Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


ARANAR SALLAH
Marubuci:- Shuraih Usman
2017
Publish:-shuraih 99%
ARANAR SALLAH
Kagaggen Labari
Shuraih 99% & mijin biza
NA
Shuraih Usman
Part 1
.
$
Tsaye nake a kofar bayin gidanmu, na daura tawul a
jikina , yadda wannan tawul din ya samu nasarar rufe
mani daga cibiyata izuwa guiwowin kafafuna .
A gefena kuwa bokiti ce cike da ruwa , hannun
damata na rike da kwandon soso, a yayin da dayan
hannun wato hannun haguna na dunkulata sannan
sa'I sa'I nakan naushi gini bayin da dunkulallen
hannuna cikin bacin rai.
.
Ba komai yake sa nake naushin ginin ba illa batamin
rai da yayana yayi.
.
Shi yayana mai suna Abdul, ya kasance A duk lokacin
daya shiga bayi yin wanka ,ko fitsari ko kuwa bayan
gida
Toh fa akalla yana shafe rabin awa bai fito ba
Sai ka rasa me yake yi acikin bayin.
.
Kamar kullum ma .yau gashu yana neman ya zaftare
awa daya (1h).
Kamar daga sama sai naji karar budewan kofa ainan
take cikin zumudi na mike na dauki bokitin ruwana
ina jiran ya fiti in sa kai.
Can sai ya leko da kansa yace dani
"Yauwa shuraih ,dama sabulun wankana ne ya kare
dan Allah dan taimakeni da taka "
.
Wani kullun kululun bacin raine ya takale min a
magogoro na yamautsa fuska tamkar zanyi kuka nace
"Yaya Abdul dama baka idar da wankan ba"
"Eh wallahi ina kanyi ke nan sai sabulun ya kare dama
guntune sabulun" yabani amsa
Mika mai sabulun nayi batare da gardama ba
A kalla dai sai daya shafe kusan Awa daya da rabi
sannan ya fito.
.
A gurguje nayi wankana na fito , ina fita ban zame
ko'ina ba sai dakina
Ina kan shafa maine wayata kirar blackberry ta dau
ringing ina dauka sai naji muryar mujahid(mijin biza)
Anan yake sanar dani nayi sauri gashinan tahowa
,agurguje na kammala shafa mai, sannan na dauko
wata rigata zariya fara sol, daidai guiwa na buga, na
sanya wandonta sannan na dauko babbar riga wacce
ta kasance na dinkin ne itama,
.
Ko karyawa ban tsaya yi ba a sakamakon saurin dana
ke da kuma farin cikin daya Addabi zuciyata ,
.
A ranar yau Babbar ranace ga duk wani musulmi
dake doron kasa baki daya , don babbar ranace
wacce A shekara sau daya tak take fita wato
A RANAR SALLAH
Eid el kabir/ma'ana babban Salla,
.
Toh ya zata kasance a wannan rana shin wata iriyar
ce zata afku .MAI KARATU KA BIYO Shuraih 99% a
labarin
ARANAR SALLAH
Kagaggen Labari
Shuraih 99% & mijin biza
NA
Shuraih Usman
Part 2
.
,
Na fito bakin titi na tsaya a yayin da mutane ke ta rafka sauri don su isa masallacin eidi.
.
Wasu kuwa a babura suke wucewa yayin da wasu a motoci suke wucewa.
.
I na tsaye a bakin titin ne , A lokacin dana fara gajiya da tsayuwar.
Ji nai an kwala min kira "shuraih"
Duk da muryar a shake take amma na gane wanda ya kirani ,
.
Ina juyowa kuwa mukayi kicibus dashi, bawani bane illa mujahid , yana sanye da farar shadda dinkin babban gare
.
Yana karisowa wajena na mika mai hannu mu kai musabiha, can sai nace masa
"Sai yanzu kaga daman zuwa"
"No na tsaya goge ma hajiyata kayantane" yafada
Na dubeshi da kyau ina nazarin maganarsa don na riga na sanshi da Bula (karya)
.
"Toh mutafi koh" nace da shi
Ya dubeni cikin rashin fahimta yace
"Ina zamuje"
"Masallaci man, ko bazaka je bane"
"Me zai hanani tafiya " yafada a lokacin daya ke kokarin tare dan acaba
.
Akalla ya tare yan acaba kusan biyar kenan amma duk cikinsu babu wanda suka daidaita,
A sakamakon shi mujahid shi mujahid bazai iya cire Naira dari #100 ya biya kudin acaba ba.
.
Daga wajen da muke zuwa masallacin iedi tafiya ce ta kusan kilomita daya
Sukuwa yan acaba muddin tafiya ta kusan kai mil daya toh fa kudin da zaka biyasu bazaiyi kasa da #150 ba
.
Dan acaban farko daya tare wani dan sililine baki, yana sanye da jaket da kuma hula hana salla,
Dan acaba:- yauwa mallam tafiya ne
Mujahid:- (ya dan gyara tsayuwa) eh masallaci zaka kaimu
Dan acaba:- Na wa zaku bada
Mujahid:- Naira talatin 30
Dan acaba:- (ya burga wutan mashin ) mallam dan Allah kar ku bata mani lokaci. Ina da aikinyi, in zaka biya naira dari 100 toh in kuma bazaka biya ba inyi tafiyata
Mujahid:- maganar gaskiya mallam naira hamsin 50 garemu in zaka taimaka ka agaza ka kaimu a haka toh
Dan acaba:- (ya murda totur) yi hakuri yan samari ba taimako na fito yi ba, wai ace duk wannan wankan da kuka dauka kuce bakwada sisi inba hamsin ba ,mtssssssss( yayi tafiyarsa)
.
Mun tare yan acaba hudu kenan mujahid nace dasu naira hamsin gareshi, wani ma har kusan kaDan ya rage ya zabga mai mari, a yayin da wani kuma kadan ya rage ya damuko wuyan rigarsa.
.
Ni kuwa ina gefe ina kallon wannan diramar
Nasan mai karatu zaiyi tunanin mai yasa ni banje munyi ciniki da yan acaban ba
Toh hakan ya samo nasaba ne da rashin danshi danshi a aljihuna,
.
Maganar gaskiya ban tashi da sisi ba balle kobo
Toh tayaya mutumin da baya da sisi zaije suyi ciniki da dan acaba alhalin bani zan biya ba .
.
Amma maganar gaskiya nasan ba hamsin ce kadai ajikin mujahid ba , a zahirin gaskiya duk nisan tafiya mujahid ya fison yayita a kafa , maimakon ya cire kudi ya biya acaba yakaishi,
.
Kuma koda ma zai hau acaba toh kudin da zai biya baya wuce Naira 40
.
TO SHIN MAI KARATU
Da wani suna kenan zaka kira mujahid
Ni ma KUMA Shuraih DA wani Suna zaka kirani
.
Part 3
ARANAR SALLAH
Kagaggen Labari
Shuraih 99% & mijin biza
NA
Shuraih Usman
Part 3
.
,
Muna tsaye a bakin titin ne duk na kosa na gammu a masallacin eidi don ji nake tamkar da na rufe idanuwana na bude na zan ganni a masallaci ne
Na duba agogon dake hannuna naga ya nuna karfe tara da mintuna arbain da uku 9:43am
.
Sannan kuma shi wannan masallaci karfe goma daidai suke fara sallan eidi.
Nan da nan wata dabara ta fado mani na dubi mujahid nace mai
" Duk dan acaban daka sake tarewa kar ku tsaya ciniki, mu hau kawai kaga da mun isa masallaci sai mu mikamasa Naira hamsin din sannan mu bashi hakuri muce mai cikon hamsin dince ta fadi a hanya"
"Lallai ka kawo shawara mai kyau abokina shi yasa kake burgeni" yafada alokacin da ya ke bubbuga kafafuwansa a kasa.
.
Cikin sa'a kuwa sai ga wani dan acaba nan ya sulalo, in ka gansa zai tuna ma da irin kartin bosawan film din INDIA nan
,
Garjejen katone wanda na tabbata zai iya yin gammo ya daga babur din daya ke kai ya azata bisa kansa,
.
Sanye yake da farar jaket , bakine irin baki mai daukar idanu(shining) a saman kansa babu ko silin gashi a sakamakon wata kwalkwal daya sha(skin cut)
Kana kallon wannan kaga jan wuya , nan take na tsaida shi,
Koda na tsaidashi sai mujahid yazo dab dani yace
"Kai shuraih wannan katon basamuden katare, gaskiya ina jin tsoro, domin idan wannan ya fara hajijiya da ni toh Allah kadai yasan abinda zai biyo baya izan ya sakeni"
Duk da wannan zancen da mujahid yayi yaban dariya amma sai na matse nace mai
"Kar ka damu ai dabara zamuyi masa daga baya kuma saimu lallabashi mu bashi hakuri kaga shikenan " gyada kawai yayi alamar ya fahimta
Dan acaban na tsayawa nace mai "malam masallaci zaka kaimu"
Batare dana tsaya na saurari amsar da zai bani ba ,kawai sai na haye bayan mashin din,
Koda mujahid yaga na hawa shima sai ya haye.
.
Dan acaban dayaga mun zazzauna abayan mashin din sai ya tasheta ,murda totur yayi sannan yafara tafiya,
Acikin zuciyata kuwa sai tunanin irin badakalar da zata faru nake , don nasan wannan dan acaban bazai amshi naira hamsin ba , sannan kuma bazai tolerating wani cuku-cuku ba,
Nidai nasan duk rintsi duk wuya dan acabannan bazai amshi naira hamsin ba, hakanan duk rintsi duk wuya mujahid bazai iya biyan kudin acaba sama da naira hamsin ba don shi aganinsa ma a hakan ba karamin kwaransa dan acaban yayi ba
.

Ina cikin zancen zuci kenan sai mujahid ya ce dani lokacin daya miko mani wata yamitsatstsiyar naira hamsin
"Rike mani kudinnan bazan gyara zama"
Na karbi kudin a lokacin mun iso gangaran tudu
Kadab ya rage mu isa masallacin, dan acaba kuwa ko juyowa ba yayi bare ma yasan abin da ke faruwa.
.
Acikin raina na riga dana aiyana da naga mujahid da dan acaba sun fara hayaniya zan sabe na sulale nayi tafiyata .
Kaga na barshi da rikici kenan , don nasan muddin nayi gangancin tsayawa to kuwa wannan rana ta salla ba zata kasance RANAR SALLAH A gareni ba sai dai RANAR JINYA,
.
Burkin da dan acaban ya takane ya katse mani zancen zucin da nake na dan saurara wai ina jiran mujahid ya sauka , sannan nima na sauka , amma sai naji shiru har kusan second 20 ashirin
Hakan tasa na juya don nace mai ya sauka mana,
.
Kadan ya rage na saki fitsari asakamakon abun da idanuwata suka gane mani, Abin mamaki sannan kuma abin Al'ajabi
BABU MUJaHID BABU DALILINSA
In kadubi bayana yadda nabar wadataccen space sai ka rantse da Allah babu wanda ya taba zama a wajen.
.
Koda na sauko daga kan mashin din fuskata a tsorace ina tunanin ta yaya wannan basamuden dan acaban zai karbi naira hamsin,
Ni danake tunanin zanbar mujahid acikin cukuma ashe dai nine zan tatsiye a cikin cukuma
"Ya kai mallam sallameni mana. Nayi tafiyata "
Murgujejen muryansa mai kama da kukan jaki ya katse mani tunanina,
Na dubeshi da kyau ba karamin kato bane sannan A buguwa bazan iya dukansa ba , hakanan ko guduwa nace zanyi toh wannan sai ya karemani gudu ya kamoni daganan kuma basai na fada maku abin da zai biyo baya ba
.
.
TOH YA FRIENDS
INA MAFITA
.
www.Shuraih99.nextwapblog.com
ARANAR SALLAH
Kagaggen Labari
Shuraih 99% & mijin biza
NA
Shuraih Usman
Part 5
.
Doka:- ban hana copy ba , Amma duk wanda yacanja mani tsarin labari ko ya cire sunana ya saka nasa toh Allah ya isa.
.
Ba kowa nayi arba da shi ba illa mujahid .
Yana ganina ya fashe da dariya har yana buga kafa.
.
Sai da yayi mai isarsa sannan yayi shiru don kansa,
Tabe baki nayi sannan na jinjina kai nace mai
"Lallai ma mujahid wato ni za kaiwa haka"
.
"Yakake son nayi shuraih , ai tun farko na fada maka wannan mutum daka tare ba irinsa ake wa haka ba
.
"Yanzu dai mubar wannan zancen , ya'akayi har ka zame ka sauko daga mashin din ban sani ba" na tambayeshi
.
Yasake fashewa da dariya akaro na biyu,sannan ya dubeni cikin yanayi na shegantaka yace
"Adaidai wajen go slow(bumbs) na yan rake na sauka"
"Shine ko ka ankarar da ni"
.
"Ai dana ankarar da kai toh daka bata mani shiri, da yanzu muna hannun wancan basamuden dan acaban"
.
"Bamagujene, wallahi daya kamaka daka fada wa aya zakinta"
.
Cikin razana ya dubeni "wai kana nufin dan acaban can bamagujene"
"Kwarai kuwa don Da bakinsa ya fadi mani"
.
"Allah yasa dai bai rike fuskokinmu ba "
Yafada cikin kaduwa,
.
Wata harara na dalla masa sannan na dan hambareshi nace "kace dai Allah yasa bai rike fuskana ba, domin kuwa izan muka sake haduwa na tabbata wannan bamagujen ba imani ne gareshi ba, Allah kadai yasan abin da zai aikata agareni
.
"Wai ma ya kuka karike da shine" mujahid ya fada yayin daya dafa wata bishiya
.
Nan take na zayyane masa duk yadda mu kayi da shi, aikoda ya gama jin zancen sai ya tube babbar garensa sannan ya gyara tsayuwa ,
Dubana yai a tsanake sannan yace "lallai ko ba muga ta zama ba a waje daya"
.
"Maganarka dutse , don na tabbata izan yaji shiru -shiru dole ya shiga cikin lungunnan
Kaga kenan zai bulla adaidai bakin kofar masallacinnan kenan daya shigo kuwa toh anan zai cimmana "
Ina rufe baki kenan al'amarin ya afku, al'amarin daya tarwatsa dukkan wani bakin cikin dake tattare da ni
Sannan ya kore dukkan wani zullumi da tsoro daga zuciyata,
.
Wata kyakkyawar furece na hango farace ,amma ba fara tas ba, mai matsakaicin tsayi da matsakaicin jiki, ta mallaki kewayayyiyar fuska mai dauke da dara-daran haskakkun idanu,gami da yalwataccen gashi gira a samansu,
Dogon hancinta dake makale a saman madaidaicin bakinta ,shi ya taka muhimmiyar rawa wajen bayyana cikar kyawun surarta,
Tana da duk wasu halitta da ake bukata domin cikar halittar mace hakan yasa zuciyata ta rada mata suna kyakkyawar fure.
.
Dana kai dubana ga gefen da mujahid yake tsaye sai na tsinci kaina ina maijin wata wutar tarzomar haushin mujahid na ruruwa a kasan zuciyata,
Sakamakon yadda ya bude baki sai kallonta yake ayayin da ita kuma kyakkyar furen ta nufo wajen da muke tsaye.
.
Har ta kariso wajen idandunanmu akanta suke
Sallama ta rangada da zazzakar muryarta mai kam da sautin sarewa
.
A tare muka amsa sallamar
.
Toh a sannan ne nayi Gaba-gaba wato na kara kusanci da ita
Dubanta nai sannan nai karawa na gyara murya nace da ita
"Yake wannan kyakkyawar furen ma'abociyar haske mai kore dukkan wani duhu, shin wani abune ya faru "
.
Murmushi kawai tayi wanda ya kara fidda tsagwaron kyawunta tace dani
"Sunana ba kyakkyawar fure bace,sannan kuma ni ba wajenka Na zo ba wajen dan Uwanka na Nazo"ai tana gama fadin hakan tayi wuce warta izuwa wajenda mujahid yake tsaye
.
KAI KO MUJAHID
WAI FREINDS KU BANI SHAWARA
MAI YAKAMATA NA MAI NE DON
HUCE FUSHINA
Ammafa karku manta abokina ne banda shawarar da zata cutar da shi
Lolz
$
Warnin:- Ina fadi ina sake fadi, da kwai wasu da suke Editin mani post suna cire sunana sannan su saka nasu, wato ina nufin SATAR FASAHA
Ban hana copy ba amma ban yarda a canja mani tsarin labari ba
.
Hakkin mallaka (m) Shuraih Usman
Company:- Shuraih 99%
(c) shuraih Usman 2017
Typing:- shuraih 99%
ARANAR SALLAH
Kagaggen Labari
Shuraih 99% & mijin biza
NA
Shuraih Usman
Part 6
.
Doka:- ban hana copy ba , Amma duk wanda yacanja mani tsarin labari ko ya cire sunana ya saka nasa toh Allah ya isa.
.
Shi kuma mujahid koda yaji tace wajensa tazo sai ya gyara tsayuwa .tana isowa ta dubeshi fuskarta ba yabo ba fallasa tace
"Don Allah malam karfe nawa ne agogonka ya nuna."
"Goma saura minti shida"mujahid ya fada cikin wata irin salon karya murya .
Sai ayanzu ne na gane dalilin daya sanya wannan kyakkyawar furen tace ba wajena ta zo ba.
.A sabida bana da agogo
Yamutsa fuska tayi sannan tace "kenan saura mintuna shida a fara sallah"
.
"Kwairai kuwa gimbiya "mujahid ya fadi dauke da wta guntun murmushi akan fuskarsa,
"Suna na ba gimbiya bace sannan ni ba jinin sarauta bace" tafadi tana kallon cikin kwayan idanuwan mujahid yadda tayi maganar sai ka zanta cikin hassala ne.
"Duk da kin kasance ke ba jinin sarauta bace amma sunan yayi matukar dacewa Dake"
Na fadi yayin dana ke takowa izuwa wajen da suke .
Gani nayi muddin naja baki nayi shiru toh tabbas mujahid zai iya tsara kyakkyawan yarinyarnan. Hakan yasa nace INA.
.
Gaba dayansu suka juyo da dubansu izuwa kaina daga nan ne kyakkyawar yarinyar tayi murmushi sannan tace "toh naji sauri nake , nabarku lafiya "
.
"Amma yakamata gimbiyar ta sanar da mu sunanta ko don gaba "
Nafada alokacin danaga ta fara ja da baya zata tafi
Koda taji kalamina sai ta tsaya cak awajen da take
"Suna na kursiyya " ta fadi btare data juyo ta dubemu ba ,kafin na budi baki nace da ita wani abu tuni har tayi nisa
Tafiyarta keda wuya nazo wajen Aminina mujahid nace mai "kagani mujahid kaima kasan bama haka "
"Kamar yaya bama haka "yafada cikin nuna alamun rashin fahimtar maganata
"Ina nufin wannan yarinya kursiyya ni nafara ganinta kuma naga alamun kana so kayi mani halin ojibebe"
Nafada cikin marainiyar murya wai don yadan ji tausayina , dariya yayi yace" maganar kai ka fara ganinta duk bai taso b , kokari zakai ka samu soyayyata kafin..."
"Kana nufin ka janye ka bar mani"
Na katseshi da fadin haka
"Amma baka cikin hayyacinka bane ko, wannan santaleliyar yarinya, kyakkyawa son kowa kin wanda ya rasa kake cewa na barma ka tabdi jan
.
Toh in bakasan wani abu ba bazan fadama, ni da kursiyya mutu ka raba takalmin kaza," ya fadi cikin daddaga murya amma ba yadda kowa zaiji ba
.
"Da kyau ,hakama wato kace toh shikenan ,zamuyi wata gasa da kai"
Na fada cikin nuna alamun karfin guiwa
ya dubeni fuskarsa ba yabo ba fallatsa
.
Yace"wata gasa kenan"
.
"Gasar itace: Ni da kai duk wanda kursiyya ta furta mai tana sonsa , bawai shi ya furta mata cewa yana sonta ba, toh shine ya mallaki kursiyya"
Nafadi ina murmushi
.
"Ban gane zancen kannan ba"
"Ina nufin duk wanda kursiyya ta furta mai tana sonsa , bawai shi ya furta mata ba toh shine yayi nasarar mallakar kursiyya a matsayin budurwarsa, izan har ya kasance kursiyya ta furta cewa ni take so toh dolenka ka hakura da ita, izan kuma ya kasance kai ta furtawa kalmar so ma'ana tace tana sonka , toh anan take zan janye na hakura"
.
Koda mujahid ya gama sauraran bayanina sai yayi murmushin mugunta sannan yace"na amince da wannan gasar.
"Amma fa...."
"Amma me" ya katseni
"Da kwai sharadi guda a cikin wannan gasar"
Na fada da kakkausar murya
"Menene sharadin" yafada cikin zullumi
.
"Sharadin itace lallai wannan gasar ba zata wuce yau ba , ina nufin baza ta wuce wannan ranar ba"
"Kamar yaya bazata wuce yau ba" ya tabya
"Lallai dole kursiyya ta furta tana son wani acikin mu kafin safiyar gobe" na bashi amsa
.
"Toh amma idan kuma har gobe yayi ,bata zabi daya daga cikin mu bafa" yasake tambaya akaro na biyu
.
Naja dogon numfashi sannan na bashi amsa"in har gobe yayi kursiyya bata furta ma daya daga cikinmu cewa tana sonsa ba, toh hakan na nufin mun fadi,Loosers) Shikenan sai dukkanmu mu hakura da ita"
.
"Toh amma meyasa kace kafin safiyar gobe, ya tambaya wannan karon da dan guntun Damuwa akan fuskarsa
.
Wannan cakwakiyar soyayyar awannan rana ta RANAR SALLAH ta fara don haka A RANAR SALLAH zamu kawo karshenta
.
Toh FREINDS
.
Shuraih 99% ko Mujahid(mijin biza)
Comment with your actor
.
Warnin:- Ina fadi ina sake fadi, da kwai wasu da suke Editin mani post suna cire sunana sannan su saka nasu, wato ina nufin SATAR FASAHA
Ban hana copy ba amma ban yarda a canja mani tsarin labari ba
.
Hakkin mallaka (m) Shuraih Usman
Company:- Shuraih 99%
(c) shuraih Usman 2017
Typing:- shuraih 99%

.
ARANAR SALLAH
Kagaggen Labari
Shuraih 99% & mijin biza
NA
Shuraih Usman
Part 7
.
Doka:- ban hana copy ba , Amma duk wanda yacanja mani tsarin labari ko ya cire sunana ya saka nasa toh Allah ya isa.
.
.
Zaune nake a daya daga cikin kujerun da suke makure a cikin falon , centre table a gabana , dauke a samansa kular abincine , yayin da a gefe kuma talabijin ce ke ta faman aiki
.
Gabaya Daya hankalina baya tare Dani,
A wowi na hudu kenan da dawowa gida
acikin wayannan Awannin A bubuwa dayawa sun faru ciki kuwa harda sake gamuwarmu da kursiyya.
.
Al'amarin ya farune a masallacin iedi bayan an idar da sallah kowa ya fara kama gabansa , a lokacinne Ni kuma na fara Tunanin hanyar da zanyi na hadu da ita
Kwatsam kamar daga sama ganinta nai zata wuce ta gefena , nai mata sallama ta kuma amsa toh anan ne take sanar dani cewa ta hadu da dan'uwana wato mujahid sannan kuma harta bashi lambar wayarta da adireshinta.
.
Anan ne na fada mata sunana sannan ta sanar dani unguwar da take sannan ta bani lambarta a gaban idanun ta shiga mota sukai tafiyarsu.
.
Yanzu haka zaman danake a wannan falo babu tunanin da nake face tunanin yadda zan tsara wannan yarinya ta furta cewa tana sona ;
Nadai daure na bude kular dake gabana ,shinkafane dafa duka sai kifin da'aka marmasa akanshi.
Nan take na take wannan abincin ragowar daya rage baifi cikin cokali ba
.
Firji na bude na dauki ruwa mai sanyi nasha toh
Sai asannan ne na dawo hayyacina na duba agogo karfe ukune da minti ashirin 3:20
.
Ta shi nayi naje gidan su mujahid ban sameshi ba
Don haka sai nazaro wayata na matsa namba mai dauke da sunan MY LOVE TO BE
.
Ringing daya tayi aka daga wayar "assala'mu'alaikum wane ne" daga can bangaren aka bukata
"Wa'alaikissalam" na fadi
"Dan Allah dawa nake magana "ta sake fadi a karo na biyu
"Ai bai kamata ace kin manta wannan muryar ba"
"Hmm ko dai Shuraih ne "
Nayi dariya wanda nasan sai taji sautinsa sannan nace
"SHAKKA-BABU"
"Tuntuni nake tsumayar kiranka naji shiru , nace ko lafiya kake"tamkar yadda kike " na bata amsa
.
"Kai kasan yadda nake ne a yanzu"
.
"Tabbas kina cikin koshin lafiya " ta danyi wanda inso samune banki in kwana ina sauraron sautin dariyartarnan ba
.
"Yauwa ka shirya ina jiranka a Emir palace"
"Me kuma zamuyi a Emir palace"na tambaya na kara jan hirar tamu tai tsawo
.
Babu abin da zamuyi a wajen , da shike kasan ni bakuwace a garin naku, kuma naji labarin wai da salla akwai wuraren da suke wasan salla toh shi yasa nake son kadan zagaya dani wuraren don na kashe kwarkwartar idanuwa na"
.
"Kice yawon bude idanuwa zamu"
"Duk sunan daka kirashi da shi , sannan karka manta kazo da wuri don Allah,
.
"Karki damu in don ta nine ki bani minti goma kacal"
Nan na kashe wayar, cikin sauri ma fada bayi na wanke jikina ina fitowa na dau wata bakar zariyata na sanya sannan na dauki wata hula zannan bukar na buga na feshe ilahirin jikina da turare
.
Fita nayi bakin titi ,don tsare dan acaba toh a sannan ne na tuna ai bani da sisi bare kwabo acikin aljihuna.
.
Nan take gabana yabada ras ras ras matsalar gayu kenan NAIRA DA KWABO
.
Da gudu na shigo gida na zo wajen ummana nace mata ta bani rancen dubu biyu , ba musu ta bani.
.
Da fitowata bakin titi sai ji nai wayata ta dau ringing, alamar messages sun shigi, har zan share sai kuma wata zuciyar tace kafin ka share ya kamata ka duba ka gani
.
Ina bude wannan message din sai naci karo da abinda ya sanyani.......
.
YA SANYANI ME??
FARIN CIKI KO
BAKIN CIKI
Choose one
ARANAR SALLAH
Kagaggen Labari
Shuraih 99% & mijin biza
NA
Shuraih Usman
Part 8
.
Doka:- ban hana copy ba , Amma duk wanda yacanja mani tsarin labari ko ya cire sunana ya saka nasa toh Allah ya isa.

Ina bude wannan messega din sai naci karo da abinda ya sanya ni farin ciki
Bansan lokacin da na. Kurma wata dariyar farin ciki ba .
Alhamdulillah ,alhamdulillah, alhamdulillah na fada

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2

Please Login or Register in order to submit comment