurin fa ba zai isheshi ba har ya isa
birnin Askandariyya
kafin bawan ya gama rufe bakinsa saiga manzo daga
gidan Galadima janye da wata doguwar taguwa akan
taguwar kuwa guzurin tafiya ne mai yawa ga sarki Sahibul
hairi
yayinda sarki yaga wannan sako sai ya cika da tsananin
farin ciki kuma yaji cewa kaunar Aminul has ta karu a
zuciyarsa ainun nan take yayi alkawari a zuciyarsa cewa
randa duk bukatarsa ta biya sai ya maishe da galadima
waziri kuma zai bashi dukiya mai tarin yawa da bazasu iya
cinyeta ba har zuwa karshen rayuwarsu
bayan an gama kimtsa taguwar sarki da guzurinsa sai ya
umarci wani bakin bawa nasa mai suna HALUF daya
shirya suyi wannan tafiya tare cikin murna da zumudi
Haluf yaje ya kimtsa koda fitowarsa sai ya iske yayi shigar
yaki mai tsananin kwarjini da ban tsoro gaba daya shigar
bakaken kaya sarki yayi sannan ya sanya bakin sulke da
bakaken takalma dogaye na fata iya gwuiwa hatta kufen
takobinsa da garkuwarsa ma bakakene fuskarsa ya rufeta

ruf da bakin rawani ba aganin komai face idanunsa nan
take sarki da haluf suka fito daga cikin gida
sarki ya hau taguwa shi kuwa bawa haluf yahau doki ba
tare da bata lokaci ba suka kama hanya suka bar cikin
birnin misra A wannan lokaci kuwa rana na gaf da
faduwa domin gari ya soma duhu haka dai sarki da bawa
haluf sukaci gaba da tafiya harsuka nausa cikin dokar daji
basu gusheba suna tafiya har saida sukaga duhu yayi
sosai sannan suka yada zango a bakin wata bishiyar
dabino cikin gaggawa bawa haluf ya kafawa sarki tanti
sannan yayi masa shimfida a cikin tantin ya kunna masa
fitila
koda gama wannan shiri sai ya mike tsaye da nufin ya fita
daga cikin tantin sarki Sahibul hairi ya kira sunansa yana
mai cewa
Ina zaka ya Haluf??
Bawa haluf yace ya shugabana ai zan fita wajan tantin
nanne natsaya don na tabbatar da tsaro kada wani
mugun abu ya sumamemu....
.
KODA SARKI YAJI HAKA saiyayi murmushi yace yakai
haluf ka sani cewa muddin kana tare dani babu wani abu
mai rai da ya isa ya cutar dakai abinda nake so dakai
shine ka kwance guzurinmu ka dauka abinci mu ci tare
cikin tsananin mamaki bawa haluf ya dubi sarki yace
haba ranka ya dade ina ni ina cin abinci tare dakai? Ai fiye
da shekaru goma baya ma sa adda na fara yimaka bauta
ban taba samun kusanci da kaiba kamar yanzu
sarki sahibul hairi yayi murmushi a karo na biyu yace
yakai haluf ka sani cewa wannan tafiya da ka samu ikonyi
tare dani ba karamar matsayi ta janyo maka ba don haka
ina so ka yaye dukkanin wani hijabi dake tsakaninmu na
bawa da maigidansa ka dauka cewa tare da abokinka ne
in kuwa kana sabawa hakan zan umarceka da komawa
birnin misra in yaso nayi tafiyata ni kadai koda jin haka
sai bawa haluf ya nutsu cikin hanzari ya bude guzuri ya
fidda abinci ya zuba a faranti sannan ya dauko salkar
ruwa ya tsiyaya a cikin kofi guda ya ajiye a gaban sarki,
sarki sahibul hairi ya nannade hannun rigarsa sannan
haluf ya zuba masa ruwa ya wanke hannu gama wanke
hannun keda wuya sai sarki ya karbi salkar ya umarci
haluf daya tara hannayensa shima ya zuba masa ruwan
ya wanke
cikin matukar mamaki haluf ya noke kamar ba zaibi
umarni ba amma dayaga sarki ya murtuke fuska sai yabi
umarnin da gaggawa nan dai suka kama cin abincin tare
suna nishadi tamkar aboki da aboki harma sarki na
zakulo wasu labarai yana baiwa haluf na ban dariya shi
kansa haluf bai san sa adda ya saki jikinsa yayi ta
kyalkyalewa ba basu gushe ba suna wannan nishadi ba
har dare ya fara tsalawa a sannan ne sarki ya kishingida
bisa shimfida nan da nan kuwa barci ya sace shi sa adda

bawa haluf yaga sarki sahibul hairi yayi barci saiya mike
tsam ya fita wajan tantin ya tsaya haluf ya dubi gabas da
yamma kudu da arewa baiga komai ba kuma baiji motsin
komai ba face kukan tsuntsaye sai kuma wata irin

1 Comments On SARKIN SARAKAI
avatar
sdeeq

2 years ago

Reply

dan allah babu yadda xanyi download ne

Please Login or Register in order to submit comment