Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

MAZAN KO MATAN
.
Marubuci
Shuraih Usman
.
Publish by (c) shuraih 99%
2018
http://fb.com/hausaebooks

MAZAN KO MATAN
Rubutun Shuraih Usman
@shuraih 99%
Part 1
Tangamemen Gida ne iRin na zamani
Wanda ya kawatu ainun, domin kuwa a gaba dayan fadin unguwar gidanne gida na farko da a ka
sana'anta da Bene
Gidan wani dan majalisa ne mai ci
.
Ina tsaye a bakin gate din gidan hannuna na dama rike da makulli ,yayin da hannun haguna yake
boye cikin Aljihu,
Lokaci lokaci nakan yi wasa da makullin hannuna ta hanyar jujjuyasa
.
Wani yaro na gani ya fito daga cikin gidan zai karisa bakin titi, da guduna na tsaida shi ta hanyar
kwala mai kira , yaron ya tsaya yana dubana tamkar wanda yaga wani Aljani ,
"Dun Allah yayarka Safiya tana gida kuwa"

Na tabayi yaron
"Eh tana gida" yabani amsa
"Dun Allah kai mani wata Alfarma man"
"Ina jin ka"
"So nake ka kiramin ita"
"Hmm " kawai ya fada sannan ya juya ya nufi cikin gidan
.
Duk da dai nasan abunda zai biyo baya hakan bai sa naji ko darr a zuciyata ba,
Bayan dan gajeran lokaci sai ga yaron ya fito
Haryanzu irin kallon dayai mani waccan karon itane dauke a idanunsa ,
Bayau na saba zuwa zance wajen safiyya ba don kuwa nakai wajen wata biyu, ina zuwa wajenta dai
dai da rana daya ban taba fashi ba
.
Duk abun da nake yi komenene, koya wannan abu yakai ga muhimmanci muddin karfe takwas din
Dare yayi, toh take zan saki abunnan na nufi hanyar gidan su safiyya
,
Wani tarin abun takaici kuwa shine Tunda nake zuwa wajen safiyya dai dai da rana daya bata taba
yimin kallon mutunci ba,
Ko tafito ma sai de ta gaggasa mani magana tai tafiyarta, wani sa'in ma a gabana samarita masu
hannu da shuni suke zuwa sui awon gaba da ita, cikin dankareren motoncinsu
,
Bazan taba mantawa ba akwai wata rana da na zo , naci sa'a ta fito, ranan ina sanye da kayan
aikinane na bakanike. Ko tsayawa canzaasu ban ba, kuru kuru safiyya ta fadamani wai wari nake
Muna tsaye da ita a wajen sai faman bata baki nake ina furta mata lufuzan soyayya masu sanya
zuciya tai taushi,
Wata dankareriyar motace kirar range rover ta faka wani mutum sanye da manyan kaya ya fito daga
cikin motan.
Koda safiyya ta kyallara ido taga waNnan mutumin sai ta nufeshi tana mai murmushi
,
Ni kuwa nai tsayuwata a kofan gidan cikin zaman jira lokacin data zo shigan gida
.
Sam bana damuwa da irin tarin wulakancin da safiyya take nuna mani, duk da bata fito fili tace bata
sona ba,
Nasan abu daya ne ya shiga tsakanina da ita
Kuma shine ya darsa rashin kaunata a zuciyar safiyya
Wannan abu kuwa shine NAIRA
,
Bakaniken mota ne ni,cikin kanikawan ma yaron aiki nake,
Aduk lokacin dana dan samu kudi sai na tafi kasuwa na sayomata yan man shafawa, da sabulai na
iya karfina na kawo mata, amma ko godiya bata taba min ba sai de ta amshe tai su ta kara gaba
wajen masu zuwa da dankara dan karan motoci
.
Wannan abu ya dade yana cimin tuwo a kwarya
Su kansu Abokaina ma tsiya suke min sai kaji suna kirana da dan wahala ,
,
Wannan yasa na yanke shawarar canja salon takuna tunda na fito a gaskiyana abu yaki aiki toh
bazan jarraba dayan ko zaiyi aiki
.
Wannan nema yasa naje na samu wani dan unguwanmu ana kiransa Abba Yelo, na naimi daya
taimakamin da Aron Motarsa na Dare daya kacal,
Daga nan na garzaya wajen Abokina MJ na nemi ARon kayan kanti sababbi a wajensa
,

Nai wanka na feshe jikina da turaren Daki na ci kwalliya sa'annan na dau makullin motar dana ara
nai ficewata daga gida,
Koda na fito kofan gida mutane da dama basu gane ni ba, don kuwa sun saba gani na cikin
tsummokaran Over size dina
To yau gani sai kace wani hamshakin mai dala ne
.
Na shiga cikin motan nai hanyar Gangaren Aboki
Fakawa nayi a kofan gidan su DANGADO na nemi daya bani aron wayarsa infinix finger print, da
kyar da sidin goshi ya bani, yayin daya cikani da gargadi
*****
"Wai tana zuwa" yaron ya fada
Cikin isa na zura hannu cikin Aljihuna na dauko naira hamsin na ba ma yaron, sosai yayi godiya
sannan ya kara wuta
,
Bayan dan wani lokaci sai kofan gidan ya bude safiyya ce ta fito tana sanye da riga da siket
wayanda sukai matukar yi mata kyau, hasken fuskarta wanda akullum karuwa yake,
Tun daga nesa naga tana mini kallon daga ina
Wannan yatabbatar mani da cewa bata gane ni ba
"Assalam" tai sallama
Na amsa sallamar cikin kausasa murya yanda na amsa sallaman zai tuna maka da marigayi IBRO
Allah ya jikansa
,
"Malam waye kai sannan daga ina kake" ta jero min wayannan tambayoyi bayan data jingina a jikin
motan Aro na
Nai murmushi sannan na Cire bakin tabarau din daya ke kan fuskata
Cikin dan razana ta washe baki "shuraih!"
Na gyada mata kai
Munyi hira sosai yayin da yawancin hiranma safiyya ne ke zancenta , don ni hankalina yana cikin
wayar hannuna wanda tun da muka fara hira na fiDdo,
Ni kaina nayi mamakin yadda safiyya ta zage muna hira yau tamkar ba itace safiyyan da ke cemin
ina Wari ba,
Na tattakure na shiga shirga mata karya ba kakkautawa
Don kuwa ce mata nai ai Dangote kanin babana ne Uwa daya Uba daya
Sun rabu ne tun suna yara kananu
Koda ta nemi sanin abunda ya rabasu sai na sake shirga mata wani karyan inda nace mata
Ai tun lokacinnan babana suna zaune a kano wata rana sun fita yawo shi da dangote shine barayin
mutane suka sata shi, tun daga ranan basu sake haduwa sai jiya, da dangote yazo wucewa ta nan
garin sai Allah ya hadasu
,
Ta sake tambayana yadda akayi suka shaida Juna
Nai murmushi nace mata ai naka nakane babu ta yadda zaka mance da dan uwanka, hatsari dangote
yayi a hanyan KARAN SHANU shi kuwa mahaifina yai kokari ya taimakeshi ya futo da shi daga
cikin motan to ta haka ne har dangote yaga wata sarka a wuyan mahaifina , wannan sarka itace
shedan gidanmu don nima ina da ita,"
Safiyya ta kalleni cikin mamakin zancena
,
Na basar da kallon datai mani
Ta budi baki da niyyar sake jefomin wani tambayan nai sauri na katseta da fadin
"Yanzu haka ma dangoten yana nan a gidanmu, shin kina bukatar ganin sa ne?"
Nai kasake ina shirin jin amsar daza ta bani, ni kaina na san nayi gangancin fadin wannan zance,
,

"Ai kuwa zanso na gansa ,kash sai de yanzu babana yana gida amma gobe kam dolenka ka kaini
kodan ma muyi hoto"
Tafadi cikin zumudi
murmushi nayi mai nuna cewar na tsira daga wannan takin,
,
Munyi hira sosai daga nan na sallemeta inda na zaro last cash dina Dubu daya na bata, ita kanta
dubu dayan sai da nayi kwanaki bakwai ina tarata , na bude motan aro na na kara gaba,
Zuciyata fal da farin ciki domin kuwa ji nake tamkar nafi kowa a duniya
,
Ina kan hanyata ta komawa gida sai na Tuna da abun da ya kusan sanyani hatsari,
Hankalina ya tashi, idanuwana suka zazzaro
Gabana yakama faduwa
"Wayan DANGADO"
A fili na fada yayin danake lalube aljihuna
Nai saurin faka motan a gefen titi
Babu inda ban bin cika a cikin motar ba amma ban ga wayan ba
Na tuna irin tarin gargadi da kashedin da runga kwarara mani kafin ya bani wayan
.
Fans dafatan kuna biye da Alkalamin 99%
♥MAZAN KO MATAN♥
♥Rubutun Shuraih Usman♥
♥@shuraih 99%♥
♥Part 2♥


Tamkar na fashe da kuka haka nake ji
Sabuwar wayace kwananta Uku da siya,
Sabuwa ce gal a leda ya siyota Dubu 50,
Kirar infinix
.
Shi kansa shiga cikin motan ma gagarata yai na jingina a bakin kofan ina yiwa kaina jimami dun
kuwa ko shakka banayi nasan sai na biyasa wayansa
.
Karancinn mutunci ne da Dangado,
Baya daukan asara a kayansa ,
,
Na dulmiya cikin kogin Tunanin inda akai har wayan ta bace,
Tunani kala kala suka runga ziyartar kwalkwalwata a yayin dana ke daukan wasu wasu kuwa nai
fatali da su,
,
Wani farin Tunanine ya kwankwasa wa kwakwalwata kofa duk da dai cewa na gaji da tunanukan,
hakan baisa nai fatali da shi ba, sakamakon ganinsa da nayi fari fat, sabanin tunanukan baya bakake
wuluk
.
Nai sauri na bude Tunanin nan, sai ga Hoton yadda akayi har wayan tabar hannuna
Wani dan guntun murmushine ya subuce daga lebbana, wayanda suka bushe karangus
.
Nan take naji wata irin kwanciyan hankali ta ziyarceni, dukkan fargabana suka kau, raina yai fari
tas,
Na juya da nufin na shige mota naje na amso wayan a inda na barsa
,

Akame na tsaya kikam numfashina ya kusan daukewa, sakamakon abunda idanuwana ya hango
mani
,
Wasu tsala tsalan yan matane su Uku suke jerowa akan titi, dukkansu jajayene tamkar wasu
larabawa ,
Hankalina yafi karkatuwa ga ta tsakiyarsu, wacce ta kasance gaba dayansu ta dara su a kyawu,
.
Ta mallaki madaidaicin fuska, mai dauke da kana kanan idanuwa,a yayinda tai wa girarta ado da
eyeshadow,
Tana sanye da koren doguwar riga har kasa mai dauke da rotsi rotsin ja,
Ta rike jaka irin nasu na mata ,
In ka ganta a cikin wayannan yan mata tamkar wata ran daren goma sha biyu,
.
Tun dana ke a rayuwata ban taba ganin mace da irin wannan kyawu a zahiri ba sai de a talabijin,
Suna tafiya suna hira,
Zuciyata ta fara fisgata tamkar mayen kurace a jikina, babu yadda banyi ba don na hana zuciyata
muradin kyakkyawan halittan nan amma abu ya faskara
Hakan yasa na nufi wayannan yan mata fuskana cike da murmushi,
.
Irin kallon da suke mani shi ya tabbartar mani da cewa ko kallo ban ishe su ba, yo amma da shike
nima gwarzon namijine sai na dake a zuciyata nace yau dai ko MAZAN KO MATAN
,
Na rangada masu sallama da muryata wacce nai kokarin sirantata tamkar zanja ayan kur'ani,
Suka amsa cikin hadin baki,
Kowaccensu ta daure fuska tamkar an aiko masu da sakonnin mutuwa,
Murmushi kawai nayi don nasan na jan aji ne
,
"Sannun ku yan mata, tun daga nisa na hango ku, sam bai kamata ace kaman ku kuna taka sayyada
ba, hakan ce tasa nai tattaki na iso , ga mota ta a can kuzo muje na rage maku hanya"
,
"Hmm mungode wallahi don ma mun kusan isa inda zamu"
Ta bangaren dama ta bani amsa
Nai murmushi mai nuna halin ko in kula don na riga dana san halin yan matan yanzu nace "Ok wai
dama gani nayi ya kamata , amma tunda kun nuna bakwa bukata no problem, da shike nima baqone
a nan garin yau nazo daga Abuja, sakamakon wata shara'a da muke da wani wai shi Alhaji Sale "
,
Na lura da yadda dukkansu yanayinsu ya canja duba da irin yadda suka karemani kallo, a zuciyata
nace ku gama kare mani kallo da kyau ,
Har na juya na da nufin zan tafi sai kuma na sake juyowa na dubesu nace Don Allah na tambayeku
mana
,
"Muna jinka" wacce tai magana dazun ta bani amsa
"Ina ne gidan Abdullahi Adamu, senator naku"
"G R A" ta sake bani amsa
Cikin tantama nace "ina ne kuma G R A"
Ta fara yimani kwatance sai ta iddar sannan nace mata
"Wallahi sam bana gane kwatance don Allah ku taimaka ku kaini kunga daga nan sai na sauke ku a
gida,"
Sai da na lallabesu sosai sa'annan suka yarda har suka shiga cikin motar Arona na jasu,
Na lura da tauraruwata tun da na hadu dasu bata furta ko kalma daya ba,
Ina tuki na na saita madubin gaban direba saitinta yayin dana ke kallon kyakkyawan fuskarta sai
sheki yake tamkar zinariya,

,
Na juyo na dubeta murmushi akan fuskana
"Tauraruwa ke bakya magana bane"
"Tauraruwa" ta nanata sunan
Salon yadda ta kira sunan ma abun burgewane, zakin muryanta ne yaso ya sanyani sakin sitiyari
,
"Sunan bai yi bane" na tambaya
Shiru tayi
"Kin dace da sunan ne shi isa , domin kuwa kinfi kama da larabawa , "
Dukkansu yan matan suka kyalkyale da dariya
Sai da sukai mai isarsu sannan dayan tace
"Kai amma da abun dariya kake"
"Wallahi gaskiya na fada, dun kinsan ni a saudi nayi karatuna, yo ko yammatan larabawan baza su
nuna maki kyawu ba tauraruwa,
Yanzu haka da kuka ganni a garin nan wallahi wani dan damfara ya keson ya cuci mahaifina yanzu
haka ma mun shiga kotu da shi,
Sunansa wai SALE , shi isa dukkan wani kadarorinmu muka bi muka rubuta cewa is not for sale
don mu gargadi jama'a, kinga ma wancan ginin, "na nuna masu wani tangamemen gini wanda ake
kan aikinsa, ajikin ginin an rubuta da manyan baki THIS PROPERTY IS NOT FOR SALE,
,
Na cigaba "ai duk wani gida,mota,babur,fili da dai sauransu da kukaga an saka THIS PROPERTY
IS NOT FOR SALE toh na mahaifina ne, muna sanya wannan rubutunne don mu gargadi mutane "
,
Haka dai na runga jansu da hira ina sharara masu karya babu kunya bare tsoron Allah
har muka isa G R A suka nuna mani gidan dana bukata.
Daga nan na juya akalar tafiyar zuwa angwan da suka ce da ni a nan suke,
Cikin kankanin lokaci muka iso gangaren tudu da taimakon daya daga cikinsu inda take tai mani
kwatance, bata san cewa na fita ma sanin angwan ba,
.
****
Suka fito daga cikin motan yayin da suke yimin godiya,
Fitowa nayi na dubesu nace babu komai ai
"Gashi kuma zaku tafi baku fadamin sunayenku ba, ko namban waya baku bani ba "
,
Wacce tafi kowannensu surutu tace "ni dai sunana Rashida, wannan kuma ta nuna tauraruwata da
yatsa sadiya waccan kuma balki
,
Na nanata sunan a raina sadiya gashi dai ta hadu amma sunan na tsofaffi ne a fili kuwa murmushi
nayi sannan nace "suna mai dadi, ni sunana Shuraih 99% inkiya mai dala"
,
******
Ina kwance kan kakkarfan katifan dakina wanda sau tari yasha sanya mani ciwon baya ,
Na tuna lokacin dana bar kofan gidansu sadiya yayinda rashida ta bani nambarta
Tunani nake yanzu gobe a ina zan samu aron kaya da mota dun kuwa nace masu gobe zan kawo
masu ziyara,
Ina cikin wannan sake saken ne barci yai awon gaba da ni
,
Kaman a mafarki sai ji nai ana bubbuga kofan dakina,
Na bude idanuwana masu dauke da mayataccen barci a hankali,
A sannan ne kunnuwana suka sake tsinkayo karar bugun kofan tamkar za'a balla kofan haka ake
bugunta
,

Cikin zafin rai na mike zaune na dubi kofan dakin
Har na bude baki zan yi maganna, sai na tsinkayi muryan DANGADO yana cewa
"Kai shuraihu! shuraihu!! Shuraihu!!! Ka bude kofan nan ka bani wayata,"
.
.
Ai dangado kai sai de kayi hakuri
Na fada a zuciyata
.
Hop haryanzu kuna......... Biye da Alkamin
99%

Duk da na dan razana sosai da jin muryansa amma hakan baisa na mike naje na bude kofan ba
Illa ma kasake danayi ina kallon kofan
,
Shakka babu nasan muddin na bude kofan toh fa sai dangado ya tayar mani da hankali,
Don in ta kai ta kawo ma cewa zaiyi mu tafi gidan su safiyya,
,
Kofan dakin ne ya cigaba da kara yayin da dangado yake dukansa iya karfinsa,
,
Nai ja tsaki sannan na rarumo bargona wanda a nai filo da ita na lulluba a jikina, nai kwanciyata
**********
,
Sauri nake ta zabgawa , burina shine na isa gidan su safiyya duk da nasan cewa zan fuskanci
matsala a wajenta wajen karban wayan amma na ruga dana hattama irin karyan da zan lauya mata ,
,
Yo dama gani da dogon kafa uwa wani rakumi,
Cikin kankanin lokaci na isa kofan
Cikin sa'a na hango yaron dana aika jiya yana wasa a gefen gidan, na yafuto shi da hannu,
Da gudunsa ya iso gabana
.
Na jingina da bangon gidan bayan na aika yaron ya kirawo min safiyya na duba agogon hannuna
Karfe bakwai da minti goma sha uku na safiya
Nai mamaki ainun, da yadda lokaci baya ja da gudu
.
Yaron dana aika ya futo yace dani "wai tana zuwa"
Hankalinsa gaba daya yana wajen wasan daya ke yi,
Na sallameshi da cewa "toh"
,
Ban wani dade ba safiyya ta bude kofa ta fito
Kayan da suke jikinta jiya sune haryanzu amma a wannan lokacin hulan sanyine akanta sabanin
Fatala(kallabi)
,
Tayi zunzurutun kyawu amma ni bata kyawun nake ba yanzu duk matsala ta ta bani wayan dangado
ne,
Bayan mun gaisa nace da ita
"Safiyya dan bani wayannan danA baki jiya da dare"
YaDda nayi maganar ma kadai zai tabbatarmata da cewa cikin Ujila nake
,
Tai kasake tana kallona kafin daga bisani tai murmushi, don ta jawo hankalina gareta, a zuciyata
nace aikin banza, ayanzu kam murmushin kinnan bazai tasiri ba"
Afili kuwa cewa nai "yi sauri dun Allah wallahi sauri nake ,"
.
Sai waige waige take tako ina a haraban angwan
Nasan ba komai take nema ba Illa mota, a zuciyata nace KARSHEN MAKARYACI tazo,
,
"Yo amma ina motarka"
Safiyya ta tambayeni tana kara kallon wajejen
Nai murmushi "tana gida, me yafaru"
"Babu komai kawai de ina tambaya ne,"
Tai shiru bata sake cewa kala ba
"Akwai wasu muhimman documents a cikin wayannan kuma yanzu nake so nai amfani da su, dan
Allah yi sauri ki dauko mani,"
,

Na lura da yadda yanayinta ya canza ya koma salon tausayi, ta kankantar da murya can kasa tace
"dama jiranka nake kazo na sanar da kai abun daya faru"
,
"Me yafaru " na fada cikin zazzaro idanuwa don na dauka screen din wayar ta fashe ne
"Wallahi jiya da daddare barayi suka shigo gidanmu, sun yi mana sata mai yawa kuma sun amshe
wayarka"
**************
Wasu taurari idanuwana suke hango mani, taurarin sun kasu kashi biyu kashi na farko jajayene
kashi na biyu kuwa bakakene
Jajayen taurarin nan suka hadu da babaken to amma maimakon su bada haske kala daya, sai suka
bada wani bakin haske mai dauke da dugo dugon jajaja,
,
"Shuraih ga kokonka, kosen yana cikin dakinka"
Na mike tsaye ina kallon mai maganar kanwata ce, banyi kasa a guiwa ba na dau kokon na nufi
cikin dakina,
Abun dana fara cin karo da shi shine kosen da aka ajjiye mani,
Na zauna na dau kosen na cilla cikin bakina, maimakon naji dandano mai dadi, sai naji akasin haka,
wannan yasa na mike tsaye na fito bakin kofan dakina na tofar da ragowan kosen dake bakina
,
Tun da safiyya ta fada mani wai wayan an sace naji gabadayan lakan jikina ya mutu, babu yadda na
iya haka na barta tai shigewarta gida
,
Da kyar na dawo gida don kuwa juwa ke dibata a hanya sai tangadi nake tamkar dan giya sabon
shiga,
*
Na dau kosen da kokon na fice daga dakin ba inda na nufa sai wajen ummata don kuwa ita ke toya
kosen , tun daga nesaa na runga jiyo hayaniyar mutane sama sama ,
"Baba sai nine"
"Na riga shi zuwa"
"Na naira hamsin zaki samun baba"
,
Irin wayannan hayaniya suke tashi a rumfan umma mai kose sunan da jama'a ke kiranta da shi
kenan sabanin ni da Umma kawai nake kiranta
,
Dukda tarin mutanen dana tarar a wajen tuyan kosen sun zagayeta hakan bai hanani cusa kai ba na
rrunga tutture su dolensu suka bani hanya na iso gindin wutan na durkusa nace
"Umma bazan iya cin wannan kosen ba , wallahi daci yake min"
"Toh yau kuma salon iskancin da ka fito da shi kenan ko kaka?" ta bani amsa lokacin datake
kokarin saka dusan kosen cikin mangyada
Nai shiru kafin daga bisani nace
"Allah kuwa umma daci yake"
"Toh me kake son nai maka"
"Naira hamsin zaki bani naje nasha farin shayi"
"Toh amshi" ta mikomin hamsin din
Na amsa ina mai cewa "na gode umma"
Na mike tsaye da nufin na fuce daga rumfan
Idanuwana ne sukai arba da ita, nan take kirjina ya buga da karfi, nai tunanin ko idanuwana ne
keyimin gizo hakan yasa na mummutsikesu da hannayena, amma har yanzu ita nake gani a tasaye a
gabana hannunta rike da gudan naira dari , ranta a bace,
Ba kowa bace illa Sadiya budurwan dana runga shirgawa karya jiya ahanyata na dawowa Gida
.
Toh ya zata kaya

Ku biyo alkalamin Shuraih 99%

Duk da cewa na san ta Gane ni amma sai na matse nayi tamkar ba nine jiya muka hadu ba
Na matso kusa da ita fuskata na kallon kasa cikin boye murya nace
"Dan bani hanya yan mata"
Batare da musu ko gardama ba ta matsa mani na wuce,
Zuciyata sai bugawa take ina tunanin shin bata ganeni ba kuwa,
Wata zuciyar tace ai data ganeka da iyanzu baka kawo nan ba,
,
Daidai ina shirin ficewa daga gidanmu naji muryanta tana kiran suna na
Duk da banso na tsaya ba amma sai na tsinci kaina ina mai tsayawa
,
Cikin takunta na rangwada fuskarta a bace ta tako wajena,
"Yan mata naji kaman kin kirayi sunana"
"A,a ni ba sunanka na kiraba, this property is not for sale nace"ta bani amsa
Zuciyata ce tai dumm nan take naji kunya ta lullubeni,
Nai karfin hali cikin borin kunya nace
"Dun Allah sadiya ki hakuri da karyan dana shirshirga maku jiya, dun Allah kar ki fadawa wa
umma na"
,
Tai murmushi wanda ya bayyana kyawawan hakoranta kafin tace
"Hmm shuraih kenan, shin an gaya maka ni karamar yarinyace, ko ce maka akai ni ban sanka ba, ai
tun da dadewa na sanka kuma har wajen kanikancinku na sani, kai ne dai nake tunanin baka waye ni
ba, sai gashi jiya kai fakare kanata shirgawa kawayena karya"
,
Na saki baki galala ina kallonta da mamaki
Nace "yo amma mei yasa tun jiyan baki tonan asiri ba"
Tai murmushi kafin tace
"SO, "
Na jaddada kalman a zuciyata SO kuma
Tamkar taji abun dana fada a zuciyata
"Eh shuraih , tun ba yau ba ziciyata ta kamu da tsananin sonka, hakan yasa na dunga bibiyan
al'amarinka,a kowacce rana sai na tafi wajen aikinku domin kawai naga fuskarka, da sonka nake
kwana da shi nake tashi, saide na rasa ta yadda zan sanar maka,
Cikin sa'a sai gashi jiya Allah ya wullo ka gareni, naji dadi sosai daka yaba ni, duk da cewa a jiyan
tafarkin daka kama na karyace, sam ban ga laifinka ba, domin da bakai hakaba toh kawayena ma ba
za su tsaya ba bare har takaisu ga sauraranka, ina Sonka Shuraih, ina sonka"
,
Sam ban gaskata abun da kunne na suka jiyemun ba don na fi daukan hakan ga rudana da kunne na
suke mani
Wai tayama za'ace ni da nake m.......
"Ina sauraronka shuraih, shin kana sona kuwa"
Sadiya ta katse mani zancen zucina da fadin haka
,
********************
Ta fiya nake kaina a kasa ina tunanin abubuwan da suka faru dani cikin dan kankanin lokaci haka
,
Shakka babu wannan rana ta zo mani da sa'a
Duba da yadda lokuta kankani da suka wuce
Kyakkyawa kuma dirarriyar budurwa ta furta cewa ni take so,
,
Yanzu kam ko tunanin safiyya bana yi
Har ga Allah naji darsuwan Son sadiya a zuciyata

Duk da cewa bata kai safiyya komai ba, amma itama Allah ya azurtata da kyakkyawan sura dadai
gwargado
,
"99%! 99% !! 99!!!"
Tamkar daga sama naji ana kwala min kira
Na gane muryan mai kiran
Ya karaso ya bani hannu muka tafa
Mujahid ne yana sanye cikin farar riga mara hannu, a gabanta an rubuta FILA da manyan baki, sai
bakar jeans mai aljuhu biyu a kaurinta

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2

Please Login or Register in order to submit comment