Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kasa tamu itace duk wayanda suka hada neman wani abu tare da wani, ko suke neman mace tare toh akwai wata gasa da zasuyi wanda duk wanda ya cinye wannan gasa toh shine yayi nasarar mallakar wannan abu da suke rigima akai wannan gasa muna kiranshi da GASAR FIDDA GWANI"
.
Haseena tayi mani murmushi
Wanda ke sanyaya min zuciyata, taci gaba
"Toh Masoyi kaji tarihin birnin namu mai matukkar Al'ajabi,"
Wani shauki naji ya dirga min a zuciya sakamakon yadda naji sunan da haseena ta kirani da shi, ta matso kusa dani ta kama hannuna , ai bansan lokacin dana kurma wani dan karamin ihu ba sakamakon wani shocking dana ji ya ziyarci hannuna,murmushi kawai haseena tayi sannan ta dago ni, abun ya bani mamaki domin kuwa yadda ta daga ni sai kace ba katon gardi ta daga, yadda kasan fallen takarda, har naso na tambayeta game da hakan amma sai nayi shiru da bakina, muka fice daga cikin dakin atare
.
Tafiya muke a jere yayinda hannuna yake cikin nata fuskarta kuwa yana kan fuskana ko gabanta bata kallo sosai, wani zunzurutun wutar kaunarta ne yake ci a zuciyata,
Ban yi aune ba sai gani nayi mun iso wani kayataccen fada wanda aka kawata da kayan ado irinsu, zinare,zubarjadi,lu'u lu'u da yakutu domin kuwa daben wajen ma da yakutu akayi shi,
Ga bayi da hadimai sai zirga zirga suke tayi amma da zarar sun ganmu sai su russuna su kwashi gaisuwa sa'annan su wuce,
Mun danyi tafiya mai dan nisa kafin mu iso bakin wata kofa wacce aka sana'antata da zallar farin zinare sannan akai mata ado da lu'u lu'u sai dai wani abun daya daure mani kai da kofar shine ganin wasu macizai danayi guda biyu nan na de da juna a jikin kofan,
.
Cikin mamaki naga haseena takai hannu jikin kofan ta kama macizan nan duka ta murde musu kayika, sai gashi kofan ta bude, nan muka shiga ciki har hanzu hannuna na cikin na haseena, dakin da muka shiga ya fi kowanne daki kayatuwa a cikin fadan don ni dai tun da na shigo banga wajen daya kai nan kayatuwa ba,
.
Sai a sannan na lura da wasu kirda kirdan mutani sanye da kayan karfe, suna rike da makamai a hannunsu, kallo daya nai masu na gane cewa Dakarune masu tsaron gidan, nakai dubana ga gabanmu inda muka dosa toh a nan ne naga tarin mutane suna zaune bisa wani dogon kujera wanda ya kusan kaini tsayi,
.
Wayannan kujerun suna jere ne, layi biyu kowanne kujera yana fuskantar daya, mutanen sunyi shiga ta alfarma wanda da gani kasan ba kananan mutane bane, mai karatu kar kaji nace mutane ka dauka ko bil'adama ne wayannan mutanen , a'a dukkansu Aljannune amma a siffar mutane suke rayuwa, sai kuma wayansu fuka fukai dake bayansu,
.
Wani dattijon aljani na gani kyakkyawa da shi, yana sanye da fararen kaya masu daraja, zaune yake akan wata karaga ta sarauta, wacce aka sana'antata da zallar lu'u lu'u aka kuma yi mata ado da takubba na farin yakutu, a gefen karagar sa wayansu sadaukan samudawan aljanu ne su goma cikin shirin kota, fuskarsu a murtuke tamkar wayanda aka aiko ma sakon mutuwa, ko motsi basa yi sai kace Gumaka
kwana kallo daya nai ma samudawan aljanun nan na kau da kai don kuwa muddin na cigaba da kallonsu toh zan iya Sumewa
wajen wayannan aljanu muka nufa ni da haseena muna zuwa gabansu haseena ta durkusa sannan ta kalleni tai min Alama dana durkusa ba musu nima na durkusa, kawai sai ji nayi haseena tana magana da wani irin yare wanda ni ban taba jin sa ba, bayan ta gama maganar ne wani daga cikin Aljanun nan yace mar habanki dake da wannan bako, yake gimbiya daga nan sai haseena ta mike tsaye ta karasa gaban wannan dattijon mai fararen kaya ta rungumeshi sannan ta tsaya a gefensa, dattijon aljanin ya dubeni har yanzu ina durkushe ban dago ba,
.
Yafara magana yakai wannan bako kuma masoyi ga yata kai sani cewa muna marhaban da zuwanka, kuma a sannu zamu sanar da kai dalilin daya sa muka kiraka izuwa wannan duniya tamu amma kafin nan yanzu za mu bari ka huta tukunna, aljanin yana zuwa nan a zancensa sai ya dubi wani wani bafaden aljani yace mai zirwanu ka kaishi masaukinsa dun ya huta nasan ya debo gajiya, wanda aka kira da zirwanu ya russuna angama ranka shi dade,
**********
Ina zaune a cikin dakin da zirwanu ya kawo ni , nayi tagumi bana tunanin komai sai na gida,
Yanzu a wani hali iyayena suke nasan dole su shiga wani irin hali izan har ya kaasance basu ganni ba,
.
Nan take naji bana marmarin komai sai gida dun kuwa nima ina so na gansu ko hankalina ya kwanta, sai de ba anan gizo ke sakar ba, aduk lokacin dana tuna cewa ina da zukekiyar budurwa kamar haseena sai inji zanma iya yin shekaru hamsin muddin zan zauna da haseena
.
Tunane tunane kala kala suna ta zuwanma kwakwalwata, ina cikin wannan hali ne sai na fara jin wata zazzakar waka tana tashi daga bayan dakin danake, cikin zumudi na nufi taga na bude don naga wacce keda wannan zazzakar muryar,
Wani kayataccen lambu ne yaiwa idanuna maraba acikin wannan lambu kuwa yan mata ne su ashirin, suna rike da kayan kida sai kidi sukeyi, dukkan matan nan kyawawane na gaban kwatance domin kuwa in ka dauke haseena har yau banga macen da ta kaisu kyawu ba,
A tsakiyar wayannan yan mata wata mace ce ta lullube kanta da mayafi zazzakar muryarta ne kawai yake tashi, ......
.
.
Kuyi hakuri da rashin post nawa akan lokaci rashin wadatuwan lokaci shi ya janyo haka
,
Ni dinne dai Shuraih Usman
Inkiya 99%
Daga:- www.facebook.com/hausaebooks
BUDURWAN SIRRI
Marubuci:- Shuraih Usman
@hausaebooks.cf
@shuraih 99%
Page 5
.
A tsakiyar wayannan yan mata wata mace ce ta lullube kanta da mayafi zazzakar muryarta ne kawai yake tashi,
Zuciyata ce ke fisgata irin fisgar da ruwan kashe gobara yakeyi yayin fitowa daga cikin bututun ruwan
.
Ni kaina ban san lokacin dana je na bude kofar dakina ba da nufin nayo waje naga ko wacece wannan mai wakar, har na saka kafa na fita kuma sai nai wani tunani ,
Ayanda nake jin ana labarta min cewa nan duniyar aljanu ce , na tashi na nufi wajen wayannan kyawawan matan, kila ma aljanu ne ban sani ba,
Wannan tunanin dana yi shi yasa na dawo da baya nai kwanciyata cikin dakina,
Dakyar na samu nasarar yin bacci sakamakon wannan zazzakar wakar dake tashi daga waje, aduk lokacin dana runtse idanuwana domin nai bacci sai na wannan zazzakar murya ya farkar dani,
Har takai da saida na samu wasu yanki na toshe kunnuwana da su sannan na dena jin wannan waka
.
Washe gari na farka a gajiye na tashi na nufi dan wani kofa dana gani a cikin dakin wanda tunanina ya bani cewa bayi ne, kama yadda na zata dun haka yake dun kuwaina budewa na shiga na samu ruwa cikin wata randa na zinare batare da bata lokaci ba nayi wanka da wannan ruwan sai de abun daya daure shine a duk lokacin dana debi wannan ruwa sai naga ya karu
Har na iddar da wankan na fito daga bandakin na nufi kan gadona domin na saka kayan dana cire ajje ,
Amma kayan sai sukace daukanmu inda ka ajje, na neme su sama da kasa na rasa, can na bayan na gaji da nema sai na dawo kan gadon na zauna nayi tagumi, wani haske naga dan kashe mani idanu, na kai dubana ga wajenda hasken ke fitowa sai naga ashe ma a gefena ne, nakai hannu don ganin menene wannan yake wannan haske, cikin mamaki sai gani nayi hannuna ya tabo wasu lallausan abu duk da ban ko menene ba sai na daga abun sama toh anan ne aka samu mishkila abun ya kubuce daga hannuna ya fadi a kasa ai yana faduwa sai naga ashe ma kayane riga da wando irin na sarautar mutanen garin
Cikin tu'ajjibi na dauki kayan na sanyasu a jikina sannan na nufi wajen madubin dayake dakin nayi mamaki ainun alokacin dana irin zunzurutun kyan danayi, kai alokacin sai dana koda kaina nace ashema ni kyakkyawane haka,
,
Karar Kofan dakin ne ya katse ni, lokacin da ake kwankwasawa, na nufi kofan nabude su ukune kamar yadda na fara ganinsu, har yanzu babu wani sauyi atare da su, yan matan jiya ne daya daga cikinsu ta dubeni tace "ran ka ya dade gimbiyace ta turomu mu tafi dakai wajenta don kuyi kalaci"
"Wacece kuma gimbiya" na tambaya
"Wacce ta kawo ka nan garin"
"Wai HASEENA ki ke nufi"
Na lura da cewa wannan kalma danayi na karshe yasa dukkansu sun tsorata duk da bansan dalilinsu na tsoratan ba,
"Eh itace , amma yallabai kasani duk fadin kasarnan babu wadda yake kiran ta da sunanta hatta mahaifinta ma, "
"Saboda me ba'a kiranta da sunanta"
"Wannan kuma wani sirrine na gidan sarauta"
Na jinjina kai sannan nace masu
"Toh muje "
Suka juya suka fara tafiya ni kuma na take masu baa
.
Mun danyi tafiya mai dan nisa sa wacce takaimu izuwa wani kayataccen lambu wanda ya yalwatu da yayan itatuwa, su kansu bishiyoyin dake cikin lambun ababen sha'awane, domin kuwa bishiyoyin dukkansu yana yinsu daya ne, tsayinsu da komai na su,
Furannin lambun kuwa sun kasance a duk bayan dakika daya suna dunkule wa waje guda,
Muka nufi wani waje daban a inda muka bi ta kan gada, wannan gadan de an kerashi ne da zallar itace da igiyoyi aduk lokacin da muka taka gadan sai kaji wani kara na tashi
.
Tun daga nisa na hango kyakkyawar fuskarnan nata sai sheki yakeyi, farace kyakkyawa gata da dirarriyar jiki domin kuwa shape dinta na kwalbar cokacola ne,
Ta mallaki tsastsaikan fuska wadda ke dauke da dara daran idanu, wayanda jure kallonsu, dan mitstsin bakinta wanda idan ka lura da kyau alokacin data ke magana zakaga tamkar baya so ya bude,
.
Ayau tana sanye ne da irin kayan duniyanmu kuma irin na kasarmu, riga Atamfa da sikert, abun ya bani mamaki ainun, ni danake zaton babu irin wannan kaya a wannan garin, sai de dana tuna da abu guda sai nama dena mamaki
.
Ayau tafi kowanne lokaci kyau fuskarta sai sakin tausasan murmushi yake a gareni, ai ban san lokacin dana kura mata idanu ko kiftawa bana yi ba,
Muka kariso wajen yan matan nan sukayi saurin russunawa akasa zasuyi magana kenan ta dakatar da su ta hanyar daga masu hannu sannan ta sallamesu, sukai tafiyarsu
.
Ta dubeni tai wani murmushi wanda yake zuzuta wutar kaunarta a zzuciyata, "ka kwana lafiya"
"Lafiya lau"
Ta riko hannuna , awannan lokacinma sai da naji shocking ya ziyarci kwakwalwata, har nayi dan kara karami, ta jani muka karisa gindin wata bishiya, inda naga an shimfide gaba dayan wajen da wani babbar tabarma, a tsakiyar ta barmar ga abubuwan ci da sha nan birjik,
Takalmi na cire alokacin da nake shirin hawan tabarmar,
Wani laushine ya ziyarci tafin kafafuwana ,ko kadan wannan baiyi kama da tabarmar dana sani ba mai uban gurza-gurza
Haseena ta zaunar dani itama ta zauna kusa dani yanda muna iya jin numfashin juna
"Shuraih tun da nake a duniya ban taba ganin dan Adam lokaci daya naji sonsa ba saikai, hakan nema yasa yau dinnan zan fada maka sirrin dake tattare dani ina sonka shuraih so ,kuma ina muradin zama abokiyyar zamarka na duniya da lahira,
Jina nake tamkar wanda akaiwa kyautar Aljanna domin kuwa a wannan lokaci na tabbata babu wanda yakaini farin ciki
"Haseena kiyi sani cewa nima ina sonki , kuma babu abunda bazan ma don na mallakeki, nasan cewa kina shakkun wannan gasa ta fidda gwani ne, toh ki sani muddin akan ki ne sai de na mutu awannan gasa don kuwa bazan bari wani daban ya sameki ba, ki kudurta a zuciyanki nine mijinki"
Hannu ta saka ta dauki wani tuffa ta mai gaza daya, har zata kai na biyu sai nayi sauri na karbi tuffan daga hannunta ina mai yimata wani irin murmushi na zolaya, sannan nima na gaza daidai wajen da ta gaza
Anan muka luluka izuwa duniyar soyayya domin kuwa hira muka shiga yi sosai yadda take bani labarin garinsu, sosai naji dadin wannan lokaci
.
Muna tsaka da hiran ne wani lokacin izan ta fadi abun dariya sai mu dara , wata kakkausar murya ce ta katse mu da fadin "BUDURWAN SIRRI bata bil'adama bace,
.
Dukkanmu muka juya don ganin mamallakin wannan murya,,,,,,
.
www.facebook.com/hausaebooks
BUDURWAN SIRRI
Gajeran labari
Marubuci Shuraih Usman
@hausaebooks page
@shuraih 99%
Page 6
.
Gabjejen katone mai kirar mutanen farko yana da tsayi wanda na tabbata yayi ni Uku a tsayi don sai dana daga wuyana sannan nai nasarar ganin Fuskarsa
a turbune fuskar yake babu alaman murmushi ko kadan a tare da shi, kwayan idanunsa jane, gashin kasumba ya rufe mai baki yayin da ya hade da gashin gemunsa wanda ya zura ma wani zobe ya kulle
.
Yana sanye da riga falmara mara hannu hakan yasa na samu nasarar ganin kwanjinshi, gaba daya jikinsa a mummurde yake, ga jijiyoyin jikinsa sun tashi sunyi burdum burdum kai kace igiyace
.
Hannunsa na dama yana rike da gashin gemunsa wanda ya rike daidai wajen da ya zura zoben yana dan liliyawa ,fuskarsa na yatsinewa wanda shi a zatonsa murmushi yake,
Shi ba mummuna ba haka kuma shi ba kyakyawa ba, amma kallo daya kadai nai masa na gane cewa wannan dakare ne, domin kuwa akuibin cinyoyinsa hagu da dama akwai wasu takubba manya manya cikin kufensu , wayanda na tabbata in aka ce na daga daya cikinsu bazan iyaba
.
Cikin firgita da tsoro na saki baki galala ina kallonshi har ya kariso garemu,
Abun daya daure mani kai shine sam babu alamun firgici a fuskar haseena
A zuciyata nace yo ta ina zata firgita bayan itama yar uwarsu ce, na sake maimaita wannan suna da naji ya kira haseena da shi a cikin zuciyata BUDURWAN SIRRI
.
Yana tafiya takubban dake jikinsa suna dan kara sakamakon yadda yake tafiyar din
.
Ya kariso wajen da muke zaune
Neman waje yayi ya zauna sannan ya harde kafafuwa irin zaman da yayi sai ya tuna mani da lokacin da nake makarantan Allo, fuska cikin fuska ya dubeni sannan ya takarkare da mahaukacin dariya mai matukar amo, ba shiri na sanya yan yatsuna na toshe kunnuwana sakamakon yadda naji dodon kunena na neman agaji
.
Sai da yayi dariya mai isarsa sannan ya dubi haseena yace
"Budurwan sirri, wai dama wannan dan tsakon ki ka je kika samo, ai nayi mai girma ina laifin ki samo dai dani, "
Ya nuna ni da yatsa batare daya kalleni ba sannan yacigab da magana da muryansa mai kama dana jaki
"Ina mai tabbatar maki da cewa nine zan aureki ,kuma nine nan zan lashe wannan gasa wacce zamu kara wata mai zuwa ni da wannan dan kwaron "
.
Duk da cewa ina jin tsoron wannan basamuden aljani wanda bansan sunansa ba , ai koda naji irin kalaman dayake furtawa ga haseena sai na fahimci cewa shine SALMAN, nan take na nemi tsoron dana ke mai na rasa cikin kunan rai na daka masa tsawa
"Kai Aljan mutun bisa kanka, girman jiki bashi bane ke nuna cewa mutun yana da karfi, to kayi sani nidin dai daka raina da yardar Allah sai na baka mamaki" ai sai dana gama furta maganar sannan nayi nadamar furtawa
Domin kuwa alokacin fuskar aljani salman ta yamutse , yadda kasan an aiko masa da sakon mutuwa,
.
Badon ina da dauriya ba da babu abunda zai hana ban tsiyayo fitsari ba kasancewar irin kallon danaga yana yimin
Cikin kunan zuciya ya daga girjejen hannunsa mai kama da tabarya da nufin ya zabga min mari, rufe idanuwa na nayi don kuwa nasan babu makawa zai aikata, ko kadan banyi kokarin kare kaina ba ta hanyar rufe fuskata don nasan muddin hannunsa ya taba jikina to take zan baje a kasa sumamme ko matacce
.
Cikin sauri haseena ta daka masa tsawa wanda ya sanya shi tsayawa cak tace "salman izan ba kana son kaaga fushina bane toh ka gaggauta barin wajennan , in kuwa ba haka toh zakayi daana sani wanda ba zai maka Amafani ba, "
cike nake da tsoro kamar ace kyat na ruga na dubeshi a yayin da ya dunqule hannunsa ya naushi kasa , a hassale ya tashi sa'annan a dubeni yace "ka shirya nan da wata daya bil'adama maza bisa kanka," yana gama fadin hakan sai naga manyan fuka fukai guda biyu sun fito daga bayansa cikin kankanin lokaci ya tashi sama ya luluka cikin gajimare
Na dawo da dubana ga haseena tambayoyi fal bakina
.
Murmushi tai min wanda shine ya mantar da ni dukkan wannan tambayoyi dana ke shirin jera mata su
Tace "nasan ka tsorata da Al'amarin Salman amma karkadamu akwai wanda zan kaika wajensa ya koyar dakai fada da kuma yaki"
.
"Toh" kawai bakina ya samu fadi a yayin da muka cigaba da hirarmu in ka ganmu sai ka rantse mun yi shekaru da ita, na saki jiki sai zuba zance nake

******
.
Washe gari tunda sassafe wayannan yan mata uku suka sake zuwa kirana sai de yau dukkansu sun canja kayan dake jikunsu irin kayan dana sanya jiya shi na sake sakawa duk da ban san wanda yake kawo mani kayan ba hakan bai hanani sakawa ba
.
Wannan karon ba yalwataccen lambunnan muka nufa ba wani bangare ne daban wanda kallo daya naiwa bangaren nagane cewa mutane ba su cika shiga wajen ba duba da yadda naga wajen yayi kura, kuma yanan gizo gizo duk ya gauraye rufin wajen,
.
Muka iso bakin wata kofa mai kauri wacce aka sana'antata da zallan bakin karfe daya daga cikin matannan ce ta ciro wata tsohuwar kubba daga jikinta ta zura a cikin dan siririn ramin dake jikin kofan sannan ta murda
Dan karamin dakine mai dauke da kayan tarkace iri iri , a karshen bangon dakin muka hango ta naayi mamaki kwarai da ganinta anan
.
Na kariso ni kadai a yayin da yan mata ukunnan suka tsaya a bakin kofan dakin rufe kofar dakin sukai
Na budi baki zanyi magana haseena ta dora yatsanta a kan lebbana alamar nayi shiru ta nufi wani kusurwan dakin daban wata tsohuwar tayan keken doki naga ta daga, ta kama wani katako ta murda shi
.
Nan take jiri ya fara dibana sakamakon yadda naga dakin yana juyawa da sauri haseena ta ruko hannuna sannan itama ta rike wani karfe , kafin kace kwabo sai dakin ya runga juyawa dukkan tarkacen nan suka fara tashi sama suna haduwa da junansu, baki kawai na saki ina kallon ikon rabbi, sai da gaba dayan tarkacennan suka gama hadewa waje guda suka dunkule kaman dunkulin magi
.
Sai da suka gama dulkulewa tukunna sai kuma dunkulin ya fara fitarda yar karamar kofa, kan kace kwabo har wannan dunkulin ya canja siffa izuwa na Kofa,
Babu abunda zai baka mamaki ma kaman yadda kofan ta kasance sai haske take tana daukan idanu
.
Adai dai lokacinne dakin ya daina juyawa komai ya tsaya cak sai a sannan haseena ta ce "wannan shine babul hajir, ta cikin wannan kofa zaka iya tafiya ko ina a doron kasa, tun daga kan duniyarku har zuwa wasu duniyoyinma,"
.
Shiru kawai nayi na saki baki ina kallonta ni yanzu ma har na saba da abubuwan mamakinsu koda na gani ma banayin mamaki sosai kamar yadda nake a baya
.
Ta ja hannuna wanda hakan yasa nima nabi bayanta bakin kofan muka zo muka tsaya ta sanya lallausan hannunta ta bude kofan sai a sannan dukkan wani mamakina ya karu domin kuwa babu komai a gaban kofan banda hazo daya ke gittawa lokaci lokaci, banga alaman wani abun ba
.
Haseena ta jani muka shiga cikin kofan ai sai dukkanmu muka ji kamar mun fado daga saman wani katon tsauni ne, saboda tsaban firgici kulle idanuwana nayi yayin da muke fadawa kasa iska sai gittani yake ta ko ina hakan yasa na saki wata kara
.
Kamar daukewan wutan nepa sai mukaji mun fado a cikin wani rami, abun da ya kara dauremin kai shine da kafafuwanmu muka fado kuma ko dan zogi banji kafata tayi min ba
.
Haseena tai murmushi "tace haka ka iya ihu dama ban sani ba, ai kuwa sai ka tanadi wani ihun da yafi wanda kayi a baya, domin kuwa yanzu ne za'afara ainahin tafiya" cikin sigar zolaya ta fada
Na sosa keyana "ai ni kaina ban san lokacin da na saki ihun b....."
Wani kara ne ya katse mani maganata karan kuma daga kasan inda muke yake fitowa sai a sannan na daga kaina na kalli sama
Gani nai tamkar mun fada cikin rijiya gaba dubu ne
Ban gama wannan tunanin ba kasan wajen ya wawake take muka fada ciki amma wannan karon a tsaye muka fada kuma ahankali muke sauka kasa,
Cikin wani daji mai yawan guntayen bishiyu muka sauka , sosai yanayin dajin ya burgeni dukkan wasu ganye na dajin jane maimakon kore mun danyi gajeriyar tafiya da kafafunmu sannan muka riski wani Bukka irin na mutanen da shi kansa bukkan da jajayen itace aka sana'anta shi, bakin bukkar muka tsaya sannan haseena tai sallama, wata tsakurarriyar muryace ta amsa sallamar, daga bisani sai wani dattijon Aljani ya fito daga bukkar yana sanye da dogon yar shara har kasa sam sam fuskarsa bata nuna alamar tsufa ba ,zai yin kama da saurayi mai jini a jika
Har kasa ya zube yayi gaisuwa wajen haseena ta durkusa ta dagoshi tace "baba zaikid nasan dai basai na maka bayanin abunda ya kawoni wajenka ba, amma duk da haka zan sake maimaitawa, wannan shine Mijin nawa In Allah ya yarda ina so a cire masa dukkan wani tsoro na jinsun mu kuma ka koya masa dukkan wasu dabaru da salon yaki, nan da wata daya zan dawo na daukeshi"
Murmushi tsoho zaikid yayi "an gama ranki shi dade"
Ni dai na cika da mamaki ainun jin cewa wai ni za a cire ma tsoro sannan kuma wai za a koya min yaki da dabarun fada
Haseena ta dubeni a lokacin da fuskarta .......

Kwana biyu kun jini shiru
Bani da lafiya ne shi isa
BUDURWAN SIRRI
Marubuci Shuraih Usman
@hausaebooks.cf
@shuraih 99%
Page 7
.
Haseena ta dubeni a lokacin da yanayin fuskarta ya sauya , ta kankame hannuna sosai tace" shuraih muddin muna son mu rayu har abada amatsayin mata da miji toh dolene ka koyi wasu abubuwa na yaki, da kuma ka kuma cire tsoro a zuciyarka, ina matukar sonka irin son da baki ba zai iya fasaltashi ba, hannu ba zai iya rubutashi ba ko na dakika daya bana son rabuwa dakai, amma dole na na barka anan domin ka koyi yadda zaka kare kanka daga sharrin Salman"
.
Har na budi baki zanyi magana sai ta sanya yatsanta a akan lebena alamar nayi shiru ba musu nayi shirun duk da irin tarin tambayoyin dana ke shirin jefamata
Ta dan ja baya kadan sannan ta soma tafiya har tayi nisa idanunawana suna kanta ta juyo muka hada idanu ta sakarmin murmushi daga haka ta cigaba da tafiyarta har ta bacemin da gani ina nan tsaye a gun
.
Tsono zaikid ya dubeni da kyau yace "yaro shin meye sunanka"
"Shuraih" na bashi amsa batare dana kallesa ba haryanzu idanuwana na kan hanyar da haseena ta bi
Tsoho zaikid ya sha gabana sannan ya turbune fuska yace "shuraih kake ko wa to bari kaji Abunda kazo yi nan shi za kamai da hankalinka gareshi , domin kuwa in kai wasa toh kana ji kana gani ta rabu da kai kenan"
Sosai hankalina ya tashi da maganganun wannan tsohon
Batare daya jira amsana ba ya juya ya shige cikin bukkarsa yana cemin" ka dai shirya don kuwa daga gobe zamu fara atisaye "
....

Har magriba ta gabato banga alamar tsohon nan zai fito ba hakan ya sani ta shi na kwankwasa kofan bukkar daga ciki muryan tsohon naji yace "ya akayi ne"
"Yun wa nake ji ,kuma gashi dare ya fara yi baka bani makwanci ba" na fada
Sautin dariyarsa naji alamar dariya yakeyi
"In tambayeka mana" ya fada
"Ina jinka "na bashi amsa
"A rana sau nawa kake cin abunci"
"Sau uku"
"Toh daga yau ka sanya a ranka kuma a jikinka baza ka sake cin abinci ba sai bayan kwana daya,kuma ka sani baka da abunci sai yayan itace"
Sosai na girgiza da jin batun tsohonnan
"To shi kuma makwanci fa"
"A nan zaka runga kwana kuma ka tabbata asubar fari ka farka yanzu dai ga ruwa kayi alwala kai sallah," ya jefo min wani batta na ruwa
Na karba nai alwala nai sallah daga nan na zube wajen durkushe duk da yanayin wajen yana da kyau kuma ko kadan babu kwari ko wasu muggan

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment