Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dabbobi masu cutarwa a cikin dajin domin kuwa tunda muka shigo dajin kawo izuwa yanzu bamuyi gamo da wani abu mai rai ba
.
Haka na kwanta akasa kan ciyayin dajin masu tsananin laushi duk da ya kasance ina rawar dari saboda sanyi da nake ji, bai hana bacci daukata
Ba
.
A fiirgice na farka sakamakon jin an kwara min ruwa da nayi waige waige na fara yi don ganin mahalukin daya kwara min ruwa dan tsakurkurin tsohon ne dai a gabana ya bata rai yana rike da wasu mayan mangala guda biyu
Ya ce"shin jiya ban sanar dakai cewa asuban farko taimaka a farke ba, shine ka shagala har asuba ta biyu baka tashi ba"
Bai jira cewana ba ya jefo mani mangalolin nan masu dan karen nauyi da kyar na iya cafe guda daga cikinsu
Yacigaba "maza maza ka tashi ka tafi wancan kogin yai nuni da hannunsa zuwa wani gefe dabam, ka debo ruwa ka runga zubawa anan ya nuna mani wata katuwar rijiya wadda tun zuwana wajen ban lura da ita ba
.
A kasale na tashi na rarumi mangalalolin na nufi inda ya nuna mani nayi tafiya mai dan karen nisa kafin na iso bakin koramar na zauna kan daya daga cikin mangalolin nan ina hutawa bayan nagama hutun ne na cika mangala daya da ruwa sannan na kinkimeta da kyar da sidin goshi na dorata akaina irin nauyin danaji akaina yafi kama da na Mota ko wani katon dutse a daddafe da kuma ikon Allah har nakai bakin rijiyar na zuba ruwan na sake komawa rafin kai in takaice maku sai wajejen la'asar na idda kai ashirin din daya ce na zuba, na samu waje na baje a kasa ina numfashi sama sama alamar na jikkata naji karar budewan bukkar tsohon ya zo ya tsaya daidai gabana sannan ya bushe da dariya yace "kai amma bil'adama da ragwanta suke yanzu wai dan wannan aikin shine har da numfarfashi sai kace wanda yai aikin azo a gani, maza ka mike tsaye"
A daddafe na mike tsaye don kuwa tun da nake a rayuwata ban taba yin wani aiki mai wahala daya kai wannan ba
.
Yanzu kam da sauki tunda dai na dan rage nishin da nake tsoho zaikid ya shige cikin bukkarsa yadan dau lokaci kafin ya fito rike da sanduna guda biyu, sandunan dogayene sosai don kuwa sunyi tsayina biyu
Ya jefo mani guda daya duk yanda naso na cafe ta amma na gagara saboda irin saurin zuwan da tayi sai gashi sandan ta wuce ni tamkar walkiya , ta sauka nisa dani tsoho zaikid yayi murmushi "
Maza kaje ka daukota"
Ba musu na nufi wajen da sandar take ina zuwa na sanya hannuna da nufin na rabata da kasa amma sai wani nauyi ya ziyarci hannuna ji nai tamkar na ina kokarin daga katon dutsene na daddage na tara karfina har ina nishi na daga sandan daga kasa na kafata tsaye , sai nishi nake haka na fara jan sandan a kasa har na kawota wajen tsoho zaikid,
"Da alama wannan tayi ma nauyi toh bani ita ka amshi tawa"
Ya karfi wannan daya bani ya kuma mika mani nashi da sauri na karfa don dama ni nasan kuskure yayi wanda ya kamata ya bani shike hannunsa , ai mugun nauyin danaji shi yasa na saki sandar ta fadi a kasa don kuwa hartafi waccan dinma nauyi tsoho zaikid yai kasake yana kallona kafin yace "muddin zaka runga yimasu irin wannan daukan toh baza ka taba iya rike koda daya daga cikinsu ba"
"Yaya kake so na dauka toh"
"Kasanya a ranka cewa zaka iya , sannan kana nan ne kawai don BUDURWAN SIRRI, haka kuma ka cire tunanin duniyarku daga ranka ka dauka tamkar a gidanka kake, sannan ka tausasa zuciyarka, a natse zaka ji mamaki ainun don kuwa ba wannan sandan ba hatta wancan tsaunin zaka iya yin gamo a dora maka shi"
Nai kasake ina kallonsa yayin da na kalli tsaunin daya ke nuna mani a zuciyana nace "toh ko nine ILYA DAN MAI KARFI sai haka"
.
Na nufi sandan nayi tamkar yadda yafada na rufe idanuwana na shafi sandan da hannuna na kama na daga cikin matukar mamaki sai naji tamkar na dau fallen takarda don kuwa ko kadan sandan bata da nauyi yanzu na juya na dube shi yai mani murmushi yace "shin yanzu ka yarda da magana ta"
"Shakka babu na yarda"
Daga nan ya fuskanceni yace "daga yau zamu fara darasin mu na koyan fada , da kuma yadda zaka kare kanka,
.
Ya koyar dani abubuwa da dama a wannan rana don kuwa in ba sallah ba babu abunda yake tsaida mu, da shike ina da saurin daukan abubuwa , har magariba tayi ya ce mani "je kai sallah ka kwanta kuma gobe ka tabbatar kafin safiya ka gama diba ruwanka nai godiya sannan nai wucewata izuwa inda na kwanta jiya
*******
Kwanaki suna ta wucewa tamkar yadda takarda ke zukar ruwan biro yau saura kwana daya wata daya ta cika,
A cikin wayannan kwanakin na koyi a bubuwa da dama, dun kuwa ji nake babu wanda ba zan iya tunkara ba yanzu batun tsoro kuwa babu ita ,
Tunda kuwa ni da kaina nake fada da manyan zakuna da kadoji kuma na kai su kar
.
Shi kansa tsoho zaikid yana mamaki ainun da saurin daukan fada na, kaman kullum yauma muna filin koyon fadanmu ni da tsoho zaikid sai fafatawa muke in ka ganmu a lokacin sai ka rantse wasu a bokan gaba ne domin kuwa kowannenmu burinsa shine yaga ya cutar da dan uwansa, ni dai na dage sai kare hare haren tsoho zaikid nake wanda shi kuma ya kufula ainun ganin sam bana kawo hari, sai da muka shafe wasu sa'o'I kafin ya samu nasarar buguna da sanda akafa nan take kafana ta gurde amma saboda juriya irin nawa sai na dake na kama kafar na murda ta sai ta dawo dai,a lokacinne na fusata na fara kaimai hari ba kakkautawa kan kace kwabo sai ga tsoho zaikid a kasa wanwar sakamakon bugunsa da nayi da sanda akansa
.
A gigice na nufeshi na tallabo kansa ina mai bashi hakuri yayi murmushi sannan yace "lallai na yarda yanzu kam ka kawo karfi ina son ka shiryaa don kuwa gobe BUDURWaN SIRRI zata zo ta dauke ka"
Na gyada mai kai ina susa keyana
*******
Washe gari tunda sassafe na iddar da debo ruwana don kuwa yanzu ji naake tamkar zan iya diba kai dubu ma,
Nai sallah sannan na taho kofan bukkan tsoho zaikid na tsaya ina nan tsaye a wajen har gari ya waye,
Tsoho zaikid ya fito daga bukkar hannunsa rike da sanda guda, na dubesa da mamaki don kuwa a kullum da sanduna biyu yake fitowa ya zauna kusa dani yace "shuraih ka tashi lafiya"
"Lafiya lau"
Daga haka ban sake magana ba
Kaman a mafarki sai naji muryan haseena tana gaida tsoho zaikid na dago kai na dubeta da mamaki don kuwa shi kansa zaikid bai san lokacin da ta zo ba iyaka dai jin muryanta yai har kasa ya rissina ya gaiisheta sannan ya nuna ni da hannu yace "ranki shi dade yanzu matsoraci kuma ragon bakon ki ya juya izuwa jarumin saudauki wanda sam baya jin tsoron komai gaba dayan tsoronsa sun juya izuwa naciya da juriya"
Tai murmushi wanda ya sake fitta kyawunta ta matso kusa dani ta kama hannuna da mamaki sai naga hawaye akan idanunta
"Shuraih kayi hakri nasan cewa na cuci rayuwarka na sanyaka a kunci sakamakon son zuciya da sonkaina, kana zaman zamanka a duniyarku na daukoka na kawo ka nan gashi yau a kaina ka...."
Na yi sauri na dora hannuna na rufe mata baki sannan nace "yana daga cikin rukunan imani yadda da kaddara mai kyau da mara kyau, wannan mukaddari ne bayin ki bane kuma ki sani muddin ina numfashi a doron kasa ba makawa sai na aureki bana tsoron mutum bare Aljan, ni kawai abunda nake bukata dake yanzu shine mu tafi izuwa filin wannan gasa domin na nuna ma salman cewa DAN ADAM HATSABIBI NE,
Babu abunda baya sarrafawa komai girmanta koya takai da cutarwa"

*********
Zaune naake bisa wata lallausan kujera yayinda haseena take fuskanta ta
Kura mani idanu tayi bata ko kiftawa nim dai idanuwana akan nata suke, cikin kwayan idanunta babu digon baki sai wani digon jaja ja, haka nan naji ina matukar farin ciki tun ma bamuyi gasan ba
Tace "shurai nasan cewa kana da tarin tambayoyin da kake son kai mani musamman ma akan wannan suna daka ji ana kirana wato BUDURWAN SIRRI, toh yau zan baka amsar dukkan tambayoyinka
.
Toh fa
Nasan ku kanku kuna son jin labarin budurwan sirri kui kasake da kunnuwanku
BUDURWAN SIRRI
Marubuci Shuraih Usman
@hausaebooks.cf
@shuraih 99%
Page 8
.
"shurai nasan cewa kana da tarin tambayoyin da kake son kai mani musamman ma akan wannan suna daka ji ana kirana wato BUDURWAN SIRRI, toh yau zan baka amsar dukkan tambayoyinka"
Nai murmushi "ni tambayata guda ce itace wannan suna dana ji ana kiran ki da ita BUDURWAN SIRRI, shin meye ma'anarta"
,
Haseena tai murmushi sa'annan tace "kaman yadda na baka labari a baya cewa mahaifina acan duniyarku yai aure kuma bil adama ya aura, nasan cewa kana mamaki inda har Aljani ya auri Bil'adama toh kama daina don kuwa jinsi ne kadai ba daya ba, domin kuwa a zamanin da Aljanu da yawa sun auri bil'adama haka suma Bil'adama da dama sun auri Aljanu sannan suka hayayyafa,
Hakance ta kasance da mahaifina bayan an haifeni na kasance kyakkyawa wacce babu kamarta a duk fadin wannan duniya tamu , hakan yasa yayan saraku da Attajirai sukai ca akaina kowannensu yana so aureni ni kuma duk cikinsu babu wanda ya kwanta min arai hakan ce tasanya na ki amince masu,
A kudancin duniyarmu a akwai wata babbar birni na Aljanu ana kiranta da BULZUM sai de su Aljanun sun kasance kafirai ne kuma matsafa, sarkin birnin azzalumine sunansa RAVA yana da 'da daya tilo daya haifa mai suna bishmalu, sarki rava yana son bishmalu sosai hakan ce tasa duk wata bukata da bishmalu ya nema duk wahalarta duk tsaurinta sai sarki rava ya biya masa ita wannan tasa shima bishmalu yake son mahaifin nasa sosai,
Bansan tayadda akayi har bishmalu yaga fuskata ba, sai ganin dan aiken sarki rava mukayi yazo har fada da mummunar wasika wasikan da ta zama sanadiyan mutuwan rabin Aljanun wannan gari namu, "tana zuwa daidai nan ta fashe da kuka
Banyi yunkurin hanata kukan ba cikin sheshsheka ta cigaba "mahaifina ya karbi wasikan ya bude shakka babu daya san abunda yake cikin wasikan nan toh da bazai bude ba, yana budewa sai wani farin hayaki yai fitar burgu daga cikin wasikar da ganin haka sai dan aiken daya kawo wasikan ya bace bat, ba afi minti daya ba sai gaba dayan fadan yadauka da dariya bakajin komai sai sautin dariyar sai da akayi dariyar sosai sannan wata kakkausar murya tafara magana "yakai wannan sarki kai sani cewa nine sarki Rava na birnin BULZUM musabbabin isowata wannan birni naka shine na nema wa Dana bishmalu auren zukekiyar yar nan taaka, bijirewa umarnina zai janyo da mugun tashin hankali ga Al'ummanka, don haka ina umartarka da ka gaggawar fitowa da ita don na kaita ga dana"
.
Hankalin mahaifina ya tashi , ya dugunzuma cikin muryan fada "kai kana ganin wanene kai da har zaka zo har birnina kuma cikin fadata sannan ka dau yata ,toh kai sani cewa mu ga Allah muka dogara, babu abunda ka isa kai mana ,"
Muryan ya bushee da dariya "dama an sanar dani cewa kana da girman kai, kuma sam ba zakai mani biyayya a bisa kudirina ba, kuma tun fil azal dama ina da muradin na murkushe wannan birni naka da dukkan wasu aljanun da suke ciki
Amma bokana ya haneni ga aikata hakan
Toh yau kai sani sai Rabin mutanen wannan birni sun ziyarci lahira,ziyarar da baza su taba dawo wa ba"
.
Kamar daukewan ruwan sama sai muryan ta dauke dif tamkar bata taba wanzuwa ba,
Mahaifina yaa koma kan karagarsa ya zauna yai tagumi yana tunani
Bayan dakika dari da hamsin sai ga wani badakare ya sukwano a guje akan dokinsa
Badakaren bai tsaya a ko'ina ba sai gaban sarki gaba daya jikinsa ya baci da jini, kallo daya zaka mai kasancewa a firgice yake
Wani dogari ya daka masa tsawa "kai meyafaru ne muka ganka haka, shin ina sauran abokan aikinka masu tsaron gari"
"Wata muguwar masiface ta afku a cikin gari ranka shi dade , rayuka da yawa sun hallaka gidaje da dama sun ruguje, kana nun yara,mata,samari da tsofaffi dukkansu sun rasa rayukansu"
Badakaren ya fada ayayin da yake numfarfashi
Sarki ya mike tsaye cikin firgita da dimaucewa ya ce "menene ya faru da su"
"Muna aikin bada tsaro a cikin babban kasuwa , mutane sai cinikaiya suke , yara,maza,mata,tsofaffi suna ta zirga zirga cikin yanayin nishadi
Kwatsam sai mukaji wata kara daga karkashin kasa hakan yasa mutane sukai saurin barin wajen da karar yake fitowa mu kuma muka durfafi wajen cikin shiri,
Kasan wajenne ya tsage tamkar an saka wukane aka tsargeta, wani mummunan halitta ne ya fito daga cikin kasan halittan babbane don kuwa tsayinsa yafi na gidajenmu sau goma, halittan yana da kaho guda akan goshinsa sai ido daya rankwalele daya ke gefen hancinsa
Hannunsa na rike da wata katuwar Al'amudi wacce inda mutum dari zasu taru baza su iya rabata da kasa ba,
Ai nan take sai wannan halitta ya hau ruguza gida jen mu duk abunda ya duka da al'amudin dake hannunsa sai de kaga ya ruguje hakan yasa muka cire tsoro muka far masa muka runga sara da sukan sassan jikinsa,
Sam ko yasan munayi, cikin kankanin lokaci ya gama rushe rabin godajen birnin nan sannan ya hau Aljanu , duk aljanin daya taba da Al'amudin hannunsa sai kaga ya zama toka mun tsorata ainun da lamarin wannan halitta, gaba dayan Askar din daka hadani da su sun halaka ni kadai ne kawai na tsira"
Askar din ya karasa maganarsa yana aman jini
Hankalin mahaifina ya tashi ainun
Hakan yasa sukai sauri suka garzaya cikin gari domin ganin barnan da halittan tayi,
.
Abun da suka gani ya basu tausayi sosai
Gidaje sama da Dubu sun rushe, Aljanu sama da dubu sun halaka, sama da dari biyar sun ji munanan Raunuka, kowa sai neman taimako yake
Anan take mahaifina ya fashe da kuka ,yana cikin kukan ne akaji wata kakkausar murya ta bushe da dariya sai tai mai isarta sa'annan tai shiru askarawa da yan majalisu sai waige waige suke ko zasu ga ta wajen da muryan ke futa,
Muryan ta cigaba da fadin "ayanzu ina amfanin Gardama, Ayanzu ina Amfanin girman kai, da a ce ka yarje da bukatata da duk wannan abu bai faru ba, na rantse da karfin mulkina muddin ka ce baza ka aurawa dana yarka ba, toh nan da shekara mai zuwa sai irin wannan bala'I ta kara samunku, kuma kai sani cewa na gaba ba gidaje da jama'a kadai zai kashe ba 'a'a gaba dayan birnin ne zai Kone ta ta koma Toka,
Gargadi na karshe da zan maka, ka daukesa a matsayin Doka ko umarni duk wani Talikin daya sake Kiran HASEENA da sunanta sai de wani ba shiba , da ga yau saide ku runga kiranta da BUDURWAN SIRRI, don kuwa ita ta kasance mai matukar rabo da sa'a da har zata auri dana,na baka nan da shekara daya muddin baka aiko da yarka zuwa marautata ba toh duk abunda ya faru daku, kui kuka da kanku"
Muryan na gama fadin hakan sai ta dauke dif tamkar an zabga ruwan sama an dauke
.
Gaba dayan yan majalisan suka hau mahaifina suka suna cewa akan mace daya jal, an rasa dubban rayuka anyi asaran Arziki mai yawa mai zaisa ba za a bashi ita ba ko dan a kare bala'in da ke tunkararmu, shi de mahaifina shiru yayi yaki tanka masu
.
Yana dawowa gida ya shige turakarsa babu wanda yasan me yake a cikin turakansa din,
Washe gari da sassafe na nufi turakar mahaifina ko kwankwasa kofan ban yi ba nasa kai,
Na sameshi a zaune bisa kan sallaya alaman ya iddar da sallah kenan
,
Koda mahaifina ya ganni sai na ga kwalla suna gangarowa akan kuncinsa nai sauri naje na runugmesa ina mai fashewa da matsanancin kuka
,
Cikin shishshikan kuka nace "Abba ni na yarda na amince zan auri bishimalu , muddin hakan zai tsaida wannan masifa data ke tunkaromu, nasan cewa in na auri bishmalu Al'umma dayawa zasu tsira da rayukansu, da dukiyoyinsu"
"A'a yata kada kiyi saurin yanke hukunci, shi rayuwa da mutuwa dukka Allah ne yake yankesu, ki tashi yanzu kije ki kwanta, ayau dinnan zanyi istahara naga abunda Allah ya zaba mana"
Mahaifina ya fada cikin dakewa
,
Sum sum na tashi na fice daga turakar naje dakina na kwanta
************
Shin kuna biye dani kuwa fans
,
Alkalamin Shuraih Usman ne inkiya 99%
BUDURWAN SIRRI
Marubuci Shuraih Usman
@hausaebooks.cf
@shuraih 99%
Page 9
.
Washe gari da safiya naje na iske mahaifina a turakarsa domin jin abunda ya samu daga istaharan da yayi
,
Da sallamata na shiga cikin turakar na sameshi a zaune a wajen dana iskeshi jiya,
Ya dago kai daga kallon kasa dayakeyi yana mai amsa sallamata,
Na samu waje na zauna,
Mahaifina yayi gyaran murya sannan ya fara bayani "haseena hakika Allah ba azzalumin bawansa bane,
Jiya nayi istahara domin neman zabin Allah akan wannan mugun al'amari dayake tunkaro mu,
An nuna mani a mafarkina cewa wani Dan Adam ne kadai zai iya tseratar da mu daga sharrin sarki Rava, dolenmu muje duniyar mutane mu dauko wani yaro wanda bansan sunansa ba, sannan zamu dukufa wajen sana'anta wata makami wacce ba'ataba yin irinta ba a doron kasa, da taimakon wannan makami ne zamu samu nasaran murkushe Garin Bulzum, an nuna mani dukkan wani abun da zamu bukata wajen sana'anta wannan makami a cikin mafarkina, "
Yayi shiru yana mai dubana domin jin abunda zance
Cikin doki nace "toh Abba waye wannan shi Dan Adam din da zai kubutar damu "
"Bansan ko waye ba amma an nuna mani alomin da zan iya ganeshi, kuma kece da kanki zaki futa nemansa,"
Cikin tantama nace mai "toh amma Abba da wasu alamomine zan iya gane sa, ?"
"Alama na farko shine a lokacin da kuka hadu da shi hadari zai hadu, kuma zaiyi hatsari a babur har ya karye a kafansa na dama, a lama na biyu shine yana da makaken tabo a tafin hannunsa na dama, wayannan sune alamomin da zaki iya ganeshi da su, "
,
Daga nan mahaifina ya tsara mani dukkan wani shiri da kuma tsari na yadda zanyi na daukoka daga duniyarku, harda irin shirin da zamu shirya maka"
Haseena tayi shiru tana dubana a lokacin da mamaki da Al'ajabi suka dabaibayeni, nama rasa tacewa
Haseena ta cigaba
"Inhar bazaka mantaba shuraih akwai wani lokacin da ka taba yin hatsari har ka karye a kafarka ta dama, tun daga wannan lokacin na lura da tabon dake tafin hannunka, wannan yasa na daukoka tundaga duniyarku na kawoka nan dun ka taimakemu , shi kansa SALMAN shirine muka hada amma babu wani burbushin soyayya a tsakaninmu , "
Sai ayanzu na gane dukkan manofofi da inda maganar haseena BUDURWAN SIRRI ya nufa iyayena,abokaina,kasata,mahaifana duk na rabu da su akan mace guda wacce a tunanina tana Sona da gaskiyane, tabbas na kamu da kaunarta irin kaunar da bazan iyya rayuwa imbabu ita ba,
Irin kaunar da zan iya sadaukar da duk abun dana mallaka don ita
Irin kaunar da zan iya bayar da rayuwata don ceto nata amma ashe ita ba kaunata take ba,
Bansan lokacin da kwalla suka fara zarya akan kumatuna ba, haseena ta budi baki da niyyar ta sake furta wata kalma
Cikin gaggawa na daga mata hannu alaman bana son sake jin wata magana daga bakinta na tashi tsaye fuskata ta sauya lokaci guda numfashina ya fara fita da sauri, zuciyata na tafasa nace da ita
"Babu komai haseena NAJI NA GANI zan taimaki Al'ummanku da duk wata taimako da kuka nema daga wajena, amman bai kamata ......"
Sai kuma nai shiru ga barin maganar duk da naso na furta wata magana amma na fasa
kwalla ne suka kara gangarowa daga idanuwana ,
Na lura da haseena sai kallona takeyi tana son tai mani magana amma ganin irin yanayin dana ke ciki yasa taja bakinta tai gum
.
Jiki ba kwari ta fice daga dakin,
Wani tsatsauran ciwon kaine ya fara ziyartar kwalkwata , na dafe kaina ina mai runtse idanuwa , babu abun da idanuwana suke hango mani face kyakkyawan suran nan na haseena , madaidaicin bakinta wanda baya rabo da murmushi , suke ta zarya a cikin kwalkwata,
.
A haka bacci yai awon gaba dani
Bani da farkawa ba sai cikin dare koda na tashi na bude kofa na fice daga dakina, iyanzu kam na gane cewa haseena ba kaunata take ba, na gane cewa haseena ba sona take ba duk wasu abubuwa da suka wanzu a baya duk yaudarace don na biya mata bukatarta, nai murmushin takaici bisa ganin irin wasa da hankalina da tunanina da haseena tayi
,
Na mike wata hanya wacce zata sadani da babban falon fadan, cikin yan mintuna na isa falon kaman yadda na zata hakan take Al'umman aljanu ne cikin shigar mutane suna ta harkokinsu, na nufi wata kofa na bude
Hasken rana yai wa idanuna maraba,
Na fice daga falon na nufi farfajiyan masarautan ina mai kallon irin salon da akai amfani da shi wajen ginin gidan,
Kai tsaye babbar kofar fita daga Gidan na nufa bansha wahala ba wajen tuhuma ta da masu gadi sukai, daga baya suka bani hanya na fice daga gidan sarautar gaba daya,
Ni kaina bansan me ya futo dani ba kuma bansan dalilin fitana ba ni dai na tsinci kaina ina mai
Tafiya nake ina mamakin irin ginin gidajen Garin, kwata kwata tsawon ginin bazai wuce kamu goma ba , kuma da zallar zinare suka sana'anta gidajen,
Gaba dayan gidajen suna kamanceceniya da juna
Sa'I sa'I nakan cimma jama'a suna harkokinsu baki kawai nake saki ina kallonsu duk daya kasance Aljanu ne amma ba zaka taba iya banabacesu da mutane ba
,
Ina cikin tafiya ban aune ba sai jin wata kakkausar murya nayi ta kwala mani kira
Shakka babu na taba jin wannan murya, na juyo don ganin mai kiran nawa
Salman ne na gani yana falfala a zabababben gudu a bayansa akwai wasu askarawa su hudu dukkansu suna masu falfala gudu don cimmini
Cikim yam dakikoki suka iso gabana salman ya dubeni murmushi dauke a kan fuskarsa yace
"Shuraih! Fitarka daga masarauta yana da hatsari sosai, don kuwa akowane lokaci sarki rava zai iya kawo ma ziyara don ya dade da jin labarinka"
**************************************
.
Ina zaune a gaban mahaifin haseena kaina ya na kallon kasa , yan majalisan sarki suna kewaye da shi kaman kullum
"Shuraih kai hakuri bisa rabaka da mukayi da iyayenka da kasarku, sannan muna rokonka daka taimakemu daga masifan dake tunkararmu"
Maganganunsa ne suka sanya na dago kaina ina mai dubansa, acikin zuciyata nace toh waishin ni da ban kwarance wajen fada ba tayaya har zan iya taimakonsu,
"Nasan kana mamaki da jin cewa da mukai kaine zaka iya taimakonmu ka tserartar damu daga halaka da iznin Allah SWT"
Salman ya fadi sannan yaci gaba "kamar yadda budurwan sirri tai maka bayani, ajiyane muka karashe aikin sana'anta wata makami wacce ba'ataba sana'anta makamanciyarta ba a doron kasa, wannan makamin tamkar nakiya take saide ita tana aikine kawai akan jinsin Aljanu , Gobe da safe zakaayi shiri mu baka wannan makami ka nufi garin Bulzum ka dasa ta "
,
********
Shuraih ! Shuraih !! Shuraih!!!
Muryan mahaifiyata na tsinkaya da sauri na futo daga cikin dakina na
A tsaye na taras da ita a kofan dakin
"Kazo wata ce tazo wajenka"
"Toh mama"
Amsar dana iya bata kenan
Na mike na nufi kofan dakina
Turus nayi ina kallonta murmushin dake fisgo zuciyata gareta dauke a kan lebbanta,
"Haseena !"
Firgigit na farka daga nannauyan baccin dayai awon gaba dani dazu, nan take dukkan abubuwan da suka faru dani suka fara dawowa cikin kwalkwata sai ayanzu naji ina matukar kewan gida, na tuna da mahaifiyata inna mairo,
"Kwab kwab kwab"
Karan bugun kofa ya katse mani tunanina
,
Na tashi naje na bude kofan
Tsaye a gabana cikin kayan daana saba ganinsa ,
Fuskarsa sai murmushi take tamkar wanda aka mai kyautan Aljanna,
"Kayi sauri ka shirya, maimartaba na nemanka "
"Toh "kawai na iya cewa
Cikin yan mintuna nai wanka na shirya cikin wasu kayan dana taras da su akan katifa
,
Nayi mamaki ainun da ganin kayan, bakin suite

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment